Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito ta soma tattare parlorn incident ɗin jiya na dawo mata lokaci lokaci tana share hawayen baƙin ciki.

BAYAN WATA ƊAYA

Yammaci ne sakaliya tun safe bata fita daga ɗakin ba, bata jin karfin jikinta sam ganin yunwa ze iya mata illa don daga kwance ma jiri take ji yasa ta miƙe ta fito sanye da dogon hijab as usual ta shiga kitchen.

Rabin taliya ta dafa da kwai dafaffe guda biyu ta zuba a plate, ta juya frigde don ɗauko ruwa se ga Rita ta shigo kai tsaye plate ɗin ta ɗauka zata fice, shan gabanta Alaya tayi tana jin ranta na ɓaci

"Baiwar Allah lafiya?"
Da mamakin tsaurin idanun yarinyar Alaya tace
"ba lafiya ba kam, taya zan dafa abinci don na ci ki zo kawai ki ɗauka ba magana ba komai kaman zamanki nake?"
Idanu Rita ta ɗan fitar cikin mamakin yau Alayar tayi magana haka ita bata taɓa ma jin dogon magana daga bakinta ba.
"Karfi ya ci daru ya danne, bani hanya in wuce hai village girl kawai"
Ranta ta sake ji ya zo mata wuya yarinya fitsararriya ta shigo har cikin gidanta tana zaune duk kauda kan da tayi be isa ba sai ta haɗa da zagi da cin zarafin ta ko da shi ke ba laifinta bane, cikin ɓacin rai tace

"Ai kuwa gwara da ni sau dubu saba'in in ma na amsa ni village girl din kenan, ko ba komai village girl ta fi ashawo...."
Watsa mata abincin gabaɗaya Rita tayi jiki yayinda ita kuma Alayah ta dauketa da zazzafar mari.
   hango Mukhtar bayan Alayar yasa ta dafa kumatu ta saki razananniyar ihu, cikin kuka tace
"Wallahi yau zan bar maka gidanka Mukhy, har ni matarka zata ɗaga hannu ta mareni akan banza taliya? Ni dae?"

Da sauri Alayah ta juya zata yi magana ya kifa mata mari, yayi ball da ita bata san ta tafi kaman wacce iska ya ɗauka ba seda taji ta sauƙa a kafafun mutum, ɗagowa tayi bata gani daidai sai taga Maami ce da sauri ta miƙe ta faɗa jikinta ta soma kuka me cin rai, kan Maami tace tayi wani yunkurin kawai Alaya ta yanki jiki ta faɗi ƙasa...

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Mukhtar ka kashe musu ƴa ka huta, nace ka huta.."
Tana nufo shi ne take maganan
"wani irin zuciya ne da kai? Wani irin baƙin zuciya ne Allah ya halicceka da ita? Ashe baka da tausayi Mukhtar dubi yadda yar mutane ta koma"
Kwalan riganshi ta chakwamo
"Allah ya saka mata, wallahi Allah se ya bi mata hakkin ta, Allah ya mata sakayya tun a duniya, mugu azzalumi.."
Hawaye take yi bibbiyu, hannunta yake kokarin cirewa a wuyan shi tana sakin shi kuwa ta soma zuba mishi maruka hagu da dama tana kuka.

Ganin hakan baze mata ba ta soma neman abinda zata kwada mai ko zata huta bata yi taku biyu ba itama ta yanki jiki ta faɗi ƙasa. Se a lokacin ya gigice cikin hanzari y dago ta yana kiran Maami Maami, sede Maami tayi nisa, daukanta yayi da gudu zuwa motanta driver ze ja yace ya jira shi, da sauri ya koma ya ɗauko Alayah da banda haushinta babu abinda yake ji dama tsakanin shi da mahaifiyar yaya gashi tana kara ɓatawa, ta wannan ne kawai zasu iya samun matsala da Abbansu don yana son matarshi.

