Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar me tsoron wani abu.

Wani irin tsararren parlor ne da kana kallonsa zakasan ilimi hankali da dukiya duka sunyi amfani. Well designed parlor me wani irin sassanyan yanayi me jan hankali. Babban swarovski crystal chandelier din dake tsakiyar falon ce kawai a kunne,amma duka fitilun dake zagaye da falon a kashe suke,saidai duk da haka hakan bai hana fitar ainihin kyau da tsaruwar falon da aka qawata da kujerun qasar Italy.

Kutsa kai taci gaba dayi cikin falon kamar me tsoron sautin takunta,tako ta ina tsarin gidan yana dada kwance mata kai. Wani irin tsari dake da matuqar sha'awa da daukan hankali. Idanunta suka fada daya sashen falon.

Glass door ne da zai baka damar hangen wani guri da aka qawata da wani irin shuke shuke masu launika daban daban masu daukan hankali. Wajen yafi mata kama da qaramin lambun da zai taya mazaunin falon debe kewa. Ta sake wurga idonta.....ba wata qofar a nan data mata kama da qofar kitchen,sai wata qofar shigen qofar farko data bude.

Ita ta nufa kai tsaye,tana jin yadda qafafunta suke nutsewa cikin lallausa Italian Versace carpet daya dace ta kowacce fuska da kalar tsarin falon.

Steps hudu masu fadi ta soma cin karo dasu,wanda ta nan zata taka ta sauka cikin wani falon na daban da yasha banbam dana farko ta kowacce fuska. Furniture din ciki girma da tsari,saidai kusan komai nacan akwaishi anan,illa na wannan falon yafi na wancan yawa da girma. Rukunin kujeru biyu ya dauka saboda girmansa.

Sabanin wancan falon,wannan tafkekiyar tv plasma din da tafi qarfin Wall wooden TV stand din aka girketa samanta ce a kunne. Saudi qur'an ce kunne,saidai kuma sautin karatun sam baya fita. Lullube kowanne bango yake da tsadaddun curtain masu wani irin kwarjini da haiba,kowanne maqale jikin Drapery hardware,abinda zai baka daman ganin qifofin da sukayi saura ta wajen banda yalwataccen dining area da aka yiwa ado na musamman da roman shade curtain da zai baka daman kallon wani sashe na kitchen da glass door ya rabasu.

Qaramin tsaki taja tana janye kallonta daga kallon kowanne tsari na parlor din. Finally bayan ta gama duk bulayin ta samo kitchen din da qyar,don haka ta taka a nutse tana hawa steps din da zai sadata da dining din zuwa kitchen din.

Sak tayi canma tana kallon kitchen din,don wata aljannar duniyar ce da bata san ta ina zata fara ba. Komai a kitchen din baqonta ne,ba wani abu da zatace ta masa farin sani idan ka debe kayan amfani na yau da kullum da kowanne kitchen ake samu. Ya qawatu sosai da custom cabinets da aka sarrafa da wani irin gogaggen katako datayi imani badai daga qasar nan ba,yabi sauran kayan cikin gidan yazo ne daga wata qasar daban.

Tunaninta ya dawo da baya,shin yaushe duka suka samu wannan kudin?,a ina?,da har aka samu daman zuba mata wannan uwar dukiyar cikin gidan?. Anya kuwa bayan mutunci da kawun ya saida mata ba hada harda 'yancin jere ga kowacce diya budurwa ba?.

Iya wannan tunanin ya sake sanyawa taji komai na gidan ya fice mata a rai,baya kuma burgeta ballantana taba haskenshi. Taja qafafunta da sukayi mata nauyi tana nufan gas glass stove din tana fatan ta kunnashi daidai kama kowanne. Sai data bata lokaci shi kansa wajen gane kansa sannan ta saki ajiyar zuciya. Taja da baya tana baza ido don hango inda zata samu koda ganyan shayi ne,don dama cimar bata wuce haka. Daga can ta hango wata qofar,ta taka zuwa wajen tana addu'ar Allah yasa ta samu abinda takeso,don duka ta gwada duba cabinets din bata samu komai ba aciki,da alama shi kam banda kayan kitchen din da aka jera ba'a taba komai ba.

