Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiyaye,mari ko dukan fuska haramunne a musulunci_



"Biri yayi kama da mutum,tsananin qaunarta da duniya da kuma dukiya,shine silar qoqarin mallakar d'anta ta qarfi da yaji?,wannan shine daliinta?". Numfashi ta fitar me nauyi tana saka hannuwanta saman fuskarta

" Adda......maamah keson magana dake" Amna da sunan maamah din ya fito ta true call din ya gaya mata wace ta fada kai tsaye,duk da bata da tabbacin da sabreen takeson magana.

Hannu kawai ta bawa amna,tana maida wayar kunnenta.

"Har yanzu kina kan bakanki?,kinci gaba da lamuntar jefa rayuwarki cikin hatsari maimakon tseratar da rayuwar taki?,a naki tsammanin kin tsira kin tseratar da yan uwanki?"

"Idan kura tana maganin zawo ta yiwa kanta mana?". Dif maamah tayi,batayi gaggawar amsa mata ba,don maganar ta jefeta da wani qudundunanniyar ma'ana.

"Kece kike sake tafka kuskure akan kuskure......kuma kwanaki dukka wani sirrinki yana qarewa.......komai yana dab da bakaduwa tamkar yadda iska ke diban lallausan gari tana watsashi cikin mutane........ashe ba kaina kika fara nuna rashin sanin darajar halittar D'A ba......ashe baiwa ce sanin darajar haihuwa a zuciyar iyaye......d'anki bashi da muhalli ko daya a zuciyata ko rayuwata,.....kaman yadda banda sha'awar zaman aure dashi......saidai fita a gidansa da rayuwarsa duka sai sanda naga dama... Kinsan yaushe nake nufi?" Bummm zuciyar maamah ta buga tun bataji qarshen zancen ba

"Zan fita ne a sanda na gama karanta masa ainihin WACCE KALAR UWA yake da ita......ba don ina sonsa ba......sai don alkhairi guda daya tak da yayimin........ya karbo 'yan uwana daga hannunki ya kawominsu......abinda yayi silar takawarsu tudun muntsira......ya sanyasu hayewa duk wasu qananun qullinki.....zan saka masa da iya wannan,don bashi da wata nagarta ko guda daya da zata sanya sabreen sha'awar kasancewa dashi......ki riqe wannan......ki rubuta ki ajiye......sabreen ce zata zame miki silar BANKADA!" Tana kaiwa nan saita kashe wayar ta azata saman cinyarta tana ci gaba da lullube fuskarta

"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" Ta dinga maimaitawa,tsanar uwa da danta duka suna turereniya cikin zuciyarta.

Ko da amna ta dawo abinci kawai taci ta fara list na abubuwan da zasu buqata lokacin tafiyar da abinda zasuje dashi. Ba wani abu data tofawa amna sai idanu da take binta dashi. Ba qaramin jarumta tayi ba da take iya binta da murmushi ba,gaba daya ganin abun take a wani abu maras yuwuwa,ita ba ahalinsu bace,bata kuma tunanin zata zama ahalin nasu.....hasalima gaba daya lissafinta yafi karkata ga qarawarta gaba kafin sukai ga dawowa daga yawon qasashe hudun da suka tsara zasuyi,kowacce qasa zaman sati guda zasuyi,ciki kuwa harda umra data zame musu dole duk lokaci irin wannan.

Dukka maganganun sabreen sukayi mata tsaye a rai,a daren ranar duk inda ta juya furucinta ne ke mata kai kawo a rai.

Tanaso jin rauni game da yarinyar yana sauko mata,amma wannan dakakkiyar zuciyar da shedaninta dake gefe suna gaya mata

_karamar halitta irin ta mace......yarinya qarama me qananun shekaru bai kamata taga rauninki ba.....bai kamata ace itace taci galaba samanki ba_. Abu daya ta kasa samun aminci akan yarinyar shine
'Yiwuwar aikata komai". Ko ba'a fada ba ta sani......sabreen zata iya aikata komai,tana da taurin zuciya da qwarin zuciya dama zarrar da zata iya yin komai.....wannan zarrar tata ita taja hankalinta ta zabota zuwa ga aikin da bata taba kawo komai zai warware da wata irin faduwa da rashin nasara haka ba.

