Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali tana kallonta, gani take kmr xata gane bata je sch ba, tana gama ci ta shiga neman littafinta na xuwa makaranta don gobe xata je kada Altine da mamarta su xo su ca ma Ammi bata je ba. Yau kmr kullum Ikram ta dawo daga sch bayan Ammi ta sallameta ta bata abinci ta dauki hijabinta ikram tace "ina xaki Ammi," Ammi tace "kasuwa xanje siyo yakuwa, kina gama cin abincin ki wanke kwananon kije kiyi bacci, saura ki karar min da ruwan randan," da sauri Ikram ta mike tace "Ammi ni meyasa baki aikeni ba ai ni kike aika," Ammi tace ai ni ynxu na yaye aikenki Ikram, na dinga xuwa da kaina in siyo abinda nake bukata," Ikram ta fashe da kuka tace "wllh Ammi ni se kin aikeni, malamar mu tace mu daina barin mamarmu tana fita siyo abu da kanta bbu kyau, bad children ne ke yin hka," kuka ssae take, Ammi tace "to ai ke din ce ba kya ji Ikram," tana share hawayenta tace "kiyi hkuri Ammi Allah xan dinga ji," da kyar dae Ammi ta bata naira talatin din taje bakin kasuwa ta siyo yakuwar bayan ta ja mata kunnen kar tayi tsokana kuma kar ta dde, ta saka dan hijab dinta ta fita tana share hawayenta, har wani bari jikinta yake kawae ita dae ta ganta a kasuwa, a xuciyarta tana raya kila ma yau xata kuma ganin matar nn ta daukar mata kaya, sae tace ta kai ta yawo a katuwar motarta.

~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 5..... Sae da Ikram ta fara siyan yakuwar da Ammi ta aiketa snn ta shiga cikin kasuwar tana rike da shi a hannu bayan ta cire ledar ta jefar, fada ta tarar wasu nayi ta shige tsakiyarsu da sauri tana kallo duk da irin tunkude tan da ake yi har aka gama fadan ganin kowa ya kama gabansa yasa tayi gaba ita ma, can bangaren groceries tayi tana kalle kalle, dai dai inda ta fara ganin matar nn ta tsaya ta juya tana kallon mutumin dake xaune wajen tace "kai, kai wnn matar nn da ta taba siyan Ayaba a nn da Apple ta kuma dawowa," kallonta kawae ya tsaya yyi ta karaso kusa da shi tace "kai baka ji na ne," yace "A'a ina jin ki mana yarinya, ke hka aka koya maki a gidanku" da sauri ta daga hannu sama tana xaro ido tace "kai ni Ammina shara kawae take koya min da gyaran daki kuma na fara iya wa wllh kaje ka tambayeta ma, amma ita Altine mamarta tace ma Ammina bbu abinda ta iya sae cin abinci, kaga idan Ammina ta aikeni gidansu shafa ma ina ganin tana hura itace tana daura roba a kai xata yi girki amma fa yarinyar lukuta ce kuma bana sonta don tana dukana ni kuma ban iya dukanta ba amma akwae watarana da salame tayi mata duka wae in ji sadiya, kasan sadiya kawar salame ce kuma duk a islamiyyar mu suke, malamin mu kuma yana dukan duk wanda bae iya karatu ba ni dae kuma na iya wllh," shiru tayi tana kallon mutumin ganin ynda yake dariya ga Neighbours dinsa ma na tayasa, ta nemi benci ta xauna tana kallonsa tace "me yasa kke dariya hka, Ammina tace min mahaukaciya kadae ke dariya hka shi yasa nima na daina," dariya yake ssae yana kallonta yace "ya sunanki yarinya," tace "sunana Rabi'a amma Ammi da Abbana da yan unguwarmu suna kirana Ikram, baba yace kawu na lado ne yace a sa min Rabi'a wae sunan yayarsa ce da ta mutu kuma baxata sake dawowa ba, Ammi tace min wae da sunan mamarta xa a sa min amma sae kawu na lado yace baxa a sa ba, kasan kawu na ladon nn mugu ne kuma baya sonta....." ganin ynda mutumin nn ke dariya yasa Ikram tayi shiru tana kallonsa, can ta dan tabe