Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ana ukun sannan ya daga yana sosa kai.

"Ku kwana a can,ku biyasu kudin kwana daya.....but kakaimin amna gidan saudat acan nakeso ita din ta kwana"

"Okay.....in sha Allah" Farouq ya amsa shima yana jin dadin hakanma da tace,don shi kansa a yanzu ji yake ya zama surukinta,ina ga fuad din. Yadai tabbatar ba zasu qarke lafiya ba idan ya dawo hayyacinsa,to amma wa suke dashi sama da anni?,itace qawarsu abokiyarsu kuma.


_uhmmmm....tofa,sabreen naga kin dauki zafi da yawa=ØÞ=ØÞ.....amma dai muje zuwa_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 77


77


Da wani irin yanayi yake wanke mata kowanne sashe na jikinta da ruwan shower gel din. Wani kuka take saki kawai tana ji har a ranta ya gama da ita,bata da wani sauran qarfi da zata dakatar dashi ko guda daya,cizo kam ta masa shi har batasan adadi ba,amma ko a fuska baya nuna mata yaji zafinsa bare akai ga dakatawa da abinda yakeyi,tamkar ma ba jikinsa take ciza ba,idan ta saka bakinta ma tsaiwa yakeyi har sai ta cire don kanta. Shi kadai yasan me yake sake ji cikin jikinsa,ji yakeyi kaman baiyi komai bama,wani sabon feeling ke taso masa saboda santsin shower gel din dake sassan hannuwansa wanda da tafin hannu kawai yake dauraye mata jikin ba tare daya nema loofah ba. Kafin ya gama wanketa launin idanunshi sun sake canzawa sosai,numfashinsa yana masa nauyi tsakanin qirjinsa da hunhunsa,inda zai samu....inda zai yuwu yana buqatar sake kasancewa tare da ita ko yaya ne.....koda na mintuna kadanne,amma shi kansa yasan yadda take a yanzu dole tana buqatar medical care. Bai taba jin ya zama addicted to wani abu ba irin wannan abun,cikin qasa da wasu awanni qalilan yana jin kamar an halicci abunne sabodashi shi kadai.

Hannunsa ya sanya ya riqo qugunta bayan ya fiddota daga bathtub din. Idanunta yake kalla sosai wadanda suka rine saboda azabar kuka. Taqi kallonsa ta kuma sanya duka hannuwanta biyu tana turashi baya,amma ko motsi baiyi ba bare tasa ran zai matsa. Yadda takejin dumin fitar numfashinsa a rarrabe yana sake dasa mata matsanancin tsoronsa,shigen wannan yanayin taji daga gareshi dazu,a yanzun idan yace zai maimaita abinda yayi dazun ta tabbatar saidai ta taqaitawa kanta wahala kawai tayi sallama da duniya......ita kadai tasan abinda takeji,ita kadai tasan radadin da takeji yana ratsata a duk wani motsi da zatayi.

"Sabrrrrr....." Ya fada da sautin dake kama da rad'a,wani irin narkakken sauti dake da amo na can qasan maqoshi,idanunsa cike fal da wata irin mahaukaciyar soyayya da baiyi zaton cikin zuciyar tasa akwai wani space daya ragewa wata halitta ba.

Kanta ta dauke gefe,maganganu takeson gasa masa amma tana jin idan ta tsaya ta maida masa koda kalma daya ma yana da wannan darajar ashe?.

"Sabreeennn" Wannan karon ya kira sunanta full da wani irin sassanyan kuma kwantaccen sauti. Idonta ta lumshe tana mamakin jin sunan yau radam saman bakinsa,kiran sunansa a bakinsa daban yake da yadda kowa ke kiranta,kaman yadda komai nashi yake daban haka furucin sunanta a bakinsa.....amma kuma zuciyarta saita ture hakan,haushinsa ya taso ya maye gurbin wannan.

