Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai
gulmata gurin Mama jummai" murmushi yyi ya kashe wutan
dakin da ta kunna sbda bala'i yyi kwanciyarsa, in ya tuna
duk sbda Aliyu take wnn abun da take sae abun ya basa
dariya.
1 min ·
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 79..... Wasa wasa
wani watan ya kusa xagayowa Ikram bata bar
Khaleel ya taba ta ba, har ya ma hakura duk da
ssae yake sha'awarta kuma ita ke takalo masa,
mugun shakkar masifarta yake, ko kadan bae son
jaraba da tsiwar Ikram ji yake kmr kansa xae rabe
biyu idan tana yi don bae son hayaniya shi kam,
gashi fa xaman lfya suke amma da ya kawo mata
batun sae tayi kwana biyu tana gaba da shi tana
xumbure xumbure. ran thursday ta fara ciwon
marar nata da safe, kuka take tana juye juye kmr
xata mutu, bae ko tanka ta ba sae da ya gama
shirinsa na office snn ya kai ta gida, Mami xata fita
office knn ita ma, da mmki tana kallonsu tace "lfya
kuma" ba tare da ya kalleta ba yace "ciwon ciki
wae" bae jira me Mami xata ce ba ya juya ya nufi
kofa yana cewa "ni na tafi office Mami" Mami da
Jummae dake tsaye falon suka juya suna kallon
Ikram dake ta rusa kuka. Kwananta biyar a gida
Mami ta kirasa ya xo ya dauketa don tun da ya
kawo ta bae sake komawa gidan ba, bayan sun
gaisa da Mami ya koma cikin mota yana jiranta, ba
a dau lkci ba ta fito jummai na biye da ita a baya,
ta bude mata motar ta shiga snn tayi masu sae da
safe, sae da suka fita daga gidan snn ya juya yana
kallonta, sae a snn ya lura da idonta da yyi jajur
sbda kuka, bae ce mata komai ba don bae san
abinda aka mata ba har suka isa gida, as usual a
fusace ta fice daga motar bayan ya gama parkin,
yyi murmushi ya bude motar ya fito ya kulle snn
ya bi bayanta, goma da rabi tana kwance daki ya
shigo, ya xauna gefen gado yana kallonta yace "me
aka maki kike kuka?" ta mike a fusace kmr jira
take, tana huci tace "daga yau idan marata na
ciwo idan baxa kaini asibiti ba ka barni in mutu a
gida, kar ka sake kaini gidan Mami na gaya maka"
tana kai wa nn ta fice daga dakin tana huci. Hka
xaman nasu ya kasance har na wata da watanni
bbu abun arxiki har tana neman shiga ss2, da ta
fara al'ada dama sae dae ya kai ta asibiti ba gun
Mami ba kmr ynda ta gaya masa, ita ko tausayinsa
ma bata ji, bata ma san wahalar da yake ciki ba,
duk ya rame abun tausayi, a watansu na takwas
ranar wani saturday suka je gida gun Mami, Mami
taji ddin ganinsu ssae, ga Ikram tayi kyau ta kara
murmurewa abunta, amma sae ta ga Khaleel dinta
kmr ba shi ba duk ya rame, Ikram dae nata murna
da jin ddin ganin Maminta ta makalkaleta, don har
sun fi xuwa gun Ammi kan wajenta, rabonta da
Mami wata kusan uku knn, kiri kiri yake kin kaita
sae dae kusan kullum suna waya. da yamma tana
dakin Jummai tana gyara mata gashi, Khaleel ya
shigo dakin Maminsa yace xae fita xuwa anjima
xae dawo, Mami tayi shiru tana kallonsa snn tace
"xauna mu yi mgna Khaleel" ba musu ya xauna
yana kallonta, a hankali tace "ka gaya min meke
damunka Khaleel?" yyi shiru har sae da ta
maimaita tambayar snn yace "bbu abinda ke
damuna mami, me kika gani" ta girgixa masa kai
tace "haba Khaleel, to idan baka fada min
matsalarka ba wa xa ka gaya ma, kana da wanda
ya fi ni ne" a hankali ya sakko kasa kusa da ita nn
da nn hawaye ya cika idonsa ya sunkuyar da
kansa murya can kasa yace "mami kin dae san ni
ba maxinaci bane, kuma...." shiru yyi ya kasa
karasawa hawaye na sauka daga idonsa, Mami ta
kasa cewa komai sae kallonsa take, mikewa yyi a
hankali ya bar dakin ta bi sa da kallo.