baki ta mike xata yi gaba ya kirata da sauri ta juya tana kallonsa yace "har xaki tafi kawata," tace "ehh mana Ammi ce tace in siyo mata yakuwa xa muyi miya da shi yau, kila baba ya samu kudi ne ya bata, don kullum bashi da kudi yake cewa," Mutumin yace "to dan xauna muyi hira kawata," ta dawo ta xauna tana cewa "amma fa kafin dare yyi xan wuce don Ammi tace kar in dde kuma har ynxu bn dde ba ae, to ya sunanka yaro" yana dariya yace "sunana sani," tace "lah sunan baban Altine ne ae, kasan me yasa na xo nn" mutumin yace "A'a," tace "akwae wata mata da ta taba siyan Ayaba a nn gurin har na taya ta daukan kaya na kai mata bakin titi ta bani Ayaba da apple da kudi, katuwar mota ya xo ya tafi da ita, gurinta na xo ko xan ganta," yyi shiru yana kallonta tace "ta kara xuwa nn," yace "A'a ina xan sani kuwa yarinya, kwastamomi masu kudi da yawa gareni," Ikram tace "to xo ka ban Ayaba don Allah," ta fada tana nuna masa bunch din banana, ya yo waje da ido yace "ina kudin ki," ta dan marairaice tace "ni bani da kudi Ammi da baba basa bani," ya dan yi dariya yace "to idan na baki xaki dinga xuwa taya ni hira kawata," da sauri ta gyada masa kai ya dauki wuka ya yankar mata Ayaba uku ya mika mata yana murmushi don yarinyar ta burgesa ta karba tana tsalle ba ko gdya tayi gaba ta bar masa yakuwar nn kan benci, sae bayan tayi nisa ya gani ya dinga dariya neighbours dinsa na taya sa, yace "lallai yarinyar nn ta tona ma uwarta asiri, kun ga fa ta bar min yakuwar," da gudu da gudu ikram ta isa gida rike da ayabarta guda uku, wajen karfe shidda saura ita da aka aika tun biyu, rabe rabe ta shiga yi bakin xauren, Ammi har ta gaji da jira ta kada kukarta da ruwan miyan taushen, ido hudu suka yi da Ammi tana lekan tsakar gidan, Ammi ta dauke kanta bata ce komai ba, ikram na nn tsaye bakin xauren har Abbanta ya dawo ya kama hannunta suka shiga ciki yana tambayarta me tayi. Tun ranar da Mami suka hadu da Ikram bata sake samun shigowa kasuwa ba sai yau Asabar tana isa gun mai fruits dinta ya gaidata cike da ladabi ya tambayeta me xae bata yau, Mami ta xauna ta lissafo masa abinda take so snn tace "ina son nayi maka wata tambaya malam sani," yace "tambayar me Hajiya," Mami tace "wata yarinya ce ranar da na xo nn karshe ta taimaka min ta daukar min kayana dai dai can," ta nuna masa gun da yatsa, snn ta ci gaba da maganarta "shine nake son tambayarka ko ka santa," malam sani ya dan yamutse fuska alamar tunani yace "Anya kuwa Hajiya, ya yarinyar take kuma meye sunanta, ko dako take yi," Mami tace "tace min sunan ta Ikram," malam sani ya yo waje da ido snn ya fashe da dariya har da kyakyatawa, mami ta tsaya kallonsa da mamaki, yana rike ciki yace "daxun nn ta bar nn Hajiya, ki ce kawata kike nema," Mami ta mike da sauri tana kallonsa tace "don Allah ka santa, wllh ita ce dalilin xuwana kasuwar nn yau," malam sani na dariya yace kwarae kuwa ko ba Ikram Aku ba" Mami tayi murmushin jin ddi tace "to don Allah kasan gidansu,"


