Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai take mata yanayi da hudan.

"Yaushe kika shigo?,afwan ban sani ba ina ciki ina wanka" Ta fada tana neman gefan wata kujerar daban ta zauna. Da murmushinta tace

"Adda sai an miki uzuri,matafiyi ba'a rasashi da gajiya a jikinsa,ni har zan kunna wayata ma na duba wani assignment kafin ku samu fitowa" Kyawawan fararen idanunta sabreen ta fiddo waje.

"Haba dai,ya zaki zauna kiyita jira,da kin qarasa kinmin magana ai". Bakinta ta rufe da tafin hannunta

"Kinaso hamma ya ballan qafa?,ba'a shiga shiyyar dakinsa direct ai,BB farouq ne kawai ya isa". Tabe baki tayi a fakaice,can qasan ranta tana fahimtar tsananin izza gareshi da shegen mulki.

Fara sako mata zancansa da tayi yasa sabreen miqewa cikin qarfin hali da son nuna komai lafiya

"Bari na baki ruwa kisha"

"Am full adda.....saidai na rakaki kitchen naga kaman kitchen zaki shiga" Kafada ta daga da murmushi

"Alright.....muje"

"Yau hamma za'ayi full da abincin addana.....yadda yakeson abinci me dadi na tabbatar adda na ba daga baya ba.....in fact ma tunda har kikayi nasarar samun hamma na na tabbatar komai kin hada" Tayi maganar da dariya dariyar tsokana. Bata ce mata komai ba,tadai qoqarta sauke mata murmushi kawai.

Sanda suka shiga kitchen din duk sai taji ta takura,ta rasa ta inda zata fara,saboda idan maganar qwarewa ake ta fannin girki tasan bata cikin jerin wadannan matan,infact ma ita ba gwanar shiga kitchen bace sam.....to ina ma taga time?,tana ta abinda qannenta zasuci susha su lulluba sutura,suyi magani idan lalura ta taso?. Tasan huda ta tsere mata sosai ta fagen iya girki,don tun tana fita tana barinsu hudan tana musu tsumburin burin har tazo ta qware.

"Kaman ya kamata kiyi surprising hamma na ko?" Amna ta fadi da murmushi tana duban sabreen. Kallonta kawai tayi kallon dake nuna alaman tambaya,sai amnan ta daga kafada

"Gift dina na yau zan gaya miki best food nashi da daddare.....but nima zaki bani tukuici ki gayamin sirrin skin dinki adda don Allah?" Ta qarasa fada a shagwabe. Abun dariya yaso bawa sabreen saidai batayi ba illa murmushi data saki,ta kalli fatar tata ta kalli amna,ita bataga wani kyau da fatarta tafi ta amna ba

"Seriously adda kina burgeni at the first time dana fara ganinki.....kawai naji jinina ya hadu da naki" Ta fadi da gasken ta yadda a furucinta zaka fahimci da gasken take.

Kusan tana zaune amna ta hada duka ingredients din na kalar abincin. Ta miqe tana daura apron data gani tana bawa amna daya,sai qararrawar dake kitchen din ta dauki tsuwwa.

Amna ce ta duba,saita waiwayo ta kalleta

"Kira ne daga bakin gate" Tayi maganar tana miqa mata wayar

"Ki daga" Tace da ita,ba musu ta saka a kunne,bayan wasu sakanni ta dawo da dubanta kan sabreen

"Wai baqi ne dake.....zuwaira daga wajen hajiya mariya maamah". Maganar taji ta bugu qirjinta don tazo mata kamar a bazata,sam ta mance da issue dinsu,sai ta fara zare apron din tana cewa

"Kice a barsu su shigo" Yadda ta fada mata haka ta gaya musu,ta zare apron din ta ajiyeta ta soma dosar kitchen din tana cewa

"Ina zuwa amna"

"Ba damuwa adda" Ta amsata tana matsawa kitchen din don ci gaba da aikin.

Kasa tsaiwa tayi daga cikin parlor din,ta taka har qofar qarshe wadda daga ita sai balcony din da zaka sauka zuwa farfajiyar gidan. Tsaye tayi kawai riqe da qofar,ba abinda ya hanata hango wajen sai lafiyayyen curtain din daya raba tsakaninsu.

"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta fara rasa falon kafin ta bayyana Laila na biye da ita a baya da luggage dinta dake da girma,tana takawa d'ai d'ai,tana sake ganin alatun da aka xubawa gidan,sai take ganin wancan zuwa bataga komai bama.

"Wa'alaikumussalam" Ta amsa mata idanunsu yana haduwa waje daya dana laila.

Wata faduwar gaba ta saukarwa lailan lokacin da idanunta ya shiga cikin na sabreen dake tsaye tana jiran shigowarsu

"Kambu.....who's she?" Ta samu kanta da furtawa a qasan zuciyarta saidai kuma labbanta a sarari ma rawa sukeyi.

Yanayin kallon da lailan ke mata sam baiyi mata ba,a nutse da wani irin jan aji ta debe kallonta daga kan lailan tana maidawa kan zuwaira dake qoqarin gaidata

"Basai kin tsuguna ba......ta nan ga qofa nan a nan din akwai dakuna a ciki,ku zabi duk wanda yayi muku" Ta amsata a taqaice don ko tsaiwarsu a wajen sai taji bata qauna. Tasan da qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dinga yi cikin gidan


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 32


_Daga abdullahi dan umar R.A yace."manzan Allah S A W ya hana auren shigaari,shi kuwa auren shigaari shine,mutum ya aurar da d'iyarsa ga wani,bisa sharadin Shima wancan zai aura masa tasa 'yar,kuma babu biyan sadaki a tsakaninsu(musanye kenan)_

_bukhari da muslim ne suka rawaito_

___________________________

32


Tasan qofar ne cikin ranakun zaman kadaicin data dingayi cikin gidan da kuma Yanayin wajen kuma tasan guri ne baqi na kusa bayan boys quaters da gidan ya mallaka na musamman da yake daga can bayan gidan. Bata da matsala dasu,koda dakunan hallway suka zaba kuwa,don kowacce rana a lissafe kwanakinta cikin gidan suke.

"To.....to madallah......bari mu qarasa" Xuwaira ta fada tana wucewa gaba laila tana biye da ita. Duk wani taku daya biyu na lailan saisun hada idanu da sabreen din wadda ke tsaye yana karantar yanayin kowanne a cikinsu.

Dauke dubanta tayi,sai ta koma saman kujerar falon ta zauna kawai yanayin jikinta yana neman sauyawa.

"Assalamu alaikum" Muryar zuwaira ta sake ratso falon. Idanunta ta daga a hankali tana duban zuwaira sanda take takowa falon riqe da waya a hannunta fuskarta a sake

"Ranki ya dade.....hajiya nason ganawa dake" Tayi maganar tana miqa mata wani qaramin akwati da sabreen din ta kasa amsa sai binsa da kallo da tayi. Daya hannun waya daya akwati,kuma dukkaninsu idanun zuwaira suna gaya mata ana da buqatar karbar kowanne.

Cikin kwanyarta taji ana umartarta data karba,ba wani laka a jikinta ta karba dukkaninsu

"Sirri yana da matuqar muhimmanci......hajiya nason sirri matuqa" Ta tsinci muryar zuwaira tana gaya mata. Idanu ta waiwayowa ta zubawa zuwairan,sai kawai ta dauke kanta tana nufar hanyar hallway don komawa dakinta.

Kaman ana jira ta shiga dakin wayar tahau kadawa,ta zubawa sunan da zuwaira tayi saving dashi wato hajjaju. Tattaro dukka wata dauriya tata tayi,ta hadiye wani yawu me kauri sannan ta daga kiran ta sakashi a hands free hana ajiye wayar saman cinyoyinta.

"Ka kula da ita.....huda kuje ya baki magani kisha kafin ki kwanta.....sannu qawata". Abinda kunnuwanta suka fara jiye mata kenan wanda ya sanya tsigogin jikinta tashi. Ta runtse idanunta tanajin kamar an daukk guduma an kwada mata saman kanta.

"Huda kuma?" Ta motsa labbanta tana furtawa a wahalce. Murmushin maama ne ya soma riskarta kafin tace

"Eh,huda.....ko bazatayi lalura ba?......kowanne sakaci da zakiyi akwai sakamakonsa kan halittar da kika fi so fiye da komai da kuma kowa......"

"Bani huda din" Ta fada kanta tsaye da wani irin yanayi me kaushi. Wata qaramar murmushi me kama da dariya ta saki

"Da wuri haka?,zabin cetonsu ai yana hannunki tunda na gabatar miki da dukka kayan aiki.......bansan me yasa kika yanke sadarwar dake tsakaninmu ba.....saidai koma meye wannan ba damuwa ta bace......kowanne ganganci kuskure ko sakaci sakamakonsa rubutacce ne a nan......"

