Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya amsa masa yana katse wayar ya maidata ya ajiye. Shi a yanzun kasuwancinsa shine abinda yafi damunsa shine kuma gaba da komai,bai takurawa kowa ya matsawa kowa ba,don hatta da saddiq daya Kamata ace a yanxun suna tare suna duba al'amuran da suka taso musu bai masa magana ba,bai kuma ce komai dashi ba saboda yaga ya sanya kanshi cikin hidimar bikin sosai,ya bashi lokaci ya qare ya dawo hayyacinsa.....tafiya ce dai dasu tsakanin jibi da gata,kuma bazai dage masa qafa ba dole ya shirya su wuce. Girgiza kai kawai farouq din yayi,halin fu'ad saishi,baisan ma yaushe ya fita din ba bayan sun shigo cikin gidan tare. Ya sanshi sarai ya kuma sani,wani irin mutum ne shi da kasuwancinsa ke gaba da komai idan ka dauke shi anni abba da su saddiq,amma koma meye yana ji a jikinsa,yana Kuma fatan duk yadda yakai ga gujewa auren da bashi wani rashin muhimmanci ya zame masa silar shiryuwa da saituwa kaman kowanne magidanci.

A nutse farouq ya ratso cikin mutane ya yiwa anni rada. Kai kawai ta gyada sanda idanunta suke kan sabreen dake zaune waje daya bata ko qwaqwaqwaran motsi. A iya haka tana iya hangen nutsuwa a tare da ita,sannan haka kawai takejin qaunar yarinyar cikin ranta.

Tana iya hangen wasu abubuwan ta cikin mayafin dake lullube saman kanta,a sanda walima tayi nisa..... Kai kawo na mutane ya qara yawa tata zuciyar cike take da lissafe lissafe kala kala. Lumshe idonta tayi sanda aka fara gabatar da miqa gudunmawa ga amarya,wato kowa zaizo ya zube mata tasa gudunmawar adan wani babban qwarya dake ajiye a gabanta maimakon yin liqi,wanda daga nan za'a fara gabatar da lectures akan zaman aure. Numfashi ta sauke daga can cikin hunhunta,duk cika da batsewar mutanen dake a wajen bata hangi wani nata ko mutum daya ba. Sai takejinta bare a wajen da wani irin rashin sukuni da takura.

*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 21


21


A nutse aka fara zuwa daya bayan daya ana zube sabbin 'yan dubu dubun fil a miqe cikin bundles dinsu a gabanta. Ta rasa tsakanin burgewa da rashinsa wanne takeji cikin zuciyarta?,duk da ta hangi tarin nutsuwa da kamala a komai na taron.

Idanunta ta sake dagawa a hankali ta cikin mayafin tana kallon bakin qofar shigowa gurin dake facing dinta......tamkar abinda ake jira kenan saita hangi huda na shigowa. Da farko ta dauka kaman gizo idanuwanta sukeyi mata ko kuma me kama da ita ne,saidai shigowar nadra da haneefa ya qarasa kore mata dukka shakkun data soma ji cikin ranta. Wannan bai saketa ba taga abinda ya kusa doka zuciyarta saboda firgici.....maamah ce.......tana biye dasu da dukkan alamun da zasu gwada maka tare suke......tare suka shigo,don waiwayawa haneefa tayi da alama kiran sunanta tayi,sai taga ta riqe hannunta haneefa na mata murmushi tana maida mata sukaci gaba da takowa wajen tare.

"A ina ta gansu?,a ina ta daukosu?,ya akayi taje ko sukazo wajenta?,tun yaushe?,me kuma take gaya musu?" Tayi tambayar sanda taga ta tsaidasu duka su ukun kuma kowacce ta tattara mata hankalinta.

