Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sam,saidai kuma ya cika da mamakin yadda tun daga farfajiyar gidan ta zama sak irin yanayin ginin da yake so,kuma zabinsa.

"Alhamdulillah" Farouq ya furta yana dubansa,shima shi din ya kalla,yaja numfashi kadan sannan yace

"Shikenan?,hankalinka ya kwanta?,saika wuce gida ka kwanta" Murmushi kadan farouq ya saki,ya miqa hannu bayansu. Kyakkyawan bamboo basket ya fiddo,wanda aka yiwa wani irin ado da tsari,can qasan ransa yana jin tsoro sosai kan yadda yake ganin rashin baiwa komai daya shafi auren muhimmanci daga wajen fu'ad din. Baya jin tsoro akan zaiyi wani maras kyau ba......saidai bashi da tabbaci ko guarantee din zaiyi komai daidai.

"Ga tsarabar amarya" Ya fada yana ajiye basket din a tsakaninsu. Harara ya watsawa farouq din sannan ya fara yunqurin bude murfin motar,sai daya fice din sannan yace masa

"An gaya maka harda ni a wannan wasan yaran?"

"Please mana fu'ad,waye ya gaya maka ana shiga wajen amarya haka?,take it.......it's sunnah fa" Baiko waiwayeshi ba ya fara nufar hanyar dake nuni da shine ainihin qofar shiga gidan gaba daya.

"Aurenma sunna ne kuma jihadi zanyi".

"Jihadin daukan fansa?" Ya fada a ransa a fili yana dariya qasa qasa. Murfin motar ya balle shima ya biyo bayansa duk da baida niyyar shiga cikin gidan don duka ba tsarinsu bane,a qasan ransa yana fata da addu'ar Allah yasa reshe ya juye da mujiya.

Dab da bakin kyakkyawar qofar ya dukansu suka tsaya kamar wadanda aka yiwa umarni,a nutse farouq ya sunkuya ya ajiye basket din sannan ya dago yana duban tsakiyar idanun fu'ad. Koda baiyi magana ba fu'ad din ya fahimci magana yake gaya masa da idon. Farouq ya cancanci kowacce girmamawa da qauna,don haka sai ya sunkuya kawai ya dauki basket din yaci gaba da takawa

"Muhammad" Yau farouq din ya kirashi da zallar sunansa da ya jima da manta rabon da yaji ya kirashi dashi. Waiwayowa yayi suka hada idanu.

"Don Allah......kayi dukkan abinda ya dace,ka riqeta yadda ake riqe kowacce macen aure". Idanu fu'ad ya lumshe yana budesu lokaci guda,shima nasa idanun cikin na farouq

"Banyi maka alqawarin zaman aure irin na kowanne miji da mata ba......ban maka alqawarin cewa zataji dadi kaman kowacce mace ba.......amma zan kyautata idan ta kyautata.......manufar aurendai kuma banajin zata canza,dole tayi wannan karatun,saidai shima zaizo a duk yanayin data zabi yazo" Daga haka ya juya yana shigewa don bayason farouq ya sake neman karyashi da kowacce kalma daga bakinsa.

Ba zata iya cewa ga yanayin data wanzu a ciki ba tunda su momma bahijja da sauran mutanen da basufi ashirin ba suka juya suka barta a gidan da suke fama jaddada kyau da tsaruwa da kuma dukiyar dake ciki wanda babu daya a ciki da yayi mata. Ko bayan wucewarsun shuru ne yaci gaba da wanzuwa cikin gidan,jifa jifa tana jin tamkar haushin kare daga dan nesa kadan daga inda take. Ko sau daya bata janye mayafin kanta ba,saima qara duqunquna da tayi tana daga zaunen saboda yadda azababben zazzabi yake sake sauko mata. Wani irin tsoro mara misali yana saukar mata,kalar tsoron da bata taba jin irinsa ba. Empty takejin kwanyarta,kaman an kwashe komai dake ciki an zuba tsoro da rashin nutsuwa,sai muryar matar dake da sunan surukarta a yanzu wadda keta mata kai kawo ita da dukkan dokokinta cikin tsakiyar kanta tamkar ana mata bita kada ta mance.

"Assalamu alaikum warahmatullah" Ya furta qasa qasa yadda baya zaton akwai wanda zai jishi,saidai don kawai yasan sallamar wajibi ce a musulunci koda babu kowa cikin gida,Ko ina da haske tarwai tamkar rana,ba wani qwai da yake a kashe. Da idanu yake bin parlor din da kallo,wani tsari me kyau da ya dace da ra'ayinsa tamkar dashi farouq yayi shawara wajen tsarin gidan,tun daga kan color na paint dana furniture din.