"Idan kikayi kuskuren cutar da ko farcen daya daga cikinsu ne......to lallai ba shakka ba mallaka miki danki zanyi ba......zan sadar dashi da kabarinsa ne,zan mallakaws barzahu shi a madadin ki" Sabreen ta fada cikin tsawa da wani irin birkitaccen sauti daya ratsa maamah,taji kuma har cikin jikinta da gaske ta fadi maganar. Ta danyi jim kadan tana jin wata shakka tana ratsa ta,sai kuma ta saki wata dariya

"Bismillah mana......indai har kina ganin hallaka mutum kamar muhammad jadda abune me sauqi....."

"Akwai abinda yafimin wannan sauqi?.....aikinki ya ninka shi wahala sau dubunnan da bazasu qirgu ba.......idan naso a safiyar gobe za'a wayi gari da sanarwar jana'izarsa hajiya maamah.......saboda haka ki kula......akwai kadarata a hannunki......a nan kuma akwai ruhinki dama kadararki gaba daya a tare dani" Daga wannan ta yanke wayar.

Zare wayar daga kunnenta maamah tayi tana kallo. Wani irin mamaki da tsoro yana kamata,wacce irin yarinya ce wanannan?,wadda bata tsoro ko shakkar duk wani abu girman tsoron dake tattare dashi?.

Gabanta yayi mummunar faduwa sanda ta tuna zancan idan taso za'a sanar da jana'izar fu'ad din a gobe. Ta motsa da wani irin hanzari ta miqe sai kuma ta koma ta zauna. Waye zata gayawa?,shi fu'ad din?,tace yakula da za'a iya kasheshi?,to waye zai kasheshin?,ya kuma zatayi masa bayani akan yadda akayi ta sani?,ya daina cin abinci?,wannan kuma shine burinta babba a yanzu ya karbi abinci daga hannunta don samun cikar burinta,ta yaya zata sanya idanu akan wani abu daban da zata shirya wanda zai sauka daga kan tsari da kuma muradinta?. Zuwaira ce ta fado mata rai,sai taji tana samun sassaucin tsoron da kuma firgicin da take ciki.

Hannunta dukka biyun ta sanya ta dafe kanta.

"Huda,ya kula da ita ya bata magani tasha?,who's she?" Abinda ta dinga maimaitawa kenan. Hudan da har yanzu take ganin tana buqatar therapy tana buqatar counselling akan mikin da nasir yayi mata.......yanzun kuma tana shirin sake fadawa wani abun na daban?,kanta da zuciyarta kuwa zasu iya dauka?,ya kamata ta ciyar da d'anta ta kowacce siga muradinta.....idan yaso in taga dama bayan ta mallakeshi ta yayyankashi ta cinye.

Abu daya ta kasa jurewa ya kuma gaza barin zuciyarta huda,ta yaya zata ji muryarta?. Bata taba jin dauke wayoyin ya dameta ba irin yau,ta dinga jin kamar tayi hauka idan ta tuna ba wata sauran hanya da zata iya samun damar magana da huda.

Sosai tayi qoqarin ganin amna bata gane komai akan fuskarta ba. Ta kama mata aikin sukaci gaba dayi,tana ci gaba da mata hira tana bata labarin fu'ad. Kwata kwata bata jinta ma ballantana ta fahimci abinda amna din ke fada,a haka suka kammala amna ta fito tabar mata kitchen din. Sosai ta zazzaga dukkan abinda ya kamata ta sake juya abinci ya koma ainihin launinsa. Ta tsaya kaman ko yaushe ta zubawa abincin idanu zuciyarta na wani yamutsawa,mafi rinjaye na zuciyarta tana jin kamar wani yanayi mara dadi,wani yanayi da yafi kama da rashin jin dadi?,rashin kyautatawa?,ko aikata abinda ba daidai ba?. Itama bata sani ba,bata taba zaton da hannunta zata iya ciyar da kowanne dan adam abinda bai kamata yacishi ba......saidai abu daya ta sani shine....itadin guba ce ga duk wanda yace zai kawowa innocent rayukan nan guda uku  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~farmaki.

Takun da taji dake alamta mata an shigo kitchen din shine abinda yayi bala'in razanata. Da sauri a kuma birkice ta daga kanta tana duban me shigowar. Zuwaira ce fuskarta da murmushi ta qaraso cikin girmamawa.

