Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan.......don Allah hadamin yaji naman rago cikin sosai" Ta fada kanta tsaye da sigar umarni.

"Tom" Madeena ta amsawa lailan wadda a qalla tayi qanwa ta hudu da ita,ta miqe ta kwanukan tana sauka.

"Idan da a rayuwa tsaiwa ake duba abinda ya kamata......inda a rayuwa jira ake sannan ayi abinda ya dace........tabbas ke kanki da baki juya matan yayunki kamar haka ba" Hajja tayi zancan tana tsare laila da ido tare da qoqarin maida mata girman zancan cikin zuciyarta.

Dan muskutawa laila tayi tadan kashingida,har yanzu a ranta ita batajin damuwar komai,duk da kuwa bayan kowacce daqiqa sai hoton kyakkyawar fuskar nan tasa ta gilma ta gaban idonta,abinda ke sakata sakin ajiyar zuciya lokaci lokaci gami da sakin qaramin murmushi.

"Inaso komai sauya.....inason ki canza akalarki daga yau.......dole gobe ki dawo ki karbi naki kayan aikin......ki kula da zuwaira......banason tasan komai.....bana son kuma ta fuskanci komai" Ta fada tana tsareta da ido. Saidai bata kai ga amsawa ba wayarta dake saman kanta ta dauki tsuwwa. Tana daga kwancen ta daga kanta tana duban me kiran,saidai ganin sunanta kadai ya sanyata wani irin zabura hadi da tashi zaune.

Hakan kuma baiyi mata ba sai data zamo daga saman gadon ta durqusa a qasa sanda take daga kiran hade da sallama. Dukka wadannan abubuwan da tayi su suka ja hankalin hajjan sosai taji tanaso taji da wanne mutum me matuqar girma da daraja haka a rayuwarta take waya?.

"Ina kwana maamah.....kin tashi lafiya?,kiyi haquri inata zuci zucin na kiraki na gaidaki da safen nan.....amma na kasa tuna waye zan kira". Maganar ta yiwa maamah banbarakwai,to amma bata wani kawo komai a ranta ba,duk da laila bata taba mata magana da ladabi rusunawa da kuma kirki irin haka ba

"Ba komai,kina gida ne zan baki wani aiki?". Rawa jikinta ya hauyi saita miqe tana daukan mayafinta

"Bana gida maamah.....amma bani minti goma sha biyar yanzu zan isa gidan,saiki gayamin abinda kikeso ayi miki ko mene". Mamaki kadan ya sake kamata,to amma a yanzu garkuwa kawai take nema don haka ta amsa mata da

"Okay......idan kika isa ki kirani"

"Ko kibar wayarma kawai on hold karki kashe yanzu yanzu zan isa,zanyi sauri ma saboda agama komai da wuri". Wani mamakin dai still ya kamata,amma sai tace

" Zan sake kiranki"

"To" Ta amsa mata tana sauke wayar. Jakarta ta kaiwa sura,kamar ma ta manta da hajja dake wajen,kowanne sashe na jikinta rawa yakeyi,ta jefa wayar a jaka ta rataya tana yafa mayafinta. Sai a sannan hajja da mamaki ya kasheta ta kira sunanta da qarfi

"Waike da waye kike waya haka lokaci guda hankalinki ya tashi?". Murmushi ta sakarwa hajjan sanda take saka takalminta

"Maamah ce fa?,ta tambayeni ne ina gida?,wani aiki zata sakani kinga ya kamata na koma ai.....bai kamata ma ace na fita ban tambayeta ba,amma zan bata haquri daga baya.....hajja na tafi,idan na gama mata da wuri zan tambayeta,idan ta barni gobe na dawo zan dawo".

Mamaki da ganin almarar abun ya hanata cewa komai,ta sanqame a wajen kawai baki bude tana bin laila da kallo wadda keta sambada sauri kamar zataci da baka.

