Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba jin ta zata yi ba yasa ta dauko sandar mopper da ummin ke aiki dashi ta zungureta wai ita nan kyamar taɓa ummin take, Juyowa ummin tayi saide Meelah ba maganan kurame ta iya ba masifarta ya fito da Hajiya Zeenat
"a'a Shalele mai ta miki ne?"

"Mommy ina sarkar da Abba ya sai min last business trip din shi daga Lagos?"

"Eh na zinarin nan"
Mommyn ta amsa

"Mommy daga shiga ta min shara kawai in fito ban ga sarka ba? Kan uban chan kayyasaaa! Wlh sai ta fitar min da sarkata "
Meelah ta faɗa tana wani hararar ummi cikin tsantsar fitsara da rashin kunya.

Mommy ta juya ga ummi tayi mata alama
"ina sarkar da Kika sata a ɗakin Meelah?"

Dafe kirji ummi tayi a firgice kan ta soma girgiza hannu da kai da sauri alamar ba ita ba ce, daidai lokacin Abba ya fito hakanan Shigowar Alaya don kamawa ummin aiki ta sani in sun matsa ko na awanni ne ayyukan da su kan samu a gidan ba na wasa ba bare har kwana biyu, kalaman da taji ne yasa hankalinta tsananin tashi da sauri ta ƙarasa ta rike hannun umminta tana kallon meela da mommy tace

"Sata? Ummina fa?"
Yadda tayi maganan a karye lokaci ɗaya hawaye na gangaro mata dole ta baka tausayi, wani sabon bita da kullin kuma za'a bisu dashi?

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment




                🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page 4*

"Hajiya! ummi bata saci komai naku ba, don Allah kar ku fara yi mana wannan sharri, ba halinmu ban...." Buge mata baki da Hajiya Zeenat tayi yasa ta saurin dafe bakin tana zub da hawaye kaman yadda ummi ma kanta ke ƙasa tana hawaye.
Faɗa suke yi ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba har da zunguri Abban Meelah dae be ce komai ba yana tsaye yana nazarinsu, kansu ƙasa suna aikin zub da hawaye na wannan tozarci da ake musu da kazafi, suna cikin wannan masifar se ga Hajiya Fanta da ɗiyarta Zaliha suma suka shiga sahu har da aje a chaje sashensu. Meelah tace
"ba wani sashe a nan jikinta zata ɓoye don ai bata fita ba"

Hajiya Fanta tana dubansu cikin kyama tace
"ku chaje ta maza maza toh in dae haka ne"
Dukewa ummi tayi ƙasa tana rufe idanu a sadda hameeda da Meelah suka fara chaje jikinta suna yatsina fuska da sunan kyama yayinda Alaya ke kuka harda gunji, ganin irin halin da suka shiga yasa Abba da ya taɓe baki yana yiwa ummi kallon 'duk laifinki ne' yayi gyaran murya yana duban Meelah yace
"my dota kyale su idan ma su suka sata zamu ga yadda zasu yi dashi idan don sarka ce zan sake sai miki wata.."

Tura baki tayi harda hawaye sbd ba yadda ta iya tana kallo yayiwa su ummi alama da hannu akan su fice, kama ummi Alaya tayi suka fita daga parlorn zuciyoyinsu baƙi kirin, hajj Zeenat kuwa haushi sossai taji tana kallon sbd wani manufar ne Alhj Hassan ya sa suka tafi alhali sun musu sata bata damu da gaban ƴarsu ko baƙin su ba tace cikin faɗa
"Haba Abban Jameelah ai wannan ka basu damar sake wa gobe ne, baka da hujjar saka su barin parlorn nan alhali ka san babu wadda zai saci sarkar nan in ba su ba in har dae ba da wata manufar ka tseratar dasu ba.."
Wani irin kallo ya watsa mata kan ya juya har ya nufi barin sashen ya sake Juyowa
"baki da hujjar tuhumata akan abunda yake ni na saya ko yanzu zan iya sayawa mamana Goma irin shi don haka ki daena shiga min hanci da kudundini"

Gabas da yamma ta haɗa da fuskanta da ta turbune wadda yafi yanayi da na shanu zata soma sakin zance Hajiya Fanta ta ja hannunta suka yi ɗakinta.
Meelah ta ja hannun Zaliha tana cewa
"zo kawata mu je kiga wani guy da ya tafi da imani na a intsgram ban taɓa sanin akwai me kyau da charisma irin shi a duniya ba"
Suna shiga ɗakin ta sa hannu bedside don ɗauko wayanta se ta sauke kan sarka da ya ɓuya a bayan flower portal dake daure bisa bedside dinta fiddo shi tayi tana nunawa Zaliha
"Ai ke banza ta faɗi miki adana wannan daddynki ya sake sayo miki wata"

"haka ko za'a yi"
Ta ja bedside ta saka kan ta kamo instagram ɗin ta ta fara nunawa zaliha gayen ba Jameelah kadai ba har zaliha gayen ya tafi da imaninta sake kallon handle ɗin tayi a ranta tana maimaita
"captain cold" wow ko sunan na daban ne.

A ta ɓangaren su Alaya haka suka jima jugum cikin damuwa da tunani da Alayah ta gaji ta dubi ummi
"Ummi don Allah bamu da kowa a duniyan nan ne? Ummi Meyasa kika dage sede mu cigaba da zama a wannan baƙin gida? Meyasa ba zaki bani labarinku da Abbana ba? Umm..."
Dakatar da ita tayi
"Ki adana tambayoyinki akwai lokacin da da kaina zan baki waennan amsoshi Alayah.."
Hawayen ta ta share ba tare da ta sake cewa ummi komai ba.

****

Tafawa suka yi suna dariyar su irin ta asalin Ƴan siyasa kuma waenda suka gogu da duniyanci, daga kallo ɗaya zaka san sun jiƙu da naira iya jiƙuwa da alama hirar tasu mai daaɗi ne...
"Ai ina gaya maka Hon Hameed chanji a tafiyar da muke gab damo ke shirin isa ga harawa"
Dariya suka sake sakewa kan Hon Hameed chanji ya ɗan tsagaita hankalinshi ya tafi ga wani tunani da yake damun shi a rai..

"Lafiya kuwa honourable?"
"Wlh ina cikin wata ƴar damuwa ne, na san bazaka rasa sanin mukhy ba".
"Ah taya ba zan san Mukhtar ba? Shine fa yaro ɗan babansa mafi soyuwa a cikin zuciyarka".
"ka san a sadda na tura shi chan ƙasan waje karatu a maimakon karatun sai lalacewa yayi, ya faɗa shaye shaye, abun bai tsaya nan ba suka yiwa wata yarinya fyade sanadin kaisu gidan yari kenan, ka san chan ba kaman nan ba duk wata hanya da zan bi don ganin kuɗi sun fidda shi hakan ya gagara seda yaci prison na shekara takwas, daga nan suka koreshi a ƙasar lalacewar da Mukhtar yayi a prison yafi karfin wadda yayi kan zuwanshi da kyar na samu ya karanci business a Nile Abuja shima da laifuka iri daban daban, duk dae kuɗi nayi ta anfani wurin kashe su har ya kamalla na buɗe mishi kamfanin motoci ya fara business ɗin.."

Kai Alhj Hassan ya gyaɗa duk wannan ya sani ai labarin tantirancin mukhy babu wadda be sani ba in har dae Kano kake.
"Yanzu menene matsalar baya sana'ar ne?"

"Hmm sana'a ba karamin karbarshi yayi ba yana samu ba na wasa ba sede kuɗin a banza yake tafiya Ƴan mata, abokai, Ƴan shaye shaye, su tatooo da ya cika jikinshi dasu da dai sauransu, da nake shawara da wani aboki na se yake ce min ai aure na nitsar da irin Muktar ni kuma ban cika son takura mishi ba duk abunda yake so shi nake so nayi ta bin shi ya kawo mata ya min kunnen uwar shegu, yanzu ina tunanin samun mace dalleliya wacce ba ze iya ƙin aurenta ba in aura mishi amma ban san wace yarinya zan samu ba, irin  yaran malaman  nan haka dae"

Wani tunani Abba ya tafi kan ya dubi Alhj Hameed ya ce
"ka kawo kuka gidan mutuwa abokina"
Dariya suka yi a tare Alhj Hameed yace
"na san ka abokina duk inda matsala take ka san maganinta, wacece wannan da iyayenta zasu iya aura mata mukhy?"

"Fatima ɗiyar Amadu"
Wani irin dariya suka yi sossai  kan Alhj Hameed yace
"kana ganin wannan Hawwar zata yarda kuwa?"
"Dole ma ta yarda, kai ko bata yarda ba ni na ba wa muktar auren Fatima kuma ka tabbatar wannan aure an yi an gama ka kwantar da hankalinka kaman kayi baƙo ya mutu"
Kashewa suka sake yi suna dariya daga nan suka yi sallama, Alhj Hassan ya tashi don raka Hon Hameed se ga Alayah ta fito daga sashensu zata shiga sashensu Jameelar don ɗaura abinci sbd zazzabi ne ya rufe ummi...

Har ta wuce Alhj Hassan yace
"ke!"
Da sauri ta iso ta duƙa a ƙasa ba tare da ta kalle shi ba ta gaida bakonshi ya amsa yana me kallon ta kan Alhj Hassan yace
"je ki"
Ta miƙe ta wuce.
"Ka ganta nan bana tunanin Mukhtar ze iya ƙin irin wannan"
Kai kawai Hon Hameed ya gyaɗa wannan ai ko shi ya samu irin wannan ba ze ƙi ba shar da ita ga kyau da natsuwa kaman nunanniyar gwanda...

Ranshi kal yayiwa Mukhtar mata ya isa gida, parking driver ɗin shi yayi a kofar mashigar parlorn ƙawataccen gidan da ya tsaru ya gaji da tsaruwa, kofan parlorn ya buɗe ya shiga sanyi da kamshin da parlorn ke yi na asalin matan shuwa ya shaka ya lumshe ido, wannan kamshi da tsabtar na daga cikin abunda yake hana shi fushi me tsawo da hajj binta Dukda yadda take bakanta mishi rai a kullum tana mai dashi yaron goye.

A kan kujera ya sameta kaman kullum cikin ado da kwalliyar da bata rabo dasu sanye da laffaya me tsadar gaske hannu da kafafunta sun sha jan kumshi gata fara sol kaman ka taɓa jini ya fito, ɗaga idanunta tayi ta kalleshi kan ta girgiza kai cikin hausar ta da har yanzu be zama cikakke ba tace
"Alhj ban ji kayi sallama ba"

Tsaki yaja yana yarfa hannu yace
"woohuhu ke kam Binta Meyasa bakya rasa abun complain bane a kullum, ni na zo miki da labari me daaɗi ke damuwarki wata sallama"

"Ai ko dae sallama na da matukar muhimmanci, kuma wajibi ne a musulunci"
"to Naji Assalamu Alaikum shikenan?"

"Wa'alaikissalam warahmatullah" ta faɗi tana kallonshi yana zama.
"Na samarwa muktar mata"
Da hanzari ta kalle shi
"wani uba ne ze baiwa Muktar auren ƴar shi? Ko dae ƴar irin Muktar dinne?"

Harara ya maka mata cikin takaici yace
"Meyasa ke kam a kullum bakinki baya taɓa fadin alkhairi akan wannan yaro ne? Ƴar mutunci nitsatsiya kuma ya samu sai ki haɗiyi zuciya ki mutu"

"Me yayi zafi Alhj? Ni dae na san uban kwarai ba ze taɓa ba muktar auren ƴarshi ba wallahi, kuma ni ban yiwa muktar baki ba a kullum adu'ata Allah ya shirye shi sannan wallahi ku guji hakkin ƴar mutane sbd wallahi haɗa ta da muktar zalunci ne mai girma, idan har ba ya chanza halin shi ba"
Tsaki yaja yana Miƙewa
"Babu anfanin faɗa miki Binta ki sani bukin ba ze dau lokaci ba in kin ga dama ki fara shiri, muktar dae ɗan ki ne da kika haifa da cikin ki babu abunda ze chanza hakan, fifikon ki na banza akan Umar yaron da be ma san kina yi ba"
Daga haka ya wuce fuuu
Da ido ta bishi a fili tace
"Allah ya shirya to"
A zuciyarta kuma tun kan ta san yarinyar tausayinta ya rufeta, muktar danta ne kaman yadda mahaifinshi ya gama faɗa saide duk halayen muktar babu na zaɓe, ga zafin zuciya da saurin fushi, ga shaye shaye idan ya bugu iya buguwa har ita bata tsira daga cin mutuncinshi ze iya zuwa tsakiyar parlorn nan ya gayamata duk maganar da ta zo bakinshi se abubuwan sun sake shi kuma ya zo yana neman yafiyarta yana cewa shi be san yayi ba, to taya ze iya zama da mace a haka? Ƴan matanshi har gidan nan suke zuwa neman shi mahaifinshi be taɓa ganin hakan a laifi ba se ma goyon bayan da yake bashi, duk da sana'ar da yake sede idan be nemi kuɗi a wurin mahaifinshi ba duk ywansu haka ze bashi ba tare da ya tambayi abinda za'a yi dasu ba, ko kwana nawa muktar ze yi a waje mahaifinshi baze taɓa tambayar inda yaje ba bare ya binciki me yayi tun ma be kai haka ba bare yanzu, duk wani faɗa na club mukhy amma uban ba ze taɓa tsawatar mishi ba sede ya biya kuɗi a kashe case ɗin, ita dake yawan yi mishi faɗa da nasiha se suka maida ita makiyiyarsu daga shi har mahaifinshi, kullum a ganin da yake mata bata ƙaunar Mukhtar wanene ze kaunaci ɗa duniya sama da uwa?
Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tana girgiza kai...

***

Yau sunday ummi na chan cikin gida tana aikin abincin dare yayinda Alaya ta gama yiwa Hajiya Zeenat da Meelah wanki ta shanya se ta nufi ɗakin su ta gyare tsab, ta fara tattare wankinsu don zuwa ta musu ta san idan ba yau din ba ummin ce zata yi idan ranakun makaranta suka shiga, taje ta fara kenan ta ɗauko wani zanin ummi dagawar da zata yi se taga wani ƙulli murmushi tayi tana ayyanawa kila ɗan chanjin asibiti ne ummi ta ƙulle a bakin zanin kaman wata tsohuwa warwarewa tayi don ta adana mata se taga paper ne, buɗewa tayi tana mamakin wani paper ne wannan ɗin..

Rubutun ta fara karantawa daki-daki gabanta ne ya faɗi ummi na da hanyar tseratar dasu daga wannan rayuwar? Menene wannan kalma ɗaya tak da zata faɗi don saya musu Ƴanci ta kasa? Gabaɗaya ta rude haka ta gama wankin tana Allah Allah dare yayi don ta tuhumi umminta akan abunda take boye mata, tana gama wankin ta nufi komawa sashensu don gab magarib ne ta san ummi zata gama abinci a lokacin ta koma sallah, da Abban Jameelah suka ci karo da sauri ta tsuguna kasa gabanta na faɗuwa sbd yadda take matukar tsoron wannan mutumi, ya azabtar da ita ba na wasa ba da tana yarinya ta ɗauka shine mahaifinta hakan yasa a duk sadda ta gansu da Jameelah se taje a kuma duk sadda taje da kuka zata dawo, tun tana zuwa har ta daena kwata kwata idan kuma wani abu ya hada su da Jameelah har suka yi faɗa to lallai jikinta se ya gayamata hakan ne ya koya mata respecting Jameelah karfi da yaji.

har ze wuce se ya dakata yace
"Ke! Idan kin koma ki fadawa mamarki na yi miki miji, a kowani lokaci za'a iya tada maganar aurenki don haka ku zama cikin shiri, sannan zaki iya amsar baƙuncin shi anytime from now don ze zo ya gan ki"

Ji tayi kaman bata ji da kyau ba tsabar yadda maganar ya zo mata bagatatan, a razane ta ɗaga ta kalleshi tace
"miji? Ni?"
Harara ya zabga mata yana cewa
"A'a ƴarki ta fari to uwarta"
Da sauri ta maida kai ƙasa tana jin wani kullin tashin hankalin dake taso mata, ita ze yiwa aure? Me ta mishi? Meyasa? Akan me? Mulkin mallaka kawai? Da gudu a kuma kiɗime ta isa sashensu tana zuwa kawai ta faɗa jikin ummi da zata tada sallah kenan ta fashe da wani irin kukan tashin hankali...

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment



                🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
. *Page 5*

Kasa riƙe balance ummi tayi suka tafi tare zuwa kan gado, a gigice ta ɗago ta ganin tana zub da hawaye fuskanta da alamun gigicewa ko ɗimaucewa da bata taɓa ganinta dashi ba, cikin alamar kurame take tambayarta abinda ke faruwa, ta ma rasa da wanne zata fara, kuka kawai take na baƙin cikin kasancewar su a wannan gida kuma ummi na da yadda zata yi amma ta zaɓa musu wannan rayuwa da rayuwar ƴancin da ake tallata mata.

"Alaya menene?"
Ummin tayi mata alama bayan ta ɗago ta tana dafe da kafaɗun ta.

"Ummi wai ni Abban jameela yake cewa zai yiwa aure nan kusa, ummi wlh in har hakan ta kasance ba zan iya cigaba da rayuwa ba! Ummi zuciyata zata buga da baƙin cikin wannan rayuwa..."
Ummi da tafi Alaya gigicewa tayi saurin sake mata Alama
"ban gane ba!"
Bayani ta mata yadda suka yi cikin kuka ta kara da
"Ummi karki ce in yi haƙuri wlh ba zan iya wannan aure ba, ba zan taɓa tafiya in barki cikin wannan gida ba!"
Kasake ummi tayi zuciyarta na fin na Alaya bugu, maganar ya zo mata wani iri, aure? Wani irin aure? Me Alhassan ke nufi? Bata iya tayi magana ba illa kurawa Alaya idanu da tayi tana kuka sossai.

Sai kuma ta warware papern tana nuna mata
"Ummi wannan a kayanki na samu, me hakan ke nufi? Ummi zaki iya tseratar damu amma kika zaɓi ƙiyawa?"
Karɓan papern ummi tayi ta dunkule bata cewa Alayar komai ba banda kanta da ta mayar ƙasa tana sauke numfashi.

Daga magarib har isha sun yi shi ne kawai babu cikakken natsuwa dukkaninsu a tsorace suke da lamarin wannan aure da Abban yayi, sanin kansu ne babu kaunar su ko na second a zuciyar Abba to taya zasu yi tsamannin zai zaɓarwa Alayar ma miji nagari in ma ya kama ya zaɓar mata kenan, tambayar ma itace; Meyasa ze tsallake buduruwar yarinyar shi ya zaɓi Alaya? Me manufarsa?

Har sun yi shirin kwanciya ummi da take wani nazari ta dubi Alaya dake ganin kaman duk wani abunda ke faruwa laifin ummin ne tunda tana da hanyar samar musu Ƴanci amma tayi shiru, ummin na kallo Alayar ta kwanta ba tare da ta sha magungunanta ba gashi sai zub da hawaye take har lokacin.

Miƙewa tayi ta dauko magungunan da ruwa tazo ta ɓaɓallesu ta ɗago Alayar ta mika mata, karɓa tayi ta sha tare da sake komawa ta juyawa ummin baya, kaman yadda bacci ne ɓarawo ya dauki Alaya haka ummi da ta raya daren bisa sallaya tana zub da sassanyar hawaye na abubuwa masu yawa da suka faru a rayuwarta Dukda bata nadamar ko guda sede tana jin tsoron abunda hukuncin da zata yanke na gaba ze iya kawowa..

Washegari kaman yadda suka saba haka suka kama ayyukansu da sassafe saide duk jikkunansu a mace suke aikin babu wani kuzari, har Alaya ta kamalla breakfast ta shirya dining zata juya kenan sai ga Jameelah da Hajiya Zeenat sun fito, ƙasa ta duƙa cikin sanyin murya ta gaishesu babu wacce ta amsa ta miƙe ta ƙarasa ta ja wa Hajiya Zeenat kujera ta zauna, abincin ta fara serving nasu pepper soup na kayan ciki ne sai dankali da aka soya cikin kwai aka kuma yi mishi egg sauce da tea, pepper soup din Jameelah ta janyo ta sanya spoon ta kai bakin ta da sauri ta furzar tana zaro ido, a ruɗe Hajiya Zeenat ta miƙe kaman yadda Alaya ta zaro ido zuciyarta cike da fargaba.

"Mommy harshena ze tsinke wannan baƙar muguwar zata kasheni da yaji!"
Mugun kallo Hajiya Zeenat ta watsawa Alaya cike da gargadi tana kokarin bawa Jameelah evaporated milk da ta fasa.
A ruɗe Alaya ta matso tana cewa
"kiyi haƙuri wallahi ba...."
Ƙara ta saki a lokaci ɗaya tana ambaton Allah sbd zazzafar pepper soup ɗin da taji a jikinta inda Allah ya taimake ta be kai fuskanta ba amma babu tantama wuyanta ya samu sbd radadin da ya ratsa ta a lokaci guda.
Hawaye ke gudana a fuskanta tana jin faɗan da ya biyo bayan watsa Miyar har suka gama bata iya taji kalma ɗaya ba sbd radadin da jikinta ke yi, da sauri ta bar parlorn a sadda suka sallameta tana fita ta gamu da Ummi dake shirin shigowa ɗauke da kayan share share, bata tsaya yiwa ummin magana ba ta wuce ta da sauri, da hanzari ta ajiye abubuwan hannunta ta bi bayan ɗiyar tata ganin farin uniform dinta daga wuya har ƙasa ɓace da miya.

Alaya na isa ta zube ta cigaba da kukanta tana jin radadin na ratsa ta, da sauri ummi ta ɗago ta tana tambayarta abunda ya faru amma bata amsa ba duk laifin ummin take gani, sai da ummin ta jijjigata da karfi tana mata alama bakin ta na irin ɓaɓatun maganan kurame dinnan
"Alaya ki dawo hankalinki, duk abunda kika ga na yi sbd ke ne da rayuwarki, nima ba zan zuba ido a zalunceki a ɓata miki rayuwa da gangan ba, menene ya faru? Ki min magana..!"

Alama take mata tana sakin wani kukan a haka ta bata labarin abunda duk ya faru, hijabin ummi ta zare mata abunka da farar mace nan da nan jikinta ya tashi yayi jajazir daga wuyanta har kirjinta, wani abu me ɗaci ummi ta haɗiye ta miƙe ta fice chan ta dawo da kƙullun kunu sbd ana yiwa Abban Jameelar tazo ta shafa mata duk wurin kunar ta zauna ta sanya ta a gaba tana kallo yayinda baccin wahala ya ɗauke ta.

Bayan kwana biyu

Tun daga randa ta ƙone bata kara fita daga sashen ba komai ummi ke yi Dukda damuwa da ya mata yawa, yake kuma cin zuciyarta hakan be hana tayi musu duk aikin da suka saba yi ba, Alaya kuwa tun ranar bata iya zuwa makaranta ba duk son ta da boko kuwa.
Yau dae ta miƙe ta shiga cikin gidan don kamawa umminta aiki tana cikin jera abinci taji gyaran muryan Abba da sauri ta juyo se ta kai gwiwowinta ƙasa kanta kasa gabanta na tsananta bugu.

"Muktar ze zo yau ku gaisa, make sure baki yi abunda ze zubar min da ƙima ba, parlorn baƙi na zaku zauna and ki tabbatar kin tsaftace kanki na rana ɗaya dae"
Yana kai nan ya wuce abun shi.

Bata iya ta miƙe daga tsugunon ba tsawon mintuna kan ta yunkura kitchen da bata koma ba kenan tayi chan baya ta fara zirga zirga...
Na shiga uku na wai da gaske Abban Jameelah ke yi? Shikenan haka zamu kare kaman bayi a chan lokacin jahiliyya? Babu irin nazarin da bata yi ba har da tunanin ko ta gudu se kuma ta tuna in ta gudu umminta fa? In ma ta gudun ina zata? Bata san kowa nata ba banda gidan nan da makaranta sai asibiti bata tunanin ta san wani wuri a fadin birnin jihar Kano.

Har aka kira la'asar bata iya ta taɓuka komai ba banda tunani da wani irin fargaba da ya cika mata zuciya fal, ganin lokacin Sallar na shirin fita yasa ta nufi sashensu sukuku da ita haka tayi sallah tana nan zaune ummi ta shigo ko kan tayi maganar yadda ta ganta ɗin taji sallamar iro me kula da shuke shuken gidan alama tayiwa ummi na ana sallama kan ta fice, a mutunce suka gaisa ya shaida mata tana da baƙo a sitting room na Alhaji..

Dawowa tayi tana share hawaye ta faɗawa ummi har abunda Abban Jameelah ya faɗa, bata ce komai ba har Alaya ta juya ta fice da kayan jikinta dogon riga da hijab da ya wuce mata gwiwa kaɗan, da idanu tayi ta bin zazzafar motar tashi kirar McLaren Mp4-12c wacce murafanta ma ta sama ake ɗagasu Red colour mirrors ɗin baƙaken sidik banda sheki babu abunda yake yi har ta isa kofar parlorn, ta dan jima anan tana daidaita bugun zuciyarta da fargaba hade da tsoro da suka cika ta kan ta tura kofar da sallama.

Ba'a amsa ba kutsa kai tayi ciki bata yi gigin dagowa ba ta ƙarasa ta tsaya a tsaye tace ina yini? Ba tare da ta ko zauna ba.
Buɗaɗɗiyar muryarshi da ta kara zurfi da amo sbd shaye shaye ya dira bisa kunnuwanta
"Kin ƙara mintuna ashirin da biyar daga kiranki zuwa yanzu mind you next time karki kuma, ba'a ɓata min lokaci a banza!"

Sai a lokacin ta iya ɗaga idanu ta kalleshi tana kokarin auna kalaman da yake faɗa mata cike da gadara da isa kaman shi ya ajiyeta, bata ce komai ba se kallonshi da take ba laifi don kyau kam kyakyawa ne na

Please Login or Register in order to submit comment