Cikin sa'a ta tadda yalwataccen guri da yafi mata kama da store saidai na musamnan. Don ba abinda yake zube a qasa hatta kuwa da buhunhuna da kwalaye,kusan duka wajen shima an masa kanta sosai kamar kanti ko shago,an saka komai a bangarensa daidai da kwalayen maggi kuwa. Daga gefe babbar freezer ce wadda batabi ta kanta ba,don ko sha'awar budewa bataji ba,to ta bude taga me?,ba wannan ne a gabanta ba.

Bangaran spices na tea ta nufa,ta bude ta debi kowanne daidai yadda zai isheta,daga wannan ba abinda ta qara ta dawo ainihin kitchen din,ta bare tukunya daya,ta nufi sink ta kunna famfo ta debi ruwa,sannan ta dawo ta kunna gas stove din ta dora bayan ta zuba komai.

Minti goma tsaf ya tafasa,ta soma duba mazubin da zata juye ta wuce dashi,don sam batason zamanta kitchen din.

Tea set ne kala kala,ta rasa ma wanda zata dauka. Taja qaramin tsaki still,komai na gidan ya fiya fi'ili da feleqe,tunda ta tashi komai ma sai tasha wahala take laluboshi,iya yau kawai.....neman kitchen da dafa tea ya zame mata alaqaqai?,ina ga sauran rayuwarta cikin gidan.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 15


16


Qarshe dai wani Wedgwood tea set din qasar chaina ta dauka ruwan sararin samaniya,ta juye duka ta zuba sugar a mazubin sugar din sannan ta dauka tray na set din cak tana wucewa ciki dashi.

A yanzun tafi fahimtar hanyar da take komawa ba kamar dazu ba. Tabbas duk yadda takai gason ta kushe komai ta kasa,duk.yadda takeso komai kada ya burgeta a gidan hakan ya gagara,dole ta sallama saidai still zuciyarta na gaya mata

"Allah yasa da kudin halal akayi komai"
(= yarinya tunda dai kin fara mora ai magana ta qare).

Bata tashi tunawa da personal wayan da ta bata ba sai data kusa kammala shan tea din. Qarar wayar ya Haifa mata da wata irin faduwar gaba. Wayace data jaddada mata cewa ta bata ita ne kadai saboda personal use dinta,bata bata ita don ta kira kowa ba sai ita kadai. Hannu ta tura qasan inda wayar ta fada tun a jiya da zazzabi ya kamata,ta duba fuskar wayar sunanta ya bayyana baro baro

5H5V5g5^5n5V 5h5V5a5^5]5j 5V5Y5V5b shine sunan data zabi ta sanya mata saman number. A zahiri tana qoqarin hana kanta daga wayar ne,don bata da buqatar jin muryarta kwata kwata.....amma a badini sai taji kamar ana tilastata daga wayar. Can qasan zuciyarta ta dinga jin bata da wani sauran sukuni saina daga wayar,a sanyaye ta latsa ta kuma kara wayartata a kunneta

"Amarya.....ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da taja wani nannauyan numfashi tana qoqarin daidaita kanta kafin ta furzar da iskar a hankali a kuma sirrance

"Ina kwana?" Ta fada da sassanyan murya. Murmushi maamah ta saki,da gaske aikinta na jiya ya ratsata yadda takeso,ta tabbatar banda haka bataga alamun zata samu gaisuwa wajen yarinyar ba koda na minti daya ne

"Lafiya lau....ya baqunta?" Batasan wacce kalar amsa zata bata ba,don haka ta zabi tayi shuru. Itama shirunta ba shine damuwarta ba,isar saqonta zuwa ga kunnuwanta shine damuwarta don haka ta dora.

"Zuwa anjima kadan zan aike miki da me aiki da kuma 'yar 'yar uwata......zata zauna daku nadan wani lokaci ne.....me aiki zatayi aiki ne kadai da umarninki,da tayaki abinda kike da buqata......amma kula da muhammad da dukkan abinda zaici ban dorawa kowa ba yana wuyanki......kada ki damu da wanzuwarsu.....dukansu sunsan da tafiyar.....saboda haka ba buqatar boye boye wajen gudanar da aikinki,kiyi komai kawai gaba gadi. Abu na gaba muhammad bame sauqi bane.....kada ki sanya rai koki damu da rashin cin abincinki a zangon farko......kawai kici gaba da dafawar.....kici gaba da shiga lamarinsa.....kici gaba kuma da dukka qoqarin ki na ganin yaci yasha din.....yana da tsananin miskilanci......yana kuma da tsantsamin da sai kin zama me tsananin tsafta kafin ki samu abinda kikeso.....ina fata kin fahimta?". Can qasan ranta suya sosai zuciyarta takeyi. Tanajin maganganu na taso mata da ya kamata ta maidawa maamah.....amma sai takejin kamar biyayya wa umarninta ya zame mata tilas ne kawai,ba buqatar musu ballanta jayayya

"Kin jini?" Ta sake tambaya don tabbatar da taji komai din

"Eh naji"

"Yauwa.....saikin sake jina ko?,idan akwai tambaya ko wani abu daya shige miki duhu......qofa a bude take". Kasa cewa komai tayi,sai kawai ta sauke wayar daga kunnenta tana ajeta gefe tare da binta da kallo.

