Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗauke ta ma ya ƙi sai juyi take tana tunanin rayuwarta, ita bata zama mai sa'a ba sam babu mai mata ƙaunar tsakani da Allah bayan mahaifiyarta sai Maami haka zata cigaba da rayuwa?
Shin ya zata je ta tarar da ummi? Wani irin tarba zata samu daga mutanen gidan barin ma Alhj Hassan dala? Wani irin ma tunani zata yi akan Mukhtar da zama dashi bayan ta riga ta sakawa ranta ba zata iya cigaba da zama dashi ba?

Washegari haka ta yini duk jikin babu daaɗi da misalin karfe huɗu ta shirya tsab cikin atampharta da aka mata ɗinkin riga da skirt Dukda ramarta sai dae tayi haske yanzu ta ɗan yi kyau sbd karan hancinta da ya kara fitowa idanunta suka kara girma, she's so pale bata da wani walwala, daga ɗakinta ta fito sai ta tsaya chak tana shakar daddaɗar turaren da kamshin shi ya danne duk wani kamshi na Maami da baya rabo da babban parlorn saman, bata taɓa jin turaren ba, ko dae Mukhtar ne ya sauya turare? Da wannan tunanin ta tura ɗakin Maami ta shiga Maamin ce kawai zaune tana duba wani littafi da ya fi kama da na addini.

Kamshin ya fi yawa a ɗakin hakan yasa tayi tunanin dae wani sabon turare ne Maami ta buɗe mai daaɗi, a gabanta ta zauna tana mata sannu da gida, cikin kulawa ta amsa tana tambayarta babu abin da yake damunta? Ta girgiza kai kan tace
"Maami zan je dubo ummin"
Maami tace
"Toh Binty ki gaisheta kin ji? Sannan ga wannan dama tun jiya na tanada ki kai mata in akwai wani matsala kiyi gaggawar ƙirana kin ji?"
Kai ta gyaɗa tana karɓar jakar tare da godiya da Adu'a ga Maamin kan ta miƙe, har ta isa kofa Maami ta kirata ta dawo.
Kiran me aikinta tayi dattijuwar mata Maama Laami tace su tafi tare da Habu driver, babu gardama suka fice a tare.

Banda faɗuwar gaba babu abin da take ji har dafe kirji take akai akai har suka isa gate ɗin gidan, Habu yayi horn shazali ya buɗe mai gate din ya kutsa kanshi ciki yayi parking, idanunta ne suka sauƙa akan Alhj Hassan dake zaune riƙe da jarida a rumfar shaƙatawarshi wanda hakan yasa gabanta sake bugawa da karfi, Habu ne ya buɗe mata kofa sai ta kasa sauƙa ganin Hajj Zeenat sun fito a tare da Jameelah kaman wani wuri jameelar zata ita kuma Hajiya wurin alhaji ta nufa bayanta me aikin da bata sani bane rike da tiren kayan marmari.

Rashin fitan ta ya dawo da hankalin Alhj Hassan kan motar, har jikinta na rasa ta sanya kafa ta sauƙa daga cikin motar dukkaninsu Dakatawa suka yi suka zuba mata idanu, baba Musa ne cikin mamaki da wani ɗan farin cikin da ya bijiro mishi yace
"Alayah kece?"
Wannan suna da ya kira yasa dukkanin fara'ar fuskokin iyalan gidan ya kau, Miƙewa Alhj Hassan yayi ya nufo ta yace
"Ke! Uban me ya kawo ki gidana? Me na faɗa miki randa aka ɗaura miki aure?"