"I know.....nayi abubuwa masu yawa......na bata miki rai da yawa......na gaya miki maganganu masu yawa......i hurt you.....i really hurt you even...." Sai ya kasa qarasawa saboda yadda zuciyarsa take rauni.

"Na bata miki da yawa.....na sani,but dukan abinda nayi shine akan hujja da evidence da binciken da nayi wanda yazo da negative reviews......sabrrrr" Ya sake kiranta a karo na uku yana sake zube qwayoyin idanunsa dake cike da shauqi a kanta,yana jin kamar ya dauketa ya bude qirjinsa ya boyeta,yana jin kamar ya hadiyeta ya huta da abinda yakeji qasan zuciyarsa.

Ganin da gaske ba zata kalleshi ba sai ya sanya hannu qasan habarta yana juyo da fuskarta. A zafafe ta qwace tana hadiye kukan daya taso mata,ba abinda take muradi a yanzun irin ya sake mata qugunta tayi nesa dashi,ya gama kalle komai da komai nata.....wannan laifin nasa batasan yadda zata gogeshi ba.

Sake kamo fuskar yayi ta qwace,sai kawo ya jawota cikin jikinsa ya mata wata kyakkyawar runguma. A karo na biyu fatar jikinsu ta sake haduwa guri daya,wani qaton numfashi ya qwace mata,kaman yadda qaramin yaron da yasha kuka kan saki ajiyar zuciya sanda ya samu kyakkyawar runguma da lallashi daga wajen mamansa.

"My heartfelt apologies" Ya sake fada da wani sassanyan sauti me tada tsigar jiki yana miqa hannu ya sake musu ruwa saman kansu shi da ita. Saukar ruwan ya sake tayar masa da abinda yakeji ninkin na dazu,abinda ya qarasa gigitashi kenan,ya dagata yana hadeta da bangon toilet din,ya fara abubuwan da yasan zai samu sauqi da sassaucin abinda yakeji.

Wani irin tsoro ne ya sake kamata,takaici da baqincikin yadda yake sarrafa jikinta yadda yaga dama,sai ta sake sakin kuka me sauti tana sake tureshi dakai masa duka da siraran tafin hannunsa. Ba abinda yaji saiji da yayi ma kaman tana sake zugashi,sautin kukanta kawai yake iya ji daya sake zame masa kaman zuga zugi,don sai ya dinga jin kaman kukan wani abu daban takeyi bana baqinciki ba,deep inside yasan na baqinciki ne,but bazai iya qyaleta ba ko yaya......yana buqatar samun sassauci koda baiyi me gaba daya ba,yanajin zuciyarsa da rayuwarsa tana sake mannuwa da ita,yana jin kamar duk wani fitar numfashinsa ya ta'allaqa da ita ne.

Sai daya tabbatar ya samu nutsuwar da yake da buqata sannan ya jata jikinsa yana fitar d wani zazzafan numfashi,ya gama kashe mata jiki da tsoro itama,dole ta jingina da jikin nasa tana jin yadda zukatansu ke wani irin gudu,musamman shi da bugun zuciyarsa ke shiga cikin kunnenta sosai saboda kan nata dake kwance a qirjinsa.

Duk da ruwan dake zuba saman kansu yana kwaranyewa a sassan jikinsu gaba daya amma hakan bai hanashi tantance dumin hawayenta saman fatar jikinsa ba. Ya gaza bude idanunsa,sau hannunsa guda daya yake shafar sassalkan gashinta daya watsu har gadon bayanta,ya kuma manne sosai saboda ruwan dake zuba

"Am sorry......I'm genuinely sorry,My apologies from the bottom of my heart" Ya fada yana kissing goshinta softly.

Ture fuskarsa tayi tana sake qayyade adadin rashin imaninsa......tadai san saboda itace kawai ya gwada mata wannan rashin tausayin,banda haka ta tabbatar inda duka mata haka sukeji ba abinda zai sanya su zauna ko suci gaba da yin aure.

