Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi yace"Bari in Kira maka ita"be jira cewar aslim ba ya shige ciki can sai gashi sun fito tare

Ni'ima na ganin Yana binta tace"Wai miye?"..

Yace"magana Nike so muyi dashi"

Suna kaiwa Abba yace"dama fad'a maka zanyi machine dina ya lalace ka siya min wani"

Aslim yace"toh dama Nima Ina son ganin ka,Ina son in roki al'farman dan Allah a d'aura aurenan a massalaci da asuba"

Ni'ima tace"saboda me Kamar auren Yar akuya,ko d'an lunching da akeyi ni bazanyi ba"

Yace"no baby wallahi Ina da Mara lafiya shiyasa Bani son biki"

Abba yace"ke ko ai hakan ya fi Lada"

Aslim yace"toh yauwa hakan yayi Yar dubu ya Ciro a mota bandir uku yace"gashi"

Baba ya dinga godiya, hararanshi Ni'ima tayi,bayan ya shige ciki Ni'ima ta kalli Aslim ba tare da tayi magana ba ya Lura jikinta a tsanyaye yake

Yace"dear what wrong?"

Tsayawa tayi tana kallonshi tace"kasan fa bana Jin turanci,banyi makaranta ba"

Yace"me ke damun ki?"

Murmushi yake tayi tace"b'ata min rai akayi,tunda nike ba a tab'a b'ata min rai irin ta yau ba,mutane Basu tunani da uzuri a rayuwa sai ka dade kana yiwa mutum alkhari Amma rana d'aya Dan sab'ani ya Shiga bazai baka dama Kare kanka ba"
Jikinshi yayi sanyi yace"waye yayi Miki laifi?"

Tace"step mum' dina ne tayi min laifi"

Dafa hanunta yayi yace"please karki sa damuwa a ranki ke da zakiyi aure ki bar musu gida,please karkiyi stressing kanki bana son kina damuwa"

Tayi murmushi sosai ya kwantar mata da hankali ko ba komai ta samu relief,shi ko a ranshi yace"hmmm ranan da Kika zo gidana Zaki gane ne"

Itako NI'IMA ta d'auka duk kalaman da yake fad'a mata ya Kai zuci cikin kwana biyun nan ba karamin kulawa yake bata shiyasa bata kawo komai a ranta ba

Bayan sunyi Hira yaje zai Kama hanunta tayi saurin janyewa yace"miye haka?"

Tace"haramune yin Haka"

Yace"ok please ki Kira min ishaq Ina son magana dashi Ina ne gidansu?"

Ni'ima tace"d'azu fa na gan shi Yana dawowa aiki ranshi a b'ace ko kulani beyi ba"

Yace"sab'ani Muka samu please ki kirashi in bashi hakuri Ina son ya yafe min"

Ni'ima tace"ok Bari in dubo shi"fita tayi a motar ta shiga makota bayan minti biyar ta fito ta gan Yana waya yana ganinta ya razana ya yanke wayar,hade rai tayi tace"dawa kake waya?"

Yace"k'anwa ta"

Tace"a gaskiya duk randa na gane kana b'oye min abu wallahi dukanmu biyu zamu fuskanci b'acin rai"

Yace"kedai kin fiya kishi ina ishaq din,ni'ima tace"cewa yayi bazai fito ba"

Shiru yayi na d'an lokaci kafin yace"Zan d'an bashi lokaci ya huce nasan dole ranshi ya b'ace Amma in ba na bashi hakuri ba hankalina bazai kwanta ba"

Ni'ima tace"toh ni zan shiga sai munyi waya"

Yace"ok then"

Tana shiga Bata zarce ko Ina ba sai d'akin Abba Aiko baya ciki ya shiga wanka bincike ta farayi har ta gan inda ya b'oye kudaden da yake samu gurin Aslim tas ta kwashe shi sanan ta fito ta Kai d'akinsu ta b'oye baba da sauri yake ya fito ya je niman bazawara daga nan ya leka chamber shiryawa yayi saf ya zo zai d'auki kudi,kudi yace"d'aukeni ai wani ihu yayi ya fito tsakar gida ihun daya fito da kowa na gidan waje ana tambayarshi meya faru ciki harda Ni'ima

Ya karaso gaban ni'ima yace"Ni'ima ba kina Nan lokacin da sirikina ya bani dubu d'ari uku in siya sabon machine ba?wallahi ban gan kudaden ba gabad'aya"

Ummi tayi tsaki tace"malam Dan rashin sanin ya kamata rokon kudi kayi gunshi??"

