Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗa mata umar ya ce bayan lafawar komai in har babu wani cigaba za'a fitar da ita waje, tana cikin total coma ne tsakanin rai da rayuwa.

Alhj hammad Abdulhameed chanji a yadda al'amari ya zo mishi ta sa dole zuciyarshi ta durkushe, laifukanshi suka dawo suka lulluɓe shi, idanunshi sun rine kwarai a kwanakin da suka biyo baya a jere, kwanakin da suka kasance na zaɓe da kuma kirga kuri'u tare da faɗin sakamako, babu abinda ya fi girgizashi irin mummunar shedar mutane, yana ji yana gani ya faɗi wanwar hakan ta sa ya tafi tunanin kalmomi na karshe da suka haɗa shi da ɗan shi na biyu a lokacin da shi da Mukhtar suka sanya shi gaba da kyara da kuma hantara haɗe da baƙaken maganganu masu zafi don kawai ya dage da iyakar karfinshi wurin hana su saɓon ubangiji, yayi uwa yayi makarbiya akan duk wani mummunan sana'a da zasu yi, a lokacin gani suke kaman sanya idanu ne, toshe cigabansu ne yake tunda baya taɓa bari kayakin su ya shigo Nijeriya bare har ya shigo hannunsu su sayar, sun kasa tuna cewa yana da daman ɗaure su amma ya ki yin hakan a duk son shi su shiryu su dawo kan hanya, lallai da be raini Mukhtar bisa gurbatacciyar hanya ba duk wannan abubuwan ba zasu faru ba, kalaman mutane da shaidarsu a kan Mukhtar da ma shi da ake ɗaurawa laifi da mahaifiyarshi da bata ji ba bata gani ba baza su kawo karshen rayuwarshi ba kuwa?

"Ban taɓa ƙin ku ba, ba kuma zan taɓa hakan ba, zan nesanta kaina da ku Dukda hakan ya zame min wani babban giɓi da abin baƙin ciki musamman in na duba cewa kun tura ni nesa da farin cikina wato mahaifiyata, hakan ba zai taɓa sa na bari kuyi abin da kuke so ba Abba, ku sani in har baku neme ni ba ni ba zan taɓa neman ku ba sai dae idanuna suna kanku, haka kuma a duk sadda na yi ra'ayi zan tako har cikin gidanka in ga mahaifiyata don ita bata ƙi ni ba, bata sanya min bakin cikin da zai farauci farin cikina da nesanta kaina da jama'a ba"

Har ya miƙe sai ya juya yayi taku biyu uku kan ya ja tunga ba tare da ya juyo ba ya soma cewa.

"Idan Yaro ya faɗi tashi yake ya ruga a guje, idan babba ya faɗi ya kan waiwaya ne ya ga me ya kayar dashi, idan ba ku yi nazarin jiya ba gobe ba zata taɓa yi muku kyau ba, ku daurewa zuciyoyinku kuyi rayuwar da zata zamto abin koyi ga na baya abin sha'awa ga na tare da ku, abin kishi ga makiya sannan abin alfahari ga dukkan masoyanku, ku kiyaye saɓani da mutane watarana za'a yi shaida walau da rai walau babu, wannan ɗin kusan saƙon mahaifiyata ne gareni inda take bani kwarin gwiwar zama Kunkuru cikin macizai na zaɓi na raba da ku ne saboda kuma ku rabauta... Na barku lafiya"

Daga wannan rana ba zai ce ya sake ganin umar ido da ido ba, shekaru sama da Goma sha biyar, ya wofintar da rayuwarshi saboda kawai yana gyara musu tasu, umar ya kan zo har cikin gidan amma baya taɓa bari ko da a hange ne su hangi juna, hakan be taɓa damunshi ba sai a yau, hawaye kawai yake zubarwa motsin kofan shi ya ji, be damu da share hawayen ba har Maami ta shigo, kusan yanzu tana rayuwa dashi ne akan dole, haushi da takaicinshi karara yake gani cikin idanunta, abincin hannunta ta ajiye ba tare da ta tanka ba ta juya ta ɗauki na safe yadda ta ajiye shi be taɓa ba, taku uku tayi tace