"Leave me" Ta fada tana qoqarin tashi daga jikinsa. Hannunsa ya sanya ya damqota sosai yana cewa

"I can't......ko mutuwa bata isa ya rabani dake ba sabrrrrrr.....zan yita baki haquri har ranar da numfashina ya fita daga gangar jikina......zanta baki haquri ko sau dubu a rana kikeso.....karki wahalar damu gaba daya ta hanyar cewa na barki ko na nisanceki.....don wallahi wallahi wallahi bazan iya ba......i can't do it" Ya qarasa fada yana sake matseta jikin bango sosai sannan ya fara tsarkake jikinsa idanunsa a kanta.

So yake qarfi da yaji sai ya cire kowacce kunya daga idanunta,tsaiwarsa haka a gabanta tana jin shine abu mafi girma firgici da razani da suka taba gani. Cikin mintuna kadan ya gama ya kashe shower din,ya jawo babban towel ya wareshi. Ta dauka zai rufa ne ko ita ya bata daman rufawa.....maimakon haka sai ya jawota jikinsa ya bude towel din ya nadesu su biyun a ciki.

Shi da ita ba wanda numfashinsa baiso yin qaura ba saboda yadda jikinsu ya sake gauraya dana juna

"Shshshsh" Ya fada yana qoqarin daidaita numfashinsa,don bayason tace komai,hannunsa ya sanya a gadon bayanta ya matseta cikin jikinsa gami da rabata da qasa kaman yadda zaka rungumi yaro a haka suka fita a toilet din.

Batasan da gangan yayi ba?,oho.....amma gaba daya suka zube a gadon yana fadawa samanta. Ya aje mata nauyinsa sosai har sai da numfashinta ya fara nauyi

"Oh....sorry" Ya furta yana dagata gami da bar mata towel din a tare da ita. Rintse ido tayi tana qin dubansa,bai damu ba ya jawo boxer dinsa dake yashe a gefe tun dazun ya saka,ya sanya hannu ya sauketa zuwa sofa bed ya fara tattare comforter da bedsheets din harma da pillow case din,don bayason anni ta sake dawowa idanunta su gani. Toilet ya koma ya shiga sheqa musu ruwa,jikinsa yayi wani irin sanyi ganin yadda ruwan ke wanko jinin. Da gaske ya shigeta ne da tabbaci da yaqinin ta riga ta saba......ya kuma samu qofar a kulle gam....dole taji ciwo koma wanne iri akace masa taji. A yadda yakejin cikakkiyar lafiya a jikinsa ya sani,koda bazawara ce yaje mata da irin yanayin jiya lallai saita yabawa aya zaqinta ballantana ita din da take sabon hannu.

Luggage dinta ya bude,ya fidda mata kaya bayan ya saka wata sassauqar riga a jikinsa over sized shirt da wandonta. Fara ce qal data dace da black trouser dinsa. Sama sama yake jinsa shima,saidai abinda ke gabansa ya shafe komai.

Da rinannun idanunta ta dubeshi sanda ya aje mata kayan,tana so ne ya matsa ya bata waje ta shirya amma bataga alamun xai matsa din ba,hasalima tsaye yake a kanta ya zube duka hannayensa a aljihun wandonsa kaman zai lasheta,ya zube mata nauyayan idanunsan nan yana jin kamar ya buda qirjinsa ya fiddo mata mahaukaciyar soyayyar data sakar masa.

"Ka fita zan shirya" Ta fada a taqaice ba tare data kalleshi ba,hannayensa ya fidda daga aljihunsa ya juya a hankali ya fita.

Duk yadda taso ta miqe sosai don ta shirya amma hakan ya gagareta,ba zata iya tsaiwa normal kaman kowa ba,abinda ya sanya hawaye yaci gaba da zuba a idanunta,saita dinga jin data sani ta barshi ya taimaka mata,amma kuma batason komai da zai dinga hadata dashi. Da qyar ta lallaba ta saka underwears dinta ta maida rigar,sannan ta lallaba hannun damanta ta kwanta tana ci gaba da fitar da ruwan hawaye.