[1/2, 10:13 AM] ‪+234 706 205 5793‬: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 6...... Malam sani yace "A'a gskya ban san gidansu ba amma kullum sae ta xo nn" Mami ta dan yi shiru snn tace "to shknn malam sani, amma karfe nawa take xuwa nn din," yace "yawanci idan an tashi daga sch takan yo nn kan ta tafi gida wajajen karfe biyu knn, wani lkcn kuma da yamma take xuwa," Mami tace "talla take yi ne," yace "A'a ko daya wllh shiriritan ta ne ke kawota nn," mami tace "gobe lahadi kana ga xata xo nn," yana dariya yace "ae Hajiya bbu ranar da bata xuwa nn," Mami tace "to shknn gobe da yamman na xo," yace "to Allah ya kai mu Hajiya, in ji dae ko lfya" Mami tayi murmushi tace "bkm malam sani ina son ganin iyayenta ne kawae, bani fruits dina in tafi," ya shiga xuba mata fruits din da take siya yana bata lbrin Ikram da halinta tana dariya. Ikram ce tafe tana dawowa daga sch da su Altine, duk tunaninta na gun ynda xa ayi taje gun mai Ayaba kmr ynda ta sa mashi suna, jiya kwata kwata Ammi bata bari ta leka ko xaure ba, ynxu kam ba daman tace xata tafi ga su Altine su je su gaya ma Amminta, su kadae ke surutunsa ita ko tafiyarta kawae take, har suka iso kusa da wata bishiyar gauva, ikram ta dan tsaya ganin maxa biyu sama suna tsinkar gauva ga wani kuma a kasa yana kwashe su yana xuba su cikin jaka, tana kallon yaron kasa tace "xo ka ban gauva don Allah," ba tare da ya kalleta ba yace "ba a badawa," warce jakar tayi ta sheka a guje yaron ya bi ta da gudu, sauran biyun da suke sama ma suka sauko suka bisu a guje, har suka wuce su Altine, Altine tace "wllh ikram barauniya ce kuma sae na gaya ta da malama gobe a makaranta,"gudu kawae Ikram take da duk karfinta suna biye da ita a baya ga jakar gauva a hannunta yyi mata nauyi, jefa jakar tayi cikin wani katon kwata ta ci gaba da gudunta rike da jakar makarantarta ssae kar ya fadi, da kyar da ikon Allah ta iso gida don sun kusan kamata, ta sakala sakatar kofar xaurensu bayn ta shiga tayi cikin gida tana mayar da numfashi kmr xata shide, Ammi dake alwala ta mike da sauri tana kallonta tace "me ya faru Ikram ke da wa," ta shige dakinta tare da cewa "ba kowa." kofar xauren suka dinga bubbugawa hkn yasa Ammi ta yafa mayafi ta fita tana Adduar Allah yasa ba magana Ikram ta dauko mata ba da rana tsakar nn. Washegari tuesday ikram ta fito tsakar gida bayan ta ci baccinta sanye da sweater dinta don ruwa ssae aka yi daren jiya, hkn yasa Ammi bata tasheta xuwa sch ba da safe, mika tayi tare da hamma snn ta xauna daga bakin kofar dakinta tana kumbure kumburen dukan da Ammi tayi mata jiya don har dare bata bar kuka ba, Ammi na xaune tsakar gidan bakin murhu tana dama koko, ta galla mata harara tace "uwarki xata maki sllhr, sha sha sha kawae," ta mike tana bubbuga kafa ta dauko buta, tana gama break Ammi ta jika mata uniform dinta ta wanke ta yo waje da ido tace "ni safa kadae na iya wankewa," Ammi bata tanka ta ba ta shiga ciki abunta, sae kusan karfe daya ta gama wankin snn ta shanya, ta diba ruwan wanka da gudu ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta shiga dakin Ammi tace "xo ki bude min akwatina na dauki kaya Ammi," Ammi ta mike ta shiga dakin ta bude ta ciro mata yar doguwar riga iya gwiwa ikram tayo waje da ido tace "wllh baxan sa ba ni ki bani rigana da skirt," ganin ynda take kuka yasa Ammi ta ciro mata riga da skirt din ta karba tana sharewa hawayenta, Ammi ta fice daga dakin, ta daga doguwar rigar da Ammi ta fara ciro mata tana kallo tace "da da wnn kayan xanje gun mai Ayaba yyi min dariya," ta murguda baki ta wurgar, snn ta saka kayanta ta sa hula ta dan shafa powder ta fito ta shiga dakin Ammi tace "Ammi ni xanje gidansu shafa na karbo littafina," Ammi ta galla mata harara tace "baxa ki je ba don ubanki, fice ki ban waje," tayi waje da gudu ta fashe da kuka, Ammi ta bita