Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

AL'AJABIN SO
     (heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO... Paid*

*BOOK 1*
*Page 1*

SHIMFIƊA
Tarihi yana nuna mana abubuwan da suka faru ne kafin mu a rayuwa!
Rayuwar duniyar cike take da kalubale, haɗari, wahalhalu da musibu daban-daban, kusan in ka ga ka gujewa hakan to fa alƙalamin ƙaddara bata zana maka ita a shafin ƙaddararka ba, a lokacin da kaddara ke wasa da rayuwarka ya rage maka ɗaukan wannan kalubale a matsayin darasi, ka kuma yi haƙuri da jarabawar Allah (S.W.T) a gare ka.
Ni Fatima ban taɓa sanin cewa igiyar ƙaddarar wani na iya shafan na wani har su sarƙe wurin zama abu guda ba sai da na tsinci kaina cikin alkaba'in rayuwa, zafi da kunci suka yawaita a gareni, farin ciki yayi min nisa irin tazarar dake tsakanin sama da ƙasa, na kasa tantance wai ƙaddarar wanene ya shafe ni, shin na mahaifiyata ne ko na mahaifina? Ko kuma nawa ne ni a karan kaina ba'a tsaga ni cikin masu rabauta da duniya ba?
A mafi yawancin lokuta in har nayi irin wannan tunani, na kan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sa mana wani tabbataccen al'amari ba, farin ciki ko baƙin ciki yana da lokaci, komai kuma yayi farko to fa yana da karshe, wani karin maganar ma sai ya ce abinda ya baka tsoro a yau babu shakka ko tantama a gobe ya iya baka tausayi, rayuwar tamkar tafiyar hawainiya ce tana tafe tana chanza launi.

Al'amuran da suka faru a rayuwata sun sanya min karsashin bayar da labarina.

*****

Cikin matsakaicin speed motar ta shigo kayatacciyar harabar gidan, a natse take ratsa duk wasu shukoki da parking lots masu tsari da suka yi wa harabar kawanya zuwa ainihin kofar mashigar babban parlorn gidan kan ta dakata.

Da hanzari kuma cikin sauri wata farar matsakaiciyar budurwa sanye da kayan dake nuni da cewa daga makaranta take don baƙar skirt ne jikin ta wadda iyakacinsa gwiwarta sai farar shirt da baƙar blazer ta ɗaura jan necktie daga wuyanta, farar doguwar safa ce a ƙasan baƙaken sau cikin ta wadda ya shiga har karkashin skirt din na jikinta, a kanta baƙar hula ce wadda ya rufe mata gashi tsab kan ta ɗaura baret dinta a karkace daga sama hakan sai ya baiwa kyakyawar fuskarta daman haskawa da kyau, a hankali ta taka zuwa seat na baya ta sanya tsiraran hannunta ta buɗe kofar.

Wata buduruwar ce again da zasu iya yin sa'anni sanye da irin uniform din wacce ta bude kofar sak ta fito, da mugun kallo ta fara bin wacce ta buɗe kofar kan ta ja doguwar tsaki ta hankaɗeta ta wuce.
Cikin sauri ta dafe motar don gujewa kaiwa ƙasa a kuma sanyi irin tata na tsantsar natsuwa da zaka hanga daga gareta ta ɗago kyawawan idanunta da suka cika tab da kwalla sbd a makaranta ita da friends dinta yau ba karamin mutunci suka ci mata ba, haka gun shiga mota saida ta zagi iyayenta kaman yadda suka saba sanin cewa hakan ne abun da ke ci mata zuciya yake kuma ƙona ranta a take sossai, gashi yanzu m...

"Alayah...!"
Firgigit ta maida idanunta kan drivern da ya ɗauko su ɗin ta amsa da
"na'am baba Musa"

Ya ce
"kin mance jakar karatun taki ai yarinyar kirki"

Murmushinta me kyau ta sakar masa tare da komawa inda ta fito ta buɗe ta duƙa ta dauki jakar tata ta rataye daga kafaɗarta guda tace
"Na gode baba, bari na shiga ciki, a huta gajiya"

Da murmushi ya bi ta har ta ɓace ta wani tsiririn hanya saɓanin wadda waccan yarinyar ta shige, sarai ya ga abin da ya faru ya kuma san ba mance jakar tayi ba sauri kawai take ta buɗewa Meelah kofa kar tayi laifi se gashi bata tsira ba.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da furta
"Allah ya kyauta ya rufa mana asiri" daga haka be kara ba ya shiga motar ya kai ta ma'ajiyarta kan ya wuce bakin gate wurin hirarsu.