Tunda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba. Ta jira har sanda gari yasha,sannan tayi wanka,ta shirya kaman kullum da qasaitattar shigar nan tata dake qara mata jin izza da jin takai inda ya kamata ace takai din,saidai bata qarasa gabar da take da muradin qarasawa ba.

Wayarta ta fitar ta kira driver dinta,ya tabbatar mata yanzu haka yana cikin mota yana jiranta,kai tsaye ta dauki jakarta tana yafa mayafinta ta fice.

Dab da zata bar falon taji laila na kiranta

"Maamah" Tsaiwa tayi tana jan tsaki,don bata shirya komai ya dakatar da ita ba. Qarasowa lailan tayi,ta kuma zube a gaban maamah din. Sam tun daga waccan ranar bata iya tsaiwa gaban maamah.....magana ce ko gaisuwa zubewa takeyi a gabanta tamkar bawa da uban gidansa.

"Ina fatan ba wani abu nayi miki ba maamah?" Ta tambaya da tsananin tsoron kada ranta ya baci

"Naga zaki fita baki tasoni ko kisa an gayamin ba" . Wani qaramin tsaki maamah din ta saki,wannan abun ya fara isarta,ba wani motsi da zatayi sai yarinyar ta buwayeta. Irin wannan abun da akan fu'ad ya fada tabbas zata iya cewa tafi kowanne mutum sa'ar zuwa duniya. Ko yaya taga fuskarta ta canza takanyi kaman zata fashe da kuka,komai kuma har abinda bai dace ta sani ba game da lailan lailan saita gaya mata

"Unguwa zanje,kafin na dawo ki gyara falo din,ki hada da bedroom din,duk abinda kika gani ki ajiyeminshi inda kika ganshi,kada kibar kowa ya hauramin sama,akwai underwears dina dana cire ki wankesu ki shanya a backyard ki jira su bushe ki dawo min dasu ciki"

"In sha Allah an gama,Allah ya dawo dake lafiya"

"Amin" Ta amsa tana yin gaba. Sau tari idan taso bautar da laila sama da haka sai wata zuciyar ta gaya mata lailan kome tayi bisa jagorancin mahaifiyarta ne,wannan ya sanya take sassauta mata akan abubuwa da dama.

Tafiyar awa daya da rabi cif suka fara gangarawa mummunan jejin,sai da suka sake kashe wata awar sannan suka isa. Daga nesa ta sanya driver din ya sauketa,sannan ta tattare zanin tsadaddar atamfar jikinta ta fara tsallake qayoyi da busassun tsirrai tana wucewa ciki.

Gurine da zaiyi wahala kaje ka taras d wani duk da tarin al'ummar dake zuwa wajen a kulli yaumin neman duniya,tamkar sun manta da wata rana da zaa shimfidesu babu wannan ruhin daya zama masarrafi na motsinsu da kai kawonsu izuwa gurare daban daban.

Ba wata kafa a jikinta da bata fitar da gumi sanda take zaune a gabansa tana jiran bayanansa na qarshe. Da qyar ta samu ya ganta.....don sharadinsa ne baya aiki biyu akan matsala guda daya.


"ZANGON NASARAKI guda daya ya rage miki......BANKADA zata sameki.....tonon asirinki zai fara daga yanzu zuwa kowanne lokaci.....zangon nasararki zai iya narkewa ya dulmiya sanadin hakan!!!" Ya furta da wata irin murya maras dadin amo.

Dukkanin 'ya'yan hanjinta taji sun tattara sun cure guri daya,idanunta suka qara girma saboda wani sabon kalar tashin hankali da bata taba jin makamancinsa ba

"Kanaso kacemin itace zatayi nasara a kaina?!!!"