"Afuwa,dama cewa nayi bari nazo naji ko akwai aikin da za'a kama miki?" Tayi maganar tana duban warmers din da a gaban idanunta tana labe sabreen din ta cika aikinta tsaf. Idanunta ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,sannan ta tattaro dukka qarfinta ta bude idonta akan zuwairan

"Wannan shine kuskurenku na farko,bana buqatar ki sake shiga wani guri a cikin gidan nan ba tare da kin tsaya kin nemi izini ba an kuma baki" Kai ta rusunar

"Ayi haquri bazai sake faruwa ba in sha Allahu" Bata iya amsa mata ba,sai kawai warmers din data mata nuni dasu

"Ki kaisu kan dining" Tayi maganar tana dosar qofar fita a kitchen din,don sam bata da qwarin tsaiwa ci gaba da magana.

Tana sanya qafafunta da zummar fita tana sako tata qafar abinda ya sanya suka kusa karo da juna,yatsun qafarta suna caki na sabreen haka gwiwarta saita tsaya cak bata ja baya ba bata kuma koma ba. Tsaiwa cak itama sabreen din tayi tana danjin qafarta na dan radadin kadan saboda qafafunta akwai alamun tana ajiye farce.

Shirun da sabreen din taji ya sanyata daga kanta ta sauke dubanta akan laila. Tana tsaye cak ba alamun zata kauce mata ta bata hanya. Bisa dukkan alamunta tana jiran sabreen ne ta kauce mata,kota koma sai ita ta wuce. Cikin qasa da second biyu sabreen din taji wani abu ya saukar mata,wani abu me kama da izza da jin mallaka ya mamayeta. Ta lumshe idanunta sannan ta zubesu fes akan laila tana duban tsakiyar qwayar idanunta da wani irin kallo dake qure qarfin halin mutum. Da farko itama laila din ta zuba mata idanu,saidai a hankali wani kakkaifan abu ke ranqwafar da nata idanun. A hankali taji ta gaza jurewa,saita dauke dubanta daga kan sabreen din tana ja da baya,ba tare data sake dubanta ba ta rabata ta wuce a tsanake ba tare data sake duban sashen da take a tsaye ba.

Da idanu tabi sabreen din har ta wuce,ta maido dubanta cikin kitchen din tana jin kamar yau karon farko ta tozarta......a karon farko taji wata 'ya mace tayi mata kwarjini,har kuma ta juyata ba tare data furta kowacce kalma daga bakinta ba. Hada ido sukayi da zuwaira,sai zuwairan ta tabe baki tana dauke kai. Cike take dama da lailan,cike kuma take da yadda maamah ta dinga jaddada mata ta girmama lailan,don gidan fu'ad a wajen lailan tamkar gidan mahaifinta yake,tammar kuma gidan yayanta da suke uwa daya uba daya yake.

"Idan me guri yazo dai me tabarma nadeta yakeyi,nan din dai akwai macen data amsa sunan matar gidan,komai ayishi bisa takatsantsan". Sarai ta fahimci abinda zuwairan ke nufi,amma sai taga sam bata da lokacinta,don abinda sabreen tayi yafi tsaye mata a rai,yadda zaiyi handling nata. Da gaske komai na gidan yayi mata,da gaske zuwa yanzu tanaso ace itace mamallakiyar gidan. Ta cika gidan da izzarta da mulkinta da kuma ikonta kwatankwacin hajja,tako ina ta zama ME MULKIN gidan.

Samun amna tayi tana shirin tafiya.

"Har me?" Ta fada cikin nuna kulawa. Murmushi ta saki

"Driverna na aje adda tun dazun fa,daga cewa anni zanzo na miki sannu da zuwa". Fararen idanunta da a yau take jinsu wani iri ta kada,bata da energy din dogon magana.

Closet dinta ta bude kawai tayita fiddo abinda take ganin ya kamata ta bawa amna. Ta hada abubuwa cikin qaramar jaka me kyau da daukan hankali.

Ido amna ta fiddo tana nuna tsananin murna da mamaki

"Duka adda?" Ta fada da murmushi. Abun ya burge sabreen sosai,yadda amna din ta nuna,duk kuwa da cewa tasan tafi qarfin duka abinda zata bata din.

Fitowar zuwaira da laila daga kitchen din ya danja hankalin amna dake qoqarin ficewa,ta bisu da kallo kawai kafin ta juya a hankali ta fara takawa tana fita daga falon.