"Ban sani ba ko har yanzu wannan soyayya ta Mukhtar na nan dankare a zuciyarka, na shiga dumbin mamakin sanin cewa har yau baka iya zuwa inda yake ba baka kuma damu da halin da yake ciki ba, hasali ma maƙiyinku shine yayi uwa yayi makarbiya wurin ganin cewa ba'a zalunci ɗan uwanshi ko an illata shi ba, duk ba wannan ne ya sa na tsaya ba, na tsaya ne in ce maka gobe da misalin karfe takwas za'a shiga court an tsagaita sabd zaɓe, ban roƙi ka shiga lamarin don ɓinne gaskiya ba sai dae akwai buƙatar zuciya ta ɗanɗani azabar aikinta..."
Tana kai nan tayi gaba, kanshi ya shafa yana huro iska, rudanin da yake ciki yasa be san komai akan abin da ke faruwa da Mukhtar din ba, be ba Mukhtar laifi duka ba ya raba ne a tsakaninsu hakan yasa ya mance Mukhtar din na ɗan lokaci, kuma a yanzu bashi da wani kwarin gwiwar fuskantar kowa da wannan lamari...

COURT

A yadda aka fito da su zaka yi tsammanin babu wadda ze iya magana cikinsu sbd yanayin wahala da suke ciki wadda ba sabon su bane, shi Mukhtar be iya ya kalli kowa ba, yayinda Alayah ta maida hankalinta kanshi tana kallonshi, har yau bata jin komai akan Mukhtar bayan ƙimar mahaifiyarshi da kakanshi, tunaninta na kai kawo ne akan shin ko shi ya aikata ko ba shi ya aikata ba zata iya cigaba da zama da shi kuwa? Zuciyarta ta riga ta kuntace shi, duk yadda tayi kokarin chusa tausayi da soyayyar Mukhtar a ranta ta kasa bata san cewa duk daɗewar sanda a ruwa baya taɓa zama kifi ba...

"Shin kun amsa laifukanku?"
Kusan shine tambaya na karshe da alkalin yayi bayan gabatar da duk hujjoji daga bangarorin lawyoyin masu kare wadda ake kara da masu kara, duk wasu shaidu sun fito karara, Nawwaz ne ya dubi mukhtar da har lokacin be ɗago kanshi ba, har yanzu basu faɗa cewa babu Mukhtar cikinsu ba, shima kuma tun da ya fada a gaban su Maami be sake furtawa ba, ko da suka zauna wuri ɗaya banda istigfari babu abin da yake yi, be musu magana ba duk kuwa irin surutan da suka dinga yi mishi, sun mishi adalci kenan idan suka sake dulmiya shi cikin damuwa bayan damuwar da suka san yana cikinta?

"A ƙarshe bayan duk wasu hujjoji da shaidu da suka gabata, kotu ta yankewa waennan matasa huɗu shekaru goma goma gidan yari tare da azaba me tsanani, da kuma tarar naira miliyan ɗaiɗai daga kowannensu zuwa ga iyayen yarinya don a cigaba da kula da lafiyarta"

Hannu ya sa ya ɗauki kulkinshi ya buga aka miƙe gabaɗaya, alkali ya juya don komawa office nashi hankali kwance. Yayinda polisawa suka yi kansu tare da ma'aikatan kotu don tabbatar da isansu prison lafiya.

