Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin sallahnts ya fara nafilfili, tun tana kallon shi har bacci ya sure ta.

Karfe uku ta sake tashi fitsari ta samu yana karatun alqur'ani da yanzu yayi nisa sossai kuma yana fitar da duk wani makharij da kiyayewa sossai a karatu, ta jinjinawa namijin kokarin shi don yanzu ko ita bazata nuna mishi ibada ba, taje tayi fitsari itama tayi alwala ta zo tayi raka'a huɗu kan ta koma ta kwanta, sai asuba ya tashe ta ya wuce masallaci.

Ko da ya dawo a kitchen ya samu Maami tana shirin haɗa abin kari
"barka da safiya Maami na"
Tace
"barka dae my son Fatan ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah Maami yau ke da kanki ne a kitchen, to da me zan taya ki nima in samu ladan?"
Cikin raha tace
"Me ka iya? Da Kai da ɗan uwanka duk jirgi daya ya kwaso ku ruwan zafi wannan baku iya tafasawa ba in ba da kettle ba"

Yana dariya yace
"Ai kitchen ɗin nan sai ku mata Maami ina ganin kokarinku duk abu da ƙuna, yanka bani ciki"
Sukayi dariya a tare, Maggi ta bashi yana ɓare mata chan yace
"Maami autan ki zuciyarshi tayi yawa, har yau ya kasa sakewa da ni be san kuma bamu da wani lokaci ba"
Itama hakan na damunta har yau be zo ba, babanshi ma na complain na ko ya kira daga sun gaisa shikenan
"ko da shi ke ma Maami kyale shi, dama zaani ne ya tadda muje ni, ga hali kuma ga yanayin aikinshi"
Ya katse ta don ya san tunanin amsar da zata bashi don kar yaga tana kare umar ne ta bar shi take yi.
Wani hiran suka kama har ta gama breakfast din yana tare da ita, shi ne miko wannan miko wanchan, dibo ruwa.

Masu aikinta ne suka fitar da abincin zuwa dining daga shi har Maami suka je suka yi wanka kusan a tare su huɗun suka fito, Mukhtar ya ja wa Abba kujera yana zama yace
"Abba yau zaka ci girkina na san sai ya kai maka karo bari na tabbatar da lafiyar kujerar nan kar santi ya kwashe ka"
Dariya suka yi Abba yace
"tafi nan, da de bamu san asalin balbela bane kai yaushe ka iya ko kunna gas din ma? Ko binty ya iya?"
Ya faɗa kaman yadda ya riƙe bakinshi saboda yawan faɗan Binty da Maami take. tana dariyar yadda ya kwabe fuska tace
"Babu abin da ya iya Abba"
Yace
"Maami faɗa musu don Allah ba ni nayi ba?"
Tace
"kwarai kuwaaa"
Yadda ta faɗa da alamun tsokana a muryarta yasa suka kwashe da dariya Abba na cewa
"faɗi gaskiya dai daga jin wannan amsawan naki da walakin goro a miya"

Abincin suka fara ci cikin natsuwa, jujjuya cokalin kawai Alayah take yi, Mukhtar da ya lura yace
"Fatee lafiya? Ko wani abu na damun ki ne?"
Shima ba ci yake ba ruwan zafi yake ɗan kurba.

Maami tace
"Binty akwai matsala ne?"
A hankali tace
"Maami kirjina ke ciwo sossai"
Abba yace
"Subhallahi Meyasa baki yi magana tun ɗazu ba? Mukhtar tashi maza mu wucenku asibiti"
Duk abincin suka bari Maami taje ta ɗauko musu mayafi zuwa lokacin ko tsayuwa Alayah bata iya yi tuni suka yi meddy specialist hospital hankalinsu a tashe.

