Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare ya fara" A nan ya barsu ya gangara ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa.

Wani mummunan horo kawai yakeji farouq yayi masa na hadashi kwana daki daya da ita. Gaba dayansa sai yake jinsa kaman a birkice yake,tun yana qaryata wanzuwarta daki daya dashi ne ya sanya yanayinsa komawa hakan,har yayi amanna cewa hakanne. A dare daya tak ya kasa samin isashen bacci har zuwa wayewar gari,wayewar garin da ya tashi da ninkin rashin kuzari da karsashi a tattare dashi,fiye ma da yadda ya kwana jiya.

Kowanne motsi farouq yana ankare dashi,dariya qasan ranshi kaman zata kasheshi.

"Duk dacin ranka.....duk miskilancinka halittar mace tafi qarfinka ko kai waye......qaton tuzuru dakai sai taurin kai da kafiyan da ba inda zasu kaika?,dama can sarari ka samu,nisan tazarar dake tsakaninku ya sanya kake ganin kamar baka da wata buqata ko sha'awa irin ta d'a namiji.....wallahi qarya kake fu'ad......a wannan fannin ni kaina na sallama maka.....zan gani idan tusa zata hura huta......daga yau zuwa gobe kawai na baka,if kaci gaba da taurin kai.....nasan matakin da zan dauka a kanka" Farouq yayi dukka wannan gulmar cikin zuciyarsa yana duban fu'ad dake zaune yana kurbar maca and ginseng tea. Kaman baiso yake daga cup din zuwa bakinsa,shi kansa,ranshi a jagule,baiso irin wannan yanayin ya tasammasa a irin wannan lokacin ba sam,saidai koma meye zaya faru bayajin zai yarda koda da wasa ya hada jikinsa da ita. Jikin da akullum ya kalla sai yayita lissafin adadin maza nawa ne suka rabeshi?,adadin maza nawa ne suka tabashi?,dame dame sukayi da ita?. Yana da bala'in qyanqyami na fitar hankali,wannan qyanqyamin ya sanya bayajin shikam ko mata biyu zai iya aura,gwara ya tattara mutuntakarsa a muhalli daya. Uwa uba wani irin kishi ne dashi,ba kuma wai yanzu ba,tun tale tale zai iya cewa da kishin ya tashi,dashi aka halicceshi. Baisan maruka nawa yasha daga hannun maamah ba sanda take kawo maza gidan abokan kasuwancinta da suke siyan shaddodin da ta soma business dinsu ba,baisan adadin yawan dukan da yasha a kansu ba......saboda muddin zaka sanya qafarka a gidansu,to shi kuwa zai kafe ya cake a qofa ya hanaka qarasawa ciki.

"Babanmu baya so......ya hana maza shigar masa gida,ka koma ka aiko qanwarka ko yayarka" Wadannan sune lafuzzansa a yayin da fuskarsa kan cika da wani irin fushi da zafin zuciya. Kusan baki suke sakewa,kusan duka duka shekarunsa a sannan ba zasu wuce goma sha daya ba,amma zuciyar manya gareshi,zuciyar data kubuta daga dukkanin tsoro saboda kare martaba da haqqin mahaifinsa. Wani lokacin idan ta jawoshi ta daka ta daka,abbansa dake daki kwance yana jiyya shi zaita kiransa,shi zai lallasheshi,yakan ce

"Komai na duniya me wucewa ne me babban suna.....komai kuma haquri ne yake zama silar cin nasararsa......ka daina bari ana tabamin lafiyarka me tsadar nan kaji?" Sau tari duk kalan dukan da zata masan ba kasafai ya fiya kuka ba,duk da cewa duka ne ba kadan ba,wani lokaci harda abinda bai kamata ayi dukan ba. Idanunsa saidai suyi jajir,yayita hadiyar yawu da wani irin tsauri

"Abba......gidanka ne fa,ta yaya kana kwance zasu dinga tsallakowa suna shigo maka?" Murmushi yakan yi,duk da yakan tsinci ciwo cikin murmushin nasa

"Watarana sai labari me babban suna". Ire iren wadannan hirarrakin da abbansa har yau ya kasa sabawa da tunasu,har yau ya kasa jin Normal ne a rayuwarsa,har yau kansa baya iya jure tunasu,duk sanda sukazo masa sai yaji kaman kansa zai tarwatse,sai ya sakejin wani abu yana sanya nisa me tarin yawa tsakaninsa da maamah din,yakan ji kaman bazai iya qara idanu ya kalleta ko ya mutuntata ba......amma ta wani fannin.........uwa data cancanci a kirata mahaifiya irin ameenatu anni......itace ke riqo da hannunsu a ko yaushe,ta kuma qarfafesu da yi mata biyayya. Rana daya daya fahimci ta fara sana'ar dalilin aure,adadin maza da matan dake kai kawo a gidan suka dadu,a ranar ya yiwa wani mummunan rotsen da da qyara aka kashe maganar a police station. Ranar nisan kwana ne kadai ya kawoshi yau da ake magana,don ta sakashi a daki ne ta masa wani irin duka da sai da ya daina numfashi,tun abban nasu dake daga kwance ba daman tashi ya ceceshi yana kiran sunanta gami da qoqarin dakatar da ita,har yawun bakinsa ya dauke tsaf,yayi shuru ya zubawa sarautar Allah ido,yana jin sautin dukan da maganganunta,amma baya iya jin koda tarin muhammad. Yasan halinsa.....sha wuya ne dake iya shanye zafi da tsananin duka,yasan kowanne irin nau'in azaba take masa bazaiyi magana ba.

"Me shegen baqin hali irin na ubansa.......baka isa ka hanani neman kudi ba wallahi,yadda talauci ke neman kai ubanka ramin qabarinsa tun lokacinsa baiyi ba......ni bazan zauna talaucin yayi ajalina ba". Qarshe dai musaddiq ya aika ya dinga zuba masa ruwa kafin ya farfado.

Ta dauka zai rusuna daga ranar,amma sai taga kaman ma bashi ta daka ba,sai ya canza sabon salon kora da hali wajen yayyanka musu takalmi,karta mota da sace tayoyin motar ko na babur.......still marasa haquri a cikinsu police station suka.kaishi da qyar ta karboshi,zuciyarsa kuma na a tsaye bai rusuna ba,dolen dole ta tattara ta canza sana'a,waccan din saidai tayi a wani wajen daban amma ba cikin gidansu ba.

Ajiye roban maca root din dana ginseng farouq yayi yana kallonsa.

"Amma yallabai......wadannan abubuwan biyu kaman suna enhancing libido fa.....and..... ". Wani kallo fu'ad ya watsa masa da idanunshi da sukayi laushi qwarai,ya miqa hannu yana fusge container din ya ajiye a gabansa

"Baka lura kuma yana boosting energy ba?" Ya fada cikin jin haushi. Dariya sosai ya qunshe farouq din yana gyada kai kaman qadangare

"Yes.....yes na gani,kaman kai kenan da kayi loosing energy dinka ko?.....wannan bazai boosta maka komai ba dude.......you need a......."

"Zip it" Ya katseshi da kakkausan kallon nan nasa. Shikam farouq bai gama maganansa ba,baiga abinda zai sanya a hanashi fadin abinda yai niyya ba,sai ya janye baya yana daga kafadu.

"Duk wani abu da zai maidaka namijin gaske you're Comsumpting......but ka kasa kunna engine din kadan......" Bai qarasa ba ya cire spoon din cikin mug din ya jefeshi dashi,abinda ya sanyashi kasa qarasa maganan......amma kuma ya kece da dariya,wanda shigowar anni parlor din ya dakatar dashi daga dariyar.

"Farouqu.....zoka miqawa muhammadu ya dubamin wannan address din.........wata qawata ce muna magana dazu ashe sun shigo suma". Karbar address din yayi ya kalla,bai gane gurin ba don haka ya miqawa fu'ad.

"Few kilometers ne tsakaninmu,zaki je ne anni?" Ya tambaya yana dubanta.

"Eh amma sai wajen gobe nake tunani.....tunda yau kaman naji amna tana fadan inda zasuje,ba zaa bar gidan ba kowa ba duk da ba wani abu bane". Kai ya jinjina ya ajiye takardar,sannan ya daga mug dinsa yana shanye ginseng tea dinsa abinsa,ba tare da ya maida kai ga kallon da farouq yaketa binsa dashi ba.

Dukkaninsu farouq ya xuba a mota suka fice. Sosai suka zaga garin,guraren da sukaje sun kusa biyar,amma duk da haka amna bata gaji ba,fadi takeyi

"Ya farouq.....don Allah mu zaga Maldives gaba daya kafin mu tafi,tunda island ne baida girma can can". Dariya musaddiq ya bushe dashi yana kallonta

"Kinsan yawan guraren da suke dashi kuwa amnee......a qalla fa gurare dari da tamanin amnee,yaushe zamu iya zagayeshi?"

"But......amma please BB,gobe ma ka fita damu,inason naci rihaakuru fish paste.......kifin Maldives please ya musaddiq" Ta fada tana narke murya.

"Ki bani cin hanci mana saina roqar mana shi,harda traditional market dinsu.......rannan naga suna saida abubuwan gargajiya sosai.......i assured zakiji dadin gurin" Maganan musaddiq ta sake gigita amnee,ta dinga roqar farouq,har sai data saka sabreen a ciki.

"Please BB farouq......a taimaki autan anni mana" Sabreen din ta fada da sassanyar muryarta dake da wani irin nutsuwa. Murmushi farouq ya saki,tana da kima a idanunsa da martaba me yawa,yana ganin mutuncinta sosai saboda yanayin nutsuwarta da kamun kanta.

"An gama tunda.matar.oga ta saka baki" Dariya ya basu dukkaninsu har ita sabreen din sai data murmusa kadan. Har yau ya kasa yarda ko sau daya da binciken fu'ad a kanta......baisan meye dalili ba,duk da ya sani shi din mutum ne mara gaggawa akan kowa da komai......amma gaba daya halayensa sun canza a kanta,bazaice kuma ga wani dalili babba guda daya ba.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 72


72



Kusan dare ya soma nisa sanda suka isa gida,basu kuma lura da hakan ba sai da suka shiga parlor din gidan suka sameshi zaune saman qananun sofas din dake a falon. Yau idanunsa suna saye cikin farin glass wanda hasken allon system din gabansa ya sake fidda hasken kwalbar glass din. Kallo daya farouq ya masa yasan ta baci,ba kasafai ya fiya amfani da glass din ba sai idan idanunsa suna masa wani iri,don yana zuqe hasken kowanne abun amfani kafin ya samu shiga kai tsaye cikin idanun nasa.

Gaba dayansu kowa sum sum ya soma shigewa cikin falon yana dosar qofar dakinsa. Mamaki ya cikata ganin har suka tako veranda din farko na gidan sunata karadi abinsu kuma cike da karsashi......amma da ganin wanzuwarsa kowa ya kama kansa.

"Sai da safe" Ta tsinci muryar farouq da shima ya kama kansa zuwa dakinsu,abinda ya sanya jikinta yin laqwas itama ta qara hanzari zuwa nasu dakin ganin kowa ya fashe daga parlor din.

A gaggauce ta shige toilet da duka kayan wankanta,tayi wankanta ta kuma shirya a can,tana fitowa kuwa ta nade saman sofa din data kwana jiya akai tana curewa waje daya cikin comforter din data dauke. Bawai sanyi takeji ba ko wani abu,kawai tanason takurawa kanta ne tayi bacci kafin ya shigo.

