Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Duqar da kansa yayi da sauri cikin rawar jiki yana cewa

"Sorry sir". Bai ko kulashi ba ya kalli amna,da idanu yayi mata sign na ta wuce,sai tayi qasa da kanta tana yin gaba. Ganin amna ta wuce itama saita taka zata bita,bai hanata ba,yabi bayanta shima,saidai ya gasa mata maganar da sai da qwalla ta diga ta samu sassauci

"Shi abun qwarai da mummuna tabo gareshi......mu'amala da tarin mazaje ba shine mutuntaka ba ta d'iya mace.... Mutuncinta namiji daya da zai amsa sunan mijinta,bariki bata da riba kota rana daya ce kuwa......duk wanda zai hada zuri'a da macen bariki saiya shirya......ba qaramin cutarwa bace ga 'ya'yan da zasu haifa idan aka ture nashi matsalan na qashin kansa".

"Macen bariki......mu'amala da tarin mazaje" Wadannan kalmomin su sukafi komai tsaye mata a rai.

Wanne irin mummunan kallo yakeyi mata ne wai har haka?,wanne mummunan fassara yake mata ne?. Tana ji ta soma gajiya,ta fara kaiwa iyaka,daga yanzu zuwa kowanne lokaci zata iya fashe masa.......ba zata iya ci gaba da dauka ko jurar irin wadannan tuhume tuhumen da maganganunsa da basu da tushe ba,tana jin zuciyarta da idanunta na mata wani irin suya,bata samu sassauci ba sai bayan da jirginsu ya doshi Maldives......hirarrakin family din da uwa me goya marayu wato anni ita ta sama mata relief a zuciyarta,saidai tana jin ta wani irin sake tsanarsa,ta kuma sake tsanar hada komai dashi.

Gabanta ya tako,abinda ya sanya amna gocewa da sauri tunda ita ke first seat da zummar yin gaba

"Karki fita......ki jirata" Ya fadi da husky voice dinnan nasa data sake dakewa,tun daga tashinsu daga lagos din bayan wancan abun daya faru zuwa yanzu tana ankare da hamman nata. Sai dacin rai kawai yakeyi wanda shi kansa baisan yana yi ba,jifa jita take satar kallonsa,har a sannan kuma ta tabo sabreen

"Adda........wai dama haka hamma yake da kishi?,daga cewa you look familiar?.....haka hamma yake sonki?" Ta fada tana murmushi kaman abun yana burgeta. Sau daya tak ta kalli fuskarsa sanda yake fama da system dinsa,saita maida idanunta ga window din jirgin tana duban yadda suke dai da daidai da gajimare. Abun yana burgeta,tunda shine karon farko data fara keta hazo......saidai can qasan ranta yana cunkushe da halayensa.

"Ba kishi bane.....izza ce wulaqanci da kuma izgili.....har yanzu banga wani kyakkyawan halayensa guda daya ba......koma dai meye saura kwanaki kadan suka rage na barshi shi da halinsa dama tarin dukiyar dake sanyashi dagawa izgili da girman kan ma" Tayi dukka maganar a ranta,amma a fili murmushi kawai ta yiwa amna. Amnan bata damu ba taci gaba da dauko mata gulmarsa kadan kadan,tunda ta saba da halinta na wannan fannin. Ba komai sabreen din ke bude baki ta bada amsa ba a maganganu da dama.

To a yanzun da yake tsaye a gabanta bata dubeshi,sam bata qaunar hada idanu dashi.

"Ko meye zakiyi a yanzu ki dinga tunawa akwai igiyata a kanki......bazan kuma lamunci kowanne abu da zai zama tozarci ga igiyata ba......zan iya daukan kowanne mataki mara dadi muddin kikayi wani abu daya sabawa shari'a......ki kula,ki kula da kyau". Kasa jurewa tayi,haka siddan daga saukarsu a qasar,kowa ya sauka da walwala itama ta samu ta fara tattalin tata zai watsa mata ita. Fararen idanunta ta daga ta watsa masa wani.kallo tsakiyar idanu. Wani haske suka fitar sosai saboda fushin dake cikinsu,wani salon kallo da baiyi kama da harara ba,shi kuma ba kallon banza ba. Ta motsa siraran lips dinta zata ce wani abu,sau kuma taga hakan baida ma wani fa'ida......bata da sauran lokacin batawa,don haka ta soma qoqarin rab'eshi ta fice.

