Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayiwa wannan likitar kyauta ta bajinta da ban mamaki.
  Ko a wurin shiga mota shi ya buɗe mata kofar cikin kulawa ta shiga ya gyara mata laffayar da ta ɗaura kan wani tsadadden zani ya zauna mata sossai kan ya rufe ya zagaye ya shige ya tayar suka bar asibitin.
   Hannunta ya kama ya riƙe cikin nashi cikin murmushi ya ce
"hawwa ƴa mace mai tsananin kama da ke zaki haifarmin in shaa Allah in raine ta kamar sarauniya don ita ɗin zata zama princess kuma uwata"
baki ta taɓe cikin murmushin ganin irin kwantaccen fara'a dake fuskanshi tace
   "ni kuwa namiji nake so mai tsananin kama da kai ya zama jarumi, jajirtacce irin ka, mai kulawa da duk wani hakki na ubangiji, wadda ko kallonshi nayi zan tuna da sadaukin maza na."
Cikin murmushi ya lakace mata hanci ya ce
"We shall see! Allah ya bamu me albarka amma ina me tabbatar miki mamana na ajiye a nan" ya karashe yama me shafa ƙasan mararta da hannushi ɗaya, ɗayar na sarrafa stirring mota dariya suka yi a tare tana amsa adu'ar tashi....

*****

Tashin da Alayah tayi a firgice shi ya katse mata tunanin da ta tafi har tsorata tayi, sai ta ga tayi wurin landline da gudu tayi picking sbd saura kiris ya tsinke, da alamu kira ake ita ummin bata ji ba sbd babu kunnen, mintuna biyu taga Alayar ta dawo tare da ɗaukan hijab ɗin ta ta saka fuskanta sam ba walwala, da hannu ummi tayi mata alama..
  "Menene? Ina zaki je a daren nan?"
Seda ta sauke ajiyar zuciya tace cikin alamar kurame
"Ummi Jameelah ke nema na wai dare yayi bazata iya cin tuwo ba in je in dafa mata indomie in soya mata plantain in kuma dibi Miyar as pepper soup in kai mata ɗakin ta"
Shiru ummin tayi kan ta ɗago ta ce
"Ki kwanta bari na je na yi mata"
Da sauri ta girgiza kai tana mata alama
"a'a ummi babu ta yadda za'ayi ina kwance kina chan kina yiwa Jameelah girki bari naje yanzu zan dawo"
Kanta ƙasa har Alayar ta fice..
Lallai dukkaninsu Allah ya amsa adu'o'insu, ya bata mace me tsananin kama da ita kaman yadda mahaifinta ya roka, se kuma ya amsa nata wurin bata halayya mafi rinjayi na mahaifinta me haƙuri, juriya da kuma jin ƙanta, sanin kanta ne Alaya ta ci sunan inkiyarta na princess, smart and beautiful, kwata kwata bata son ganin ummintata na wahala Dukda a ciki ta tashi ta sameta, bata ƙaunar jin wani kalmar ɓatanci in har dae akan umminta ne, hakan ya sa wahalhalu dayawa takan ɗauke mata na ayyukan gidan da kankantar shekarunta, ɗaga hannu sama tayi tana rokon Allah ubangiji ya kawo musu karshen wannan rayuwa da suke ciki don suna tsananin jiggatuwa...
   
Cikin mintuna da basu fi arba'in ba ta gama tare da kai mata har daki, ba zata iya jira ba tunda ta san ko yau ko gobe din ne itace dae zata fitar da kwanukan don haka ta wuce sashensu, da kyar ta iya sauya kayanta ta koma bayan umminta ta kwanta a take bacci yayi awon gaba da ita se lokacin ummin ta juyo ta tofeta da addu'a kan itama ta shafa ta lumshe idanu tana sake sake har bacci ya ɗauke ta.