Kanta ƙasa ta ɗan duƙa tace
"Ina yini Abba..."
"Zan zazzage ki, zan kwalfe ki anan kika sake juya tambayata zuwa wani abu, nace uban me kika shigo yi min cikin gida?"
Hajj Zeenat tace
"zata nuna maka itama ta soma gwamutsuwa da masu maiƙo ba, wuyanta har yayi kauri..."
Jamila dake gefe tayi wani dariya tace
"abin da ya bani mamaki ma har wani buɗe mata kofa ake, ita gata surukar wani da dae ba'a san asalin balbela bane da sai ta ce daga Masar take, ko kuma da bamu san wani thug kike aure ba da shine za'a mana wannan feleke"

Duk maganganun su bai dameta ba damuwanta ɗaya ta samu ta ga umminta ita ko gilamawanta ta gani ma Alhamdulillah ta san lafiyanta ƙalau,
"Nace me ya kawoki gidana???" Ya daka mata tsawar da ya firgita ta cikin rawan murya tace

"U..mm..i u..mmi..na na zo ga...ni"
"da gaske kenan wuyanki kauri yayi da zan kafa miki doka ki take? Fitar min daga gida tun kan ban yi miki abinda kare ma baze ci ba in ya gani"

"Don Al...."
"I Said get out...!!"
Ya daka mata tsawa yana yiyowa kanta, da sauri Maama lami ta riƙe ta tace
"Hajiya mu tafi"
Girgiza kai tayi tana me sakin kukan da take riƙewa
"Maama mahaifiyata ce fa... A nan ciki... Ba..n sa..n ha..halin da take c..ciki ba, ba za.."

Marin da Alhj Hassan din ya kawo mata ne ya sameta tayi baya saura kaɗan ta faɗi baba Musa da yake kusa ya tare ta chan ƙasa yace
"idan akwai wadda zaki iya tara ya taimaka miki karki je ki zuba ido mu karan kan mu bamu da tabbacin lafiyar mahaifiyarki"
Ɗagota yayi, hajj Zeenat tace

"ka ganka Musa!! Kai shashashan ina ne da Alhj na hukunci zaka shiga? Da ka tare ta uban me ya haɗa ku da zaka bata kariya? Ashe ma goyon baya zaka bata tayiwa uban gidanka rashin kunya? Shiyasa na tsane ku ku din nan ma'aikatan tsakar gidan nan, akwai wani abu daban cikin ranku to ya ƙare a kanku"

Habu da ya buɗe mota ne yayiwa Maami Laami magana tayi saurin saka Alaya da har lokacin kuka take tana tirjewa bata son tafiya cikin motar, yayi saurin shiga suka bar gidan hajjiya Zeenat na cigaba da surfa bala'in ta son rai.

A jikin Maami ta zube tana kuka sossai
"Maami kila sun kashemin ummi, Maami sun hanani ganinta, Maami ya zan yi? Ina zan sa raina idan wani abu ne ya samu ummi? Bani da kowa ban san kowa nawa ba ta ina zan fara ni Fatima?"
Har shaking Muryar keyi saboda kuka.

"Binty kiyi shiru in shaa Allahu ina tare dake, ina nan tare dake kuma ba zan taɓa bari su ida mugun nufin su ba, a jikina ina jin ummin ki babu abin da ya sameta, ki natsu kin ji? Kin ga ba ke kaɗai ba ce, ki bani hankalinki in shaa Allahu yanzu zan soma ɗaukar mataki"
Ita dae ta san Alhj Hassan fuskantarshi ba abu bane mai sauƙi tunda Ummi nunawa take Abbanta ma ya gaza, sannan abokin Alhj hammad ne baban su Mukhtar baze iya bari Maami tayi wani abu ba, idan kuma bata yi ba shikenan ta rasa ummi kenan ko yaya?