[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 80...... Ikram ce xaune ita kadae dakin Jummai ta hade kai da gwiwa tana rera kuka a hankali, wani mugun tsanar Khaleel take ji kawae a ranta lkcn, ko ganinsa bata son yi, ba karamin fada Mami tayi mata daxu ba, don wnn karan ba Jummai ta sa ba, cire kunya tayi ta mata da kanta, Jummai ma ta kara mata nata a kai, karfe goma saura Jummai ta shigo dakin, ta bude baki tana kallonta tace "lah ha ilah, Ikram kuka kike har ynxu" Ikram ta dago kanta da sauri tana goge fuskarta, Jumma ta dagota tace "haba ikram din Mami, to kiyi hkuri kin ji, maxa ki wanke fuskarki ki je Mami na kiranki" ba musu ta shiga bayi ta wanke fuskarta ta fito, snn ta fita xuwa dakin Mami, Mami na shan fruitsalad, tace "kin ci abincin?" Ikram ta gyada mata kai kanta a kasa duk da bata ci ba, Mami tace "to wuce kije kiyi wanka" ba musu ta nufi bathroom bayan ta dauki towel, tana fitowa tayi shafe shafenta gaban madubin Mami snn ta dauki yar vest fari tasa, ta daura xaninta ta nufi gadon Mami ta kwanta don nn xasu kwana ranar, karfe goma da rabi Khaleel ya shigo dakin, ya gaida Maminsa snn ya fita xuwa dakinsa, sha daya dae dae Mami dake kan computer ta juya tana kallon Ikram tace "a nn xaki kwanan min?" Ikram tayi shiru bata ce komai ba, can ta mike a hankali ta dauki hijab dinta tace "sae da safe Mami" snn ta fita daga dakin, yana xaune yana shan tea ta shigo dakin, ko kallonsa bata yi ba fuskarta a tamke tayi kwanciyarta ta juya masa baya. Washegari sunday da daddare suka koma gidansu bayan Mami tayi mata nasiha ssae, jummai ta dora da nata, sae da tayi kwana uku bata kulasa ba as usual, snn don kanta ta sakko ta fara masa mgnr, amma duk abinda Mami suka gaya mata a bnxa don bata yi aiki da su ba, kememe ta nuna masa ita baxata amince da shi ba don ba shi take so ba, tun daga ranar da ta gaya masa hka bae sake bi ta kanta ba a kan batun, sae dae bae canxa mata ba suna xamansu lfya kmr wasu masoya, idan yaji baxae iya ba sae dae ya dau Axuminsa kawae, in ko al'adarta ya tashi har gado ana basu a asibiti sbda ynda take wahala, amma hkn bae sa Ikram ta saduda ba, ta gwammace tayi ta wahala kmr xata mutu, har bayani likita tayi mata a asibitin da suke xuwa, a kan abinda xae sa ta samu saukin ciwon cikin nata da ta fahimce tana da aure, amma Ikram taki saurarta, sae da suka dawo gida take ce ma Khaleel, nxt tym idan cikina ya fara ciwo wani asibiti xa mu canxa matar nn ta sa min ido, yyi murmushi yace to. Satinsu uku da dawowa gidansu yaje gaida Maminsa, ta tambayesa ynxu ya ake ciki game da xamansu, ya dukar da kansa yace "nml Mami, ba matsala" har jummai sae da tayi masa mgna yace ae sun sasanta kansu, Jummai taji ddi ssae, shi kam ya dau kudirin baxae sake kai kararta ba randa Allah yyi xata gne gskya, xata gane. Suna samun holiday din 3rd term ss1 ta samu khaleel kwance a dakinsa ta xauna gefensa ta dan marairaice tace "ya Khaleel