Sanye take cikin wata 'yar ubansun super embellished me asalin tsadar da jikinta ke bada wani irin santsi tamkar ba atamfa ba. Tun daga yanayin shigar zaka tabbatar da gaske ta dauki duniyarta dama rayuwarta gaba daya.....hakanan da gaske komanta yana mata dadi yana kuma tafi mata yadda takeso. Daga bayanta hajja harira ce data shirya kanta itama cikin applique lace ruwan sararin samaniya. Ita dinma duba daya zakayi mata ka tabbatar da halin yazo daya kamar yadda abotar tazo daya.

Kai tsaye ta daga yatsa tayi musu nuni da kujerar da sabreen ke zaune a kai,sai dukkaninsu suka maida idanuwansu kanta. Fuskokinsu suka cika da farinciki duk da basa iya ganin fuskarta sosai,suka motsa kamar zasu taho zuwa wajenta,amma sai taga ta sunkuya tana magana dasu. Cikin qasa da second talatin taga sun maida hankalinsu gareta.......sun kuma juya suna binta a baya zuwa hanyar data nufa,daidai lokacin da me gabatarwa ke bada sanarwar

"Mahaifiyar ango ta shigo......uwarsa kuma zata marabceta" Maganar data finciko hankalin sabreen daga shingen tunanin data afka sanda take binsu da kallo suna biye da maamah sau da qafa.....kai kace ummeensu ce ta dawo duniya.

"Uwa?.....mahaifiya?,wacece?" Ta samu kanta da shiga wannan rudanin tare da fatar a yau ta samu warwarewarsa,don haka ta buda dukka idanunta tana bin kowanne kusurwa da kallo tanason samun warwarar rudaninta.

Cikin nutsuwa da girmamawa anni ta miqe tana dosar inda maamah ke a tsaye,fuskar annin shimfide da fara'ar data ratsa har qasan zuciyarta. Har yanzu gangar jikinta da ruhinta basu daina jin farinciki da alfaharin aurar da fu'ad ba......wani abu guda daya daya zamewa maamah tamkar dafi tsakiyar tsokar zuciyarta

"Ameenatu ce ta aurar dashi" Kalmar da inda tana da ikon gogeta tsaf saita gogeta daga dukkan wata ma'adana ta kalamai.

"Barka da zuwa......sannunku da zuwa......"

"Uwa kuma mahaifiyar muhammad fu'ad jadda ba,ai haka ya kamata ne gabatarwarki ta fadi" Hajja harira dake tsaye gefan hannun hagun maamah ta furta da wata irin izza.

Kallo daya anni tayi mata ta watsar da ita gami da bawa banza ajiyarta,idanunta suna sauka akan fuskar 'yammatan su uku da take ganin tamkar ta taba ganin fuskar a wani waje. Kallonsu kawai tayi suka fara gaidata daya bayan daya,ta amsa musu tana dafa kan kowaccensu da madaukakiyar fara'a da kuma kulawa,kulawar da ta sauka har cikin idanun sabreen wadda ruhinta gaba daya yana a wajen,saidai babban qalubalenta bata iya jin me aka tattaunawa akai.

Tun daga tashin anni har tsaiwarta a wajen sabreen na tuna guraren data taba ganin fuskar matar ne. Indai da gaske itace anni......itace uwa ga fu'ad ba shakka ta santa......amma ta yaya haka ta kasance?,ya akayi yake da uwaye biyu?,me yasa anni data taba sani duk da alkhairi ya hadasu ba ita ta nema masa ita ba?,sai waccar baquwar fuskar da bata taba ganinta ba kafin faruwar wannan abun kaf tsahon rayuwarta?.

"Barkanki kade Ameenatu.......sannunki da hidima" Maamah ta maida mata da wani irin salon murmushin da ya sanya anni tajishi har cikin jinin jikinta.

"Ina tayaki murnar aurar da fu'ad da kika samu damar yi......wannan babbar dama ce da zata zame miki tarihi kuma abun tunawa watan watarana.......ina aka tanadarwa mahaifiyar fu'ad domin ta zauna ita da qannen matarsa?" Tayi tambayar kai tsaye cikin isa......

"Ai albarkacin kaza qadangare kansha ruwan kasko mariya....muhalli har sai kin baiwa wani" Anni ta fadi duk da rabin hankalinta yana kan yaran abubuwa masu yawa suna yawo a ranta. Waiwaya tayi ta yafito muhsina inna uwaisha dake shirin wucewa

"Itace mariya.......a cikata da irin karamcin nan da aka gada,koda zata cika hall dinnan da jama'arta.....a tabbatar an gamsar da buqatarsu,a nuna mata dattako da dattijantaka" Dukka anni tayi maganganun da kai da bakasan komai ba zaka dauka zallar magana ce kai tsaye,saidai gasu hajja da maamah din dukkaninsu sunsan magana ce akayi musu me harshen damo. Juyawa abinta anni tayi tana komawa cikin jama'arta,maamah tabi bayanta da kallo tana jin zafin jirwayen datayi musu me kama da wanka. Zafafan baqaqen maganganun data fahimci kowaccensu,amma kuma saiga murmushi yana subucewa daga saman fuskarta

"Kwanaki kadan suka ragewa izzarki ameenatu.....na rantse koda pant din dake jikinki da kudin muhammadu aka siyeshi saikin zareshi kin miqomin.......na rantse sai na sanya fu'ad ya gaya miki maganganun da zasuyi silar ajalinki......maganganun da zasu zame miki dafin da zuciyarki zata buga ta tarwatse pieces " Tayi dukka maganganun ita da zuciyarta tana me cike da alwashi.

Duk da wadannan abubuwan data samu ta kuma aiwatar zuciyarta ta kasa samun nutsuwa ko qanqani.......sam farincikinta har yanzu rabi ne......daga sanda ta iso bakin qofar mansion House din Alhaji hamza kibiya duka sai taji ta raina nata gidan kwata kwata. Batajin akwai wani gida ko gini da fu'ad zaiyi mata komai kyau da dukiyar da aka narkar ya zauna mata a rai muddin zai zamana muhallin Alhaji hamza kibiya yafi nata......indai zai zamana matsugunnin ameenatu zai d'ara nata.

Daina fahimtar komai tayi......daina fuskantar duk abinda ake gudanarwa tayi,dukka idanunta dama hankalinta suna kan 'yan uwanta,suna kan kowanne motsi da kai kawo nasu. Hankalinta taji yana tashi,bata qaunar kowacce mu'amala ko alaqa kome qanqantarta tsakanin maamah dasu,saidai yadda taga tana jansu a jiki,ta wani.mugun sake musu ko ita batajin ta sake musu haka. Haneefa duk girmanta tana saman cinyarta tana wani lallabata,irin lelen da haneefa din keso a matsayinta na auta take kuma qishirwarsa.

Cafko hannun amna tayi wadda ta zuge tata jakar ta fara fiddo sabbin 'yan dubu dubu kaman ba'asan ciwo da zafinsu ba.....kamar ba wasu abu masu muhimmanci ba tana zubewa sabreen din.

"Kiramin su nadra.....kice suzo yanzu yanzu injini". Dubanta amna tayi duk da bata iya ganin fuskarta sosai.

"Su waye?" Ta tambayeta don bata gane ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana qoqarin saita kanta,sai sannan ta tuna amna din bata sansu ba

"Sun shigo yanzu su da......." Ta dakata tanason tuna sunan da ake kiranta dashi

"Su da maamah" Kai amna ta daga tana hangensu daga nan inda take,kwata kwata bata qaunar abinda zai hadata da matar,bata qaunar kallon da take binta dashi irin kallon dake fita daga idanuwanta zuwa kanta,amma zuwa aiken sabreen ya zame mata dole

"Okay" Tace da ita

"Na gode" Sabreen ta fadi da sauri saboda jin dadin zatayi mata abinda takeso a sanda bata da damar tashi.

Da ido take bin amna sanda take nufarsu,duk wani taku dake qara kusancin ama dasu bugun zuciyarta qaruwa yakeyi,ta kasa dauke idonta daga kansu daidai da second guda har zuwa sanda ta qarasa gabansu. Taga amna ta mata magana,ita kuma ta waiwaya tayi magana dasu kafin ta sake dubanta still ta gaya mata wani abu daya sanya amna din juyowa ta dawo mata.