*_turqashi?,wai meke faruwa?,nace meke faruwa ne jama'a?,shin qaiqayi ne koma kan masheqiya ko kuwa yaya?,wanda lamarin nan ya yiwa dadi ya danna 1=,wanda baiji dadi ba ya danna 2_*

*_gasu huda a hanyar zuwa gidan addansu,yaya zata kasance kenan?_*

*_yanzu wasan zai fara tafiya daidai=ت<_*

*_muje zuwa=L<_*

45


_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_



Ware idanunta tayi sanda ta isa dining area,sai ta tsaya cak tana sake ware idanunta da kyau tamkar wadda bata gani sosai,kwanyarta na gayawa zuciyarta kawai yaudarar kanta takeyi,basu huda dinta bane.....ba nadra a wajen......auta haneefa tana hannun waccar azzalumar

"Adda.." Muryoyinsu suka zame mata kamar tsani a gareta na tashi daga wani dogon mafarki,kamar wadda aka daki bayanta,sai ta fara nufarsu tanason ta tabasu don ta tabbatar shin su dinne?.

Allah ne kadai ya sauko da ita daga steps din,don qafafunta hardewa kawai sukeyi har zuwa sanda ta isa garesu. Haneefa da tafi kusa da ita ta jawo,ta miqa hannu tana shafar fuskarta,sai kuma taja hannun huda ta riqe d kyau,sannan ta dafa kafadar nadra.

Murmushi suka fara yi mata,da alama sun gane abinda take nufi,kuma dariya sukeso suyi mata,saidai yanzun ba Lokacin dariya bane.

"Ku tsaya a nan ina zuwa" Shine abinda ta fada kenan tana juyawa ciki cikin gudu gudu sauri sauri. Ko ina a jikinta rawa yakeyi,batasan ya akayi suka kubuto ba,tana ji a jikinta addu'ar data tsananta a wannan Lokacin Allah ya karba mata.

Birkice closet dinta tayi wajen neman hijab daya tamkar idanunta basa gani,da qyar idanunta suka nuna mata wani ruwan sararin samaniya,ta sanya hannu ta fuzgoshi ta saka,sannan ta dawo falon.

"Ku taso......ku taso mj tafi" Ta fada da wani irin hanzarin daya sanyasu tsaiwa kawai suka zuba mata idanu,har sai data fusgi hannun nadra da haneefa sannan huda ta biyo bayanta a mamakance.

Tana riqe da hannuwansun take ratsa farfajiyar gidan,girmanta yasa take ganin kamar ba zasu fita daga ciki ba maamah zata riskesu,kamar tayi nisa da yawa. Security da sauran ma'aikata nata zubewa suna gaidata,amma ita ba wannan bane a gabanta,don ko gane gaisuwar nata basa yi.

Kai tsaye kuma a karon farko security suka bude mata gate ta fice. Taci gaba da jan hannunsu da wani irin sauri da kaf rayuwarta bata tana yin tafiya da irinsa ba

"Ina zamuje adda?,ko zama baki barmu munyi ba?" Haneefa ta tambaya adan shagwabe saboda saurin da suke zubawa din ya fara isarta

"Zaki gani auta......karki damu" Ta ambata tana duban hanya,daidai sanda ta hangi tahowar motar da tafi mata kama da motar da akan kawo maamah a ciki.

Hagu da damanta ta duba,ba wani gurin labewa. Unguwa ce da dukka gine ginenta ke bisa tsari,layukansu shimfide da wadatacciyar kwalta,manyan gidaje da kowanne gate yake a kulle dame gadi ko kuma kare.

Cikin ikon Allah ta hangi gida daya da qaramar qofar dame gadi kan fito a bude,saita jasu zuwa can ta kuma turasu ciki itama tana me shigewa.

A gabanta motar tazo ta wuce da gudu,saita sake kamo hannun haneefa tana cewa

"Kuzo mu tafi" Zuciyarta na tsananta bugu qwarai.