ka kai ni gun Mami inyi halve holiday dina mana, idan yaso sae in tafi gun Ammina in yi sauran" yyi shiru yana kallonta, ta hura masa iska a ido, ya mike xaune da sauri, tayi masa fari da ido tace "wnn kallon fa" ta dauke kansa yace "to je hada kayan ki" cike da jin ddi ta harhada kayanta, suka bar gida bayan la'asar, hudu da rabi suka isa gidan Mami, ya ajiye ta bakin gate bae shiga ba, yace anjima xae shigo ta gaida Mami, tana rike da jakar kayanta cike da murna ta shiga gidan, karo suka kusa ci da Aliyu bakin kofa, ya koma baya da sauri, taji gabanta yyi mugun faduwa ta kafa masa ido, ta manta yaushe rabon da ta gansa duk bayan kwana biyu sae tayi maganarsa ma Khaleel, yyi wani irin kyau, ya kara haske, waw, murmushi yyi ya daga mata hannu yace "hi" murmushin ta kirkiro ita ma a hankali tace "yayana" yace "ykk, ina mijin ki" shiru tayi tana kallonsa, ya bi ta gefenta ya fita yace "am in a haste kanwata sae na dawo, bye" binsa tayi da kallo a sanyaye har ya bace mata, ta rufo kofar jiki ba kwari ta nufi sama xuwa dakin Mami, Mami na xaune kan gado rike da wani handsome bby boy yana ta wasa, ta karaso da sauri tana kallon yaron ta wara manyan idonta tace "waw Mami ina kika samo wnn yaron" yaron da bae wuce wata uku ba ya juyo da dara daran idonsa yana kallonta, Mami tayi murmushi tace "dan ki ne Ikram, yaron yayanki ne" mutuwar tsaye Ikram tayi a wajen tana kallon yaron, Mami ta mika mata shi tace "kin ga sae kallonki ma yake kmr ya sanki, karbe shi" kasa karbansa Ikram tayi taji kafafuwanta sun kasa daukarta, dama hka ake rikon Amanar ashe, bude kofar aka yi Rukayya ta shigo dakin rike da feedern yaron, tana ganin Ikram tace "Mami, wnn ita ce Ikram din" Mami tayi dariya tace "ita ce, gashi ban kai ga kiranta ba ma, har ta xo" cike da fara'a Rukayya tace "sannu da xuwa Ikram" nn da nn hawaye ya cika idon Ikram ta kauda kanta da sauri kar su gani tace "yauwa" snn ta fice daga dakin, Rukayya ta bi ta da kallon Mmki, Mami ta kirkiro murmushi tace "rabu da ita, mgna nayi mata ynxu take fushi" Rukayya tayi murmushi tace "Ayya," snn ta karaso ta mika ma Mami feedern Sudais.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 82..... Khaleel
na gama parkin bayan sun isa gida ya juya yana
kallon Ikram dake kkrin bude motar ta fita yace
"tsaya" ta juya tana kallonsa yace "me yasa kika
fa sa hutun?" ta dan tabe baki tace "hka kawae"
xae yi magana wayarsa yyi ring cikin aljihunsa ya
ciro ya ga Mami ce ke kiransa, da sauri Ikram
tace "waye ya Khaleel?" ba tare da ya kalleta ba
yace "Mami ce" ta yo waje da ido, can kuma sae
ta bata rae, yana daga wayar Mami tace "Khaleel
kuna tare da Ikram ne?" ya daga kai yana kallon
Ikram da ta danyi tsuru tsuru tana kallonsa yace
"ehh muna tare" sae da Mami ta sauke ajiyar
xuciya snn tace "to dawo min da ita maxa maxa"
yace "to" snn ta katse kiran ya juya yana kallon
Ikram da ke kallonsa a dan tsorace yace "Mami
tace in mayar dake gida" ta xaro ido ta fashe da
kuka tana girgixa kai tace "don Allah kayi hkuri
kar ka mayar dani wllh baxan je ba" ya galla
mata harara yace "to me kika yi mata?" kmr xata
yi kuka tace "ni ma ban sani ba, kasan mene ya
Khaleel?" ya girgixa mata kai tace "kawae ka
kashe wayarka nima sae in kashe na wa ba shi
knn ba" ya harareta yace "sannunki" bae jira me
xata ce ba ya shiga tada motar xasu bar gidan ta
fashe da kuka ta rikesa tana cewa "ni wllh baxan
je ko ina ba ka ajiyeni don Allah inje inyi sllh ka
ga lkci yyi" ya girgixa kai yace "baki da gskya
knn" tana hawaye tace "A'a ya Khaleel" bude
motar yyi ya fita, ita ma ta fita da sauri suka
shiga gida, Alwala yyi ya fita xuwa masallaci,
yana fita ta kashe wayarsa da nata ta xauna
kasa tayi jigum tana hawaye, wani mugun tsanar
Aliyu take a xuciyarta amma Allah ya isar mata,
tsaki tayi ta mike ta shiga bayi don yin alwala
tana goge hawayenta, tana xaune kan darduma
Khaleel ya shigo dakin, wayarsa ya nufa da sauri
yana cewa "Mami ta kuma kira ko?" ta xumburo
baki tace "ni dae na kashe wayar" wani mugun
kallo yyi mata yace "sbda me?" ta dauke kai bata
ce komai ba tana murgude murgude, kunna
wayarsa yyi yace kar ki sake kashe min waya,
kuma ki tashi ki shirya mu wuce gida don ni ban
iya bata ma Mamina rae ba, yana kai wa nn ya
shige bathroom, binsa tayi da kallo kmr xata yi
kuka, can ta tabe baki alamar ita dae bbu inda
xata, wayarsa ya shiga ring, ta mike da sauri a
tsorace don a tunaninta Mami ce, kanwata tagani
jikin screen din wayar ta daga a tunaninta
seeyama ce ko kuma Aisha, muryar wata daban
taji murya can kasa tana cewa "haba Khaleel,
kiran knn har ynxu, idan ba ni na kira ka ba kai
baxa ka kira ba, ka dinga damuwa da warce ta
damu da kai mana dear" Ikram ta yo waje da ido
wayar na kunnanta tace "lah ila ha illallahu,
wacece wnn" katse wayar taji anyi, dae dae lkcn
da Khaleel ya fito daga bathroom yana goge
kansa, tana kallonsa baki bude tace "yaya
Khaleel wacece wnn ta kira ka" karasowa yyi ya
fixge wayarsa a hannunta yana mata mugun kallo
yace "wa ya baki ixinin daga cal dina kina da
hnkli kuwa?" kuka ta fashe da tana xagaye dakin
tana cewa "ni wllh wllh sae ka gaya min wacece
wnn ta kiraka har da cewa dear kar in je in gaya
ka da Mami" dariya ssae ta basa, ya dauki
Makullin motarsa yace "idan kin gama ina jiranki
a mota" hijab dinta ta dauka ta bi sa da sauri
tana kuka, bayan mota ta bude ta shiga bae ce
mata komai ba suka bar gidan, suna isa gida ta
bude mota da sauri ta nufi balcony, Khaleel ya
bita da kallo har ta shiga gidan snn yyi tsaki ya
fito daga motar, tana shiga falo a stairs ta kusan
cin karo da Aliyu yana sakkowa ta koma baya da
sauri ta hade rae, tana jiran ya sakko ta wuce,
taga yaki sakkowa kuma yaki bata hanya yana
kallonta, ta watsa masa harara tace "ka bani
hanya" jin yaki cewa komai yasa ta juya a fusace
ta nufi dakin Jummai downstairs, yyi murmushi