A motanshi ya saka ta yana gaba drivern Maami na bin su a baya har asibiti, cikin gaggawa aka Karɓe su emergency, likitoci suka rufu a kansu wasa wasa har aka yi Magrib kan suka samu kan Maami, Alayah kam se kusan bayan isha ma likita mace ta fito tana kallon Mukhtar
"kaine mijinta?"
Kai ya gyaɗa yana kallonta
"Toh Congratulations matarka tana ɗauke da ciki na tsawon sati biyar sede akwai karancin nutrient a jikinta, and ciwon zuciyanta yana so ya tsananta kaman yadda jininta ke hawa duka wannan illah ne ga lafiyarta a gaskiya ya kamata ku kiyaye, a ka'idar aiki ma bayan an mata wanchan aikin zuciyar be kamata kuma ya sake hitting haka ba"

Shi duk sauran jawaban ma baze ce ya ji ba banda batun cikin nan da ya ji.
"Ciki???"
Ya maimaita kan ya sake cewa
"do you mean pregnency?"
Kai ta gyaɗa, ya ja wani dogon tsaki ga ta inda ya tsani auren ai, yarinya ta zo banda gidahumanci babu abinda take mishi kwata kwata ko shekara bata rufa ba ace wani ciki, shiyasa ya fi son hulda da wayayyun mata shi be shiryawa haihuwa yanzu ba...

"Look likita ina so ki zubar da shi ko nawa ne zan biya"
"wannan ba aikina bane, kuma bama haka a asibitin nan amma zaka iya zuwa gaba se ayi maka"
Har ta juya yace
"ko don lafiyanta? What if cikin ne yake triggaring ciwon zuciyar? I th....."

"MUKHTAR"
Maami ta kira sunan, se kawai ta sulale ta zauna a wurin tana hawaye a ranta tana istigfari bata san me zata yiwa Mukhtar ya shiryu ba, babu me fahimtar ciwon ranta babu me gane abinda take ji da takaici da haushin ɗan da ta haifa a cikinta se wacce jarabawa irin wannan ya faɗarwa, muryarta a rarrabe tace
"ka fice daga asibitin Mukhtar wallahi na tsani ganinka"
Da sauri ya ɗago ya kalleta, ze yi magana ta daka mishi tsawa tana dafe kanta dake juyawa.

"I Said Get outttt!"

Miƙewa yayi ya fice, da sauri likitar ta ƙaraso ta riketa ganin tana shirin sake collapsing.
"Se hakuri Aunty, Adu'a itace maganin komai ki kara akan wanda kike"
Maami na hawaye tace
"Wallahi ina yi Likita, ina yi bana bacci amma kaman bana yi astagfirullah Allah na tuba Allah"
Tausayinta sossai ya rufe likitan, ita tayi ta kwantar mata da hankali amma ta koma ɗakinta firr ta ƙi tace zata zauna da Alayah gudun sharrin Mukhtar.

Se kallon yadda kasusuwa suka yiwa yarinyar sarka take yarinyar gwanin tausayi, rayuwarta duk ya daidaice sbd Mukhtar, matakin da ta yanke kawai shine na riketa ta nema mata saki wurin Mukhtar shine kwanciyar hankalinsu duka, in ya ga dama ya tara matan duniya a gidanshi yana zina dasu tunda abinda yake so kenan, share hawayenta tayi ganin Alayah na motsi ta riƙe hannunta....

"binty kin farka?"
Kai ta gyaɗa tana sake lumshe ido tace a hankali
"Maami cikina kaman ana karta"
"ai dole, taya me juna biyu zata zauna da yunwa sossai haka har ya fitar da ke hayyacinki? Ruqayya na hanya bari in kirata tayi sauri"

"Juna biyu???"
Bata san a fili ta maimaita ba seda Maami ta ɗago ta kalleta tace
"Eh, kina dauke da juna biyu na tsawon sati biyar..."
Dibbbbbb haka duniyarta ya tsaya, komai nata ya tsaya chakk kaman robot ta sake maimaita
"Juna biyu dai?"