Sosai taji an damqi hannunta da wani tsatsauran riqo,ta waiwayo da hanzari tana dubansa,ya damqeta ne ba tare da ya ko waiwayo ya kalleta ba,qeyarsa kawai take iya gani,da hannu daya ya jawota ya dawo da ita gabansa,ya sanyata a tsakanin idanunsa yana mata wani irin kallo da taji ya tsaye mata a sassan jikinta,ya kuma soma sauke rashin kunyar da taji tana taso mata

"Duk sanda kika       

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  sake gangancin wuceni ina magana.....na rantse da Allah sai na gwada miki ina da banbancin da lusaran mazan barikinki marasa daraja......dole ki amsa min kowacce magana kaman yadda nakeso.....don banajin muryarki tafi tawa tsada ko daraja.....ko banza adadin mazan da sukaji muryarki baikai adadin matan da sukaji tawa ba......kinjini?!" Ya furta da dan tsauri idanunsa na kallon wani gurin daban sabanin cikin idanunta

"Eh naji" Ta amsa a sanyaye kanta yana kallon qasa. Shigowar farouq ta gani daga bayansu,wanda ta tabbatar shi bai gani ba,sai ya sakar mata hannun yana juyawa gami da takawa a hankali yana ficewa a jirgin.

Hawayen da take riqewa ne suka yiwa kansu da kansu hanya. Ta sanya tissue tana daukesu

"Ya isa......ya isa" Take gayawa kanta da kanta. Tana cin alwashi a ranta ko ya bata takardarta.....ko bai bata ba,sauna sauka a nigeria zaman aurensu ya qare......ko ya sallameta ko bai sallameta ba wannan duka damuwarsa ce,alwashi ta ciwa kanta.....wannan karon babu abinda zai dakatar da ita......ba kuma wanda zai hanata.

A hankali ta fara takawa itama tana nufar qofa da shimfidadden matakalar da aka jinginewa jirgin. A nutse take sauka tana qoqarin daidaita mode dinta gudun saka damuwa a zukatan amna da anni.

Three pieces turkish gown ne a jikinta,wadda take hade da strips skirt da kuma blouse data zauna daidai jikinta,tayi kuma took in da ita kaman yadda tsarin kayan yake,sannan ta kawo doguwar gown din kayan me budadden gaba data sauka har qasa ta kuma bude sosai daga qasan. Qafafunta high hill ne masu madauri da suka dace da kalan rigan. Sosai kayan suka karbeta,baka ganin komai sai fuskarta,zaka rantse da Allah bata hada nasaba ta kusa ko ta nesa da nigeria ba.

"Wallahi anni adda sabreen kyau takeyimin......komai nata me kyau ne.....duk kayan data saka sai naga kaman don ita aka yisu" Ta fadi maganan tana matsawa kunnen anni,saidai fuad dake tsaye daura dasu yaji abinda ta fada din.

Haka kawai ya samu kansa da daga kan nasa,suka kuma yi masa jagora a kanta duk da yadda yake qoqarin hana hakan faruwa. A kasalance take tafiya saboda bacin rai,sai hakan ya sake zama kaman cikar adon tafiyartata. Idanunta suna lumshewa kadan gami da bude kansu duk a qoqarinta na hana zuciyarta karyewa,ta kuma hana idanunta zubda ruwan hawayen da takeji suna tattara kansu. Amna dake mata murmushi ta maidawa martanin murmushinta,abinda ya sanya pink lips dinta motsawa kadan.

