Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'in "

Bud'e baki tayi zatayi magana yayi saurin tamke fuska yace

" kusameni a mota "

Dan yasan idan bahaka yayi mataba cewa zatayi abarta gida


Tagumi Hajiya Aysha tayi tana kallon tuwan masara da miyar d'anyar ku'baiwar dake gabanta wasu zafafan hawaye suka shiga gangaro mata saman fuska kallon ta inno tayi ta ta'be baki tace

" Hajiya sedefa ha'kuri mu haka muke rayuwa kuma cikin farinciki ni idanma kin rage tuwan kubani zan 'kara dan mundad'e bamuyi miyar ku'baiwaba kullum se kuka wai wallahi kinada sa'a Hajiya "

Tofa Hajiya Aysha tun yanzu kinfara kuka hmmm


Kuyi ha'kuri da wannan wayana babu caji sun'kin bamu wuta

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine plsss

Love u all sisters
[09/07 11:58 am] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE All SISTERS 🀝🏻😍🌹

Assalama alaikum all sisters ykk kuyi ha'kuri najina shiru kwana 2 banida lafiya ne sekuma akayimin rasuwa kaka ta 😭 Allah yaji'kanki darahama Allah yasa aljannace makoma Ameen

Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🀝🏻πŸ₯° all sisters love u

πŸ…Ώ { 47 to 48 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Wani irin kallon ba'kinciki Hajiya Aysha tayimata sannan tace

" nikam banga abinci a wannan tuwon da wannan miyar mai kamada anwanke kai dan haka zoki d'auka ke kebu'kata "

Murmushi tayi sannan tayi saurin d'aukar tuwon da miyar tace

" Alhamdulilah niko nike bu'kata Hajiya dama kinsan hausawa nacewa abincin wani gubar wani "

Daga haka tanufi dakinta tabar Hajiya Aysha datarin ba'kinciki tashi Hajiya Aysha tayi tad'akko mayafinta dasauran 'yan canjin hannun ta tafita tana fita tasamu napef tacemai yakaita Restaurant

Seeyama tariga Kausar isa parking space gaba tabud'e tashiga kallonta DON yayi yacigaba da latsa wayarshi babu jimawa Kausar ta'iso cikin takunta mai d'aukar hankalin DON ganin tabud'e baya zatashiga yasa DON cewa

" Hayateey ba'a wannan motar zamutafiba "

Daga haka yanufi d'ayar motar yashiga bin bayanshi tayi tashiga gaba tada motar yayi ganin bashida niyyar yimata magana yasa tafito daga d'ayar motar ranta babu dad'i tabud'e motar tashiga sukafita kallon Kausar yayi yace

" hayateey wane Restaurant zamuje ? "

Kafin tayi magana Seeyama tace

" haba baby ayni yakamata nayi magana akan haka tunda nice nace kakaini ba itaba "

Had'a fuska yayi sosai batare dayace komiba ganin haka yasa Kausar kallon fuskar shi cikin damuwa sannan tamaida idanunta kan yatsun hannun ta wani 'karamin restaurant yanufa ganin haka yasa Seeyama saurin cewa

" haba baby kamarka mutsaya a wannan 'karamin Restaurant d'in ? gaskiya banason wannan "

Ko sauraranta baiyiba yayi parking fitowa yayi itama Kausar tafito sukanufi ciki cikin sanyin jiki Seeyama tafito cikin zuciyar ta tace

" lalle dole nacanza taku hmmm zakazo hannune baby "

Sannan ta'idasa shiga ciki ganin DON yasa wasu daga ciki sukayi saurin mi'kewa nufar inda yake sukayi suna mi'kamai hannu bayan sungaisa da jama'ar gurin wasu dabasusan shiba suka shiga tambayar waye shi

" abokina waye wannan danaga kowa yanasonyin musabaha dashi haka gashi dagani babbane danko ba'asanar dakai ba kadan gidan kud'i ne "

Murmushi yayi sannan yace

" wannan shine DON Saban d'an kwangila mai ayki irinna margayi Alhaji Isma'il kuma babban jami'in tsaro namusamman daga Saudiyya "