Ire-iren tunanin da ta zurfafa kenan ta daena kukan sai ajiyar zuciya, Maama lami ke faɗawa Maami duk yadda aka yi tana jinjina rashin darajar mutanen gidan, da lallamin Maami ta ɗan ci wani abu sai dawo mata maganganun baba Musa yake, yana faɗa mata ne akwai damuwa, har ta kwanta bayan isha sai saƙe-saƙe take bata da yadda zata yi, babu gata cikakke babu galihu, wanda hakan ya sakata kuka mai yawan gaske daga karshe ya haddasa mata zazzafar ciwon kai me tafe da zazzabi, da kyar ta ga safiya ko da Maami bata ganta ba bayan sallah saboda tana idar da sallah take zuwa gaisheta hakan yasa ta shigo ɗakin don dubata yanayin da ta sameta ne yasa kawai suka yi asibiti, gabaɗaya tausayin rayuwar Alayar ne ke rufe da Maami har kusan bayan awanni biyu ma kan Dr Philips din ya fito yake mata bayanin stage din da take na da hatsari tana bukatar kwanciyar hankali da natsuwa, hakan ne kawai zai sa da taimakon magani sai ta samu sauƙi tunda ba'a jima da mata aiki ba kuma it was successful.
Duk Maami ta ji kuma ta san hallayyar Muktar gareta ne yayi triggaring ciwon da ya kamata ace ya lafa sossai da sossai, sai kuma wannan Alhassan ɗin da babu mugun abu nashi da bata sani ba, bashi da imani ko na miskala zarratin, godiya ta mishi kan ta ƙarasa ɗakin da aka kai Alaya din baba ne ya kirata don jin jikin Alayar sai ma yaji suna asibiti hakan yasa yayiwa Daada magana ta sa driver ya kai musu abin kari.

Riƙe da hannunta Maami ta zuba mata idanu, wani irin tausayinta na sake ninkuwa a ranta, hawaye ta tsinci kanta da yi tana saka kanta a sahun Alayar, kiran da ya shigo wayanta ne yasa ta share hawayen kan ta miƙe ta fita tana danna recieve...

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment


                     🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Fifteen*

*Alhamdulillah Abdul ya samu sauƙi na gode da Adu'o'in ku*

Wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunshi dake runtse tuntuni, club ɗin ya zubawa idanu a hankali yake bin mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya da kallo kaman yau ɗin ne rana na farko da ya soma shigowa a rayuwarshi, daga masu tiƙan rawa rungume da Ƴan mata, zuwa kan masu kiɗan da suke buga beat suna ihu, zuwa kan waenda suke rage zafi da Ƴan matan da ba muharramansu ba babu wani kayan arziki zuwa masu busa hayaƙi da shan barasa, duk yadda yake tunanin anan yake samun natsuwa sai yaji gabadaya natsuwar ma ta ƙi zuwa, tsanar wurin ma yake ji a ranshi hatta da mutanen cikinta, idanunshi ya ɗaga sama yana shafa dadar kanshi tambayar kanshi yayi a lokaci ɗaya menene jin daaɗin wannan rayuwa? Mecece ribarta?
Sake lumshe idanun yayi sai fuskan Maami ya faɗo mishi tana zub da hawaye tana mishi karyayyen kallo mai cike da tausayi, jimami da damuwa, da sauri ya buɗe yana kallon Rita dake tsaye a kanshi a maimakon ya ga fuskanta sai fuskar Alaya ce take faɗo mishi, magana take mishi amma sautin sassanyar Muryar yarinyar yake ji yana shiga kunnuwanshi, da karfi Abokin shi Pepe ya jijjigashi yana ƙiran sunanshi wadda hakan ya dawo dashi natsuwarshi

"Kana lafiya kuwa?"
Ajiyar zuciya ya sake sauƙewa kan ya ɗan girgiza kai sai kuma ya gyaɗa kawai.
Rita tayi saurin cewa
"Ko dai Maaminka ce ke pressurizing ɗin ka? Matar abin da take yi bata kyautawa, kaman babu zuciya a ƙirjinta? Anya ita ta haif..."
"Shut uppp! U are very stupid mahaifiyata kike kokarin jefa da kalaman raini? I won't take that wlh kika sake ko da ambatan sunanta ne sai kin sha mamaki na.."
Yana kai nan ya ture ta ya fice daga wurin kujerun ya koma gaban table da masu kula da wurin ke ta sarrafa barasarsu ana cigaba da bawa masu siye wasu har da ƙanƙara ciki.