Shawarwari kala kala zuciyarta ke bata game da wayar,wata zuciyar na cewa ta zare layin ta karyashi ta yar,wata nace mata ta kashe wayar ta wurgar a dustbin,wata kuma na gaya mata ta sakata a silent tayita kira ba'a dagaba,amma daga qarshe ji tayi ko guda daya ba zata iyayi ba. Bawai don bata buqatar hakan ta faru ba....aah haka kawai taji aikata hakan bazaiyi ba,saita nutsa yatsunta cikin gashinta kawai tanajin kanta kamar ana yamutsashi......umarninta kadai take da muradin cikawa.

Kusan saman idanunsa hasken alfijir ya fara keta duhun sararin samaniya yana kore duhun daya mamayeta,duniya ta fara haskaka da siririn hasken nan dake juyewa izuwa hasken rana dake wadatar duniya da halittun cikinta.

Wayarsa ya kalla,a gida a lokuta irin wadannan ya kammala duka wasu addu'insa.....yana shiri ne ya fita gym da yake bawa awa daya.....so amma a yau din yadda yakejin jikinsa da sauran gajiya bazai iya komai ba,sai ya miqa hannunsa yana jawo wayarsa da yaga tana haske sanda qarfe bakwai da rabi na safe ya cika.

Joshua ne.....ma'aikacinsa dake kula da bangaren marketing da price na gold da Diamond a kamfaninnikansa. Yana cikin manyan ma'aikatan da baya iya tsallakema kiransu. Cike da mamakin kiran sassafe irin wannan ya sanya wayar a kunnensa

"Hello......" Fu'ad ya fadi da muryarsa maras hayaniya musamman daya kasance yanzun safiya ce

"Hello sir........good morning sir......ina expecting zuwa yanzu baka duba business side news paper da magazines ba ko?"

"Morning Joshua.......what's going on?"

"Sir......sun karya darajar gold da Diamond duka tsakanin tsakiyar daren jiya zuwa yau da safe".

"La'ilaha illlallah" Labbansa suka motsa ya furta a nutse idanunsa suna lumshewa. Daga yadda Joshua ke masa magana adan rude ya tabbatar abun ba qarami bane.

"Cool down Joshua......i will be online yanzu in sha Allah"

"Okay sir......but sir a irin wannan yanayin da sabon kamfani ke shirin fara aiki akwai hadari sosai a ciki.....akwai barazanar tsayawar abubuwa da yawa mo durqushewarsu......sir inaji a jikina an shirya wannan abunne kawai".

"Calm down Joshua,ba abinda zai faru in sha Allah.....let work together okay?".

"Okay sir....." Ya amsa da damuwa sosai a cikin muryarsa.

Kiran ya yanke yana sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da maida hankalinsa kan fuskar wayar tasa. Dole ya miqe a nutse ya fara bincika inda system dinsa suke da sauran kayan aikinsa.

Cup rabin qaramin cup tasha taji tea din ya isheta. A nutse ta maidashi ta ajiye tana bin cup din da kallo. Ya mata kyau sosai,amma kuma ba wannan tunanin bane a qasan ranta,ta janye idanunta tana lumshe. Ta ina rayuwa zata fara?,yaya rayuwar zata kasance?. Idanunta ta bude,sai suka sauka akan wayar da matar dake amsa sunan surukarta ta bata jiya. Daga jiya zuwa yau sai takejin komai kamar ya canza. Har a ranta da zuciyarta sam bata jin matar ko kadan.......tana jin wani qaqqarfan abu a kanta da yafi kama da qiyayya......qiyayyar batasan ta mece ba.....saidai koma meye baya rasa nasaba da katsalandan da suka yiwa rayuwarta ita da d'anta. Tanason kiran momma amma batasan me zatace mata ba.....kuma kaman a yanzun ma yayi safiya da yawa ta kirata din.