*karki manta book 2 na kuɗi ne, da Naira ɗari biyar kachal zaki mallaka, a sha karatu lafiya*
3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta
09039206763*

                       🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Thirteen*

*A cikin satin nan ina da hidima sossai so it depend da yanayin comments naku, in yi Page ban ga comments na arziki ba ga gajiyar hidima ga al'amuran yau da kullum gaskiya ba zan iya ba, sai in bari sai sati na sama in cigaba*

Yanayin fuskanta sai ya so ba Maami tsoro don ƙiri-ƙiri ya nuna bata na'am da lamarin cikin, lumshe idanunta tayi tana jin hawayenta na sake yi mata nisa sbd tsabar zubar dasu da ta ke, sai ciwon zuciya mai tsanani da take ji kaman ko yaushe zai iya yin ajalin ta, sam bata yi farin ciki da cikin ba, ba wai bata so bane ba kuma wai ta tsani ɗan bane kawai bata shirya haihuwa da Mukhtar bane cikin wannan hali da suke ciki na rayuwa, bazata taɓa so ɗan da zata haifa ya tashi ta nuna mai muktar a matsayin mahaifi ba, sam be chanchanta ya zama uba ba bashi da nagarta da wannan nasabar taya zai iya baiwa yaronsu tarbiya da taimakon da ya dace?

Dafata da Maami tayi ne ya sa ta buɗe rinannun idanunta ta kalleta
"Binty Dukda ban san yanda kike ji a cikin ranki ba nayi imani baki son wannan ciki, na tabbatar ba don wani abu bane sai don hallayyar Mukhtar in har baki shirya yanzu ba sai a zubar a yi miki planning zuwa wani lokaci.."
Da sauri kuma sai ta dafe cikin, gudan jininta za'a zubar? Girgiza kai tayi tana barin hawayenta zuba tace
"Maami ba zan ɓoye miki ba, hasashenki gaskiya ne sede ba zan iya zubar da wannan ciki ba, tunda Allah ya bani ya san dalilinsa na yin hakan watakila sanadin shiryuwar Ya muktar din kenan don Allah a bar min"

Murmushi Maami ta saki tare da shafa kanta tace
"Allah ubangiji ya miki Albarka binty, Allah ya shirya muktar ya san cewa dami a akala ce ya tsinta kar daga karshe yayi faɗuwar baƙar tasa, a lokacin da nadama bashi da anfani"

Shigowar ruqayyan ne ya katse su, da kanta ta zubawa Alayar abinci Maami ta taimaka mata ta zauna kan ta soma bata abincin, cikin natsuwa take karɓa har seda ta ƙoshi kan ta ce ya isa Maamin ta mika mata ruwa ta sha, kan ta sake kwanciya sai bacci, Aunty ruqayya ce tace
"Amma yarinyar nan na da tsananin haƙuri Adda, ina tsoron kar shiga hakkin nata yayi yawa, idan mariƙinta ya mata muguntar haɗa ta da muktar mu da muka san halayyarsa maras kyau kuma be kamata mu zuba idanu tana shan wahalarsa ba kiyi hakuri in abinda na faɗa ya ɓata miki rai"

Murmushi me ciwo Maami tayi tana kallon Alayar tace
"a yanzu ruqayya zaman yarinyar nan da muktar ya fi cin raina fiye da yanda kike zato da asalin hallayyar muktar ɗin, tausayinta nake ji har ƙasan raina da ita nake kwana da ita nake tashi, amma in shaa Allah daga yanzu hakan ya wuce, Fatima ta gama zama da muktar in shaa Allahu, ko da mariƙin nata bai karɓeta ba ni zan zauna da ita har Allah ya kawo mata wani mijin da zai share mata wannan bakin cikin"

Tattaunawa suka cigaba da yi duk akan matsalar Mukhtar, chan sai ga Alhj ya shigo yau kam seda yayiwa Mukhtar faɗa akan abinda yayi wanda hakan be wani ɗaɗa muktar din da ƙasa ba wayan ma ya ajiye a gefe hands free yana zuƙar shisha ɗin shi hankali kwance, bayan ya gama ya kashe.