"Me muka gaya miki wancan karon?!!!!......" Wasu muryoyi da tafi tsammanin sun kusa guda goma sukayi amsa kuwa a wajen kafin bokan ya karba

"KINYI GANGANCIN ZABOTA......SAIDAI TAURARONSA DA NATA TAURARIN KADAI SUKA DACE......ITACE KADAI MAHADIN AIKINKI........zabi biyu gareki.....ko ki kasheta duk wani burinki ya dulmiya ya koma mafarki......ko ki barta ta rayu kina kallonta kuma naki burin shima yana raye amma babu wata dama ko hanyar cikashi.....zan miki wani aiki guda daya......amma daga kansa!....ina me gargadinki kada ki kuskura ki sake dawomin akan matsalar data shafesu.......aiki yayi kyau ko akasin haka......".

"Na gode da wannan dama daka bani.....na tare dakai su dafa maka" Ta fada jikinta yana rawa da jin qarin dama guda daya,abinda a tarihinsa bai taba ba maimaicen aiki.

"Zaayiwa na tare dani da ma'aikata yanka......zasusha jini wadatacce da zasuyi aikin jinkirtawar tonuwar asirinki........yayin da zangon nasararki ya kama......nan da kwanaki goma sha hudu zuwa ashirin da daya......kiyi duk abinda zakiyi wajen ganin muradinki ya cika......ke zaki yiwa kanki wannan aikin.....mun miki alfarmar samun jinkiri kadai.....amma ki sani tabbas RANAR HASARA DA RANAR TABEWA TANA NAN ZUWA.......DOLE KI FUSKANCETA DA DUKKANIN ZUNUBANKI.........KIYI NESA NESA DA MATSANTAWA TAURARINTA........BA NASARA TA KUSA KO TA NESA......NATA ZANGON NASARAR YANA DAB DA FADOWA HANNUNTA".

Duka bayanansa bai wani dameta ba......zangon nasararta da damarta guda daya daya tabbatar mata ita tafi komai yi mata dadi. Kudade masu kaurin da suka haura million hudu ta zube masa,sannan ta fita da baya da takalmanta a hannu ranta fes,tana gayawa kanta dogon zangon tunani ya zame mata dole don samun kyakkyawar mafita.

Tabbas ta kowacce fuska tana da buqatar barin sabreen gidan koda itace murfin nasararta.......gwara tasan yadda zatayi ta maye fareeda da ita a madadin cikar burinta.


&Hadith yana daya daga cikin karatuttukan da suke mata dadi qwarai. Sau tari idan suna karatunsa da rumaisa yafi kowanne littafi daukan musu lokaci.

Ko a yanzun da take zaune tana bita amna na zaune a gefanta,sunata hira da anni wanda rabinta kusan na tafiyarsu ce jibi,lokaci lokaci kuma da tsare tsaren abinda zaa gudanar da bikin farouq.

"Anni....gata karatu take,ki mata magana don Allah" Ta fada a narke. Duk da sabreen batasan akan me amna ke magana ba,amma sai data daga kanta da sauri. Tana balain jin kwarjinin matar da ganin kimarta,daidai nan amnan ta miqo mata wayar tana danne dariyarta hadi da hade hannun alamun am sorry. Da idanu ta nuna mata zan kamaki sannna ta karbi wayar tana sakawa a kunne

"Barka da dare d'iyata.....ina fatan dai bata miki shirme?"

"Barka da dare anni....." Ta fada tana murmushi

"Ya jikin naki?...ina fata dai kinji sauqi?"