Yace

Maman nur
9/10/20, 6:32 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ3️⃣3️⃣-3️⃣4️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"nidai Babu abinda ya dameni da wanan surutun wallahi bazan yarda ba a fitar min da kudina in ba Haka ba wallahi kowa ya tafi gidansu bazan yarda ba"

Saude tace"ah'ah wallahi Babu inda zani ko sakina kayi Zan zauna inyi zaman ya'yana wallahi in Kuma kaki yarda in Kai ka kotu Kuma kap duniyar nan nice na baka abinda kake so nice na baka ya'ya maza har hudu ka gan ai inada lasisi zaman gidan ka"

Talatu tace"sannu me gindi haihuwar maza sai ki fadawa Wanda be haihu ba Wanda guda d'aya garesu kamar soka d'aya a Miya Amma ba ni da nake da ya'ya tara ba ai na wuci gori Kuma kema sanin kanki ne da a ce za a sakeni da ban Kai yau ba sai dai a zo a tafi a barni"

Tsawa ya daka musu dayasa kowa firgicewa yace"ni ba wanan ya dameni duk shegiyar da tasan ta d'auka min kudi ta fito dashi kafin raina ya b'ace"

Talatu tace"kowa yasan kap gidan Nan ba Mai d'auke ma Abu sai Ni'ima ko akuyan Nan ma da aka sace kai Ina da tabbacin itane"

Kallon ni'ima yayi ta harareshi ya tautausa murya yace"ya'ta nasan Wasa kike min dan Allah bani kudin sauri nike ana jirana"

Ni'ima tace"watoh kaima ka yarda ni na d'aukar ma kudi ko?toh shikenan Wallahi daga yau in saurayi ya zo wuri ka kuskura je sai nayi maganin ka tunda b'arauniy......."

Tsawar da ummi ta daka mata ne ya katseta,yace"ah'ah shalele ai bance ke Kika d'auka ba Yi hakuri,amaryar da yayi satin daya gabata ne ta fito tace malam dama kana da kudi har dubu d'ari uku kake Bari muna kwana da yunwa lailah ka cika Mara tsoron Allah"


Shidai zaman dirshen yayi a kasa ba tare daya damu da shadda shi zai b'ace ba

Deluwa tace"Allah ya ya sauke"

Jan hanun Ni'ima ummi tayi Suka shige d'aki,suna shiga ta kalleta tace"ke Kika d'auke me kudinshi?"

Ni'ima tace"ni Dan Allah ummi kyaleni,ni ban d'aukar me kudi ba"

Ummi tace"toh ai shikenan tunda ke bazaki ji magana ba"

Da misalin karfe 8:30,Ni'ima ce zaune da ummi suna d'an hira,karamin wayarta ne yayi Kara ta d'aga toh kawai tace"sai ta juyo ta kalli ummi tace"Wai Yana waje"

Ummi tace"toh ki d'an fesa tularai tunda Allah yasa kinyi wanka sai dai karki dade"

Tace"toh"sanda taje tayi brush domin Ni'ima akwai safta ta dawo ta fesa tularai tace"ummi sai na dawo"

Tana fita taje motarshi direct ta zauna

Ko amsa gaisuwarta beyi ba yace"please kun had'u da ishaq?"

Hade rai tayi tace"Wai miye tsakanin ka da ishaq da kake takura ni tun d'azu ka dameni yanzu kuma ka zo ko gaisawa bamuyi ba kana kiran ishaq"

Yace"please kiyi hakuri ishaq abokina ne nayi me laifine da in ba na roke ba bazan iya bacci ba"

Zatayi magana sai ga Abba ya fito zaman dirshan yayi a gaban motar ya saki ihu da ya razana Aslim

Fitowa yayi yace"subhannallah meya faru??"