"Me suka ce?" Ta fara da tambayar amna din tun bata gaya mata komai ba

"Zasu zo.....zasu taho tare da maamah din wai". Idanunta ta maida ta lumshe tana girgizawa amna kai kawai. Wani irin rikitaccen yanayi yana sauko mata,kada dai ace suna jin wani sauyi na daban akan maamah kamar yadda takejin wajabcin bin umarninta tako ina yana ratsata?.

Tun daga wannan sa'ar nutsuwa tayi mata qaura,ta kasa debe idanunta daga kan 'yan uwan nata,duk wani motsi murmushi da kuma fara'ar fuskarsu ya tabbatar mata suna jinsu ne cikin sukuni da farinciki,har zuwa lokacin da aka bada sanarwar isowar mahaifiyar ango zuwa inda surukarta take.

Tamkar mejin tsoron wani abu haka zuciyarta taci gaba da bugawa sanda maamah ke kusantota tana takowa wajenta dasu nadra gaba daya. Idonta ta lumshe da sake budesu akansu gaba dayansu tana me kyautata zaton saisun iso gareta ne kai tsaye kafin aiwatar da komai......saidai kuma akasin haka ne ya faru. Kamar kowa suma wajen zuba kudin suka nufa,kowacce ta dire rafas na dubu dubu sabbi guda uku dake hannunsu huda kuma ta zuba biyar. Bin kudin tayi da kallo,suka kuma tsaye mata a rai.

"Wai ina momma bahijja?" Tambayar da bata da amsarta batasan kuma wanda zai gaya mata amsar ba. Ta tabbatar daga kansu har zuwa momma ba wanda zai basu wannan kudaden son suzo su zuba a wajen.....amsarta ta fito sanda maamah ta cire wani rafas din ta bawa nadra da zummar ta qara a ciki.

"To kuje ku gaisa" Maamah ta basu umarni sanda ta fara zube nata kudaden da suka ja hankalin mutane da dama.

"Waye ya kawoku?, yaushe kukazo?,ina momma?" Ta damqe hannun nadra da tafi kusa da ita tana jera musu tambayar a gaggauce daya bayan daya.

"Momma ta tafi yau....tun da safen mukazo,mun dawo gidan maamah......"

"Tana da kirki adda.....kuma tace kema kina nan,zamuci gaba da ganinki.....kayanmu ma tace basai mun taho dasu ba......kawu yace muyi zamanmu zamufi samun kulawa".

"Baki da hankali huda?" Ta fada da sauti me qarfi tana qoqarin janye lullubinta don ta samu damar saka idanunta cikin na huda.

"Yi a hankali......idanun jamaa suna kanki" Maamah data sunkuya saman kanta tana maida mata lullubinta ta fada da murmushi akan fuskarta kamar wani abun arziqi take gaya mata.

"Ku tafi mu zauna daughters" Ta fada da kulawa sosai a muryarta da cikakkiyar fara'a.

Tana jin takunsu sanda suke sauka a wajen,ba damuwa ko wani abu cikin muryoyinsu,tana jin tafiyar nasu na buga zuciyarta sosai,tanaso qwalla ta fita daga idanunta komai qanqantarta ko zataji sanyi,amma ko daya bata samu wannan damar ba.

Koda aka kirayi anni saita aike amna da wani qaramin akwati da ba wanda yasan meye a ciki aka ajiye cikin wani salo na siyan girma.