Littafin nan ba kyauta bane, book 2 na kuɗi ne a yanzu mun fara jin ƙamshin karshen book 1 ku hanzarta biya saboda yanzu muka soma tafiyan, zaku iya biya ta wannan asusun
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai shaida ta wannan layi
09039206763




🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Page Twenty*

"Ya mai girma me shari'a!!"
Chak kowa ya tsaya a cikin kotun saboda yadda tayi magana da amo, fuskanta gabaɗaya ya cika da zallar gigita da kuma ruɗani wadda ta kasa ɗaura shi a mizanin hankali bare ta iya daidaita tunaninta, bata jira cewar shi ba tunda ya riga ya tsaya ta soma sauƙowa cikin sassarfa har ta isa gaban Mukhtar da ya zura mata idanu baya ko kyaftawa, zuciyarsa na wani irin fusga da wutar ƙaunarta da bashi da masaniyar sadda ta ruru har ta zame mishi wutan daji, ta cinye ilahirin zuciyarshi da duk wani sassa da jini ke gudana.

Gabanshi ta isa ta kalle shi cikin idanu ta ɗago ta kalli alƙalin cikin Muryar roƙo da karaya ta ce
"Don girman zatin Allah me shari'a ka taimaki macen da take dauke da juna biyu na wadda aka yankewa shekaru goma gidan firsuna, ka taimaki uwar da take shirin shiga tsananin tashin hankali saboda yanke wannan hukunci bisa kuskure, ka bamu dama ta biyu ina me tabbatar maka babu hannun mijina ciki..."

Be tanka ba don yanayinta ya fi kama da mahaukaciya wacce take cikin sabuwar kamu, bata damu ba tunda dae yana tsaye ta juya ga Mukhtar da banda kallo babu abinda yake binta da shi ta sanya hannu ta riƙe nashi, cikin karyayyen murya me cike da tausayi a gauraye da son da bata san tana mishi ba saida taji hukuncin da aka yanke mishi ta soma cewa
"Ya Mukhy a rayuwa muna kuskure, kowa yana kuskure kawai abinda ya kama ce mu a duk sadda hakan ta kasance shine muyi imani, mu kuma rayu da wannan consequences ɗin da kuskuren mu ya janyo mana, tunaninmu ya karkata ga tunanin tayaya! Ta kuma wani hanya zamu bi wurin gyara wannan kuskure"
Hannunshi ta kara gimtsewa tana roƙonshi da idanunta

"you don't have to blame yourself all for that Yaa mukhy, ba sai ka shigar da kanka cikin bala'in da baka da masaniya bane za'a san ka chanza wlh we all believe you... Ko Maami?"
Ta juya tana kallon Maami da banda hawaye babu abin da take zubarwa sai ta gyaɗa musu kai, da sauri ta juyo tana mishi kallon ka gani ko? Sai ta sake cewa da sauri
"Duk yadda kaddara ta zo a haka zamu karɓa mu kuma cigaba da rayuwa, karka nesanta kanka da mu da tunanin mun tsaneka, halayyarka ce bama so kuma ka sauya don Allah kar ka bari in haifi yaron da zai shekara goma cikin duniya ɗaya da mahaifinshi ba tare da ya san shi ba, maraici akwai ciwo Don Allah"
Ta haɗa hannayenta wuri guda tana kuka.

Da sauri ya sa hannayenshi duka biyu ya riƙo hannunta ya sauƙar ya mayar da ɗaya kan fuskanta yana share mata hawayenta a hankali cikin sanyi ya furta
"Ban aikata ba Fatee, Na rantse da wadda raina yake hannunsa ban aikata ba..."
Nawwaz da hawaye ke ta zuba mishi saboda sai yanzun ne yaji basu kyauta ba, barin ma da Alayah ta juyo kansu ta haɗe hannayenta
"Don Allah kuji tausayin ɗan dake kwance a cikina, ku tausayawa mahaifiyar da ita kaɗai ta kan mance adu'a akanta wa kanta da rayuwarta saboda ta shagaltu wurin yiwa wannan ɗan nata Adu'a ku tsage gaskiya, kar ku kasance masu Son zuciya please"

Nawwaz ne yace
"Be aikata ba wallahi, hasali ma be san sadda muka yi hakan ba sai bayan mun gama"
Smrt ma ya ce
"hakane wallahi, Mukhtar baya cikin mu"
Alkalin da gabaɗaya jikinshi yayi sanyi da tausayin Alaya da irin maganganunta sai ya dawo ya zauna, kowa ya koma ya zauna shari'a ta sake dawowa daga baya, kai tsaye duk su ukun suka bayyana gaskiya inda yarinyar m ta tabbatar da cewa mutum uku ne ba huɗu ba, shari'a saɓanin hankali sai gashi an wanke Mukhtar, Alayah kaman ta tiki rawa sai ta koma inda mazauninta suka rungume juna da Maami.

