Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su sosai DON yaji mutuwar Seeyama Kausar kam seda taga DON yana niyyar yimata kuka sannan tadena kuka

Washe garin mutuwar Seeyama Alhaji Umar ya iso Nigeria hankalin shi amatu'kar tashe sosai yaji tashin hankalin mutuwar Seeyama cikin kuka Ammi tace

" Alhaji dan Allah kayafemin nice nayi sanad'in mutuwar Seeyama sabida son zuciya da son abinduniya gashi ita Kausar d'in tana raye amma ita Seeyama tatafi nashiga uku "


Rai 'bace Alhaji Umar yami'ke yace

" nagodema Allah dayanunamuku iyakarku yanzu gashi kin rasa 'yarki kema Saratu kin rasa d'anki sedananuna banason zamanku a gidan Seeyama amma kuka 'kiji don haka bazan iya cigaba dazama dakeba nasakeki saki 3 sannan ayau nikeson kubar wannan gidan duk indama zakuje kutafi amma ba gidan Affan ba kai Affan kayi ha'kuri ha'ki'ka sun cutar da kai amma kabarsu da ubangijinsu shine zebima Jabir da Seeyama hak'kin su akansu ko yanzu sunga ikon Allah kema Kausar kiyi ha'kuri Allah yanatare da mai gaskiya "

Sosai Ammi da Umma ke ro'kon Alhaji Umar amma yace wallahi sesun bar gidan cikin damuwa da 'bacin rai DON yami'ke yace

" basai anbaku kud'in jirgiba Umma wannan kud'in dakika d'auka cikin bedroom d'ina kuyi amfani dashi "

Daga haka yanufi cikin bedroom d'in shi itama Kausar tashi tayi jinjina kai Alhaji Umar yayi yace

" ikon Allah duk wannan abun har yake maganar kud'in jirginku gaskiya Affan Allah yabaka zuciya irinta mahaifin ka su Ammi da Umma sunaji suna gani sukabar Nigeria zuciyoyinsu cikeda ba'kinciki Sosai Ayman yayi nadama amma Alhaji Umar ya'ki sauraran shi seda Momy tasa baki sannan yace yayafe mishi amma kodawasa karya kuskura yayi wani abun da ba daidai ba

Zama DON yayi bakin bed yana tuna maganar Seeyama ranar dazata mutu wasu irin hawaye suka gangaro daga cikin idanun shi hannu Kausar tasa tashiga goge mishi tanayi tana lallashin shi har seda taga yasamu sassaucin damuwar

Bayan kwanaki 7 Alhaji Umar da Ayman suka koma Sudan sosai Kausar take tarairayar DON dan batason ganin shi cikin damuwa bayan watanni 5 cikin Kausar yashiga watan haihuwa sosai takesamu kulawa wajan DON shiko Abdulhakim har yanzu Ameera takasa shawo kanshi ko Skul yahanata zuwa tanason sanar da DON amma takasa ga cikin jikin ta yatsufa sosai take shan wahala

Don yaninkama wanda yase gidan su kud'i ayanzu haka Momy takoma cikin gidan dan tace bazata iyazama cikin gidan DON ba batasan takura su

Don yashirya musu tafiya Saudiyya shida Kausar dan yafison tahaihu acan da 'kar Momy ta yarda ganin cikin yashiga watan haihuwa lallashin ta DON yaitayi yasanar da ita yawan hutun daya d'auka sabida tafiyar 2 weeks da zuwansu Saudiyya

Safiyar ranar litini Kausar tatashi da ciwon na'kuda sosai Don yarikice cikin gaggawa aka nufi Asibiti da ita

Kuyi ha'kuri da wannan

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters 😘πŸ₯°
[22/07 5:36 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌸 NOORUL HAYAT 🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels writers 🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans 🀝🏻πŸ₯°

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT
2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
typing...... ✍🏻

HAYATUL MAHAYAT
Coming soon
After RUFAFFIYAR ZUCIYA in sha Allah

πŸ…Ώ { 67 to 68 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Koda aka shigada Kausar DON shima 'ko'karin shiga yayi amma suka dakatar dashi dole yaha'kura amma ko zama yakasa se kai komo yakeyi bakin room d'in kimanin 4 hours amma shiru sosai hankalin DON yayi matu'kar tashi

Fitowar wata doctor yayi saurin biyota yana tambayar ta halinda Kausar keciki girgiza mishi kai tayi tayi gaba ganin haka yasa DON binta cikin sauri shan gabanta yayi fuskar shi atamke yace

" doctor bangane mai kike nufiba ? taya natambayeki halinda matata takeciki amma kinyimin shiru "

Ajiyar zuciya tasauke sannan tace

" kayi ha'kuri in sha Allah matarka zata haihu lafiya kasancewar ba baby d'aya bane a cikin ta shiyasa karka damu in sha Allah zuwanan da 2 hours zata haihu "

Daga haka tayi gaba cikin sauri komawa bakin room d'in DON yayi yana kallon 'kofar yanajin wani irin matsanancin tausayin Kausar ga farincikin ji dayayi nacewa Kausar ba baby d'aya zata haifamai ba

Awannin da doctor tace suka wuce amma shiru babu labarin haihuwa cikin room DON yasakai suna dakatar dashi amma ina 'ko sauraran su baiyiba yanufi inda Kausar take ganin irin halindatakeciki yasa DON jin wata irin fad'uwar gaba zuwa yayi yari'ke hannun ta cikin raunanniyar murya DON yace

" Hayateey ki dauke in sha Allah zaki haihu lafiya "

Girgiza kai doctor yayi yace

" a gaskiya sede kasa hannu ayi mata ayki dan zaiyi wuya ta'iya haihuwa dakanta sabida tasha wahala sosai "

Kallon fuskarta DON yayi ganin bata sakar mai murmushi ba yasa DON saurin cema doctor babu matsala zansa hannu nide burina matata rayu koda zan rasa babys d'in "

Shirin shiga aykin akashigayi DON yana office d'in doctor wajan saka hannu cikin sauri wata doctor tashigo kai tsaye tacema doctor

" doctor kan baby yafara fitowa "

Tashi doctor yayi suka fita tare room d'in suka koma shima DON binsu yayi ganin doctor yanufi wajan Kausar kai tsaye yasa DON saurin ri'ke hannun shi rai'bace yace

" kabar mace ta amshi haihuwar amma bazan iya kallon namiji akan matata ba "

Ganin babu alamun wasa yasa doctor basu umarni yaja hannun DON suka fito sosai Kausar tasha wahala dan seda tacire rai da rayuwa bayan 2 hours misalin 06:00 pm Kausar ta sunbulo kyawawan yaranta guda 4 biyu maza biyu mata ganin yadda DON yarikice yasa suka'ki danar dashi seda suka kintsa babys sannan wata daga cikin su tafita fuskarta d'auke da murmushi tace

" Congratulation matarka tahaihu da kanta kuma lafiya ta haifi yara 4 "

Zaro idanu DON yayi yamarasa mai zece tsayuwar 2 minutes yayi kamar ya'kame sannan yaruga aguje har yana bangaje doctor yana shiga aka nunamai kyawawan yaran shi masu 'koshin lafiya ita kuwa Kausar baccin gajiya takeyi sabida anyi mata allura dan tasamu ishesshan bacci rasama wazaifara d'auka cikin yaran yayi

Haka yad'inga d'aukar su yana ajewa yad'auki wannan ya'aje ya d'auki wannan ya'aje cikin tsananin farin ciki gabas yakalla yayi sujuda yanamai nuna tsananin godiya ga Allah tashi yayi yafara yimusu picture ba'iyaka kiran wayar momy yayi cikin farin ciki yake sanar da'ita haihuwar

Bakin Momy kasa rufuwa yayi sabida tsananin farinciki bayan kiran Momy yakira barrister yasanar dashi shima farinciki da murna wajansu ba'a magana shiko Abdulhakim yanaji yafara had'a kaya shiwai adelo jirgin dare zaibi dan yamatsu yagano babys

Seda 'kyar Momy tashawo kanshi akan yabari zuwa safe sutafi tare harda matar shi akan dole taha'kura dan babu yadda zaiyi

Ahankali Kausar take bud'e idanun ta saukesu tayi kan babys d'in tanajin wani irin farinciki cikin zuciyar ta aje babyn hannun shi DON yayi yakamo hannu Kausar yasumbaceshi yanajin wani irin yanayi cikin zuciyar shi kallon cikin idanun ta yayi yace

" Hayateey ha'ki'ka kinbani farinciki marar misali babys 4 alokaci d'aya Allahu Akbar Allah mai yanda yaso shine kika 'kisanar dani ba baby d'aya bane a wannan cikin naki ko ? ashe shiyasa girman cikin yake tsoratani "

Murmushi Kausar tayi cikin rashin 'kwarin jiki ta kwanta tad'aura kanta akan cinyar shi muryarta a sanyaye tace

" naji tsoro lokacin da 'akace ba baby d'aya bane cikin cikina amma sede nima bansan sunkai 4 ba na'ki sanar dakaine sabida inason kaji farinciki marar misali a irin wannan ranar "

Wani irin murmushi DON yake saki namusamman shafa kanta yashigayi haka suka kwana cikin Asibitin zuciyar kowa cikeda farinciki washe gari misalin 9 su momy suka isa Saudiyya babu jimawa su barrister suka iso sosai sukayi farin ciki

Zuwa yamma akabasu sallama dan antabbatar lafiyar Kausar 'kalau itada babys d'inta DON babu kunya yake 'kwa'kubai yaranshi ko kunyar ganin su Momy bayayi haka akaita shagalin murnar zuwan wa'innan babys d'in tundaga wannan ranar sosai DON yake facaka da kud'i kamar baisan ciwonsuba yayi gayyar abokai sosai kowa yaji DON yana gayyatar shi se yayi mamaki sabida ada bayakulakowa saukar Qur'ani yasa akaitayi sabida zuwan babys akan Allah ya albarkaci rayuwar su

Ranar suna yara sunci sunaye kamar haka

Isma'il da Ibrahim Aysha da Seeyama Isma'il Sayyit Ibrahim Haneef Aysha Noor Seeyama baby masha Allah yarayasu

Bayan 2 weeks su barrister zasu koma Nigeria mom tayi maganar tafiya da Kausar kai tsaye DON ko kunya babu yace shikam bazai iya rabuwa da Kausar da babys d'in shiba koda na kwana d'aya ne haka dole suka ha'kura itako Momy cewa tayi ay babu inda zata zama daram shiko Abdulhakim dole yakoma sabida Skul amma Momy tahanashi komawa da Ameera danta fuskanci babu wata jituwa a tsakanin su tasha alwashin seya ro'keta akan yanaso Ameera tadawo tayi kudirin koda sun koma Nigeria agunta Ameera zata zauna harya haihuwa idan bai nemi takomabama harta yaye

Bayan wata 2 yara sunyi wayo amma DON baya maganar komawa Nigeria ganin haka yasa Momy yimai magana amma yace mata bayanzuba wasawasa lokaci setafiya yakeyi har Ameera ta haihuwa tahaifi namiji sosai sukayi farincikin zuwan babyn amma Abdulhakim bai zoba har seda akayi kwana 2 sannan yazo yasama d'an sunan brother shi wato Affan anayin suna yadawo Nigeria hakan yasa Ameera cikin ba'kin ciki sosai nunama Momy tayi tanason komawa Nigeria ha'kuri Momy tabata akan tabari zuwanan da wasu kwanaki

Seda Ameera tayi wata 1 da haihuwa sannan suka dawo Nigeria amma banda su DON koda suka dawo Nigeria Abdulhakim baya shiga harkar Ameera koda tana cikin bedroom d'in Momy idan yashiga d'anshi yake d'akkowa yafito sabida yana matu'kar son yaron wasawasa yau 1 year kenan da haihuwar Kausar amma DON babu maganar komawa Nigeria yama cigaba da aykinshi acan

Shiko Abdulhakim rashin Ameera yafara takura shi amma girman kai yahanashi nunawa itama Momy tahana Ameera takoma gidan shi amma tasa dole yabarta takoma Skul sosai Ameera takejin zafin abinda Abdulhakim yayi mata musamman idan tashiga Skul taga babu abokan karatun ta sena 'kasadasu ayanzu dasu take jerawa su Kausar dasu Amina da sauran 'kawayen ta duk sun tsere mata

Kwance Abdulhakim yake saman bed yakasa koda rintsawa sabida wata azababbiyar shi'awa data taso mishi wayar shi yad'auka yashiga kallon pic din Ameera da Son d'in shi