Alayah kuwa saida tayi ɗan tafiya mai ɗan nisa kan ta isa ɗan wani karamin sashe a natse ta hau varender ɗin ta isa kofar tare da turawa bakin ta ɗauke da sallama duk da ta san babu me amsa mata, ta san anfanin hakan ne sbd an sha karantar da su cewa sallama a wuri kaman dole ce musamman in zaka shiga gida ko da babu wadda zai amsa a zahiri mala'iku zasu amsa kuma zaka samu ladar hakan.

Idanunta take warawa tana neman hasken rayuwarta, majinginar ta kuma sanyin idaniyarta, ganin bata parlorn yasa tayi hanzarin nufar kofa kwalli ɗaya da sashen dake yanayi da kango wadda bazaka taɓa kawowa akwai irin wannan sashe a cikin tamfatsetsen gidan daga waje ba ke dashi.

Tana sa kai idanunta suka sauka kan abinda take nema kayatacciyar murmushi suka sakarwa juna, kyakyawar farar macece wacce bazata haura 40yrs ba mai tsananin kyau da cikar kamala kai tsaye zaka iya kiran ta da mahaifiyar wannan buduruwar da aka kira da Alaya sbd fusgan kama da suke yi.

Da hannu matar tayi mata alama da
"kin dawo?"

Murmushi cike da fuskarta wadda bazaka taɓa ganin ta dashi a wani wajen ba face nan cikin kangon nasu ta amsa da kai tana alama irin ta maganar kurame
"eh ummi na dawo, ya gida?"

Ba tare da ta tsaya sake jiran maganan ummin ba ta sake yi mata alama bakin ta na furta wa a hankali tace
"Ummi bari nayi sauri na watsa ruwa na shiga cikin gida kar nayi laifi wurin mommy"

Kai kawai ummin tata ta gyaɗa kan ta bita da ido har ta shiga bayin nasu, saida ta fara wanke uniform din nata ta shanya sbd bata da tabbacin samun lokacin kanta in har bata yi a yanzun ba kan ta watsa ruwan cikin hanzari, ta ɗaura alwala a bakin famfon da banda shi da matsuguni (squats) babu abunda aka bar musu a bayin na more rayuwa.

Dukda hanzari take amma hakan Sam baya nunawa sbd sanyin ɗabi'a da natsuwa a jinin ta yake kaman gado ne tayi daga iyayenta duk su biyun, da kallo ummi ke bin ta har ta shafa mai ta nufi Ghana must go ɗin su da bayan katifa da sallaya se bakko guda biyun babu komai cikin ɗakin.

Sallar azahar ta tayar wadda ta ja lokaci a cikinshi sossai tana sallamewa landline dake parlorn na ɗaukan ƙara har tuntuɓe ta ci garin saurin isa parlorn ta ɗaga kar ta kara laifi, sallama tayi a ɗarare gabanta na faɗuwa don ta tabbatar a kap rayuwarta bata taɓa ɗaga kiran alheri daga mutanen gidan ba.

Ba tare da an amsa daga ɗaya ɓangaren ba aka soma magana cikin faɗa
"Ke! Wato tsabar kin cika cikakkiya wani sabon rashin kunyar da kika tsiro dashi yanzu kullum kuka dawo makaranta se na buga na nemoki kan ki zo ki kama min ayyuka? To na rantse da Allah yau ne na karshe daga wannan an gama! in kin ga dama karki zo kin san kan wacce zan sauke iskancin naki...."

Kit aka tsinke wayar, a hankali ta kai ta ajiye zuciyar ta Sam babu daaɗi, damuwa da gajiya na neman fin karfinta dama already sun fi karfin shekarunta ga raunin zuciyarta, a haka ta tashi ta samesu cikin wannan tsanani, a haka ta girma cikin bauta, hantara da zagi wadda bata san farkonshi ba bare karshen shi.

Sau tari se tayi yunkurin yi wa ummintata magana akan wannan rayuwa da suke ciki se taji tausayinta ya danne mata zuciya, bata san daga ina matsalar take ba. Shin ummin tata bata da kowa ne bayan waennan azzaluman mutanen? Me yasa tun tashinta ummin kawai ta sani matsayin uwa, uba da danginta? Babu wadda zai so dawwama cikin ukuba bare ma irin nasun nan, bata da me bata amsa hakan ysa take iya kokarinta wurin taya ummin tata da addu'a kaman yadda ita karan kanta bata gajiya ba a neman mafita daga  mai kowa mai komai.