Har suka iso gida bayan kammala komai Alaya bata iya ta ce komai cikin motan ba saboda yadda duk ya cike wurin, lallai natsuwa wani rahama ce ta daban, ɗakinshi na sashen ya wuce yayi wanka Maami ta tura a kai mishi Abinci, a chan ya ci ya kwanta bacci ba shi ya tashi ba sai azahar yayi wanka ya fito a wurin mashigar suka haɗu kiribb da Abba, kallon juna suka yi na seconds kan duk suka nufi ciki don karyawa.

Abin mamaki wai na kwance ya faɗi yau Abba ne da Mukhtar suka hadu babu wadda ya iya yiwa dan uwansa magana, Alayah da Maami already sun ci hakan ya sa Alayah isowa gaban dining ɗin Sin serving ɗin su.

"Abba ina yini?".
Ya faɗa saboda gaisuwar kaman dole ce a gareshi
"Lafiya..."
"Ka kuwa san kana buƙatar neman yafiyata? Ashe duk hanyar da ka ɗaura ni kai ina ganin gata da soyayya ce babban halaka ne? Abba baka kyauta min ba sam, kaine sanadin duk wani kuskurena a rayuwa I hate you for that"

Banda kallo da idanu babu abin da yace da Mukhtar din wadda hakan ya saka zuciyarshi hasala ya fara watsawa mahaifin nashi baƙaƙe maganganu cikin ɗaga murya, da gudu Alayah ta ajiye maheer ta tare Mukhtar tana mai rufe mishi baki a lokaci ɗaya tana girgiza kai cikin firgicin kalaman da yake jefawa mahaifin nashi...

Ayi haƙuri da wannan wlh bacci ne ya ci karfi na.

🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Page Twenty one*

"Ya Mukhy ka dawo cikin hayyacinka Abba ne fa"
Abba da yake zaune shiru ba tare da ya ce komai ba duk maganganun Mukhtar ɗin ne suke dawo mishi, a hankali ya ɗago idanu ya kalli Maami da ta iso wurin ta tsaya ba tare da tace komai ba, ashe haka take jin nauyi da zafi a ranta a duk sadda yake ba Mukhtar goyon bayan faɗa mata abinda be dace ba ba tare da kwaɓa ba, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah kan ya buɗe ya kalli Mukhtar da ke ta huci har lokacin Alaya bata sauƙe hannunta daga kan lips ɗin shi ba yace

"Fatima kyale shi, barshi ya faɗi duk abinda ke ranshi ko me zai faɗa na tabbatar babu ƙarya cikinta, na riga na cuci rayuwarshi na mishi illah, ban nemi yafiyarshi bane ba don ban yi nadama ba, nayi shiru ne saboda ban san me zan ce ba, ban kuma san ta wani hanya zan bi wurin taya shi gyara kuskuren da nine silar faruwarsa ba, amma ke ina rokon yafiyarki akan kalamaina na jiya"
Cokalin ya ajiye ya miƙe zai fita Alaya tace
"Abba!"
Tsayawa yayi daidai kusa da Maami ba tare da ya juyo ba tace
"abin da na faɗa a kotu ɗazu shi zan sake maimaitawa, kowa yana kuskure hakanan kowa na laifi saidai wadda ya fahimci laifin shi ya kuma tuba yayi niyyar gyarawa be yi kuskure ba, hasali ma abin da ake fata kenan, Don Allah karka saka damuwa a ranka Abba.
Ya Mukhtar na fahimci yadda kake ji a ranka, sai dae ba hakan ne ya baka daman aibata mahaifinka ba, babu inda ya bamu wannan daman idan har da gaske ka gyara kuma ka chanza daga Mukhtar na da to kayi kokarin saita harshenka wurin magana da iyaye don Allah ya ɗaga darajarsu.
Maami Don Allah da manzonsa kiyi haƙuri, fushi ko rashin yafiya duk ba zai chanza komai ba, mu haɗu duk mu gyara abin da ya ɓaci a baya adu'ar ki ce a yanzu Allah ya ƙarba, muyi kokarin zama one Big happy family Don Allah"