Tofa Abdulhakim kasauke girman kai karungumi matar ka ammafa shawara CE

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters 😘🌹
[23/07 12:13 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌸 NOORUL HAYAT 🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels writers 🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans 🀝🏻πŸ₯°

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT
2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
typing...... ✍🏻

HAYATUL MAHAYAT
Coming soon
After RUFAFFIYAR ZUCIYA in sha Allah

πŸ…Ώ { 69 to 70 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Wata dabarace tafad'o mishi tura mata text yayi kamar haka

" Ameera wato kinsamu gurin zamane anan ko ? to kisani idan kika wuce wannan satin tabbas zan 'kara aure "

Yana turamata yakashe wayar shi gabad'aya adede wannan lokacin Ameera tana zaune tsakiyar bed Son yana garun Momy 'karar shigowar text yasa Ameera d'aukar wayar ta ganin text d'in yasatajin fad'uwar gaba dama babu alamar bacci a idanunta setaji tasake wastsakewa sabida tasan zai iya tunda basonta yakeyiba ita kuma baza'iya sanar da Momy zata koma gidan mijin taba


DON rungume da Kausar kam kamar wani zai'kwace mai ita cikin sanyin murya tace

" Sweety time yana tafiya barinaje nahad'a kama break kafin su Sayyid sutashi abin yayimin yawa kuma gashi kakusa makara "

Sake jawota jikin shi yayi cikin rashin sonyin magana yace

" ay bazani office ba yau nabaki lokacin nawa duka yara kuma ay sunawajan masu renonsu ko ? bagamar breakfast kuma aybanajin yunwa tayaya zanji yunwa bacin muna tare sake rungumo ta yayi sosai yashiga romantic d'in ta biye mishi tayi dan bata son yakasance da wata bu'kata bataredata biyamai ba

Tsayin lokaci DON yakasa rabuwa da Kausar dukda yasan yagajiyar da'ita amma yakasa ha'kuri itama takasa dakatar dashi jin kukan Haneef yasa DON saurin janye jikin shi daga nata ahankali tatashi kyara jikin ta tayi sannan taje ta amsoshi mi'ka mishi shi tayi tanufi toilet bin bayanta yayi da kallon yanajinta sabuwa dal cikin ranshi d'aura shi yayi saman 'kirjin shi yashiga bubbuga bayan shi yana fad'in

" haba my dady tayaya zakahanamu hutawa bansanka darigimabafa "

Shiko Haneef sake saka ihu yayi dole DON yatashi zaune yana jijjigashi har seda yakai yasauka daga kan bed yasa'bashi saman kafad'ar shi yana jijjiga shi koda Kausar tafito sedata kintsa sannan tanufo su tana kunshe dariyar ta sabida yadda taga dukya rikice mi'ko hannu tayi zata amsheshi d'aure fuska yayi ya'kibata shi cikin mamaki tace

" Sweety kabani shi nabashi yasha "

Sake had'e fuska yayi sannan yace

" seyanzu zakice nabaki shi bayan kinajin kukan shi tund'azu kije kawai nizan lallashi dadyna "

Murmushi Kausar tayi tace

" ayimin afuwa natuba kuma kainefa kacemin kafini iya reno to amma gashi Haneef kad'ai kakasa lallashin shi balle suduka "

had'e fuska yayi yami'ka mata shi sannan yace 'ay kema dan kinada abin basune kuma ay anatayaki reno amma ni nasan duk wani yaro yafison Dadyn shi "

Wucewa yayi batare daya tsayajin maizata fad'iba murmushi tayi tabishi da kallo tace

" aydaka tsaya kaji amsa uwa dabance Sweety "

Kimanin kwanaki 5 kenan da Abdulhakim yaturama Ameera wannan text d'in amma babu alamar zata dawo zaune Ameera take a parlour Son yana kan cinyar ta se kuka yakeyi amma hankalinta baya gurin shi cikin mamaki Momy tanufo inda take d'aukar Son tayi se'a lokacin Ameera tayi saurin kai hannu zata amshi Son ganin Momy yasa taji wata irin kunya zama Momy tayi sannan tace

" Ameera lafiyarki kuwa naga cikin kwanakin nan duk kin canza kinada damuwa ni tamkar mahaifiyar ki nike kisanar dani in sha Allah zanyi miki gamanin abin "