Bata jima da kwanciya ba kuwa taji shigowarsa,ya ajiye komai a muhallinsa ya taka zuwa toilet. Da alwalarsa ya dawo dakin,kamar jiya ya shimfida abun sallah ya fara sallolin da batasan sanda ya gamasu ba,don gajiyar da tayi yau din ya dinga sassauke duk qashin jikinta gajiya tana fita.

&W A S H E G A R I&


K'arfe hudu na yammaci dukkaninsu suna tsaye gaban motar suna qoqarin shiga,saidai gurin ya kaure da hayaniya wanda kusan qananun fada ne da musu tsakanin saddiq da amna wanda dukkaninsu bakinsu baya iya shuru.

Tuni Jordan yayi zaune mazaunin driver yana jira su kammala shiga

"Anni tayi warning na kaiwa dare......i think wancan hamman naku yakai qararku an fitar masa da mata har dare.....oya guys.....hurry up muje mu dawo" Ya fada yana dan buga seat din motar,abinda ya sanya musaddiq soma shiga yana cewa amna.

"Yau zai gane qaramin talaka ne....... Don't argue with him.......shigo auta" Musaddiq ya shiga maganan don ya kawo qarshen fadan.

Juyawa amnan tayi ta miqawa sabreen wani baqin kati da yafi kama da atm

"Matar oga.....yau ina jakanki.......ga wannan anni tace na baki,naki kudin tsarabar ne da boss ya saka miki kiyi siyayya". Bin card din tayi da kallo,ita bata taba ganin card ma irinsa ba,to amma kuma ita me zatayi da kudinsa?. Ko fitarsu jiya ma ba wani abu ta siya ba,amma duk da haka saida farouq ya cikata da siyayyar da ko budewa ma batayi ba. Hannu tasa ta karba card din kawai,ta daga qafanta tana niyyar shiga motar sautin musaddiq ya sauka a kunnenta

"Wow........kallemin guy dincan" Ya fada yana tabo sadiq

"Tashin sense" Saddiq ya furta yana kallon fu'ad dake tahowa. Cikin wani irin taku me dan sassarfa,sanye yake da wasu lafiyayyun suspenders da suka sake bayyana ainihin zallar quruciyarsa,suka kuma sake kwashe shekarunsa suka boyesu tas......saika rantse da Allah shi din sa'ansu saddiq ne.

Saman kansa homburg hat ce data fidda kyakkyawar fuskarsa da wani irin kwarjini da kwantacenn kyau da zai iya gaya maka lallai shi din ruwa biyu ne da ake kira da halfcast. Sosai kayan suka zauna masa a jikinsa,rigan na dan bayyana muscles din da jikinsa ke dashi,wannan kadai zai gaya maka qaqqarfa kuma ginannen jikin da yake dashi.

"Gayennan yana wuta.....anya ba zamu koma ciki mu canza dressing ba......kada maldivians dinnan su dauka age mate dinmu ne fa" Musaddiq ya fada sounding seriously. Dariya sosai amna ta fashe dashi tana dora kanta kafadar saddiq

"An gaya muku ya fu'ad wai sa'anku ne?,ku sallama kawai ku huta......idan kanajin babban kifi to shine.......kunga maza kun raina kanku ko?" Dungureta saddiq yayi yana janye jikinsa

"Zakiyi dariya da kyau ai......abinda ya kamata ki fara tambaya ko ki damu dashi shine dalilin da yasa ya fito.....ku koma ciki ba zaku je ba,ko ya fito ne mu fita tare kinga yau shikenan......ba sauran sakewa" Tsit dukkansu sukayi,saboda sunsan halinsa zai aikata da gaske. Kowa ya dauke wuta a cikinsu suna fargabar hukuncinsa,har zuwa sanda ya qaraso.