"Wadda ya fi kowanne ƙarfi"
Abinda ya faɗawa bar attendant ɗin kenan, shi kuwa ya san waye mukhy ya soma haɗa mishi kaman yadda ya buƙata ya gama ya tura mishi, cup ɗin ya zubawa idanu ya jima yana kallo kan ya kai hannu ya ɗauka yana ɗan jujjuya shi a hannunshi da alama dae contemplating yake ya sha ne ko kar ya sha, bakinshi ya kai da nufin sha sai yaji kaman muryan Baba na ce mishi
"Duk wadda ya dawwama yana shan giya har ya mutu Allah ya haramta masa aljanna, ko ƙamshinta ba zai ji ba bare ya shige ta"
Jifa yayi da kofin ta tarwatse ya miƙe ya nufi waje kaman kumurcin maciji, motanshi ya buɗe zai shiga yaji an riƙe shi

"mukhy Meke damun ka ne haka? Is something wrong?"
Juyowa yayi sai ya kallesu har su uku ne, Pepe, smart da Nawwaz ne, Smart da yayi maganan ya maida hankali kanshi yace
"I don't really know wlh smart, bana jin daaɗin komai i feel lonely, tired nd lost"
Pepe yace
"ko dai ka gaji da Rita kana son chanza Babe? Though na san Dukda kana tare da ritan kayi Ƴan mata dayawa."

"Ko sha'awar jin sunansu bana yi bare har in raɓesu, I hate everything wallahi tun jiya ko runtse idanuna na kasa da sunan bacci"
Shiru suka ɗan yi kan Nawwaz yace
"maybe you need space for Little bit ka ɗan huta, da dai zaka iya da mun koma ka zama high sai ka fi samun natsuwa da bacci yadda ya kamata"
Kai ya girgiza ya juya zai shiga mota smart ya riƙe hannunshi
"ba zamu barka kake driving kai kaɗai cikin wannan hali ba, zamu dinga kasancewa tare da kai har ka dawo daidai ko ya kuka ce?"
Ya tambayi saura suka ce hakane a tare suka shishiga motar, Smart ya ja suka fice daga harabar wurin.

****

Hawayenta ta share tare da ɗaga kai ta kalli saman ɗakin mutane are very wicked a wannan zamani namu, su kan manta cewa duniyar kwata-kwatarta bata da wani girma kuma aron rai aka bamu muke zama cikinta, bata san me zata kira iyalan Hassan dala dashi ba, menene suke dashi against waennan bayin Allahn? Ko rantsuwa tayi bazata yi kaffara ba akwai tsantsar son zuciya, hassada da baƙar kyashi a tare dasu waenda duk mugayen ciyuka ne masu zaftare imani ya ɗaiɗaita natsuwa da farin ciki, godiya ta cigaba da yiwa Allah da ya sa umar na gari da bata san yadda zata fuskanci Alayah ba idan ta farka, dole hankalinta ya tashi ta shiga damuwa saboda uwa ai wata giɓi ce da rasa ta rayuwa babban asara ce wadda mai da irin ita babu har Abadan Abada.

Banko kofan da aka yi ne yasa ta buɗe idanunta tana kallon Alhj hammad da ya shigo har huci yake sbd fushin da bata san a ina ya kwaso ba yake shirin zuwa kanta ya juye mata kwandunansu.

"Lafiya kuwa Alhj? Ya zaka bangaje kofan asibiti haka kuma babu sallama ka s...."

"Shut uppp!! Ki dakata min Fatima, uban wa ya baki izinin kutse cikin ahalin Hassan dala? Menene naki da rayuwar gidanshi? Ina ruwanki da komai na gidan?"