Ita Maami bata wani yi maganan Alayar da shi ba don ta san duk inda aka je aka dawo yana bayan Mukhtar don ba ganin laifin shi yake ba sam, saida ta kwana biyar a asibitin kan aka sallameta, a wannan karo Maami ita ke yini ta kuma kwana duk yanda ruqayya tayi da ita akan ta bari su kwana ko ta kawo mai aikinta su kwana ta ƙi tace bata so ko kusa Mukhtar ya sake yunkurin cutar da ita, daga asibitin gida suka yi direct ɗakin dake gefen nata Maamin ta mata masauki don ta sake.

Da kanta ta tura aka haɗo mata kaya akwati har biyu da wayanta da take ta magananshi sbd son jin Umminta da take, ɗaki ne me girma da tsari babu abin more rayuwa na kuɗi da babu ciki, Maami ta mata umarni da ta dinga kulle kofan in an yi knocking sai ta tabbatar da waye kan ta buɗe don ta san Mukhtar farin sani, ita kuma zata cigaba da kula Dukda ta saka securities hana shi isa sashenta tace duk shigowan shi iyakaci sashen mahaifinshi bata amince ya zo mata sashe ba.

Zaman Alaya a gidan ya matukar yi mata daaɗi duk wani kulawa na me juna biyu tana samu daga Maami, da kanta take shiga kitchen take dafa mata duk wani abu da ta san zai ƙara mata lafiya, haka a asibiti ma an yi recommending ta yawaita cin irin su vegetables, jan nama da dai sauransu, laulayinta ba mai yawa bane saide zazzafar zazzabin yamma, sai kuma wani sa'in amai shima ba sossai ba, kaman yadda ta ɓangare ɗaya Mukhtar ya gigice don duk yanda yake tunanin hukuncin Maami ya wuce nan tayi rantsuwa ko ya kawo mata takardar Alayah ko su haɗu a court ya bata ta karfin tuwo tunda yarinya bata son shi, Alhj hammad din ma bata ragar mai ba gashi yana ɗan busy sbd siyasa da ya kawo kai gadan-gadan.

Damuwar Alayah guda ɗaya takkk na rashin jin mahaifiyarta duk text message da zata yi mata ba reply tayi ta kira tun yana shiga har ya daena, wannan na daga cikin abinda ya shigar da ita sabuwar damuwa da zaƙuwar son ganin mahaifiyarta, suna zaune da Maami suna ɗan taɓa hira yayinda Maamin ke chat kaɗan kaɗan tana murmushi me sanyi sbd da sanyin zuciyarta take magana, Dukda ɓacin rai yake nunawa ita kam lallashin shi take ta kuma lura har da Shagwaɓar da baya rabo dashi in dae yana gabanta kaman ba shi ba.

Kira ne da ya shigo wayan ya sa ta gyara zamanta a natse tayi picking ta sanya a kunnenta cikin ladabi kaman tana gaban na cikin wayan ta soma miƙa gaisuwa cikin kulawa yake amsawa kan a natse yace
"Faɗimatu yanzu mijinki da ɗan ki suka bar nan"
Haɗe fuska tayi kenan kararta suka kai wurin baba.
Kanta ƙasa tace
"Baba kayi haƙuri na jin wani abu na laifina da kayi daga gidan aure saide ƙullin na da girma dole sai na warware maka zaka fahimceni, na san baka daga cikin masu goyon bayan zalunci da kai da me sunanka zuciyoyinku iri ɗaya ne a wanke a kuma dake, cike da gujewa duniya da kyamatar azzaluman cikinta, don Allah ka bani dama zan zo har gida ka ji uzurina"

Ajiyar zuciya ya sauƙe yace
"Ina fata ba hikiman zancen da Allah ya miki bane kika kanainaye ni da ita, ina jiranki"
Daga haka ya yanke wayar, saukewa tayi ta saki ajiyar zuciya bata fata ko kusa baba yayi mata dole na ba Mukhtar Alaya sam bata wannan ra'ayin.

Duban Alaya da sai juya wayanta take tayi tana karantar damuwar fuskanta kaman ma bata san da wayan da Maamin ta gama yi ba tace
"Binty"
Bata amsa ba ta sake cewa
"Fatima.."
Nan ma shiru, Miƙewa tayi ta isa gareta ta taɓa ta sai tayi firgigit ta zubawa Maami idanunta dake cike da ruwan hawaye, Maami tace
"Binty yawan tunani hatsari ne ga lafiyarki, menene? Me damuwar?"

Hawayen ta ne ya gangaro tace
"Maami yau sati na uku ake shirin shiga ban ji daga Ummi na ba, hankalina a tashe yake ina tsoron kar dae wani abu ne ya sameta"
Ajiyar zuciya Maami ta sauƙe kan ta dubeta tace
"In shaa Allah lafiyanta ƙalau kila ɗan wani abu ne kalilan in shaa Allah jibi sai driver ya kai ki ki dubo ta don bana tunanin Alhj Hassan chanji yana nufin furucinsa akan ki"

Murmushi mai ciwo Alaya ta saki ita kam ta riga tayiwa Abban Jameelah farin sani babu ko shakka abinda ya faɗa ɗin har ranshi ne sede zata je ɗin, ko yanka naman jikinta yake zata je taga mahaifiyarta.

Washegari da misalin karfe huɗu na yamma Maami ta ɗauketa suka nufi family house ɗin su, babban gida ne me sashuka uku, matan gidan ba dae karamci ba haka ma'aikata da kalilan yara dake gidan wasu na kiran Maami yapendo yayinda wasu ke cewa Goggo ta fahimci duk masu ce mata Adda ɗin kannenta ne, anan taga daga inda Maami ta samu zuciyar daraja ɗan adam ko yaya yake, ba karamin kudi ne dasu ba daga tsarin ginin zuwa kayan ciki kaɗai ya isheka shedar hakan amma ji yadda suke Haba Haba da ita.

A sashen mahaifiyarta suke dattijuwa ce me tarin ilimin addini, kana ganinta zaka iya kiranta da Ba'abziniya ko kuma shuwa cikin biyu dae kaman yadda Maami take kama da ita sak, haka ma Mukhtar, sai bayan Magrib baba ya aika kiransu.

Cikin natsuwa suka zauna daga ƙasa a gabanshi, ita dae Alayah tayi farin gani don dattijon duk inda ake son samun kamillale natsatsen dattijo ya kai, wannan shine tsufa me riba a tsufa da mutunci karkashin inuwar addini, bayan sun gaisa ya dubi Maami yake ce mata yana sauraren ta, tiryan-tiryan ta soma bashi labarin abubuwan da suka faffaru nan ma bata san wasu ba kaman na ɗura mata kayan maye da yawan duka kaman jaka, ga siyar da mutunci.

Ita dae Alayah kanta ƙasa ko daga shirun da wurin ya ɗauka bayan gama bada labarin Maamin ta san ran dattijon be mishi daaɗi ba

"Muktar sam be kyauta ba, hukuncin da kika yanke ma ban ga laifinki ba, ba zai yiwu a bashi mace da ciki yaje garin duka ya raunatata ba, ina zuwa"
Ya ɗaga waya ya kira muktar yace ya same shi a gida yanzun nan.

Tambayoyi ya dinga ɗan jefowa Alayar tana amsawa da iyakar gaskiyarta akan gidansu da sauransu, duk abinda ta taɓa fadawa Maami haka ta faɗa mishi ba chanji, suna nan zaune sai ga Mukhtar, ba Alaya kaɗai ba hatta maami seda ta shiga tsantsar mamakin ganinshi da wani half jumpa blue yadi me taushi har da hula da ya rufe tsinannen askin kanshi, dama ta san duk duniya mahaifinta kaɗai yake iya yiwa wannan tsoro da ladabi, a hankali ya zauna gaban baban, bayan shiru na sama da mintuna biyu baba yace

"Muktar na raina wayonka, kwarai baka kyauta ba anan ɓangaren dukan macen aurenka kuskure ne babba, Allah be amince da wannan ba ko kusa ko alama, mace da aka sani da rauni Abar a tausaya mata a riritata, a lallaɓa rayuwarta ita ce zaka dinga sakarwa kwanji? Haba Mukhtar! Yanzu da ka kawo ƙara me kake bukata?"

Shiru yayi na seconds kan yace
"a yi haƙuri hakan ba ze sake faruwa ba"

Daga Maami har Alaya ba wai sun yarda da zancen shin bane sbd sanin hali da suka yi, duka wannan ladabin na en wiwi ne
"Ashe baka san hadithin da yake magana akan dukkan shugaba abin tambaya ne akan kiwon da aka bashi ba? Kana tunanin in an ce shugaba ana maganar kawai masu mulki ko sarauta ne? La la la kowani mutum mai kiwo ne akan iyalansa kuma abin tambaya ne, shari'ar musulunci ta tsoratar akan duk wani me take haƙƙin wani ɗan uwansa na kusa ko na nesa kai hatta akan dabbobi bare matarka ta sunna, ka san wanene addinin musulunci ya ƙira da dayyus?"
Kanshi a ƙasa jikinshi ya ɗan yi sanyi ya girgiza kai.
"Wato sakarai, shashasha wadda baya kishin matarsa kwata kwata ya ɗauketa ne kawai a matsayin wacce zata mishi girki ya ci sai in bukatar shi ta tashi ya sauƙe ko kuma yaje yayi ta mu'amala da wasu matayen wannan sharri ne mai girma, domin irin wannan ne yake janyo shaidan ya ci galaba kan matar ko a samu akwai ƙarancin tsoron Allah sai itama ta halaka, ko ka san dayyus basa taɓa shiga aljanna? Ko kamshin ta bazasu ji ba, sahihin hadithi ne ya zo daga manzon Allah cewa mutane uku bazasu shiga aljanna ba an karboshi ne daga Abdullahi dan umar, mutane uku Allah ya haramta musu aljanna wadda ya dawwama yana shan giya har ya mutu..."
Da sauri Alayah ta ɗaga kai ta kalleshi kaman yadda Maami ma da hawaye ya zubo mata take kallonshi, gabaɗaya kaman ruwa ya ci shi haka ya ɗago ya kalli matar tashi da mahaifiyarshi.

Baba da ya kula da irin sanyin da jikinshi yayi ya cigaba
"da kuma mai yawan saɓawa iyaye, sai kuma dayyus wanda baya kishin matarsa wanda yake tabbatar da ɓarna cikin iyalansa..."
Kukan Alayah ne ya fito fili sossai a chan ƙasan ranta take maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun duk hallayyar Muktar ne a cikin nassi ɗaya, taya zata soma haihuwa da muktar da wannan hali? Taya zata iya cigaba da zama dashi alhali be san darajarta ba be san ƙimarta ba bare ya kare mata martaba? Idanunshi da suka sauya ya ɗago ya kalli baba da yake cewa

"idan har ba tuba yayi ya daina dukkan waennan abubuwan da na lissafo ba, tuba na gaskiya da gaskiya tsakanin shi da Allah, Mukhtar kaji tsoron Allah! Ina ƙara nanata maka wannan kaji tsoron Allah a dukkan lamuranka ka tashi ka tafi zan neme ka da kaina"
Baba ya ƙarasa!
Shiru ya sake yi chan dae ya gyaɗa kai, ba tare da ya sake cewa komai ya miƙe ya fice daga parlorn.