Yadda taji zuciyarta nason karyewa taji bataso......batason ta karaya tun bata gama fuskantar komai ba. Gidan yayi mata shuru da yawa,duk da dama can ita ba ma'abociyar son hayaniya bace....ko a gidansu zaka samu dakinsu a rufe kirif don rage yawan hayaniyar mutanen tsakar gidan nasu,a mafi yawan lokuta ma tafi qaunar shurun,sai takejin wata irin kewa tana shigarta.....kewar huda.....kewar nadra....kewar haneefa. Takan tsinci kanta a wani yanayi maras dadi idan ta tuna dasu.....ta yaya zasuci gaba da rayuwa?. Tana da nutsuwa kadan idan ta tuna suna tare da momma bahijja,tayi imani zata cika abinda tace din,amma duk da haka bata shirya barinsu a wannan matakin ba.

Yunqurawa tayi ta miqe dauke da tray din don ta maidashi inda ta daukoshi,tako ina tanaji komai da zatayi amfani dashi a cikin gidan na wucin gadi ne kuma na aro ne a wajenta,bata da hurumin zafafa mu'amala da komai na gidan.

A karo na biyu ta sake duban stair case din sanda zata wuce ga qofar da zata sadata da parlor din. Sai a sannan ta sake qare mata kallo sosai. Tamkar gine ginen turawa haka aka tsara gidan,wani irin staircase ne me kyau da aka qawata bangonta da wani irin woods royal frames da shukoki masu kyan launi da fararen furanni qananu qananu. Idanunta ta janye tana jin bata da hurumin maida hankali da wajen,saidai girma gidan yana saka mata shakka da tsoro a ranta,tana kuma cike da shakka da tantamar ita kadai ta kwana ne wai a cikin gidan?. Saidai basket din data gani ajiye saman table din falon bayan ta dawo a kitchen din ya fara alamta mata ba ita daya bace ba.

Tana shirin janye idonta ta wuce ciki taji sallama daga parlor din farko. Da dan tsoro da mamaki ta maida idanunta kan pivot door din cikin tantamar wanda yake sallamar. Tsahon second talatin tayi,sai taji ta wuce ciki kawai,don bata jin akwai wani abu a cikin gidan da take da haqqin lallai saita kula da yadda zai tafi,saidai taku uku kacal ta sakejin muryar na sake jaddada sallamar. Sallamar tayi mata nauyin da takeji bai kamata ta wofantar da ita ta Kuma wuce ba,dole ta dawo da baya tana dosar qofar,ta turata ta bude tana saka qafanta kan step din idanunta cikin parlor din.

Kamilalliyar macace cikin kyakkywar shiga da lullubi,tana a tsaye,gefanta kuma kyawawan kwanduna ne guda biyu ajiye a gabanta. Murmushin data sakarwa sabreen shi ya sassauto zuciyarta,sannan ya zabge kokwanton dake ciki,saita samu qwarin gwiwar ci gaba da saukowa idanunsu cikin na juna

"Ina kwana" Matar data kusan haifarta ta gaidata kafin ita takai ga gaisheta.

"Ga waje ki zauna" Tace da ita cikin qarfin hali ba tare data amsa gaisuwan ba. A nutse kuma cikin girmamawa ta zauna,sai itama ta samu gefen kujerar ta zauna tana maida mata gaisuwar

"Ina kwana?"

"Barka da asuba,mun tashi lafiya?"

"Alhamdulillah......ya baqunta?" Ta fada da murmushi da kuma kulawa a muryarta

"Alhamdulillah" Ta amsa mata har yanxu tana tunanin wace ita.

"Anni ce ta aikoni.....tace kuyi haquri har yanzu akwai baqi cikin gidan,shi yasa ba'a kawo breakfast da wuri ba,amma gashi nan harda lunch don kada ayi delay na kawowan da wuri shi yasa ta hada.... Tace da fatan hakan ba damuwa?" Sunan tadan juya cikin ranta,amma kuma farat daya hankalinta sai yakai kan matar. Murmushi tadan saki tana mamakin damuwar da tayi dasu haka

"Ba komai.....ayi mata godiya sosai" Ta fadi tana jin wani abu na daban akan matar. Miqewa matar tayi