Washegari da safe kaman yadda al'adarsu take a gidan suna Sallar asuba suka miƙe suka fice, ummi na tsaftace gidan yayinda Alayah ke ta zirga zirga a kitchen wurin haɗa breakfast, tayi nisa a aikinta tana cikin soya doya taji ƙarar fashewar abu a lokaci ɗaya ta tsinci gigitacciyar tsawar Hajj Zeenat wadda ta tabbatar umminta ce kawai take yiwa irin wannan tsawa, wani mummunan faɗuwa gabanta yayi wadda ya haddasa bugun zuciyarta tafiya fat fat fat kuma hakan barazana ce ga lafiyarta, da sauri ta saki cokalin hannunta tayi parlorn Dukda ta san laifi take shirin aikatawa amma bazata bar umminta ta muzanta gabansu ba, da gudu ta shiga gaban ummi marin da hajj Zeenat ke shirin sauke mata ya sauƙa kan fuskar Alayah ji kake tassss, tsabar zafin marin da karfin shi seda ta fadi jikin ummin ta baya baya, ko gama dawowa hayyacinta bata yi ba tayi saurin zubewa bisa gwiwowinta tana cewa..

"Mommy don Allah ki yi haƙuri, mun tuba ki yafe mana"
Cikin faɗa me hade da ihu hajj Zeenat tace
"ke har kin isa? Ke kika min laifi ko uwarki? Wallahi yau ko zata buɗi baki da kanta tace min yi hakuri ba zan hakura ba"
Ummi da har lokacin ranta tafasa yake da marin da hajj Zeenat ta saukewa Alayah idanunta kan flower vase din da ta fasa wadda tunani ta tafi na sadda aka saye shi da yadda aka saya mistakenly ta ture shi ya faɗi ya tarwatse, idanunta gabaɗaya suka sauya duƙawa tayi ta ɗaga Alayah tare da juyawa da ita zasu fice, wani irin fusgowa da hajja Zeenat tayi mata seda suka juyo gabaɗaya ta ɗaga hannu da niyar tsinke fuskar ummin da mari taji karaf an riƙe hannunta.

Da kallo ummi take bin su dukkansu biyu, shimfide cikin idanunta kana iya hangar zafi da turirin zuciya da take fama dashi a lokacin, soyayya da kulawa irin ta uwa ya wuce a ce a zabgawa ɗan ka mari me wannan zafi a gabanka ka kasa tabuka komai, wani irin zafinsu take ji barin ma shi, duban su ta sake yi a karo na ba adadi kan ta janye Alaya suka fice daga parlorn.

"Me kenan kake kokarin yi Abban Jameelah? Ƙaskantar da ni a gaban waennan ƙaskantun mutanen? Ka kuwa san laifin da ta aikata min?"
Hajj Zeenat ta faɗa a kufule
"ban sani ba kuma bani da ra'ayin sani, abunda kawai na sani shine sau ɗaya tak kika yarda kika sauke hannunki kan hawwa ranki idan yayi dubu to se ya ɓaci, duk abunda kike kallonki kawai nake ba wai bani da ikon hanawa ko dakatarwa bane, ni na san anfanin da hakan ke min don haka ki kiyaye, don yarinyarta ban damu ki mata ko ma menene ba amma banda hawwa"
Yana kai nan ya juya ya buɗe wani kofa da ze sada shi da sashen shi ya shige.

Zaune hajja Zeenat ta kai tana jin zafin wannan abu da Alhj ke mata, wani irin turirin tsanar hawwa da Alaya take ji kaman ta shafe babinsu a duniya, a kan hawwa duk wani farin cikinta na gidan aure ta rasa shi, ga kuɗi har kuɗi amma bata da kwanciyar hankali, menene manufar Alhj akan hawwa ne da ya zuba ido shekara da shekaru ina mata yadda na so? Ta tambayi kanta daidai lokacin da Jameelah ta fito tana tambayar ƙaurin da take ji a gidan gabaɗaya.

Da hanzari suka yi kitchen masifa sossai hajiya Zeenat ke yi na duk laifin Ummi ne gashi Alaya ta ɗaura tea a glass pot dinta ruwan ya ƙone har ya fashe, tambayarta Meelah tayi se take bata labarin abunda ya faru cikin jin haushin Alhj har yanzu.
  "Ai ko wlh sun yiwa kansu yau azumin dole zasu yi babu me samun abun kari"
Hajiya ta karashe da hakan, kwafa Meelah tayi tana tunanin yadda zata ci zarafin Alaya, mommyn ta saka ta dafa mata indomie da tea ta ci kan ta nufi ɗakinta don ƙarasa shiryawa, mommyn ma ɗakinta tayi tana danna kiran wayan aminiyarta Hajiya Fanta...

A ta ɓangaren Ummi kuwa cike da tausayi irin na uwa take duba fuskan Alaya bayan ta zaunar da ita bakin katifarsu
"Alayah me yasa kika shiga marin ya same ki? Kin dae san baki da wadataccen lafiya"

"Ummi lafiya ta ƙalau i promise" tayi mata alama tana danne radadin zuciyarta.

Shiru duk suka yi babu wadda ya iya sake cewa komai kowa da tunanin da yake a zuciyarshi, daga karshe Alaya ta miƙe tana cewa zata je ta ƙarasa breakfast kar ya zama laifi, ummi ta ce ta shiga tayi wanka ta shirya makaranta zata je tayi da kanta, komawa sashen ummi tayi ta fara soya doyar da Alayar ta fere, tana juyewa a kuloli Meelah ta shigo tsab a shirye cikin full uniform din ta, wani irin kallon kyama da tsana ta watsawa ummin kan ta nufi fridge ta buɗe ta dauki hollandia youghut da ta shigo ɗauka ta tsiyaye cikin wani bottle flask ta zuba mishi kankara ta juya ta fice.

Ko da Alayah ta shigo Hajiya Zeenat bata fito ba bare ta basu abunda zasu ci, se kawai Alaya tayi wa ummi sallama akan se ta dawo kawai yanzu in ta ajiye Meelah Abbanta ze kusa kasheta.
   Rayuwa baka samun yadda kake so, ga dae abincin ummi ta gama jujjuyewa saide babu halin su taɓa sbd gudun tashin hankali da tozarci, tana ji tana gani Alaya ta fice ba tare da ta karya ba.
   
Ko a makaranta Alaya bata yarda ta shiga sabgar Meelah ba duk da yadda sukan zage ta da kawayenta ko su zungureta bata ce musu ci kanku gudun fitina, karfe 1:30pm suka tashi daga makarantar hadari ne sossai ya haɗu a sararin samaniya banda iska babu abunda yake kadawa alamar ko da yaushe za'a iya tsugewa da ruwan sama, dubawa Alayah tayi taga baba Musa be kai ga zuwa ba hakan ya sa ta nufi masallacin su don gabatar da Sallar azahar kar ta je gidan ga aiki ga yunwa tana ji, banda ruwa babu abunda ta sakawa cikinta gabaɗaya yinin tana kallo a break yadda Meelah ke kashewa kanta da Ƙawaye kudi a cafteria, ita ba mai shiga mutane ba ita ba kawa ba don tana matukar kama kanta da tsayawa matsayarta, duk makarantar ƴaƴan masu hannu da shuni ne hakan ya sa tun farko ta kama kanta ta keɓe rayuwarta, duk duniya bata da kawar da ta wuce umminta.
   Ko da ta fito ta duba agogo biyu saura mintuna sha biyar, da sauri tayi wurin ajiyar mota don duba baba Musa ko ya zo kar ta ajiye Meelah ta kara laifi duk dubawar duniya bata ga Meelah ba bare baba Musa da ta san har ta shiga masallaci bai zo ba, wurin gate man ɗin su tayi take tambayar motar gidansu ta fita?

Makaranta ce me matukar tsaro hakan yasa babu motar da zai shiga ya fita ba tare da gate man ya tantance ba.
"Eh sun fice tun mintuna biyar baya"
Gabanta ya yanke ya faɗi sun tafi basu jira ta ba? Ya zata yi da nisar tsakanin unguwar su da makarantar? Ya zata yi da yunwar da take ji kaman ze kasheta? Bata da ko sisi babu dalili, ko bashi ta karɓa ina zata samu ta biya su? Su da suke rayuwa sai abin da aka tsakura aka basu.
    Iskar ruwan dake shirin zuba at any moment ne ya kara karfi, takawa tayi ta sa hannu a karamin gate ta buɗe ta fice sbd Kusan duk school din babu kowa, takawa ta fara bata ko yi taku biyar ba aka soma yayyafi kan ka ce kobo ruwan ya tsuge a take ya kuwa sameta ba ɓata lokaci ya fara bugunta, bata tsaya ba kaman yadda bata fake ba sai tafiya take, daidaikun mutane dake neman mafaka se kallon ta suke, yayinda ita kuma tana ji bazata iya jiran ruwan ba, umminta zata shiga damuwar rashin ganinta sannan ya ayyuka zasu mata yawa.

Ruwa ne ke zuba sossai ɗauke da walkiya da tsawa gudu yake tsugawa a bisa shimfidadden titin sbd karancin abun hawa kuma yana sauri, sam bai zaci ko tsammaci ganin mutum bisa titi ba a wannan yanayi na ruwan sama mai karfi dake zuba kawai se ganin halitta yayi kaman daga sama a gabanshi kuuuuuuuuuu haka wani irin ƙara ya karade wurin ya haɗu da wani tsawa da aka saki....

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment


              🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1 *
       *Page 3*

A matukar tsorace cikin gigita ta tsaya kyam hannayenta bisa kunnuwanta idanunta a runtse jikinta kuma ya ɗauki kyarma, kaman yadda baƙar motar kirar jaguar XJ baƙa sidik wacce ba'a iya kallon komai nata ta tsaya chak, jin shiru motar bata bugeta ba har lokacin yasa ta sauke hannunta a hankali, idanunta dake rine ta ɗaga ta kalli gefen da mota yake ganin yana nan tsaye yasa ta miƙe a sanyaye, uniform nata a jike shakab ta cigaba da tsallakawa a hankali tunda ta tsira daga sharrin kaɗewar motar, har ta tsallaka bata ji motar tayi wani motsi ba seda ta bar kan titin gabaɗaya kan taji wucewar motar da karfi kaman iska, juyawa tayi ta bi motar da kallo na second kan ta cigaba da tafiyarta.

Sai wuraren uku ta iso gida a lokacin yayyafi kadan kadan ake, jikinta babu inda baya rawan sanyi, gabaɗaya hankalinta a tashe banda tunanin umminta babu abunda take ta san tana nan tana jimamin rashin ganinta bayan Jameelah ta dawo tuntuni, karamin gate nasu ta kwankwasa Malam shazali ya zo ya buɗe ganinta ya sa ya kauce ba tare da ya ce komai ba ta shigo, cikin sassanyar murya tace
"sannu da aiki malam shazali"

Yace
"sannu Alaya haka ruwa ya jika ki? Meyasa baki hakura ruwan ya tsagaita ba kan ki taho? Tun dazu baba Musa ke ta jimami akan ki wallahi Hajiya karama ta hana shi jiranki kaman yadda ta mishi barazana da aikinshi Idan har ya fita ya koma don ɗauko ki"

Hawayen da ya gangaro mata ne ta share tace
"ba damuwa malam shazali, ba zan iya zama ne ba tare da na san sadda ruwan zai tsaya ba ga ayyuka na tabbatar sun ma ummi yawa kuma na san itama hankalinta tashe bata ganni ba"

Ya girgiza kai yace
"zuwanta nan uku tana neman baba Musa kuma tunda ya sauke Hajiya karama Hajiya babba ta aike shi chan mariri har yanzu be dawo ba"

"na gode bari na ƙarasa ciki"
Ta faɗa kan ta wuce don shiga cikin gidan, kaman yadda ma'aikatan suke respecting nata da ummi haka itama take basu girma kasancewarta me tsananin biyayya da ganin girman na gaba da ita, kuma ko bayan haka ta kan zo wurinsu tana karama su yi ta mata wasa musamman Idan ayyuka suka yiwa umminta yawa kuma bata da abokin wasa, so kaman kusan iyaye ta ɗaukesu.

Wucewa tayi zuwa sashensu tana shiga ta fara kokarin raba kanta da kayan jikinta sbd irin rawa da jikin nata ke yi na sanyi, da wasu kayan ta chanza tana kokarin tsugunawa don tattare kayan taji kirjinta yayi wani irin riƙewa, sunan Allah ta kira tana dafe kirjin da kaman ze tsage don azaba, cikin karfin hali ta ja ta isa kan gado ta janyo zannin ummi ta lullebe jikinta ta dunkule hannunta dafe da saitin zuciyarta tun tana dauriya har kuka ya kwace mata tana kiran ummi...

Ummi kuwa Dukda aiki take sede hankalinta rabi da kwata baya tare da ita, gashi dae sun haɗu da Meelah sau biyu amma tsoron tambayarta Alayar take bama ta san ta yadda zata fara ba don mutunci be taɓa hada ta da Jameelah ko na minti ɗaya ba, in zata iya tunawa har miyau Jameelah ta taɓa zuba mata a fuska, wa kuma ya san irin zagin cin mutuncin da suke sha don ma bata da kunnen ji, a gaggauce ta gama wanke wanken da take ta nufi komawa sashensu don duba ko Alaya ta dawo.
Karo ta ci da jikakkun uniform nata daga tsakar daki seda gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta ƙarasa ciki tabbas da tana da kunne zata iya jin irin kukan da Alaya take cikin ciwo, da gudu ta ƙarasa ta ɗago ta tana kokarin maganan su irin na kuramen nan sede babu abunda yake fita, hannun Alaya ta kama se taga ya chanza yayi wani abu blue tinge wadda a turance ake kira (cynosis) gabaɗaya ilahirin hannun, jijjigata tayi ta buɗe idanunta da kyar nan ma duka haka ne alamun ciwon zuciyarta ya tashi, ganin yadda numfashi ke shirin dauke mata kaman bazaka kyapta idanu ka buɗe ka sameta da rai ba yasa ummi Miƙewa da sauri tayi waje..

Tana fita motar Alhj Hassan Dala na parking a tsakar gidan da sauri ta nufe shi, a gabanshi ta tsaya hawaye na zuba mata, duban ta yayi na mintuna ya san in ya kalleta cikin wannan hali ƴar ta ce ba lafiya, baki ya taɓe kan ya koma motarshi  hankalinshi kwance yayi rubutu a jikin wani joter ya ɓalle ya fito, hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin da baza su wuce dubu talatin ba ya watsa mata da papern, duƙawa tayi tana kuka tana tattarewa cikin sauri sauri daga haka ta miƙe tayi sashensu.

A hannu ta riko Alayar dake tafiya da kyar da karfin hali don bata ma sanin tana ɗaga kafa sbd azabar ciwo, baba Musa da dawowarshi kenan yake tambayan shazali me gadi ko Alaya ta dawo shi kuma yana bashi labari ya hango Fitowar su duk hanaklinsu seda ya tashi ummi kuka Alaya kuka, baba Musa ne yayi kundunbalar fita ya samo abun hawa da kyar sbd irin tsaron unguwar, ya cewa malam shazali idan har aka tambayeshi ya ce ya tafi gida an kirashi iyalinshi ba lafiya.

A napep din banda faɗa cikin tausayawa su ummi babu abunda yake, har yaushe wannan rayuwar zaluncin? Ina ma yana da wani iko da ko se ya ga abunda ya turewa buzu nadi akan iyalan Alhj Ahmad marafa, har hawaye yayi jin yadda Alaya ke kirar sunan Allah cikin azaban ciwo, asibitin murtala suka isa sbd nan ne su kan je idan irin hakan ta faru don basu da dalilin na kuɗi ɗan abunda yake basu idan ya ishesu Toh falillahil hamd idan kuma be isa ba sede su bar jinyar a haka idan har an ɗan samu sauƙi hakan yasa kullum Alayar take a wahale babu kuma ƙiba se rama.
   Cikin hanzari aka karbesu aka fidda file ɗin ta aka yi emergency da ita, ummi zama tayi bakin wurin tana zub da hawaye masu zafi, ita kadai ta san irin tashin hankalin da take shiga a duk sadda ciwon Alaya ya tashi irin haka, ita kadai take dashi idan ta rasata ina zata saka rayuwarta?
   Bata da tabbacin ko likitan zuciya ne ya shiga kan Alayar sun dae ɗauki lokaci a kanta kan suka fito, baba Musa yake tambayar su ya jikin nata?
"Baba wannan ɗin ƴarka ce?"

Ya amsa da"eh"
"Kwanaki na bada shawarar zuwa wurin Dr philip sbd kwarewarshi a harkar zuciya chan meddy specialist hospital ban san Meyasa kuka kasa daukar shawarata ba, ina me tabbatar muku yarinyar nan tana kara shiga yanayi me hatsari ne a yawan attack da take samu idan mun iya tseratar da rayuwarta yau gobe babu abunda zamu iya, so prevention is better than cure"

Baba Musa ya jinjina kai yace
"in shaa Allahu zamu yi kokari akan hakan mun gode likita"

Wucewa doctorn yayi yayinda ummi ke ta kallonsu cikin zakuwa da son jin me suke cewa sbd gabaɗaya hankalinta yana kan lafiyar gudan jinin ta, Juyowa yayi tare da yi mata bayani bata iya ta ce komai ba se hawayen da take sharewa a kai kai ba basu je Meddy din bane sun je sede irin kuɗin da suka ji daga karbar kati ma zuwa ganin Dr ba karamin kudi bane basu dashi babu kuma dalili.

Ummi ce rike da hannun Alaya dake ta aikin bacci sbd alluran da aka yi mata lokaci lokaci ta kan kalli mutanen ɗakin, kowa da kalar ciwonshi, ward ne me ɗauke da gadaje kusan ashirin dogo ne sossai, Malam Musa ya samu ya tafi sbd gudun matsala zaninta ta kwance ta fiddo papern joter din da ta nannade ta ɗaure a wurin ta fara warewa a hankali.

"Kaman yadda na faɗa miki a baya na kuma maimaitawa yanzu ma ba zan gaji ba zan sake faɗa, hawwa duk wani abunda yake faruwa daku laifin ki ne, lafiyar ƴarki a hannunki yake kaman yadda lafiyar kunnuwanki suke hannunki, Da kalma ɗaya tak! Zaki ƴanta ku zuwa sabuwar duniya amma kin kasa anfani da wannan dama, a yau Idan Fatima ta mutu karki ga laifin kowa se kanki, ke ce kika kasheta..."

Dukunkune papern tayi tare da runtse ido da karfi hawaye na gangaro mata sossai, da sauri take girgiza kai kan ta ɗaura kanta jikin gadon Alaya ta saki sassanyar kuka, shin ya zata yi? Har abada bata jin zata iya abunda Alhj Alhassan Dala yake so, amma ganin ƴarta a hali irin na dazu ya sa take jin zata iya yin komai sbd samun lafiyarta, in tace komai tana nufin komai amma buƙatar Alhassan ya zarce da tunaninta, Allah ka min mafita... Abunda take ta nanatawa kenan a ranta.

"Ummi!"
Alayah ta faɗa tana me dafa ta idanunta da suka sauya sossai suke lumshewa da kansu ta zubawa ummin da ta ɗago take share hawaye a lokaci ɗaya tana tambayarta ta farka? Ya jikinta? Me take so? Duk cikin alamu irin ta maganan kurame.

"Yunwa ummi, yanzu karfe takwas na dare babu abunda ya shiga bakina tun safe banda ruwa"
Tayi alamar cikin tsananin jin yunwa ga ciwo, bakin ta duk ya bushe.

Miƙewa ummin tayi tace mata tana zuwa ta fice, maida idanunta tayi ta kulle tana jin yadda surutan matan masu jinya da masu kula dasu na ta tashi kaman kasuwa hakan ne fa ya sa ta tsani asibiti, tana nan kwance har ummi ta dawo ta taimaka mata ta wanke bakin ta, da kanta ta wanke hannu take ciyar da ita dafaffen  doya da Miyar sauce ɗin da ta saya a bakin asibiti daga cikin ledar, bayan ta ci sossai ta ɓula farin ledar da aka kulla mata kunu ta bata ta sha sossai kan ta sha magungunan da ta sayo duk tana bacci lokacin ta sha.

Rokar roba wurin makotarsu tayi ta saka ta tayi alwala ta rama sallolin da ake bin ta, ummin se kallon ta take tana tunanin wani shawara zata yanke, duk wadda ta zaɓa babu sauƙi...

Kwanansu biyu asibitin banda ma'aikatan gidan babu ƙafar wadda suka gani a ahalin gidan dama sun saba Dukda da ciwo matuka, duk faɗar ka da mutum ai ciwo ya fi gaban komai, yanzu haka zasu koma su ɗaura musu da bauta ba tare da kyautatawa ko na minti ɗaya ya shiga tsakaninsu ba, banda abinci da shima se an ga dama a basu da kuma makarantar Alaya ba zasu ce ga wani abun arziki da suke tsinta a rayuwar gidan ba, amma ya suka iya? Ya kuma zasu yi? Nan ne kaddararsu kuma nan Allah ya zaɓar musu su yi rayuwa.

Landline ɗin sashensu ne ya ɗauki kara ko gama tattare sashen ummi bata yi ba sbd tunda suka tafi babu wadda ya dawo se yau, ummin kuma ta hana Alayar kama mata sbd har yanzu jikin se a hankali, ƙarasawa tayi ta ɗauka Muryar Meelah ne ya karade kunnenta
"Ki zo ki yi min gyarar daki"

Shine abunda ta faɗa kan ta kashe babu ko amsa sallamar da tayi mata, ummi ce ta tambaya me take so? Nan ta faɗa mata, girgiza kai tayi tacewa Alayar ta je ta kwanta zata je tayi mata.
Babu dae yadda ta iya ne haka tana gani ummin ta fice, zama tayi a wurin ta sanya kanta cikin kafafunta tana tunanin abunda kaddara ya zaɓar musu se yaushe ze wuce? Anya kuwa zasu samu chanjin rayuwa?

Kwarai ummi tayi mamakin ganin irin yadda Meelah ta maida ɗakin a kwana biyu kaman ba mace ba? Duk wasu ledojin kwalamarta na zube tsakiyar ɗakin wasu kayan sawa wasu takalma duk gasu nan ɗaiɗai baje a ɗakin haka ta soma tattarewa a natse ta jima kan ta samu ɗakin ya dawo daidai ta juya ta fita ta tsaya parlorn ta gyara ta koma na Hajiya Zeenat ta fara kenan Meelah ta fita daga dakin uwarta tayi nata ba'a yi mintuna goma ba ta dawo ta tsaya kan ummi tana mata magana cikin tsawa.

Ganin

Please Login or Register in order to submit comment