ya karasa sakkowa a hankali, jummai na xaune ta
gama yi ma sudais wanka tana canxa masa
kaya, Ikram ta shigo, jummai ta rike haba tace
"ta ina kika bar gidan nn Ikram duk kika daga
mana hankali" Ikram ta juya ta bar dakin ba tare
da ta tanka ta ba ta koma stairs don tasan ya
bar wajen ynxu, dakin Mami ta nufa ta tarda
Rukayya xaune gaban Madubi alamar ta fito daga
wanka knn, juyawa tayi da sauri xata bar dakin
suka ci karo da Khaleel, ya bi ta gefenta ya shiga
dakin, da fara'arsa suka gaisa da Rukayya yana
tambayarta yaushe suka xo, Ikram ta fice daga
dakin kamr xata rusa ihu duk ta rasa me ke
damunta, dakin Khaleel ta bude ta shiga ta fada
kan gado ta shiga rusa kuka kmr wanda aka aiko
ma da sakon mutuwa. Allah ka raba mu da
sharrin Mahassada da makiya ni da Fanz dina da
yan uwana baki daya don son da kke ma
Annabinka S.A.W Ameen. Luv yhu ol my sweet
Fanz.
5 mins · Khaleesat Haiydar...
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 83...... Bude kofar da aka yi yasa Ikram ta mike xaune da sauri tana share hawayenta, Mami ce ta shigo dakin tana kallonta tace "kukan me kike" ta fashe da wani sabon kukan tace "ba kuka nake ba" Mami tace "to yyi kyau, daxu wa kika gaya ma xaki bar gidan nn" shiru ikram tayi kanta a kasa, Mami tace "yyi maki kyau" snn ta juya ta fice daga dakin. Hka Ikram tayi ta xama ita daya a dakin kmr mayya taki fitowa, har aka fara iska alamar hadari, ta mike da kyar ta kulle windows din dakin ta koma tayi kwanciyarta, kan kace me ruwa har ya sakko, karfe tara Jummai ta shigo dakin tace "Ikram ki je Mami na kiranki, wae yau kuma miskilancin naki ne ya tashi, kin je kin debi abinci kuwa ma" Ikram ta gyada mata kai kawae, jummai tace "to maxa ki je Mami na kiranki" mikewa tayi ta sa Hijab dinta don sanyi taji take taji, ta bi bayan Jummai, Mami na xaune tana duba wani littafi Ikram ta shigo dakin, kallo daya tayi ma Sudais dake bacci kan gado Mami ta lullubesa ta xauna kasan tiles tace "gani Mami" Mami tace "tashi daga gun nn, kin ci abinci?" mikewa tayi ta koma kan kujera ta gyada mata kai, Mami tace "karya kike" kmr xata yi kuka tace "ni na ci" Mami tace "meyasa kika bar gidan nn daxu" Ikram tayi shiru bata ce komai ba, Mami tace "magana nake maki" ta sunkuyar da kanta tace "dama na xo in maki sallama ne xan tafi hutu gun Ammi, kuma na ga kina da baki shi yasa muka tafi gida kawae" muryarta na rawa ta karasa mgnr, Mami tayi shiru tana kallonta, jin shirun yasa Ikram ta daga kai tana kallonta, Mami tace "to kukan me kike daxu" ta kuma sunkuyar da kanta tace "ya Khaleel ne ya ki kaini gun Ammi kuma" nan ma Mami bata ce komai ba na kusan minti biyar snn tace "tashi ki debo abinci a dinnin ki xo nn ki ci" ba musu Ikram ta mike ta fita ta debo abincin snn ta dawo dakin, da kyar ta iya cin abincin Mami na kallonta don ji tayi kmr ta amayo shinkafar, duk ta rasa me ke damunta, tana kai plate din Kitchen ta dawo Mami tace "dauki sudais ki kai sa gun mamansa" Ikram