Sai da sukayi tafiya me nisa kafin su samu adaidaita sahu,kasancewar unguwar unguwace ta masu kwalli masu hannu da shuni,zai wahala kaga abun hawa na haya a cikinta. Koda zai shigo ma sai ainihin security da suke gadin unguwar sunyi checking sun tabbatar da amincinsa da ingancinsa. Basa wasa ta wannan fannin saboda dukka unguwar manyan mutane ne a cikinta.

Sai data tabbatar me abun hawan yayi nisa da unguwar sannan ta sauke ajiyar zuciya,ta juya a hankali tana kallonsu sai taga dukkaninsu ita suka zubawa ido,da alama qarin bayani suke nema. Murmushi kawai ta saki,ta dora hannunta saman kansu ta shafa tana cewa

"Zakuji komai......bari mu isa".

Kamar yadda zama ya gagareta haka tsaiwar ma sai taji kamar tana neman gagararta. Wani tashin hankali takeji mara misaltuwa,yaran su kadai ne hope dinta,idan har tayi loosing yaran tabbas bata da wani sauran hope.

Yadda take juya yarinyar tayi imanin bawai girman asiri bane.....don dama ya bata tabbacin abun bame qarfi bane,idanma me yawan addu'a ce kwana uku zai saketa. In kuma me qarfin kurwa ce da tsananin hasken taurari sati biyu zuwa wata daya zai iya sakinta.

A yadda take maida mata magana da tsananin izza da rashin tsoro,ta tabbatar komai ya saketa,kawai tana biyeta ne saboda yaran da suke hannunta.......idan babu su ya zata kaya mata kenan?.

Wani tashin hankalin ya sake rufto mata data tuna da waya fa a Hannun huda. Ita ta siya mata ita sati guda daya wuce kenan data sake jawota jikinta. Yau idan sukayi amfani da wayar suka kira wani fa?. Abinda ya sakata rarumar tata wayar don sake kiran zuwaira ta karbo mata wayar ko da qarfi ne,tana me manta ma wayar zuwaira din a kashe take.

Cikin sa'a bugu biyu ta dauka,muryarta na nuna alamun bacci. Ashar ta lailayo mata wanda ya sanya zuwaira miqe ta zauna da duwawunta

"Dama bacci na aikeki kiyi?Kinsan aikinki kuwa?,kinsan muhimmancin abinda na aikeki kiyi zuwaira?!" Maamah ta tambaya a tsawace tana jin kamar ta jawo zuwaira daga cikin wayar ta zabga mata mari. Rawa jikin zuwaira ya dauka,batason tayi asarar maamah tun yanzu alhalin bata samu tudun dafawa ba.

"Kiyimin aikin gafara hajiya......tuba nake"

"Ki rufemin baki,ki tashi ki dubamin cikin gidanku,daga parlor din matar gidan har bedroom dinta,akwai qannenta da sukazo,ki fara karbamin wayar hannun babbar,minti goma kuma nace ki qara musu su taso ki biyosu har sai kin kawominsu gidannan".

"Angama ranki ya dade" Ta fada tana miqewa da hanzari har dankwalinta yana faduwa,duk da ranta a bace yake ainun da irin tsawar data daka matan.

Parlor ta duba na farko dana biyu duka ba kowa. A kitchen ta samu ma'u tana juye mata kunun a flask gudun kada yayi sanyi jin shuru bata dawo ba.

Ido suka hada mau ta dauke dubanta a wajen. Haka kawai jininsu baizo daya da zuwairan ba,duk da ma'u bata nuna mata komai,saidai ita zuwairan cike take da haushin ma'un ganin yadda sabreen din ke mu'amalantarta sama da yadda take sakar mata.

Ko ina na gidan ta duba,tana shirin fita farfajiyar gidan ta duba can sai ga laila ta shigo afujajan

"Ina matar gidan?" Lailan ta tambayi xuwaira.