Wasu irin hawaye Ameera taji suna gangarowa saman fuskar ta asanyaye tace

" Momy Abban Son bayasona yaturamin text akan idan bankomaba zaiyi wani auran kuma nasan zai iya "

Abdulhakim dayake gaf dashigowa parlour tsayawa yayi yanajin abinda Ameera take fad'i murmushi Momy tayi tace

" Allah yabashi sa'a bari yazo seyabaki takardar ki nida kaina zan Samar miki wani mijin wanda yafishi dan bazaki zauna da kishiya ba "

Wata irin fad'uwar gaba Abdulhakim yaji idasa shigowa yayi jiki a sanyaye yagaida Momy cikin girmamawa Ameera tagaidashi d'anjim yayi cikin zuciyar shi yace

" kai Abdulhakim ka'aje komi ka amshi matarka dan Momy batada wasa " du'kar da kanshi yayi yace

" Momy dan Allah kiyi ha'kuri zantafi da matata yau banajin dad'i gidan ni kad'ai "

Tamke fuska Momy tayi sosai sannan tace

" wace matar taka ? ina kakusa aure to ina jiran takardar Ameera dan bazata koma gidan kaba tunda bakasonta kanaso takoma dan tayima gadin gida badan kayi kewartaba ko ? to babu inda zata kaje can ka auro wadda kake so "

Mi'kewa Momy tayi zatabar parlour Abdulhakim yayi saurin ri'ke 'kafarta cikin raunanniyar murya yace Momy dan Allah ki taimakeni bazan iya sakin Ameera ba wallahi ina sonta dan Allah Momy kasa bacci nikeyi akowane dare bazan iya zama batareda Ameera ba haba Hajiya Aysha kibashi matar shi mana "

Cewar Alhaji Umar daya shigo yanzu cikin murna Abdulhakim yami'ke ya tarboshi seda yazauna itama Momy zama tayi yace

" Abdulhakim d'auki matarka kutafi tundaga haihuwa ace har yanzu baki bashi matar shiba Ameera tashi kibi mijinki "

Kallon shi Momy tayi tace

" duk abinda kayanke akan su dede dan basuda uban dayafika ayanzu Ameera kuje Allah yamiki albarka kinyimin biyayya tamkar nice mahaifiyar ki kai kuma Abdulhakim wallahi idan kasake naji wani abunda badedeba senayi mugun 'batamaka rai "

Ajiyar zuciya suka sauke suduka godiya Ameera tayima Momy da dady akan kamarcin dasukayi mata shima Abdulhakim godiya yayi murmushi Momy tayi tace

" idan Son ya'isa yaye akawomin shi "

Jinjina kai Abdulhakim yayi yace

" tab salan daganan ki amshe min shi gaskiya Momy sede yazo miki yawo "

Sakin baki Momy tayi sabida mamaki ta'be baki tayi tace

" dayawanma banaso bari Affan yazo yabarmin Sayyid da baby kai kuma kari'ke "

Dariya Abdulhakim yayi yace

" tab Momy wannan uban son yaranne zaibaki ? Kumama har 2 tab "

Tamke fuska tayi ganin haka yasashi yin ciki wajan Ameera shiru yaratsa parlour na wasu da'ki'ku Alhaji Umar yafarayin magana

" Hajiya Aysha najiki shiru akan maganar mu ? bafa kinwuce munzalin aure bane daki auri wani ay garani ko dan Allah karmu wahalar da juna sabida mubaraya bane shiyasa nataho naji amsa baki da baki zan dawo nan Nigeria nacigabada business d'ina sabida ke "

Ajiyar zuciya Hajiya Aysha tasauke tace

" nace kabari zanyi shawara da Son zasuzo bikin Ashiraf da Amina saura 2 weeks nafison muyi magana baki dabaki dashi akan nakira shi a waya hakan zaifi "

Murmushi Alhaji Umar yayi yace

" ayni tuni mukagama magana da Affan yakuma amince 100% shima Abdulhakim yasani kuma yabada koyan baya kamar yadda brother danshi yabayar "

Mi'kewa Hajiya Aysha tayi tace

" kace seda kuka yanke hukunci kafin kayimin magana ? to ay shikenan Allah yasa hakan shiyafi alkairi "

Cikin matu'kar farin ciki yace Ameen

Soyayya mai 'karfi Abdulhakim da Ameera suke gudanarwa Ameera tayarda dacewa namiji baya kad'an shima Abdulhakim d'aukar ta yakeyi tamkar yar 'karamar yarinya wadda batafi 18 years ba


