Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gasken gaske duk inda kake neman namiji wannan din da Abba ya kira da Mukhtar to ya kai, saide dressing dinshi na three quater da armless shirt ya bayyana munanan halayenshi kaman yadda baƙin lips ɗin shi ya nuna karara hayaƙi na aikinshi a wurin, daga kirjin shi zuwa dantsen hannun shi na dama tatoos ne da aka zana ya zanu sossai kaman kan zaki ko damisa ne oho..

Wani irin tsawa da ya daka mata yasa ta razana tayi baya tana wara kyawawan idanunta
"ba'a yi min shiru in ina magana am I clear?"
Bata amsa ba, hakan ya saka shi Miƙewa a harzuke ya nufeta gadan gadan, a tsorace ta fara ja baya yana kara matsowa har ta isa jikin gini ya matso sossai ya mata rumfa yana kare mata kallo
"young, beautiful and stubborn!" Ya faɗa yana taɓe baki
"ba laifi Dad ya iya zaɓe but kina bukatar sabbin karatuttuka a wannan lunatic brain ɗin"
Ya faɗa yana dannan saitin brain ɗin da hannunshi kauda kanta tayi idanunta suka cicciko, ya sanya hannu ya shafa fuskanta a firgice ta Buge hannun tare da sauke mishi marin da bata taɓa tunanin tana da wannan karfin halin ba, kankame jikinta tayi sbd kusancinsu tana kokarin zamewa ya fusgota tare da fusge hijab ɗin jikinta, ƙara ta saki ya Buge mata baki da gwuiwar hannunshi har saida jini ya fita yana furta...

"Shhhhh" idanunshi kaman garwashi da alama ma wani abun ya sha kan zuwanshi nan ɗin
"Lallai yarinya kin yi kokari, Marin Muktar abu ne da ya kamata a tafa miki, trash like you, villager, wacce ke cike da rashin wayewa yau ke kika sa hannunki a fuskata, fuskar da mata dubu ke marari hmmm marin nan zan fanshe su ta hanyoyi daban daban ki rubuta ki ajiye the First one za ki tantance yanzu, sauran sai kin zo.."

Ko kan tayi wani yunkuri ya sanya hannu ɗaya gaban rigar ta ji kake Kyaaaaat ya farke har farin vest dinta ya bayyana, ihu ta tsala tare da saka iyakar karfinta tana kokuwar kwace kanta sede shi ɗin namiji ne da gaske ko gezau ta kasa motsa shi, kuka da ihu take tana neman ɗauki daga Allah...

Gaban ummi ne ke ta faduwa tun fitan Alaya ɗin ta kasa natsuwa, daga karshe sake aikin da take yi tayi ta nufi sitting room ɗin tana kuma jin gabanta na tsananta faduwa.

Tura kofar da tayi ya ɗan yi karar alamar Shigowar mutum ne ya saka shi dakatawa daga abunda yayi niyya chakk, jajayen lumsassun idanunshi ya ɗago ya kalleta irin kallon zaki yi bayanin nan kan ya ja baya yana gyara wandonshi ya juyo, ita kanta ummin wani irin kallon banza yayi ta aika mata har ya isa daidai inda take kan ya daga hannu yayi mata alamar ta matsa, abunda ta gani ne ya daskarar da ita, idanunta na kan Alaya da ta zube bisa gwiwowinta tana gunjin kuka bata ankara ba taji an tureta an wuce, bata iya riƙe balance dinta ba se ta tafi a haka ta faɗi ƙasa sumammiya....!

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*


#Vote
#comment




🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
     (heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*


*BOOK 1*
*Page six*

A hankali ummin ke buɗe idanunta da suka yi nauyi, zuciyarta na bijiro mata da abin da ya firgitata, da ido ta bi environmemt ɗin sai ta fahimci a asibiti take babu tantama hawan jininta ne ya tashi. Idanunta ta kai gefen ta sai suka faɗa kan Alaya dake dunkule cikin kujera idanunta a lumshe kaman mai bacci duk sun kumbure alamun ba karamin kuka ta ci ba, wani irin tausayin ɗiyar tata ne ya rufe ta, lumshe idanu ta sake yi, ta gama yanke hukuncin amincewa Alhj Hassan da bukatar shi in har dae hakan shi zai sa ya kyale Alaya daga wannan mummunan rayuwar da yake shirin jefa ta, ko a mafarki kai ko a labarin tatsuniya bata fata ace wannan dodo da ta gani da idanunta yana shirin keta haddin ɗiyarta a cikin gidan ubanta ya zama mijin Alaya. Me yasa ta kasa rike amanar Ahmad? Me yasa mutuwa ta mata yankan kauna? Ita kadai babu yadda ta iya da Alhassan, dole abin da yake so din nan shi zata yi...
Kuka ne ya kwace mata wadda ya saka Alaya da dama ba bacci take ba tunani take akan sabuwar ƙaddarar dake shirin riskarta tayi saurin ɗagowa da hannu take mata alamar ta tashi? Ya jikin? Ta dena kuka haka pls.

Har malam Musa ya shigo da zumar tafiya dasu gida sbd likitan da ya fita yanzu ya sallamesu amma kaman yadda aka umurceshi Alhj Hassan ne ya kira ya sanar wa shi kuma ya turo malam Musa ummi bata ce komai ba ta dai bar zubar da hawayen sai azkar da take tayi, duk su biyu bayan su ubangiji ne kadai ya san abin da suke kullawa da warwarewa, suna sauƙa daga motar ummi ta dubi Malam Musa da yake mika mata wani takarda ta karɓa ta buɗe...
"Idan kina da magana ki sameni yanzu a parlor na"
Duban Alaya tayi tare da mata alama akan ta tafi, da kallo Alaya ta bita saide bata saba saɓa maganar mahaifiyarta ba haka ta wuce zuciyarta a kuntace cike da tunanin abin da ummi ke ɓoyewa a gareta sai taji bata ma son ji, kila rashin jin Alkhairin ta ne.
A natse ta tura kofan parlorn ta sanya kai zuciyarta cike da addu'a irin adu'ar nan na fuskantar mummunan abu daga cikin halittar ubangiji wato a'uzubikalimatillahi tammat min sharri ma khalaka, daga tsaye ta tsaya tana kallonshi
"hawwa kina da kafiya da taurin kai!"
Ya mata alama yana taɓe baki.
"Me kake buƙata?"
Sai da ya dara kan yace
"A tambayi kaza hanyar rafi kuwa? Hala kin mance tun ran gini tun ran zane, ba tun yau ba kika kwana da bitar bukatata a gare ki, da Kalma ɗaya tak zaki samar muku Ƴanci"
"idan na amince maka na kuma yi maka duk abin da ka buƙata shine kadai zai sa ka fasa auren da kake shirin kakabawa Ƴa ta na tozarci da rashin galihu?"
"Ko kin amince abu ne mawuyaci a fasa sbd yaro ya gani ya yaba, Marin da ta mishi kuwa daidai yake da ta yankarwa kanta tikiti na rayuwa dashi har abada, abu ɗaya na sani ko da kin amince nayi yadda nayi muka bar maganar auren nan to ɗiyar Ahmad bazata kara minti guda cikin gidana ba! Daga lafiyarta, cin ta, shan ta da karatunta duk sun yanke daga kaina babu abunda zan kara iya yi mata kuma a rayuwa sbd Ahmad be cancanci abubuwan da nake yi mata a yanzu ba.."

"Me Ahmad yayi maka a rayuwa banda hallaci?  Kai butulu ne, kai azzalumi ne Hassan, ba zan taɓa bari ka samu abunda kake so a rayuwa ba zan barka da SON ZUCIYARKA cikin AL'AJAB NA SO kana ji kana gani ba zaka taɓa samun biyan bukatar ka ba in har dae akan SO ne ka aikata duk abunda ka aikata, Allah yana gani kuma ya san komai idan kaga Fatima ta auri wannan mutumi da ka kawo to haka yake rubutacce ne tun fil azal, ba zan iya chanza mata kaddara ba, addu'a kuma shine maganin komai..."
Tana kai nan ta share hawayen dake gangara mata ta juya ta fice.

Hajj Zeenat dake tsaye tana kallonshi yadda gabaɗaya yanayin shi ya sauya Ranshi ya kai kololuwa wurin ɓaci ta san ba komai bane sai danganta Ahmad dashi da Hawwa tayi har tana ikirarin cewa Ahmad ya fishi daraja da komai a idanunta, taɓe baki tayi ganin yadda ya wuce har yana buga kofa tace a fili
"Kanku aje ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya yace kanku aje ji ni wankana nake"

Ko da ummi ta dawo bata iya tayiwa Alaya magana ba, kaman Alaya ta shiga ran ummi ta yagi fallen takarda daga takardar ta sbd so take ummin ta fahimci maganar daga zuciyarta yake rubutu tayi me ɗan tsawo kan ta ajiye mata ta tashi ta fice daga ɗakin.