"Ya salam" Ya fada can qasan ransa saboda tsigar jikinsa da yaji ta zuba yarrrr.....tun daga tafin qafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Wanccan ranar ya tuna.......ranar daya sanya lips dinsa saman nata......shi.kadai yasan me yaji,shi kadai yasan yadda ya iya qwace kansa daga yanayin daya shiga......yayi imani a ranar inda ace shi din manemin mata ne,baisan adadin mata nawa zai nema ba a ranar.....inda shi mashayi ne,baisan adadin kwalba nawa zaisha ba......inda ace shi din asharari ne bayajin cikin kwana uku ma wata macen zata sauke masa abinda yaji a jikinsa a wannan lokacin. Bayajin zai iya ci gaba da tsaiwa a wajen bare ta fahimta ko farouq ya gano canzawarsa,don haka sai ya juya kawai yana takawa a nutse yana matsawa daga wajen gami da sake kame kansa da kyau gudun zubewar kima.

Dukkaninsu motar da tazo tararsu ta dauke,mota ce me seat kusan hudu bayan wajen hutawa daga can baya. Shi da farouq suna seat guda,sabreen anni da amna suna set na qarshe.

"A ina ka samar mana gida?" Fuad dake gyara agogon hannunsa ya tambayi farouq. Takardun hannunsa ya fara budewa daya bayan daya kafin yace yana tsaida idanunsa akan wata takarda guda daya.

"RANGALI ISLAND RESORT......garden villa na masa mana gida.....baiyi tsada cancan ba,duk da Maldivian Rufiyaa mukayi cinikin,ahmad ne ya siya gidan ta hannun wani,da nayi converting kudin da naira sai naga basuyi yawa ba" . Kai kawai ya jinjina,farouq akwai iya aiki,musamman idan akazo batu na tafiya tourism.

"Ina fatan yalwatacce ne,kasan mun sake qaruwa this time?". Idanu ya zuba masa,kaman yace masa waye ya qarun da sukayi yawan da zaa nema bangajejen gida?,amma sai yaga kulashi ma bata time da plan ne,don haka ya bishi da

" Yes" Kawai farouq yace masa yana boye dariyan dake qasan ransa.

Idanunta akan hanya sanda suke wuce lafiyayyun hanyoyin da suka sha banbam dana qasarmu nigeria. Ko daga iya nan ta tsaya ta tabbatar wata duniya ta daban ta shigo. Ta shigo wata duniya da tayi nisa qwarai da tata DUNIYAr data rayu cikinta. Qarfi da yaji takeson komawa 'yar qauye,ta sauke nannauyan ajiyar zuciya sanda motarsu ke shiga wani street me dauke da lafiyayyar hanya da wadatar tsirrai. daga gefe da gefan hanyoyin tana iya hangen ruwa can nesa dasu,wani irin ruwa dake bada blue colour,bata sani ba.....color dinshine haka ko kuma 'yar tazarar dake tsakaninsu take nuna mata haka.

Daidai qofan wani madaidaicin kyakkyawan gida motar ta fara slow kafin ta samu wajen tsaiwa. Su suka fara fita suka jira fitowar anni,sannan ita da amna suka biyo bayanta.

Tare suka jera da farouq har qofan gidan su kuma suna biye dasu,jordan da drivern motar suna biye dasu da luggage dinsu.

Dab da zasu isa qofan gidan qofar ta bude da kanta. Farin matashi ne ya bayyana wanda duka duka shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas ba,daga gefansa musaddiq ne da suka jero tare,wanda kamanninsa da fuad ta wasu bangarori da yawa suke bayyana kansu. Yana sanye da jeans da shirt yayin da musaddiq jikinsa ke sanye da jallabiyya saqar marocco,kansa kuma akwai qaramar hular da mukafi mata laqabi da tashi ka fiya naci haka ma mutumin dake gefan musaddiq din. Akwai haske sosai saman fuskar tashi dake bayyana musulunci tattare dashi.