"Ban sani ba nima" Ta bata amsa cikin jin haushi zuciyarta tana raya mata itama aikin dubata ta bata.

Dole data gama dube dubenta ta dawo parlor din,daidai sanda ma'u ta kammala komai tazo ta rabesu tana ficewa abinta ba tare da tace da kowa komai ba.

Dukkansu qoqarin kiran maamah suke don k 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~owa ya fara shaida mata yadda ake ciki. Laila ce ta fara samunta,cikin tsananin biyayyar data sanya zuwaira sakin baki tare da tunanin ko wani sabon makircin shiga jikinta suka qullo ta tsaya tana dubanta

"Maamah kaman bata gidan nan fa?". Wata zazzafar zufa ce ta karyo mata,taji kamar gudawa zata tsinke mata. To amma yaushe suka shigo da har za'ace basa cikin gidan?.

"Kun duba ko ina da ina?" Kai laila ta girgiza tana duban hallway din

"Banda bedrooms dinta"

"Me kuke jira?,ku dubamin har can" Ta bata umarni a tsawace har sai da wayar hannun lailan ta kusa faduwa.

"Zan shiga na duba" Lailan ta fada tana duban zuwaira. Wani kallo ta watsa mata tana samun daya daga cikin kujerun ta zauna tana tabe baki.

Da karsashinta ta soma nufar dakunan,har cikin ranta tana jin dokin shiga taga dakunan ya suke?,tunda koda hallway din bata taba takawa ba bare akai ga shiga ciki.


"Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa lokacin dame napep ya ajiyesu a qofar gidan. Sai a sannan hankalinta ya dawo jikinta,ta tuna bata riqo komai a hannunta ba.

"Don Allah dan yi haquri,bari a karbo maka kudinka,fitar ce ba'a tsanake ba" Ta fada tana dubansa. Bai wani damu ba sam,saboda yanayinta kadai ya tabbatar masa idan bai samu qarin abinda ya kamata a bashi ba to tabbas ba za'a rageshi da komai ba. Waiwayawa tayi ta kalli su huda

"Ku shiga ciki ku karbomin dubu biyar wajen titi". Huda ce tayi gaba suka bita a baya. Basu jima ba nadra ta fito da kudin ta miqawa sabreen din,ta karba ta bashi sannan suka wuce cikin gidan a tare.

Tana sallama aishatu ta fara gani,tana duqe tana wankin uniform dinta daga can bakin famfon da akayi musu saboda hidima irin wannan. Tadan zubawa yarinyar idanu farinciki yana ratsata. Ko a iya aishatu kawai idan ta kalla tana jin wani farinciki da sassauci yana ratsata,kamar ba aishatun da aka debe tsammani da rayuwa da ita ba,kamar ba aishatun da idan ka fita ba zakayi tsammanin zaka dawo ka sameta a raye ba. Sai data dago don yin shanya suka hada idanu,ta watsar da uniform din,ta rugo da gudu tana kiran sunanta

"Adda sabreeennn" Ta maqaleta da kyau,sai itama ta tsugunna tana rungumeta cikin jikinta qwallar farinciki na sauka a idanunta.

"Aishatu......haka kika koma?......alhamdulillah" Ta fada tana shafa sumarta me santsi.

"Adda na warke.......na samu sauqi adda" Ta fada itama tana kwantar da kanta a kafadarta.

"Ki barta ta qaraso ciki mana aishatu" Muryar titi ta ratso kunnuwansu tana dubansu cikin murmushi,daga nesa kuma tana kallon yadda sabreen din tayi wani irin kyau,fatarta ta qara tsananin haske da wani irin murjewa,sai glowing takeyi duk da tadan fada kadan qibarta ta ragu.

Tana riqe da hannun aishatun suka shiga parlor din titi. Duka sauran yaran falon suka miqe don basu fahimci ita ake magana ba.