Dafata da aka yi yasa ta ɗago tana kokarin maida kwallar da suka cika mata idanu..

"Kin gaji ko? Ko bakya jin daaɗi ne? Ki je ki kwanta bari naje Naji abinda zaki yi ɗin se nayi"
Ummin tata tayi mata alama da hannu wadda tsab take fahimtarta sbd Kusan shi ne First language da ta fara koya a rayuwarta don har so yayi yayi affecing mind ɗin ta sai ta ga kaman magana da fatar baki ciwo ne a sadda tana yarinya karama.

Da sauri ta girgiza kai tare da riƙe hannun ummin tace
"Ummi da ina da dama da iko da ba zan taɓa bari ki je inda suke ko su kusanceki ba, ummi na fi jin zafi da ciwo a zuciyata idan naga suna ci miki mutunci suna jifanki da munanan kalamai fiye da abinda ni zasu yi min"

Siririn hawaye ya gangaro mata ummin ta sa hannu ta share, ta ɗaga ido ta sanya cikin nata Dukda rauni da damuwa da suka bayyana mata sossai hakan be hanata sakarwa ummin tata murmushi mai ƙayatarwa ba tace
"Ummi zan je kar na kara yin wani laifi"

Sake mata alama da hannu ummin tayi
"kin tabbatar kina dai lafiya ko?"
Cikin murmushi tace
"lafiya ƙalau ummi"
Daga haka ta juya ta fice murmushin kan fuskanta na disashewa.

Da kallo ummin ta bi ta har ta ɓace mata, da sallama ta tura kofar tamfatsetsen tsararraren parlorn da ya haɗu ya kuma gaji da haɗuwa, a share yake a kuma tsabtace kal kal kaman ka lashe tsabar kyau da walwalin da abubuwan ciki ke yi wadda duk aikin umminta ne tsabtar duk wani muhalli na gidan, wani corridor da shima ba'a bar shi a baya ba wurin kyale kyale da kwayayen fitilu masu kyau aka ƙawatar da cikinshi, akwai kofa guda ɗaya kitchen ne a hade da katon store kofar wurin dining shi suka fi bi nan ɗin na shigar masu gidan ne.

Daga chan karshe ta buɗe wani kofa da ya sada ta da wani babban parlor wadda na matar gidan ne mommy kenan, kaman wanchan shima a share kuma a tsabtace yaji kujerun alfarma ga sanyi da raɓar Ac.

A cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun ta samu mommy zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana sanye da wani ɗan ubansun lace na manyan mata taji adon gwala-gwalai hannaye da wuya, hannunta rike da waya kirar Samsung wadda ake cewa Fold tana latsawa, a kan gwiwowinta Alaya ta zube tace...

"Mommy sannu da gida"

Kaman ba da ita take ba, kaman ma bata san da zaman mutum a wurin ba saida ta bushi iska don kanta bayan kafafun Alayah sun fara tsami a tsugune kan ta ce

"wato ke don uwaki tsabar kwakwalwar kanki a toshe yake kaman yadda kunnuwar uwarki kurma suke a doɗe Sau nawa zan faɗa miki in sake nanata miki karki sake ki haura mintuna talatin daga dawowarku daga makaranta zuwa ganin ki a parlorn nan?"

Kanta a ƙasa idanunta cike da kwallah saide bata bari sun zuba ba tace
"kiyi hakuri mommy sallah na tsaya yi"

"ke a gidan uban wa na zama mommyn naki? Ban ce ki dinga kirana Hajiya ba? Ko kin ga nayi kala da uwarki? Sunnu limamiyar Makka! Tukuna ma me ya hanaki wankewa jameelah bayi yau da har ta kasa shiga bayan ta dawo daga makaranta sai na ɗakina taje ta shiga tayi wanka?"

Bata ɗago ba a duniya babu fuskar da bata ƙaunar gani irin ta Hajiya Zeenat sai taga kaman idan ta kalleta zafin da zata ji daga zagi da cin mutuncin sai ya fi wadda take ji idan bata kallon ta.