A nutse anni ta murda qofar tana shigowa da sallama,wata kunya ta taso ta lullubeta,saita rufe idanunta tamkar me bacci,tana fata annin taji kaman baccin takeyi ta juya ta barta.

"Sannu....." Anni ta fada a hankali da alama ta fahimci ba baccin takeyi ba.

"Zaki iya tashi?,doctor zata shigo ta dubaki". Kai kawai ta gyadawa anni ba tare data iya furta komai ba,ta motsa a hankali tana tunanin yadda zata tashi din. Matsawa annin tayi ta kamata a nutse tana cewa

"Yi a hankali" Tausayinta yana kama annin. Yanayin yanayine bame dadi ba,iya yau kawai ta fahimci yaron nata yadda jikinsa ke agine hakama komai nasa

"Allah ya baki ikon jurewa" Annin ta fada cikin ranta. Sai a yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake kaucewa abubuwa da dama,azumin litinin da alhamis akai akai,harma wani lokaci yakanyi azumin annabi dawud,yau yayi gobe ya huta. Wani lokaci takance

"Ka dinga hutawa mana me babban suna......ga azumi ga aiki,shi kansa aikin busy din da kake sakawa kanka pressure din tana yawa". Sau tari murmushi kawai yakeyi ko ya kafa mata hujja da



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 78


78


"Ba isashen time na tsayawa cin abincin,wani lokaci azumin yafi,idanma banyi ba coffee ne sai ruwa sai fura ko yoghurt ". A yau ta fahimci ainihin dalilinsa,saita dinga furta

" Alhamdulillah" Qasan zuciyarta. Da gaske Allah ya tsare mata yaranta gabansu da bayansu kaman yadda take yawaita addua a dukka salllolinta na nafila ko na farilla. Tayi imanin inda wani ne ya samu cikakkiyar dama irinta fu'ad din,tarin dukiya kyau ilimi da suna da yayi a duniya ba irin haramtattun ayyukan da bazai aikata ba,ta sani akwai dubban mata dake a shirye su bada kansu ga irin wadannan mutanen,koda ba zasu samu komai ba a wajensu daukaka ce ace yau suna tare dasu.

Sai data zaunar da sabreen yadda zataji dadin zaman sannan ta juya a hankali tana fita parlor din.

Minti daya ta dawo tare da baquwar fuskar. Dr fadwa siririya fara tas,duba daya zaka fahimci shekarunta duka duka ba zasu haura arba'in ba zuwa da biyu. Anni tana gaba dauke da tea tray,Dr fadwa na biye da ita.

Qasa sabreen tayi da qwayar idanunta,ba zata iya kallonsu ba dukka su biyun,har Dr fadwa dake matsayin baquwa a idanunta. Ajiye tea tray din anni tayi tana duban Dr fadwa. Kai Dr fadwa ta gyadawa anni,sai annin ta maida dubanta ga sabreen

"Ga likita na.....zata dubaki in sha Allah,ki saki jikinki.....itama 'yar gida ce" Kai ta dagawa anni a hankali,tana jin takun anni da fitarta a dakin,ta kuma ja qofar ta rufe musu.

Dubanta Dr fadwa take tana kuma karantarta. Ko ba'a gaya mata ba ta fahimci ita din bame saurin sakewa da mutane bace,ta miqa hannu a nutse ta kama hannunta ta sanya a nata,abinda ya sanya sabreen daga kanta ta kalleta da risunannun idanunta. Da sassauqan turanci take tambayarta da sakakkiyar murya.