Da sassarfa musaddiq din yake qarasowa garesu,idanunshi duka suna kan anni,yana isowa gaban nata baiyi duba da wani girmansa ba,ya bude dukka hannayensa ya rungume annin yana fadin

"I missed you so much anni......sai naji kaman ba zakuzo ba.....kwana biyu kawai amma sai naji tayi nisa" Murmushin dake shimfide kan fuskarta kadai ya isa ya gaya maka farincikin dake ranta na ganinsa da tayi,zallar qauna irin wadda ba kasafai ake samunta wajen wani ba idan ka dauke uwa.

"Kayi nisan kiwo yaro na......ka tayani roqon hammanku kada ya sake daukemin kai har haka" Ranqwafowa yayi wajen fuskar annin,yana yin qasa qasa da muryarsa don kada fu'ad yaji

"Na rantse anni nima bazan sake yarda ba.....ki jawa danki kunne"

"Kai kai......hamman?,ai kuwa kaman a kunnensa" Amna data zuro musu kai ta fada tana raba idanu. Duban amna yayi yana dan yamutsa fuska

"Bama haka dake auta......kinsan ni dake duk muna together" Ya furta yana daga mata yatsunsa biyu cikin salon son samun goyon bayanta. Fuska ta shagwabe tana cewa

"Zan iya haqura nayi shuru idan tsarabata tafi ta kowa yawa" Tayi maganar tana kashe ido daya sannan ta dora

"Idan kuma ba haka ba.....ga addana a gefe,ita zan gayawa ta shaida masa abinda kace da mijinta" Ta qarasa maganar tana nuna sabreen da yatsa.

Sai a sannan ta lura da sabreen din dake gefansu. Ya dora idonshi a kanta yana dan kafeta da kallo na wasu sakanni. Sosai yaji yasan fuskartata,ba yau ne ranar farko daya fara ganin fuskar ba. Cikin qasa da second biyar ya tuna inda ya santa. Tabbas bazai taba iya mantawa da fuskar ba.....fuskar data dinga fada saboda lafiyar anninsu.......fuskar data zama silar ceto rayuwar anninsu,to amma kuma sai yaji kaman bai kamata farat daya haka a matsayinsa na baquwar fuska a gareta yayi gaggawar tuhumarta inda ya santa ba.....ballanta ma ita din da take matsayin yaaya a wajensa.

"Tuba naki adda.....ayimin aikin gafara.....da gaske hamma baida dadi shi yasa takeson hadoni dashi" Ya fada yana hade hannayensa duka biyu waje daya.

Batasan ya akayi murmushi ya qwace mata ba,murmushin daya afku saman idanun fu'ad dake dan nesa kadan dasu yana karbar takardu hannun ahmad tare da sake karbar wasu bayanai,don tuni farouq ya wuce cikin gidan yana sake duba yanayinsa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

69


Wani abu ya hadiye da baisan meye shi ba,wato ita duk inda taga maza sakin jikinta takeyi?,a ina tasan musaddiq da daga haduwar farko xata sake masa fuska da murmushi har haka?. Idanu ya xuba mata yana kallon yadda take duban musaddiq kai tsaye.

"Anyi maka.....amna ma na tabbatar tsokanarka take,don kullum cikin kewarka take,nasha labarinka a wajenta sosai". Ta fada har zuciyarta tana mamakin family din. Kowa na gidan kenan me kirki ne,shi kadai ne maras kirki,maras fara'a,marason jama'a?. Ta tambayi kanta sanda idanunta ya sauka a kanshi. Cikin sa'a idanunsu suka sarqafe guri guda,kusan tare kowa ya dauke dubansa daga kan dan uwansa,sai ya miqa hannu yana karbar takardar hannun ahmad. Da yaren dhivehi asalin harshen mutanen qasar ahmad din yake masa godiyan da batasan ta mece ba. Ga mamakinta sai taji ya maida masa shima da yaren sannan ya
ya soma takawa shima yana wucewa ciki da qasaitaccen takun nan nasa. Tana jin muryar musaddiq yana fadin

"Godiya nakeyi" Tare da maida kansa ga anni.

"Zan kamaki,saikin gayamin dalilin da yasa kina kewata amma baki taba fadimin ko sau daya ba".