Ranta ta haɗe tace
"ban gane ba, saboda na ceci ran da yake gangaren mutuwa a hannun waenchan azzaluman laifi ne? Na san abokinka ne Dukda abotarku be taɓa burgeni ba hasali ma na tsani alakarku saboda Hassan zuciyarshi babu Allah cikinta na daɗe da fahimtar hakan to ba zan zuba idanu a cigaba da zaluntar bayin Allah nan ba ko me zaka ce sai dae ka ce"

"kin san me kike kokarin aikatawa? Kin fa san siyasata idan ba Hassan kaman babu ita ne, taya zaki yi kokarin yi min asarar mutum irin shi a gab sa'ar da burin raina ke gab da cika? Har ki aiki wanchan banzan ɗan n..."
Da sauri ta katse shi
"Umar ba banza bane Muhammad, kuma ba zai taɓa zama banza ba, ina zuciyar imaninka ya shiga ne? Cikin fa najasar kashi da fitsari, ɗauke da zazzafar stroke da hawan jini ya haddassa wanda ya assassawa matar chan shiga cikin come ya fiddo ta, shin wannan be zama abin alfahari ba? Menene laifin umar da ka ɗaura mai karan tsana saboda kawai ya saka idanu kan al'amuranka ya kuma tsaya tsayin daka wurin hana ka aikata mummunan laifin illata rayuwar matasa a cikin al'umma? Kar ka zama Hassan din mana! Kar zuciyarka ta yaudare ka wurin auren duniyar nan mana Abban Mukhtar.."
Ta ƙarasa da karyayyen hawaye.

"Ina ruwanku? In ma abinda ya fi fitsari da kashi ne ko comar banza ne duk babu ruwanki, ina ce nine na ɗauki yarinyar nan na aurawa Mukhtar? Toh zan saka shi ya sake ta ki tattara ta da ita da uwar da kuka jajibo ku watsar don wallahi zaki fuskanci mummunan ɓacin raina idan kuka yi sanadiyar lalacewar siyasa ta"
Ya ƙarasa kaman zai kifa da ƙasa don masifa, har ya juya ya nufi kofa yaji Maami na cewa
"ko menene zaka yi yanzu kam sai dae kayi Abban Mukhtar yanzu case ɗin ba tsakanina da Hassan bane tsakanin Umar da Hassan ne, shi zaka ja wa kunne amma ba ni ba"


Juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo kan ya juya ya fice yana sake buga kofar, kanta ta maida ƙasa ta sake silalar da hawaye kan ta share ta juya ta fice don duba Ummi dake ICU tun jiya ko motsi bata yi ba kaman yadda Alayar ma take ta bacci tun a jiyan don daga ta tashi za'a sake mata allura ta koma tana bukatar cikakken hutu.

Maami na fita ta buɗe idanunta tare da kurawa kofan, hawaye ne taji yana cika mata ido wato in ka hangi Maami daga waje zaka rantse da Allah cewa ta gama samun komai a rayuwa tana cikin daula da hutu ga kuɗi masu maganin matsaloli amma ba hakan ba ce mai ɗaki shi ya san inda yake mishi yoyo, ashe bayan jarrabawar Mukhtar tsakanin ɗaya ɗan ta da mahaifinshi babu zaman lafiya? Amma kaman maganan ummi ake? Sai yanzu kalaman ya ɗaukota cikin najasar kashi da fitsari da stroke wanda hawan jini ya haifar sanadiyar hakan tana cikin coma da wani irin hanzari ta miƙe zaune tare da fisge ruwan ba tare da ta damu da jinin da ya cigaba da bin tsintsiyar hannunta ba tayi saurin saka takalmi tayi waje.

Bayan Maami kawai ta hanga hakan yasa ta haɗa da gudu tana kiran sunanta, da sauri Maami ta juyo tana ganinta ta nufeta tana salati
"Menene haka Alaya? Meyasa zaki fusge ruwa daga jikinki haka? Dubi fa jinin dake zuba?"

"Maami Ummi na ce? Ummi ce kuke maganar Shiga coma? Me ya sameta ummi? Garin yaya? Taya hakan zata kasance.....innalillahi wainna ilaihi rajiun..""
Gabaɗaya ta ma ruɗe ta gigice
"Ki natsu Alayah tana cikin salama in shaa Allah Adu'a kawai take buƙata a halin yanzu daga gareki ba wannan kukan da ɗaga hankalin ba, in shaa Allahu yanzu ummi ta dawo wurina kenan har Abada ko da tana so ba zan bar ta komawa cikin uƙubar da ta fito ba"
Maami ta ƙarasa da alhini, da sauri Alayah ta rungumeta
"Na gode Maami mun gode sossai Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya biya miki buƙatunki na alkhairi ya saka ki cikin aljannah maɗaukakiya"
Har lokacin bata daena hawaye ba, tana cikin wani sabon damuwar duba da yadda saɓani ke shirin shiga tsakanin Maami da Abban saboda su kuma.

Jan ta Maami tayi zuwa ɗakin da aka kwantar da ummin, daga jikin window suka tsaya Alayah ta ɗaura hannunta bisa kai tana sake zub da hawaye, ummin ta ce haka? Me ya faru bayan barin ta gidan? Taya duk waennan abubuwa suka faru ba tare da ummin ta sanar mata tun wuri ba? Ummin ta aka bari da najasa Allah andi tsawon lokacin da ta ɗauka a hakan, kuka ta sake saki.
"Ashe ba zaki ji magana ta ba Binty? Ban ce ki daena ɗaga hankalin nan ba saboda yanayin ki? Toh shikenan kiyi ta yi"
Ta ƙarasa tana juyawa alamar tayi fushi da sauri Alayah ta riƙe hannunta tana anfani da ɗayan hannun wurin share hawayenta tace

"Na daena Maami, wlh na daina ki yi hakuri"
"yauwa ko ke fa? Mu je ki kimtsa ki samu ki ci wani abu sai a ƙara duba ki ko?"
Kai ta gyaɗa suka juya suka nufi ɗakin ta, wanka tayi bayan ummi ta haɗa mata ruwa ko da ta fito ma ta samu ƙannen Maami Aisha da ruqayyah tare da wasu ƴaƴan yayyunta maza sun shigo, da farin cikin ganinta hakan suka shiga amsa gaisuwar ta suna mata ya jiki? Tana amsawa da jikin da sauƙi sossai, abinci ta ci wanda yayi mugun mata daaɗi faten dankalin turawa ne aka saka mishi ugwu ya ji kifi ice fish, bayan ta gama nurse da Maami suka shigo ta kara dubata kan ta mayar da ruwan, kwanciya tayi tare da juya bayanta idanunta a lumshe.

Bayan tsawon lokaci hira tsakanin en uwan na tashi Aisha ta dubi Maami tace
"Adda Bintu yanayin ki kaman kina cikin damuwa, Mukhtar ne?"
Girgiza kai tayi sai yanzu ma ta tuna da Mukhtar din tun jiya bata ganshi a nan ba, ta san ba zai taɓa chanzawa ba ai.
"Aisha wato dukda abubuwan Mukhtar na damuna sai dae abinda ke damuna a yanzu ya shallake wanchan, na rasa wani hanya zan bi wurin shirya tsakanin Umar da mahaifinsu da basa jituwa sam sam, Dukda ban taɓa ganin laifin umar ba duk na Abban nasu ne sai de abin na ci min rai sossai wallahi"

Ruqayya tace
"har yanzu ne rashin jituwar nasu? Na zata bayan doguwar nasiha da faɗan baba komai ya wuce?"
Maami tace
"kusan an samu sauƙin hakan amma daga sadda umar ya kama masa wani kaya ya kirashi ya cicci mishi mutunci shi kuma umar yayi rantsuwar har Abada idan har zai yi wani hulɗa da ya shafe lalata rayuwar al'umma ba zai taɓa bari ba, daga shi har Mukhtar ko inuwa basa haɗawa dashi saboda kowa da abinda ya fassara irin kariyarshi, yana nuna jarumta akan lamarin sai dae na lura abin na damun shi shiyasa sam baya son zaman ƙasar nan"

"Ya cigaba da haƙuri wata rana duk zasu fahimce shi in shaa Allah, yanzu ki duba irin taimakon da yayi a kan baiwar Allahn nan, kina tunanin ko Abbansu Mukhtar ya isa fidda matar chan daga gidan Hassan a yadda ya kafa tarko yake kuma da gogewa da duniya? In ba irin umar ba bana tunanin zata tsira cikin sauƙi haka"
Cewar ruqayya a hankali.

Aisha tace
"Allah ubangiji ya kyauta amma tabbas akwai wata rana da duk zasu yi nadamar hakan"

Lumshe idanu Alayah tayi ta sake maimaita sunan Umar a ranta, ya taimaketa ita kam bata da abin da zata saka mishi anan duniya sai dae da Adu'a, lallai zuciyarshi a wanke take ko bata ganshi ba tunda zai iya saka hannu ya ɗauki umminta cikin najasa ya sakata a motar shi har ya kawo ta asibiti bayan ya fuskanci barazana daga Abban Jameelah.

A haka bacci ya sure ta, bata farka ba sai dab Magrib, a hankali take motsi ta ɗan shaki numfashi tana jin kamshin turaren da taji rannan a sashen Maami me daaɗi, waigowa tayi don ganin me wannan kamshi sai suka haɗa idanu da Mukhtar, wani kakkauran miyau ta haɗiye cikin kokarin danne fargaba da tsoron da ya bijiro mata musamman idan ta tuna abinda ya mata kwanaki a asibitin chan da aka mata aiki.

Da idanu yake bin ta har ta miƙe zaune, muryanta ta ɗan gyara ta ce
"Ina yini?"
Albarkacin ya girme mata kuma ɗa ga Maami.
Be amsa ba sai kallon da ya cigaba da bin ta dashi, chan ƙasa ta ja tsaki tana kokarin sauƙowa taji ya ce cikin buɗaɗɗiyar muryarshi
"Ke! Ni kika ja wa tsaki???"

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment


                     🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Sixteen*

*Na riga na yi alkawari in ba haka ba ina zan iya typing karfe 12🥲 sorry guys class nayi da ba zan iya dodging ba*

Bakinta ta tura gaba ba tare da tayi magana ba Dukda tsallen da ƙirjinta ke yi kaman ana dakan sakwara, sai dai abu ɗaya da ta lura dashi da ya bata lasisin hakan shine ba'a chake yake ba kuma idan hakan ne ta san zafin ran nashi da sauƙi, ba zata taɓa gigin yi mishi hakan ba idan yana buge don zai iya ƙas da ita a wurin ba tare ma da ya san ya aikata hakan ba, ƙarasa sauƙa tayi tare da sanya silifas ɗin ta
"Ke! Ina miki magana kin mai da ni banza?"
Nan ma bata ce komai ba taku biyu tayi ya sanya hannu ya fusgo ta tayi baya luuu ya mata masauki a kan kafafunshi hannunshi ya sa ya zagaye ta yana me kurawa fuskanta idanu for the First time a rayuwarsu irin kallon nan na kurilla yace chan ƙasa
"ba da ke nake ba Fatee?"
Ba tare da ta kalleshi ba ta zumɓura baki tace
"to ai ni sunana ba ke bane, ba gashi da ka kira sunan na amsa ka ba??"
Ta karashe

Please Login or Register in order to submit comment