"Kinci abinci?" Kai ta girgiza mata a hankali. Ba zata iya tuna wani abincin kirki da taci ba,tun na dazun kafin su fita,ko acan wajen cin kifi ma bata saki jiki taci komai ba,kasancewar ita ba ma'abociyar cin abinci cikin jama'a bane. Kai tsaye Dr fadwa ta jawo tea tray din zuwa saman cinyarta tana matsawa dab da sabreen

"Ki saki jiki kici abinci......sai na dubaki,kada ki damu da yawa......hakan yana faruwa ga 'ya'ya mata da yawa,musamman da yake yadda kowacce mace halittanta daban,haka kowanne namiji shima nashi halittan daban......fashewar budurcin mace yana iya kawo fitar jini.....amma komai zai zama daidai kinji?" Kai ta daga a hankali,ta kuma miqa hannu tana karbar mug din da anni ta hada mata tea me dumi sosai da kauri.

Ita kanta tasan ba komai a cikinta,ballantana kuma da abun ya faru sai taji kamar anyi mata yasa,kamar an kwashe 'ya'yan hanjinta gaba daya,kamar iska tana turata zuwa gaba.

Kadan kadan take shan tea din,dr fadwa bata matsa wajen kallonta ko yi mata wata tambaya ba ta daban,ta bata time sosai tana duba wayarta har taga ta ajiye. Wayar ta bari ta daga kai tana kallonta,batasha da yawa ba amma saita qyaleta don tasan lallai yanayin bame dadi bane.

Kauda tray din tayi ta matso kusa da ita tana dubanta

"Sunana fadwa kefa?"

"Ameenatu" Ta furta idanunta suna dan lumshewa

"Sabreen sunan inkiya?" Kai ta gyada,saita fidda takarda fara ta rubuta sunan akai.

"Eheennn......ina ne yake miki ciwo yanzu?" Shuru tayi don tamabayar tayi mata nauyi da yawa,uwa uba ma gurare da yawa ciwon suke mata,tun daga lips dinta......qirjinta....hatta da tafukan hannunta da suka sha murxa zafi zafi takeji suna mata.

"Ki sake sosai kiyimin bayani,shi yasa madam ta fita ta bamu guri......zai iya zama ciwo me zafi nan gaba idan baki bayani ba". Hannu tasa ta nuna mata wajen ba tare data iya kallon idanun fadwa ba.

"Alright......zan duba wajen idan ba damuwa?" Ta fadi da nufin neman izini. Dif tayi abun yana mata wani iri,shikenan ita kuma jikinta ya zama wani budadden guri?

"Kiyi haquri....saboda lafiyarki,bazai dauki lokaci ba" Ta fada da sigar lallashi. Kai ta gyada mata a sanyaye.

"Kin shirya?" Dr fadwa ta fada tana kallonta sanda ta kwanta kamar yadda ta kwatanta mata. Kai ta gyada mata tana rufe idonta saboda kunya.

A hankali ta fara dubata cikin qwarewa da nutsuwa yadda ba zata fama mata ba.

"Oh my god.......subhanallah" Abinda ta fada kenan tana maida mata doguwar rigarta.

"Kin masa gardama ko musu?" Dr fadwa ta fada tana kallon fuskar sabreen din da tuntuni ta canza kala zuwa red. Tambayar sai ta zama kaman ta bata license din sabon kuka,ita me zata ce mata?,batasan ma me tayi ba.....musu ko taurin kan batasan wanne ne tayi a ciki ba,batasan wanne ne ya faru ba.

"Irinsu sir.......ba kasafai za'ayi musu musu a irin wannan lokacin a wanye lafiya qalau ba.....next time kada ki qara musu ko gardama,mijinki yana da duk wani personality da kowacce 'ya mace zatayi alfaharin samunsa a matsayin miji,.....kulawa da tattali yake buqata,ko don gaba kada ki sake matse jikinki da hana masa kanki haka". Sanda take fadin next time din ji take kaman ta ture Dr fadwa,itakam wacce irin sauna ce da zata yarda taci gaba da zama da mutum irinsa?,wanda bisan ciwo ko darajar dan adam ba?,balle ma har hakan taci gaba da faruwa wai a gaba?.