"Alhmdlh na warware....anni na gode"

"Ba godiya ai tsakanin uwa da d'iyarta......nace ba,nasan halin yarona sarai,duk sanda tafiya irin haka ta kama saidai a tayashi shirya kayanshi shi kansa,nace idan akwai wani abu da kuke buqata na tafiyar kiyi magana....karki daukeni suruka ameenatu ni mamarki ce,ki rubuta sai a kawo,idan kuma ta amnan zakiyi to saiku fita tare goben,saiki masa magana" Kunya ta sake kamata,bangare daya kuma tana jin wani iri. Ta aza an soke zancan tafiya da ita ne kwata kwata,don tun randa akayi maganar da amnan tace BB farouq yace ta bada details dinta da sauransu bata sakejin komai akai ba.

"In sha Allah anni......Allah ya saka da alkhairi ya qara girma"

"Ameen ameen,a baya magaji ne yake hada masa necessary abubuwan da zai tafiyar dasu.....ina fata yanzun zaki maye gurbin hakan?" "In sha Allah" Ta amsawa annin tana jin wani qaton nauyi ta aza mata akai,daga nan ta miqawa amna wayar ta maida kanta kan karatun.

Amma kuma sai karatun ya gagareta,saboda batasan yadda zata cika maganar anni ba. Batason haduwa dashi kwata kwata,hakanan idan batayi yadda annin tace ba zai zama kaman rainuwa,kuma amna da akayi a gabanta ba zataji dadi ba.

Dabara ce ta fado mata,ta rufe littafin tana duban amna data gama wayar.

"Kina da number magaji din?"

"Eh ina da" Amna ta amsa mata

"Faka faka kiramin shi" Ta furta tana gyara daurin dankwalinta. Sosai abun ya yiwa amna dadi,ta kira magajin ta hadata dashi.

"So nake nasan da meye da meye ake hadama boss idan zaiyi tafiya?". Tayi maganar tana miqawa amna hannu alamun ta bata takarda da abun rubutu.

A ladabce ya dinga zayyano mata tana rubutawa,har ta gama tsaf tayi masa godiya ta yanke kiran,ta miqawa amna bironta ita kuma ta miqe da takardar a hannunta,amna ta bita da kallo tana murmushi. Tasan abinda take shirin yi,zataje ta hada masa jaka tana tunanin baya nan kafin ya dawo,saidai tun daxun taga shigowarsa,kawai bata gaya mata bane tunda ta lura ba hawa saman take ba,itadai adduarta daya Allah yasa adda sabreen din bata cikin sahun shashashun matan nan da basu iya baiwa miji kulawa,duk da itadai a hakanta a halittarta bataga alamun hakan ba.

Duk da tana da yaqinin baya nan,amma duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,kaman yadda numfashinta ke fita da nauyi.

Bude smart door dinsa bame wahala bane a wajenta,saboda tuntuni ya sanyata cikin sahun masu shiga kai tsaye.

Ko ina fes kaman yadda ta saba,yana fita da safe take shiga,tasan lokacin fitarsa,zai kuma wahala ya wuce wannan time din be fita ba,zata shiga ta kintsa komai. Duk da baya barin komai sai dan goge goge da qananun datti,bai taba barin underwears dinsa ba koda kuwa singlet nashi bata taba gani ba,abinda ma ya sanya mata qaramar nutsuwa kenan.

Bedroom dinsa ta wuce,tayi kuma amfani da details din da magaji ya bata ta dinga fiddo da komai,sai data hada shi tsaf sannan ta rufe briefcase da luggage din ta ajiyesu a gurbin da ta tabbatar zai wahala ya kasa ganinsa.

Yadda batayi zaton ganinsa ba haka shima baiyi wannan zaton ba. Batasan ya shigo saman ba kwata kwata. Ta zare idanunta daga cikin nasa idanun da yau take ganin kamar sun rusuna sunyi kuma laushi,can qasan ranta tana mamakin yadda ya balbalawa kansa A.c tayi qau a falon,abinda iya saninta dashi ba sabonshi bace. Idan kaga ya kunnata ma to tabbas ranan ana zafi,ko kuma bai samu irin fresh air din da yakeso ba.

Kanta ta dauke sosai ta fara takawa zata wuceshi,yau daya sai taji tana jin shakkar giftashi,koda kuma bata kalleshi ba tana jin kaman idanunsa a kanta suke.

