Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lado ya daka masa yace "ohh munafukar matar taka ce
ta kitsa maka abinda xaka fada min ko, to sayar da Ikram nayi
karewarta knn, kuma ku tashi ku ban waje" kuka ssae Ammi ta
fashe da tace "wllh wllh Na lado ka fito min da ya ta kar in kai ka
kara police station," Shatu ta leko tace "gidan yari xaki kaisa ba
police station ba karewarta knn, yo idan bnda tsiya meye abun
damuwa don mun raba ki da masifa, ke fa da kanki kinsha fadin da
da ynda xaki yi da yarinyar nn da kin yi, to ynxu ga shi Allah ya
kawo ynda xa ayi da ita, har ma xa a dinga baku kudi duk wata"
Ammi ta mike tana huci tace "to mu xuba da ku wllh sae kun fito
min da ya ta mugaye kawae axxalumai mara su tsoron Allah,
meyasa baku dauki shafa kun basu ba, ae wllh bbu ubanda xae
hanani daure ku" tsawa Abba ya daka mata yace "kina da hankali
kuwa Aisha shi yayan nawa kike fada ma mgna hka" tayi masa
wani mugun kallo tace "xa ko kasan bnda hankali yau," tana kai wa
nn ta fice, Abba ya dinga kiranta ko juyowa bata yi ba, na lado yace
"to kai ma tashi ka ban waje munafuki kawae, sae kace ba kai ka
tsara mata abinda xata fada ba, Rabi ce dae na bada ta birni duk
sati xa a dinga kawo maku ita ku gani" Mikewa Abba yyi a sanyaye
ya fice daga gidan. Karfe shidda na yamma Shatu na xaune tsakar
gida tana kulla kuka, Yakumbo da Ammi da wasu yan sanda uku
suka shigo gidan, mikewa Shatu tayi tana salati ta shiga kwala ma
Na lado dake bayi kira "Malam, Malam fito" ya fito rike da yar
butarsa yana cewa "ni fa ban son kira hka kmr wata tsohuwar
makauniya" sororo ya tsaya kallon yan sandan, Yakumbo na nuna
su tace "su ne wa innan, maxa ku kame shegu barayi" Na lado yyi
kofar gida da gudu wani dan sanda ya chafke shi, yan sandan suka
ja shi suka fita hka ma Shatu da sae xaxxare ido take. Ikram na
xaune gaban Makeken plasman dake falo tana kallon cartoon da
duk hankalinta, Mami ta sauko kasa tare da Khaleel da fuskarsa ke
daure ya nufa dinnin, Kashe TV Mami tayi tce "karatu xa kiyi Ikram
gobe xa ki sch" Ikram ta xumburo baki kmr xata yi kuka tace "ni
Anty ki kunna min" Mami ta dagota tace "bari to ki gama karatun
kinji dota" textbuks din hannunta da excercise buk ta ajiye kan
Kujera tana kallon Khaleel tace "son idan ka gama gashi kayi
assistin dinta don Allah ya[truncated by WhatsApp]
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 25.... Washegari da asuba Mami ta gama shirya Ikram cikin kayan makarantarta, ba karamin kyau Ikram tayi ba cikin dark nd light pink uniform dinta, na cikin light, pinafo din dark, sae ddi take ji ta kasa barin gaban madubi bayan Mami ta gama parkin din mata dogon gashinta da ribbon, tana tsaye gaban mirror har lkcn Mami ta shigo dakin rike da breakfst dinta bayan ta ajiye na Khaleel a dinnin, Mami tace "maxa ki cinye kafin in fito Ikram" kai kawae Ikram ta gyada mata ta xauna gaban break din, Mami ta shiga wanka. Ikram ta mike ta bude kofar a hankali ta fice tayi dakin Khaleel, tsaye ta gansa yana knot din tie dinsa ta washe hakora tace "yaya Khaleel nayi kyau" grin din hakoransa yyi yana mata mugun kallo cikin tsawa yace "get out kar in taka ki, ni kike tambaya kin yi kyau" Ikram ta murguda masa baki tace "shi yasa bana sonka, kuma ko kyau ma baka yi ba, wnn abokin nawa ya fi ka kyau" kanta ya yo ta fice a guje tayi dakin Mami tana kwala mata kira, yyi kwafa ya koma dakinsa, dariya ta dinga yi kmr wata tababbiya bayan ta shigo dakin, tayi mai isarta snn ta fara shan tean ta, ko da Mami ta fito ta gama, Mami ta hade rae tace "me ya fitar da ke? Baki ji ko Ikram" ikram ta dan turo baki bata ce komai ba, Mami tace "dauki kofin nn da plate ki kai kitchen" ba musu ta dauka ta nufi kitchen da su, Khaleel na xaune kan dinnin, ta hararesa ta koma sama da sauri, karfe bakwae da minti goma suka sauko da Mami tana goye da jakar makarantarta, Mami na kallon Khaleel dake xaune dinnin har lkcn tace "ka ba Mai gadi makulli, jummae ta kira ni tana hanya" bae ce mata komae ba har ta isa bakin kofa snn yace "Allah ya kiyaye," tace Ameen snn suka fita, gaban mota ta bude ma Ikram snn ta xaga ta shiga driver seat ta tada motar tayi warm dinsa suka bar gidan, har cikin makaranta ta shiga da Ikram ta hada ta da dari biyar kudin break nn da nn Ikram ta hade rae xata yi kuka wae ita baxata xauna ba, Mami tace "anjima kadan xan xo in dauke ki dota," a hka ta samu suka rabu ta kama hanyar office. Ammi na xaune tsakar gida ta rafka uban tagumi sae kallon Abba da yasa ta gaba sae masifa yake mata, wae suje su sa a saki yayansa da matarsa da suka daure da ita da yayarta, sae da Ammi ta bari ya gama snn ta mike tsaye tana masa mugun kallo tace "su fara fito min da ya ta tukun, ae ko rance xanyi sae nayi naga karshen wa ennan mutanen wllh" a fusace Abba yace "kina da hnkli kuwa Aisha yayana ne fa" Ammi tace "na fi ka sanin wnn" tana fadin hka ta shige daki hawaye cike idonta don ba karamin kewar Ikram dinta take ba ko wani hali take ciki ynxu oho, su Na lado kuwa ana can station ana shan axaba, gashi bae karbi nmbr Mami ba kuma bae san gidanta ba da tuni ya fdi inda ikram take da wnn axaban da yake ci hannun yan sanda. Karfe hudu da minti goma sch bus ya ajiye Ikram a kofar gidan Mami, rana daya a sch duk ta rame ta ci kuka har ta gaji kmr warce bata taba xama a sch ba, ko dayake can gida karfe daya suke tashi daga sch, sae da teacher ta tabbatar Ikram ta shiga gida snn motar tayi gaba, Ikram ta karasa bakin kofar shiga gidan da gudu tana kwala ma Anty kira cikin kuka, Jummai ce ta fito tace "sannu da xuwa yarinya" Ikram ta shige gidan ba tare da ta kalleta ba ta haura sama da gudu sae dakin Mami amma taga ba kowa, saukowa tayi tana kuka tana kallon jummai tace "ina Anty" Jummai tace "tana nn xuwa yarinya xo kiyi wanka kici abinci kafin ta dawo" Ikram ta fasa ihu tana tsalle tana kiran Anty, da kyar da kyar jummai ta lallabata ta cire uniform tayi wanka snn ta bata abinci ta ci, tana ci kuwa tayi bacci nan kan kujera a falon, karfe biyar Aliyu ya shigo gidan sanye da kananan kaya, suka gaisa da jummai dake faman girki a kitchen snn yyi gun Ikram, a hankali ya durkusa gabanta yana kallon fuskarta, hannu yasa ya shafi fuskar ya kira sunanta murya can kasa ta bude idon da sauri, mikewa tayi ta xauna tana mitsike ido tace "ni kaina ciwo yake min" ya kamo hannunta yace "da gske, Ikram ta gyada masa kai" yace "kinci abinci?" ta gyada masa kai nn ma ya mike da sauri ya haura sama ya shiga dakin Mami sae gashi ya sauko da magani ya dauko mata ruwa a kitchen, ba musu ta karba ta sha tana yamutse fuska, yace "ya sch Ikram" ta bata fuska tace "ni baxan sake xuwa ba wllh bna son makarantar" shiru yyi yana kallonta, shigowar mota da yaji yasa ya mike da sauri ya leka yaga motar Khaleel ne, ya dawo ya xauna yana kallonta yace "sbda me Ikram" kmr xata yi kuka tace "malamar muguwa ce wllh" dariya Aliyu yyi yana kallonta, Khaleel ya shigo gidan ba tare da ya kallesu ba ya haura sama, Aliyu ya mike ya dagota yace "xo muje in gaya maki abu" ba musu ta mike da dan gown dinta iya gwiwa, Jummai ta fito da sauri tace "Dr Mami tace kar in bar kowa ya fita da ita wllh" yana murmushi yace "ae ba nisa xa muyi ba kuma Mami sae takwas xaki ganta ta tafi meetn," da dan damuwa tace "to ni dae ka rufa min asiri snn ka bari in canja mata kaya" yace "karki damu" bae kuma jiran me xata ce ba yaja hannun Ikram suka fita daga falon.
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 26.... Garden din
gidan ya nufa da ita yana rike da hannunta, tace
"lah ina ne nn?" yana kallnta yace "garden knn,
fadi in ji" tace "garden" yyi murmshi yace "yauwa
Ikram" kan carpet grass ya xauna snn ya xaunar
da ita yana kallnta yace "me aka koya maki a sch
yau Ikram" ta bata rae tace "nima ban sani ba,
kuma ae baxn sake xuwa makarntar bama" yyi
shiru yana kallnta snn yyi murmshi ya kwanta kan
carpet grass din, ita ma ta kwanta tayi ruf da ciki
a gefensa tce "ka kawo min wnn sweet din nn" ya
juya yana kalln gashinta ya mike xaune ya cire
ribbon din da Mami ta sama ta yace "waw kina
da gashi mai kyau Ikram" ta xumburo baki tace
"abnda ma ni aske shi xance Anty tayi min, idan
tana taje min sae yyi ta min xafi" yyi murmushi
yace "Mami xaki dinga ce mata ba Anty ba kinji
Ikram" Ikram tace "sbda me" yace "sbda ba
sunanta Anty ba" tayi shiru tana kallonsa snn
tace "kai ya sunanka to" ya wara ido yace "au
baki san sunana ba Ikram" ta gyada masa kai ya
kamo hannunta yana kallon cikin idonta yace
"Aliyu ne sunana" tace "nima Aliyu xan dinga ce
mka" ya girgixa mata kai yace "yayana xaki dinga
cemin" tace "to bani sweet din yayana"
murmushin jin ddi yyi snn yace "to ki fara min
duk abnda nayi maki tukun" tace "to" ya daura
hannu kan dimple dinta ita ma tayi masa hka, yyi
murmushi ya daura yatsunsa biyu kan lips dinta
ita ma tayi masa hka, dariya yyi ya rungumeta a
hankali yace "I luv yhu bbyna" ikram ta wara ido
tana kallon fuskarsa tace "lah ni ba bby bace, ni
da na girma" kmr ance ya daga kansa sama yaga
Khaleel xaune cikin balcony din dakinsa laptop
gabansa yana kallnsu, suna hada ido da Aliyu ya
fashe da dariya har da sauka daga kan kujera
Aliyu ya mike tsaye yana kallonsa ya hade rae
yace "wats funny guy" mikewa Khaleel yyi ya
shige dakinsa yana ci gaba da dariya, Ikram ta
bude baki tace "lah ashe yana dariya, ni ban sani
ba" Aliyu bae ce komai ba ya xauna ya sauke
ajiyar xuciya yana kallonta yace "je dauko sch
bag din ki" ta mike da gudu tayi cikin gida, A falo
ta tar da Khaleel ya fito daga kitchen rike da cake
da juice a plate, ta wara ido alamar mamaki tace
"yaya Khaleel ashe dama kana dariya ni ban sani
ba" ya xabga mata harara yace "kinsan Mami
bata nn dukan tsiya xan maki idan baki shiga
hankalinki ba" ta harare sa tace "to ae yayana
yana nn" Jummai tace "lah ashe baku je da nisa
ba" Ikram bata ce komai ba ta wuce sama tana
murguda ma khaleel baki ya bi ta da kallo yana
gyada kai a hankali alamar xae yi maganinta,
yana nn tsaye ta sauko rike da jakar makarantar
ta, ya fixgota da karfi yace "wa kike harara"
muryar Aliyu yaji yana cewa "hey ka taba ta kaga
idan ban rama mata ba" Khaleel ya juya yana
kallonsa ya fashe da dariya yace "girma dae ya
fadi, wae yar cikin ka ka xaunar kke ce ma I Love
Yhu, na sha suprise dinka Aliyu, ina manyan
babes dinka" dariya ssae yake ya haura sama,
Aliyu ya ma rasa me xae ce masa ya bi shi da
kallo don bae yi xaton yaji ba, Ikram tace "ni
baxan taba son yaya Khaleel din nn ba sbda yana
da bad habit, yau a sch Anty tayi mana Moral
Education ta gaya mana menene Bad Habit" Aliyu
yyi murmushi ya dafa ta yace "yauwa kanwata xo
muje ki fada min me dame Anty ta koya maki" ya
karbi jakarta suka nufi garden din tana gaya
masa menene bad habit kmr ynda taji Anty tace
yau. Ikram na xaune a falo ita da Jummai tana
cin abinci bayan Aliyu ya wuce Mami ta shigo
gidan taje ta rungumeta da gudu tana jin ddin
ganinta, Mami tace "dota kinyi karatu da kyau
yau ko" Ikram tace "eh mana yayana ya koya min
assignment dina kuma na iya bari in kawo in
maki ki ga" ba karamin mamaki Mami tayi ba
ganin ynda tayi solve din Bodmas da kanta, tace
"Ikram wa ya koya maki wnn" Ikram tace "wnn
yayana din nn mana shi ya koya min, har da
dayan ma na iya bari ki ga" Mami na kallon
Jummai tace "Khaleel ne ya koya mata?" Jumma
tace "A'a doctor ne ya koya mata" Mami ta dan
yi murmushi tace "to ya kyauta" da daddare xa
su kwanta Ikram ta ishi Mami wae ita gun
Amminta xata, Mami tasan kewar uwarta take
ssae don hka ta shiga kwantar mata da hankali
tace "kar ki damu dota ran sati xan kai ki kinji"
da kyar Ikram ta yrda don har da kukanta Mami
ta hadata da wayarta tana ta danne2 daga nn
bacci ya dauketa. Cikin sati dayan da Ikram tayi
tana xuwa sch ba karamin mmki ta ba Mami ba
don bata manta duk abinda aka koya mata, duk
da da kuka take barin gidan idan sch bus ya xo,
snn kuma da yamma Aliyu na assistn dinta ssae,
Mami ta shiga neman islamiyyar da xata sata na
yamma idan ta dawo daga sch in yaso sae lesson
din da Aliyu ke mata ya dawo da daddare, ko
kadan bata bari Ikram tayi kallo sae dae ta
hadata da wayrta tayi ta dannawa daga nn bacci
ya dauketa. Ranar asabar Mami ta shiryata cikin
kananan kaya da hijab dinta tayi kyau ssae, cikin
jin ddi tace "Mami ina xa mu" Mami tayi
murmushi tace wajen Amminki xamu dota, tsalle
Ikram ta shiga yi tana jin ddi Mami ta hade rae
tace ban hanaki wnn tsallen ba Ikram" khaleel ne
ya sauko rike da car key Mami tce "na fa ce mka
xamu fita son"

[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 31...... Mami da kanta ta shimfida tabarma ta xauna tsakar gidan bayan sun shigo snn Ikram ta xauna gefenta don Ammi tsaye tayi inda take kmr an dasa ta tana binsu da kallo jikinta a sanyaye, sae da Mami ta gaisheta snn ta kirkiro murmushi ta jawo karamar kujera ta xauna tayi mata sannu da xuwa, Ikram tace "Mami da yaya Khaleel kika xo," Mami ta girgixa mata kai tana murmushi, ganin Ammi tayi shiru yasa Mami tace "to Mmn Ikram gani dae na dawo" Ammi tayi murmushi tana gyada mata kai tace "nayi masa mgna ya kuma amince Hajiya" Murmushin jin ddi Mami tayi snn ta shiga mata gdya, Ammi dae sae kirkiro murmushi take, Karfe biyar saura suka tashi tafiya, Mami ta ciro kudi mai yawa ta mika ma Ammi, Ammi tace ita ba don a basu kudi ta bata Ikram ba, dole yasa Mami ta mayar da kudinta, har sun kai kofa Ammi tace "to ajiyarki na jiya fa Hajiya" Mami tace "ni sbda Allah na baku mmn Ikram, ba don kun ban yar ku in rike ba" tana fadin hka ta kama hannun Ikram dake daga ma Amminta hannu kmr xata yi kuka suka fita, Ammi ta bi su da kallo hawaye na bin kuncinta, anya kuwa hkn da tayi dai dai ne, komawa tayi kan tabarma ta xauna jin kafarta sun kasa daukarta ta rafka uban tagumi tana hawaye, ta bada Ikram ba tare da yrdan Mahaifinta ba, to ko ya xa su kwashe ynxu idan ya dawo, wata xuciyar tace kawae tace nemarta tayi ta rasa, mikewa tayi da sauri ta fita ta kira Almajira ta basu kayayyakin abincin da Mami ta kawo suka nufi gidan yakumbo da shi tana biye da su a baya, tasan Babn Ikram na ganinsu xae san bada Ikram tayi ba nemanta tayi ta rasa ba kmr ynda ta yanke hukuncin xata gaya masa, tasan kuma Yakumbo xata fahimce meyasa tayi hka. Dae dae wani makeken gida kmr na Mami driver yyi horn kmr ynda Mami ta umarcesa da yyi, aka bude masa gate ya shiga yyi parkn a parkn space, Ikram tace "Mami ae nan ba gidanmu bane ina ne nn?" Mami ta fito ta fito da ita snn tace "nan gidansu Aliyu ne" Ikram tace "waye Aliyu" Mami tace "baki san shi ba, wnn mai koya maki Home work" Ikram ta wara ido tana tafa hannu tace "lah yayana, to Mami dama gidanku ba gidansu bne, to shi ba yaron ki bne" Mami bata kuma ce mata komai ba ta ja ta suka shiga babban falon gidan, yan mata biyu da baxa su wuce 14 ba suka tarar xaune falon suna kallon korean Film, duk suka ta so cike da jin dadi suna ma Mami sannu da xuwa, Mami tace "ku dae ba ku gajiya da kallo ina Momynku" dayar da ke rike da remote tace "Momy ta fita amma ynxun nn tace xata dawo Hajiya ce kawae a sama" Mami ta xauna snn ta xaunar da Ikram gefenta tace "to bari in dan jirata, Mujaheed fa" yarinyar tace "ya je raka wani frnd dinsa ynxun nn xae shigo" Mami tace "yauwa gwara ya xo muyi ta ta kare tunda shi bae da mutunci, ina farida da Saiham" dayar yarinyar Aisha da bata ce komai ba tun bayan gaishe da Mami da tayi tace "farida na sama, Saiham kuma taje saloon" Mami tace "to yyi kyau ni ma daga wani wajen nake nace bari in biyo mu gaisa kwana biyu duk ba mu hadu ba" Seeyama tace "Mami ya Khaleel fa yana nn?" Mami tayi murmushi tace "yana nn, baya xuwa nn knn?" Seeyama tace "ae wnn ya khaleel din nn baya son mutane" Mami tayi murmushi kawae, yaran sae kallon Ikram suke, Ikram a hankali tace ma Mami "su waye wa ennan" Mami tace "duk kannin Aliyu ne Ikram" Ikram ta xaro ido tana kallonsu, Wata mata fara da baxa ta wuce Mami bace ta sauko kasa cikin shiga ta alfarma tana dan yamutsa fuska, tana kallon Aisha tace "uban me kike yi a nan Aisha" Aisha ta dan turo baki tace "to Momy ba kallo muke yi ba" ta galla mata harara tace "xo ki wue kar in bata maki rae, bbu TV dakinku ne magulmaciyar bnxa kawae" Mami na kallonta tana mmrshi tace "kwana da yawa Hajiya" Hajiyar ba tare da ta kalleta ba tace "lfya qlau" snn tayi hanyar kitchen tana taka tiles din kmr bata son takawa, Aisha na bubbuga kafa ta wuce sama, seeyama ta tabe baki ta ci gaba da kallonta, Ikram na kallon Mami tace "Mami wacece wnn, ni bana sonta" Mami tayi murmushi tace "mamar Aliyu ce fa" Ikram ta xaro manyan idanunta tace "wnn matar, A'a ba mamarsa bace muguwace wllh" Bude kofa aka yi wani kyakkyawan handsome guy da baxae wuce Khaleel ba ya shigo falon cikin kananan kaya yana danna wayarsa, bae lura da Mami dake xaune falon ba yace "seeyama xo kiyi min transfer don Allah banki sun ki bani kudi kuma ban son fita xuwa siyan kati kawae" kmr ance ya kalli gefensa suka yi ido hudu da Mami dake kallonsa, ya wara manyan idonsa ya juya mata baya da sauri yace "innalillahi," hanyar stairs yyi da sauri tace "ba sae ka gudu ba Jaheed dawo kawae" tsayawa yyi yana dariya snn ya juya yana kallon Mami yace "amma fa naji kunya Mami don Allah kiyi hkuri tare xamu tafi ma ynxu, jiya ma mun hadu da Khaleel......" ba shiri yyi shiru ya wara manyan idonsa yana kallon Ikram yace "waoww Mami ina kika samo wnn cute Angel din" karasowa yyi da sauri yana kallon Ikram dake kallonsa, Ikram ta juya tana kallon Mami tace "Mami yyi kama da yayana wllh, kalli shima yana da irin abun mu," ta nuna ma Mami dimple dinta.
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 33.....
Mujaheed ya wara idonsa ya karaso gaban
Ikram ya durkusa ya kamo hannunta yace "da
gske pretty" tana washe hakora tace "ehh
mana, Allah kayi kama da shi" ta shafa sajensa
tace "shima yana da irin nn hka ma Yaya
Khaleel amma ni bana son yaya Khaleel din nn
sbda kullum...." kwace hannunta Mami tayi
daga na Mujaheed da ke kallonta wit much
interest, ta hade rae tace "bana son hka, maxa
nemi square root dinka" Murmushi yyi ya mike
har lkcn yana kallon Ikram yace "to Allah ya
baki hkuri Mami amma ina kika samo yarinyar
nn wllh she's so cute" ba tare da Mami ta
kallesa ba tace 'ya ta ce" dariya yyi yana kallon
Ikram yace "pretty ya sunanki?" Ikram tace "ni
sunana Rabi'a amma Ammi da Abba da 'yan
anguwarmu suna ce min Ikram, Ammi tace...."
hararanta Mami tayi tace "rufe min bakin nn,
ban hanaki surutu da wnda baki sani ba" Ikram
tace "to ae naga yana kama da yayana ne, in
gaya masa?" Mami ta rungumota bata ce mata
komai ba tana duban agogo, Mujaheed yyi
murmushi xae yi mgna sae ga Hajiya ta fito
daga Kitchen tana kallonsa tace "Mujaheed ina
sakon da na aike ka jiya" ya juya mata baya
yace "mum na ba Aliyu" tace "Aliyu na aika ko
kai" Mujaheed yace "ban samu xuwa bne shi ne
na basa ya siyo maki" tace "to yyi maka kyau,
ae da uwarka ce ta aike ka baxa ka ce mata
baka sami xuwa ba, dan rainin hankli" tana
kaiwa nn ta haura sama, murmushi yyi ya
xauna yana kallon Mami yace "wae Momy kike
jira Mami" dae dae nn Momyn ta shigo gidan,
ba karamin farin ciki tayi ba ganin Mami, ta
wuce sama da su xuwa bedroom dinta, sae
kallon Ikram Matar take, bayan ta kawo masu
ruwa da lemo da kayan ciye ciye take tambayar
Mami inda ta samo Ikram, Mami tayi murmushi
tace "sae dae munyi waya Hajiya," matar tace
"to shknn, oga Khaleel fa yana nn ko ya koma?"
Mami tace "aa yana nn, ni ban san irinsa ba
sau biyu nake cewa yaxo nn sae yace min ya
xo ashe baya xuwa daxu su Seeyama ke fada
min" Saiham ce ta shigo dakin tace "lah Mami
yaushe kika xo shine baki nemeni ba ko" Mami
tayi dariya tace "ae na tambayeki aka ce kinje
saloon" cikin girmamawa ta gaida Mami tana
kallon Ikram da ta rungume hannunta ta tsuke
baki ita nn fushi take bata gama gaya ma
Mujaheed sunanta ba. Karfe shidda saura Mami
tayi sallama da Momy tace xasu tafi, ta rakosu
har compound suna hira, Mujaheed da ke tsaye
balcony yace "Mami kawo in maki drivin din"
ba musu ta mika masa makullin ya nufi motar
yana yafito Ikram, da sauri ta bisa ya bude
mata gaban motar ta shige shima ya shiga
driver sit, snn ya juya yana kallonta yyi
murmushi xae yi mgna ta riga sa, tace "dama
Ammi tace min kawu na lado ne yace a samin
Rabi'a sbda sunan....." Mami ce ta bude motar
Ikram tayi shiru da sauri, Mami ta hade rae
tace "me kike yi nn Ikram" Mujaheed da sae
kallon Ikram yake yace "sunanta fa take gaya
min Mami" cikin fada Mami ta fara mgna "ni fa
bana son hka Mujaheed, bani makullin motata
ka fita wnn ae wlknci ne kke min" da sauri
yace "don Allah kiyi hkuri Mami ba fa ni na
tambayeta ba wllh" cikin tsawa Mami tace
mata "dawo nn" kmr xata yi kuka Mujaheed ya
bude mata motar ta fita snn ta dawo baya ta
shiga, Mami ma ta shiga, Mujaheed ya tada
motar yana murmushi suka bar gidan. Har
suka isa gida Ikram bata ce komai cikin motar
ba tana rungume da hannayenta, yana gama
parkin Mami ta kamo hannunta tana murmushi
tace "yhu re sulkn ko dota" Ikram ta sunkuyar
da kanta kmr xata yi kuka, Mujaheed dae sae
kallonsu yake, Mami ta rungumeta tace "to yi
hkuri dotana" fito da ita tayi daga cikin motar
suka yi cikin gida, Mujaheed ya kulle motar ya
bi bayansu. Kitchen Ikram ta nufa Mami tace
"ina xaki" ba tare da ta juyo ba tace "ni ruwa
xan sha" tana shiga kitchen din ta juya tayi
facin din bango ta shiga rera kuka a hankali
amma fa ba hawaye, sae faman murxa idon
take, muryar Khaleel taji a kitchen din yce "ke"
ta juya da sauri ta karasa kusa dashi kmr xata
yi kuka tace "yaya Khaleel shi ne Mami tayi min
masifa" sae kuma ta fashe da kukan tana
kallnsa, juyawa yyi kmr baxae ce

Please Login or Register in order to submit comment