Mukhtar da kanshi ke ƙasa hawayenshi na ɗiga bisa kan dining ɗin a ranshi yake jin Alayah is too good for him, be yi abinda Allah zai bashi ita matsayin mata ba, bayan duk abubuwan da suka faru ji yadda take magana kaman be gallaza mata ba, har ta yafe mishi kenan? Lallai idan zata iya yafe mai kuma har ubangiji zai iya yafe mai ya barshi da mace irin Alayah to shi me zai hana shi yafewa Abba? Maami ya ɗago ya kalla tana zub da hawaye itama idanunta na kan Alayah, har ranta take son yarinyar Allah ya mata baiwa na daban, idanunta ta maida kan Abba da jikinshi yayi matukar sanyi, kwarai suna bukatar cikakken farin ciki na tsawon shekarun da suka rasa a gidan ko da kuwa ba zai tabbata ba, shiyasa yake ganin gazawarshi ya kuma tabbatar komai ya faru tun farko daga shi ne, idanunshi ya lumshe yana jin kanshi na sarawa babu tantama hawan jininshi ne.

Mukhtar ne ya yanke sad moment ɗin don tunda Alayah ta gama magana tayi shiru kowa da abinda yake saƙawa cikin ranshi, a hankali yake jan kafafunshi har ya isa gaban Maami ya zube bisa gwiwowinshi kanshi a ƙasa yace
"Na san ni gagarumin me laifi ne a gareki Maami, tabbas a da na zama wawa, jahili, marar amfani na bi sahun waenda Allah ya ƙira da Ƴan wuta nayi ta saɓa miki cikin sani da kuma rashin sani, kin yi kuka har ba adadi, kin shiga damuwar da har ki kan yanki jiki ki faɗi, amma duk da haka baki tsane ni ba, baki daena min adu'ar shiriya ba, baki zare hannunki a kaina ba ba kuma ki yi min mummunan furuci ba saboda ke uwa ce! A yanzu ina tsananin jin kunyar kaina da na mahallacina, ina jin nauyin neman gafararki saboda abubuwan dayawa, Don Allah Maami ki yafewa Mukhtar ɗinki, ki yafe mini ko zan samu kwarin gwiwar tunkarar mahallacina da neman gafara, Maami ki ɗaukeni kaman jinjirin yaron ki da kika haifa a tsumman goyo in baki ragamar rayuwata ki yi min sabon tarbiya uwa ta gari, na tuba don Allah"
Yadda yake kuka sai ya sa su duka kuka har Abba hawaye yake yi, kafaɗanshi ta kamo ta ɗago shi kawai ta rungumeshi Allah ya sani kukan farin ciki take, kukan jin daaɗi yau Mukhtar ya zama mutum, ɗagowa tayi tare da sanya hannu tayi cupping fuskanshi tana kallonshi cike da sabuwar soyayya tace
"Na yafe maka Mukhtar, har Abada na yafe maka duk wasu laifukanka gareni da wadda na sani da ma wadda ban sani ba, Allah ya yafe maka... Ina so ka zama kaman ɗan uwanka a kusa dani duk abinda ya shige maka duhu a sabuwar tafiyar nan taka da zaka fara kar ka ji nauyi ko kunyar tambayata kaji?"