*Har yanzu dae ana nan a free pages karku manta book 2 na kuɗi ne zaki iya biya ta wannan asusu
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763*



🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
     (heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Page Twenty Four*

Dr Philips ne ya yanke musu tsawon lokacin da suka ɗauka suna jiran tsammani, da hanzari duk suka isa kusa dashi kowa na rige-rigen tambayar ya take?
"Akwai contraction between her illness nd the baby, dole za'a yi mata aiki a cire shi a watanni bakwai in ya so a bashi duk wani kulawa a incubator she cannot take it for completely nine months”
Duk jikinsu yayi sanyi, sai da ya basu kwarin gwiwa ya tabbatar musu da ikon Allah in an cire they will be all safe, tuni aka kawo papers Mukhtar ya saka hannu.

Bai sani ba ko don saboda firgicin da yake ciki ne ko kuma wani abu na daban wani irin hajijiya ya kwashe shi saura kiris ya faɗi Abba ya tare shi, suka zauna suka shiga kwantar mai da hankali, nurse ce ta fito tace zasu iya su ganta kan a shiga aikin, duk suka miƙe suka nufi ɗakin, murmushi ne kwance a fuskanta ta kalli Maami ta miƙa mata hannu, da sauri Maami taje ta riƙe Alayah tace
"Maami ko a yanzu na mutu kun gama min komai, kun bani farin cikin da na rasa tsawon shekaru, Maami ko da wani abu ya sameni ina da tabbacin zaku cigaba da kulamin da ummi, idan kuma Allah yayi ikonsa bamu yi sallama ba ku tabbatar mata da cewa na mutu da ƙaunarta kuma ku ce don Allah ta yafemin"

Da sauri Mukhtar ya sa hannu a bakinta ya rufe
"Haba fatee wani irin zance kike yin nan? Mata nawa aka yi wa Cs suke cigaba da rayuwa har ma su cigaba da haihuwa, ki daena irin wannan furuci kin ji, zaki haihu lafiya zaki rayu ki kular min da baby har zuwa jikoki"
Abba ma yace
"zaki samu lafiya kin ji? Allah ya raba lafiya yasa ayi cikin nasara"
Maami dae ta kasa magana sai shafa kanta da tayi tana mata Adu'a suka fice suka bar Mukhtar.

Zama yayi ya riƙo hannunta tana kallonshi a hankali tace
"Ya Mukhy ba zaka faɗa min abin da yake damunka ba ko? Kana so in mutu ban san menene matsalarka ba ko?"
"Fatee na!"
Ya katse ta, ta lumshe idanu shi kadai ne yake kiranta hakan a duk fadin duniya
"Ya Mukhy"
Yace
"in kina so mu shirya karki sake maganan mutuwa, in shaa Allahu ba zaki mutu ba, not now not any moment from now..!"
Bata yi mamakin ganin hawaye kwance cikin idanunshi ba, peck yayi mata a Goshi ya sake yi mata a lips yace
"Ina sonki!"
Murmushi me kyau ta saki tace
"Nima ina kaunarka Yayana"
Miƙewa yayi saboda Shigowar nurses ya sake mata peck a Goshi yana shafa kanta yace a hankali
"Allah ya raba ku lafiya"
Ficewa yayi ba tare da ya sake kallonta ba sbd hawaye dake zuba mishi, ashe yana da rabon ganin ɗan shi ko ƴar shi, ajiyar zuciya yake ta saukewa a kai a kai.