Jinjina kai dayan yayi yace

" lalle shid'in namusammanne idan wanine yanaganin yanada irin wannan matsayin bazaizo cin abinci a wannan 'karamin restaurant d'inba kuma hadda matanshi "

Cikin sanyin jiki Hajiya Aysha dake zaune cannesa dakujerar su DON takasa cin abincin dake gabanta tajuyo bayan DON kawai tagani sabida shi yabama indatake baya Kausar tazubama idanu sannan takalli Seeyama tanajin fad'uwar gaba matsananci maida bubanta tayi kan abincin amma takasaci

Kowa yasa aka kawo mai irin abincin dayake bu'kata amma shi DON zaune kawai yake yana latsa wayar shi itama Kausar bawani abincin kirki takeciba itako Seeyama cin abincinta takeyi sosai cikin sanyin murya Kausar tace

" Sweety bakaci komiba ? "

Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba sannan yace

" amma kinsan bandad'e dayin breakfast ba ko ? kuma kinsan banacin abincin kowa senaki bari mukoma seki had'amin lunch idan zaki iya dan nasan jikinki babu karfi "

murmushi Kausar tasakar mai sannan tace

" maizai hanani iyawa Sweety banida farinciki senaka dole nad'auke maka dukkan wata matsala da damuwa "

Wani irin kallo yashiga yimata cikin zuciyar shi yace

" tabbas Hayateey kece macan da duk wani namiji yake nema zanbaki kulawa fiyeda yadda kike bani "

Jiyayi kamar yarungumeta take yaji tsananin bu'katar ta tataso mishi cikin ba'kin ciki Seeyama tasar'ke wani irin mugun tari tashigayi ganin haka yasa DON saurin mi'kewa amai Seeyama tafarayi sosai cikin rud'ewa Kausar tashiga taimakon ta tareda jama'ar gurin ganin yadda DON yanuna damuwa yasa Seeyama 'kara langwa'bewa

Bayan tarin yalafa tafarayin wani irin rawar sanyi baya tayi zatafad'i DON yayi saurin tarota cikin sauri ta 'kankamai shi sosai cikin wata irin murya tace

" baby please rungumeni sosai sanyi nikeji "

Sake rungume ta DON yayi sosai sannan ya kalli Kausar yace

" Hayateey d'auki wallet d'ina gatanan kibiya Kud'in duk wani wanda yaci abinci anan kisamemu a mota "

Daga haka yad'auki Seeyama cak yanufi mota da'ita nufo inda Kausar Hajiya Aysha tayi tace

" sannu 'yarnan gaskiya mijinku mai adalci ne kiyimai godiya ance yabiya makowa dakecikin Restaurant d'innan kud'in abinci kiyimai godiya idan babu damuwa kibani number ki madinga gaisawa "

Murmushi Kausar tayi tace

" haba Momy maizai hana ? "

Bata number tayi dawasu kud'i sannan tafita bud'e baya DON yayi ya kwantar da Seeyama yana 'kokarin fitowa Seeyama tayi saurin jawoshi jikinta cikin sexual voice tace

" Baby sanyi dan Allah karungumeni "

Jiyayi jikinshi ya'karayin sanyi cikin 'kasada murya yace

" towa zaiyi driving d'in ? "

Bakinta takawo setin kunnan shi tace

" Baby Kausar tayi please kaji babyn ka yajawo haka "

Jinjina kai yayi bai kawo komi cikin ranshiba sema tausayin ta adede lokacin Kausar ta'iso ganin yanayin dasuke yasata saurin d'auke kai bud'e motar tayi tashiga ahankali DON yakira sunanta yace

" Hayateey kijamu muje Hospital sabida tanajin sanyi matsananci "

Cikin sauri Seeyama tace

" a'a Baby muje gida kasa Umma takira doctor banason ganin cikin hospital "