Abba yace

Maman nur
9/10/20, 6:32 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ3️⃣5βƒ?-3️⃣6βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim

Abba yace"wallahi duk kudaden da ka bani an sace ko kwandala ba a barmin ba,ka taimaka in akwai wani ka Kara min"

Ni'ima ta ji wani abu ya taso Mata ya tsaya mata a makogoro she has never been this embarass in her entire life,hawaye ne ya cika idanunta,kallonta Aslim yayi sai yayi murmushi ya d'auke kai yace"ok baba sai dai bazai Kai na d'azu ba dan bani da cash tare Dani"

Abba yace"eh ba damuwa in har za a rage takaici"

Aslim ya bude mota ya Ciro bandir din Yar dubu ya bashi baba ya zube kasa Yana godiya

Can sai su saude da talatu sun karaso cikin hijabi duk datti suka duka suna gaidashi kallon ni'ima yayi sai tace"my step mum'"

Talatu tace"ranke dade ka taimaka ka bamu kudi mu ja jari"

A ranshi yace"duk gidan haka suke da roko"

Saude tace"ai mu iyayenta ne"

A aljihu yasa hanun ya Ciro kudi ya Basu

Abba babu kunya yace"ko wacce ku sai ta bani dubu biyu-biyu

Talatu tace"saboda muna tsoron ka ko??'

Yace"toh ku addana domin Babu maganar kudin abinci daga haka ya buga akwalan mashin dinshi ya kara gaba Suma Suka shige suna lissafo abinda zasu siya

Kallon ni'ima yayi yace"toh miye?"

Kuka ta fashe dashi ta koma mota tace"dan Allah kayi hakuri banyi dacen iyaye ba Ina son yau Zan baka labarina in ka gan bazaka iya Zama dani ba tunda wuri ka janye"

Aslim mahaifina is not responsible ya mayar da mace Riga,sawa yake ya cire a duk lokacin daya ga dama,baya siyan abinci ga ya'ya sun fi a kirga,ni kadai ne wajen mahaifiyata Kuma ta sha wuya kafin in girma,mahaifiyata ita ce duniya ta itace gabana itace bayana,bΓ yan Allah da annabinsa bani da kowa sai ita,mahaifiyata tana da lurar ciwon sugar Wanda yayi sanani sosai,wallahi na bi hanyoyi da dama Wanda be dace ba Dan in faranta mata Amma kuma bana sab'awa addini"hanunta ta d'auka ta aza akan nashi tace"Dan girman Allah in kasan Babu d'igon Sona a ranka,ka fad'a min in hakura,Amma Ina rokon ka da karkayi amfani da daman Nan ka yaudareni,karkayi amfani da condition din gidanmu ka kaskanta dani nasan Yanayin da muka had'u zai iya jawo min raini but Ina son ka sani ni ba Haka Nike ba,ni mutum ne me son tsokana kuma zan dawo ma da kudin ka "

Jikin Aslim yayi sanyi ya kasa cewa komai tace"badan komai nike son in aure Mai kudi ba sai Dan in Samu gidan rufin asiri in taimakawa ummi ta,ka ga laifina?toh in na ce zan auri talaka wa zai jikanta?"

Shidai shiru yayi Kuma ya kasa kallonta cikin kuka t tace"tun Ina yariya mahaifina ya tsaneni duk wanan soyyaya dan ya ganni da Kai ne,kaima ka gani da Idonka in ba inrresponsible father ba waye zai zo gaban sirikin shi yayi wanan "

Aslim ya tausaya mata sosai ammabeyi magana ba saima ce Mata yayi zai wuce

Yana komawa gida be zarce ko Ina ba sai side din mummy dama be fad'a mata zaiyi aure ba domin Fatima tasa yayi alkawari"

Mummy dake kokuwa da hajiya mariya a falo akan tana son ta fita Fatima na taimakonta,ganin Taki komawa yasa haushi ya dibe mummy ta wanka mata Mari da yasa yatsunta fitowa a kuncinta suna Jin sallaman Aslim Suka Fara kokarin turata Amma taki shiga d'akin saima hanyar waje da tayi da gudu ta b'oye bΓ yan Aslim

Kallon fuskarta yayi ya kalli mummy da zuciyarta ke bugawa cikin tsansan b'acin rai besan lokacin da yace"waye ya mareta ba"

Fatima ta kalli mummy,mummy ta dukar da kai

A fusace yace"Fatima magana nikeyi Miki"

Fatima ta kalli walida dake kwance a 3seater tace"fasawa walida waya tayi shine cikin b'acin rai ta mare ta Amma mummy tayi mata fad'a"

Mummy tayi murmushi tace"eh hakane"

A fusace ya jawo walida dake Jin music tasa earpiece a kunni Bata masan me ke faruwa ya wanka mata mari yace"tsarar ki ce da Zaki duke ta?"


Kuka walida ta fashe dashi tace"me nayi maka?"