"Diyata zo mu wuce ciki,wadannan idan kika biye musu zaki wuni a tsaye ne kam" Anni ta furta tana saka hannunta ta kamo hannun sabreen suka fara wucewa cikin gidan. Duk kunyar anni sai ta kamata,tayi qasa da kanta tana biye da ita. Batasan wani abu a duniya da takejin nauyinsa haka ba kaman annin,tana da wani kima a idanunta na musamman.

"Yanzu nake shirin leqawa na kiraki ki shigo ciki......wancan shirmammiyar tunda ta hadu da dan uwanta kuma ai shi kenan.....may be daga nan ma yawo zasu wuce iyayen zumudi".

" Saddiq....." Fu'ad dake zaune hannun kujera yana duba takardun daya karba yayi kiran Sadiq dake qoqarin daukan ruwa a fridge. Samun kanta tayi da lumshe idonta,batasan me yasa muryarsa take mata nauyi da yawa ba,ba ita ya kira ba,amma sautin kiran yakai mata har tsakiyar qirjinta. Muryarsa tana da wani irin amo me ratsa mutum koda ba dakai yake magana ba.

"Na'am" Sadiq yabar abinda yakeyi ya waiwaya yana dubansa,bai daga kai ya kalleshi ba yace

"Fita ka gayawa musaddiq kada suje ko ina"

"Okay" Ya fada yana ajiye ruwan gami da kama hanyar fita. Numfashi kawai ta aje tana tabe baki,kowa a sake yake amma bandashi,ya iya bada umarni,daga wannan sai wancan,kuma yana iya gama magana dakai kaf ba tare da ya kalli fuskarka ba,ta rasa wanne irin mulki ne haka a cikin jininsa?. Idan kuma muguntarsa ya motsa,ta lura kowa ma da idanu yake hukuntashi,ko don yasan akwai wani abu me nauyi a cikin kallonsa oho?,saita dauke kai gefe tana tabe baki,idanunta kuwa suka sauka kan wani glass door wanda daga nan kana iya hangen wani ruwa nesa kadan dasu dake lullube da farin yashi kaman ta miqa hannu ta kamo.

"Gidan ya miki anni?" Ya fada yana sauke takardar daga fuskarsa bayan ya gama jan ajin nasa.


"Tubarkallah ma sha Allah" Anni ta fada cikin walwalar data bayyana har saman fuskarta tana kallon kowanne sashe na gidan

"Allah ya qara rufa muku asiri duniya da lahira.....Allah ya ninka albarka cikin rayuwarku"

"Allahumma ameen" Suka fada shi da farouq a kusan tare.

"Anni ta shiga ta huta.....akwai awa kusan daya da rabi kafin sallar magarib.....inajin yau ba wanda zai fita sai gobe idan Allah ya kaimu" Ya fada yana duba agogon hannunsa sannan ya sauke.

Cikin aljihun trouser dinsa farouq ya sanya hannu ya ciro key,ya kuma nufi wani daki cikin dakunan dake parlor din,ya bude dakin ya tura qofan yana duban amna

"Ja luggage dinki dana anni kikai muku ciki" Yace da ita daidai sanda take shigowa, Amsa masa tayi to tana yin yadda yace din,ya waiwaya yana kallon musaddiq da musaddiq

"Bude dakin can musaddiq ku sakawa addanmu nata kayan" Ya fadi yana miqawa musaddiq din key din,sannan ya kalli Sadiq

"Saka mana namu a dakin musaddiq sai muyi squatting......addanmu ki shiga ki huta" Ya fada cikin murmushi da girmamawa fal muryarshi,qasan ransa kuma wasai da yadda plan dinsa ya tafi daidai.

Harde hannayensa yayi kawai a qirji yana qarewa farouq kallo,wato abinda ya tsara ma ran shi zaiyi kenan?,shi yasa koda ya buqaci picture ko video na gidan ya hana mishi gani.