Dukkaninsu suka baibayeta suna qoqarin kiran sunanta,sai ta zame kawai ta zauna tana rungumesu cikin jikinta gaba daya tana kiran sunansu daya bayan daya.

Ruwa da lemon zobo da titi din ke saidawa ta dire musu tana zama gefanta. Sai a sannan yaran duka suka tashi suna ficewa don basu sarari.

"Banyi zaton sake ganinki nan kusa ba" Titi ta fada bayan sun gama gaisawa da gaske farinciki yana nunawa saman fuskarta,duba da sanin babban mutumin data aura. Murmushi sabreen din tayi wanda yakai mata har zuci,musamman data tuna daga rana irin ta yau ta nesanta maamah din da rayuwar qannenta kenan,nesantawa ta har abada

"Me zai hana titi?,ban fara fita bane kawai" Ta amsata tana gyara zamanta

"To ma sha Allah,ubangiji ya sanya alkhairi,ya bada zaman lafiya ya kade fitina". Bata amsa duka wadannan addu'o'i na titi din ba,sai tace da ita

"Alfarma nazo nema titi don girman Allah" Kallonta titi takeyi wani yanayi yana bin fuskarta

"Haba sabreen.....haba don Allah,aike din kifi qarfin alfarma......saidai bada umarni kawai" Murmushi ta saki tana girgiza kai,har yanzu suna mata wani madaukakin kallo.

"Su huda na kawo miki,inaso kuma ki riqemin su zuwa wani lokaci,don Allah titi ko nan da qofar gida bana so su leqa idan zai yiwu bare sukai ga fita waje.......akwai gagarumar matsala da take tunkararmu gaba daya,akwai masu bibiyar rayuwarsu,ki kulamin dasu don Allah". Sosai maganar ta shigi titi,saita girgiza kai tana fadin

"Aiko su din ba jininki bane sabreena sai inda qarfina ya qare......ba abinda bakiyi mana ba,banda ke da Allah ya jefo mana da yanzu bansan a wanne bigire rayuwarmu take kai ba......zan kula miki dasu fiye da yadda kike muradi"

"Na gode titi......kina da tsohuwar waya da bakya amfani da ita?"

"Banga abun godiya a nan ba,hasalima kamar wajibi na na aikata.....akwai wayata da kika canzamin sanda zamuyi tafiyar nan......bari na dauko miki ita"

"Idan zan samu da wata wayar daban zanyi kira" Ta fadi tana qoqarin hada numbers din momma a kanta.

Banda tana da kaifin basira da saurin riqe abu ba yadda zata iya hada number wayar momma din,saidai cikin ikon Allah ta hadasu tsaf ta kuma kira zuciyarta na bugawa da fatan ta kira daidai.

Bugu uku aka daga,muryar momma ta mamaye speaker din tana amsawa da sautin da yake kama sak dana ummensu,sautin da har tata mutuwar ta risketa ba zata manta dashi ba.

"Mom......momma" Sabreen din ta kirata bakinta yana rawa idanunta suna cika fal da hawaye.

"Sabreena?.......kun dawo?,yaushe kika dawo?"

"Daga ina?" Ta tambayi momma din a mamakance qwallar idonta suna tsagaitawa.

"Tafiyar da kukayi mana ke da me gidan.......ko sanda zan koma ai naso haduwa dake dole sai hannun surukarki nabar qannenki.......saboda dole sai passport dinsu ya zama ready.....duk dama dai munyi magana tana ta iya bakin qoqarin ta,kuma kusan kullum sai munyi waya da yaran". Mamaki ya sandarar da sabreen,sai ta bude bakinta a hankali

"Momma me ya faru?,ban fahimta ba,ita ta nema ki bata su?"