"Sai haquri ranki ya dade....laila kenan..... D'iyar hajja harira.....hajja harira 'yar majalissar zartarwa hajiya mariya maamah". A badini kyakkyawan masauki maganar zuwaira ta samu,hajja hariran da sukayi tattaki har cikin gidansu suka kai qudurin aurota don su cimma buqatarsu?,ta yaya zata manta wadannan fuskokin,ranar,dama abinda ya faru a ranar....har maamah din tana da qarfin halin ajiye budurwa irin wannan a gidan d'an data haifa?,wanne irin kwado ne wannan?,budurwar da babu wata alaqa tsakaninsu face ta zallar qawancen dake tsakaninsu?,a tsarin abota da mu'amala da zata fishshi dan adam tasu bata kan ko guda daya. Kai ta jinjina,information din ya mata kyau da ma'ana,amma kuma batajin zata sakewa zuwaira ko ta nuna jin dadin hakan.

"Ya kamata ki dinga tsaiwa a iyakokinki kawai" Abinda tace da ita kenan tana takawa zuwa hallway dinta don komawa dakinta,duk da har yanzu ba wani cikakkiyar nutsuwa ko sukunin data samu daga uban tunanin dake addabarta,gefe guda kuma tana cike da fata da fargabar sanya abincin a bakinsa ya zarce zuwa cikinsa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 33

_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_





33


&"ma sha Allah,sannunta da qoqari" Anni ta fada sanda ta gama ganin kayan da amna ta kawo wanda sabreen ta bata.

"Tana da kirki anni......amma sai nake ganin hamma me irin halinsa ya dauko,she's so quite,batason hayaniya da yawa,bata fiya bada amsa ba ko magana,tafi yawan murmushi kawai". Murmushi anni ta sauke,har zuciyarta tana sake jin yarinyar tayi mata,a duk wani lokaci da maganarta zata tashi tana sake jin sabreen ta kwanta mata ne.

"Ai dama sai hali yazo daya ake iya zama ko?,Allah ya qara hada hankulansu......yauwa farouq yayi nemanki kuwa sanda kika fita......naji kaman yana maganar zaku abuja passport dinki yayi expired,za'a sake miki wani". Idanu amna ta fiddo sannan ta qanqame anni

"Anni hala Lokacin tafiya ya kusa?". Dan tureta kadan tayi daga jikinta

"Gashi kuwa kin gani keda tafiye tafiye basa isarki" Dariyar jin dadi ta qyalqyale dashi.

"Amna wannan tafiyan daban yake a rayuwata Allah,ba wani trip da yakaimin wannan dadi....whole family fa anni.....wannan karan kuma abun zaifimin dadi saboda nima na samu partner addana,adda sabreen,na daina maqalewa su ya saddiq suna wulaqantani,wannan karon tafiyar zai zama na musamman" Tayi.maganar with full excitement. Da kallo kawai amna ta bita kafin ta saki murmushi,ita kanta tasan tafiyar zata qara dadi musamman da idanunta zasu dinga gane mata fuad dinta da iyalinsa a gefe,cikon mafarkinta kenan

"Anni bari naje na sameshi" Ta fada tana daga yatsunta gami da lissafa watan da tafiyar tasu zata kama

"Yes" Ta furta tana jin farinciki yana lullubeta,saita cilla da sauri zata fita tana cewa

"Dis time har abba fa sai na karbi kudin tsaraba a hannunshi,komai bibbiyu zan dinga siya nida addana"

"Kunfi kusa ai" Anni ta bata amsa. Dakatawa daga fitar da anni taga amna tayi shi ya sanyata daga kai tana dubanta zuciyarta cike da tambaya. A sanyaye taga amna din ta dawo tana zama gefanta

"Lafiyarki ke kuma?" Ta tambayeta tana nazartarta da kyau

"Wani abu na gani anni a gidan hamma". Jin an ambaci fu'ad din ya sanyata tattara hankalinta akanta

"Me kenan?" Ta amsawa amnan cikin zuciyarta tana fatan ba wata matsala bace a tsakaninsu.

"Anni.....me aikin gidan maamah na gani,ita da wata budurwa......bansan budurwar ba amma tana kama da wannan qawar maamah din aminiyarta dinnan....."

".....hajja harira" Anni ta samu kanta da fada ba tare data shirya ba

"Eh ita" Ajiyar zuciya anni ta fesar

"To shine me amna?" Ta furta cikin hikima. Tun asalin tarbiyya anni irin matannan ne da basa bari yaro yana kawo musu hira ko maganar wani guri. Qasa amna tayi da idonta

"Ba komai,kawai anni ji nayi jikina bai aminta dasu ba,daga yanayinsu fa anni kamar a gidan zasu kwana fa,qilan ma komawa gidan sukayi Allah anni". Ta fada tana bata rai. Da kallo tabi amnan,amna din ba yarinya ce qanqanuwa har can can ba,kome ake ciki ko yake faruwa tabbas dole tana gani tana kuma fahimta.

"Hammanku majibancin lamura da jama'a ne,bazai zama abun mamaki ba idan anga sabbi ko baqin fuska a gidansa ba,kedai kici gaba da taya dukka 'yan uwanki da addu'a". Kai kawai amna ta gyada ba tare data samu cikakkiyar gamsuwa da bayanin anni ba,ta miqe tana fita daga dakin kamar yadda tayi niyya da farko.

Fitar amna dukka sai hankalinta ya dawo jikinta,sam sam taji bata gamsu da wanzuwar zuwaira da waccar yarinyar a gidan ba. Tasan wacece maamah,tasan kuma dukkanin wanda ya rabu da ita yaya dabi'arsa zata iya kasancewa. Indai da wata manufa ko wani qullin daban aran maamah din,muddin tana raye ba zata taba bari haqarta ta cimma ruwa ba. Koda ta dauke idanu akan abubuwa da yawa,koda tayi kawaici akan abubuwa masu yawa....amma a nan ba zata bari ba,ba zata bari tabi fu'ad har rayuwa cikin gidansa ta ruguzata ba. Saita jawo wayarta tana qoqarin danna kiran.


*SABREEN*

Batasan adadin sau nawa ta leqa dining din ba da zummar ganin ko ta samu nasara ya taba kayan abincin?. Saidai a duk gewayen da zatayi bataga wani alamun taba komai ba cikin kayan dake danqare a table din ba.

Ba iya yaci abincin bane kawai damuwarta ba aah......tanaso tayi amfani da wannan damar ta karbi wayarta a hannunsa,tanaso duk yadda za'a yi ta samu cikakken bayanin yadda su hudan suka koma qarqashin kulawa da mulkin maamah. Abun yana tsananin daure mata kai......ta yarda da momma bahijja....ta kumayi imanin haka siddan ba zata bari haka ta faru ba,duk dadai ma batasan ainihin wacece maamah din ba. Sam bata sako kawu rufai a ciki,shikam tasan ko ya fita sanin wacece mariya to zai aikata fiye da hakan ma.

Zuwa sha daya na dare haqurinta ya gaza,ta miqe da wani irin kaiwa maqurar haquri tana yafa mayafinta saman doguwar rigar jikinta ba tare data buqaci dankwali ba ta sanya slippers dinta tana bude qofar dakin ta fice.

Kamar magen dake kwanton farautar kamun bera haka ta dinga tafiya a hankali tana durfafar stair case din dake facing dinta. Duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,amma kuma tuna huda nadra da haneefa kadai ke qara mata qwarin gwiwa.

Tana jin a kansu zata iya komai,zata kuma fuskanta da tunkarar komai da kowa.

Cak ta tsaya a stairs din farko tana jin kaman wanda ke kusa sosai da ita idan ya qurawa qirjinta idanu zai iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa ma.

"Shi waye?,mutum ne kamar kowa,mutum ne kamar ni,bashi da wuta bashi da aljanna,bai isa kuma ya yankani ya cinye namana ba" Ta gayawa kanta da kanta murya can qasa qasa dukka tana zaton BUGUN ZUCIYARTA zai daidaita. Aqalla ta tsaya jiran mintuna kusan goma amma still ba abinda ya canza,sai kawai ta runtse idanunta ta kama makarin stairs din ta fara haurawa saman da wani irin confidence da batasan daga inda ta aro shi ba.

Idan ba jikinta da hancinta ne ya mata qarya ba,to tabbas atmosphere da weather na wajen daban yake dana kowanne bangare na gidan. Wani irin lullumsan yanayi da wani irin kebantaccen qamshi da bata taba jin makamancinsa ba. Bata taba lura da cewa shimfidadden carpet bane kan stairs din sai a yanzun da qafafunta ke barazanar nutsewa a cikinsa. Bayan qafafunta sun nutse din kuma wani irin sassanyan yanayi tafukan qafarta ke riska a can cikin carpet din. Duk yadda taso jure qauyancinta amma abun

Please Login or Register in order to submit comment