"Fatima!" Baba ya kira ta, shesheka take saki a hankali ta riga tayi developing tsanar Mukhtar bata son shi, bata ƙaunar shi, bata jin ko kaɗan zata iya son shi bayan duk abubuwan da yayi mata, bata tausayin shi saboda shine ummul aba'isin duk halin da yake ciki he's responsible for that don bazata ɗaurawa Maami ba mutumiyar kirki!

Cikin muryan kuka ta amsa, gabanta na faɗuwa tana Adu'ar kar ya mata dole zama da Mukhtar a yanzu bata ko ganin ƙimar shi.

"Fatima zaman aure ɗan haƙuri ne..."
Idanunta ta lumshe da sauri ta dafe zuciyarta da yayi wani irin harbawa, zafi da raɗaɗi ya soma bin jikinta, numfashi ya soma yi mata wahalan fita wadda fusgan da take mishi yayi sanadiyar dakatar da Baba ya kuma maida hankalinsu gabaɗaya kan ta.

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment


                     🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Fourteen*

"Binty lafiya kuwa? Ko ciwon zuciyar ne?"
Girgiza kai tayi tana riƙe hannun Maami da kyau, ruwa Maami ta zuba a cup da sauri ta bata ta sha, runtse idanunta ta sake yi da karfi tana sauƙe ajiyar zuciya a jere a jere, baba ya gyara murya kan yace

"sannu Fatima, Allah ya baki lafiya"
Maami ya duba yace
"Faɗimatu ko zaku je asibiti ne?"
Alayah ce ta girgiza kai tace
"ba komai Baba ya sauƙa!"
Ya so su je ta samu ta sha magunguna ta huta amma ta ce babu komai tana sauraran shi hakan ya sa ya cigaba.
"Mace ga mijinta ta kan zama ƙyaure ne ko wani garkuwa wacce ba zata taɓa cimma rabautar aure ba idan bata haɗa da haƙuri da jajircewa ba, dukkan wasu iyaye ko yaya su ke baza su taɓa farin ciki da mutuwar auren ƴar su ba bare wannan da baku rufa watanni biyar ba, sannan ga rabo Allah ya kawo, na san abin da zan kawo zaki iya jinshi ba daaɗi sai de Fatima kaman yadda na ɗauki Mukhtar jinina jika a gareni haka kema na ɗauke ki ba zan taɓa miki dole zama da Mukhtar ba saide ina so ki je kiyi tunani, ki sanyawa zuciyarki natsuwa ki zama mai haƙuri duk da na san yana da matuƙar wahala sai dae fa yana da riba mai tarin yawa, duk yadda ka kai da son abu ko ƙin sa saida amincewar Allah shi kuma yana duba zuciyoyin mu ne wurin yi mana hisabi, idan kin koma ki yawaita tashin dare kina roƙon Allah a kan mijinki, ki fawwalawa Allah lamuranki ki zama mai ƙan ƙan da kai da zubda wa ubangijinmu hawaye, a duk bayan adu'ar ki ki haɗa da
La'ilaha illa lahul azimul halim, La'ilaha illa lahul hakimul karim, La'ilaha illallah, subhallah, Rabbissamawatissaba'i wa rabbul arshil azeem, Alhamdulillahirabbil alameen.
Kaman yadda na faɗa kiyi nazari sossai zan neme ki bayan sati ɗaya"

Godiya sossai ta mishi Dukda ba daaɗi take ji ba a haka suka fice daga gidan, saida suka biya asibiti saboda Maami ta kasa gane mata a take likitan da take gani yayi referring ɗin su to meddy specialist hospital wurin Doctor Philips saboda ya tabbatar musu lamarin ta sai a asibitin za'a iya tackling ko kuma waje, godiya suka mishi daga nan suka yi gida dare yayi sossai so bata wani zama ba ta watsa ruwa ta kwanta, duk yadda ta so bacci ya

Please Login or Register in order to submit comment