"Hawayen uwa abu ne me zafi da daraja a idanun ƴaƴa, ummi karki sake zubar da hawayenki akan wannan matsalar kin manta ke kika ce min Aljanna ana kewaye ta ne da abunda rai baya so yayinda ake kewaye wuta da abunda zuciya take so? Ko a makaranta an koyar dani cewa a cikin suratul baqarah Allah yana cewa zai kasance kuna matukar son abu sai ya kasance sharri a gare ku yayinda zai zamana kuna matukar ƙin abu sai ya zama shine alkhairinku, Allah shine mafi sani amma da na zurfafa tunani sai na ji ina da bukatar wannan aure watakila shi zai yi sanadin Chanza rayuwarmu, ba zan kara tambayar ki abin da baki so na sani ba na san in lokaci yayi zan sani, Don Allah karki sake yunkurin dakatar da Abban Jameelah akan auren nan idan har cutarwa yake nufinki dashi!"
gabaɗaya hawayen Ummi ya gama jike takardar, kowace uwa bazata so jefa yarta cikin rayuwar da tafi wadda suke ciki ba amma ta san Hassan shu'umi ne zai iya anfani da wannan dama ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan ko ta amince da kudurinshi sai ya san hanyar da ya bi ya muzgunawa Alaya saboda ita ɗin ɗiyar Ahmad ce.

Haka suka kwana cikin wannan damuwa amma Alhamdulillah da yake sun fawallawa Allah sai suka tashi wasai da safe kaman basu da wata damuwa ayyukansu suka kama kaman yadda suka saba...

****

Kishingide yake hannunshi rike da shisha Pen yana zuƙa sa'i da lokaci, ɗayar hannun nashi kuwa a kumatunshi daidai inda ta mareshi in ya shafa sai ya saki murmushi yana kallon fuskar yarinyar, Red eyes ɗin shi suka sake rinewa yana wassafa yanayin ƙirar jikinta yadda in tayi motsi komai nata yake girgiza, Allah ya zuba ƙira gata yarinya ƙarama, wannan in har ya same ta lallai yayi zarra cikin abokanshi, kaman yadda yake piya-piya a duk inda ya shiga baya jituwa da kananun kwari sai masu kumbar susa haka a aure ma, dole ne ya gayyaci duk wadda ya san zai iya gayyata ya nuna musu ya ƙere kowa...
"bala'i! This gurl is morethan beautiful.."
Gani yayi ba zai iya jira a dau lokaci ba hakan ya sashi Miƙewa daga kan sofa na rantsatsiyar club ɗin as usual sanye da kananun kaya three quater da shirt da bashi da maraba da vest, fitowa yayi cikin takunshi na nuna isa da jiji da kai wadda ze tabbatar maka da lallai shi wani ne ya isa ga motar shi ya shige tare da bata wuta yayi gida.

Kaman yadda ya fita daga club ɗin haka ya shiga cikin parlorn sai de idanunshi da suka sauka kan mahaifiyarsu ne yasa ya ɗan seta kanshi..
"Sannu da gida Maami"
Girgiza kai tayi tana kare mishi kallo ba tare da ta amsa ba, ze wuce tace
"Mukhtar"
Juyowa yayi ya dawo ya samu kujera ya zauna nesa da ita
"wani magana ne nake ji daga bakin mahaifinka?"
"Wai zancen aure? Na je na ga yarinya kuma na yaba ni yanzu ma so nake ko gobe ne tunda juma'a ne a ɗaura kawai"
"ban gane a ɗaura gobe ba! Ƴar tsana ce? Ba ma maganan nan ba me kayiwa ƴar mutane da har zata mareka a cikin gidansu?"

"Maami yarinyar nan fa dakikiya ƴar talakawa ce da alama kaskantacciya ce ko wayewa bata yi ba, daga in ɗan shafa fuskarta don tana da kyau da ɗaukar idanu shine fa"
Tana girgiza kai cikin takaici tace
"ba kawai bane, ta san girman mahaliccinta ne tana kuma tsoron fushinshi tana kiyaye azabarshi, innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Wace ɗiyar mutunci ce zaku sa cikin bala'i da uku?"
Yanayin fuskanshi ne gabaɗaya ya sauya ya miƙe yana yiwa mahaifiyar tashi wani kallo dama ya riga ya san ba son shi take ba, ba kuma ƙaunar shi take ba, mahaifinshi kawai ke son shi
"Maami yanzu aurena ne bala'i da uku? Dama na san ba zaki taɓa farin ciki da cigaba na ba Maami ba ni kike so ba, wadda kike so yana chan yana aikin da kike ganin yafi na kowa a duniya, ni dae Allah na gani ba don kamanni ba kai tsaye zan iya cewa ke yaddikona ce...!"
Miƙewar da tayi yasa yayi shiru tare da komawa baya sbd ya mata farin sani bata sake mishi sam, be kuma gameta yace ze faɗa mata wani abu ta tsinka mishi mari ba don ba yau suka fara ba
"Ina maimaita maka wallahi Mukhtar kaji tsoron Allah ka sani komai zaka yi mai sauki ne da raina nin da kake, uwa nake a gareka baka isa ka faɗamin duk abunda ya ke bakinka in zuba maka ido ina kallonka ba don ba kai ka haife ni ba.."

"Toh fa, waye ya taɓo rina uwar faɗa.."
"Abba kaima ka sani in kana jin Muryar Maami a sama da ni ne ai Umar ba haka ake mai ba"
Cikin takaici take kallon uba da ɗan, ta rasa Meyasa suke kunsa mata bakin ciki, Abbansun nan ya so muktar har ya wuce misali duk abin da zata yiwa muktar tun yana ɗan karamin shi gani yake ƙi ne har yaron nan ya zo ya kangare, abun takaici kuma har yanzu basu ganin abin da suke aikatawa ba daidai bane, runtse idanu tayi cike da tausayin wannan yarinya da ake shirin jefa ta cikin ka-ƙani-kayi tana ji sadda Mukhtar ya bijirowa da uban nashi shi gobe yake so a ɗaura mishi aure wadda ya zo ya zo, wadda be zo ba duk damuwar su a take mahaifin nasu ya amince akan zai ƙira Alhj Hassan yaji yadda za'a yi shi dae ya kwantar da hankalinshi.

***

A natse ta sanya kafafunta ƙasa ta sauƙa daga cikin motar bayan driver ya buɗe mata kofar, karewa gidan kallo take tana nazari, gidan dae ya fi ƙarfin irin wannan aure da ake shirin aiwatarwa a gobe, tafiya take tana ɗan kalle kalle ko zata hadu da wani ko wata ta nemi iso, chan ta hango wata farar kyakyawar yarinya tana tafiya ne kawai amma daga dukkan alamu hankalinta yayi nisan kiwo, idan ta kula da kyau ma kaman yarinyar na sa yatsa sa'i sa'i tana dauke kwallah, sam yarinyar bata kula ba har seda tayi karo da ita kan tayi mugun komawa baya a firgice idanunta da suke fari tas a waje gabaɗaya.

Alaya kam ita ta zata irin cikin kawayen hajj Zeenat ne yanzu su juye abu su ci musu mutunci, a tsorace ta zube ƙasa tana baiwa hajiyar da kai tsaye ta saka ta a top class hajiyoyi masu naira da isa haƙuri, bata taɓa ganin irin ta cikin ƙawayen hajj Zeenat ba don duk yadda zata misalta kyau da haiba irin na wannan mata me cike da annuri ba zai misaltu ba.

Hannu ta sanya ta ɗago ta
"Babu komai ai baki kula bane, yi min iso zuwa ciki ban taɓa shigowa gidan ba sai yau"
Matar sam bata da girman kai irin na manyan masu kuɗi ɗin nan Alaya ta ayyana a ranta kan ta shige gaba Maami ta bi bayanta har cikin parlor, bata je kiran Hajiya ba seda ta kawo mata ruwa da ɗan abun motsa baki kan ta shiga wurin hajiyar ta jima a tsaye kan ta amsa mata ta dawo ta shige kitchen ta cigaba da aikin da take kan a kira sallah ta saki taje tayi.

Cikin ƙasaita Hajiya ta fito Dukda ganin wannan gansamemiyar hajiyar ta san ba irin wacce za'a dagawa kai bane hakan be sa ta saita kanta ba ta samu wuri ta zauna a hakimce tana lura da kyau da kayan alatun dake jikin matar.
"Sannu da zuwa"

"yauwa Hajiya, kece mahaifiyar yarinyar da Abban muktar ya nemarwa aure?"

Daidai Alayah ta fito don tambayar hajiyar abinda ta ce za'a ƙara bayan na time table yau.
Idanu duka ta fitar kaman an danganta ta da wani mummunan abu tace
"Allah ya tsare ni da haihuwar mugun iri, kin ganta chan sai ta dangana ki da kurmar uwarta tunda dae kun ji kun gani, a sauƙa lafiya in kin tashi!"
Tana kai nan ta fice daga parlorn babu ko waiwaye, da farko jin irin gidan da za'a aurar da Alayah ta so ya haɗasu da jamila ne saide jin irin hallayyar yaron tayi tirrr da aurenshi, don a ganinta bashi da wani anfani, ko da uban ya faɗi ya mutu ko uwar dukiyar da zai gada bazasu je ko ina ba zasu ƙare a shaye shaye da bin mata, bata Gaza ba wurin tabbatarwa da Abban jameelar cewa in har dae suna da wani ɗan natsatse sai yayi kokari wurin ganin ya haɗa jamila da shi, be dae tanka ba amma ta san zai yi nazari akan hakan.

A chan parlor kuwa, idanu mami ta zubawa Alayah da kanta ke ƙasa cike da kunyar matar sai a lokacin ma ta fahimci kamanni dake tsakaninsu da muktar din, amma me ya kawota?

"Daughter ko zaki iya rakani wurin mamanki?"
Ta tsinci Muryar hajiyar, da sauri ta ɗaga ta kalleta sai matar ta sakar mata kyakyawar murmushi, itama kakalowa tayi ta mayar mata kan tace cikin sanyin muryarta
"Toh Hajiya mu je"
Miƙewa Maami tayi ta bi bayanta har sashensu, da ɗan mamaki take kallon yanayin parlorn, kujerun da suka gama tsofewa duk dollof ɗin su waje Alaya ta nuna mata
"bismillah bari na kira ta"
Tana kai nan ta nufi kofa guda ɗaya dake sashen ta bar Maami da tsananin al'ajabi...

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment



                  🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page seven*

Cikin tsananin tausayi da mamaki take kallon sashen nasu sai de tayi matukar kokari wurin boye yanayinta har ta kai zaune tana ɗan kallon kofan ɗakin da Alaya ta shiga, bata fi minti ɗaya ba sai gata da matar da bata bambance dayan biyu mahaifiyarta ce sbd kamanni Dukda Alaya ta zarta ta kyau nesa ba kusa ba.

A hankali Alaya tace
"Hajiya bazata iya jin ki ba"

Tsananin tausayinsu ne ya kara rufe Maami tace
"Sunana Maami bana so ki sake ce min Hajiya, tana iya karatu?"
Kai Alaya ta gyaɗa.
Jaka Hajiya binta ta buɗe ta fiddo joter da biro tayi rubutu kan ta mikawa Ummi da biro ɗin, ummi da yanayin matar ya kwanta mata ta karɓa ta karanta cikin tsananin mamaki ta sake ɗaga idanu ta kalli Maami sai yanzu take iya hangen kamannin, tattaunawa mai ɗan tsawo suka yi a rubuce, duk yadda Maami taso ummi ta nuna kirkiri bata son haɗin hakan bai samu ba sai ma bi da tayi ta wata siga irin ta mai hankali da sanin addini wadda hakan ya mugun yiwa Maami daaɗi, taji matukar daaɗin kasancewa dasu daga karshe ta fara jefawa Alaya tambayoyi yawanci akan karatunta ne kan tayi mata alkawari ko ta auri muktar karatun ba zai tsaya ba wadda hakan yayi mugun sata farin ciki tayi ta godiya, su ko cikin kunyar ko ruwan da zasu bata babu Alaya ta fara bata hakuri tayi saurin nuna ba komai da ta tashi tafiya kudi masu yawa ta fiddo ta ajiye duk yadda ummi taso ta bari ta ƙi haka ta tafi cike da tausayin waennan rayuka biyu da Allah ya tsirga mata.

RANAR JUMA'A

Tunda gari ya waye gaban ummi ke aikin faɗuwa sbd Maami ta faɗa mata a yau ne suka yanke za'a ɗaura auren, ta kwana kan sallaya ta kwana tana kaiwa Allah kukanta, da safen kuwa lokaci lokaci ta kan share hawaye, ba irin tunanin da bata yi ba idan har suka tsallake suka bar gidan nan shikenan tayi sallama da Ahmad da komai nashi, idan suka bar gidan saide su koma kaman sauran Abzinawa masu bara a titunan Nigeria, bata da wadda zata komawa a yanzu bata da kowa da zai iya rungumarta a wannan yanayi.

Aiki take saide lokaci lokaci ta kan ɗaga idanu ta kalli Alaya hawaye na zuba a idanunta, daidai sadda Abban Jameelah ya shigo da karfi ya jefa mata ledar hannunshi wadda yayi sanadiyar watsewar alawa da goro dake ciki, a firgice Alaya ta miƙe tsaye tana kallonsu yayinda ummi ta runtse idanunta daidai lokacin da Abban ke cewa Alaya
"Ga Alawar aurenki an ɗaura yau kuma ki shirya da dare zaki bar min gida, nayi matukar jinjinawa kokarin da nayi akan ki alhalin ke ɗin ɗiyar wadda ban taɓa so bane a rayuwata, ke ɗin ɗiya ce da mahaifinki bai taɓa ƙaunata ba, duk wani dama da ya ga zan samu ya kan yi hanzarin sha min gaba ya karɓe hatta kaunar iyayena bai barni da shi ba! Ki sani daga sadda kika fita daga gidan nan ko da sunan ziyara bana kaunar sake ganinki cikinta bare ki kashe aure ki dawo min, in kin fita duk abin da zai same ki ya kare a chan don Wallahi kika shigo min gida duk ya faru dake kiyi kuka da kanki"

Razananniyar kukan da take ta yanke daga karshe tana kallonshi irin kallon da bata taɓa tsayuwa tayi mishi ba, kalamanshi ba abunda zata iya aiwatarwa ba ne taya yana tunanin zata tafi ta ƙi juya baya alhali ta san ta bar mahaifiyarta cikin wannan gida?
"Alhaji mahaifiyata fa? Da kake wannan magana taya zan rayu cikin kwanciyar hankali in kasa waiwayen gidan nan alhali ka san duniyata na cikinta?"

"Wannan kuma ke ya shafa Fatima, abunda na sani mahaifiyarki kamar mallaki na ce babu inda zata kuma ban amince ki shigo min gida ba and this is my final decision"
Daga haka ya fice.

Zubewa tayi akan tile ɗin kitchen din tare da ɗaura hannu a kai tana me sakin sabon kuka, da sauri ummi tazo ta ɗaga ta tare da sanya ta jikinta tana jin yadda jikinta ke ɗaukan rawa kuka take kaman ranta zai fita, bata san me tayiwa wannan rayuwa ba, shin ummi bazata faɗa mata abin da mahaifinta yayi mai zafi haka ba?

Da kyar ummi ta samu hankalinta ya ɗan kwanta Dukda bata bar zubar kwallar ba, idanunta gabaɗaya sun sauya haka numfashinta da zafi zafi yake fita, wani mumman zazzabi da ciwon kirji ya kwantar da ita haka ummi ta saka ta a gaba tana zub da hawaye babu mai taimako, Dukda ta sha duk magungunanta saide hakan be kwantar da ciwon da ya fara barazanar ganin karshenta ba, addu'a ummi ta dinga yi har Allah yasa bacci ya ɗauketa na wahala.

Haka ta koma cikin gidan ta ƙarasa aikin da suka bari ta dawo ta zauna jugum tana tunanin rayuwa, Dukda ta kasance marar gata irin Alaya saide aurenta bai zo a haka ba, aurenta da rufin asiri da kuma taron mutane aka yi shi, sallah ne kawai ke dagata har dab magarib kan Alaya ta farka, da taimakon Ummin tayi wanka ta sake shan magunguna abinci kam ya kasa shiga cikinta, a kwance kan cinyar ummin ta lumshe idanu bayan ta idar da sallolin da aka biyo ta ta fara jin Shigowar motoci da ƴar hayaniya kaɗan na mutane.

Bata motsa ba har aka yi musu sallama, da gangan ta ƙi amsawa kila in bata amsa ba su juya su koma inda suka fito a yau me rabata da ummi kilan sai mutuwa bare in ta tuna irin furucin Abban Jameelah a kanta, Shigowar Maami ne ya sa Ummi sakin ɗan murmushi bayanta mata ne akallah zasu yi ashirin.

Danginta ne kadan sai

Please Login or Register in order to submit comment