"Kiyi haƙuri Hajiya makara muka yi"
Maimaicin abun da ta riga ta sani ne tunda tana hakimce Meelah na kwance kan cinyarta da safen ta kawo mata noodles and egg da shi ɗin tace ta dafa mata, bayan ta kawo kuma ta chanza zuciyarta chips da cripsy drumsticks guda biyar take so babu yadda ta iya ta koma ta sake farawa hakan ya makarar da ita sossai, kuma ta san idan ta kuskura ta saka Meelahn letti har aka taɓa ta a school Se Umminta ta mata gashin ruwan zafi sbd mahaifinta baya tolerating duk abunda ya shafi Jameelar.

"Ki wuce kije ki wanke mata bayi, ki chanza mata beddings don ta ce ƙaiƙayi suke mata ki tattara laundry ɗin ta ki je ki wanke sannan ki zo ki ɗaura dinner don kurma ta riga ta ceceki tayi na rana ita me ƴa"

Cikin ladabi ta amsa da
"Toh Hajiya"

Mikewa tayi ta nufi kofan hagu daga cikin parlorn shima yana da karamin parlor da dakuna biyu na hagu ta sake isa ta yi sallama, ba amsa, ta sake yi Dukda ta san Meelahn na jin ta amsawa ne bata yi niyyar yi ba, in kuma ta ƙusa kai ba izini ma wani maganan ne.

A na huɗun ne ta riski wani tsawa...
"Ke Dallah Muguwa kawai! Kin dameni da wani shegen murya kaman Drum so kike se kin kurmantar min da kunne kin maida ni kamar kurmar tsohuwarki ne ko kuma me? Mtseeew"

Ba tare da tace komai ba ta buɗe kofar ta shiga, ko kurmar ne da take faɗa ta tabbatar ta shafa muryarta ta shafa na Jameelah ta san ta fita zaƙi da taushin murya nesa ba kusa ba.

Tana zaune cikin ɗaya daga cikin kujeru guda biyu dake ɗakin hannunta rike da waya tana latsawa haka kunnuwanta sake da babban baby pink headphone saide bata tunanin tana using ganin baya haske, ba tare da tayi kwakwaran kwaraniya ba ta wuce toilet ɗin ta wanke shi tsab bayan ta gama ta dawo ɗakin bata sameta ba hakan ya sa ta fara cire zannuwan gadon ta chanza wani tare da gyare ɗakin tayi mopping da goge goge, hannunta dauke da kayan cikin laundry basket ɗin Meelahn ta fice zuwa chan baya inda suke wanki.

Bayan ta zube su ta koma kitchen bayan store akwai wani karamin laundry room dauke da abubuwan shanya, washing mashings da sabulai da omo kala kala wasu a goruna wasu a ledoji, zaɓar waenda ake yi wa Jameelar wanki dasu tayi ta koma ta hau wanki, ta jima sossai tana yi sbd kayan da ɗan yawa saukinta ma babu wani datti sbd sawar mugunta ce sai a sa kaya kala uku huɗu a rana, tana gama sanyawa ta tsuguna a wurin riƙe da kanta dake sarawa, bayanta kaman ta cire ta ajiye sbd yadda yake yi mata wani irin ciwo, hawaye masu zafi ne suka zubo mata tana jan numfashi da kyar ta sa hannu ta goge, ta jima haka kan ta miƙe ta nufi kitchen wanke wanke ta fara na kwanukan rana da aka ɓata bayan ta gama ta goge ta shanya kan ta matsa ta duba time table na abinda zata yi na dare.

Miyar ganda ce ta kan Sa sai tuwon shinkafa, fiddo naman kan tayi daga freezer ta sa a pressure pot ta zuba mishi ruwa me yawa ta ɗaura kan hot plate tare da kunnawa, chan gefe inda ta ga kular abincin su ta nufa ta ɗauka dama ta riga ta san ba daga tukunya yake ba wadda suka rage ne suka juye musu a kular da ya kasance nasu, sashensu ta koma ta samu umminta ta idar da Sallar la'asar kenan, zama tayi gefen ta cikin tsantsar gajiya ganin zaman baze yiwu ba ta zame ta kwanta a wurin tare da lumshe idanunta da suka fi yanayi da na Larabawa farare sol mai ɗauke da baƙi sidik ɗin kwayar ciki, zara zaran gashin har ya sauka fuskanta don tsawo da kyaun su.

zuciyarta a chunkushe ta gaji iya gajiya da irin rayuwar da ta tashi ta same su da mahaifiyarta a kai, wasu kan ce abunda ka saba yau da kullum ya kan shiga jiki ya zame maka jini saide kai bata tunanin ana iya yin sabo da wahala, a hankali ta buɗe idanunta jin saukar hannun ummin ta bisa goshinta ta zubawa ummin idanu, banda rama da tsantsar damuwa babu abunda take karanta daga ummin tata.

Murmushinta me kyau ta sakarwa ummi ko kusa ita karan kanta bata Fatan tashin ciwon ta don ta san ummin zata bari da wahala da kuma damuwa, cikin yatsina fuska ta miƙe zaune ta fara yi wa ummin tata magana

"Ummi lafiya ta fa ƙalau na ga kina ta damuwa"
Ummin tana mata kallon tuhuma itama tace
"Ai na daena yarda da maganarki in har dae akan ciwon ki ne, sau nawa zaki ce hakan bayan kina nan kina shan wahala?"

Murmushi ta saki sossai har saida fararen hakwaranta dake jere reras zuwa dimples ɗin ta guda biyu suka bayyana.

"Ai ba wai ƙarya ba ce ummi bana so hankalinki ya dinga tashi ne" tana kai nan ta janyo kular abincin tana yi wa ummi alama da

"wallahi Sallar nan ba zan iya yinshi ba matukar banji sauƙar abu cikin ƴar hanji na ba, yunwa nake ji kaman in ci babu".

Murmushi kawai me cike da ma'anoni daban daban ummin da suke tsananin kama da Alayar sai en abu kalilan da bata ɗauko nata ba ta saki kan tayi mata alamar a ci dae da bismillah, inaaa ita kam tayi nisa a cin abincin ta, tunda take a duniya bata taɓa jin abincin da ya kai na umminta daaɗi ba, lokuta dayawa ta kan tambaye ta wai wani makarantar koyon girkin tayi? Lura da ta yi tambayar kan taɓo mata wani fanni chan na rayuwarta yasa ta daena.

Sai da ta fara kai wa geji kan ta lura da ummin tata bata ma soma ci ba, da sauri ta dakata tare da ɗago idanunta farare sol ta dubi ummin da tayi nisa da kallon ta fuskanta dauke da murmushi sannan hawaye na zuba mata daga saman fuskanta.

"Ummi.." Ta faɗa tana sa hannu ta taɓa kafafunta.
Da sauri ta ɗauke kai tana share hawayen wadda nan take Alaya taji abincin ya fice mata daga rai, ba karamin So da shakuwa ne ke tsakanin su ba ko don basu da kowa ne sai junansu oho, amma abunda ta sani yanayin ɗaya baya chanzawa ba tare da ya taɓa na ɗayar ba.

"Ummi menene?" Ta tambaya cikin tsantsar damuwa Dukda ba yau ne na farko da ta kan tsinci ummin tata cikin irin wannan hali ba.

"Babu komai Alayah, kawai kin tuna min da mahaifinki ne da abubuwa guda biyu yanzu".
Itama Alayar yanayinta ne ya sake sauyawa jikinta a sanyaye tayi wa ummin alamar

"wani abu nawa na yanayi da nashi ko ummi?"
Cikin murmushi me bayyana tsantsar ciwo ummi tace
"Cin abincin ku iri ɗaya sak! Haka kuma bai taɓa zama cin abinci ba tare da ya tambayi inda na koya girki ba, wani lokacin ya kan sanyawa iyayena Albarka, na kan zauna cikin murmushi da jin daaɗi ina kallon yadda zai ke ta santin abinci na har ya gama ci, kai har ta kai ta kawo mahaifinki baya iya cin komai koma menene a waje, duk wata ƙasa da ze je se ya ɗauke ni mun tafi tare sbd girki kawai...."

Katsewa maganar yayi ta sa bayan hannu ta ɗauke hawayen ta Allah sarki mutuwa, mutuwa baya barin wani don wani yaji daaɗi.

A sanyaye Alaya tace
"Allah ubangiji ya gafarta maka Abbana"

Daga nan se walwalarsu ta kau, a koyaushe dama walwalar tasu bata wuce na dakiku, a duk sadda zasu tuna da jigon rayuwarsu kowa da abunda ze ke kitsawa a ran shi.

"Ummi a duk sadda kika yi wani zance na Abba alamu su kan nuna Yana da dukiya, sannan yana da kirki ga mutane da kyakyawar alaƙa, yana da son mutane kaman yadda su ma suke son shi? Ummi ina dukiyar? Ina mutanen nashi? Ummi Don Allah mai ya ajiye mu anan cikin azaba da kuncin rayuwa??" Tayi maganar cikin zubar hawaye, da sauri ummin ta hadiye ƴar walwalarta cikin sanyi da siga na bada umarni tace

"in kin koshi wuce kiyi sallah ki komawa aikin ki..."
Kuka sossai Alayah ta saki kan ta tashi ta nufi bayi.......



*karki manta book 2 paid ne a naira 500 kachal ze zo muku immediately after an gama book 1, zaki iya biya tun yanzu ta wannan asusun
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin, se ki turo shedar biyan ki ta wannan layi
*09039206763*

#comment
#Vote


              🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page 2*


Tana Sallar tana zubar da hawaye tana kuma adu'ar Allah ya sassauta musu ya gafartawa mahaifinta da take jin kila da yana nan da ba haka rayuwarsu zata kasance musu ba cikin rashin gata da galihu, wulakanci da tozarci ya zame musu ruwan sha don da yana tsiro da babu masaka tsinke jikin su, cikin matsanancin kaskanci da rashin Ƴanci, ta san ko menene zai tsaya yayi tsayin daka don samar musu walwala da rayuwa mai inganci a matsayinshi na mahaifi kuma miji ga ummin ta, mutuwa mai tonon asiri.

Umminta gani take har yanzu ita ɗin yarinya ce ko gani take da already dama zuciyarta da aka haife ta da rauni na ciwo ba zata iya ɗauka ba shiyasa har yanzu bata iya bata labarinsu daga ita har mahaifinta ba, da yadda aka yi suke zaune cikin wannan baƙar gida, abubuwan da zata ce ta sani akan mahaifinta kalilan ne wadda take tsinta a wurin su baba Musa su ɗin ma se subutar baki ko in tayi wani abu da yayi yanayi da nashi, addu'a sossai tayi kaman kowani bayan sallah tana share hawaye da bayan hannunta se tayi looking very cute and adorable kaman baby.

Ummi ta santa sarai da shegen shagwaɓa wadda rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ya koya mata juriya, ta kure ta da ido tana banbance kukan ta ne na sakalta ko kuwa daga zuciyarta yake fita? Se ta fahimci wannan ɗin hawaye ne masu ciwo da dumbin damuwa, ajiyar zuciya ta sauke har Alayah ta miƙe ta mata alama da ta koma cikin gida ta kama aikin dare.

Har ta fice ummin bata ce komai ba, Allah ya gani ba labarinsu bane bata son bata, sam bata so yarinyar ta sawa kanta kiyayya ko fansa ko wani abu makamancin haka a raunataccen zuciyarta da babu cikakken lafiya bare hutu, she cannot risk the life of her only daughter wacce itace hapiness ɗin ta a yanzu.

Ita ko Alayah bayan ta koma kitchen din aikinta ta fara cikin son ture damuwowinta sbd umminta, cikin kwarewa da gogewa a girki da ta samu daga umminta ta haɗa Miyar kan San banda kamshi babu abunda yake tashi, a gefe ɗaya ta ɗaura tuwon shinkafarta, kan Ace an kira magarib ta gama ta kuma kimtsa kitchen ɗin tsab kaman ba'a yi komai ba, anan kitchen din tayi Sallar magarib, seda ta jira Masu gidan suka fito tukuna hajj Zeenat ta dibar musu abincin su, godiya tayi ba tare da ta samu amsa ba ta ɗauka ta fice.

Kaɗan ta ci ta samu tayi isha da kyar sbd tsananin gajiya da baccin dake ɗawainiya da ita Dukda tarin assigments da take dasu gajiya be barta ta bi ta kan bokon ba, tunda ta kwanta a sallayar ko motsi bata yi ba haka bacci ya ɗauke ta.

Ummi ta tsira mata idanu tana tuna chan shekara kusan 17 baya.....

****

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!! Hawwa na gode.. Na gode" Abin da yake ta maimaitawa kenan tun a sadda kalmar likitar na tana dauke da ciki sati biyar suka shiga kunnuwanshi, ba zata ce ta taɓa ganin tsananin farin ciki a fuskanshi ba irin na ranan, ɗagowa yayi daga sujudushukr da yayi fuskarshi kamar gonar auduga

Please Login or Register in order to submit comment