"Sunana baraka.....dadaddiyar hadimar anni ce ni,zan koma,a huta lafiya" Kai kawai ta gyada mata,har ta fice idanunta suna kanta. Sai ta ajiye ajiyar zuciya tana maido kallonta ga basket din gabanta. Tadan xuba masa idanu tana nazarin matar,komai nata cikin dattako.....kuma komai nata akwai alamun nutsuwa me yawa a tattare dashi,waishin WACECE UWA a cikinsu?,wacce mahaifiyar ta ainihi?. Wannan tambayar kusan ita daya ce abar data damu da ita cikin lamarin kaf,sai ta miqe a nutse kaman zata bar wajen,sai kuma ta fasa,ta tsugunna ta dauki basket din,ta taka a hankali zuwa dining area din da aka qawata da wani dunqulalle kuma mulmulallen dining data kasa tantance glass ne ko kuwa dutse?,ta dora basket din kawai akai,sannna ta juya tana sauka ta wuce zuwa dakinta.

Sai daya daidaita komai sannan ya hada connection din duk da yakeso. Bincike ya fara yi a kasuwannin hannun jari na gold da Diamond.......da gaske an masa wani irin mummunar faduwa da bai taba ganin yayi hakan ba tsahon fara kasuwancinsa. Baya ya koma ya jinginar da bayansa jikin kujera yana shafa lips dinsa da yatsansa guda daya. Da gaske akwai faduwa da hasara me yawa data samesu,musamman a irin wannan lokacin da kwanaki kadan suka rage kamfani ya fara aiki. Zai zamana kome xasu fitar ko su samar asara ce a garesu,dole su saidashi a qasa da farashin da aka tsara za'a fiddashi. Saqonnin da aka yita turo masa suka dawo masa akai,ya lumshe idonsa ya kuma budesu yana kiran sunan Allah,sai ya sake maida hannunsa kan system din.

Kusan duk wani ma'aikaci dake aiki qarqashinsa na kusa dana nesa sai daya nemeshi. Ya bata lokaci sosai yana urgent meeting dasu,wanda hakan ya daukeshi aqalla a wanni masu dan dama. Baisan kuma ya jima din a zaune ba sai da cikinsa ya fara qara. System din ya rufe yana furzar da iska daga bakinsa. Ya tabbata babu abinda zasu iya sakeyi......dole su rungumi dukka hasarar data tunkarosu lokaci guda......

Akwai manufa.......kuma anyi ne da gayya,kuma hakan ya sake bashi tabbacin dukkanin saqonnin da aka aike masa da gaske suke.....sun shirya shiga yaqin tare dashi.....sun shirya jan daga shi dasu. Sai ya saki wani qaramin murmushi. Sunyi gangancin fara tsiro irin wannan abun dashi......ya tabbatar basu gama sanin ainihin waye muhammad a kasuwancinsa ba.......wannan abun koma waninsa bazai sauyashi ba......bazai kuma sakashi ya tsaida kowacce harka tashi ba.

Har a jikinsa yakejin a baqon guri yake,banda haka zuwa yanzu da tuni Ameh ya dameshi da batun abinci. Hannunsa ya miqa ya dauki wayarsa ya kunnata daga kashetan da yayi

"Subhanallah" Ya furta da hanzari ganin har azahar ta sanyo jiki. Bai kira anni ba.....bai kira farouq ba,baima kira kowa ba wanda aqalla ya dace ya yiwa kowa bangajiya koda kuwa ba shine ya gayyatosun ba,amma aqalla sabodashi suka zo. Anni ya fara kira amma sai yaji wayar a kashe,yasan har yanzu gidan akwai sauran baqi don haka yafi kyautata zaton uzurin daya sakata kashe wayar kenan.

Yayi zaton zai samu saqon farouq amma sai ba tarar ba. Ya danji ba dadi,don haka kai tsaye ya fara kiransa.

Bugu daya ya daga kamar dai dama wayar tana hannunsa yana jiran kiran nasa ne. A nutse ya masa sallama,daga can background yana dan jin muryar mutane.

"Kaji muryar ango......so fresh" Farouq din ya fada kansa tsaye.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 16






"Sai yanzu aka tashi kenan?" Farouq din ya sake fada ba tare daya damu da abinda zaice da farko ba a lallai sai ya tsokalo shi

"Eh.....ka nemeni ne?"

"Wa?,ni?,ya za'a yi na batawa kaina lokacin nemanka?,waya gaya maka ana kiran ango a irin wannan time din?"

"To hell with you farouq a'ahhhhh" Ya fada sounding bored kadan kadan.

Murmushi me kama da dariya ya saki wanda har sautinsa ya bayyana sosai.

"An maka uziri kome zaka fada you're forgiven" Hannunsa ya dora saman sumarsa yana shafawa,ya fuskanci farouq so yake kawai ya haukatashi

"Where's anni?"

"Na barta a gida tana preparing na walima....."

"Ya salam" Fuad ya fada yana lumshe idonsa. Sam ya mance da batun walimar kwata kwata.

"Su haajj na yiwa rakiya airport......they're leaving".

"My regards to them please.....idan na sake nutsuwa zuwa anjima in sha Allah i will give them a call"

"Ance maka daga yau har wani satin an maka uzuri fa.......ka samu nutsuwa yadda ya dace dudu" Ya rigashi katse wayar wannan ya hana fuad gaya masa abinda yayi niyyar fada din,sai kawai ya zame wayar daga kunnensa,qasan ransa yana fassara maganar farouq da kuma sakata a inda farouq din ke nufi

"God forbid" Ya fada qasa qasa. Hasashen gaba days banbarakwai yayi masa sanda ya dora tunanin a muhallin da farouq ke nufi,tattara tunanin yayi ya azashi a mizanin shirme gaba daya,ya fara lalubar number amna.

Sai data kusa yankewa sannan ta daga

"Hamma" Ta fada a shagwabe.

"Hamma ka manta dani.....adda tayi taking dinka away.....as far as yadda zata iya" Ta qarasa fadi da qaramar dariya a muryarta da ba sosai ta bayyana ba

"You amna.....lovey dovey will never be forgotten........hayaniya yayi yawa amna.......bansan haka ake abun ba"

"Hamma yafi haka fa.....don kaqi bada hadin kai ayi komai" Hannunsa ya dora a goshinsa yana furzar da qaramar iska. Shikam ko zancan bayaso,abinda yake gabansa kawai yanzun shine damuwarsa.

"Ya gidan?" Ya tambayeta.

"Full with 'yan biki dake jiran walimar anni......ina yini hamma" Ta hade amsa tambayar tasa da gaisuwa.

"Alhamdulillah.....how about anni da abba?"

"Abba dai ya fita tun dazun.....kuma ina jin sai dare zai dawo........anni tana daga baya da mutane"

"Okay.....bata wayar"

"Okay hamma" Ta amsa shi tana miqewa gami da ficewa.

Bai yanke kiran ba saita maida kunnenta,tana tafiya wajen annin tana ta bashi labarai kala kala. Bai yanketa ba yayi shuru yana saurarenta. Yasan halin amna sarai,bata gajiya sam sam da hira.

"Kice ameh ya kirani....."

"Okay hamma.....ga anni" Saita miqawa anni wayar,ta samu plastic chair daya daga cikin kujerun dake wajen ta zauna tana kallon yadda aka qawata wajen walimar da wani irin tsari me kyau,tamkar wani hamshaqin event center.

"Barka da warhaka anni......ya hidima ya rana?" Murmushi ta sauke,har cikin ranta farinciki yana mamayarta idan ta tuna a yau muhammad dinta ya zama cikakken magidanci

"Barka kade me babban suna.....mun tashi lafiya zance ko mun yammata lafiya?". Tambayar tata tadan sakashi yaji nauyi,kada itama fa ta dauka wani abune ya boyeshi,kada ta fassara wani abu na daban akan yarinyar ma da bai samu daman ganinta ba

"Lafiya anni alhamdulillah"

"Haka akeson ji.....na aika baraka takai muku breakfast da lunch.......nayita so nace idan ta isa ta hadani da d'iyata mu gaisa saina sha'afa......in tana kusa bani ita" Rasa abinda zaice yayi,yadan diririce kadan har hakan yaso ya nun alamu a muryarsa,yayin da annin ta dauka wani abunne na daban ya kawo hakan,kodai baiso aji muryarta a fahimci wani abu,don haka ta katseshi

"Kaga rabu da ita.....anjima idan kun iso wajen walima ma gaisa.....za'a fara immediately after asr prayer"

"Allah ya kaimu anni.....Allah ya qara girma da lafiya"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ta fada tana jin dadin yadda sam baya gajiya da mata addu'a.

Ita ta fara katse wayar,sai shima ya sauke yana kallon fuskar wayar. Inda anni ta sani data qyale walimar nan,duk da ita walima duk inda

Please Login or Register in order to submit comment