Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafi qarfinta,dole ta dinga bin carpet din da kallo har zuwa sanda ta riski wata pivot door wadda gefe da gefanta duka glass ne da bazaka iya hango ainihin parlor din ba,yayin da daga tsakiya ta kasance ta gogagen katako da aka yima design na zamani wanda ya maidata smart door. Tun daga zubin qofar tasan wajene na musamman kuma kebantacce,ta bangare guda kuma taji dadin samun qofar a bude,banda haka da sai tayi tsaiwar da qofar zata gama tantance wace kafin ta bata daman shiga parlor din.

Mutum ne shi me wani irin jiki wanda baya qaunar zafi tun asali,saidai duk da hakan tsananin kare lafiyarsa ya sanya bai fiya kwararawa kansa A.c ba. Duk wanda ya sanshi ya sanshi da wannan dabi'ar na kaucewa abubuwa masu sanyi ciki kuwa harda ac din.

Zaune yake saman wata qawatacciyar minotti sofa qwaya biyu dake bayan qwatattun Belgium sofas din da aka yiwa yalwataccen parlor din ado masu wani irin design me daukan hankali. Daga bayan Belgium sofas din aka yi wani muhalli na daban da aka zuba minotti sofas guda biyu wanda suke bashi daman kashingida ko miqe qafafunsa a duk sanda yaso.

Dogayen qafafunsa na miqe saman sofa din,yayin da night shirt dinsa ke ajiye a gefe,daga shi sai gajeran wandon rigar wanda iyakacinsa cinyoyinsa. Hakan ya bayyana zallar halittar fararen cinyoyinsa dake lullube da baqa sidik din gargasa. Madaidaiciyar Ac ke kadawa cikin dakin,wadda ba lallai yanayin sanyin ya sanya ka fahimci itace ba saboda glass door din dake hannun hagu na falon da yake a bude,tatacciya iska me kyau dake tasowa daga jikin tsirran da aka qawata wajen dasu tana busowa zuwa cikin falon. Tattacciyar iskar data sanya masa kasala da mutuwar jiki,duk karsashin aikin da yakeyi ya soma raguwa.

Turo qofar da akayi shi ya sanyashi dauke idanunsa daga karanta saqon da William ya tura masa ta email da suke buqatar ya duba da kyau ya karanta ya kuma sanya hannu.

Fes yake ganin fuskarta wadda ke tsaye daga bakin qofar,fuskar data bayyana tsakanin lullubin mayafinta wanda yadan zame baya kadan ya bawa kwantacciyar sumar dake gaban goshinta daman bayyana sosai. Fararen idanunta da suke da wani irin haske ta zube a kansa wani abu na dukan zuciyarta saboda yadda ta sameshi.

Ba wani abu da gajeran wandon jikinsa ya suturta sai qasan cibiyarsa zuwa cinyarsa,don bai samu daman qarasawa gwiwarsa bama sam. Ginannen jikin nasa daya samu kulawa ta kowanne fanni,motsa jiki,tsananin tsafta da kuma cima me kyau. Kwantaccen gashin dake cike da qirjinsa shi ya zamewa faffadan qirijinsa tamkar adon baqin abu bisa farin yanki ko farar takarda. Wani irin kwantaccen gashi daya shirya kansa da wani irin siririn layi har zuwa cibiyarsa ya zarce har qasa.

Har cikin jikinta taji rudewa sosai,don wani abune da tsahon rayuwarta bata taba gani ba,hakazalika bata taba hasashen zata shigo ta sameshi a haka ba. Cikin zafin nama ta juya da niyyar komawa inda ta fito,don batajin zata iya ci gaba da daurewa kallon wannan halittar tasa. Da nasa salon hanzarin da kuma son qurewa rashin kunyarta tare da qoqarin fuskantar wani abu daga gareta ya dauki remote na qofan ya dannan close,take ta rufe kanta da wata irin gaggawa kamar qiftawar ido. Cak ta tsaya zuciyarta na bugawa sosai,tsoro yanaso ya kamata Amma kuma wannan dakakkiyar zuciyar ta taso mata,taji a ranta cewa idanma ta juya ta fita ta nuna masa ta damu dashi kenan ta kuma damu da wanzuwarsa a haka.

Nasa idanun ya janye daga kanta yana hade ransa tsam waje daya. Duk da kallon data masa bai wuce na second biyar ba amma ya fahimci lallai ta qarewa jikinsa kallo.

