Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dangin mijin da suke ta kananun maganganu na mamakin zuwanta ɗaukar amarya alhali ɗan ta ne na fari kuma kowa ya san rashin jituwarsu saide tayi kunnen uwar shegu dasu kaman bata san suna yi ba wai an tsikari kakkaura, a hankali da taimakon ummi Alaya ta samu ta zauna tana zub da hawaye ta gaida Maami, cikin kulawa ta amsa kan tace
"Binti ya baki shirya ba?"

Murmushi me ciwo tayi ina wani kayan shiryawan mutanen gidan kaman basu san da zaman su ba bare su yi tunanin kyautata mata a yau dai ɗaya.
"Maami bani da lafiya ba zan iya tafiya ba, ba zan iya tafiya in bar ummi a wannan gida ba Maami don Allah ki ce ya barni ban shirya aure yanzu ba, don Allah karki rabani da ummi wallahi zan iya mutuwa"
Tayi maganan cikin sanyinta da kuma alamar roƙo da sallammarwa rayuwar gabaɗaya.

Da kyar Maami ta iya mayar da hawayenta tana karbar farin takardar da ummi ta miƙo mata
"ƴata na haifeta da ciwon zuciya! Don Allah ki kula min da ita da lafiyarta, ki riƙe min amanarta, ban san ko zamu sake haɗuwa nan kusa ba amma don Allah ina roƙon ki alfarma guda ɗaya a matsayinki na uwa kema, ki yi min kokari kan karatunta idan kika min wannan alfarma zan kasance me saka miki da addu'ar rahama da jin kan ubangiji har illa ma sha Allah..."

Kasa rike hawayenta tayi ganin yadda Alaya ta koma jikin ummin ta rike hannunta gam tana kuka sossai, Aure yakin mata hakane amma wannan kukan na Alaya ba na auren bane kawai harda na taradaddadin yadda zata rabu da mahaifiyarta alhali an gindaya mata sharudar sake ganinta gashi ummi ba fita take ba, matan wurin dangin mijin Maami sai kananun maganganu suke wasu na taɓe baki saɓanin dangin Maami da tausayi da kuma jin kai aka raine su Dukda iyayensu suma masu arzikin ne sossai da sossai.

Duk yadda Maami ta rarrashi Alaya ta kasa samun galaba a kanta, yadda ta rike ummi seda kowa yayi mamaki duk yadda akyi ta sake ta ta ƙi banda kuka babu abunda take, ummin ma sai hawaye take da kyar da sudin Goshi aka raba su ummi tayi saurin yin daki aka fita da Alaya a yadda take.

Maami ta kasa yin shiru kaman yadda tayi niyya har a sadata da gidan ta ta kalli drivern tace
"Ghali juya motar nan mu tafi gidana"

Ƙanwarta dake gefen ta tace
"Ah yaya binta gidanki kuma?"

"Aisha sa hannu kiji jikin yarinyar nan, ciwon zuciya ke gareta in muka kaita Mukhtar da haukashi ya kashe wannan yarinya me zan cewa mahaifiyarta? Bana tunanin an yiwa waennan bayin Allah adalci wannan zalunci ne wallahi"
Ta karashe tana share hawayen fuskanta tana kuma sake rungume Alaya da har lokacin kuka take sossai.

Duk wasu kananun maganganu da aka yi tayi bata kula kowa ba kuma sun santa babu wadda ya fuskance ta yace komai har ta sada Alaya da ɗakin baccin ta ta kuma sallamesu akan sai ta shirya amaryar zata kaita da kanta.

Bayan watsewar kowa ta koma ɗakin inda ta barta nan ta sameta dunkule bisa tsararriyar gadon na Maami, a natse Maami ta ƙarasa ta ɗago ta
"Fatima.. Don Allah ki daena wannan kuka haka, kin san condition naki Its not good for your health kin ji?"

Maamin ta faɗa tana share mata hawaye wasu sabbin na zuba tace
"Maami hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, ba zan taɓa farin ciki ba ba kuma zan taɓa daena zubar da hawaye ba matukar mahaifiyata na wanchan baƙin gidan, Maami zasu kashe min ita wallahi babu imani a zuƙatan su ko na second guda ya zanyi? Wani mataki zan bi in iya taimakonta a wannan rayuwa da na tsinci kaina? Wayyo Allah na na shiga uku!"