Wayan Abba ne ya ɗauki ƙara bayan tsawon lokaci suna zaune, dubawa yayi sai ya ga Umar ne, ɗagawa yayi da sallama suka gaisa yake tambayarshi Maami fa tun asuba yake kiran wayanta ba'a picking.
"Muna asibiti ne da matar Mukhtar za'a yi mata Cs, ga Maamin naku"
A hankali yace
"Allah ya raba su lafiya"
Maami ta karɓa suka gaisa ta ɗora da
"Lafiya kuwa auta kake ta kira tun asuba?"
Don ta ji maganansu da Abban ta sake ɗorawa da cewa
"tunda nayi sallah na bar wayan ɗaki zuwa kitchen ko da na gama abin kari ma naje nayi wanka ban duba ba kuma ka ga daga wurin karin ne muka yo nan asibiti ko abincin bata ci ba baiwar Allah"
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe ta ɓangaren shi tana jin sautin iska da ya fesar yace
"Ummi!"
Don haka ya ji Maamin na kiranta, da sauri ta miƙe tsaye
"Me ya sameta? Sun ƙiraka daga asibitin ne? Me suka ce?"
"Calm down Maami, ta farka ne cikin dare, farkawan kuma be zo daidai ba sai jikin ya rikice, tun 2 suka ƙira ni akan if possible ayi gaggawar fita da ita i don't want to call you that time so we arranged emergency craft aka ɗauketa daga nan zuwa saudi saboda chan ya fi kusa da nan Lyon, am presently at the hospital Doctors basu fito ba dai tukuna".

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana zama cikin sanyi ta soma jero mata adu'ar samun lafiya tana kuma godiya wa autan nata, ta san ko Abban shi ne zai yi wannan dole za'a samu delay ba kaman shi ba da yake da connections masu yawa, bayan sun kashe take yiwa su Abban bayani adu'ar samun lafiya suka yi mata da kuma burin a fito da Alayah lafiya bayan ta warke su tafi chan gabaɗaya.

Some hours later

Dawowansu Abba daga Sallar azahar kenan likitoci suka fito suna musu albishir samun ƙaruwar ɗa namiji yana ma nursery a incubator zasu iya zuwa su ganshi.

Mukhtar yace
"maman fa?"
Cikin murmushi suka ce itama lafiyanta ƙalau bacci ma take, sai a lokacin tsantsan farin cikinsu ya bayyana a take Maami ta karbi wayan Abba ta soma kiran en uwa tana gaya musu matar mukhtar ta sauƙa lafiya, an sha mamaki kam don bakwaini ne aka haifo musu, kan ka ce karfe biyu en uwa da abokan arziki na ta zuwa sai dae a ga yaro a incubator tarr kamanninshi da Mukhtar kaman an tsaga kara.

Shi kam ba'a tantance wani yanayi yake ciki, yana nan zaune tare da Alayah har bayan la'asar ma Abadan kan ta farka, lafiya ƙalau ta tashi jikin kuma da ɗan ƙarfi dayake plaster ne aka mata ba ɗinki ba, ta ji daaɗi kwarai da ta samu labarin ɗan ta lafiyanshi ƙalau, saida aka kimtsata ta ɗan ci wani abu kan Mukhtar ya taimaka mata zuwa nursery don yaron ya ci abinci sai kuka yake, sun so ta matse aje a bashi sai dae Maami tace gwara dae ya ji ɗumin mahaifiyarshi.

Da ita da shi ne gaban incubator ɗin wata nurse ta ciro musu babyn, Mukhtar ne ya soma karbar shi ya rungume a kirjinshi sassanyar hawaye na bin fuskanshi a kan lips dinshi yake ta furta
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!"
Adu'a yayiwa yaron don musamman ya koya saboda burin kaiwa ranar da zae ga ɗan nashi a duniya Dukda bashi da wani kwarin gwiwa.

Miƙa mata ɗan yayi saboda nurse ta gama taimaka mata ta wanke bakin nonon kar yaro ya sha bacteria saboda kula irin tasu barin ma wannan da yake bakwaini dukda lafiyayye ne, saida ya ba yaron zamzam da dabino kan ya taimaka mata ta soma feeding nashi Dukda zafin da ya ziyarceta, ya sha kuwa yana ta sauke ajiyar zuciya.

Sun jima sossai wurinshi dab Magrib suka fito, ya kaita har ɗaki kan ya wuce masallaci.