ta kulle kofar xauren da dan kwado, daki ikram ta shige tana ta rusa kuka, can ta mike da sauri ta fita, bokitin karfe ta dauka a hankali ta shiga bayin wankansu ta kifa shi a kasa , snn ta hau kai tana lekan waje, dan Zinc din da ya kare bayin ta sama ta cire a hankali ta ajiyesa cikin bayin, snn ta hau kan bangon bayin ta dira kasa, sae da ta fara kakkabe jikinta snn ta saka kai sae kasuwa gun mai Ayaba. Yana jera Apple ta isa tana washe hakora, yace "lah ikram kwana biyu ina ta nemanki kin ma kasuwa kaura," Ikram tace "ba Ammina bane sae tayi ta rufe kofa tana hana ni fita kullum kullum kuma hka jiya tayi min duka don wasu yara sun nemi tsokanata, to shine yau na haura katangar bayinmu na fito" dariya yake ssae yace "kai ikram," ta dan marairaice tace "wllh" yana dariya yace "kinsan wata Hajiya da kika taba daukar ma kaya?" da sauri ta ce "eh ehh" yace "yauwa yau kusn kwana uku knn kullum sae ta xo nemanki," ikram tace "lah ha ila, to me kke ce mata?" yace "nace ban san gidanku ba mana," ikram ta yo waje da ido ta daura hannu biyu a ka tace "ohhw ba gidanmu na can kasan layi kusa da gidansu altine da shagon mai treda ba xaka ce mata baka sani ba," dariya yyi ssae yace "to ki xauna ma ki jirata nasan xata xo anjima," ikram ta xauna da sauri tace "to,"
[1/2, 10:13 AM] ‪+234 706 205 5793‬: Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 7...... Hudu saura Mami ta iso gun mai Fruits, har lkcn ikram na kasuwar amma gun wata mata mai saida cherry ta tafi tana ta mata xuba duk don ta bata cherryn matar dae sae dariya tke, malam sani ne ya shiga kwada mata kira don ba nisa daga shagonsa ta taho da gudu ba tare da ta lura da Mami dake tsaye tana kallonta dauke da murmushi a fuskarta ba, ikram tace "matar nn muguwa ce bata ban agwaliman ba," mami tace "Ikram," ikram ta juyo da sauri tana kallonta da gudu taje ta rungumeta tace "lah Anty yaushe kika xo," Mami tayi murmushi tace "ynxu na xo Ikram, ynxu ki fada min ina ne gidanku mu tafi" Ikram tayo waje da ido tace "me xa kiyi a gidanmu Anty," Mami tace "iyayenki nake son gani" ikram ta dauke kai tace "ba kowa a gidanmu ni dae," Mami ta dafa kafadarta tace "haba Ikram xan siya maki Ayaba da yawa fa," ikram ta washe hakori da sauri tace "to xan nuna maki, amma ni sae kin fara kai ni yawo a motarki" Mami tayi murmushi tana kallon kyakkyawar fuskarta tace "to naji ikram" Banana bunch daya ta karba gun malam sani, ya sa mata a leda snn ta karba ta mika ma Ikram, da sauri ikram ta karba, Mami tace "to muje," bata yi musu ba ta shiga gaba Mami na biye da ita a baya har suka iso bakin titi gun motarta, Driver ya fito da sauri yace "sannu Hajiya," Mami tace "yauwa Habu, snnu da jira," mami ta bude motar tace "shiga Ikram," ikram ta shiga motar tana cewa "wnn ma yaronki ne Anty," Mami tayi yar dariya tace "A'a driver ne," driver yace "ina muka nufa hajiya?" mami tace "mu tafi gida kawae" hka Ikram ta dinga mata surutu barkatae cikin motar har suka shigo cikin garin Abuja, nan fa ta manna goshinta da glass din mota tana kallon manya manyan Buildings din Abuja da tituna, kauyanci ta dinga yi ma Mami, ko me ta gani sai tayi magana, driver dae sae murmushi yake, ikram duk ta rude ita a barta ta fita tayi tafiya da kafarta wani gun ma idan an wuce sae tace ita bata gani ssae ba, sae Mami tasa driver ya koma snn su ci gaba da tafiyar, wani lafiyayyan Anguwa suka shigo driver yyi horn a wani makeken gida mai kyan gske, mai gadi ya wangale gate, ya ja motar suka shiga, idanuwan ikraam kmr su yi magana tana kikkifta su tace "nan ne gidan mamarki Anty," mami tayi murmushi ta gyada mata kai kawae, snn ta bude motar ta fito da ikraam suka yi balcony din shiga gidan, sae waige waige Ikram take, har suka shiga wani kantamemen falo, ikram ta yo waje da ido tace "ina ne nn Anty, ni dae ki maida ni gidanmu," murmushi Mami tayi ta ja ta suka haura sama, snn ta bude dakinta tana rike da hannunta suka shiga, ikram ta dan marairaice kmr xata yi kuka Mami ta xaunar da ita gefen gado tace "kar ki damu dota, nn ma gidanku ne kin ji," kai kawae Ikram ta gyada mata, Mami ta bude fridge ta ciro lemon five alive ta ajiye gabanta tace "bari na dauko maki kofi dota," nan ma kai kawae ta gyada mata, mami ta fita xuwa kitchen, a hankali ikram ta xamo daga kan gadon ta dawo kasa ta xauna ta cire hijabinta da hula snn ta jawo lemon gabanta ta bude da kyar da hakorinta ta kafa kai, mami ta shigo dakin rike da cup tace "kai dota, ga cup na dauko maki," ko kallonta ikram bata yi ba idonta lumshe sae kwankwadar five alive take, mami ta xauna tana kallonta, cike da sha'awa, Allah yasa iyayenki su yrda su bani ke ikram, abinda ta fada a xuciyarta knn, don kanta ta ajiye lemon bayan ta koshi ta lafta uban gyatsa, Mami ta dawo kusa da ita tace "kina jin yunwa ne ikram," kai kawae ta girgixa mata, mami ta shiga kwance roban da Ammi ta nade mata gashinta da, gashin suka xubo har kusan bayanta, mami ta dauko comb dinta da man kai da ribbons, ta shiga gyara mata gashin, ita ko sae kallon cartoon din da Mami ta kunna mata take, duk inda ta ga ana fada sae ta fasa ihu, mami sae dariya take, har ta gama gyara mata gashin snn ta dauko mata gasasshiyar kaxa a fridge ta dumama mata, tana cikin ci aka bude kofar dakin, wani dogon handsome ya shigo sanye da 3qtre da polo ya fada gefen mami ya kwanta, ta juya tana kallonsa ganin bata ce komai ba yasa a hankali yace "mami ban fa ci komai ba har ynxu, am jet hungry," mami tace "to ban san me kke so
[1/1, 6:29 PM] Aishat muhd: TSAFI 💀 💀TSAFI
💀
~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar
8.....
Ikram ta mike bayan ta rasa inda xata yi da naman gabanta kmr xata yi kuka tana kallon Mami dake gaban computer tace "Anty ki kai ni gidanmu kar Ammina tayi min duka," Mami tace "ynxu xan kai ki Ikram, shiga bayi ki wanke hannunki ki kuskure baki," Ikram tace "ina bayin yake, waje xan je?" Mami ta nuna mata kofar bayi ta shige da sauri, tana shiga da minti uku ta fasa ihu, mami ta mike da sauri ta shige bathroom din a rude, tsaye ta ganta karkashin shower ruwa na xuba tayi jagab, Mami tace "me ya kai ki nn Ikram, ga buta nn kina gani ki tsallake sa," tsalle Ikram ta shiga yi tana cewa "ina son in ga ko menene, ashe abun ruwan sama ne," mami ta kashe showern ta jawo ta tace "haba Ikram dubi ynda kika jika jikinki, to maxa ki cire kayan," ba musu ta fara tube kayanta, Mami ta dauko towel dinta ta mika mata tace "daura wnn," ta karba ta daura, tabi Mami suka fito, dai dai nn Aliyu ya shigo dakin da sallama, Mami ta amsa tace "amma ba dae daga gida kke ba," ya tsaya daga bakin kofar yana kallon Ikram yace "A'a nn kusa nake," Ikram tace "lah wnn yaron naki ne na ranan n Anty," Mami tayi dariya tace "ashe kin ganesa," Aliyu ya xauna kan kujera yace "ina yini Mami," Mami tace "lfya lau ya aiki," murmushi yyi bae ce komai ba, Ikram ta matso kusa da mami a hankali tace "amma Anty yana da kyau yaron nn naki," Mami ta fashe da dariya tace "ko Ikram," tayi fari da ido tace "wllh" dariya ssae Mami take, shi ko sae kallonta yake bae dae ce komai ba, Mami tace "Aliyu don Allah siyo mata dan gown nan kasuwa ta jika kayanta," ya girgixa kai yace "a gajiye nake Mami," Mami tace "to bari in aiki Khaleel, ka bude fridge ka dauki lemo mana," bae ce komai ba Mami ta fita, ya hade rae yana kallon Ikram yace "xo nan ke," ta taho gabansa ta tsaya tana kallonsa tace "gani," ya kauda kansa yana murmushi ganin ynda ta taho ko tsoro bbu, hannu ta daura kan dimples dinsa tace "lah irin abu na," ya juyo da sauri yana kallonta, ta nuna masa nata tana dariya, ya kamo hannunta yace "me kika ce ma Mami" tace "nace mata yaronta na da kyau," wara ido taga yyi yana dariya, ita ma ta fashe da dariyar har da kyakyatawa, baki ya bude yana kallonta, dae dae nn Mami ta shigo dakin, ta hade rae tana kallon Aliyu tace "meye hka Ali," sake hannun Ikram yyi, cikin harshen turanci ta shiga ce masa bata son hka, murmushi kawae yyi ya mike ya fice daga dakin, Mami na kallon Ikram tace "dariyar me kike," Ikram tace "shi naga yana dariya shine nima nayi," Mami bata ce komai ba ta shiga goge mata ruwan jikinta da towel, ta gama ta dauko manta ta shafa mata snn ta gyara mata fuskarta tace "bari Khaleel ya kawo maki sabon kaya ki sa kin ji ko," tana washe hakoran jin ddi tace "to," gefen Mami ta xauna tana ta kallon cartoon har Khaleel yyi sallama, mami ta amsa ya shigo ya tsaya daga bakin kofar yace "gashi Mami," Mami tace "ikon Allah to ka karaso mana ka tsaya daga bakin kofa," karasowa cikin dakin yyi ya mika mata, ya juya da sauri xae fita Mami tace "ka ci abincin Khaleel," bae ce komai ba har ya isa bakin kofa, Ikram tace " kmr tsorona yake Anty," juyawa yyi ya galla mata wani mugun harara snn ya fice, Ikram tace "lah ashe mugu ne ma harara na yake Anty, ni dae na fi son wnn mai kyan, meyasa kika haife shi Anty" murmushi kawae Mami tayi ta fito da ready made din gown din da ya siyo kmr an gwada ta ko dae dae ita, nan ikram aka shiga tsalle tsalle ana juye juye har da rawa, Mami sae dariya take tana kallonta cike da sha'awa, makullin mota mami ta dauka, tasa Ikram ta sa Hijab dinta snn ta kama hannunta suka fita, kwance suka tarar da Aliyu a falo, ya mike da sauri yace "ina xaku Mami" Mami tace "gida xan mayar da ita mana" yace "to bari in kai ku" Mami tace "kai da ka gaji, kayi xamanka kawae xanyi drivn din" da sauri yace "A'a na huta" Mami bata ce komai ba suka fita a tare ta bude back seat suka xauna da Ikram, snn ya tada motar suka fita daga gidan, Ikram ta dasa surutunta daga inda ta tsaya yi take ba full stop kmr radio, mami murmushi kawae take, shi ko sae kallonta yake ta madubi, wani babban supermarket Mami tace ya tsaya, ya samu waje yyi parkin, snn Mami ta fita tace tana xuwa, juyawa yyi da sauri yana kallon Ikram da ke bin Mami da kallo kmr xata yi kuka yace "Ikram" ta daga kai tana kallonsa yyi mata murmushi yace "tana xuwa kin ji," kai ta gyada masa snn tace "wa ya koya maka tuka mota," yace "dawo nn in gaya maki" ta dawo front seat din da yake nuna mata, yana kallonta yace "babana ne ya koya min" ta wara ido tace "lah, to ae ni babana bae da mota bare ya koya min"

Please Login or Register in order to submit comment