Daidai nan anni ta tura qofar ta shigo,da murmushi take tambayar Dr fadwa

"Kin gama?" Kai ta girgiza tana dan murmushi itama

"Aah fa......madam yaronki aiki ya baro.....bleeding din data dinga yi ta samu tier ne.....so dole sai an mata stitches..." Idanu kadan anni ta fiddo,har jikinta tana jin wani iri. Lallai Allah kadai yasan azabar da tasha tunda har an kai ga batun dinki.

"Gurin yayi ciwo sosai gaskiya.....harda bruises banda tier din,dole a dinki wajen,inda first degree tier ne da sauqi....so amma yanzun ma idan kina ganin a bari......"

"No.....a dinke Dr" Anni tayi saurin dakatar da Dr fadwa din. A yadda taga yanayin fu'ad din da idanunshi ba yadda zata bari a bar sabreen din a bude,tun sanda momma ta gaya mata marainiya ce takejin kamar kula da sabreen din wani haqqi ne daya rataya a wuyanta.

"Kiyi haquri a dinke sabreen kinji?,wannan gurin shine mutuncin duk wata d'iya mace a wajen mijinta.....akwai zafi amma zai wuce kaman bai faru ba,wannan shi ake kira da cikakken mutunci mijinki ya zamana shi ya karbi wannan abun ba wasu shashashai a waje ba.....nayi alfahari da hakan......na kuma yi alfahari dake kaman yadda nasan yake a wajen mijinki" Anni ta fada a tausashe hannunta saman kan sabreen da kunya ta hanata koda motsawa bare ta bude idanunta.

Sake fita anni tayi ta basu waje don sabreen din ta sake sosai. Dr fadwa kuma ta shirya komai,ta kuma yi mata allurar da sai data zubda qwalla kafin a gama,batasan azaban yana gaba ba sai da aka fara dinkin.

Neman sakayya wajen Alla data dinga yi har batasan sau adadin nawa ta fadi ba,saidai duka cikin ranta takeyi,bakinta baya iya furta komai sai ruwan hawaye dake fita Dr fadwa na mata sannu.

Kasa zama yayi a falon,sai kawai ya tura qofar dakinsu saddiq ya shige. Kwance yayi kawai saman gadonsu,ya kasa tuna komai sai hankalinsa dake can dakin inda ya barosu,yaji shigar dr fadwa da anni da fitowar annin duka,baisan me yake faruwa ba don haka ya kasa samun nutsuwa. Gefe guda wani irin sarqaqiya ya shiga.

"KARUWA" Sunanta ma farko kenan daya fara zuwa kunnensa,yaci gaba kuma da zuwa masa daga bakunan mabanbantan mutane. Kenan dukka wadannan bincike da shaidun duka shaidan zur ne?,duka shaidan qarya ne?. Idan har hakan ya kasance kuma ganin da yayi mata a hotel fa?,mashkur dake hannunsu a yanzu haka yana nemanta afujajan da sunan wadda ta kwashe masa komai nasa?,ganinta da yayi fa tare da mika'il?,a cikin kamfaninsa tana fitowa daga toilet dinsa?,binciken daya tabbatar kuma ita ta kwashe kudaden asusun kamfaninsa fa?,wannan kuma mene?. Ta yaya zai fahimta?,ta yaya zai gane?,waye zai warware masa?.

"Ka nutsu fu'ad.......diban kudi yasha banban da bada mutunci.....don tana kwashe kudaden maza.....don kana ganinsu tare hakan ba yana nufin tana basu kanya bane,kowanne matsayinsa daban,cakudasu waje daya kuma shine zai sanya ka kasa banbance inda komai ya dosa" Wani sashe can qarqashin lungun zuciyarsa ya gaya masa.