Kan ka ce kwana bakwai tuni ta koma normal tana komai da kanta har wanka, sai su sa leda a bakin wurin su ɗaure da zani ta yadda ruwa ba zai taɓa ba tayi wankanta, yaddikon Maami ce ta zauna da ita tana kula da ita sossai kuwa, kullum asibitin a cike, Mukhtar ya ce ba za'a yi taron suna ba walima ce a ci a sha ayiwa yaro Adu'a so a gidan Maami aka yi dukda ba yaro bare mahaifiyarshi, yayi hakan ne saboda sanin cewa haka annabi ya umurta da a yi ba irin na yanzu ba da za'a tara jama'a a saka dj wurin suna bayan albarka ake nemawa yaron.

Kowa ya shiga mamakin jin sunan ɗan wai Mukhtar sai dae babu wadda ya ce don me tunda uban shi ne ya sanya mishi hakan, ganin bashi da wani matsala a duk checkups da aka yi sai kawai suka sallame su bayan sun ƙara week kuma har lokacin Alayah bata san ummi bata ƙasar ba, a duk sadda Maami zata yi waya da Autanta ficewa take kuma yana tabbatar mata da tana samun sauƙi sossai yanzu har tana iya gane wadda ke kanta.

A sati biyun sau wurin uku yana zuwa daga wurin aikinshi a Lyon ya koma, taji daaɗi kwarai yadda ya ɗauki ummin da muhimmanci Dukda be san ma wacece ita ba bayan surukar gidansu, wannan tausayi a jininshi yake.

Yau bayan Maamin ta gama yiwa baby komai yayi bacci a lokacin tabawa suka fito da Alayah daga bayi a bakin gado ta zauna ta soma kokarin shiryawa, ɗakin banda ƙamshin turaren wuta babu abin da yake fitarwa, wani kalar kunu ne da bata ma san ko sunanshi ba banda wani fitinannen kamshin kayan yaji da yake babu abin da yake Dada ne ke aiko mata kullum kuma tana jin daaɗin shan shi, ƙamshin shi da taji ne yasa ta kalli gefen gadon Maami ta tsiyaya mata sai turiri yake murmushi ta saki, jegon gata take ita kam bata da abin cewa ga Maami don ko ɗiyar da ta haifa a cikin cikinta karshen abin da zata yi kenan.

"Oya hanzarta kar kunun ya huce"
Ta amsa da to kan Maamin ta fice, agogo ta kalla karfe goma da rabi, sam bata ji motsin Mukhtar ba yau don haka ta nufi ɗakinshi, a kwance cikin bargo ta same shi zazzaɓi mai zafi ya rufe shi banda rawan ɗari babu abin da yake, da sauri ta ƙarasa kanshi ta yaye bargon tana cewa
"Subhallahi Mukhtar zazzaɓi kake yi shine ka shigo ɗaki ka kwanta kai kaɗai haka? Tashi mu tafi asibiti maza"
Tana kokarin juyawa ya riƙo hannunta, a hankali ya buɗe idanunshi da suke lumshe wa da kansu yace
"Maami ba wani abu bane ba fa, in na watsa ruwa na sha panadol zan samu sauƙi"
Girgiza kai tayi tace
"inaa ba zai yiwu ba Mukhtar, wannan ne kake cewa ba wani abu ba? Yaushe rabon da ka ci abinci a cikinka? Ina fa kula da al'amuranka zazzabin nan ya jima a jikanka kake yin shi tsaitsaiye ga rama marar dalili gwara dae mu je asibitin sai ya fi"

"Maami don Allah dae ba sai na je ba, bari na ƙira Dr Ahmad ma kawai zai zo ya duba ni a gida"
Ba don ta gamsu ba ta miƙa mishi wayan ya ƙira Dr Ahmad akan ya zo gida ya duba shi please, shakuwar dake tsakaninsu a yanzu ya wuce na patient da Dr sai na friends sun zama abokai sossai don a yanzu bashi da abokin da ya wuce Dr. Ahmad, ko kayan suna na ban mamaki ya aiko matar shi dashi kuma sau kusan uku tana zuwa asibiti da abinci niki-niki wa me jego har za'a iya cewa sun ɗan saba da Alayah.

Komawa ɗakin Alayah Maami tayi ta samu ta gama shan kunun, dubanta Alayah tayi tace
"Maami ya jikin Ummi? Har yanzu ba wani chanji ko? Kullum da ita nake kwana nake tashi har na haihu ummi bata sani ba"
Ta ƙarasa hawaye na gangaro mata
"Ummi ta farka Alayah tana cigaba da samun kulawa"
Wani irin zabura tayi
"tana iya magana? Tana iya gane komai? Maami don Allah zan je asibitin na ganta! Na san tana chan tana tunanina babu bakin da zata ce a kira ni"
Maami tace
"in shaa Allahu zaki je Alayah, yanzu dae ɗauki Wannan mijin nawa ku je ya gaida babanshi babu lafiya likita ma na hanya"
Tana cikin farin ciki kwarai da jin ummi ta farka tana samun kulawar da ya dace, Adu'a tayi ta yiwa su Maami, cikin jin daaɗi ta miƙe ta saka kayanta plain riga da zani, duba system ma dama take son yi sbd lectures dake ta wuce ta nan ma don farkon semester ne da a tsakiya ne ta haihu da ta ga bone, ba laifi kuma dayake tana da fahimta sossai ko a hakan tana ganewa sossai, dama su suna online class sossai sbd yanayin course na su.

Yaron ta ɗauka yana ta muimui da baki, ta lakaci hancinshi da sak na babanshi tace
"dube shi, yanzu ya sha baccin shi anjima yace bamu isa mu yi bacci ba"
Murmushi ne kwance a fuskanta in ta ga wannan yaron sai tace oh yau ni Alayah ce na haihu, ni ke da yaro kyakyawa irin Wannan Alhamdulillah!

Ɗakin Mukhtar ta nufa, a natse ta sanya hannu zata tura kofan ta ji yayi magana da ɗan ƙarfi
"Dr. Ahmad Don Allah ka kyaleni ba zan yi ba! Ba zan yi ba nace! Me ya saura? Kar ka sake min barazana da sanar da iyalina saboda a yanzu bana buƙatar tashin hankalinsu, don Allah ka rabu dani da zancen nan..."

"Mukhtar ka yiwa Allah ka bari a gwada, sai fa an gwada ake samun dacewa, zamu dace don Allah ko ɗan uwanka mu sanar wa in ya so ko ba anan ba sai ayi, its getting late please don't let it be worse than this u really are sufferring"

Mukhtar zai yi magana kawai suka ganta a kansu?
"Me za'ayi? Menene ba'a so mu sani? Me kake ɓoyewa ya mukhy?"

*****

Zaune take cikin tantsamemen parlorn nasu, iyayenta na kan dining suna cin abinci, a yanzu ta san babu wacce ta kai mommy jin daaɗi saboda hankalin Abbanta da ta kawar kan Waenchan banzayen, yanzu burinsu ya cika suna rayuwa cikin jin daaɗi su ukun su babu wata matsala, hankalinta ya rabu gida biyu tana jin hiran irin kayen da Abban su Mukhtar ya sha saboda abinda Mukhtar ya aikata Dukda daga baya an gane ba sa hannunsa sai dae baƙin alƙalami ya riga da ya bushe.

Mommy tace
"ko dae farar kafafun waennan sadaka yallar da ya kwasa ba, ai sun ban mamaki daga shi har matar tashi da basu san menene ma'anar arziki ba ai arziki shine a ci a sha a nunawa talaka wutsiyar rakumi tayi nesa da ƙasa"
Abban Meelah yace
"nayi mamaki daga baya wai akan mutanen nan Alhj Hammad Abdulhameed yake gayamin magana hmm gashinan nan wadda be ji bari ba ya ji hoho"

Wani irin Miƙewa da Meelah tayi tare da buga salati tana wani zazzare idanu shi ya firgita su suka yi kan tilon er ta su a rikice suna tambayar me ya faru? Ta kasa magana sai kawai ta sake fasa ihu