Duk da mummy ba karamin haushin taji ba be hanata Kara mata ba tace"Dan iskanci mu kike tambaya me kikayi"

Zatayi magana mummy ta daka mata tsawa tace"Yi Mana shiru"cikin kuka walida ta haura da gudu

Hajiya mariya ta kurawa me Ido murmushi yayi mata ya zaunar da ita
.mummy ta zo zata Kama hanunta tace"muje oh mariya ki kwanta dare yayi"

Yace"barta abinci zan bata"be jira cewarta ba yaje kicin ya d'ibo tuwon semo da Miya ya zo yana Bata tana ci sai murmushi takeyi

Kallon juna mummy sukayi da Fatima

Ko loma 7batayi ba taki amsa Wai sai shima ya ci,ci ya fara yi yana goge Mata baki

BΓ yan sun gama ya kaita har d'akinta ya kwantar da ita be bar wajen ba sanda ya gan bacci ya d'auketa

Yana fitowa ya kalli mummy yace"please mummy a kiyaye wanan ai maltreting dinta ake "

Mummy tace"toh"

Ko kallon Fatima beyi ba ya bar falon

Kallonta hajiya mariya tayi tace"akwai matsala kodai ya fara ganowa ne?"

Fatima tace"shiyasa Nike ce Miki muyi duk abinda zamuyi da wuri gashi ya fara dukan mutane kanta Nan gaba bamu San waye next ba

Mummy tayi wani murmushi tace"hmmm zaisan ya tab'a walida da a ce yasan irin tsana Danayi me da bai kuskura ya tab'a walida ba kedai kiyi kokari ki tabbatar yayi auren

Tace"hajiya in Kuma asirin mu ya tonu fa?"

Mummy ta mike tace"hakan bazai faru ba domin na d'au lokaci Ina wanan Shirin,ke kisan irin Shirin dana dade ina yi?in baki sani ba Bari yau in baki labarin komai"

Wanene Aslim

Maman nur
9/10/20, 6:32 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ3️⃣7βƒ?-3️⃣8βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim..

Mohammed Kabir Mai naira shine asalin sunan shi Amma ana ce me Aslim

D'an ne ga Dr Kabir Abdallah wanda duniya tafi sanin sa da Mai naira saboda ba karamin attajiri bane kasancewar shi d'an d'aya tilo ga iyayensa,mahaifiyar sa,hajiya Aisha watoh kakar aslim kenan ita balarabiya ce Yar Dubai business din gwala-gulai takeyi itama ta tara ba kad'an ba mahaifinsa kuma Mohammed d'an kasuwa ne d'an Nigeria a wajen kasuwancin ya had'u da ita sukayi aure inda Allah ya Basu Kabir

Alhaji Kabir babban likita ne Dan har Yana da asibiti a Dubai da wasu kasashe mutum ne da duniya take alfari dashi kasancewarsa me illimi Kuma ya kware a aikinsa

Bayan mutuwar iyayensa ne ta hanyar asarin mota yasa shi dawowa Nigeria bΓ yan ya tattara dukiyoyin mahaifiyarsa,Niger state direct ya sauka domin nan ne asalinshi kasancewar mahaifinshi d'an bida ne nupe but sai ya bude babban asibiti a minna Nan ya nimi mata yayi auren,ya auri hajiya hauwa saidai sun shekara goma sha biyar Amma hajiya hauwa Bata tab'a b'atar wata ba an zaga ko Ina da ita gargajiya da asibiti Amma ba result,sosai ya shiga damuwa domin yana bukatar haihuwa in be haihu ba waye zai barwa dukiyarshi abu dai kamar Wasa har sukayi Shekara ashirin shiru,hakan yasa Dr Kabir tunanin kara aure,babu inda hajiya hauwa bata Yi ba ko ta shiga dan ganin auren mariya da alhaji be yiwu ba sai dai Kash komai na rayuwa rubbutace ne ta kashe kudi Amma sanda akayi auren ya auro mariya marainiyar allah,Babu abinda ya rage su dashi yana adalci iya gwargwado tsakaninsu saidai hajiya hauwa bada zuciya d'aya take zaune dasu ba,aurensu da wata uku sai hajiya mariya ta samu ciki,farin ciki gun alhaji baya misaltuwa domin yama kasa b'oye farin cikin shi Nan fa ya d'auki soyyaya duniya ya d'aurawa cikin tun ba a haihu shi ba,bakin ciki duk ya cika hajiya kamar ta had'iye rai addu'anta Allah yasa Kar a haifeshi lafiya,sai dai Bata nuna musu ba,saima Jan mariya da take a jiki tana nuna tana son ciki Nan ko ita kadai tasan irin plans din da takeyi,hankalinta be tashi ba sai Randa Suka je sacarning aka tabbatar namiji mariya zata haiho,alhaji yayi ta murna har mota ya canjawa mariya harda kyautar gida Wai ta cika me burin shi ba tare da yayi la'akari hauwa zata ji ba Dadi ba