A nutse yaci gaba da takawa cikin parlor din hannunsa zube a aljihun shaddarsa. Bai tsaya ba sai daya isa tsakiyar parlor din,ya aza basket din hannunsa saman wani dan qaramin table dake tsakiyar falon.

Juyawa yayi yana ci gaba da bin kowanne makunnin fitila dake falon yana kasheshi daya bayan daya,har sai da hasken daya rage kawai dake farfajiyar gidan wanda ke ratsowa ta lafiyayyun curtains din da aka zagaye falon dashi.

Sai daya tabbatar ba wani sauran abinda ya rage sannan ya sauya akalarsa zuwa upstairs da yake kyautatan zaton a can ne sashensa yake.

Stairs na farko kadai ya taka wayarsa tayi qara. Ya dakata ya sanya hannunsa a aljihunsa yana cirota da niyyar kasheta gaba daya,don a matuqar gajiye yake,baya buqatar duk wani abu da zaiyi disturbing nasa. Sanda ya bude da nufin kashewar saqo ya cika screen na wayarsa.

*_welcome home mr jadda,Its strongly warning Cease all preparation,Stop all activities,good night,have a nice night_*.

Maimaita karanta saqon yayi kusan sau uku,zuwa yanzu ranshi ya fara baci,ya kuma hango zallar rainin wayo daya fara shiga cikin lamarin. Koma su waye suna bibiye da duk wani motsi nasa kenan?. A irin wannan saqon da suke aike mishi,ya tabbatar inda suna da ikon cimmasa da tuni sun cimmasa din.

Da baya ya dawo ya zauna saman daya daga cikin kujerun falon wadda tafi kusa da stairs dinsa. Mutum uku ya nema,ya aike musu da komai,sannan ya saka binciken cikin schedule dinsa na gobe,ya kashe wayar ya jefa a aljihu ya miqe a nutse yana wucewa saman.

Babban parlor ne da akayi masa wani tsari na musamman,wanda ke dauke da dining area well designed,sai dakuna bedroom biyu da Master room guda daya dake da lafiyayyen balcony da zai baka daman ganin gidan gaba daya gaba da baya.

Abinda ya bashi mamaki komai nasa an jera masa,kayanshi da komai nasa,abinda farouq kadai bai taba ba abinda ya shafi dakin sirrinsa dake wancan gidan nasu.

Master bedroom din ya zaba,ya tura ya shiga yana rage hasken fitilun,ya qarasa a hankali ya zauna daga bakin sofa bed ya ware hannayensa dake saman cinyarsa yana karanto addu'o'in wanzuwa cikin sabon muhalli


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 13


Page 13


yana sauke dubansa akan ko ina. Bai jima ba ya shafa duka addu'o'in sannan ya miqe. Har cikin ransa yana jin gidan yayi masa,komai ma na gidan kuma ya dace da tsarinsa,tabbas farouq din dan uwa ne kuma amini ne na gaske.

Bathroom ya shige kai tsaye,ya hada ruwa me dan dumi kadan bame yawa ba,don garin an dan fara zafin da ake sanya rai zai kaimu zuwa ga damuna. Sosai yayi wanka,ruwan dumin ya ratsashi,ya hada da alwala ya fito.

Wasu milk color pajamas ya sanya masu tsananin taushi na kamfanin Ralph Lauren,gray color da suka fidda haskensa da kuma wani kwantaccen kyau nasa daya mallaka,idanunsa sunyi laushi sosai saboda tsananin gajiya,don a daddafe yayi wuturi kadai ya wuce saman gadon.

Sasai yaja numfashi yana furzarwa sanda gabbansa suka samu sakewa sosai cikin tattausan gadon da aka lullube da luxury bedsheet dan qasar italy kamfanin feretti. Sosai yaja qamshin da yakeyi har can cikin cikinsa sannan ya fesar da iskar waje.

Qamshi......qamshi yana daya daga cikin abinda ke matuqar burgeshi a rayuwa,shi yasa yawa yawan gift din da yake samu suna da alaqa da abu me qamshi,walau turare body mist ko makamancin hakan......farouq ya dade da sanin wannan,shi ya sanya ya saka company din da sukayi aikin shirya gidan suka tsumashi da qamshi.