Allah ne kadai ya sauko da ita,don bibbiyu bibbiyu take hada stairs din tana saukowa,tana jin kamar zai biyota yayi jan masifar daya saba,tana kawowa bakin bedroom dinta ta saki numfashi tana danne qirjinta.

Sai data bacewa ganinsa ya dauke kansa daga wajen yana maida hankalinsa kan wayar huda dake hannunsa wadda yakewa kallon wayarta. Tun ranar yake sake zurfafa bincike cikin wayar......amma kullum abinda zai gani a ciki taba masa rai yakeyi. Tarin massages na nuna zallar soyayya da kewa,zuciyarsa ba irin abinda bata raya masa yayi ba amma yana danneta d wani irin qarfi dashi kansa baisan yana da ita ba. Abu daya ke taka masa burki,cases din da zaiyi tafiya ya bari,amma ya tabbatar zuwa sanda zai dawo komai yayi settling......a lokacin zata kwashi kashinta a hannu,zaikaita ainihin kurkukun da itace asalin wadda ya tanadar mata.

Qarar wayarsa ya janye hankalinsa daga wancan tunanin,ya dauka yana dubawa don kusan duka saqon da zai shigo masa me amfani ne.

_ko a kusa ko a nesa duk inda zaka ina tare da kai,toshe kirana bawai yana nufin toshe soyayyarka daga zuciyata bane........ferree dinka ce_ ta saka sign na kiss da love daga qasa

Matse wayar yayi a hannunsa,yanajin bai taba jin tsanar wani abu a duniya ba irin yarinyar......tabbas tace zataci gaba da bibiyarsa nan da sati daya zai nema mahaifinta yayi magana dashi. Y janye diyarsa ya siya mata girman da ita ta gaza siyawa kanta.

&A daren washegari zai shigo mata amna tayi kawai da wata irin luggage da itadai idan tace ta taba ganin akwatin daya mata kyau irin wannan tayi qarya. Komai da matafiyi zai buqata an kammala mata shi an damqa mata a hannu. Wayar amna ta karba tayi kiran titi bayan ta zuba numbers din titin data rubuta ta aje saboda gudun bacewa. Har yanzu tana mamakin yadda wayar huda ta sake bacewa a dakin,saidai zuciyarta tanata qarfafa mata zargin shine ya sake daukewa.......don tun randa wancan incident din ya faru bata sake ganinta ba.

Magana sosai sukayi da titi din dasu huda,ta kira momma bahijja ma ta mata sallama,hankalinta ya kwanta sosai data samu yaqinin cewa kwana uku da tafiyarsu suma zasu isa mali,kunya tadan kamata sanda momma din ke tsokanarta honeymoon zasuje?

"Saura satittika kadan ya rage nima na biyo bayansu zuwa tushen mahaifiyata momma" Ta furta a ranta.

Sosai taji zuciyarta sakayau,hankalinta ya sake kwanciya,amma saita dinga jinta cikin wani kadaici,tana jin kamar ita daya tayi saura a Nigeria,saidai kuma tana jin sassauci idan ta tuna itadinma kwanaki kadan zata iskesu su sake shimfida sabuwar rayuwa me inganci tare.

_hmmmm,nace ko dama zata bada daman hakan?_


*_MALDIVES........_*


*KOMAI NISAN JIFA*=ØGÜ<Øþß=ØGÜ<Øþß=ØGÜ<Øþß=ØGÜ<Øþß=ØGÜ<Øþß=ØGÜ<Øþß


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

68

*_Na muku post saboda jiran kwana biyu da kukayi,don Allah banason complain,dole zaa zo inda kuketa zakwadin>ØÏÝ<Øýß>Ø&Ý<Øýß
@&þ=ØDÞ_