Yau Dan da Kausar suka sauka Nigeria shida 'yan 4 shi cikin farinciki yau bikin Ashiraf da Amina yarage saura 10 days kuma agobene za'a d'aura auran Alhaji Umar da Hajiya Aysha


An d'aura auran Hajiya Aysha da Alhaji Umar cikin farin ciki Alhaji Umar yadawo Nigeria dazama shida yaranshi 2 Ayman da Zahra Allah sarki Seeyama lokacin da labarin auran Alhaji Umar ya'iske Ammi suma tayi bayanta farfard'o ciwonta yatashi wanda mutuwar Seeyama tasa tasameta wato hawan jini

An shiga shagalin bikin Ashiraf da Amina bikine akayi nagani nafad'a abin sede ace masha Allah bayan bikin Ashiraf da Amina da 2 weeks DON suka fara shirin komawa Saudiyya Momy tanuna tafison zaman shi anan ganin tadamu yasa DON yayi mata Al'kawarin dawowa Nigeria gaba d'aya amma bayan 5 years

Sosai Momy tarazana dajin shekarun amma seta danne tace " Allah yasa munada raban ganin lokacin idan Sayyid da baby sun isa yaye zanzo nad'aukesu seku ri'ke Haneef da Aysha "

Sosai DON yagirgiza dajin bu'katar Momy har su biyu saurin dannewa yayi da bazai iya yimata musuba amsawa yayi da Allah yakaimu yanamai bayyana murmushi saman fuskar shi

Murmushi Momy tayi taji dad'i sosai dukda tasan Murmushin 'karfin hali kawai DON yayi tana jindad'in biyyayar da DON yakeyimata afili tace

" Allah yayi miki Albarka Kausar nasan dukda taimakonki wajan dawoda soyayyar DON gareni da baiyi sa'ar mataba da 'kila yabarni har abada Allah ya albarkaci rayuwar ku baki d'aya

Alhamdulilah ala kulli halin ana nakawo 'karshen wannan book d'in RUFAFFIYAR ZUCIYA darasin dake ciki Allah yabamu ikon amfana dashi kuskuren dake ciki Allah kayafemin

Love u my Hajjaju Allah yabaki ciki rayayye mai Albarka musha suna muzomu kwashi shaku shaku πŸ₯°πŸ’ƒπŸ»

Jinjina da d'inbin godiya gareku masoya na Allah yabar zumunci

Bazan manta da tarin masoyan RUFAFFIYAR ZUCIYA ba ina matu'kar 'kaunarku dankun nunamin soyayya ga kyakkyawar addu'ar dakukemin godiya nike marar adadi all sisters muna tare πŸ‘πŸ»πŸ€πŸ»

Ha'ki'ka bazan manta da d'inbin masoyana nacikin wa'innan groups d'inba kamar

RUFAFFIYAR ZUCIYA FANS
HAYATUL MAHAYAT FANS
XUMUNT@ NOVELL
EYMAN & TEEMA NOVEL'S
DANDALIN MUN KHADY NOVELS
NOVELS WORLD
AZAL NOVEL FANS
MAKIRIN ZAMA FANS
GORGEOUS WRITERS FANS
STAR PLUS FEMALE
ONTOP HAUSA CHAMBAER
BANYI DACEBA GROUP
MARUBUTA AWARD THIS YEAR
RAYUWAR SAFIYAH GROUP
STER GIRL'S
ALMAJIRAI FANS GROUP
TEEMAH__NGAMA NOVELS
LATEST HAUSA NOVELS
REAL PMLW FANS GROUP 12
PRINCESS AND ZINARIYA FANS
HAUSA NOVELS

wai Allah kunada yawa fiyeda haka idan nace sena zayyanaku gaba d'aya zan d'auki lokaci sosai aduk inda kuke masoya ina ina mi'ko dumbin gaisuwa da godiya agareku marar misali ANA TARE πŸ€πŸ»πŸ‘ŒπŸ»πŸ˜˜

Sekun jini a saban novel d'ina HAYATUL MAHAYAT

NAGODE πŸ‘πŸ»

daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY ADDEENAN AJI

Comments and shine please

Love u all sisters 😘🌹
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment