Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana ɗagowa ta kalli idanunshi da suke nan launin jaja kuma a lumshe, runtse su yayi yana jin yadda wani abu ke fusgar shi zuwa gareta, ji yake zuciyarsa na tsukewa wuri guda ga dukkan alamu ginin da babu shakka na so ne yake ginuwa daki daki cikin zuciyar shi, ɗauke kai yayi daga kallonta tare da ɗan tureta, ta kuwa sake taɓe baki alamun kai ka jiyo dama ba ni na ajiye kai na ba, toilet ta shige ko da ta fito ma bata same shi ba.

Da yammacin ranar aka bata sallama, gida suka dawo Dukda ta so tsayawa asibitin sbd ummin ta amma kuma ba hali don har yanzu tana ICU ne ba'a yarda ba ma da isa kanta bare a fara jinyar ta, likitoci da nurses ne kaɗai ke zuwa kan ta, ko da suka koma gida ma bata bar zazzabin laulayi ba, kuma ta fahimci har lokacin babu shiri tsakanin Maami da Abba kai tsaye zata iya cewa sune sanadi, iya kokari Maami na yi wurin nuna mata komai lafiya ai dae bata san ta riga ta fahimta ba.

Kwance take kan kujera hannunta yalo ne take ci Dukda wani irin zazzabi da ya rufeta tana dukunkune sai rawan sanyi take kuma ta ƙi kashe Ac ko rage wa, Maami ta fita sai mama lami ne ke zuwa jin ko akwai wani abin da take buƙata ta kawo mata, bacci ne ya fara fusgar ta sam bata san Shigowar mutum ba ashe har ya kashe Acn bayan taɓa fuskanta da yayi ya ji jikinta raurau, baya baya yayi ya zauna kan kujera Red eyes ɗin shi ya zuba mata a ranshi yana ayyana dama haka mata suke fama ne ko ita ce kaɗai?

Tun da aka ce tana da cikin nan ba zai ce ga sadda ya risketa lafiya ƙalau cikin ƙarfi da kuzari ba, ko yaushe gata nan dai ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali yake jin duk wani rayuwarshi na baya ya fita kanshi fit, iya kokari yayi na daina shaye-shaye haka matan ma rabon shi da mace zai iya cewa ya manta, bashi da wani aiki sai na tunanin wannan yarinyar, wani sa'in ma yana son zuwa ɗin ya kalleta sai kuma wani sashe na zuciyarshi ya mishi nauyi, kunyar Maami ya lalaɓo ya rufe shi ruff ta yadda baya so ko haɗa idanu su yi.

Shisha Pen da smart ya bashi ya fitar yana ɗan jujjuyawa sun ce zai rage mishi wannan damuwan da ya shiga a kwanakin sai dai yana shakka don ya san zasu iya sa wani abu na bugarwa ciki, bakinshi ya kai kaman ya sha sai ya ja tsaki yana ƙoƙarin sauƙewa suka haɗa idanu, girgiza kai tayi tare da Miƙewa bata ce mishi ci kanka ba ta zo zata wuce yayi saurin riƙe hannunta kula da yayi kaman ranta ya ɓaci kuma hakan ya nuna har a fuskanta, fisgewa taso yi ta mance ma riƙon maza ba irin na mata bane...wani zafi ne ya ratsa ta mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu a take ta fashe mishi da kuka sossai har sai da ya tsorata.

"Ni ka sakar min hannu..."
Da sauri ya miƙe yana kokarin duba hannun ko ta ji ciwo ne sam be san masu ciki da wannan mood swings ɗin ba ya haɗu kuma da wani tunani da tayi kanshi, ganin ya sake ta yasa ta nufi sama, taku biyu yayi ya tare ta
"Menene? Kin ji ciwo ne a hannun?"
"Ina ruwan ka da ni? Menene damuwarka? Ba tunani aka ce in yi akan auren mu ba? To na gama ba zan iya cigaba da zama da kai ba wallahi, tuban muzuru ne kayi ba na Allah da annabi ba..."
Shesheka ta ja tana matsawa baya ganin ya matso ta sossai yana kokarin taɓa ta don sam be fahimci inda matsalar ta taso ba tace
"kar ka taɓa ni, burin kowacce mace a rayuwa shine ta samu miji nagartacce, mai gaskiya da tausayi, wanda zata iya ƙarasa rayuwarta a tare dashi, sannan bayan aure su samu New wonderful family, burin kowace macece ta samu abokin rayuwa wadda zai agaza mata wurin cika duk burikan ta na rayuwa, ya taimaka mata a sadda take neman taimakonshi, ya so ta ya kasance mai kishin ta, sannan wadda zasu fuskanci duk wani matsalolin su a tare, ayi nishadi wasa da dariya, a yi salloli cikakku guda biyar a rana nd inspire one another to increase their deen, ayi respecting juna nd live peacefully in this nd the life hereafter, ka gayamin wanne kayi daga ciki? Ko kuma wanne kake shirin yi? Ya Mukhtar ɗan ka ne ke shirin zuwa duniya amma gaban idanunshi Shisha ne kake shirin sha wadda babu tantama na san flavor din ba zai rasa surkin abin bugarwa ba? Idan ba zaka ji kunyata ba ni karamar dangar ka da ka saba shawowa ka juye min shi be chanchanci kunyar ka ba? Maami bata chanchanci ka mata kawaici ba a cikin parlorn ta zaka yi shaye-shaye? Ka matsa min na wuce ka sha kayanka amma ka sani wallahi ni dae na gama zama da kai.."
Hawayenta ta share kan ta zagaye shi tayi sama da gudu tana kuka.

Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka yake jan kafafunshi jin gwiwowinshi na shirin sagewa su butulce mishi wurin kasa ɗaukar gangar jikinshi, zubewa yayi kan kujera zuciyarshi na wani irin yamutsuwa tare da kwakwalwan kanshi dake ta aikin tariyo kalamanta, wani irin sanyi yaji yana ratsa shi a hankali zazzafar zazzabi ya soma sauƙo mishi, kalamanta sun mishi nauyi sossai, rashin fahimtar shi da bata yi ba sai ya so haukata shi,
Miƙewa yayi don barin gidan ko zai shaki iska mai kyau sai ga Maami ta shigo.

A hankali yace
"sannu da dawowa Maami"
Kallon shi tayi da mamaki don ba halin shi bane hakan, sai kuma ta kula kaman bashi da lafiya ne kaman bazata yi magana ba sai kuma tace
"yauwa! Lafiya kake kuwa? Ko dai cikin shaye-shayen ka shayo abin da yafi karfin ka?"
Idanunshi ya runtse da ƙarfin gaske wani zafin ya sake ratsa zuciyar shi, dama haka ake welcoming wadda ya ɗauki hanyar tuba? Dama wannan na daga cikin kalubale da illar shaye-shayen ko kuma daga mahaifiyarshi da matar shi ne?

Be iya ya tanka ba ya fice daga gidan, da kallo ta bishi har ya bace kan ta haura stairs, ɗakin Alayah ta tura don dubata sai ta sameta zaune tana game a wayanta kaman ma bata yi kukan matsalar gidan aurenta ba, taji sauƙin abin sossai da ta samu fitar da abin da ke ranta kuma da gaske ta gama zama da Mukhtar.
"Sannu da dawowa Maami"
"yauwa binty ana hutawa ne?"
Kai ta gyaɗa tana murmushi
"Maami kin yi waya da asibitin? Sun yarda zasu bari a ganta nan kusa?"
Kai ta gyaɗa tace
"Eh mun yi magana, baba ma dai ya bada shawarar a fitar da ita waje kawai amma dai muna nazarin hakan da umar, kar ki damu zata samu sauƙi in shaa Allahu. Yanzu dae albishir"

Murmushi ne kwance bisa fuskanta da ya ƙara mata kyau sossai tace
"Goro Maami fari ƙal ma ba ja ba"
"Kin samu admission a skyline university"
Tsalle ta tashi zata yi da hanzari Maami ta riƙe ta tana dariya, rungume Maamin tayi hawaye na tsillo mata tace
"Alhamdulillah Maami na gode, na gode sossai Allah ya saka miki da alkhairi ya shirya miki zuri'a, Allah ya amsa dukkanin Adu'o'in ki ya biya buƙatun alkhairi"
Cikin murmushi ta amsa da Ameen, sai kuma ta ɗago ta
"Amma me ya sa kika zaɓi cyber security bayan baya cikin duk courses da kika lissafo min kina so?"
Cikin murmushi tace
"haka kawai na ji ina son karantar shi, kila shine Allah ya zaɓa min"
Har daren ranar murna take da samun admission nata, Allah sarki Da ummi na cikin koshin lafiya da sai tafi kowa murna ta tabbatar da hakan.

Da dare ta isa jikin kofa don rufewa kenan taji kaman ana magana murya sama, idanunta ta lumshe babu shakka muryan Abba ne kuma ta tabbatar da Maami yake don kaman magana ne da ya dangancesu Dukda bata jin shi clearly, da jikin kofan ta jinginu ba zata taba son su kasance tasgaro ga rayuwar Maami ba, ita ce mutum na farko a rayuwarsu da ta nuna musu suma mutanene kaman kowa suna da muhimmanci kuma suna da Ƴancin rayuwa yadda kowane mutum ke yi, ita ta basu mafaka a sadda suke tsakiyar rana da kunar zafin ta, da ba don ita ba da kila yanzu babu Umminta don ta tabbatar ba jinya Abban meela ze yi mata ba, sannan ga damar karatu ta bata wadda zai sauya mizanin rayuwarta, amma su kuma suna kokarin dakile farin cikinta da zaman lafiyanta, tana jin irin barazanar Abba har da aurenta yayi mata kan ya zo ya wuce kaman iska.

Ta jima tsaye wurin kan ta isa ga gadonta ta kwanta idanunta runtse tunaninta ya tafi gabaɗaya ga neman mafitar wannan matsalar kuma, cikin bacci ta ji ana buga mata da sauri kuma a ɗan tsorace ta miƙe zaune, idanunta ta kaikaya kan ta sauko gabanta na faɗuwa ta tsaya nesa da kofan

"wa....waye?"
Shiru aka yi sai aka sake knocking
"waye ne?"

****

Zaune su ke a club ɗin shi dae ko idanunshi baya buɗewa in banda ma matsawar su Nawwaz babu abin da zai kawo shi club ɗin amma sune kaɗai abokan shi su ne masu debe mai kewa cikin sabuwar rayuwar da ya tsinci kanshi, En matan dake ta damunshi ne ɗaya ta matso ta shafa shi
"Mukhy whats wrong with you? We dont like this mukhy we want our old mukhy back, menene kake so? Ka zo mu debe maka kewa mu mantar da kai duk wani damuwa, mu baka farin cikin da ka jima baka samu ba..."
Hannun da take shafa shi ya ture ba tare da ya buɗe idanun ba
"don't you dare touch me again"
Ya faɗa chan ƙasa ƙasa har yanzu kalaman Alayah ne ke farautar rayuwarshi, idanunshi ya buɗe ya sauke kan smart dake rungume da yarinyar da ta gama lafaza shi a yanzu tsaki ya ja me karfi barikin fa kenan, Tsam ya miƙe tare da miƙawa smart din hannu ya bashi key.

Ture yarinyar smart yayi tare da Miƙewa
"ka san bama barin ka driving cikin situation din nan muje in kai ka inda zaka"
Nawwaz ma Miƙewa yayi suka fito su huɗu zuwa motar shi, da gudu suka bar club ɗin, sauran su biyu duk a Buge suke yayinda smart dake driving ke bankawa cikinshi Shisha, shi dae oga kwata Kwata na kishingide abin duniya ya dame shi, daidai wani unguwa motar ta tsaya chak, idanunshi ya buɗe ya dubi smart
"ya dai?"

"Wlh ban sani ba mukhy ko zaka duba mana don ko na je babu abin da idona zai gani?"
Gaban motar ya buɗe ya fice yayin da smart ya buɗe mai bonet daga ciki, ganin ya ɗan jima yasa duk suka fito, wurin shiru sannan hasken wurin ba sossai bane, layi ne a chakude da gidaje kala uku akwai na masu kuɗi jefi jefi haka akwai na daidai misali sai kuma na talakawa da suka fi yawa.

Wata yarinya ce da bata wuci 16 ba ta taho hannunta riƙe da tray tana kuka, kuɗin cinikin ta ta ɓatar gashi matar ubanta bata da sauƙi akan sana'arta shiyasa ta kai yi warhaka bata koma gida ba, ta sa baban ta da Yayanta yanzu sun dawo idan kum yaddikonta ta kanainayesu da maganganun ta ɗaure ta zata kara yi yau ta shiga uku da babanta tunda duk abinda yaddikonta ta faɗa daidai ne, har ta wuce su ma bata maida hankali kansu ba sbd nata matsalar.

Nawwaz ne yace
"kai yarinyar nan tayi smart, anya ba zamu latsa ba?"
Area ɗin suka dudduba jin shiru sossai yasa babu wani tunani yadda suka saba kayansu sa'i da lokaci suka bi bayanta, da bakinta suka fara da karfi suka ɗaure suka jata gefen ciyayi, sam Mukhtar be san me suke ba don hankalinshi na kan duba motar sbd babu abinda yake so a yanzu irin ya je gida ya kwanta ya cigaba da tunani.

"Smart tada motar mu ji"
Yayi maganan ba tare da ya ɗaga kai ba, jin shiru ya sa ya ɗago ya dae san sun fito waje to komawa suka yi? Sake motar yayi yana zagayowa sai de be ga kowa ciki ba, jin kaman nishi ya sanya shi ɗaga kai da sauri ya kallesu chan da alama ma sun gama lalata rayuwar yarinya da gudu ya isa ya ture Nawwaz, ɗagowa yayi ya tsinkawa smart mari
"Me kuka yi? Me kuka aikata? Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Daidai lokacin yarinyar ta kwalla ihu sai ga hasken touch ana kiran sunan da basu gama gane na wacece ba, da gudu suka yi mota Nawwaz janye da Mukhtar da da alama tsayuwa ya so yi, ihu yaron ya fara yayinda tuni smart ya figi motar baban ne da yake gani dishi dishi ya riƙe plate number ɗin, babu shakka sun kassara rayuwarsu ko daga yadda yayan yarinyar ke kuka sossai yana dagota ya rungume ya san hakan....

*Toh fa, Mukhtar sawu ka taka ko ya abin yake ne?*

*karku manta book 2 na kuɗi ne, muna gama book 1 zamu ɗaura in shaa Allah zaki iya yin payment ɗin ki anan kan a gama ɗin
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shedar biya ta
09039206763 in shaa Allah za'a saka sunan cikin list na paid da muke dasu ƙasa.
Thank you sai na ji ku


🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Seventeen*

"Me kuka aikata Nawwaz? Akan me zaku yi raping yarinya alhali kun bar yammata sama da hamsin waenda suke shirye da tayin ku? Why? Why??"
Gabaɗaya hankalin shi ya tashi irin yadda ba'a zato, su karan kansu sun shiga mamaki, sun ga dae har a ƙasar da ma ya fi Nigeria tsaro da komai yayi raping yarinya wanda ma sanadiyar zamanshi prison kenan har aka kore shi ya dawo Nigeria da karatu, to me zai dame shi anan da ma ba lallai a bi diddigi ba ko ma an bi suna da kuɗi wadda sun tabbatar a ƙasar nan zai musu maganin komai.
Ganin suna kokarin tursasashi maida komai ba komai bane yasa ya daka wa smart tsawar ya tsayar da motar kuma su fitar mai daga cikin mota, haka ya baɗe idanunshi da toka sai da suka fita ya zagaya ya figi motar kaman baya son ranshi, har lokacin wani irin tension yake ji a cikin jikinshi gidanshi ya ƙarasa a parlor ya zube, ya rasa ma kalar tunanin da zai yi me yaran nan suka aikata haka?

Bai san iya adadin lokutan da ya ɗauka a haka ba, a hankali ya buɗe idanunshi da suka sake shanyewa wayanshi ya zaro ya duba sai ya ga biyu saura, contact ɗin shi ya shiga ya samo Layin Maami ya zubawa idanu, a hankali abinda be taɓa zaton ze yi ba a rayuwarshi tun tashin shi wato hawaye ya cika idanunshi, damuwar da yake ciki yana son jin ko da muryarta ne kila ya samu sassauci, kira ya danna mata ya zubawa wayan idanu ba lallai ta ɗauka ba, dab zai tsinke ta ɗaga, a hankali ya sa a kunnen shi ya ji muryarta cikin bacci tana furta
"Assalamu Alaikum warahmatullah Mukhtar? Lafiya?"
Idanunshi ya runtse hawayenshi suka zubo, a hankali yace
"Wa'alaikissalam warahmatullah Maami..."
Sai yayi shiru ya rasa ma me zai ce mata, bayan duk abubuwan da ya mata a rayuwa ya kuwa chanchanci ta taya shi shiga damuwa saboda damuwar shi?
"Uhmm ya aka yi? Menene?"
Uwa kenan, ya faɗa a ranshi yana sake jin wasu sabbin hawayen sharr, zuciyarshi na wani irin chunkushewa cikin tsananin damuwa da karaya, gaɓɓan jikinshi duk sun yi sanyi saboda rashin natsuwa da bashi dashi gabaɗaya kwanakin, har zafi zafi yake ji a cikin jikinshi kaman me masassara.
"Maami ina cikin damuwa ne, na kasa bacci, na kasa samun natsuwar zuciya na rasa abin da zan yi na ji daaɗi, ki taimake ni please"

Wani abu taji ya tsarga mata har cikin ranta, Allah sarki uwa bata san ta miƙe zaune ba, a hankali tace
"baka da lafiya ne? Ka je asibiti?"
Girgiza kai yayi
"Maami lafiyata ƙalau kawai komai ne baya min daaɗi Maami"
Shiru tayi na seconds kan a hankali cikin son tabbatarwa tace
"ka sha wani abu ne da ya fi karfin ka ko?"
Da karfi ya runtse idanunshi dama ya san zata yi tunanin hakan, kuma ya ji a jikinshi ba zasu taɓa fahimtar nadama da tuban shi a kusa ba, yayi mamaki ma da ta saurare shi, a hankali yace
"Maami wallahil azeem rabona da in sha wani abu tun ranar da muka zauna gaban baba"
Nannauyar ajiyar zuciya da har ya ji daga inda yake ta sauƙe.
"Ka je kayi alwala ka faɗawa Allah matsalolinka in shaa Allah zaka samu natsuwa"
Kai ya gyaɗa kaman karamin yaro kan yayi mata godiya suka kashe wayan a tare, Miƙewa yayi ya nufi ɗakinshi har ya shiga sai kuma ya tsaya kaman me nazari, wardrobe nashi ya nufa ya duba ya ɗauki three quater da wani armless Black shirt tare da sabon towel ya fice daga ɗakin don be yarda da ɗakin ba har wani kyamar ɗakin yake ji.

Ɗakin Alaya ya shiga lumshe idanu yayi yana sake jin sabon hawayen tausayinta, anan ya mayar da ita prisoner a cikin wannan ɗakin ya shigo ya jata gaban abokai ya ɗura mata abin maye ba tare da ya damu da cewa ita ɗin tsarkakkekkiya ba ce, bayin ta ya nufa yayi wanka ya sanya kayan ya zo ya tsaya kan sallaya, a hankali ya ji Muryarta a sadda take ce mai a lokacin da ya ɗauketa daga asibiti zuwa Hotel zai yi sallah.
"Ya Mukhtar namiji fa daga cibiyar shi zuwa guiwowinshine al'auranshi, Kaga zaka yi sallah kuma wandon be kai guiwa ba be kamata ba"
Yana iya tuna yadda take mai magana a lokacin ma cike da tsoro.
Ɗakinshi ya koma jallabiyar nan da Dr ya taɓa bashi kyauta ya ɗauka ya saka kan kayan ya dawo ɗakin ya kabbara sallah cike da Fatan Allah ya amsa ya sassauta mishi abin da yake ji yana damunshi.

***

"Ki buɗe"
Abin da taji kenan da ya sanya gabanta dokawa.
Cikin rawar murya tace
"Abba? Lafiya?"
A harzuke yace chan ƙasa
"na ce ki bude kofar nan"
Hannunta na rawa ta buɗe da sauri ta ja baya ganin ya afko ya rufe
"ke! wace irin mutum ce ke? Dama Alhassan ya min gargadi duk inda kuke babu alkhairi a tare daku musamman ma ke, kin san me kike shirin aikatawa?"
Girgiza kai tayi tana jin tashin hankali na bijiro mata.
"Zaki kashe auren macen da ta taimake ki ta taimaki mahaifiyarki ta so ki tsakani da Allah, kin mata adalci kenan? Kin san me uban su ya fi tsana? To babu abin da ya ƙi jini a duniya irin saki, barin ma na ƴar cikinshi, me kike tunanin zata fuskanta ta koma ga mahaifinta tsofai-tsofai da ita da takardar saki?"
Zuwa wannan gaɓar tuni hawaye ya wankewa Alaya fuska, sai ta ji murnar karatunta ya koma ciki, in tayi wa Maami haka bata kyauta ba, sai dae ina zasu je? Ya zata yi da ummin ta?
Kaman ya shiga zuciyarta yace
"Zan ba ki makudan kudade da zai ishe ku rayuwa, kuyi nesa da mu da rayuwarmu dama Mukhtar ba soyayya tsakaninku zan sa shi sakin ki a gobe ku yi nesa da mu na har abada"
Kanta ta mayar ƙasa hawaye ya silalo mata.
"Kin amince?"
Kai ta gyaɗa a sanyaye
"daga yau bana so ki sake kwanar min cikin gida a gobe zan sallame ki"
Yana kai nan ya juya ya buɗe kofa ya fita, a wurin da ya barta ta sulale ta zauna tare da fashewa da kuka, sake tura kofan da aka yi ne yasa tayi saurin ɗagowa a firgice ta miƙe tsaye!

****

Mahaifin wannan yarinya da aka yiwa fyade ne ya riƙe hannun Yayanta dake kuka kaman ranshi, a hankali cikin lullube tsananin tashin hankalin shi yace
"karka taɓa ta Bashir, barta bari na ƙira dan uwana"
Cousin nashi ne comissioner of Police iyayensu mata sun haɗa uba, kuma kusan kaman abokai suka tashi Dukda tazarar arzikin ubanninsu ya banbanta nesa ba kusa ba, ringing uku ya dauka
"Ɗan Uwana yau kuma da mu aka tuna?"
Hawaye ya sirnanowa dattijon cikin karaya yace
"Ɗan Uwana wannan kiran na neman agaji ne, ka taimakeni ina da da bukatar ka a yanzu, an wulakanta ni an tozarta rayuwar ƴata an illata min yarinya"
Hankalinshi ya dugunzuma ya tashi jin dattijon na kuka sossai, tabbacin gashi nan ya bashi da ambulance bayan jin mummunan ta'asar da aka yi mata.

Ba'a fi awa ɗaya ba sai gasu har lokacin daga baba har Bashir an rasa me ba wani haƙuri sai kuka suke yi, da ambulance da wasu polisawa aka zo, Allah sarki yarinya abin tausayi haka aka ɗaga ta zuwa motar asibiti da wasu Police mata ya haɗa su inda ya tsaya gun ɗan uwanshi don jin kanun zancen.
Be ɓoye mishi komai ba duk ya faɗamai har da plate number ɗin, kwarai ya jinjina kokarin baban a take a daren suka soma bin hanyoyin da duk za'a bi don gane me wannan motar, abin ka da comissioner of Police ne ke ciki tsundum ba'a kira assalatu ba sai da aka gano motar Mukhtar ce, su ba ɓoyayyun mutane bane, don haka a take ya bada umarnin a je a kamo mishi Mukhtar dama kuma yana da ajiyayyen record a interpol, me hali ba zai taɓa fasa hali ba, maza maza a kawo shi.

Makara yayi, a sadda ya buɗe idanunshi yaji ana sallama a masallaci, da sauri ya miƙe be tsaya wanka ba yayi alwala ya taho ya zo yayi sallah, anan ya zauna duk wasu Adu'o'i ba wai ya iya bane tunda karatun islamiyyar shi na je ka na yi ka ne yayi, zafin mahaifinshi yake ji har ranshi, yana tuna a lokacin in an bugeshi ya ce ba zai kara zuwa ba Maami na masifa haka Abba zai baɗe idanunshi da toka ya bashi goyon baya kuma ya hana shi sake zuwa sai ranar da ya ga dama, yana tuna har a gida an sha kawo malamai musamman don shi yana korarsu da sharri kala kala Abba be taɓa cewa hakan ba daidai bane, be taɓa gyara mishi ba, be taɓa tsawatar mishi ba...

Door bell ake ta dannawa wanda hakan ya sa ya miƙe yana duba time, shidda ma be cika ba lafiya?"
Yana isa ya buɗe sai idanunshi suka sauƙa kan polisawa kusan guda biyar dake tsatsaye gaban kofan parlorn they are even armed gasu manya manya, murmushin takaici yayi dama ya san hakan na iya faruwa, sai dae kuma gabanshi dake ta faɗuwa da tsoron halin da zai jefa Maami da Alayah idan maganan ya riske su, karamin ciki ne da ita idan yayi sanadin shi fa? Sai yanzu yake jin wani irin son abun cikin nata na shiganshi, bakin Police ɗin ya zubawa idanu a sadda yake cewa
"Mukhtar hammad you are under arrest for the suspect of rape, u have the right to keep quit as anything you utter will be Proof against you in d court"
Hannayenshi ya dunkule ya miƙa musu suka sanya ankwa, sai da suka fito ya ga ashe akwai wasu zagaye da motar da ya dawo dashi jiya, daga shi har motar aka ja sai Police station.

*Kuyi hakuri da Page na yau, ban wani zauna bane. Thank you*


*karku manta book 2 na kuɗi ne, muna gama book 1 zamu ɗaura in shaa Allah zaki iya yin payment ɗin ki anan kan a gama ɗin
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shedar biya ta
09039206763 in shaa Allah za'a saka sunan cikin list na paid da muke dasu ƙasa.
Thank you sai na ji ku


🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO


Please Login or Register in order to submit comment