46


"Eh kusan hakanne,don naso ganinki ban samu ganin naki ba......tafiyar tawa bata shiri bace......abbansu ne rashin lafiya ta taso masa,dole kuma ana buqatata a kusa,a yadda na tsara zan jira passport din nasu da komai ya kammala,amna dole na tafi saboda jinyarsa,saidai ba inda zan barsu don ban aminta da hannun kowa ba. Randa nake wannan tunanin saiga surukarki Allah ya jeho ta. Ita ta roqeni na bata yaran zata sanya mai gidanki yayi magana don a kammala basu komai da wuri,tace kuma zata turosu ko ta kawominsu da kanta,to amma lokacin da nayi tsammani ma sai gashi har ya gota. Kawai abinda yake kwantarmin da hankali duk sanda mukayi waya da yaran alamu suna nunamin basu da matsala ko damuwar komai". Kai kawai sabreen ke jinjinawa tana sake girmama kaidin maamah din. Ta tabbatar ita zata kawo tsaiko a samun fasfunansu,wataqila ma kuwa an samu ta riqe ne taqi gayawa momma din. Tanason ta yiwa momma bayanin da zata fahimceta,amma kuma bataso ta daga mata hankali. Tana ji a jikinta zata iya komai,kuma wannan lokacin kamar wata dama ce da Allah ya ara mata akan maamah din

"Momma"

"Na'am sabreen"

"Komai da kike kallonsa a haka yanzu a zahiri ba'a haka yake ba........abinda zance rayuwarsu tana cikin hadari babba........basa hannunta yanzun suna wani hannun na daban,saidai bana son ki gayawa kowa,don Allah mommma......koda ta kiraki kiyi kaman bakisan abinda yake faruwa ba.......in sha Allah nan da kwanaki kadan zan turosu su biyoki". Shuru momma din tayi tanaji a jikinta ba lafiya

"Amma sabreen me yake faruwa?".

"Ba wani mummunan abu bane momma,kada ki tashi hankalinki.....kawai dai komai kiyishi kamar bakisan anayi ba" Kai ta jinjina bawai don hankalinta ya kwanta ba sukayi sallama.

Tana ajiye wayar ta sabule zobunan hannunta guda biyu na gold,ta kama hannun titi ta zubasu tana kallon idanunta.

"Yanzu bani da contact na kowa.....inaso ki saida wannan,ki nema mutumin da ya muku visa na fita india ya yiwa su huda duka su ukun komai,inaso kada su wuce sati biyu a nan don Allah titi". Zobunan ta kalla sannan ta maida dubanta ga sabreen

"In sha Allah.....zanyi duk yadda zanyi na miki abinda kikeso". Kai ta jinjina tana jin wata nutsuwa tana saukar mata. Murya ta daga ta kira huda,ta shigo ita daya,abinda ya sanya titi miqewa don basu guri.

"Ina wayar hannunki?" Ba musu ta dauki wayar daga kan cinyarta ta miqawa sabreen din. Saita karbeta tana juyata a hannunta. Waya ce me asalin tsada da kyau wanda kusan sai wane da wane. Idanunta ta maida fuskarta tana kallonta

"Huda baki dago komai ba?,bakiji komai ba game da matar da aka kira da sunan uwar mijina?" Tayi mata tambayar kai tsaye tanason samun wani abu daya danganci maamah. Shuru hudan tayi,tana qoqarin recalling komai,tun daga ranar farkonsu cikin gidan kawo yau.

Siririyar ajiyar zuciya ta sauke,a hankali ta maida dubanta ga sabreen

"Inajin kawai batamin ba.....duk kirkin da take gwadana mana sai nakeji jini na da nata kaman bai hadu ba.......sannan yadda take mana kirki kaman ba haka dabi'arta take ga masu aiki qarqashinta ba" Hudan ta fadi abinda da gaske haka takeji a zuciyarta take kuma hasashe.

Wani siririn murmushi sabreen ta saki tana saukar da kanta qasa gami da juya wayar hannunta. Anzo daidai gabar da tafiso.....anzo daidai wajen da zata gwadawa maamah shege......anzo daidai gurin da zatayi wasa da hankali da kuma tunaninta kamar yadda mage kanyi da qadangare ko bera a duk sa'ilin da yayi gigi ko kakambar shiga hannunta.