*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862

5 5 5
5 5 5 5 5
_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 62

g,D D

5K5<5B5@ 22


22


Kafin a tashi tsaf ta rasa sauran nutsuwarta,wani irin tashin hankali takeji maras misali daga kowanne lungu da sashe na zuciyarta. Ba abinda ke gilmawa ta idanu da zuciyarta sai huda nadra da haneefa......ina momma bahijja?.....ina momma bahijja?,.....da gaske ne sun bawa maamah yaran?,ya akayi haka ta kasance?,ya akayi ta tafi ba tare da sunyi sallama?,ya akayi ta tafi ta barsu bata cika mata alqawarin data dauka akan 'yan uwanta ba?......zata sakene ta kalli rayuwarsu ta balbalce?,ko xatayi dukkan abinda ya kama tayi don ta tseratar da rayuwar yaran?. Wadannan sune tambayoyin da ta dinga yiwa kanta har a sanda take cikin kebantaccen qaramin parlor din da amna ta kawota bayan tashi daga taron,tace ta zauna zasu gana da anni.

Dogayen yatsunta da suka sha lalle kawai take murzawa kanta a qasa,zuciyarta na wani irin zafi tare da jin qaguwar su koma gida ta lalubi maamah suyi magana ta sosai da ita.....koda tana jin kamar ta samu ikon sarrafa zuciyarta da bin umarninta cikin wani irin takura da takeji ana yiwa zuciyarta,.....to amma sam bata samu lago akan abinda takeji a zuciyarta game da 'yan uwanta. Qaunarsu darajarsu martabarsu da kuma soyayya da shaquwar data ginu tsakaninsu ba abinda ya sauya.

"Assalamu alaikum" Muryar anni ta ratsa falon tana murza qofar ta shigo

"Wa'alaikumussalam" Tada daga kanta kadan tana duban qofar gami da amsa sallamar. Kallon kallo suka yiwa junansu,kowanne a cikin su yanason tuna inda yasan fuskar dan uwansa. Sabreen ce tayi saurin watsar da qoqarin lalubo inda tasan fuskar annin,saboda gaba daya hankalinta ba'a nan yake ba,sai ta samu kanta kawai da zamewa daga saman kujerar tana gaidata,wata dabi'a data manta rabon data aikatata,amma a yau ta samu kanta da yin saboda wani kwarjini da taji matar tayi mata.

"Koma ki zauna abinki daughter" Ta fada da kulawa amma saita kasa hakan,saita samu kanta da zama sosai tana tanqwashe qafafunta.

"Na tsaidaki ko?,ga dare yana qara yi,duk da me babban sunan bai qaraso ba,uzuri ya taso masa daya saka dole ya fita" Kai ta sakeyin qasa dashi ba tare da tace mata komai ba,batasan me yasa matar take mata kwarjini haka sosai ba.

"Bari muyi magana a taqaice a gaggauce......da farko ina miki maraba da shigowa cikinmu da kikayi,ina fatan Allah yasa ku zama abokan arziqin junanku.....Allah ya hada hankalinku waje daya......bani bace mahaifiyar fuad,amma idan na kira kaina uwa a gareshi nasan banyi laifi ba,ni din uwar riqonsa ce tun daga quruciyarsa har kawo yau.....hajiya mariya wato maamah itace mahaifiyarsa". Dole bata shirya ba maganar ta sakata daga kai da hanzari ta dubi anni,sai kuma ta maida ta sunkuyar

"Baiyi sa'ar uwa ba.....ke kuma bakiyi sa'ar d'an riqo ba" Abinda ta fadi kenan qasan zuciyarta tana jin kamar a tsakaninsu annin ta fita daban. Anya ba halinsa Allah ya duba ba ya hadashi da uwa daidai da halinsa?. Zaren tunaninta ya katse sanda anni ke magana

"Yana da kirki.....yana karamci,yana da tausayi yana da tausasawa amma fa.......ga mutumin daya fahimceshi. Bashi da sauqi ya fiya tsauri,bashi da tausayi ga wanda bai fahimci shi waye ba,bayason qarya.....bayason saba alqawari,bayason yaudara baya son ha'inci......sannan uwa uba baya daukar raini. Abu na gaba muddin zakayi wasa da addini taku ba zata taba zuwa daya ba.....muddin ba zaka kasance karimi kamar yadda yake ba ba zasu taba daina sabani ba,wadannan sune kadan daga halayensa.......ameenatu" Ta kirata da sunanta na ainihi,abinda ya motsa zuciyar sabreen kenan sosai