Yasan sarai shi fu'ad din yake kalla,ya kuma shiryama koma meye zaice ko zaiyi,don haka ya basar yaqi kallonsa kaman baisan ma yana a wajen ba. Fridge kawai ya bude yana duba meye da meye a ciki yana kuma masa lissafin me dame ya kamata su ajiye na kwanakinsu a qasar. Wani haushi ya cikashi,ya cika yayi fam da rainin hankalin da farouq din ya shirya masa. To amma a yadda yaga farouq din ya tabbatar ya shiryawa duk wani rigimarsa ne,so dole ya fara bin komai a hankali,tunda basu kadai bane,akwai anni,bazaiso kuma anni taji ko taga komai ba.

"Wanne irin gida ne wannan farouq?" Ya fada calmly yana qoqarin danne takaicinsa. Sai daya ajiye gorar hannunsa sannan ya waiwayo yana dubansa

"Me fa?" Yayi tambayar kansa tsaye. Sai daya lumshe idonsa ya bude lokaci guda yana jin takaicin rainin wayon farouq da idan ya motsa tsaf xai iya cewa ma bai sanka ba.

"3bedroom?,why not a siya me 4bedrooms farouq?"

"Akwai baquwar halitta ne a cikinmu da bata samu waje ba?". Kai fu'ad ya girgiza yanason gajarce maganar,don ciki yakeso ya shiga yayi bacci ko na awa daya ne

"Babu.....amma dakunan sunyi kadan.....kafi kowa sanin bana iya hada daki da kowa ba ko tun ba yau ba?"

"To dawa na hadaka.....kajimin mutum zaimin sharri" Rainin hankalin farouq yakai masa ko ina,yana dab da bashi naushi idan baiyi wasa ba,sai ya ware hannunsa daga qirji yana dubansa

"Ka canza plan dinnan,ta koma dakinsu anni tayi squatting tare dasu,saddiq su kwana da musaddiq.....kai kuma muje mu kwana tare". Baya yaja da sauri yana zare ido kaman yaga abun tsoro.

"Mu kwana da kai?,alfanun uban me zanyi maka fu'ad?,me zakaji da kwana da namiji gardi dan uwanka bayan ga halalinka a gefe?" Maganar ta fara girmar kunnuwan fu'ad,tun ba yau ba yasan farouq idan baiso ba tantirin kansa ne,baisan sanda hannunsa yakai kan cup din da saddiq yasha ruwa ba ya jefeshi dashi,Allah yasa yana da zafin nama ya cafe

"Na rantse da Allah xan ruguza maka kai......kai wanne irin dan iska ne?,maganan da nake maka daban yadda zaka juyan zance daban?,ta yaya zan kwana da wata alhalin muna muhalli daya da anni?". Dariya tana cin farouq amma ya maze

"To ba dole nace haka ba?,ga mace me namiji zai maka?,nima bazan kwana da gardi ba,ka cire riga wannan qattin muscles din naka suyita bawa mutum tsoro.....in fact ma ni na fara rehearsal na yadda zan fara kwanciya daga ni sai fannah ta....anni kuma da kake magana akwai wanda zai kaita son ganinku tare....ko turmusheta kayi a gabanta ai saidai tabar muku gurin da gudu.....banson gulma banson k......" Bai qarasa ba yaji saukar abu a qeyarsa,agogon hannunsa ya kwance ya sake jifansa dashi don ya rasa dame zai jefeshi wannan karon.

Dafe wajen yayi ya waiwayo yana dubansa fuska a hade

"Amma dai kasan wannan zallar cin zali ne ko?,ni nakar xomon?,kaje ka yiwa anni bayanin abinda yasa zaka aikota kwana da ita daki daya mana da kanka".

"Ya isheka farouq" Ya fada yana nunashi da yatsa,alamun ya fara qureshi.

"Oho" Ya fada yana sungumar ruwansa yayi dakinsu baiko sake waiwayoshi ba.

Shuru ne ya ratsa falon bayan wucewar farouq din,sai motsinsu kadan kadan da yake jiyowa daga dakunansu. Maganar gaskiya farouq ya cuceshi,inda kuma yasan da wannan da tuni ya sanya an canza musu gida da yafi haka yawan dakuna kafin su qaraso. Miqewa yayi abisa dole yana soma dosar dakin,abu daya ya sani shi bayason takura,yana son bajewa sosai ya sake a duk inda ya zabi rayuwa,so wanzuwarta cikin dakin kuwa bazai bari ya zama silar hanashi sakewa ba.