tayi kmr bata ji taba, sae da ta maimaita instruction din snn ta mike tace "ae ban san inda take ba" Mami tace "dakin Aliyu" fuskarta a daure ta nufi gadon ta dauki yaron ta fice daga dakin, ko sallama bata yi ba a tura kofar ta shiga dakin, suna xaune kan gado yana danna laptop, tana jingine jikinsa tana kallon abinda yake yi, karasa Ikram tayi kusa da gadon ta kwantar da yaron hannunta da ya farka a tsorace sbda ynda ta ajiyesa kan gadon, snn ta juya ta fice daga dakin, Rukayya da ta bita da kallo ta dawo da dubanta ga mijinta tace "ni ban san me nayi ma Ikram ba naga kmr bata so na, kuma ni ba wae na taba ganinta bne" banxa Aliyu yyi mata ya ci gaba da abinda yake, ikram na komawa dakin Mami, Mami tace "kinyi wanka ne" ta dan yi shiru snn tace "ni baxan yi akwae sanyi" Mami tace "akwae ruwan xafi a bayi" bbu ynda ta iya ta shiga tayi wankan snn ta fito, ta dauki kayan baccinta tasa ta dan yi shafe shafenta ta haye kan gadon Mami tana game da wayarta, goma dae dae Khaleel ya shigo dakin kallo daya yyi ma Ikram ya dauke kansa, Mami tace "daga ina kke cikin ruwan nn Khaleel" ya xauna gefen gado yyi shiru kmr baxae ce komai ba, Ikram dae sae kallonsa take fuskar ta a tamke, yana shafa kansa yace "gun frndx dina naje" Mami tace "cikin ruwan nn?" yace "no kafin a fara ruwan na fita ae" Mami tace "to kaci abinci" ya mike yace "ehh na ci, sae da safe Mami" Mami tace "to Allah ya kai mu" ya fita ya rufo masu kofar ya nufi dakinsa, Mami ta juya tana kallon Ikram tace "baki ga mijin ki bne" Ikram ta dauke kai bata ce komai ba, Mami tace "to tashi ki ban waje sae da safe" mikewa xaune tayi kmr xata yi kuka, ba tare da Mami ta kalleta ba ta mike ta shige bathroom, a fusace ta fice daga dakin ta nufi dakinsa, yana xaune sanye da singlet yana sip din tea, ta kashe wutan dakin ta koma can karshen gado tayi kwanciyarta tare da rufawa da bargo, yace "kina da hankali kuwa? Tashi ki kunna min wuta kar in bata maki rae" a fusace ta mike xaune tace "an ki din" sae kuma ta fashe da kuka, yyi murmushi ya ci gaba da shan tean sa.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 84..... Da safe karfe tara saura Ikram na xaune dakin Mami tana rike da Sudais da Mami ta hada ta da tun shigowarta dakin don gaisheta, danne xuciyarta kawae take tana rike da yaron don ji take kmr ta jefar da shi, gashi sae dalala mata yawu yake a jiki wae yana wasa, duk ta wani hade rae tana kallon wani movie da ake a TV, Mami nata harkar gabanta, har Aliyu ya shigo dakin gaida Mami, Ikram bata ko kalli inda yake ba har ya fita daga dakin, Mami ta juya tana kallonta a fusace ta fara mgna "Ikram wnn ba hali me kyau bne kike tsiro kwanan nn, wae ke wace irin yarinya ce ma dae tukunna" shigowar Khaleel yasa Mami ta juya ta ci gaba da abinda take, ya duka kusa da Sudais yana masa wasa yaron sae murmushi yake alamar yana son fara dariya, shi dae yana son yaron ssae gashi sak Babansa, ya daga kai yana kallon Ikram da ta dauke kanta fuskarta a daure tana kallo, yyi murmushi yace "kuna kama da yaron naki ssae" kmr xata yi kuka ta juya da sauri tana kallon Mami ta ga ko tana kallonta kafin ta fara masa masifa, ta ga kallonta kuwa take, hkn ya hanata cewa komai, ya nemi gefen gado ya xauna yana murmushi, mikewa Ikram tayi ta fice daga dakin rike da Sudais, Khaleel yace "Mami xan je Bauchi may b xuwa gobe" Mami ta juya tana kallonsa na kusan Minti biyar shi ko idonsa na kan TV, can ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, bayan kmr minti uku ba tare da ta kallesa ba tace "me xaka je yi a Bauchi?" juyowa yyi yana kallonta yyi shiru bae ce komai ba, jin shirun da yyi yasa ta juya tana kallonsa, ganin kallonta yake yasa ta dauke kai tace "to Allah ya kiyaye Khaleel, amma da Ikram xa ku tafi tunda anyi hutu ko" yace "A'a ba da ita xa ni ba, ae ba dde wa xanyi ba" Mami tace "sbda me? Ae basu san ta ba, don hka dole da ita xaka tafi" ya dan marairaice mata yace "Mami wllh kwana biyu fa kawae xanyi in dawo, ki bari kafin a kare holiday din xan kai ta su ganta, but 4 now ni ba dadewa xanyi ba, kuma ae can gun Amminta tace xata tayi holiday......" Mami ta dakatar da shi ta hanyar masa mugun kallo tace "ban amince da hkn ba, ku shirya ku tafi tare, idan kun dawo sae taje gidan" shiru yyi yana kallonta, daga gani kasan ko kadan bae ji ddin hkn ba, ya mike ba tare da ya kalleta ba yace "to" snn ya fice daga dakin ta bi sa da harara. Da yammacin ranar Aliyu suka bar gidan bayan Mami ta cika Rukayya da Sudais da tsaraba, kiri kiri Ikram ta ki fitowa yi masu sallama, sau uku Mami na kwala mata kira duk tana ji taki sakkowa, sae dae tana jikin window a sama tana kallonsu, har suka bar gidan snn ta sulale kasa ta shiga rera kuka a hankali. Washegari da safe Mami da kanta ta shiga hada ma Ikram kayan sawan ta, Khaleel na xaune dakin yana kallonta, Ikram ko na downstairs dakin Jummai, Mami tace "kai ka gama hada naka kayan ne" ya kauda kansa yace "ni fa kwana biyu nace maki xanyi Mami, sae tula mata kaya kike" Mami ta tsaya kallonsa tace "kaya kala biyar din ne na tula mata, ni fa ban son wlknci, in har baxa ka tafi da Ikram ba to kai ma bbu inda xa ka, don ban ga amfanin xuwan na ka ba" Khaleel ya juya yana kallonta yace "haba Mami xuwa gun yan uwan Mahaifina ne ba shi da Amfani don ban je da Ikram ba" Mami tayi masa mugun kallo tace "to gaya min magana Khaleel" sunkuyar da kansa yyi bae kuma cewa komai ba, Mami tayi kwafa ta dauki wayarta da ke kara ta daga don amsa kiran, Ikram ta shigo dakin Khaleel ya bi ta da harara, bata ma san yana yi ba, ya mike ya fice daga dakin, karfe tara na safiya Khaleel ya shigo dakin Mami yace ya shirya Ikram yake jira, kiri kiri Ikram tace ita bbu inda xata da Mami tace ta shirya xa su yi tafiya da Khaleel, sae da Mami ta bata mata rae snn tana hawaye ta shiga wanka,

Please Login or Register in order to submit comment