Hannu ya miqa gefansa ya jawo night shirt dinsa ya zura,sai ya koma ya jingina da fuskar minotti sofa din yana ci gaba scrolling saqon yana dubawa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 34

_Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_


34


Minti daya biyu uku har zuwa biyar bataji motsin komai ba,wannan ya sanya tayi tsammanin yabar falon ne,don haka ta juyo a hankali tana sake zube idanunta a wajen da yake. Haushi takaici da bacin rai suka hadu suka lullubeta ganin aikinsa yake hankali kwance,sai ta gyara tsaiwarta sosai tana fuskantarsa ganin ya lullube wannan faffadan qirjin nasa,wannan ya dan rage mata kaifin abinda takeji,duk da cewa cinyoyinsa dake a waje nason sakata a razani da tsoro.

Rasa ta yadda zatayi calling attention dinsa tayi,sai ta danyi gyaran murya kadan cikin qufula da fusata. Minti guda kaman baisan tana wajen ba kafin ya motsa,ya daga kansa da idanunsa daga kan hasken system din yana zubesu a kanta da wani irin kallo na qurilla. Karo na farko yadda ya tsareta da ido taji kaman yanaso yayi mata nauyi,jajayen lips dinsa hasken fararen qwayar idanunsa wani abu ne da bata taba gani wajen wani d'a namiji ba sai a kansa,akan nasa ma a yau data masa kallo itama nakai tsaye.

"Wayoyina nazo karba saboda ina da buqatarsu....... Akwai mutane masu muhimmanci a rayuwata da nake da buqatar na dinga magana dasu" Ta fada tana tsuke girarta da kyau tana kuma tura dan qaramin bakinta gaba wanda sam batasan ma tanayi ba,saboda zuciyarta cike take da haushi. A hankali ya sauke idanunsa zuwa saman qaramin bakin nata data tattara lips dinta duka ta turasu gaba. Wasu irin siraran lips da sai kayi tsammanin jambaki ta shafa musu. Tsigar jikinsa ta zuba kadan saboda bayyanar daya daga cikin abinda ke burgeshi a jikin mace yake kuma lissafin ya sameshi kenan,wato cute lips masu nau'in light pink ko red me haske irin nasa.

"A hakar kamar cikakkiyar mace" Ya fada qasan ransa yana jan tsakin da baisan ma ya fito sarari ba. A duk lokacin da zai kalleta sake raina shekarunta yakeyi,hakanan a duk sanda zaya kalletan sai mamaki ya sake cikashi game da yadda ta samu cikakkiyar shaida da certificate din zama KARUWA. shi kam gaba daya ma baisan me yahau kan mazajen dake mu'amala da ita ba,a bisa qa'ida da yanayin halittarsa ta masa yarinta da yawa. Yanason macen daya tabbatar zata iya dauke lalurarsa komai girmanta,ire iren sabreen din guda goma yana ganin yafi qarfinsu nesa ba kusa ba,baima san abinda mazajen da ta dinga tatsewa me suke tsammanin samu haka daga gareta ba da har ta samu tasirin gusar musu da hankali.

"Labari kike bani?.....ko tambaya kike?,ko daukan excuse?" Yayi maganar a nutse yana dage mata dukka girarsa guda biyun bayan ya dora qafarsa daya saman daya,ya kuma yi relaxing jikin makarin sofa din.

Duk sai ta ji ya muzantata,akanme zai dinga mata tambaya akan abinda ya gama fahimtar inda ta dosa?. Tsaiwarta tadan gyara tanason hana kanta jin nauyin idanuwanta.

"Amma dai cikin zamanmu ba sharadin tabamin waya.....wayata sirrina ne,bana tunanin akwai abinda ya shafeka a ciki" Ido ya zuba mata kamar bazaiyi magana ba,yanaso yaci gaba da karantar bayan karatun da yayi mata na binciken da yayi a kanta. Ya fuskanci akwai burbishi da tasirin rashin kunya tattare da ita. Yarinyar da ko saddiq ba sa'anta bane ballanta musaddiq ko farouq.....amma tana da zarrar tsaiwa ta fadi mishi magana yadda takeso. Wannan wani abune da ba wata diya mace data iya fuskantarsa dashi....kai koda dan uwansa namiji yana matuqar shakkar hakan. Uwa uba akwai tasiri na girman kai da rashin tsoro tare da ita,yanaso yaga ya zatayi handling wadannan attitude guda biyun da wadannan shekarun nata?.