(Yawanci haka mazajen mu keyi yanzu idanun su ya rufe da son ya'ya basa la'akari da feelings din Wanda Bata haihu ba,Allah dai yasa mu dace)Amin

Sosai ya dinga nunawa mariya soyyaya wanda bawai Yanayi dan tozarci bane shidai Allah ya d'aura me kauna yara balle inda suka dade be tab'a zato zai gan jinin shi ba shiyasa duk yabi ya haukace

A lokacin da suka Sanar da hauwa abinda mariya zata Haifa ranan kasa bacci tayi zuciyarta na tafarfasa akan me ita da ta zauna dashi na tsawon shekaru ba haihuwa farat d'aya wata ta zo ta haihu me kenan in ya mutu su zasu gaje shi ita Saida a cire mata na takaba,gaskiya bazai yiwu ba da sake

Da wanan tunanin ta fara

Na so Yi muku long page Amma kun kasa hakuri



Maman nur
9/10/20, 6:32 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ3️⃣9βƒ?-4️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim


Ta fara had'a plan na kashe hajiya mariya,itako hajiya ta bala'in yarda da ita

A kwana a tashi ba wuya,har cikin hajiya mariya ya shiga watanshi na haihuwa hajiya hauwa Bata samu nasara ba,a haka ta haihu akayi sunan kece raini sunan da ya girgiza mutane Minna domin anyi b'arnan kudi an Kai abinci gidan marayu,an tallafawa marayu,anyi rabo ban mamaki inda yaro ya sunan Mohammed Amma suna kiranshi Aslim

Ganin inda alhaji yayi b'arnan kudi yasa hajiya Kara tsanar d'an saidai bayan suna Dr ya d'auki wani hali wanda yake shiga hakkin hauwa domin ko ranan girkinta ne sai ya b'ata dare d'akin hajiya mariya Wai Yana Wasa da Aslim wani lokaci ma da d'an zaije d'akin shi Wai su yi bacci saidai in kuka Aslim yayi ya kaishi gun mariya

Hakane da yakeyi ba karamin haddasa kiyayya Aslim yayi ba a zuciyar hajiya,a haka Aslim ya Kai wata uku saidai abin gaba yakeyi

Hajiya sai ta fara Shirin kashe mariyar da d'anta wata rana tana waya da kawarta hajiya halima tana fad'a mata plan dinta,da yike hakinsu d'aya,alhaji dake labe ya ji abinda take Fadi dama kuma ya fara zarginta domin akwai randa ta d'auki Aslim din ta kulleshi a wardrobe Amma tace"yar aikine tayi hakan,Amma shi zuciyarshi ya fad'a me itace

Yana komawa ya Kira babban abokin shi Kuma lawyer shi watoh barrister Suleiman yace"su had'u a office dinshi"

Yana zuwa ya fadame komai tare da bashi muhhiman takardu na kamfanoninshi Nan ya bar wassiya ko bayan ranshi Kar a bawa kowa dukiyarshi sai Aslim ya girma yayi aure ya haihu a ganinshi a lokacin yasan ciwon kanshi,itako hajiya ta ganshi a lokacin da take waya ta dai basar ne,be bar office din ba sanda yasa hannu a wasu takkardu,barisster yayi setin camera yayi me video inda ya bar wassiyar Kuma ya mikawa barrister komai nashi,duk jikin shi a sanyaye Kamar yasan bazai kwana ba

Barin office din yayi Yana sauri yaje ya d'auke mariya saidai duk kiran da yayi mata a waya Bata d'auka ba,hakan ya Kuma tada me hankali ya gane yayi kuskuren barin su da yayi ya fito shi kadai

Number police yake son yayi dialling kawai sai wani babban mota ya d'aukeshi ko da aka duba ya riga ya bar duniya kuma driver ya gudu