"Ban gaya miki duka halayensa ba don na tursasaki kula da yarona.....na gaya miki ne don na sauqaqa miki qofofin zama dashi....na gaya miki ne don kiyi hanzarin mamaye zuciyarsa......na kuma gaya miki ne don na rage miki wahalar fuskantarsa......naso ace na samu zama da wasu mutane mafi kusanci dake don na tambayi naki halayyar na isar masa dasu a shimfide.....domin cikar mafarkina shine......gidan muhammadu yafi gidan dukkanin wani magidance zama aljannar DUNIYA......gidansa ya zame masa kaffara akan kowanne abu daya fuskanta a rayuwarsa a baya" Anni ta qarashe maganar har tsakiyar zuciyarta tana fatan mafarkinta ya tabbata. Miqa hannu tayi a nutse ta kamo hannun sabreen ta sanya cikin nata

"Idan har zaki bashi dukkanin kulawa......idan har xaki nuna masa zallar soyayya irin soyayyar da uwar kewa danta.....idan har zaki kasance me addini tsafta da kwalliya.....xaki kula da abincin muhammadu tabbas kin gama samunsa a tafin hannunki......yana cikin yunwar soyayya da kulawa.....muddin ya samu isashiya da zata qosar dashi babu ko haufi kin gama mallakar zuciyarsa dama rayuwarsa gaba daya".

Ta saurara ta kuma fahimci duka zantukan annin,saidai cikin nata zuciyar wani magana takeyi na daban

"Inama ace zaki fahimci waye danki sani na zahiri ba fuska biyunsa ba......inama wata daban kike budewa sirrikansa wadda ta shirya xama dashi ba SABREEN me zaman wucin gadi ba".

Dole ta sanyashi kashe duka wayoyinsa tun a hanya a sanda abdussabur yake tuqashi zuwa gidan anni.

A cikin jikinsa da zuciyarsa yakejin wata irin galabaita da bai taba jin irinta ba saboda zurfafa da tunanin da yayi. Yana da kyau yaci gaba da tafiya a gabar da yake na sanya idanu akan kowanne motsi da abinda dukka yake da alaqa da maamah. A zarginsa me girma da qarfi ya sake hawa kan yarinyar.......ya sake samun gamsuwa da cewa akwai shirin daya shigo da ita gidan,tunda har qarfin alaqarsu yakai girman da zata kebanceta da wata number wayar ta daban wadda shi kansa baisan da ita ba. Wunin yau gaba daya fiye da rabin tunaninsa yau duka ya tafi ne akan hakan.

Bazaice maamah maqiyayarsa ce ba.....hakanan bazaice bata sonshi ba,amma ta fifita kudi dukiya da abun duniya sama da tasu soyayyar.......kusan yayi mata fari kuma cikakken sanin da dan adam kan iya yiwa zanen tafin hannunsa koma fuskarsa......bazaiyi wasa da rayuwarsa ba.....hakanan bazai barwa maamah kowacce irin dama ba.....hakanan zai saka yarinyar a wasan da zata qara fahimtar batasan komai ba cikin duniya.....zai dafata da ruwa da kuma jinin jikinta.

Yayi sallama ya shiga parlor dinne a sanda anni ke miqa mata wata irin takarda me daukan idanu dake qunshe da littatafai na addu'o'i

"Akwai tsaftatattun addu'o'in mallakar miji a ciki,wadanda basu da wani aibu illa ko shirka a ciki,saidai suna matuqar tasiri wajen kama miki zuciyar mijinki a gareki" Ko alamun fa'ida bataji cikin bayanin anni ba......wannan mallkar da take fadi inda zata yiwu ta bawa maamah ita ta mallaki dan nata kamar yadda tace,ita kuma ta sakar mata 'yan uwa tabbas shine zatafi farinciki.