Kaman zaiyi magana sai wayarsa ta dauki tsuwwa,manhajar da yakanyi amfani da ita wasu lokuta da zata gaya masa cikakken sunan wanda ke kiransa koda bashi da number wayarsa ta karanto masa sunan fareeda Khaleed mustapha. Kusan a tare suka kalli wayar shi da ita,a nutse ya cire hannunsa ya kashe wayar gaba daya bayan yayi rejecting call din,amfanin manhajar kenan ta gaya masa wanda ke kira,basai ya saki aikinsa ya dauka ba ya zamana me kira baida wani muhimmanci har haka,saboda mutum ne shi mai darajta lokaci.

Agogo ya kalla sannan a nutse ya maida dubanshi kanta bayan ya sauke qafafunsa duka qasa,abinda ya sanyata sake kame ganinta gudun kada idanun nata su gano mata abinda yafi qarfinta,don ta lura kamar bayajin nauyin zamansa a haka.

"Kin tsallake iyakarki,kin shigomin part ba tare da Neman izini ko sallama ba......and kin tsaya kina ban labari akan abinda bai shafeni ba.......wai...." Ya fada yana tsuke fuskarsa sosai gami da maida qafafunsa saman table sabanin dazu dake kan sofa

"Meye amfanin zamanki a gidan nan?.. Kina zaton na kawoki ne don na killaceki waje daya kiji dadin rayuwa?,ki samu tsaro kiji dadin ci gaba da qwamushe asusun mutane?,ko na kawoki ne don kizo kicinye min abinci na?,ko kin dauka na daukoki ne don wani abu daban?,thought ma dai nasan ba zaki taba mafarkin wannan shirmen ne wato SO ya sanya na kawoki ba....." Wani radadi takeji yana taba zuciyarta,abu daya da zata iya yabonsa akai takuma san ya qware akai shine baqar magana kamar tsohon mahauci,idaninta da suka fara canza launi takai kansa,ya gyara zamanshi sosai yana hade yatsun hannunsa guri daya yana maida dubansa kanta.

"Kina magana akan sharadi yarjejeniya da sauransu......for now ma yakamata kisan me ya shigo dake cikin gidan nan.......Initially don ki gane me ake kira da respect........attitude dinki su koma irin na kowanne mutum.....secondly kuma..........ki maida min dukka kudina da kika debe.....don ban nema kudina saboda mata irinku su mora ba......" Wani kallo harrr ta bishi dashi,sai ya daga dukka girarsa sama

"Yes......duk wanda zayaci kudina to yana da cikakkiyar hujjar da zata bashi daman cin in a polite way.......da naso a ranar da kika diba a ranar zan saka a kawomin ke har nan..... " Idanu ta zubawa Kyakkywar fuskarsa yadda yake bayani a nutse hankalinsa kwance. Ashe shi din ma mayen kudi ne?,kallon kitse akewa rogo?. Eh tasan tabbas ta cire kudade masu nauyi da yawan da ita kanta sai data girgiza,amma kuma bata dauka har xai sanya qulafucinsa akan kudin daya tsere musu ba har haka.

"Baki da hanyar da zaki biya Muhammad jadda kudinsa?......zan taimakeki tsill dai don kada kiyi prison a banza.........daga yau ya daukeki aikin shara da gyara masa bedroom da kuma wanke masa toilet dinsa......zan biyaki kaman yadda yake biyan kowanni ma'aikaci dame aiki a qasansa.......but.....i will not pay you anything.......zanyi writing down komai har ki kammala biyana" Yakai qarshen maganar gaskiyar abinda yake fada tana fita daga cikin idanunsa. Soma tattare takardunsa yayi

"You can go" Ya furta cikin halin ko in kula.

A lokacin tana jin kamar ta qarasa gabansa ta amayar masa da dukka abinda ke zuciyarta,tana jin kamar ta isa gabansa ta nuna masa wace real sabreen,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana kwabarta tare da gaya mata any mistake idan tayi itace a ciki.

"Ya soma cin abincinki shine abinda ya kamata ki damu dashi bawai maganganunsa ba......if kikayi abinda zai sake sanya masa shakkan sakewa da gidan dukka ayyukanki zasu koma baya.... Sisters dinki zasu ci gaba da zama qarqashin hadari" Maganganun da suka fito daga qasan zuciyarta kenan,suka kuma sanyata tsaiwa cak daga takun data fara don matsawa zuwa gareshi.

Remote din ya dauka ya bude mata qofar yana ci gaba da abinda yakeyi

"Hey" Taji ya sake fada sanda ta sanya qafarta daya a waje,saita dakata ba tare data waiwayo ba

"Mind you....banason qazanta,i don't want it,ki kiyaye". Da sassarfa da kuma hanzari ta soma sauka saga stairs din har kamar zata fadi. Kuka ne yakeson qwace mata amma bataso yaji ko ya gani,don ta yiwa kanta alqawari ba zata taba bari yasan lagonta ba.

Baqincikinta yadda ya fadi mata dukka maganar da ke ransa,nata zuciyar da ruhi cike maqil da maganganu amma TARKON da take ciki yasa bazaiyuwu ta fiddasu ba.


*_Washegari_*


Tun shida na safe zuwaira ke kai kawo tsakanin shiyyarsu zuwa ainihin falon da kuma kitchen din. Jin shuru ba alamun tashi sai ta fara aikin gyaran dukka falukan da kuma kitchen din. Duk wani motsi da zataji hankalinta yana kai,tanaso ta samu cikakken bayani akan komai yadda zata zama cikakkiyar informer na maamah. Tanason bata duk kalar bayanan da takeso don tana son ta doke matsayin hajja harira wajen maamah. Ta kowacce fuska da kuma yanayi tanason ta taka matsayin da zata zama aljihun daman maamah a sanda burin maamah ya cika din. Itama tata zuciyar da ruhin cike suke da nata kalar burin da take fatan zuwan ranar wanzuwarsa.

Wani irin qarfi ta sanya ta danne zuciyarta ta fito shirya masa breakfast,duk da asara akayi daren jiya na dukka girkin da sukayi,sai tashi tayi tsakiyan dare ta kwashesu ta zuba a inda ta saba zubawa.

Yau din cikakkiyar shiga tayi,ta rufe jikinta sosai tunda ta fahimci ba ita kadai bace cikin gidan. Idanunta duka sunyi nauyi saboda kuka da rashin cikakken bacci. A hankali take ratsa falon hankalinta yana qofar kitchen din.

"Barka da fitowa ranki shi dade" Taso ta tsorata kadan,don gaba daya ta manta da wata baba zuwaira a gidan. Ta sauke dubanta a kanta sanda zuwaira ke qare mata kallon qwaqwaf. A jiya batayi cikakken bacci ba sai data gama fahimtar inda kowannensu yake kwana ita dashi. A gaban idanunta ta sauko daga samanshi a gaggauce cikin bacin rai ta fada dakinta,abincin dataxo ta kwashe kuma baici ba,a daren itama bata kwanta ba ta sharhantawa maamah komai.

"Ya zama dole na matsa mata lamba ta yaudaroshi ya zama a tafin hannunta" Abinda maamah ta furta kenan,tsoron taurin kai irin nasa yana damunta. Tasan halinsa da kafiya akan abinda baida niyya baiyi masa ba......amma zata sake yin amfani da qarfinta a matsayinta na uwa karo na biyu.

"Barka kade" Ta amsa mata a taqaice ba tare data sake dubanta ba tayi kitchen

"Nace ba,ba abinda za'ayi kuma?"

"Babu....kije saina nemeki" Ta amsa mata a taqaice,don kwata kwata batason doguwar magana gaba daya. Da kallo zuwaira ta bita har ta shige kitchen din,sai ta saki murmushi tana ji a ranta ya kamata taci tudu biyu fa......bangaren maamah din da bangaren yarinyar.....abinda ta kwana kenan tana tunani akai,gwara tayi amfani da damarta,ta yadda koda gaba kome ya faru zai zame mata ribar qafa,salon maganar nan da hausawa kance idan tayi ruwa rijiya,idan kuma batayi ba masai.

Dukka 4glass stove gas din ta kunna kowanne ta dora abu akai. Da zafi zafinta ta saka 'yar basirarta ta kammale breakfast din cikin taqaitaccen lokaci,ta gyara inda zata gyara ta fara daukan luxury Warmers din tana jerasu saman dining.