Jinjina kai yayi sannan yaciro wayar shi yasanar da Umma ahankali Kausar ta tada motar hannu Hajiya Aysha tad'aga musu tanason ganin DON amma sede tahangi rigarshi sabida yayima Seeyama rumfa da 'kirjinshi itakuma tarungume shi sosai tana fad'in

" waiy Allah Baby sanyi "

'Karashiga cikin kirjin shi tayi karatun Qur'ani Kausar takunna cikin motar sabida kautar da hankalin ta akan su ahaka har suka isa gida Kausar nayin parking tayi sairin fitowa daga motar bud'e musu murfin motar tayi a rungume yafito da'ita yanufi ciki itama Kausar binbayansu tayi har cikin parlour Seeyama

Cikin sauri Umma tanufosu tana fad'in subahananlahi Seeyama sannu kwantar da'ita DON yayi saman cushion ru'ko hannun shi tayi tace

" baby kazauna kusadani karkayi nisa dani "

'Dan tamke fuska yayi sannan yace

" kibari doctor tadubaki mana "

Komawa yayi yazauna kan d'aya daga cikin cushion d'in parlour sannu Kausar takumayimata sannan tanufi gurin DON tace

" Hayateey barinaje nawatsa ruwa sena d'aura maka lunch d'in "

Girgiza mata kai yayi sannan yace

" zauna kibari sezuwa anjima "

Zama tayi kamar yadda yace gaisawa sukayi da doctor wadda tunkafin su'iso take jiransu tashi tayi tafara dubata tsayin lokaci sannan tace

" Am DON gaskiya Seeyama tana bu'katar kulawarka sosai sannan daga yau karka sake barin Seeyama takwana itakad'e harna tsawon 3 months sannan kadinga kusantar ta sabida samun kujarin babyn dan yana bu'katar kulawarka sosai "

Tamke fuska DON yayi sosai yace

" 3 months fakikace doctor ? amma aykinsan ba ita kad'e bace agurina taya zantare agurinta harna tsawon 3 months bazai yiyuwa "

Cikin kukan kiss Seeyama tace

" doctor gaskiya yafad'a kinga bani kad'ai bace karnashiga hak'kin yar uwa ta "

Jinjina kai doctor tayi sannan tace

" toko gaskiya idan har ba'abi wannan tsarin ba to babu tabbacin wannan cikin zai zauna kum ,,,,,,, "

Muryar Kausar takatse ma doctor maganar datakeyi

" Sweety babu komi idan har tanine nayafe kagama Skul zankoma kuma muna komawa zamufara Exam Sweety nayarda kabama babyn mu kulawar data dace zanyi farinciki 3 months ay kamar 3 days ne a wannan lokacin Seeyama Allah yabaki lfy "

Murmushi Hajiya Saratu tayi tace

" Allah sarki 'yata Kausar gaskiya kinada kyakkyawar zuciya hakanikeso naga kunhad'a kanku Allah yamiki albarka "

Tashi DON yayi yafita rai 'bace batare dayace komiba itama Kausar d'in tashi tayi tabi bayan shi part d'in shi yanufa kai tsaye yana shiga yanufi cikin bedroom d'in shi kwanciya yayi kan bed yana kallon sama jiki a sanyaye Kausar tashigo Cikin bedroom d'in kusadashi tazauna hannun shi takamo tasaka cikin nata cikin taushin murya tace

" haba Sweety maiye nafushi d'a yawuce wasa Sweety 3 months kamar yaune zatazo dan Allah kabata kulawa kamar yadda doctor tace "

Cikin zafin rai yatashi zaune had'ida fizge hannun shi cikin kakkausar murya yace

" a she ba sona kikeyiba abakine kawai tunda har zaki'iya ha'kura dani harna tsawon 3 months Hayateey to bari kiji zankoma wajan Seeyama harna tsawon 3 months d'in tunda kinyarda dahaka bazan sake shiga bedroom d'in kiba kema karki sake shigowa nawa harna tsawon lokacin zanhad'a kulawar dazan baki da tata duka tabbas zankula da baby kamar yadda kike so tunda ke bakishirya bani naki babyn ba karkiji haushin duk abinda zakigani "

Daga haka yatashi yafita daga bedroom d'in gaba d'aya cikin sauri Ayna 'kanwar jabir tabar cikin part d'in tana murmushi tana shiga tasanar ma Hajiya Saratu abinda taji yawakana tsakanin DON da Kausar

Dariya Umma da Seeyama suka saki harda doctor Umma tace

" yanzu game d'in zaifara "

Cikin damuwa Kausar tanufi part d'in ta cikin zuciyar ta tace

" zakagane sonkane yasa nayi haka Sweety "


Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please
[10/07 1:39 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE All SISTERS 🀝🏻😍🌹

Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🀝🏻πŸ₯° all sisters love u

πŸ…Ώ { 49 to 50 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Fitama DON yayi daga gidan gabaki d'aya zuciyar shi duk babu dad'i cikin rashin kujari Kausar tashiga kitchen dan had'ama Sweetyn ta launch

Cikin nishad'i Abdulhakim yake driving cikin sabuwar motar da DON yabashi kai tsaye gidansu yanufa dan yayi kewar Momy shi sosai duk da cewa bayason halinta amma akwai soyayyar d'ah da uwa matsananciya a zuciyar shi

Kimanin mintuna 10 Abdulhakim yanayin hon amma babu alamar za'a bud'emai get ganin haka yafito daga motar nufar 'kofar shiga yayi kai tsaye yakoci sa'a abud'e yake murmushi yayi yanufi gurin maigadi yanafad'in

" baba yau kuma bacci kakeyi nazata duk jin radio ne ? "

Sedayakai 'karshen maganar sannan yalura ba maigadin dayasanibane cikin mamaki yace

" sannu baba "

wani irin kallo yayi mai sannan yace

" lafiya ? "

Cikin mamaki yace

" dama naga inatayin hon ne amma shiru Allah yasade Momy tana ciki ? "

Tashi maigadi yayi tsaye cikin fad'a yace

" kai d'in waye ? tokayi gaggawar fita karkajamin narasa aykina "

Mamaki sosai Abdulhakim yayi yace

" nasan bakasanniba d'an gidan Hajiya Aysha ne Abdulhakim kasanar da ita "

Cikin tsawa maigadi yace

" kaga yaro maza kafita anan gidan babu wata Hajiya Aysha tun kwanaki sukabar wannan gidan Alhaji Sambo yasiyarma Alhaji yunus wannan gidan dan haka kaje kanemi mahaifiyar ka "

Cikin gigita Abdulhakim yace

" kana nufin ba mahaifiyata a cikin gidan nan yanzu ? dan Allah kasanar dani inda Momy na take "

Juyawa ma maigadin yayi seda yakai ba'kin 'kofar d'akin shi sannan yace

" kaita tsayuwa daganan har lokacin dazaka gaji kabar gidan idan kuma mai gidan yadawo yayi maganinka "

Daga haka ya'idasa shiga cikin d'akin shi cikin gigita Abdulhakim yake kallon gidan gyuwar shi asanyaye yafita cikin motar shi yashiga tsayin lokaci yamakasa tunanin komi zuwacan yayima motar shi key yafigeta aguje driving yakeyi amma baisan inda yanufaba sede jiyayi gauuuuuu yamake mutun cikin sauri da firgita yaja birki yafito agigice

Ganin wadda yamake kwance babuko motsi yasashi saurin d'aukar ta yasata a mota taredawani mai siyar da kayan fruit abakin hanya hospital suka nufa duk da yadda suka ganta cikin jini amma sun'kin amsarta sesun kira police sabida bin dokar ayki

Kiran wayar DON Abdulhakim yayi yana d'agawa yasaki kuka jin kukan Abdulhakim yasa DON saurin tambayar lafiya sanar dashi komi yayi babu jimawa da kiran wayar DON ya'isa cikin hospital d'in

Tareda security ganin DON yasa akayi saurin shigada yarinyar doctors sukafara dubata cikin gaggawa tsayin lokaci sannan akafito da ita wani room d'in aka kaita sannan doctor yabu'kaci ganin DON da Abdulhakim bayani yafarayi musu kamar haka

" ranka shidad'e Allah yasa abinyazo dasu'ki amma tasamu buguwa akanta ayanzu bazata iya tuna komiba harna tsawon 5 days ko 7 days in sha Allah zatadawo cikin hankalin ta "

Jinjina kai DON yayi sannan yace

" idan kuma batadawo cikin hankalin natabafa ? "

Kallon shi Doctor yayi yace

" in sha Allah zatawo idan kuma batadawoba sede afita da ita waje "

Jinjina kai DON yayi sannan yace zamu iya shiga muganta ?

Tashi doctor yayi yamusu jagora har d'akin cikin mamaki DON yace

" Ameera"

Daga haka yajuya yafita cikin mamaki Abdulhakim yabi bayanshi cikin fargaba da tsoro dan yadda yaga yayi matu'kar tamke fuska Abdulhakim yace

" brother kasantane ? "

Kamar bazaice mai komiba zuwacan yace

" katsaya agurin ta zanturo iyayanta zuwa anjima "

Yana 'karashe fad'ar haka yayi gaba bin shi Abdulhakim yayi da kallon haryafita komawa ciki Abdulhakim yayi kallon Ameera yashigayi yakasa d'auke idan shi akan ta afili yace

" a'a Abdulhakim har yanzu kai yarone karka saka damuwa cikin rayuwar maiyasa zanji haka akan wadda nasan ta girmaini ? a 'a tausayi ne kawai "

Zama yayi yana addu'ar Allah yasa tafarka cikin hankalin ta kai tsaye gida DON yanufi hangen wasu ma'aykatan gidan yayi daga cikin lambun gidan ji yayi bai yarda dasuba kashe motar yayi yana kallon su batare dayafitoba hangen d'ayan yayi yad'aga waya yana magana dagani tanada mihimmancin sosai jinjina kai DON yayi sannan yabud'e murfin mota yafito yanufi ciki

Part d'in Seeyama yanufa zaune yasame ta tana shan fruit kallon ta yayi yazauna batare dayace mata komiba wayar shi yaciro yakira wani dagacikin ama'aykatan gurin aykinshi sawa yayi sudubamai Address d'in mahaifin Ameera da number shi

Cikin kissa Seeyama tami'ke zama tayi kusadashi wani irin kallo tayimai cikin shagwa'ba tace

" baby sannu da dawowa "

Amsawa yayi batare daya kalletaba ganin haka tayi murmushi kwanciya tayi tad'aura kanta akan cinyar shi tana fad'in

" baby jikina babu 'karfi please ka taimaka min nayi wanka "

Tamke fuska yayi sosai yabud'e baki zaiyi magana wayar shi tafara ruri ganin sunan Hayateey yasashi jin sanyin cikin ranshi amma dayatuna abindaya faru d'azu seya kuma tamke fuskar shi sosai

'Daga wayar yayi zuwacan yace

" ina part d'in dear ki kawomin nan "

Yana gamafad'in haka yakashe kiran Wani irin muguwar fad'uwar gaba Kausar taji cikin zuciyar ta tace

" anya banyi kuskure bakuwa ? "

Saurin shre zancan tayi tasa tabawa taimaka mata wajan d'aukar kayan abincin suka nufi part d'in Seeyama bakinta da sallama suka shiga ciki ganin yadda Seeyama ke kwance saman cinyar shi yasa Kausar saurin kauda kai ganin haka DON yace

" dear tashi muje nabama babyna abinci semuje na taimaka miki kiyi wanka "

Cikin sauri Kausar ta'aje tiran hannun ta tajuya cikin muryar shi mai d'aukar hankali yace

" haba Hayateey zo kiyi saving d'ina mana kinga ita bazata iyaba sabida jikin ta babu 'karfi kema kitayani kulada babyn "

Jiki a sanyaye Kausar tajuyo wani irin dad'i da sanyi Seeyama taji cikin ranta shiko DON cikin zuciyar shi yace

" haba Hayateey ay tunda kibada goyan baya wajan wannan lamarin to sede muzauna adamuwa nidake badai ni kad'ai ba senasa kingane kinyi kuskure "

Cikin sanyin jiki Kausar tazuba mai sannan tami'ke kallon Seeyama yayi yace

" dear babyn zaici abincin kuwa ? "

'Daga mishi kai tayi tanamai fari da ido hannu yasa yashafi cikin ta yace

" Hayateey zubama babyn mu abinci "

Wani irin duhu Kausar tafara gani tana gama zubawa tami'ke har takai bakin 'kofa yace

" Hayateey kizo muyi launch d'in tare mana "

Cikin 'karfin hali murya a sanyaye tace

" se zuwa anjima Sweety "

Cikin sauri tafita kallon hanyar datafita yayi yanajin wani iri cikin ranshi Kausar tashiga cikin parlour ta tazibe kan cushion tamarasa wane irin tunani zatayi Cikin tausayawa tabawa tace

" ki danne zuciyar ki 'yata tunda naga wa'innan mutanan nasan sunada wani shiri kede kidage da addu'a kuma kiyima mijin ki sannan karki sake kinuna musu kindamu kinji kede kiyima mijinki addu'a "

Sosai Kausar taji dad'in maganar tabawa cikin ranta tace

" shiri kuma to Allah yatsaremu "

Tashi tayi tashiga cikin bedroom ganin haske cikin wayar ta yasata saurin d'auka cikin farin ciki tace

" Amina ykk wallahi dama akwai magana fa kin rikitamin zuciyar yaya Ashiraf dan Allah karki kashe min yayana "

Dariya tasaki dajin amsar Amina sundad'e suna waya sannan sukayi sallama toilet Kausar tashiga amma takasa manta maganganun DON da yadda tagansu yanzu

Tamke fuska DON yayi yace

" kisamu damar d'agani "

Cikin mamaki Seeyama tayi saurin kallon shi d'an d'akin fuskar shi yayi cikin zuciyar shi yace

" dole nasan yadda zanbi dake Seeyama banaso kigane hukunci nakeyima Hayateey na banason kirainata "

A d'an da'kile yace

" muje muci abincin ko babyn bayajin yunwane ? "

Sauke ajiyar zuciya Seeyama tayi sannan tasaki murmushi tami'ke suka nufi dining 'karar shigowar text cikin wayar shi yasashi ajiye spoon kiran number baban Seeyama yayi yasanar dashi abinda yafaru da Asibitin sannan yakashe wayar

Sosai yaci abincin dan yana matu'kar son girkin Kausar ganin yagama yasa Seeyama kiran mai ayki tace ta gyara gurin idan tagama taje tahad'ama DON ruwan wanka cikin zafin rai DON yace

" ni ? zakice wata tahad'amin ruwa to bari kiji idan har wata ke gyara bedroom d'in ki to bazan ta'ba kwana cikin shiba danni ba shasha shan namiji bane "

Daga haka yafita daga part d'in gaba d'aya ganin fitowar shi yasa Hajiya Saratu saurin cema wani matashin saurayi cikin ma aykatan gidan

" yi sauri kaje kafin yawuce part d'in Kausar kuma kayi yadda nace idan har komi yatafi dede zan 'karamaka kud'i "

Cikin sauri yanufi hanyar shiga part d'in Kausar har DON yagota ganin wannan yaron yasashi dawowa cikin a fad'ace yace

" lafiya mai zakajeyi cikin part d'in matata ? bayan kasan dokace "

Cikin tsoro yafara magana dan shikam a tsorace yake

" dama Hajiya ce ta'aykeni nasiyomata magani "

" magani ? "

DON yasake maimaita kalmar

" wane irin magani ? "

" Alhaji nima bansani ba rubutamin tayi kuma tace karna bari kowa yagani "

Cikin zafin rai DON ya amshi ledar maganin azafafe yace mai " bar gurin nan karnasake ganinka anan "

Shiga cikin part d'in shi yayi yana juya ledar maganin cikin ranshi yana mamaki wanka yashiga yana fitowa yashirya cikin 'kananun kaya yad'auki ledar maganin yafita cikin ranshi yace

" duk abinda ba'ason wani yagani to tabbas wani munafurci ne amma zangani "

Hospital d'in yakoma sabida wannan maganin kawai dan da baiyi niyyar sake komawa ba yana shiga yanufi Office d'in Doctor bayan sun gaisa ya'karajin yadda jikin Ameera yake sannan yami'ka ma doctor wannan magungunan yace

" doctor dan Allah dubamin wannan maganin maiye agurin matata nagani "

Bud'e ledar doctor yayi sannan yashiga duba maganin cikin mamaki doctor yace

" am yalla'bai yaranka nawa ? "

mamaki DON yayi sosai dajin wannan maganar seda yanufasa sannan yace

" babu ko 1 "

Sake kallon shi doctor sannan yasake cewa

" to maiyasa bakason haihuwa bakasan yara sanyin idanu bane ? karkayi kuskure Allah yabaka dukiya karka bari tatafi abanza kahaifi yara suci moriyar ta kamar yadda kaima zakaci moriyar ta mahaifin ka k...... "

Dakatar dashi DON yayi yace

" doctor ba jawabi nike nemaba ? tambayar ka nayi "

Cikin rashin damuwa doctor yace

" wannan maganin hana daukar cikine idanma akwai shi zaifita inde 'karamine shi......... "

Amsar maganin DON yayi yafita afusace yana fitowa yaci jaro da mahaifin Ameera da Abdulhakim ' ko'karin seta kanshi yayi suka gaisa da mahaifin Ameera

" nagode sosai DON doctor yacemin kad'auki nauyin komi Allah yasa da alkairi "

Fuskar shi babu walwala yace

" basai kayimin godiya ba brother na yayi sanadin komi yazama hak'ki akaina nakula da komi Abdulhakim kazo gida yanzu kadawo anjima "

Cikin damuwa Abdulhakim yace

" baze yiyu natafiba brother Ameera tafarka kafin Abba yazo ni kad'e tayarda dashi zantafi tasaka kuka koda su Abba sukazo ta'ki kulasu har Ummi shine doctor yace tunda tafara ganina bazata ta'ba yarda dakowaba seni sede idan ta warke yanzuma bacci takoma shiyasa nafito "

Jinjina kai DON yayi sannan yace

" tunda tayi baccin kaje gida kayi wanka sekadawo "

Daga haka DON yafita zuciyar cike da 'bacin rai shiga mota yayi yayi shiru afili yace

" wato Kausar baki shirya haihuwa daniba kenan ? dama kince bayanzuba sabida Skul d'inki ko shine zakici amanata hmmmm lalle zanbaki mamaki "

Ganin shi cikin mota yayi shiru yasa Abdulhakim daya fito saurin isa gurin shi cikin damuwa yashiga tambayar shi amma babu amsa zuwacan cikin fad'a yace mai

" karabu dani Abdul Aunty ka taci amanata dan tasan inason ganin jinina a jikinta shine tafara amfani da maganin hana haihuwa shiyasa tayi saurin yarda danazauna a 'bangaran Seeyama harna tsawon 3 months haba Hayateey dan kinga zuciya ta dake kad'ai ta aminta shine zakimin haka "

Cikin tashin hankali Abdulhakim yace

" kayi ha'kuri brother amma dan Allah kayi bincike Aunty na bazatayi hakaba brother ay akwai CCTV camera kaduba 'kila kaga gaskiya dan Allah brother "

Cikin tsawa DON yace

" babu abindazan duba Abdul wannan gaskiya ne sabida tafad'i haka amma banyi zaton zatayi hakaba bazan sake bitakan CCTV camera dake gidan ba se 'bangaran part d'ina da sauran gurin ma'aykatan gidan amma bazan sakeyin bincike a 'bangaran Kausar da Seeyama ba dan idan nace zanyi haka wata rana se zuciyata tabuga tunda Kausar tayi haka

Please Login or Register in order to submit comment