"Ko zata iya tsaftace gidan ya zauna a haka?" Ya raya a ranshi,sai ya tabe baki yana juyawa zuwa barin hannunsa na dama gami da jan qaramin tsaki.

"Ruwanta tayi tsafta ruwanta kada tayi" Ya raya a ranshi. Abu daya ya sani shi din zamansa a gidan bame tsaho bane,don zuwa yanzu dole ya fara tabbatar da tsaiwar company dinsa na abuja da za'a bude kafin ya sakar musu. Wani abu kadan yaji ya taba ransa daya tuna yawan massages da yake samu na barazana akan company din

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya furta murya qasa qasa

(Shin kinsan qarfinta kuwa?,kisan aikin da take yiwa me yawan ambatonta?,damuwa gareki?,ciwo ne?,ka maqiya suka sakaki a gaba?,ki kamata qamqam ki hada da salatin annabi kisha kallo,Allah ya bamu dacewa yayi mana maganin damuwoyinmu ameen).

*******Ba zata ca ga sanda wahalallen baccin dake cike da mugun zazzabi ya dauketa ba,ita dai ta bude idanunta ne kawai ta ganta kwance daga bakin gadon,wanda ta tabbatar da tayi mugun juyi cikin baccinta ba abinda zai hanata fadowa.

Tsoro gaba daya ba dabi'arta bane,amma kuma tun a jiya ta fuskanci yana neman samun wajen zama cikin zuciyarta da ruhinta. Tsoron abu guda kawai zata iya cewa ta fahimta.....girman gidan data tabbatar yafi qarfin zaman mata hudu ma da iyalinsu.....alamun motsi da shigowar motarsu dama fitar da motar ta sakeyi,daga haka bata sake jin komai ba amma kuma tsoron bai saketa ba.

Idanunta ta maida ta lumshe. Ba ciwon kan zuwa yanzu,ba kuma zazzabin,saidai tana fatan rufe idanunta da tayi dinnan ta budesu ta samu komai ya koma mafarki......komai ya shafe tamkar bai faru ba. Saidai inaaa.....akace qaddara ta rigayi fata,koda ta bude komai yana nan kamar yadda yake,agogo naci gaba da tafiya ba tare daya koma baya ko na second guda ba,wannan shi ya bata tabbacin babu abinda zai canza din,don haka ta yunqura ta miqe da wata irin kasala tana sauka daga saman gadon.

Qofa guda daya da tafi kama data bandaki ta nufa. A hankali ta shiga kamar me tsoron wani abu kada ya kamata idanunta nabin kowanne sashe na bandakin da kallo.

Komai luxury ne kuma designer daya sanyashi yasha banban da toilets da dama. Sai data bata lokaci tana qoqarin tantance komai,sannan ta isa sashen wanka dake dauke da jacuzzi da bathtub,ta soma zare kayan jikinta. Ko ina na jikinta ya mata nauyi,sam ba dadi saboda nuqurqusar zazzabi,uwa uba kuma akwai rashin sabo na kwanciya ba tare da tayi wanka ba,don haka yanzun kai tsaye taji wankan tafi buqatar yi kafin komai.

Sanda ta isa ga closet dinta kuwa sai taji gaba daya ta raina duniyarta ta baya,duk yadda taso abun kada ya burgeta amma hakan bai samu ba,dolen dole ma ya burgeta,komai a jere a tsare tamkar wani hamshaqin boutique daya amsa sunansa ta fannin saida komai da komai. Sai yanzu ta fahimci maganar da hadiyya takeyi bayan sun dawo daga gidanta,suturu ne da batasan iya sanda zata kammala sakesu ba,kusan komai ya cakude,kayanta na gida da wadanda ta taras a nan,bata ma iya ganin natan kwata kwata,duk yawa ta suturarta kuwa sun boye tsaf cikin closet din. Batason ta wahalar da kanta da yawa don bata da wannan energy din,dole ta zabi atamfa kawai riga 3quater da straight skirt ta saka.

*******Tun daga daren jiya data dawo daga gidan maamah din wato mariya,bata samu wani cikakken lokaci daya haura mintuna talatin ba cikin tunani ba. Kowanne motsi da z 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~atayi yana motsa mata da tsananin kwadayin cikar burinta,wato wanzuwar jininta cikin jinin mamallakin kamfanin sarrafa gold da diamond din. Ta sani......akwai wasu tsauraran hanyoyi daya kamata ace an sharesu fetal kafin takai ga haurawa izuwa nata bigiren......to amma shin.....mallakar fu'ad a hannun mariya kamar yadda takeso zai iya zama mataki kuma mabudin tata nasarar?.