Cikin ginshira da wani irin tsanaki gami da nutsuwa yake saukowa daga saman stairs din,kunnensa manne da Bluetooth yana amsa waya,lokaci guda kuma yana qoqarin gyara tie dinsa.

Hankalinta yayi nisa sosai cikin duniyar tunani,fargaba kuma na sake cikata kamar kullum na kada a sake tafka asara yaqi cin komai kamar kullum,asarar da take sake kusantata da faduwarta da samun matsala a rayuwarta.

Tun daga nesan idanunshi suna kanta,duk da baiga fuskarta ba amma ya gane itace. Sai ya dauke dubansa yana haurawa zuwa steps din ya wuce zuwa kitchen. Qamshinsa kadai shi ya ankarar da ita,ta daga kanta tana bin bayansa da kallo gabanta yana wani irin faduwa,cikin mutuwar jiki ta ajjiye spoons din hannunta taja kujera daya tana jiran fitowarsa cike da hope.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 35


_Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya auri nana fadima,sai manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin sadakinta),sai sayyadina Aliyyu yace "ba komai a wajena" Sai manzan Allah S A W yace "ina sulkenka?"_



35


Coffee ya hadawa kansa,yayi tsaye jikin kitchen cabinet yana kurba a hankali. Kwanakin nan duka baici wani abincin arziqi ba,sai kame kame da cin abincin waje,wanda yasan totally isn't safe musamman ga mutum sannanne irinsa da ta kowacce fuska cikin barazana da qoqarin kawo musu hari ake ta duk wata siririyar kafa da za'a samu dama. Iya lamarin maamah da yarinyar ya isa zama izina a gareshi,abu a cikin gidan.... Amma kuma farautarka akeyi.

Sai yaji gaba daya coffee din ya fice masa a kai,yana qaramin tsaki ya ajiye cup din,ya ciri paper towel ya goge lips dinsa duk da ba baci sukayi ba ya fara takawa a nutse yana fita a kitchen din.

Sau daya tak ya kalleta ya dauke kansa,ya taka a nutse yana isa gabanta. Tsaiwarsa ta sanyata daga kanta,akwai inches tsakaninsu amma tana jin kamar ba wani gap daya rage musu. Idanunsa saman lips din nan nata da suke very smooth,ba digon komai akai sai ainihin color dinsa. Smart key na qofarsa ya dora saman table din,ya kuma harbasa gabanta. Ya motsa labbansa zaice wani abu wayarsa ta fara fidda wani tattausan ring me kama da sarewa,irin ring din da zai iya haifarwa da mutum karyewar zuciya musamman ga masu karyayyiyar zuciyar. Fareeda Khaleed mustapha sunan wanda ke yunqurin samun sadarwa dashi kenan aka sanar mishi. Maimaita kiran sunan me kiran wayar ta soma yi kamar ba zata dakata ba. Saman kunnuwanta sunan ya sauka,irin sunan da taji a wancan daren. Iska ya furzar daga bakinsa yana sauke numfashi,sannan yana qaramin tsaki gami da ciro wayar da wani dan zafin nama yana yanke kiran ya jefata aljihun yana sake sakin tsakin. Baki ta tabe qasa qasa tana kauda fuskarta wani sashen,can qasan zuciyarta kuwa gulma take,tasan za'a rina.....koda dukka jikinta kunnuwa ne ba zata taba yarda mutum kamar muhammad jadda bashi da kowa ba.....mutum kamar muhammad jadda baida ajiyayyun 'yammata da yake debe kewarsa dasu ba......ba zata yiwa kanta qarya ba,idan tace mummuna ne ko bai hadu ba tasan tabbas wannan din gundumemiyar qarya ce ta zabgawa kanta......to kuwa tasan zai wahala a rasashi da wasu halaye da sukayi kama da wannan. A iya rayuwarta.....a iya mazan data hadu dasu harda wadanda basu kaishi bama,masu kudi sosai matasa masu jini a jika,taga dabi'u kala daban daban da halayen da bata ma tsammaci ganinsu ba,yaga yadda matan aurensu suke ba komai ba a wajensu......taga irin qalubalen da shuke fuskanta a tattare dasu....matasan cikinsu harma da masu yawaitar shekaru,wannan abun ya sake cire mata sha'awar abubuwan nan guda biyu a ranta SOYAYYA da kuma AURE. Gadai guda daya nan ya cimmata,saidai tana da yaqinin ba zata bari yayi galaba a kanta ba,yayin da take bawa kanta tabbacin tafi qarfin wata soyayya taci galaba a kanta,don idan ka dauke soyayyar qannenta bata taba tsintar kanta cikin soyayyar komai ba,wannan shine yake sake bata yaqini tabbaci da nutsuwan ba zata taba yin soyayya ba....saidai ita a sota
(Nace uhmmm....maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta). Idanunsa ya maida saman fuskarta,a nutse ya fara magana kamar wanda ya hada jini da gidan sarauta.

