Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taimaka mata tayi saurin ɗaga mata hannu, a ranta ta saka zata nunawa jameelar yanzu da da akwai bambanci komin ƙanƙantarshi kuwa, duban Aunty ruqayya tayi tace
"Ayyah Aunty ruqayya ɗan taimakeni zuwa bayin"
"Ok Binty"
Kusan haka bakinsu ya riƙe sbd yadda Maami ke yawan kiranta da hakan, da taimakonta ta shiga bayi tayi wanka da ruwa mai zafi, ko da ta fito ta samu Maami a ɗakin da Mukhtar Junior da kuma Tabawa, sannu duk suka mata har ta zauna sai a lokacin Jamila ta musu sallama ta fice, da kallo duk suka bita kan Alayah ta kalli Maami
"Maami ko me ya kawo ta?"
Maami tace
"yadda kika gansu haka na gansu Alayah, Abbanku ma har mamakin ganin Alhj Alhassan ya zo gaisuwa yayi itama matar tashi tana zuwa gida, bamu dae ce musu komai ba kuma ina so ki kiyaye don bamu san da wani sharrin suke tafe ba"
A hankali Alayah tace
"In shaa Allahu Maami"
Daga nan ta shirya aka ɗaura mata Mukhtar Junior kan kafafunta ta soma bashi abincinshi ya ƙarba kuwa da gudu bawan Allah, haka ta zubawa fuskanshi idanu ranta na kunar tuna Mukhtar sai dae tayi alkawari bazata sake mishi kuka ba don haka bata yin ba sai Adu'a da tayi ta mishi a ranta.

Haka ta ƙara kwanaki kusan biyar a asibitin kan aka sallameta ta dawo gida, Takaba take ga goyo hakan yasa lokaci ɗaya ta chanza rama ya sake mata sallama Dukda Maami na kula dasu sossai, kullum da tunanin Mukhtar take kwana take tashi, karatunta da take online ma sai da Maami tayi da gaske kan take ɗan bibiyan wasu abubuwan da tace sai de tayi deffering, kowa ya san yadda mutuwa yake a hankali ta rungumi kaddara da sabuwar rayuwar da littafin kaddara ta buɗe mata, burin ta guda ɗaya yanzu shine ta fita takaba ta ziyarci mahaifiyarta wadda Maami ta mata alƙawari tana fita takaba ba zasu kara sati biyu ba zasu tafi.

A lokacin da zata fita ɗin a lokacin zata soma exams kuma paper takwas zata yi cikin sati biyu zasu gama sai su wuce, sossai take kula da mukhtar Junior da yake girma so masha Allah.

Tana kwance akan sallaya Maami ta turo kofa da sallama ta shigo ɗakin, a hankali Alayah ta miƙe zaune tana gyara hijabin jikinta hannunta na cigaba da jan casbinta.
"Sannu Maami"
"yauwa binty, wannan yarinya ta zo wurin ki"
Sama Alayah ta ɗan kalla da alamun tunani don bata san wace ba sai da Maami ta ce
"Jamila"
Gira ta haɗe in confused way tace
"Me yarinyar nan kuma take nema da rayuwata?"
Maami ta matso ta zauna bakin gado tace
"shiyasa ban barta ta iso har nan ba, ina so ki yi taka tsan-tsan da lamarin ta don haka kawai ba zata soma shige miki ba bayan abubuwan da suka faru a baya, ki kiyaye kin ji?"
Kai Alayah ta gyaɗa ai ko Maami bata faɗa ba bazata taɓa son mutanen ba, da ma ita kaɗai suka kuntatawa da sauƙi amma har mahaifiyarta babu irin cin kashin da basu mata ba sannan yanzu su zo suna buɗe mata haƙori kuma ta aminta dasu? Never.

Miƙewa tayi ta fito a hankali ta sauƙa stairs tana kallon Jamila dake zaune cikin kujera hannunta riƙe da juice da aka kawo mata tana sha, tana ganin Alayah ta hau murmushi
"sannu sis"
Ita Alayah dariya ma abin yake bata ikon najahu ji take abin na mata banbaraƙwai wai namiji da suna Hajara shine wannan.
"Yauwa sannu"
"sai kika ganni, zan ɗan wuce ne nace bari na shigo dae mu gaisa"
Alayah da take ta kallonta abubuwan da suka faffaru wasu na dawo mata ta girgiza kai
"eyyah na kuwa gode"
Shiru ne ya ratsa wurin kan Jamila tace
"yauwa ni ko nace akwai ƙanin mukhtar da tunda nake zuwa ban haɗu dashi ba na kuwa so in mishi gaisuwa a matsayin relative naki"

Sai a lokacin ma wani suna umar yayi clicking mind ɗin ta, murmushin takaici tayi ita ma bata ganshi ba bare Jamila, haushin shi ma taji tana ji da wani irin takaici da ta rasa na menene, babu shakka kila na abubuwan da yayiwa Mukhtar ne bayan tuban shi, kuma ace har Mukhtar ya mutu bata ji labarin ya zo gaisuwa ba.

"Eyyaaa kin ga kuwa baya nan, ya ma koma ƙasar da yake aiki"
Tana kai nan tayi shiru, duk shiru suka yi don ba sabo bane tsakaninsu, hasali ma Jamilar kaman forcing magana da smile din duk take.
"Oh Ayyah, to bari na zo na wuce sai na sake shigowa"
Ba tare da Alayah ta miƙe ba tace
"Allah ya kiyaye a gaida mutanen gida"
Da kallo ta rakata har ta fice, girgiza kai tayi ta miƙe ta koma sama.

Wasa wasa sakanni kan juya ya zama minti, mintuna su juye zuwa awanni, awanni su zama kwanaki, kwanaki zuwa satittika zuwa watanni wai yau Alayah take cika watanni huɗu da kwana goma cifff da mutuwar Mukhtar inda a yau din take fita takaba, kaman yadda al'adarmu take an yi mata hidima na kayayyaki sossai da kyaututtuka kan aka yi sadaka aka ɗan taru aka yi Adu'a, sai a lokacin Abba ya aika a kira Alayah.

A natse ta shigo babban parlorn baba ne da wasu da bata sani ba waenda suka haɗa da aminan baban sai en uwan Abba da wasu abokan shi sai Maami, a ƙasa ta zauna kanta ƙasa, haka kawai ta tsinci kanta da matsanancin faɗuwar gaba.

Bayan sallama da ƴar nasiha da kuma Adu'a da aka sake bin Mukhtar da ita Baba ya dubi Alayah yace
"Mun kira ki nan ne akan abubuwa guda biyu zuwa uku Fatima, muna fata zaki bamu haɗin kai"
Kai ta gyaɗa baba ya cigaba
"akan maganan gadon Mukhtar, kasancewar yana da ɗa kuma namiji kowa anan ya san dukiyar kusan duka nashi ne illa iyaka za'a cire miki naki sai na iyayenshi, menene kike tunani akan gadon yaron?"

Kanta a ƙasa tace
"Baba da ni da Junior duka muna a ƙarƙashin ku ne, duk abinda kuka yanke daidai yake a gareni"
Kai ya gyaɗa kan yace
"Masha Allah, haƙiƙa ban taɓa alfahari da Mukhtar ba irin na lokacin da yayi min rantsuwa da alqur'ani cewa arzikinsa babu haram ciki, nayi murna kuma da Naji jajircewar ɗan uwansa a kansa ne ya hana shigar haram cikin dukiyarsa sai kuma karfin adu'ar uwa, a shawara ta shine a bar wa umar ya cigaba da kula masa dashi zuwa ya mallaki hankalin kanshi na tabbatar ba zai taɓa cin amanar dan uwansa ba"

Kowa yayi na'am da haka sai de ita Alayah ta ɗan ji wani iri, Allah ya sani zafin wannan umar ɗin take ji.

Abba ne ya karbe zancen
"sai abu na gaba, alfarma muke so mu nema a gareki wadda muke fata zaki yi mana shi"
Kai tsaye tace
"Abba tsakanina daku babu alfarma, ku matsayin iyaye kuke a gareni a lokacin da duniya ta yi mini kunci, rayuwa tayi zafi komai na cikinta yayi tsanani na rasa madafa ku kuka tallafeni kuka bani inuwa, kuka kula da maraicina kuka kula da mahaifiyata babu kyama ba kyara, kuka so ni fiye da ɗan da kuka haifa, in har umarninku be saɓa na mahallacina ba, ba ma sai na ji ba na amince, wallahi na amince"

Maami tayi murmushi dama ta san Alayah ba zata watsa musu ƙasa a ido ba, Baba yace
"Masha Allah, dama amincewar shine babba je ki Maaminku zata miki bayanin komai a ciki"

Miƙewa tayi ta fito yayinda maami ta bi bayanta, a ɗakin Maamin suka zauna don gidan akwai tsirarun en uwa, hannunta Maami ta kama a hankali tace
"Fatima hakika mahaifiyarki tayi matukar kokari wurin gina miki tarbiya, kowacce uwa zata yi fatan samun sirika irin ki wacce zata taya ta son ɗan ta ta kuma taya shi gyara tsakanin shi da Zuri'ar shi, wacce zata kula da dukiyar shi ta kare martabarshi, wannan nagarta naki na duba na ga ba zan bari nayi asarar ki ba, ba zan bari Junior yayi agolanci ba, ba zan iya bari ki subuce mana ba hakan yasa na nemi da a ɗaura miki aure da umar a yau kuma Alhamdulillah baki bani kunya ba kin amince, nayi matukar farin ciki ina kuma fata da burin mutuwa ce zata raba ku...."

Tun da Maami ta ambaci aure da umar bata sake fahimtar sauran zantukan ba saboda wani irin tashin hankalin da ya ziyarce ta... AURE?
bata dawo daidai ba ɗan Aunty Aysher ya shigo da hanzarin shi yana ba Maami Alewa
"Maami gashi yanzu Abba ya bani wai na auren Uncle umar?"
Murmushi me kyau Maami ta saki tana furta
"Alhamdulillah har an ɗaura kenan"
Wani irin sarawa kan Alayah yayi jiri taji tana gani.

Gwarama!
*jama'ar Allah jama'ar kwarai anan na kawo karshen book one1, kaman yadda muka sani book 2 na kuɗi ne zai zo muku akan Naira ɗari biyar kachal har yanzu akwai sauran tafiya akwai kuma tufka da bama mu fara warware shi ba, shin umar ya san da zancen auren? In ya sani zai karɓa kuwa? Ita kanta Alayar ba farin ciki tayi da wannan aure ba, ita kenan haka ƙaddarar ta? In shi umar din na da wani hali fa kaman yadda aka haɗa ta da Mukhtar a farko karfi da yaji? Ya labarin umminta zata farfado kuwa har ta warware musu tufkar dake tsakanin Hassan da Ahmad mahaifin Alayah? Ina Ƴan uwa da danginta? Shin kuna ganin Jamila zata yi hakuri ta bar wa Alayah Captain Cold ko kuwa haka zata ƙare kaman yadda mahaifiyarta ta kare cikin AL'AJAB Na So? Ta yadda tana ji tana gani abinda take so ya fi karfinta? Ku biyo ni ku sha karatu*

0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
09039206763



🖤Gureenjoh🖤 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment