Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Eighteen*

*Ku yi haƙuri ku sa min Abdulraheem a Adu'o'inku please Allah ubangiji ya bashi lafiya gobe zamu yi tafiya zan kai shi asibiti, idan na samu sarari zaku ji ni in shaa Allah*

"Maami"
Ta kira sunan da tunanin kar ta ga fitan Abba daga ɗakin nata ne, gabanta ta iso ta riƙo hannunta..
"Binty me ya faɗa miki?"
Shiru tayi kanta ƙasa ba tare da tayi magana ba sai hawayen da ya cigaba da zuba mata
"kar ki damu na jima da tashi sanadiyar kiran Mukhtar to sai na kasa komawa bacci, ina cikin nafila na jiyo motsi da kuma buɗe kofa hakan ya sa na fito, har ya fice bai san da tsayuwata ba kuma ba zan taɓa faɗa mishi na ga zuwan shi ba, abinda kawai nake son sani shine me yake so da ke?"
"So yake mu yi nesa da ku"
Girgiza kai tayi ta sake riƙe mata hannu
"kar ki ɗaga hankalinki Alaya, ban shigo rayuwarku don in lasa muku zuma a baki in kuma janye ba, na san kila har barazanar da yayi mini ɗazu ya faɗa miki don ki ji ba daaɗi karki damu na fi kowa sanin Alhj, gidan shi dae zaki iya bari amma ba dae rayuwar mu ba, mun riga mun zama en uwa, har gobe ni matsayin uwa nake a gareki yaya a wurin umminki kinji?"

Rungume Maamin kawai tayi tana murmushi me haɗe da hawaye, Maami ta zama komai na rayuwarsu, da gaske Allah ya turo musu ita ne don ta taimaka musu ta fitar da su daga uƙubar da suke ciki, lallashinta Maami tayi ta yi har sai da ta ga ta koma bacci kan ta fice daga ɗakin, bata iya ta yi baccin ba ita kam haka ta kwana kai wa Allah damuwowinta, da asuba tare da masu aikinta ta shiga kitchen suka kama aikin breakfast, tsab suka gama ta bar su su shirya ta haura sama tayi wanka, tana fitowa Alaya ma na fitowa, gaishe ta tayi ta amsa fuskanta da fara'a as always tana mata ya jiki, ita dae Alaya na matuƙar mamakin hallayyar Maamin sam bata yarda da sa damuwa a ranta har ya nuna ga fuskanta ba.

Suna isa dining da niyyar cin abinci sai ga Abba ya shigo, Maami ne ta fara gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa, Alaya ma ta gaishe shi ya amsa da kyar, Maami ce tayi serving nashi ya ja gabanshi ya soma ci, ita dae Alaya juya spoon ɗin kawai take kaman yadda ta kula Maami ma ba wani cin kirki take ba, Tv dake aiki daga parlor ne aka soma labaran safiyar...
Da wani hanzari duk su uku suka miƙe tsaye, Abba ne gaba wurin isa cikin parlorn daidai me kanun labaran na cewa
"Mukhtar dai ɗa ne ga ɗan takarar Gomna wadda aka fi sani da honourable Hammad Abdulhameed chanji... In ba'a manta ba Mukhtar dae na da tabo a hukumar na en sanda inda ya ci firsuna na wa'adin shakaru takwas a ƙasar waje to dai gashi nan labari ya sake maimaita kanshi ku biyo ni don jin cikakken labarin"

Kokarin zubewa ƙasa Abba yake Maami da ita ma take jin bata da wani karfi, firgici da damuwa haɗe da wani irin tashin hankali suka rufeta tayi kokarin tura shi a madadin ya kai ƙasa sai ya zube kan kujera yana jiƙewa da wani gumin tashin hankali.
Alayah ce da ita ma karfin hali tayi wurin riƙe Maami suka zauna a tare, babu wadda ya iya magana sai tvn da suka ƙurawa idanu suna jiran kanun labaran kaman kuwa a mafarki aka hasko hannayen Mukhtar ɗaure da ankwa

"A safiyar yau ne en sanda suka yi tattaki har gidan ɗan ɗan takarar nan honourable hammad Abdulmajeed chanji wato Mukhtar hammad chanji inda babu ɓata lokaci suka kame yaron nashi bisa zargin aikatawa yarinya karama ƴar shekara 16 fyade a daren na jiya, inda suka bar yarinyar cikin mawuyacin hali ga wakiliyar mu nan daga asibitin da aka kwantar da yarinyar"
A take aka hasko iyayen yarinyar mahaifinta na kuka, haka en uwanta tsiraru da suke asibitin ɗaukewa aka yi aka dawo kan ɗan jaridan ya cigaba da cewa
"a wannan lokaci da siyasa ke gab da wanzuwa a jibi jibin nan jama'a dayawa da suke ƙarƙashin tafiyar ta honourable sun soma janyewa, ga kaɗan daga bakunan jama'ar"
Wani aka hasko yana cewa
"mutumin da ya gaza ba ɗan shi tarbiya taya zamu yi zaton zae tafiyar da mulki, wannan halaka mu zai yi bama yi.."
Na bayanshi suka amsa da bama yi bama yi, aka sake hasko wani haka dae aka yi ta hasko mutane suna fadin albarkacin bakin su duk babu wani daaɗin ji..

Wayan Alhj en jam'iyyarsu suka soma kira sai dae motsin kirki ya gaza, jikinshi banda rawa babu abin da yake, shikenan abin da yake gudu yana tunanin yana da ikon dakatarwa ya faru, wannan shine ta faru ta ƙare ga ƙoshi ga kwanan yunwa! Ya gama shiryawa da Alhj Hassan akan in ya kori su Alayah dole in sun tagayyara su koma mishi tunda shi kadai suka sani sai gashi ɗan da ya fifita ya ɓallo mishi ruwa, ruwan da zai mishi ɓarnan da baya tunanin zai taɓa taruwa ɓallewa zai yi ya shiga gari, da sauri ya ɗauko wayanshi dake ringing ya duba, chairman na party din su ne.

Wani irin faɗa yake da masifa, akan me Abba ba zai tare danshi ba in ya san bunsuru ne yanzu suna ji suna gani haka partynsu zata ci kaye, sun yi duk yadda zasu yi sun danne batun baya amma wannan ya tashi musu kamar wutan daji kowa sai gani yayi a duniya, shi dae ya kasa cewa komai tunda hankalin Ƴan partynsu ya riga ya tashi haka wannan abu ba mai gyaruwa ba ne, Maami da ke zaune kaman mutum mutumi da Alaya da kanta na ƙasa zafin da ranta yayi ba sossai ba tunda dama ta riga ta cire rai da Mukhtar ta san ba zai taɓa gyaruwa ba, girgizan da tayi ma na don abun cikinta ne, hannunta dafe da cikin tana tunanin me wannan ɗa zai ɗauketa a rayuwa? Kawai sai faɗuwar Abba suka gani...

****

"ba za kayi magana ba?"
Shiru yayi yana kallon jibgegen ɗan sandan dake gabanshi cikin su biyar da suke tsaye, be tanka ba sai ma idanunshi da ya lumshe Allah kaɗai ya san abin da yake ji cikin ranshi, ina ma da zai iya saka hannu a kai yayi ta ihu ko duniya zasu fahimci tashin hankalin da yake ciki, duk yadda aka yi ya san zuwa yanzu magana ya riga ya kai kunnen Maami da Alayah, zasu sake yarda da shi a duniya? Menene wannan yake farautar rayuwar shi? Ko dai zunubanshi ne ya soma girba tun yanzu? Kulkin da aka sauƙe mishi a gwiwa ne ya saka shi buɗe idanun yana kallon Police ɗin ba tare da yayi motsi ba, ya tabbatar daga safiya zuwa yanzu da ake durfafan azahar da gwiwowin nan zasu fita da sun riga sun bar jikinshi, tun yana ma jin azaban dukan har ya daina ji, nauyin kirjinshi ya fi mishi azaba fiye da dukan, sai zullumi yake kila ciwon zuciyar Alaya ya tashi, kila Maami tana chan tana ta kuka watakila ma tana asibiti a kwance hawan jininta ya tashi, tsintar bakin shi yayi da furta
"Astagfirullah! Ya Allah ka sassauta musu"

Duk yadda suka yi yayi magana ya ƙi cewa komai, gabaɗaya idanunshi da fuskanshi sun sauya sai gumi yake jika shi, kafafunshi baya ko motsa su haka suka haƙura suka fice, suka je suka sanar wa comissioner, asibiti ya ƙira don jin ko ta farka aka tabbatar musu da ta farka sai dae ba kanta, statement din ta suke son samu su tura shi court don haka ya bada umarni a cigaba da mishi horror kala kala har sai ya faɗi gaskiya.

****

Daga Maami har Alayah babu wadda ya motsa tun da suka shigo asibitin, dangin Maami da na Abba na nan birjik Abba na halin mutuwa ko rayuwa sbd jininshi da yayi hitting fiye da ƙima, Ƴan uwan Maami sai jimami suke yayin da Ƴan uwan Abba ke jefo kananun maganganu wadda kai tsaye Maami suke alaƙantawa da lalacewan Mukhtar, ita dae tana jin su bata tanka ba kuma ta gode Allah da yaddikonta dake wurin ta hana duk sisters din ta magana, Baba ne ya shigo ward ɗin da sauri Maami ta miƙe ta isa gabanshi hannunta ya riƙo
"Faɗimatu!"
Kaman jira take ya kira sunanta kawai ta zame ta fashe da wani irin kuka dake cin ta a rai, Mukhtar kila sai ya kasheta ne hankalin shi zai kwanta, in ta bar mishi duniyar sai ya fi jin daaɗinta, zuciyarta ya riga ya kuntata fiye da tunani, ita kaɗai ta san me take ji a ranta kunnuwanta kawai ke jin duniya gabaɗaya na tsinewa Mukhtar, kukanta sai da ya sa mutane dayawa kuka ciki har da Alayah, mahaifinta ya ɗago ta suka isa kujerun gefe guda suka zauna nasiha ya dinga yi mata akan jarabawar Allah, har misali yake bata da ƴaƴan annabawa suma Allah be bar su ba, ko ta manta jinin Annabi Adam shi ya fara kisa a duniya? Ta mance ƴaƴan annabi Yakub ɗan uwansu suka so halakarwa mahaifinsu yayi kuka har idanunshi suka makance? Ko ta mance ɗan annabi nuhu da ya kafurce yayi ikirarin hawa tsauni zai taimaka mishi wurin gujewa fushi da azabar Allah kuma Allah ya halaka shi a kan idanun mahaifinshi? Ta natsu ta cigaba da Adu'a idan yana cikin masu shiryuwar Allah zai shirya shi, sossai hankalin ta ya kwanta da nasihun baban, inda ya duba jikin Abba kan ya ɗauki yaddikonta suka tafi kafin ya tafi sai da ya sake kwantar musu da hankali ita da Alaya.

Masallacin asibitin suka je suka gabatar da azahar, Adu'a sossai Maami tayi kan suka fito zuwa ɗakin abinci da aka yi ta kawowa ta saka Alaya a gaba ta ci ita kuma ta sha baƙin shayi, call ne ya shigo ma Aunty ruqayya ta duba kan tace
"Allah sarki umar ne, kila labarin ya je mishi hankalin shi kuma zai dawo kan Adda ruqayya gashi jiya jiyan nan da safe ya koma"
Maami ce ta mika hannu ta karɓa dama ita ma tunanin shi take a ranta, ɗagawa tayi tare da Miƙewa ta matsa daga inda suke sun jima sossai suna magana kuma shi ma ya sake bata kwarin gwiwa, so ma yayi ya zo Dukda ba don Yayan shi ko Abbansu zai dawo ba don Maami ne kawai to amma ba zasu bar shi a wurin aiki ba, abubuwa dayawa na hannunshi.

Har zai kashe tace
"Amma auta ka ji daga shi Mukhtar ɗin?"
Daga chan ya ɗan yi shiru na seconds kan cikin natsuwa ya ce
"Maami na ji, sai dae har yanzu ba wani abu be ce musu komai ba, kuma ba horon da basu mishi ba"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tace
"Toh na gode sai anjima"
A hankali ya sauƙe wayan ya bi da kallo, uwa fa kenan!
Sai kusan la'asar Abba ya farka, ko magana ya kasa, abinci ma da kyar ya sha shayi, kab rayuwarshi be taɓa jin haushin Mukhtar irin na wannan karo ba, wani irin karta ranshi ke yi, Mukhtar da ya yarda dashi shine ya cuce shi, ya tarwatsa mishi siyasa, haushin da yake ji na kowa yasa mutane suka ɗan ragu, guards sun cike wurin sbd Ƴan jarida da suka taru kaman an kira su, ganin haka yasa Maami ta ce ɗan uwanshi ƙanin Alhjn a cikin mahaifinsu zaid ya zauna dashi ita zata koma sbd Alayah, har zata fita ta tsaya ta dawo da baya kadan tace tana kallon Abban da karyayyen kallo zafin kirjinta na fita har a kan harcenta.

"Babu wata uwa da zata yi farin ciki da lalacewan ɗan ta, amma ko babu komai yau na ji daaɗi da muka raba ɗacin lalacewar Mukhtar wadda kai ne sanadi, ko babu komai Allah ya nuna maka ba sai ka zalunci wasu ne zaka yi nasara ko ka fadi ba, Allah baya zalunci kuma ba ya barin me yi, ko ka nufi gyara kuskuren da ka tabka daga yanzu ko kuma ka cigaba da girban abin da kai ka shuka dama na sha faɗa maka akwai ranan ƙin dillanci"
Tana kai nan ta juya ta fice tana goge kwallar ta, idanunta ke haska mata kaman yau ne tana shirin tarbiyatar da yaronta Alhj na rusawa daki-daki, shi karan kanshi be ga laifinta ba sai ma kunya da nauyi da suka rufe shi, idanunshi gabaɗaya sun rufe ya cutar da rayuwar Mukhtar sossai wadda sai a yanzu yake jin be kyauta ba, kunyar mutanen duniya ya rufe shi, tsoro da shakkar kamuwar tsinuwar bakinsu ya lulluɓe shi, shine da kaso mafi tsoka ya sani amma shi a ganinshi duk soyayya ce ashe ba haka ba ne, hawaye ne ya gangaro mishi.

"Yaya ka yi haƙuri kayi kokarin cire damuwa a ranka in shaa Allah komai zai wuce"
Zaid ya faɗa, murmushi kawai yayi me ciwo be sake cewa komai ba.

****

"ba mutum ɗaya ba ne...!"
Ta faɗa da kyar a sadda ta farka cikin kuka, ƴar sandar ta gyara tace
"Ki kwantar da hankalinki kin ji? Ki natsu babu wadda zai sake cutar dake yanzu kina hannun hukuma ne kuma ba sa zalunci bare cuta, ki gayamin duk abin da ya faru kin ji?"
A hankali ta ba yar sandar labari ita dai ta san mutum uku ne, kuma sam bata lura da ko sun kai nawa tsaye a wurin ba hankalinta na kan kudin da ta batarwa yaddikonta sai a lokacin mahaifinta yake jin wasu abubuwan ma da be san suna faruwa da ita a gidan ba, kai tsaye wannan Police ta nufi office nasu.

C.P ta kaiwa report din yana dubawa yace a je a sake tuhumar muktar har sai ya faɗi sauran, duk yayi ignoring calls da yake samu daga sama saboda wannan case ɗin ba mai kasuwa ba ne, ko ba familynshi aka taɓa ba sai inda karfinshi ya kare bare na gida ne, cikin kokarin cika umarni wasu daban suka sake nufan ɗakin na Mukhtar don tambayar shi da kyau..

*littafin nan paid ne book 1 ne kaɗai free
Pay ur 500 through dis account
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shaidar biya ta
09039206763*



🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Page Nineteen*

*Assalamu Alaikum warahmatullah, Fatan duk muna lafiya? Ina ganin ya kamata mu dinga yiwa juna adalci, ina nufin tsakanin makaranta da marubuta, lallai a tafiyar da muke zuwa yanzu na fahimci cewa makaranta ku ke da kaso mafi girma na sanya marubuta aran halin da ba nasu ba su yafa, kuma kun fi kowa yayata cewa marubuta na da girman kai, this and that, ina magana ne based on experience ba da ka ba so duk wadda be ji daaɗi ba yayi haƙuri kuma a gyara, Marubuci zai ɓata lokaci kwarai wurin bincike da rubutu, ya kashe duk wasu abubuwa masu muhimmanci nashi ya zauna don faranta muku dayawa kuna bibiya kuma ana ƙaruwa amma kalmar an gode ma ya zama matsala bare comment, ana tafiya dai a haka saboda burin kowani marubuci ya isar da saƙon da zai anfani al'umma, muna cikin wannan tafiyar na ce yarona ba lafiya zan kai shi asibiti billahi wasu ba su iya cewa Allah ya yaye ba, amma suna gaba gaba a wurin bi na Pc ana cewa ana ta jira shiru, a'a ana kashe musu kwarin gwiwar karatu, an shanya su this and that! Sister ashe babu daaɗi? Yanzu idan na buɗe na ga wannan saƙo saboda bin cewar Manzon Allah na ka faɗi alkhairi ko kayi shiru na ƙi magana sai fa a ce girman kai ne ko wulakanci ko? Toh Allah ya kyauta. Na kawo wannan ne ba don rashin ɗa'a ba don nan ɗin gidan tarbiya ne ba haufi sai don mu tattaru mu gyara, mu zama masu adalci a tsakanin juna, adalcin ne yasa duk ba zan yi Page ba sai na zo na faɗi dalili, don Allah mu karfafawa juna gwiwa wurin zamantakewa da kuma cigaban juna don kowa na da ƙaruwarshi a duk wani tafiya na duniya. Bissalam*

••••

"Astagfirullah"
Ya furta bayan ya shafa dogon adu'ar da ya jima yana yi tun bayan sallame Sallar asuba da ya gabatar, ya godewa Allah maɗaukakin sarki da ya kasance adalin adilai, maji ƙan bayi wadda bai taɓa tantance da yaren da za'a roƙe shi ya amsa ba, don da be san ta yadda zai fara ba, Sallar ma yayi shi ne babu tabbacin isar shi saide ya roƙa akan Allah ya shirya shi ya ɗora shi hanya madaidaiciya, ya kuma bashi ikon gyara kura-kuranshi tun kafin ya koma gareshi a zero, Shigowar wani kurtun Police ne ya sa shi sa hannu ya kare haske tarrrrr da ya bayyana mishi yana kokarin illata jijiyar ganinshi don ɗakin duhu ne yake zaune ciki.

"Ana buƙatar ganin ka"
Ya faɗa ya ja baya ya tsaya rike da kulkin shi, a hankali Mukhtar ya fito kafafunshi sun yi kumburar da baya iya taka su da kyau, dafe da gini ya dinga tafiya har suka isa office ɗin na C.p, kaman yadda be kalli duk jama'ar da suke kallonshi ba daga jami'ai har civilians haka be tanka maganganun da suke jifan shi dashi ba, ko da suka shigo be ɗaga idanunshi ba ya ja ya tsaya, a tunanin shi mahaifinshi ne zai sa a kawo shi ya ganshi alhali shi duk duniya a halin yanzu babu wadda ya tsani gani kaman mutumin da ya kawo shi duniya.

"Mukhtar"
Baba ya faɗa bayan ya gama kallonshi, babu abinda ya firgita shi irin tatoos na jikinshi kasancewar bashi da riga duk wani tatoo da ya kashewa makudan kuɗaɗe wurin zanawa gasu nan raɗau akan farin fatar shi, gashin kanshi da nashi ne yaje aka murde tsakiya ya zama dada aka kuma penta shi kalar ƙasa daga sama duk gasu nan zube har wuraren goshinshi, ɗaga idanu yayi ya kalli Baba ba tare da ya motsa ba, hannu baba ya miƙa mishi sai ya soma takawa kaman me tsoron tafiya ya isa gabanshi ya durkushe bisa gwiwowinshi a karo na biyu bayan fahimtar waye shi a duniya ya fashe da kuka me cin rai, kukan tsantsar takaicin rayuwarshi da nadamar abubuwan da ya aikata gabaɗaya rayuwarshi, kukan baƙin cikin kasancewarshi mashayi, mazinaci, azzalumi tunda yana iya zaluntar kowa ya kwana lafiya hakan kuma ya zamar mishi abin tinkaho a baya, hatta matar aurenshi ya zalunceta to me zai zauna duniyar yayi?

Ya fi mintuna ashirin yana wannan kukan wadda duk jama'ar da suke wurin suka shiga tsantsar mamaki babu wadda zai yarda sbd wannan fyade ne yake kuka kaman yadda Baba ya katse mishi kukan da cewa
"Mukhtar na tabbatar ba kukan halin da kake ciki ba ne kake yi, a duk abin da zai faru kana da yaƙinin mahaifinka zai fidda ka, shi ma kuma bashi da wani tunani in dae akan ka ne ko nawa zai iya kashewa tunda kudi ba matsalar shi bane, Mukhtar kalli jikinka kaman ba na mutane ba? Ka kuwa san haramci tatoo?
Kalli gashin kanka irin askin da annabi ya hane mu dashi ka kwashe rabi da rabi ka bar tsakiya, Mukhtar baka tsoron hukuncin Allah a kanka? Baka tsoron fushin shi ya haɗu da na mahaifiyarka ya haifar maka da babban iftila'i? Ko ka san kuɗi ba zasu taɓa ceton ka daga fushin ubangiji ba?"

Be iya yayi magana ba sai a sadda ya ji sassanyar Muryar mahaifiyarshi da ma sam be lura da ita ba tana cewa
"Mukhtar kap rayuwarka cikin kowani rana baki na bai taɓa hutawa ba wurin yi maka nasiha akan abubuwan da kake aikatawa, ban taɓa gajiyawa ba da ɗaura ka akan hanyar Allah da manzonsa haka ban taɓa gazawa da kai kukana wurin Mahalicci ba da ya shirya min kai, Mukhtar ka san irin kunar da nake ji a zuciyata daga jiya zuwa yau kuwa? Wani irin rashin imani ne wannan ku haɗu har ku uku ku haikewa yarinya karama ku zalunci rayuwarta da na iyayenta, ku shafa musu baƙin fentin da ba zai taɓa gogewa ba a rayukansu? A yau ba don umar da kake ƙi ya roƙeni da mu zo ko zaka iya faɗa mana sauran abokan cin mushenka, ya kuma yi magana da shugaban yan sandan da ya ci alwashin ba zai taɓa bari ka sarara da azaba ba har sai ka bayyana sauran ka kuma amshi hukunci daidai da abin da ka aikata ba da baka ganni anan ba, ashe abin da ka aikata kenan ya hanaka bacci shekaran jiya?"

Cikin sanyin murya ya ce
"Kiyi haƙuri Maami, bani da kwarin gwiwar neman yafiyarki kasancewar na shafe tsawon rayuwata ina chusa miki baƙin ciki, amma ki yarda da ni kaman yadda na faɗa miki shekaran jiya tun nasihohin Baba ban sake kuskuren aikata wani abu marar kyau ba, na kasance cikin tsantsar nadamar abubuwan da na aikata, na kuma shafe kwanaki cikin tunanin ta inda zan fara gyara kurakuraina, haƙiƙa na san ba zan taɓa gujewa hukuncin ubangiji ba kasancewata me saɓo a gareki, na kuma san ko da kin yafe min zuban hawayen da nayi ta saka ki a baya zai iya bibiyar rayuwata a gaba, Maami ban san ko waninku zai iya yarda cewa ban aikata laifin da ake tuhumata dashi ba, hasali ma ban san sa'adda suka aikata ba Dukda ina a wurin, na bar hakan ne cikin soman taɓin girbe laifuka na, Allah shi ne shaidata sai kuma su da suka aikata"

Idan Maami bata ce ta jijjiga da kalaman Mukhtar ba tayi ƙarya, sai de tana tsoron kar mafarki take, ko kuma wasa yake, shiriya take gani yana sauƙowa ɗan ta? Kuka ta fashe dashi na rasa abin yi, C.p, iyayen yaran da sauran manyan hukuma dake tsaye a wurin basu yarda da zancen shi ba, Baba kuwa hamdala yake adu'o'insu sun karɓu.

"Kai da su waye ne?"
Maami ta sake watso mishi tambayar
Ya ɗaga kai kaman zai kalleta sai de kunyar kallonta yake ji, a hankali ya sake maimaita
"Ban aikata ba"
Baba ya ce
"su waye ne?"
A hankali ya faɗi sunayen nasu, tuni C.p ya kwashe ya kuma aika a kamo su, sun kuma ba wa baba da Maami hakuri akan za'a mayar da Mukhtar Cell dole dae su haɗu a court tukuna a tantance me gaskiya.

Haka suna gani aka maida shi, Maami jikinta yayi sanyi sossai tana kallonshi har aka tafi dashi, ita da baba suka fito baba na sake yi mata nasiha har suka sauƙe ta gida drivern shi ya ja zuwa gidan shi.

Zaune ta samu Alayah tayi zurfi cikin tunani, dafa ta tayi
"Binty ban ce ki daina zama kina wannan tunane-tunanen ba?"
Ajiyar zuciya ta sauke kan ta kakalo murmushi tace
"Maami kun dawo?"
"Eh mun dawo, ya cikin? Ba wani matsala ko?"
Kasancewar tayi karyar ciwon ciki duk don gujewa tafiya ganin Mukhtar da ita ya sa ta kakalo murmushi
"Eh Maami ya daina"
Ajiyar zuciya Maami ta sauƙe, sai taji tana son bai wa Alaya labarin abin da ya faru
"Ko kin san Mukhtar ya ce baya cikin waenda ake tuhuma da wannan al'amari?"

Da sauri ta ɗago kai, one thing da zata iya cewa ta sani akan Mukhtar shi ne da matukar wuya yayi ƙarya
"Kuma Maami a baya ya aikata irin haka aka ce?"
Shiru Maami tayi sai Alayah ta ga kaman tambayar be dace ba
"haka ne, maƙasudin ƙarasa taɓarɓarewar rayuwar shi kenan Alaya, kila da be aikata hakan har ya shiga prison a chan Kasar ba ya haɗu da manyan thugs kila da hakan be faru ba, kaddara ta rigayi fata. Amma a yadda Mukhtar yake magana a yau har cikin raina na gamsu na kuma amince da be aikata ba ɗin, Fatana shine Allah ubangiji ya sanya ya shiryu a gasken"
Alaya ta amsa da Ameen.

Sun ɗan tattauna akan jikin ummi inda Maamin ke

Please Login or Register in order to submit comment