"You can start your work today.......but......ya kamata ki sani,nasan komai da yake every single room......sannan nasan place dinshi,so do your own business......kiyi iya abinda akace kiyi" Daga haka sai ya juya a nutse don sauka a wajen,saidai kuma muryar da yaji tana gaidashi ya sanyashi tsaiwa yana juyawa wajen.

Zuwaira ce a durqushe a wajen,da yanayin da yake tabbatar masa ba yanzu yanzu ta shigo ba. Sunkuyar da kanta tayi sanda ya zube mata kaifafan idanun nan nasa,yayi mata wani irin kwarjini da bata taba ganinsa idanun kowanne mahaluki ba sai a kansa. Wannan kwarjinin nasa ya sanya suke qauracew waje duk sanda ya shigo gaida maamah. Sosai goshinta ya soma tsatstsafo da gumi,tana ganin kamar a iya kallonsa kadai zai iya bankado komai ya kuma fallasashi.

"Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye ba wani wasa ko sassauci a muryarsa,abinda ya sanya zuwaira ta ida rudewa,ga turancin daya jefeta dashi wanda ya saka a duhu

"Eh....na'ammmm.....eh"

"Wacece ke?" Ya maida mata tambayar da hausa. Caraf ta kama maganar tasa

"Nice zuwaira.....zuwaira ce,me aikin da hajiya maamah ta aiko don taya uwargida sabgogi da hidimomin gida". Ta qarashe fada tana daddafe hannuwanta a qasa,saboda ji tayi kamar zata fadi daga tsugunnen.

Hannayensa kawai ya zube a aljihun wandonsa yana ci gaba da kallonta,yana kuma son ganin fuskarta sosai. Duk wani daya rabi maamah yana da nashi question mark din a wajensa.....duk wani wanda maamah zatayi qoqarin hada connection tsakaninsa dashi baida aminci ko nutsuwa kwata kwata dashi,don haka yake sake shawarwarin qarawa musaddiq kwanakin zamansa a qasar da ya aikeshi ba tare da wani qwaqwaran dalili ko kuma buqatar hakan ba.

Hannayensa nasa ya sauke ya soma takawa yana sauka daga wajen,zuwa sannan qiris ya ragewa zuwaira ta saki fitsari a wando.

"Kada na sake ganin gilmawarki cikin gidan nan indai ina nan......duk ranar kuma da kikayi sake hakan ya faru.....ki fara hada kayanki na barin gidan nan....basai nace ba"

"In sha Allahu ranka ya dade,tuba nake" Ta fada dukka jikinta yana rawa.

Daga ita har sabreen ba wanda yacewa da dan uwansa komai. Kusan minti biyar da fitarsa sannan ta tattara qarfinta ta miqe tana sake hawa steps din dining da sabreen ke zaune akai. Fuskarta qunshe da munafukin murmushin nan ta soma gaidata

"Barka da asuba ranki ya dade.....ashe har kin gama aikin?,ba zaki jira nazo ba?,hidimar ai sai tayi miki yawa,da sai na rage miki ai.....iyaka idan na gama abincin ki bada kalar maganin da za'a zuba a ciki......kedin abar tausayi ce ranki ya dade,kullum addu'ata da fatana ki kubuta daga hannun hajiya mariya lafiya" Zuwaira tayi maganar cikin matuqar sanyin muryar.....tsantsar alhini da kuma nuna damuwa.

Tunda zuwaira ke maganganun nan a jejjere sabreen bata daga kai ta kalleta ba sai da tazo gabar qarshen maganar tata. Kalmar tausayi data furta a maganar nata yaja hankalin sabreen ya kuma tsaye mata a rai. Sosai ta zubawa zuwaira idanu tana son tantance gaskiyar abinda ta fada,saidai kuma abun mamaki haka kawai sai taji ta kasa gamsuwa da ita.



Please Login or Register in order to submit comment