Hugging ɗinta ya sake yi, Abba ya sanya hannu ya share hawayenshi kan yayi taku kaɗan ya ƙaraso gabansu, Maami ya kalla
"Fatima ki yafemin na cutar dake a iya zaman mu, nayi kuskure me girma wadda ban farga ba sai a yanzu, bayan lalata tarbiyar Mukhtar na kuma nesanta ki da wadda zaki gani ki ji haske, lallai na tabbata mugu, azzalumi ban yi la'akari da cewar ke ɗin uwa ce ba, ban duba kasancewar ki mace me raunin zuciya ba ƴaƴa biyu da Allah ya baki duk na wargazasu na tauye farin cikin ki na tsawon shekaru na tuba"
Kai ta gyaɗa tace
"komai ya wuce Abba, in shaa Allah zamu ƙarasa sauran rayuwarmu wurin gyara duka waennan kuskuren"

Mukhtar ya kalla zai yi magana sai yayi hanzarin rungumeshi, a rungume dashi yace
"Abba kayi haƙurin kalamaina na dazu, na san duk abubuwan da kayi min a yadda ka ɗauki soyayya kenan baka min da niyyan zalunci ko don in lalace ba, hasali ma mune muka zalunci Umar, na riga na yafe maka Abbana, Allah ya bamu ikon gyara laifukan mu"
Duk da Ameen suka amsa, sai a lokacin kowa ya iya sakin murmushi a cikinsu, dawowa suka yi Maami ta sake serving Abba sbd wanchan yayi sanyi, Alayah kuma tayi serving Mukhtar dake ta kallonta wadda hakan yake sakata jin kaman ta nutse cikin ƙasa.

Basu zauna ba suka yi cikin parlor suka zauna da Maami, Maami ce ta nuna mata cinyarta sai ta zame ta kwanta tare da yin matashin kai da shi, a hankali ta zame dankwalin kanta tace
"Binty dai Allah yayi ki irin Maaminku, kema bakya son kitso sam"
Murmushi tayi tace
"Maami ai tsoron kai ne da ni, daa ummi sai tayi da gaske take min kitso saboda rigima daga baya tace na girma in ma naki ni na sani, shikenan sai dae in wanke in shafa mai"
Murmushi Maami ta sake tana cigaba da ɗan sosa mata kan tace
"Lallai Binty ke ɗin wata haske ce a cikin rayuwarmu, ina Alfahari da samun ki matsayin ƴa Allah ya albarkace ki ya ba ummi lafiya"
Tana lumshe idanu saboda baccin da yake son kwasheta don susan kan daaɗi yake mata tace
"Bani da abin da zan saka miki Maami, illa iyaka a duk sallata na kan sanya ki a Adu'a Allah ya miki abin da zato be taɓa zato ba, tunanin ɗan Adam be taɓa kaiwa ba, Allah ya miki muhalli na musamman a cikin gidan Aljanna, haƙiƙa nayi matukar dacen samun ki a matsayin uwa"

Murmushi Maami ta saki, a hankali ta ɗaga kai sai ta ga Mukhtar da Abba ma hira suke ɗan yi a hankali, idanunta ta lumshe ina ma da umar yana wurin da farin cikinta ya zama cikakke, amma ta san irin zuciyarshi ga yanayin aikinshi Allah ya sa ya yafewa babanshi da ɗan uwanshi har su yi zama da mutunci.

Ko da Suka gama wurinta suka dawo, tuni Alayah tayi bacci kan kafafun Maami, hira suka cigaba da yi su ukun kaman komai be faru ba, shawaran karatuttukan da zai fara suka yanke inda a kullum da yamma zai tafi wurin baba sai goman dare ya dawo, tuni ya kira kakan nashi ya shaida mishi ze fara zuwa ɗaukar karatu har yar raha suka yi baban na cewa ya faɗi gaskiya ko furanshi na dare zai ke zuwa shanyewa kullum suka ɗan yi dariya, ya kula kowa so yake ya ja shi a jiki, kwarai hakan ya mishi matukar daaɗi don hakan ne kawai zai kasance ya san eh zai iya, zai iya zama na kirki, shima zai iya gyara kura-kuranshi, kuma he is accepted a welcome a familynshi.