Daukewa murmushin fuskarta yayi lokaci guda,ta maida kallonta kan hudan

"Ina fata ba wani abu na cutarwa data taba muku......idan kuma akwaishi ko da da mugun kallo ne ina saurarenki". Kai ta girgiza tana kallon addar tata,tanason kuma fahimtar dalilin da yasa taketa mata tambayoyi haka

"Babu kwata kwata adda......saidai kawai nidai hankalina ya kasa nutsuwa da ita... Musamman da ya zamana kusan ko yaushe tana mana alqwarin zata kawomu wajenki sai kuma ta gaza cikawa.....har sai da mijinki yazo.....shi yace ta barmu muje". Jinjina kai take tana duban huda dake bayani,fuad ne kenan.......me yasa yace suzo din?,shima akwai yiwuwar yana da nashi boyayyen manufar?.

"Kinsan garkuwa tayi daku?,kidnapping a fakaice?" Tambayar ta zowa huda a bazata,ta zaro idanunta waje tana dafe hannunta saman qirjinta.

"Kidnapping fa adda?" Kai ya gyada mata gami da lumshe idanunta,sai kuma tace

"You are free in sha Allah.....zaku bi momma mali soon......abu daya nakeson na gaya miki ko bayan kun tafi......be smart as much as you can.......ki dinga amfani da kwanyarki da basirarki.....ki kula da nadra da Haneefa,ki zame musu garkuwa kamar yadda na zame muku.....sannan......ki zama mara saurin yarda da mutune,walau maza ko mata,a family yake ko a wajen family......saurin yarda tushen kowacce rushewa ce" Ta qarasa maganar tana nunata da yatsa.

Iska ta zuqa sosai sanda take cikin napep din sannan ta furzar da ita waje,tana jinta kamar mutumin daya dauki dutsen dala da gauron dutse yau Allah ya 'yan tashi ya samu saukeshi daga saman kansa. Sakayau take jinta,wani farinciki yana ratsata gami da iskar abun hawa wadda ta manta rabon data ratsata. Ta ware idanu sosai tana kallon titi.....Don yaushe rabonta data fito?,ko fitarta ta qarshe cikin rufaffar mota ne qarqashin kulawar jami'an tsaro.

"Sabreena Ahmad AKA MUHSEENA" Sunan da taji an ambata kenan saitin kunnenta. Ko daga bacci ta tashi tasan waye?......wannan wata shaidace kuma stamp ne daya kasance nasa shi kadai. Mashkur....ta gayawa kanta da kanta,don haka ta tattara dukka nutsuwarta da qarfin halinta ta maida sashen da sautin ya fito.

Shi dinne,zaune a seat din driver,ya dafe dukka hannuwansa saman steering din motar yana jifanta da wani zazzafan kallo. Duk da yadda haushinta da wutar son daukar fansa ke ruruwa a ruhinsa.......amma hakan bai hana shaidan harbawa zuciyarsa wutar matsananciyar sha'awarta ba. A yadda yake hangen wani lafiyayyen kyau a tattare da skin dinta......wani irin kyau da abaya fatarta bata sameshi ba,sai yakejin burinsa ya ninku zuwa gida biyu,YA DAUKI FANSA sannan kuma YA KASHE QISHIRWAR SHA'AWARTA A RANSA. Dadaddiyar qishirwar data maidashi sakarai kuma shashasha a kanta duk da tarin tsananin wayonsa.

"Damn it!" Ya furta da qarfi yana dukan steering din motar tasa gami da cije lips dinsa gami da kashe mata idanu guda daya. Salin alin ta dauke dubanta daga kansa,tana jin wani matsanancin faduwar gaba yana saukar mata. Faduwar gaban da bata taba ji ba a kansa ko akan wani d'a namiji

Please Login or Register in order to submit comment