*Maamah*


Sake juya tickets din hannunta tayi guda biyu tana sake qare masa kallo. Mamaki da wani irin dunqulallen baqinciki yana yayyanka zuciyarta. Ta rasa wanne hamshaqinne ya juya tafiyar daga farkonta ta koma qarshe?. Maldevis shine waje na farko da zasu je a qa'ida kaman yadda ta samu tabbacin dukka iyalin gidan alhj hamza kibiya can suka wuce.....saudiyya kuma shine waje na qarshe da zasu ziyarta daga nan kuma sai gida Nigeria,amma wanne hamshaqinne ya karkatar da tata akalar tafiya daga saudiyya kafin ta sauka maldevis sannan su rankaya su wuce turkey tare?.

"Hajiya ameena.....tabbas wannan aikin ameena ne" Ta fadi tana jin wutar qiyayyar matar tana sake ninkuwa a ranta. Zazzafar iska ta furzar tana fitar da idanunta waje irin na zallar takaici da kuma tunani. Ita kuwa ta yaya zata dagawa ameena qafa?,ta yaya zata bar ameena taci gaba da shaqar iska cikin aminci?,ba ragi tsakaninta da ameena har abada......yadda bata barta ta samu cikakken iko da mulki da 'ya'yanta ba.....tabbas haka zata zama silar tarwatsa nata ahalin gaba daya,duk wanda ya gaya mata cuta ba shakka ita mutuwa zata gwada masa,sai kawai taja wayarta tana laluben fareeda,tana jin wannan karon a gaban idanun ameenatun zata gwada mata nata izzar da qarfin mulkin kasancewar uwar data dauki cikin fu'ad tayi naqudarsa ta kuma haifeshi.......a gaban idanun kowa zata gwadawa sabreen ta isa da danta......zata nuna mata kuma tana da ikon sanya yaronta ya auri mata d'ai d'ai har guda uku rigis bayan ita.

Shuru fareeda tayi tana sauraren bayanan maamah,saidai kuma zuciyarta cike fal da bacin rai da baqin kishin sabreen. Wata zazzafar iska ta furzar tana ajiye bututun shisha dinta ta gyara zamanta

"Maldives ai gida ne......ina da sauran visa din qasar da ban gama cinyeta ba,muddin na samu ticket jibi warhaka ina can......ko ba ticket zan sanya daddy yamin hiring private jet......kya sameni a can" Daga haka ta yanke wayar tana latsa wayarta ba bata lokaci tana neman number wayar daddy din nata.

Tafasa kawai zuciyarta takeyi,wannan karon da zafi zafinta zata shiga,zata budewa sabreen aiki sosai kaman yadda zata budewa fu'ad,tana jin komai mai sauqi ne......amma zata bari ta tabbatar da samun private jet ko ticket to Maldives.

Bugu daya rak ya daga,ba kasafai ta fiya masa sallama ba,kusan sallamarta kiran sunansa ne

"Daddyyyy.....maldevis" Ta fada da wata irin shagwaba kamar yarinyar da aka Haifa jiya jiya

"Mamana......maldevis a daren nan?"

"Daddy gobe......ina da sauran visa na da kamin last two months.......ticket kawai daddy nakeso......please daddy,it's an urgent need daddy". Murmushi ya saki yana juya kai kafin yace

"Wani irin emergency issue ne haka ya taso mamana.....nifa mamana yanzun duk hankalina yana kan aure,kiyi aure haka mamana.....ki zabi duk kalar mijin da kk so zan tsaya miki" Maganar sai taji kaman tazo akan gaba,ta saki dariya tana cewa

"Nayi maka alqawari daddy.....indai na samu wucewa Maldives gobe ko jibi,ina dawowa zan gabatar maka da mijin da

Please Login or Register in order to submit comment