Amsoshi guda biyu ne wato eh da kuma a'ah. Eh idan har tayi nata aikin akan hajiya mariya tazo hannunta.....ita din zata zame mata tsani na mallakawa tata shalelen fu'ad. Aah idan har ta gaza samun mariya a hannunta ko kuma fu'ad ya gagara zuwa hannun mariya kamar yadda take buri......shin me zai hana tayi nata aikin itama daga gefe?,tayi amfani da tata basirar?. Wannan tunanin kadai ya sanyata yankar asubahi,bata kuma tsaya a ko ina ba sai a gaban babban bokanta wato BAHAGO.

Maida foldable basket din me zip tayi ta rufe gami da zuge zip din,sannan ta maida idanunta kan zuwaira dake zaune a gabanta

"Ina fatan kin riqe dukan baya naina......don a haka nakeso su shiga kunnuwanta tamkar ni nake bayanan......bana buqatar mantuwa ballantana ganganci ko kuma kuskure zuwaira.......zaki zauna kuma a iya matsayinki na 'yar aiki kawai" Kai zuwaira ta jinjina mata. Taji dadin wannan matsayin sosai da maamah ta dauka da danqa mata,ta wannan hanyar kawai zata nunawa hajja qarfin mulki da isarta akan maamah din. Saidai kafin tace komai anyi knocking daga waje

"Waye ne?" Ta tambaya cikin qosawa,don ta fara gajiya da yawan baqin da suketa zuwa ganin gida. Jiya a daren bata kwana da kowa ba cikin gidan,tun a daren kowanne baqo ta sanya aka dinga dibansu ana kaisu gida,na wani garin tunda asuba aka debi hanya dasu.

"Nice......baquwa kikayine tace na gaya niki"

"Baquwa kuma?" Ta tambaya a mamakance,don bata tsammanin samun baquncin kowa a wannan lokaci,hasalima ta gayawa malam Sa'adu kada a sake bari kowa ya shigo,koda sun shigo ta barwa masu aiki sallahu ko waye a gaya masa tana hutawa ne.

"Wacece baquwar?" Ta tambaya kai tsaye cikin bacin rai

"Hajiya harira" Yarinyar ta amsa mata kai tsaye

"Shigo da ita" Itama ta bada amsa kanta tsaye,saidai kuma can cikin ranta tana mamakin abinda ya kawota,don a jiya sun rabu ne tanata mata tsiya,ba zata kuma ganinta ba sai ta huta da kyau.

"Kada dai ace har kin watstsake hutun kuma ya qare?" Maamah ta fada tana tsokanarta. Wani murmushi ta saki mai nuna alamun akwai damuwa.

"Ina naga ta hutu mariya?,matsala ta tasomu gaba tun cikin daren jiya?". Idanu maamah ta fiddo tana matsa mata wajen zama

"Subhanallah.....ni wallahi har kin sanya gabana ya fadi......matsala ko yaya take banson jin koda sunanta,me kuma ya faru?". Baki ta tabe tana zama kafin ta bata amsa

"Waini harira za'a gwadawa iya shege?.wai qanin mahaifin laila ne yazo yakeson gwadamin qaramin shege ne shi.....lallai lallai wai ya bada laila.....aure nan da wata guda me zuwa". Ido maamah tadan fiddo a mamakance

"An gaya masa a ina yanzu ake hakan?,ya akayi kika bari yayi wannan bunqasar hajja?". Kai ta girgiza irin kana cike da tsananin takaicin nan

"Ki barni dashi......zan gwada masa tawa iyawar indai harira nake.....shi yasa kika ganni gab da takewar rana.....ajiyar laila nakeson kawo miki".

"Laila ai d'iyata ce.....wannan bazai zama matsala ba".

"Shege ne fiye da yadda baki zato,shi ya kusan zamemin matsala zamanin zamana da abbansu.......inda zai yiwu kuma ba takura.....kiyimin wannan alfarmar ki ajemin ita gidan fu'ad,don na tabbatar a can dinne ko daga qiyama ubansa zai dawo bai isa ya shiga da sunan koda ganinta ba ballantana daukota......wadannan qedarun sun isheshi".