Da ido kawai ya yiwa Jordan inkiya ya fito daga mazaunin driver din,ya zagayo kujerar me zaman banza ta kusa da driver ya shiga yana cewa farouq

"Shiga mu tafi". Da kallo farouq ya bishi,har ya shiga ya zauna,ya daga idanunsa masu cike da kwarjini ya kalleshi yana daga waje

"Ko ba zaka tafi bane ka tsaya kana kallona?" Kai kawai farouq ya kada yana tunanin abinda ya sauya ma fu'ad ra'ayi ya aminta da karan kansa zai bisu.

Yau fitar dadinta sai taji baikai na jiya ba tun akan hanya,duk hirarsu suna kiyayewa da hayaniya ko abinda zasu fadi. Hira suke da farouq a gaban mota duk da batajin me suke fada,a haka suka isa guri na farko.

Sunyi yawo sosai cikin kasuwannin da suke da kayan gargajiya na al'adun qasar Maldives.....sunyi siyayya kaman ba gobe,duk da bata taba komai daga card din da amna ta bata ba,hasalima a cikin mota ta barshi cikin handbag dinta da bata fito da ita ba.

Gurare da yawa idan sunje zamansa yake cikin mota,dama shi din bai damu da shiga gurare irin wadannan ba. Koda sunyi tafiya guraren da yakanje gurare ne da suke da alaqa da kasuwancinsa,ko tarihi na kasuwanci ko kuma zai amfani kasuwancinsa,shi yasa yau din suka cika sosai da mamakin ganin yabi bayansu,duk da dukkaninsu kowa ya ta'allaqa hakan da sabreen ce sila.

Guri na qarshe da suka je,suna fitowa ya miqa hannu ya karba key na motar daga hannun jordan

"Zaka iya komawa gida" Yace dashi kai tsaye. Takawa yayi a hankali ya isa gaban motar,hannunsa daya zube a aljihun wandonsa,yasa hannu ya bude motar ya shige seat din driver.

Junansu suka kalla tsakanin saddiq da musaddiq da amna,mamaki ya cika kowa ganin yau hamma da kansa zaiyi driving?,wani abu da suka jima basu ga yayi ba

"Zaku shigo mu tafi ko na wuce abuna?" Ya leqo kansa yana magana dasu da miskilar fuskar nan tasa. Har rige rigen shiga suka dinga yi kowa mamaki kwance qasan zuciyarsa.

Kaman yadda kusan komai nasa ya banbamta dana kowa haka tuqinsa,driving yakeyi cikin wata irin qwarewa da nutsuwa,gudu baiyi yawa ba......haka babu laqai laqai.

"Ina muka nufa ne sir?" Farouq daya kula ya sauya hanya ya tambayeshi yana kallon fuskarsa dake a dinke tsaf. Shi kwata kwata ma guraren da sukaje kaman basu bashi walwala ba ko kadan.

"Siyar daku zanyi na qara jari" Ya amsa masa a taqaice yana sake maida dubansa sosai ga titin. Dariya sosai farouq ya saki yana relaxing jikin kujerar motar

"Hakan yayi ai......dadin abun bamu kadai ka debo ba ai" Yayi maganar yana turo p_cap dinsa gaba. Sarai ya gane me yake nufi,shi kuwa bazai kulashi ba,saboda neman wajen da zai dan sake samun relief kawai yakeyi.

Sannu a hankali suka shiga Vaadhoo island sunan dake rubuce baro baro a allon sanarwa. Ihu amna keson saki na murna amma sanin wanda ke driving bayason magana me tsauri ko hayaniya ya sanyata danne bakinta ta dole tana duban saddiq dake zaune opposite dinta. Gira ya daga mata alamun tambaya,saita nuna masa map na inda suke ta qaramin screen din dake maqale a gefansu.

"Vaadhoo.......glowing island!......sea of stars" Ta fada da wani irin farinciki daya lullbeta don sai a sannan ta lura da sun qaraso glowing island din.

"Addana.......mijinki is very incredible wollah.......kinyi dace......kin dace....he's very calm,ya iya surprise,komai nashi unique ne" Ta fada farinciki yana kamata,farincikin yau zata ga inda ruwa yake haske......yashi da qasar gurin itama ke haske tamkar an watsa taurari,wannan yana gaya musu qila ya musu booking na kwana a wannan sabuwar duniya,ko kuma zasu kai dare a wajen suka yadda komai yake gudana.

Murmushi kawai tabi amna dashi......babu wani abun burgewa tattare da yayan nata......itace dai bata sani ba. Amma kuma sai itama ta samu kanta da fara sallamawa al'amarin sanda suka isa adhaaran prestige,ma'aikatan wajen kuma suka iso suna maraba dasu,da alama sunsan da zuwansu wajen.

Da idanu kawai take bin gurin,da gasken gaske ta zama 'yar qauye tuburan. Gidaje ko dakuna zatace saman ruwa da wani irin tsari me jan hankali. Bata da sauran abunyi illa bayansu da tabi kaman yadda taga sunbi daya daga cikin ma'aikatan saman wani shimfidadden abu daya zama hanya kuma abu daya da zai hanaka tafiya saman ruwan.

Kai tsaye zata iya kiransa hotel ko gidan saukan baqi. Suka miqawa kowannensu wani dan card da komai da komai,sai amna ta daga kai ta kalleta bayan ta gama dubawa.

"Ga inda zamu zauna can.....zamuci abincin dare a nan.......zami fita sea of stars muyi kallo harmu shiga idan da yiwuwar haka.....komai mukeso zamuje mu karba......amma adda naso kwana zamuyi......inama hamma yace mu kwana?" Amna ta fada tana duban sabreen da hankalinta yake kan ruwan dake gaban door glass din. Shimfidadden ruwa ne iya ganinka wanda yake bada kalan sky blue,abun akwai mamaki yadda mutane keta harkokinsu Kai tsaye suna kai kawo kaman cikin gidajensu suke.

"Muje dakinmu adda" Amna ta fada da doki tana yin gaba,bayan ta fidda wayarta ta fara daukan hotuna da videos.

Bata yiwa kanta da kanta qoro ba,idanu ta bude sosai tana kallo,yanayin iska da tsarin wajen ya banbanta da duk wani guri data taba zuwa.

Gaba daya hankalinta a tashe yake,kaman yadda tunaninta yake a jagule waje daya. Iya zunzurutun dollars din data kashe don tsara komai,tun daga zuwanta Maldives da zamanta a wajen ba wani abu bane na damuwa muddin buqata zata biya. Bahaushe yace ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba. Ya zuwa yanzu da take zaune gaban glass door din tunani ne fal zuciyarta,tana jin kamar tayi wauta da take zaune tana lissafin zai wahala fu'ad din ya tsallake wannan island din ba tare daya shigoshi ba.

Tayi zurfi cikin tunanin daya cika mata kwanyarta taji sn daneta daga baya gami da maqaleta da kyau.

"You didn't missed your target......you hit it!" Wanda ke maqale a bayanta ta fada da murya me qarfi.

A zabure ta cire hannuwanta daga wuyanta gami da waiwayowa gareta,tana jin abun kaman mafarki,idanunta dukka a waje take dubanta

"Ki gayan gaskiya.....bazan iya jurewa ba idan kikacemin qarya kike"

"Wallahi wallahi me jadda ya shigo......but shi da familynshi ne duka,but kaman dakuna daban daban ne"

"Thank god.......ki miqawa wannan Chinese boy din wannan abun.......banason kuskure......after 30minutes zan shiga dakin,ya saka cameran daidai yadda zai nuna komai.......ya tabbatar yayi diluting tablet din a ruwa da lemonsa".

"Done!......breaking news zaya fita zuwa ga Nigeria" Ta fada tana barkewa da dariya,yayin da fareeda ta tayata da qaramar dariya mata sauti. Juyawa tayi ta fita,sai ita kuma ta soma zame kayan jikinta da gagggawa tana wucewa wata siririn hanya da zai kaita toilet.

Cikin qasa da minti goma ta fito,ta kuma tsaya a side din dressing ta soma balle wasu turaruka tana shafe lungu da saqo na jikinta,ta ware gashin kanta da kyau ta jiqashi da sassanyan qamshin turare,sannan ta bude wani jaka ta zazzage kayan ciki tana dagasu kafin ta fara shirya kanta a cikinsu.

Wasu gantalallun riga da wando ne,very skinny,ba iya jeans din ba,har rigar data sanya. Ba wani sirri boyayye ko bayyananne da Allah ya wadatata dashi da bai fito ba walau qashi ko tsoka,me tudu ko me kwari.

"Wow......wow" Taji an fada daga bayanta. Kadan ta juya tana kallonta don batasan ta shigo ba. Hannu ta watsa mata tana tambayarta alamun yayi?

"Perfect.......kome kamun kan mutum ya ganki sai ya fada......ga kuma wadancan abubuwan na aikinsu yadda ya dace.......zance zaisha banban nan da nan......fatan nasara" Ta fada tana daga mata babban yatsa. Wani shu'umin murmushi ta saki tana takawa gaban madubin,ta sake juyawa sosai a gabansa tana qarewa kanta kallo. Ita kanta ta yaba da kanta ballantana wata halittar d'a namiji?.

"Yadda bai sassautawa zuciyata ba bazan sassauta masa ba.......sai na tabbatar na zama cikakkiyar matarsa da shaidu na halas sannan zan barshi ya shaqi numfashi me kyau" Ta qarasa maganar tana daukan chewing gum ta jefa a bakinta tana duban qawartata

"Sai na dawo?" Ido ta lumshe sannna ta budesu a kanta.

"Inajin inama ace nice yau zan samu nasarar kasancewa da namiji irin muhammad jadda......koda bai aureni ba babbar nasara ce wannan a wajena......best wishes" Wani kallo fareeda ta watsa mata

"To mayya........wata miyar ai sai a maqota,babban goro sai magogin qarfe kuma" Dariya ta sheqe da ita

"Na sani qawata" Itama saita tayata tana ficewa zuciyarta fes yau din.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 73


73


Karo na uku ya sake daukan cup din yana kurban tataccen ruwan strawberry din da shine abu na farko daya soma zaba akai masa. Ya maida cup din ya ajiye yana zare belt din suspenders dinsa. Sosai gurin ya masa kyau ya kuma qawatar dashi,banda annin da suka baro a gida ita daya ba shakka ba abinda xai sakashi qin yanke hukuncin kwana a wajen,amma ko iya hakan ma nan da eleven yasan ya samu refreshment din da yakeso ai.

Mamaki ya cikashi jin an murda qofar an kuma shigo,ya waiwaya yana tunanin saddiq ne ko musaddiq,saidai kuma fuskar daya gani tasha banban da fuskokinsu gaba daya.

Da kanta ta fito don karbawa amna grilled fish dinta don girmamawa ga yarinyar yadda take kimantata da ganin girmanta,amnan tana da wani irin kirki da sauqin kan da yake bawa sabreen mamaki,don haka tace

"Zauna addanki ne zata amso kifin nan da kiketa kwadayi".

A gurin ta samu musaddiq shima zai karba nasa order din,wani tsari ne dasu akan grilled fish......zaka je wajen da kanka,zasu nuna maka inda kifayen ki ninqayarsu cikin ruwa ba tare da sanin kwanakinsu qayyadaddu bane,zaka nuna irin kifin da kakeso take a ciroshi a

Please Login or Register in order to submit comment