"Baki shiga uku ba ɗiyata, umminki bazata mutu ba, abunda nake so dake shine ki fara ceton kanki da lafiyarki kan kiyi tunanin hanyar ceton umminki, babu ta yadda zaki iya yi mata komai idan har kika faɗa cikin wani hali, Fatima ina en uwanku? Ko na mahaifiyarki ko naki? Wani irin aiki ne wannan da babu encin kai a ciki?"

"A yadda kika gan mu haka nima na tashi na same mu cikin wannan hali, Ummi bata magana alhali tayi magana a baya, ummi bata da dangi kaman yadda ta shaida min mahaifi na ma bashi da kowa, da ciwon zuciya aka haife ni me naci da ciwon gaske na tashi cikin tsangwama, kyara da mugunta iri iri, ummi bata taɓa bani labarin wani rayuwa nata na baya ko na mahaifi na ba, abunda dae kawai na fahimta shine me gidan na mugun jin zafina da tsana ta sbd wani abu chan da ya hadasu da mahaifi na kaman yadda yake da mugun nufi akan mahaifiyata, matar gidan ta tsani mahaifiyata fiye da kowa a duniya sbd laifin da har yau ban san menene shi ba, muna rayuwa akan wani baƙin siradi a cikin gidan yanzu ya min iyaka da gidanshi alhali na san kashe ummi na zasu yi da bauta wadda basu taɓa godiya akai ba, ummi karfinta ba kaman da ba Maami abubuwan zasu mata yawa, babu ta yadda zan iya ji daga gareta bare in san halin da take ciki, Maami taɓa zuciyata kiji ji nake kaman ze fita daga kirjina sbd azabar bugu da ciwo..."

Hawaye Maami ta share tana shirin magana aka yi knocking a take ta bada izinin shigowa family doc din su ne da suka yi magana kan Shigowarta ta kuma bada umarni a chan kasa akan yana zuwa a mishi iso har ciki.

Allurai ya haɗa yayi mata a take ta fara lumshe idanu kan wani baccin wahala ya sake daukar ta.
"Hajiya ya kamata a kaita asibiti sbd yanayinta yana nuna tana wani stage me girma na ciwon nata kuma in tana sa damuwa a rai hakan ka iya kara shi fiye da yadda ya kamata ya tafi"

"za'a yi yadda kace doc, in ta ɗan yi kwari zan nemi appointment ko a waje ne sai muje in shaa Allah"
Godiya yayi kan ya fice.

Ita kuwa ta shafa tulin gashin Alaya cikin tausayawa tace
"zan taimakeku Fatima, zan taimaka muku iya yadda zan iya in shaa Allah"
Ta faɗa hawaye na gangaro mata...

Miƙewa tayi ta fito daidai lokacin da muktar ke shirin tura kofan ɗakin nata, hade rai tayi tana kare mishi kallo
"lafiya?"

"Ina fa lafiya Maami Meyasa kika hana a kai min matata chan gida aka kawota nan? Akan me?"

"Toh Ubana ka shakeni sai kaji amsa, ɓace min a kofar daki tun muna shaida juna"

Ashar yake shirin wawurowa tayi hanzarin kai hannu ta kuwa samu bakin ta Buge da karfinta, ni dae baya na matsa don na ga kokarin Maami chan fa sama take kallon muktar sbd tsawo da kuma murdewarshi don yana ɗaga karfe ba na wasa ba kuma shi ɗin dan dambe ne mafadacin gaske ne amma Maami ko a gyelenta yana shirin mata rashin kunya zata kai hannu, tana kuma saurin kwaɓarshi ne sbd gudun zunubin da ya ke tarawa kanshi yaji da iya na abubuwan da yake yi mana kar ya hada da fushin Allah akan taɓa iyaye iyayen ma uwa for that matter...

Hanyar da ta nuna mishi take kuma kallonshi cikin fushi ya bi kaman zai tashi sama yana sauka yayi ɓangaren mahaifinshi da hanzari ya san shi kam ya isa da ita kuma zai kwatar mishi yanci wannan ai ba yi ba bane haka kawai yadda yaci burin wannan dare ta kama ta lalata mishi wlh ba'a isa ba, saide duk abunda ze faru ya faru har yana haki ya fara mayarwa Dad ɗin su yadda aka yi.