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 14

15


Da farko maganar taso yiwa maamah din banbarakwai,amma koda ta tuna wacece hajja a wajen ta da kuma tata fafutukar da suka gama yi tare suke ma kuma kanyin sai taji wannan din ba komai bane.....ai rama halasci sai dan halak,banda ma plan din da take dashi batajin zai zama wani abun damuwa don laila zata zauna gidan. Ta tabbatar bata da matsala da laila,ko ita din tana iya zama me sanya musu idanu akan plan dinsu.

"Kada ki damu hajja,ni ba abinda bakiyimin ba,kinfi qarfin haka a wajena.....hakanma qarin samun tsaro ne,don yau nakeson tura zuwaira ta zauna dasu ta dinga sakamin ido akan komai". Murmushin qasan zuciya hajja ta saki,bahago shu'umi ne fiye da yadda take zato,ya gaya mata,ya sake gaya mata dama ba damar musu......mariya ba zata iya musanta mata ba.

"Na gode sosai mariya....Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci". Kai ta girgiza tana murmushi

"Ba wannan tsakaninmu,kinfi qarfin komai a wajena......ko yau tana iya shiryawa sai zuwaira ta biyo ta dauketa su wuce,don banason magariba tayi basu isa gidan ba" Ta fada tana daga wayarta ta duba lokaci. So samu ace tun da safen nan ya karya da breakfast din yarinyar da zai zama lullube da makamanta,to amma sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba'aje ba.

Da wani irin farincikin samun nasara ta isa gida. Ta samu laila din zaune a falo tana kallo. Kusan tunda ta kammala karatu aikinta kenan. Hajja tayi tayi a samar mata aiki ta fara tace sammm ita ba zata iya yawo a gari kowacce safiya ba,hasalima ba zata iya barin baccin safe ba,idan ta barshi waye zaiyi mata shi?.

Sai data sha ruwa sosai da lemo,sanyinsa ya sanyata ta fara dawowa hayyacinta sannan ta maida dubanta kan laila dake matse matsen waya.

"Mansura ta kawomin kayan nan kuwa?" Kai laila ta girgiza alamun a'ah ba tare data dauke idanunta daga kan wayarta ba. Hotunansa ke matuqar jan hankalinta,kullum kwanan duniya ta kalleshi kota tuna dashi sai taji kaman bata tare da nutsuwarta.

Tsaki hajja taja ta jawo wayarta tana mita ita daya

"Yarinyar nan inajin sai taje gidansu tayi kwana biyu sannan zata shiga hankalinta". Dab da kiran data mata zai shiga sai gata ta shigo. Niqi niqi dauke da kaya wanki a wanke a goge a hannunta. Mansura daya daga cikin surukan hajja da suke rayuwa gida daya,suke kuma karban duk wani mulki isa da izza tata hannu bibbiyu don ba yadda suka iya,an dauresu da duk wani zaren sihiri da zai bata damar mallakarsu kamar yadda ta mallaki mazajensu.

Ko sallamarta bata amsa ba sai harara data jefeta dashi

"Uban me kika tsaya yi?,na baki wanki tun bayan asuba da kadan amma sai yanzu zaki gama don bakisan muhimmancin kayan ba?" Bata amsa mata ba saboda nauyin kayan har sai data zubesu.

"Kiyi haquri hajja,sai dana sallami yara suka wuce makaranta,abbansu ya fita kasuwa sannan....."

"Sannu dadi 'ya'ya dadi miji,bakisan aikina gaba yake da nasu aikin ba su duka?,kada ki sakemin irin wannan?"

"Kiyi haquri" Ta fada kanta a qasa,saita janye kallonta daga kanta tana sake jan tsaki

"Laila tashi ki kwashe kayan nan ki zuban a wardrobe". Sai sannan ta cire kanta ta kalli kayan

"Kai.....gaskiya hajja sunyimin nauyi bazan iya ba.....saidai a barsu a nan,zuwa anjima idan na tashi na kwashesu daya bayan daya". Tsaki hajja din ta sake ja ta maida dubanta ga mansura din

"Kwashesu kikai min wardrobe,kuma bance ki zauna ba bare ayimin bincike a daki". Itadai batace komai ba ta tsugunna ta kwashe ta wuce dasu.

"Zaki ajiye wayar nan muyi magana ko sai na fasata?" Hajja tayi maganar da daga murya,abinda ya sanya laila kashe wayar ta ajiye agefe,sannan ta juyo wajen hajja

"Gani" Sai data dire cup din hannunta sannan tace

"Kaman yadda nasha gaya miki ina da plan ina da tanadi a kanki.....tanadina ba kowa bane face muhammad fu'ad jadda.....mamallakin jadda diamond chore resources.....dan qawata mariyah"

"Ahhhhhh" Laila ta fada tana fidda idanu cikin tsananin mamaki da kuma gigita. Wani abune da bata taba kawoshi cikin kanta ba,hasalima batasan akwai qawance har haka tsakanin momynta da mahaifiyarsa ba

"Wasa kikemin hajja?" Ta fada tana kallonta sosai gudun ganin samu da rashi

"Na taba wasa irin wannan dake?" Maimakon ta amsa mata saita daka wani irin tsalle tayi kanta ra ruqunqumeta.

"Wayyo Allah mamana......i love you so much mamana......you fulfill my dream"

"Kinga shashasha zata karyani......da Allah zauna muyi magana dake don gidansu zaki koma da zama na wani dan lokaci" Ido ta sake watsowa waje,tana jin komai kaman cikin shirin film ko labarun hikaya

"Serious?"

"Ubanki" Ta fada tana watsa mata zagi da yatsu biyar,saita saki dariya ta koma tana zama din kamar yadda hajja ta umarta. Baki ta daga zata watsawa mansura kira sai gata ta fito

"Yauwa saiki wuce ki tafi,ki rufen qofa.....ki gayawa madeena nan da minti talatin ta dafamin madara ta kawomin,wallahi kuma aka wuce haka sai ranta yayi mummunar baci". Kai a qasa ta amsa mata ta juya tana ficewa. Sai data fita din sannan ta maido hankalinta ga laila

"Kina jina ko?"


5N5V5W5g5Z5Z5c

Sake duban lokaci tayi,sha biyu saura na rana. Tunda ta farka tayi wanka da sallolinta bataji motsin kowa ba,don hatta securityn dake aikin kula da gidan bakajin motsin kowa,sanin da sukayi cewa hayaniya da motsi me qarfi na daya daga cikin abinda boss din nasu bayaso. Uwa uba ma su dake first gate bata yadda na ciki kamarta zai iya jiyosu. Bawai yunwa takeji ba,amma a jikinta takejin ya kamata ta sawa cikinta koda ruwan dumi ne. Kaman ba zata fito din ba amma ta miqe,ta lalubi mayafi ta lullube jikinta sannan ta sanya plate shoe dinta na jiya ta fara nufar qofa ba tare da tasan takan gidan ba ko kuma daga inda zata fara ba.

Rufaffen hallway din ta soma ratsawa,wanda aka qawatashi da wani irin wall led light na musamman,da wasu irin qananu masu haske da suka sake fidda ainihin kyan wajen. Tattausan runner carpet ne shimfide duka tsahon wajen tsakanin kowanne qofar daki zuwa na dan uwansa an qawatashi da wasu irin nature frames masu daukan hankali. Daga bangon dake facing naka kuma,babban console mirror ne da zai baka daman ganin kusan dukka jikinka har kusan cinyoyi. Akwai plants masu kyau data gani cikin flower vase masu wani irin daukan hankali,bata sani ba masu kyau ne ko ma decoration. Guri ne daya cika da hasken da koda allurarka idan ta fadi zaka iya tsugunawa ka dauka,ko ina fes da wani irin matsanancin tsaftar da babu qura ballantana ka saka ran samun wani abu waishi datti saman lafiyayyen marbles din dake lullube kuma shimfide a qasan wajen. Duk zuqar iska guda daya idan tayi da qamshi take kai mata har hanjinta,qamshin da sam bata da tabbacin daga ina yake fesowa ya karade kowacce iska dake kai kawo a wajen duk kuwa da a rufe hallway din yake.

Idanunta kafe akan staircase din dake gabanta. Batasan ina bane bata kuma fatan sani,nan din inda aka ajiyeta ma kawai tana jin ya isheta harta kammala abinda zatayi tabar cikin rayuwarsu,fatanta daya shine idan ta isa staircase din ta samu wata qofar tsakanin hagu da dama cikin dan lugu biyu da take ganin alamunsa.

Ajiyar zuciya ta sauke sanda take dab da bakin stair case din,akwai wasu qofofi hagu da dama,saidai ta daman tafi mata kama da qofar da zata sadaka da wani gurin.

Solid wood door ne me qofar biyu data dace da kalan gidan gaba daya dake bata kalan gold and off white,dayan pivot door ne wanda tafi kyautata zaton wani gurin na daban zai sadaka dashi,don haka ta nufi hannun damanta,ta sanya hannu ta murda handle din ta bude qofan a hankali

Please Login or Register in order to submit comment