Idanunshi gabaɗaya zube a kanta, murmushi ya ɗan saki yana kallon yadda ta sake lafewa jikin kujeran kaman mage, haƙuri na musamman yake son bata, sai dae baya tunanin a yanzu ne zai yi hakan, duk yadda yake jinta a ranshi da yadda yake jin a yanzu ita ce bugun numfashin shi zai mata adalci, dole sai ya zama nagartaccen mutum kaman kowa zai iya sake fuskantar ta da kokon barar matsuguni a cikin ranta.

Abin da be taɓa faruwa ba shi ya faru yau, sun yi hira sossai har la'asar cikin raha, sai tuno baya ake Maami na hiran yarantanshi yana dariya, dariyanshi ne ya tada Alayah, ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta watsa mishi, shima da baya mintuna biyu be kalleta ba idanunshi na kanta, bakinta ta turo mai na tana baccinta me daaɗi ya tashe ta, murmushi me kyau da bata taɓa gani a fuskanshi ba ya sakar mata, da sauri ta ɗauke kai tare da kokarin Miƙewa zaune.

"Sannu Fatima"
Abba ya faɗa tayi murmushi, Maami tace
"kin tashi Binty? Ko yunwa ce ta tashe ki? A kawo miki wani abu ne?"
Jinta take ƴar gata, a da ana musu kallon kaskantattu marasa galihu babu wadda ya damu da damuwarsu, cin su, shan su ko lafiyar su amma duba a yau yadda waennan ahali suke mata, ai ko menene tayi musu bata faɗi ba.

"Maami bari dae na shiga kitchen ɗin da kaina"
Ta miƙe ta nufi kitchen ɗin, Masu aikin suna aikinsu cikin tsabta, Tabawa ce ta dubeta
"Hajiya karama kina bukatar wani abu ne?"
Tayi murmushi tace
"A'a ki yi aikinki baaba, bari na haɗa da kaina"
Indomie ta dafa guda biyu, anan ta zauna suna ƴar hira tana dariya har ta cinye kayanta, ko da ta fito ta samu duk basa nan a parlorn da alama sun je sallah, itama ɗakinta ta haura ta gabatar da la'asar din kan ta kwanta a wurin cikin tunanin umminta, Adu'a take tayi a ranta na Allah ya ba ummi lafiya, Allah ya tashi kafadunta don bata san ina zata kama ba in ba ummi, bata san kowa nasu ba, ko suna dashi ko basu dashi duk bata sani ba.

Maami bayan ta idar da sallah Umar ta ƙira, a natse suka gaisa take bashi labarin abinda ya duk ya faru, ya taya ta farin ciki don da farin cikinta shima yake samun farin ciki.
"Yanzu yaushe zaka shigo?"

Ɗan shiru yayi kan yace
"in shaa Allah zan shigo idan na samu sararin aiki Maamina kar ki damu"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tace
"Toh Don Allah idan cikinsu wani ya ƙiraka ka ɗaga ka ji? Yafiya abu ne me kyau wadda dukkanmu muna son shi a wurin mahallici, ashe don mu mun yafewa junanmu bamu faɗi ba ko kaɗan, na san irin zuciyarka ka daure a maida komai ba komai ba ka ji autan Maami?"
Murmushi ya saki me sauti har tana jinshi, saboda yadda ta ƙarasa maganan da lallami kaman ɗan yaro, ita ma murmushi ta saki suka yi sallama.

Kofan ɗakin aka yi knocking ta bada izinin shigowa, Mukhtar ne ya shigo zai yi magana daga chan tayi saurin miƙa mai hannu ya iso ya riƙe

Please Login or Register in order to submit comment