Yana zaune yana sauraren anni tana jaddada mata

"Ki raqe addu'a da kyau.....a yanzun kece garkuwan mijinki,garkuwar gidanki ma gaba daya" Baki ya tabe yana siririn tsaki qasan ransa. Inda anni tasan wacece ita tabbas da bata wahalar da kanta wajen mata wannan dogon jawabin ba,da tayi saving energy dinta kawai saboda gaba,a sanda zata fahimci wala'alla ko haruffan baqin dake cikin littafin ba zata iya hadawa ba ballantana ta karanta,don shi kam daidai da karatun sallarta bashi da tabbaci akai,don ya sani cewa Allah ya fada cikin qur'ani me girma

_haqiqa sallah tana hana alfasha da duk wani nau'in abunqi_. Ya tabbatar da nutsatsiya kuma cikkiyar sallah takeyi bata yadda za'ayi ta kasa rabuwa da dabi'ar karuwanci da bin maza.

Ko a motar kamar ba wanda yasan da zaman juna. Kusan nasa tunanin ma na tafiyar dake gabansa ne daga yanzu zuwa kowanne lokaci,yayin da nata tunanin ya.lula duniyar yadda zata fidda 'yan uwanta daga wannan wasan da bata shirya shigarsu ciki ba.

Sanda suka isa gidan sam bata wani jira guard sun bude mata qofa ba,gurds din da take mutuwar jin haushinsu tun daga sanda suka hanata rawar gaban hantsi a gidansu. A yanzu kuma a wannan gidan ta fahimci dasu ake kowanne motsi,wannan wacce irin masifa ce kamar raqibu da atidu da buwayin sarki ya saukar maka da suka zama lallai ka rayu dasu don su dauki dukkan ayyukanka,masu kyau ko akasin haka.

A gaggauce ta wuce duka falukan ta zarce hallway zuwa bedroom din,burinta kawai ta isa ga gallababbiyar wayar ta hadu da maamah.

Da zafin nama ta birkita inda ta aje wayar kafin su fita,saidai kuma sama ko qasa ba wayar ba dalilinta. Cak ta tsaya tana gwama numfashi,sai kawai ta bude jakar data dawo da ita ta fidda asalin wayarta da take kiran kowa da kowa da ita.

Asalin layin maamah din ta kira,wanda bugu biyu ta daga,saidai bata jiyo komai ba sai muryar haneefa daga gefe da alama hira take mata ita kuma tana fadin

"Allah auta?" Idanu ta runtse,ta lura da gaske ta shiryawa wasan...... Ta ruwan sanyi takeso ta cutar da rayukan da basuji ba basu gani ba.

"Me kikeso?,me kike buqata?" Ta tambayeta kai tsaye ba tare data damu ta amsa sallamar data mata ba. Wani shu'umin murmushi ta aje,sannan ta jita tana cewa

"Haneefa jeki kwanta kema,idan na gama zanzo na daukeki mu wuce daki tare"

"Tom" Ta amsa mata kamar yadda yawanci haka maganarta take,abun kuma daya sake sokar zuciyar sabreen kenan.

"Mallakamin d'ana nakeso kiyi.....ni kuma zan mallaka miki 'yan uwanki ta ruwan sanyi,dama naki ne". Tayi mata bayanin hankali kwance. Suya sosai taji zuciyarta tanayi,tanason fadin maganganu da dama......tanason tayi abubuwa da dama amma kaman an danne harshensa sai zallar bacin ran dake mata zullo

"Why ni?,me yasa saini ne?" Ta fusgi kalmar daga harshenta ta watsawa maamah ita.

"Saboda ni a wajenki kawai na hango irin zarrar da nake buqata......a aikinki na gano abinda zaisa aikina ya cimma gaci.....uwa uba kina da wani irin kyau da zai iya saurin rusunar da zuciya ya kuma narka zuciyar kowanne d'a namiji". Qit kawai ta kashe wayar tana jifa da ita gami da cusa dukka yatsunta goma cikin sumarta.



Please Login or Register in order to submit comment