Sau uku yana leqa parlor din ko zaiga ko yaji motsin anni ko wani abu da zai bashi haske amma baiji ba. Kunyarsa da kawaicinsa duka suka qare,sai kawai ya buda qofar dakin ya fito kai tsaye yana tunkarar dakin.

Itace ta farko da idanunsa suka fada kanta bayan bude qofar da yayi. Ta wani sake fadawa farat daya saboda masifar dinkin. Ko baka santa ba tsakanin a wannin nan idan ka kalli fuskarta zakasan tayi kalar kukan da bata taba irinsa ba.

Idanunsa ya maida kan Dr fadwa,likitan da sai da tazo ya tuna ya taba saninta a Egypt,ta taba dubashi da yayi wani zazzabi,hankalinta kuma da nutsuwarta shine abinda ya sanya ya bata daman bashi magani.

"Welcome sir" Ta fada cikin girmamawa. Kai ya gyada yaja kujera yana zama hankalinshi a kanta. Daga kallon da yayi mata ta fahimci qarin bayani yake nema. Dama kuma dole akwai buqatar masa qarin bayanin don ta fahimci kaman yana cikin mazan nan marasa haquri akan abinda ya shafi janibin auratayya.

"Mun kammala,anyi mata stitches.....but please sir,tana buqatar hutu na koda 3to 4 weeks kafin a sake tabata,saboda a bawa dinkin daman warkewa yadda ya kamata". Ido ya lumshe sannan ya bude yana jinjina kai.

"Mun gode....ta yaya zaa biyaki?".

"Madam ta biya sir.....Allah ya qara lafiya" Kai ya jinjina yana girmama qaunarsu da anni. Tsantsar kulawa da qauna irin wadda akasan uwa kadai take da wannan zuciyar. Komai idan ya kama qoqari takeyi tayi musu shi ba tare data jira yin kowa ko cewar kowa ba.

Tatttare kayanta tayi ta fice taja musu qofar.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5ØÜ 5ØÜ 5Ø
Ü 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ 5ØÜ
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D² D¥ ³

5ØKÞ5Ø<Þ5ØBÞ5Ø@Þ 79


79


A hankali ya dauke dubansa daga kan qofar zuwa inda take zaune. Idanunsa ya zuba mata yana jin akwai wani boyayyen abu ciki rayuwarta,wadanne irin masharrantan mutane ne tattare da ita haka?,wadanda ba zasu iya fadin alkhairi a kanta ba?,wadanda ba zasu iya suturta aibunta ba a sanda akazo bincike a kanta ba?. Idan bai manta ba,ya samu tabbacin cikin wadanda suka bada shaida a kanta harda matar babanta,sanda yake jaddadawa abdul haleem bayason fake bincike,baya son kuma gurbataccen shaidu.

"Wacece a cikinsu?" Ya tambayi kansa da kansa yana takawa gabanta,tausayi da wata irin mahaukaciyar qauna tata tana hudashi. A yanzun yana jin a shirye yake da duk wani mutum da zai taba rayuwarta,a shirye yake ya bada dukkan abinda ya mallaka a kanta.....in fact a yadda ta zame masa mahadin numfashi a yanxun......ba dukiyarsa kadai ba.....hatta da rayuwarsa a shirye yake ya bata ita. Yana jin ya shirya kame duk wani wanda ya bada shaidar banza a kanta,ya shirya tuhumarsu ko su waye....komai yawansu.....komai kuma kusancin dake tsakaninsu da ita.

A jikinta takejin wanzuwarsa a wajen,wannan ya sanya ta sake zabar ci gaba da rufe idanunta,har ya iso gefanta,ya zame kan gwiwoyinsa yana aza qarfinsa akai. Hannusa ya miqa ya kamo tattausan tafin hannunta,ta motsa da sauri ta nufin zamewa

Please Login or Register in order to submit comment