_Allah don isar mulkinka,don buwayarka,don girman soyayyar da take tsakaninka da muhammadurrasulillahi,dukkaninmu bayinka ne,amma akwai bayinka dake zaluntarmu suna fitar mana da pages,Allah kafi kowa sanin yadda muke wahala,mun killace haqqinmu bamu tilastawa kowa ba akan yazo inda yake,amma suna biyomu suna zaluntarmu YA ARHAMAR RAHIMEEN KAFI KOWA SANIN BAMU ZALUNCESU BA....YA ALLAH KO WACECE IDAN BATA DAINA BA ALLAH MUN GATA NAN,MUN KAWO QARARTA KOTUNKA ME ADALCI,YA ALLAH....YADDA TAKE TARWATSA MANA KASUWANCI UBANGIJIN SAMMAI DA QASSAI KA TARWATSA NATA KASUWANCIN,ASARAR DA TAKE JA MANA ALLAH KA NINNINKA MATA WANNAN ASARAR AKAN NATA KASUWANCIN DON ISAR MUHAMMADUR RASULILLAHI A FADARKA AMEEN_




*_REPUBLIC OF MALDIVES_*

*MALÉ*

*Velana international airport malé_*


Misalin qarfe hudu agogon Maldives wanda yayi daidai da qarfe takwas na dare agogon Nigeria private jet din mallakin Muhammad fu'ad jadda wanda ke dauke da sunan JADDA WINGS ya sauka a babban filin tashi da saukan jiragen sama na velana international airport dake babban birnin Maldives wato malé.

Daidai sanda jirgin ya kammala tsaiwa gaba daya sabreen ta sauke numfashi a hankali tana lumshe idanunta gami da budesu kusan lokaci daya.

Wani abune da take ganinsa tamkar cikin mafarkanta,gata cikin qasar da koda sunanta sai lokuta d'aid'aiku ta taba jinta ballantana mafarkinta yakai ga zuwa qasar.

Tun daga kano zuwa lagos da suka sauka na wasu mintuna,kafin daga bisani jirginsu ya taso zuwa Maldives tasan tabbas duniya cike take da yalwa da fadi. Abu guda daya daya dinga bata sha'awa.....wanda ita kanta batasan abun na burgeta ba,sai data samu kanta tana fatan

"Allah yasa nan gaba kadan rayuwarmu ta kasance kaman haka....ni huda nadra haneefa". Bawai kalan arziqin jadda family bane abinda yaja hankalinta da gasken gaske ba....a'ah.....kalar qaunar juna.....bawa juna kulawa da kuma soyayyan juna da take gani a idanunsu irin na zallar 'yan uwantaka.

A tsakaninsu zata iya cewa ta zama 'yar kallo kome daukan rahoto,duk kuwa da cewa sunata qoqarin jefota cikin hirarrakinsu da kowacce magana data shafesu. Sau tari saidai ta murmusa kawai,tana karance da halayen kusan kowa a cikinsu.

Farouq nada tsananin kirki......yana da nuna kulawa da soyayya da 'yan uwansa,yana da wasa da dariya da 'yan uwansa.....amma mugun muskili ne kuma hutsu idan baiga dama ba.

Saddiq yana da zuciya,yana da saurin fushi amma kuma yana da saurin saukowa,yana da kula da damuwa qwarai da gaske da al'amarin 'yan uwansa.

Musaddiq dataji sunata waya dashi kafin tashin jirginsu,wanda a yanzu haka shi yayi landing ma a Maldives din,bazatace ga hali ko dabi'arsa ba,illa abu guda daya data lura. Shima me yawan nuna kulawa ga 'yan uwansa ne da damuwa dasu.

Sai oga boss muhammad fu'ad jadda.........shi kadai halinsa yasha banban ta kowacce fuska da 'yan uwansa......ta fuska daya sukayi musharakar halaye,wato ta fannin qauna ga 'yan uwansa......wata irin qauna da a fuska ba zaka ganta ba,hakanan a fili ba zakaga wani alamun damuwa ko kulawa da lamarin kowa bama tattare dashi,saidai kuma yana ankare da motsin kowa da kai kawonsu. Wani irin bahagon miskili da koda magana zaiyi saika rantse ya lissafe take,bayason lafuzansa kuma su qare,kaman tattalinsu yake,baya magana ya maimaita maka,kaman yadda bai fiya nuna damuwa ko zafafawa akan al'amura ba. Zaka dauka bai damu da komai ba,baya kuma kula da komai,saidai kaifin lurarsa akan komai tasha banban data kowa. Yana da wani irin fahimtar komai da kowanne motsi dake kewaye dashi,yana da kaifin lissafi,dogon tsinkaye da nazari kafin yayi magana. Ba'a kan komai kakeji yayi magana ba,ba kowanne abu bane zai kalla yace wani abu ba koda yana sane da wannan abun.

Dukkaninsu sunyi tarayya akan abu guda wato son anni......kowa a cikinsu wani unique love yake nunawa annin da qauna me tsananin yawa......takan shiga lissafi me zurfi idan maamah ta fado ranta,amma kuma idan ta tara da 'yan maganganun da amna ta fara yi mata,sai taga lallai komai yana da nasaba da wannan.

Ko yanzun ma da jirgin ya tsaya,saddiq nata fiddo musu luggage dinsu daga overhead compartment jordan na sauka dasu,shi kam sai a sannan ya rufe system dinsa da batasan abinda yakeyi ba a ciki tunda jirgi ya daga.

Tun zamansu daga lagos har kawo yanzu tana gabanshi. Tana jin farouq daya gaji da yadda ya bata hankalinsa yace

"Yallabai hutu fa zamu tafi,tun yanzu ka fara bata tsarin hutun?,ya kamata komai a ajjiyeshi a side ko?". Kai ya girgiza,kaman bazaiyi magana ba,sai daga baya ya daga idanunsa ya zubewa farouq dinsu

"Ba zaka gane ba.......koda na tafi hutu bazai yiwu har ta internet na tafi offline ba" Baki farouq ya tabe yana jinjina kansa,can qasan zuciyarsa shi yasan me yake tsarawa.

Jordan ne ya qarasa ya tattare masa dukka tarkacensa,yayin da shi kuma ya miqe yana zube hannuwansa cikin aljihun 3pices suit din jikinsa yana takawa gaban anni.

Duqawa gabanta yayi kadan yana gyara mata zaman takalmanta da take qoqarin sakawa.

"Ina fatan zaman jirgi bai saka ciwon qafarki ya tashi ba?" Murmushi ta saki,tana fatan yadda yake da tsananin kulawa a kanta taga yana yin sama da haka akan matarsa.

"Alhmdlh......last checkup din da mukaje ai sun bada dokoki,kuma na kiyaye alhmdlh......je ka duba matarka" Ta fadi tana miqewa hadi da ambaton bismillah.

A kunnen sabreen anni ta furta hakan,numfashinta yadan tsaya na wucin gadi,ta danyo rolling idanunta tana miqewa. Batason kowanne abu da zai hadata dashi ballantana ya gasa mata magana. Maganan daya gaya mata kafin tasowarsu daga lagos kadai ya isheta basai ya qara mata da wani ba.

Cikin ma'aikatan airport dinne,wani a cikinsu yaketa haba haba dasu ita da amna. Itakam bata kawo komai cikin ranta ba,don bata ma sake masa ba,amna ce kawai ke dan amsa tambayoyinsa,har zuwa sanda zasu wuce sai yace

"You look so familiar madam....." Ya fada yana dubanta da murmushi. A dan mamakance ta waiwaya tana dubansa,kafin kuma tace komai ya sake fadin.

"A abuja......hotel din....."

"Stop mr man!" Dakakkiyar muryar fu'ad ta dakatar da mutumin cikin kaduwar hanji. Sam baiga isowarsa wajen ba,mutumin tun dazu yake masa kwarjini.



Please Login or Register in order to submit comment