"Wani lokaci Binta na abunda be dace ba wallahi ta bugeka akan matar da take mallakinka? Ai yanzu ko iyayen yarinyar ka fisu daraja a gaban Allah bare ita bintan, to baze yiwu ba sam, bari naje naji me take nufi? Don a saka ta a daki a kulle aka yi auren? Ina itace ta nuna bata son auren kuma yanzu don bakin ciki tasa ƴa a gaba ta kulle ta hana ka ita? Ina zuwa ko kuma wuce muje kawai.."
Haka ya tasa ɗan a gaba suka yi ɓangaren Maamin.
(hmmm wallahi maza mu ji tsoron Allah mu sani 'ya'yayen nan kaman amana suke a hannun mu, su ɗin kiwo ne da Allah ya bamu kuma ze tambayemu akai a ranar gobe, ba ina magana bane akan duka maza saide ina magana ne akan mazan da basu taimakawa uwa wurin tarbiyartar da yaro, iyaye mazan da suke wofintar da duk wani kokarin uwa akan ganin yaro ya zama nagari, iyaye mazan da duk abunda uwa zata yiwa yaro basu ganinshi as kauna sai mugunta alhali duk duniya babu wadda ya kaita son wannan yaro, iyaye mazan da suke gurbatawa yaransu tunani suke nuna musu babu kaunarsu a rayukan iyayensu mata alhali ba hakan bane, iyaye mazan da basa taimakawa uwa wurin tarbiyartar da yara. Wallahi mu gyara mu saka idanu akan ƴaƴanmu ko zamu samu rayuwarsu ta inganta... Single mothers Allah ya saka muku da alkhairi).

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment



                 🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1
*Page Eight*

"Alhj for goodness sake kar ka sa na fara yi maka musu a gaban yarinyar da yau ne ta soma shiga cikin mu, yarinyar nan bata da lafiya kuma ciwon zuciya ke gareta idan ta mutu a yau wallahi Mukhtar bashi da asara tunda ba darajar ta ya sani ba, ni ban hana a kai mishi matarshi sbd jin daaɗi ba idan ta samu sauƙi da kaina zan sadata da ɗakinta"
Maami ta faɗi hakan idanunta akan Alhj da ta janye shi zuwa ɗaya ɗakinta na saman.

Dukda shi be wani ji tausayin yarinyar ba sede ya amince tunda bata da lafiya ne kuma ciwon irin ciwon da akan rasa mutum farar ɗaya ne don hakan yasa dole yayi shiru ya fito ya janyo hannun muktar suka yi ƙasa yana faɗa mishi situation ɗin cikin lallami kaman shine uban shi kuma Alhj ɗan, tana tsaye tana jin muktar da be gamsu ba yana alaƙanta hakan da son ranta ne in yayi ra'ayi sai ya kwana da mata sama da biyar a daren kuma ba abunda zai faru akan banzar talaka ana ƙona mishi rai.

Duk da zafin kalaman da Maami taji hakan be sa ta barshi ya kai zuciyarta ba adu'ar shiriya ta mishi kan ta nufi ɗakinta, har asuba bata yi wani baccin kirki ba Sbd Alaya, cikin ikon Allah kuma da kanta ta tashi kiran farko tayo alwala ta zo ta fara nafila don ba'a binta sallah, da murmushi Maami ta shiga bayi tana godiya ga Allah, bayan sun yi sallah komawa Alaya tayi ta lafe sbd magungunanta da basa barinta ido biyu cikin sauƙi sam bata san ma fitan Maami ba, ba ita ta farka ba se 11 na safe.

Wanka tayi ta sake mayar da kayanta ta zo ta zauna daga bakin gadon zuciyarta fal tunanin halin da umminta ke ciki lokaci lokaci ta kan share hawaye ta san ummi na chan aiki sun mata yawa ga jama'ar gidan sam basu san imani ba, Shigowar Maami ne yasa ta suluɓe ƙasa tana cewa
"Ina kwana Maami?"
"Lafiya klau bintie ya jikin dae?"
"Bana jin komai maami".
Karasawa Maami tayi ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye tace
"kinga Ɗiyata ki daena wannan nuku nukun ki saki jikinki ki ɗauke ni tamkar umminki kinji?"
Kai Alaya ta gyaɗa, Maami ta janye ta akan suje su yi breakfast suna tafiya tana kara nunnuna mata gidan tana sake jadadda mata ta saki jikinta nan ɗin kamar gidansu ne.

Breakfast me rai da motsi Maami ta zuba mata itama ta zuba kaɗan sbd ta baiwa Alayar kwarin gwuiwar ci, saide inaa kaɗan taci Dukda daaɗin shi sbd tunanin ummi da yayi mata yawa ganin abincin kadai yasa ta fara tambayar kanta ko ummin ta ci? Yanzu kila tana kitchen tana wahalar dahuwar rana..

"Aji nawa kike a makaranta?"
Maami ta katse mata tunanin da ta tafi, a hankali ta ajiye cokalin da dama jujjuyawa kawai take cikin abincin tace
"SS3 muke First term"
"Wani school ne?"
Ta tambaya a take Alaya ta faɗa mata, lallai school me kyau ne.
"Kina so a miki register ɗin waec a chan? Na san karshen second term dae zaku fara rubuta paper"
Ɗan shiru tayi tana tuna yadda Jameelah ke tsangwamarta da friends dinta gashi babu wadda ya san an mata aure tana komawa sabon kyara ne ze tasar musu hakan yasa tace
"a'a"
"Ok zan bincika wani nan kusa sai a saka ki, amma wani course kike son karantawa in kin shiga jami'a?"
Ɗan murmushi tayi
"A da dae ina sha'awar likita saboda taimakon al'umma ta ɓangaren jinya sai kuma daga baya na zo na fara sha'awar law saboda samarwa mutane ƴancin su, matasa dayawa are physically, mentally and emotionally traumatize amma babu wadda ke iya noticing, mutum na da darajar da hatta ubangiji bai yarda ka ci mutuncinshi ba tunda da kanshi ya karrama mu, ina kuma Son business saboda ina so in yi kuɗi Maami, tunda har kuɗi ne ke sa a san da kai a kuma mutuntaka ko ba don Allah ba, ina son yin kuɗi.."

Murmushi ne me kamar dariya a fuskan Maami tace
"Toh Yanzu ke kam ma baki tsayar da abu daya ba, amma kuma duk abin da kika lissafa yana da kyau, wani ɓangare kike karanta secondary?"
"Science"
Ta bada amsa tana ɗan kallon Maami
"kenan a abubuwan da kika lissafa likitanci ne kawai zaki iya yi, ki ƙara nazari da bincike duk abunda kike ra'ayi zaki yi in shaa Allah"
Cikin murmushi tace
"Na gode sossai Maami"
Magana take shirin sake yi tana daga idanu sai idanunta suka faɗa cikin nashi, cike da tsananin tsoronshi tayi saurin sadda kai ƙasa, jan kujeran dining din yayi ya zauna
"Maami good morning"
"morning"
Maami ta amsa mishi tana kallon yadda Alaya take ta wasa da fingers ɗin ta, cikin sanyin murya tace
"Ina kwana?"
"Lafiya" ya bata amsa yana ɗan jan tsaki, ai saida ya faɗa kawai Maami sbd ta kuntata mishi ne kawai tace yarinyar ba lafiya gata nan garau ɗin ta.
"Muktar ka tura min kuɗi zamu je da Fatima mu haɗa mata lefe"
Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.
Sakaka yake kallonta kan ya girgiza kai
"amma ai bamu yi haka da gidansu ba Maami, ya daga zuwan yarinya zaki fara ɗaure mata gindi wurin raina ni? Me tazo dashi ita gado ko katifa? I thought wannan abu vice versa ne yi min in maka?"

Da hanzari Alaya ta ɗaga kai tana kallonshi mahaifiyarshi yake magana da ita cikin kafin harshe da rashin tauna magana? Ya subhallah lallai akwai aiki me girma a gabanta innalillahi ta shiga nanatawa, Maami da ta jima tana kallonshi ta girgiza kai...
"Kaje gidan naka ka gyara mata sashe allura ban amince ka saka ba, za'a kawo mata kaya saboda haka karka kuskura ko da wasa ka sake yi mata gori, kai kuma dole ne ka bada kuɗi enough a yi mata lefe"

A wurin ya ɗaga waya yayi call ya bada umarnin gidan shi na jambulo a fitar da kayan part ɗaya da tsantsar mamaki Alaya ke kallonshi kallon dani kike zancen yayi mata kan yayi kwafa yayiwa Maami transfer ɗin kudi masu yawa, ta taɓe baki tace
"duk sadda na shiryata zaka ganta, bintie tashi mu tafi"
Kunkumi yayi tayi na wlh duk abunda Maami ke mishi akan yarinyar ze rama..

Da yammacin ranar Maami ta ja ta suka tafi kasuwa sayayya me tarin yawa suka yi, kasuwanni har uku suka je bata bar komai ba tsab ta haɗa mata lefenta kan ta saya mata wasu ready mades da kuma egyptian abayas da zata ke anfani dasu kan a yi mata dinki, daga nan suka tsaya wurin telan Maamin ta bada dinkunanta atamphopi masu tsadar gaske da kyau har goma sha biyar, se lesuna guda goma da shadda irin ta mata duk ta zaɓi irin zubin da take so guda biyar, tace sauran zata ɗinka a hankali.

Lokaci lokaci Alaya ke kallon Maami tana yaba irin kirkinta ashe akwai masu irin wannan halin karamcin a masu kuɗi da suka saura a duniya? Lallai Maami mutuniyar kwarai ce Adu'a tayi ta mata a sadda suka tsaya shagon wayoyi ta zaɓa mata IPhone Xs max sai ta sayi wani tecno madaidaici take ce mata
"gobe da kaina in shaa Allah zan kaiwa Umminki wannan sai ku dinga exchanging messages ko hankalinki ze kwanta"
Adu'ar gamawa da duniya lafiya tayi ta mata da cikan burukanta na alkhairi.

A gajiye tilis suka dawo duk kayan da ma'aikatan gidan suka kwaso ɗakin Maamin suka zube su yayinda duk suka yi alwala suka gabatar da magarib, suka dan yi karatu a tare sai bayan isha suka sauka dining.
Alhaji hammad da Mukhtar na zaune suna cin abinci har ƙasa Alaya ta duƙa ta gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa, ta ja kujera ta zauna tana jin idanun muktar a kanta, ita tayi serving Maami ta saka kaɗan zata juya Maami tace
"Ah ina zaki daughter? Zauna nan ni fa har na gaji da faɗamiki yanzu duk daya muke we are family already"

Zama tayi a kunyace ta soma ci duk ɗagowar da zata yi se ta haɗu da firgitattun Red eyes ɗin shi yana aika mata wani kallo, lokaci lokaci Maami kan yi magana da Alhj amma shi baya sa musu baki.

Bayan sun tashi sama Alaya ta koma sbd gujewa irin kallon da yake mata, wayoyin su da ummi ta sa a chargy cikin murna take Allah Allah gobe yayi ko zata samu taji lafiyar ummin tata, a nan ta zauna gadinsu har Maami ta same ta ta ɗan zolaye ta kunya ya sakata Miƙewa taje ta fara shirin kwanciya bata yi ko mintuna biyar da kwanciya ba bacci me daaɗi ya ɗauke ta gabaɗaya jinta take cikin wani sabon rayuwa, sai yanzu take jin ta samu Ƴanci kamar kowa matsala ɗaya in ta tuna yake ɗaga mata hankali shine auren muktar dake kanta, da irin zaman da zasu yi sannan babban abunda ke damunta yadda baya baiwa mahaifiyarshi daraja, taya yake tunanin ganin haske a al'amuranshi ta lura babu wadda ya raina irin Maami, uwa tagari irin wannan Allah ya jarabceta da samun ɗa irin Muktar kuma kaman bata da wasu da akwai da kila ace zakka ya fita, saboda irin kyautatawar Maami garesu taji a ranta zata iya zama da muktar da zuciya ɗaya kila ta sauya shi zuwa mutumin kirki...da waennan tunannuka bacci yayi awon gaba da ita.

Kaman yadda Maami tayi alkawari Washegari ta aika aka kaiwa Ummi wayar, Alaya dake ta kimtata lokaci a jikinta taji wayar ta isa hannun ummi da sauri ta rubuta text message sai ko ga reply na ummi tayi ta murna barin ma da ummin tace mata lafiyarta ƙalau kuma bata wani aikin sossai don an kawo sabbin ma'aikata girki kawai take musu, sai sannan hankalin Alaya ya kwanta ta miƙe kafa a gidan Maami ta ma manta da zancen aure in ba ta ga muktar ba, banda gaisuwa babu abunda yake hada su wani lokacin ma ko tayi niyyar sauƙa in taji muryarshi sai ta koma, sai ta tabbatar ya tafi ta fito.

Satin ta biyu Maami ta kaita wani school me kyau fiye ma da ainihin school dinta aka mata registration ko da aka zo interview babu questions da bata amsa ba har Maami seda ta burgeta sbd akwai kwazo da tarin ilimi akan yarinyar, class ɗin ta aka barta bayan an bata uniform a makarantar Maami ta barta akan driver ze zo ya ɗauke ta in an tashi.

Sossai take jin daaɗin makarantar sbd babu bullies ɗin ta su Meelah da kawayenta kuma kowa a makarantar harkar gabanshi kawai yake, yau juma'a da misalin karfe sha biyu na rana drivern da ya zama nata yayi parking kofar makarantar da ɗan hanzarin ta tazo ta buɗe ta shiga da sallama suka gaisa a mutunce kan suka kamo hanyar gida, a daidai parking lots yayi parking ta sauƙa tana mishi godiya tare da fara takawa don isa cikin gidan, spot car dake parke a tsakar gidan Red Color BMW a tunaninta ma ba kowa don bata ji karar injin motar ba se kawai gani tayi kofa ya buɗu, ko bata kai idanunta zuwa ga fuskar ba daga kafar ta riga ta shaida waye ne.....

"Ke!"
Ya faɗa a kausashe chak ta tsaya gabanta na faɗuwa tana da ilimi kuma ko makaho ya shafa ze san cewa muktar baya cikin cikakken hankalinshi.
"Don kaza kazarki ba dake nake ba?"
Ya antayo zagin yana kara kakkafeta da jajayen idanunshi, idanunta dake rawa ta sauke bisa tattos ɗin jikinshi Farin fatar shi tas duk ya lalata kaman akwai wani sabo ma daga wuyanshi....

"Na'am"
Ta faɗa tana ɗan matsowa kaɗan a kuma tsorace
"na biya sadakinki don ki zama min hoto ne? Ke wallahi tsohuwar chan tana jaza miki don sai na tabbatar na ladabtar dake bisa wannan biye mata da kike, sai kin zamto min kariya babu maganan wadda zaki iya ji idan ba na uban gidanki ba, wuce ki shiga mota mu tafi!" Ya daka mata tsawa
Jikinta na tsuma tana rawar leɓe tace
"Maami bata ce in tafi ba, and plz ka daure ka daena faɗin munanan kalamai akan Maami ko ba komai ta ɗauki cikinka na wata tara chur ta kuma yi nak....".
"Shut up bloody fool, ke har kin isa ki gayamin abunda zan yi? U r like a servant to me, na aureki ne kawai don kyaun surarki ku kuma don kwadayi irin na talaka kun ga kuɗi kuka amince, for ur own information ko Asawanyarki bata kaini daraja ba don haka ke baiwa tace na fanshe ki kuma da kuɗi wuce mu tafi tun muna shaida juna.."

Baya baya ta fara ganin yana nufo ta, kan yayi wani yunkuri ta runtumi na kare, taku biyu yayi ya.....

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment



🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Nine*

Haki take saki tana juya bayanta ganin baya binta yasa ta dafe kirjinta, in wannan ɗan daban ya riƙe ta ai kashinta ya bushe, seda ta daidaita kanta kan ta kutsa cikin parlorn Maami ta gani zaune idanunta da hawaye, da sauri ta isa ta duƙa a gabanta kaman zata saki kuka aka ce zuciya tana son me kyautata mata jin matar take kaman Ummi tace
"Maami me ya faru kike zub da hawaye?"
Shiru Maami tayi, babu me fahimtar halin da take ciki se uwar da Allah ya jarrabe ta da ɗa irin Mukhtar, ace kana ji kana gani yaro ya nemi gagararka? Allah kaɗai ya san me ya je ya sha ya zo yake mata rashin kunya akan matarshi, duk zafinta akan muktar ne tana da sanyin hali da tausayi shima kuma da farko ta bi dashi da lallami da nasiha saide abun yaci tura, ganin hakan mahaifinshi ke mishi yasa ita ta karɓi ragamar zama uwa da uban saide duk a banza man kare, zafin dake kirjinta ya wuce misali bata fata ta mutu ba tare da ta ga chanzawar Mukhtar ba, tana mishi tsoron fushin ubangiji tana kwaɗaita mishi rahamarsa...

"Maaami"
Alaya ta kira sunan hawaye na cika idanunta.
"Babu komai ɗiyata, je ki cire uniform ɗinki kizo ki ci abinci"
Gudun musu da Maamin yasa ta miƙe ta tabbatar be wuce muktar bane

Please Login or Register in order to submit comment