"Jameelah menene? Menene a wayan?"
Abba ya ƙarasa ya ɗauko sai ya ga rubutu ne kawai ta riƙe Mommyn tana ta zare idanu chan da kyar ta fusgo maganan
"Mommy....Captain cold.. Captain cold!"
"Na gane Captain cold naki, wadda kike matukar so amma baki gama bincike a kansa ba me ya same shi? Ya rasu ne?"
"A'a mommy be rasu ba! Mommy sai dae kila na rasa shi, mommy Captain cold complete name ɗin shi Umar Hammad Abdulhameed chanji... Ƙanin mijin Wannan shegiyar.. Mommy Meyasa kuka bari kuka ɓata da babanshi? Abba ka yi mishi magana don Allah ku shirya ina son Umar ba zan taɓa aure ba in ba shi na aura ba"

Duk ta rikice ta rikita iyayen nata,
"Wai kina nufin ɗan Alhj hammad chanji shine Captain din naki? Meyasa baki faɗa da wuri ba?".
Abba ya ce yana riƙo ta.
"Abba personal information ɗin shi are very very confidential saboda yanayin aikinshi, na shafe sama da shekara ina nema na kashe kudade masu yawa don kawai ko full name nashi na samo. Wayyooo na shiga uku!"

"Baki shiga uku ba! Zaki aure shi Jameelah na miki alƙawari!"

*Kar dae ku manta book 1 na gab da karewa wadda be wuci shafi biyu bane suka saura in ma na samu lokaci a goben zan gama su, ku yi hanzarin yin payment don karatu na gaba, in shaa Allah ba zaku yi dana sani ba.
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shaidar biya ta nan
09039206763
500 Naira kacal*




🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Last Page of book 1*

Ba zata ce ga yadda aka yi aka gama duk wani formalities na karɓar gawa ba, ba zata iya fasalta halin da take ciki ba har aka gama komai da ya kamata a yi, idanu kawai take bin taron mutanen da kaman yayyafinsu ake, a take ilahirin gidan Maami ya cika maƙil wasu na Adu'a wasu na zub da hawaye, lallai duk wadda ya san Mukhtar a watanni bakwai zuwa takwas da yayi bayan shiryuwar shi ya san ya rabauta, gabaɗaya alkhairanshi na kwanakin ake tunawa, da kyar take fidda numfashi bata sanin duk abinda mutanen da suke zagaye da ita ke cewa, ita dae gata nan ne ga yanayinta.

"Ina matarshi? Ta zo suyi sallama"
Wani ɗan uwan Abba ya leƙo bayan sun ƙira Maami ta jima a chan, Aunty ruqayya ce ta kama ta ta miƙar tsaye sai taji kaman kafafunta ba zasu iya daukar ta ba, abin mamaki kuma sai ta ganta tana tafiya ɗin kaman a iska har zuwa gaban gawan Mukhtar, a kan gwiwowinta ta zube, da kyar tayi kokarin fusgo kalmar
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun shikenan ko? Shikenan kai kuma ka tafi ka bar mu da wannan ruɗaɗɗiyar duniyar, ya Mukhtar Meyasa yanzu?.." Tayi saurin yanke maganan tace
"Astagfirullah na san baka yi sauri ba, muma bamu yi jinkiri ba kowa lokacin shi yake jira da yayi babu me karfin ikon hanaka tafiya, Allah ya gafarta maka Ya Mukhtar, Annabi rahama ya san da zuwanka lallai ayar Allah tayi aiki akan ka..."
Su baba ta kalla tace
"Ashe ba'a yankewa bawa tsammani? Ashe babu mahalukin da ya isa shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa? Alhamdulillah in shaa Allahu naka yayi kyau, Ba zan maka kuka ba kaman yadda na yi maka alƙawari, ba zan yi ba.."
Tana maganan ne a rarrabe hawaye na bin fuskanta da tsananin gudu, gabaɗaya ta ɗimauce, babu wadda ya hanata kowa yayi ƙasa da kai yana zub da hawayen tausayinta.

Adu'o'i ta cigaba da jera mishi ana amsawa, saida taji bata iya jan numfashi kan ta dakata, babu wadda ya tsaida ta saida ta gama da kanta ta kai zaune tare da ɗaura hannunta akan gawan ta saki sanyayyiyar kuka da ya kara ɗaga hankalin mutanen wurin, Maami ce da itama hawaye take ta zo ta ɗaga ta, haƙiƙa mutuwa akwai ɗaci kuma akwai zafi sannan aya ce me girma a garemu ga duk wadda ya san labarin Mukhtar zai gasgata faɗin Allah na ɗayanku zai kasance yana aikata sharri har sai gab da zai mutu sai ya aikata alkhairi ya shiga aljanna, haka idan babu rabo ɗayanku zai kasance yana aikin alkhairi dab zai mutu sai ya aikata sharri ya shiga wuta. Allah ka sa muna da rabo a aljanna.

Suna ji suna gani dumbin al'umman musulmi suka sallaci Mukhtar bayan an idar da sallahn juma'a aka tafi da shi gidan gaskiya, gidan da kowa zai je shi, a jikin Maami numfashin Alayah ya ɗauke rushing ɗinta aka yi zuwa hospital sanin condition ɗinta.

****

A hankali take buɗe idanunta da suka yi mata nauyi ainun, dishi dishi take gani hakan ya sa ta ɓata lokaci sossai idanun nata zube a ceiling kan ta fahimci asibiti take, daki-daki haka hoton rayuwarta daga farko zuwa yanzu ke dawo mata kaman wacce aka kunnawa magiji(television) har zuwa kan fitar da Mukhtar da aka yi wadda shine ƙarshen abinda zata iya tunawa, idanun ta maida ta lumshe hawaye na bin gefe da gefen kuncin ta, hannu taji ana share mata a hankali ta waiga sai idanunta suka faɗa cikin na Meelah.

Bata san ina ta samo ƙarfin tashi zaune ba tsabar mamaki da ya so kasheta daga kwance.
"Jameelah?"
Ta maimaita a kan lips ɗinta
Da sauri Aunty ruqayya dake zaune kan sallaya ta miƙe
"Alayah? Kin farka? Sannu ya jikin?"
Kallonta tayi ta sake kallon jameelar dake ta zabga mata murmushin da ya fi kama da na mugunta ko na makirci a hankali tace
"da sauƙi Aunty"
Ficewa Aunty ruqayya tayi da niyyar kiran Dr yayinda Jameelah tace
"Sannu Sis, sai kawai kika ganni, mun samu labarin rasuwar mijinki ne yasa nace bari na zo na miki gaisuwa sai kuma muka tarar kema ba lafiya gashi har yau kwananki goma sai dae ki farka ba cikin hayyaci ba a sake miki allura ki koma, sannu Allah ya gafarta masa"
Ta ƙarashe da fuskan damuwa.

Dukda abin da take ji ya tokare mata zuciya hakan be hana ta yin murmushin dake bayyana zallar takaici ba, wannan kuma wani sabon salon wasan kwaikwayon ne? Baya ta matsa ta jinginu da gini a hankali kan ta furta
"Ameen"
A kan labbanta bata sake magana ba har likitan ya shigo, ko duniya zata naɗe bazata taɓa yardar wa kanta saboda Allah ne Jameelah take zaune a wurin ba, ta riga ta san su farin sani son zuciyarsu kawai ke kaisu gangar wadda suka ɗauka makiyi, kuma ita bata ga dalilin sake shigowa rayuwarsu da take kokarin yi a karo na biyu ba ka guji soyayyar maƙiyi don da matukar wuya ya kai zuci.

Sossai Dr Philips ya dubata kan ya cire mata karin ruwan yace ta watsa ruwa ta ci wani abu sai a mayar, Jamila ta miƙe don

Please Login or Register in order to submit comment