A gida ko hajiya tasa anyiwa mariya allura da zai b'ata mata kwakwalwa a take ta daina magana,har ta d'auki Aslim zata kashe kawai sai Dr yace"ta barshi kila zaiyi musu amfani Nan gaba"

Bayan anyi arba'in da mutuwar alhaji hajiya hauwa tayi nasara canjawa mutane tunani da cewa"ai shock din mutuwar Dr ne yasa Mariya Shiga halin da take ciki a cewarta tunda ta sami labarin mutuwar Dr ta shiga halin da take ciki"

Bayan arba'in lawyoyi uku ne Suka zo gidan Suka zauna a falo

Barrister Suleiman yayi gyran murya yace

Maman nur
9/10/20, 6:32 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ4️⃣3️⃣-4️⃣4️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Fatima tace"toh mummy Bari in tafi na gan ranshi ya b'ace"

Mummy tace"ok ki tabbatar dai anyi auren Nan"

Tace"karki damu za ayi auren' "

Shiko Yana komawa ya kwanta zuciyarshi na tafarfasa kayan jikinshi ya cire ya shiga yayi wanka ya fito ya kwanta,kawai sai ya tsinci kanshi da shiga damuwa waya ya jawo yace"only ishaq can cheer me up Allah yasa ya d'aga,ni wanan fushin nashi ya fara sani a damuwa"

Waya ya d'auka ya fara Kiran number ishaq Amma Baya d'agawa,juyi yayi ya jawo filo ya gyra kwanciya yace"pick,pick ishaq pick"

Sanda ya Kira kusan so shidda,ni'ima dake kwance har bacci ya fara d'aukarta ta ji wayarta babba na kara,dubawa tayi sai ta gan Aslim murmushi tayi ta tashi har zata fita sai ta ji ummi tace"Ina Zaki?"

Zaro Ido tayi ta kalli ummi dake kwance tace"waya zanyi a waje ogana ne ke kira na d'au bacci kike shine banso in tashe ki"Bata jira me ummi zata ce ba ta fita,tana fita tayi murmushi ta d'auka ta canja murya

Gyra kwanciya yayi yace"thanks goodness you picked my called ishaq iam sorry please forgive me"

Ishaq yace"a gaskiya oga bazan iya aiki da kai ba tunda baka yarda dani ba,ka d'aukeni maci amana bazan iya d'auka ba gaskiya"

Aslim cikin damuwa yace"don't be like this ishaq I said iam sorry,ka zo gobe muyi magana"

Ishaq zaiyi magana yace"please badan ni ba dan Allah"

Ishaq yace"ok Zan shigo gobe"

Murmushi Aslim yayi yace"thanks dear,zan ......"

Maganarshi katsewa yayi domin Fatima ce ta shigo ta fad'a jikinshi tana baby "

Ishaq ya ji muryar mace sake bin wayar yayi da kallon sanan ya sake kai wayar kunni yace"hello sir"ji yayi an yanke wayar ni'ima tace"me hakan ke nufin Yana wajen wata kenan?

Fatima ko fadawa Aslim tayi a jiki ta saki kuka tace"dear ya maganar aure ne"

Ganin tana kuka ya jawota jikin shi yace"toh miye na kuka?"

Tace"ka gan fa har siyama ta kara haihuwa ta biyu kamar ba tare akayi Mana aure ba please kasa seriousness"

Yace"yauwa dama ina son in fad'a Miki please mu hakura da aurenan,this is not right bana son inyi betraying yar mutane,that girl is too innocent tausayin ta Nike ji"

Wani kukan ta fashe dashi tace"haba mijina meyasa zaka min Haka sanda bikin ya rage kwana biyar zaka ce ka fasa ai ko yariyar bazata ji Dadi ba Kuma in zaka saketa ba Haka za a barta ba za a bata kudi da gida ni na tabbatar inda take da kwadayin nan bazata damu ba kasan talakawa sufa kudin ya damesu ko mahaifinta ka bawa kudi tuni zai yarda kuma fa bazamu bar wani kofa da zai nuna cewa ka tab'a aurenta ba"

Shiru ya d'anyi na d'an lokaci tunawa da yayi da inda Abba yayi ta roko yace"you are right inda Kika ce haka za ayi"

Ta rungumeshi shiko sai ya fara shafata tuni ta janye jikinta tace"your phone is ringing "

Dubawa yayi ya gan ishaq sai kuma ya ajiye yace"please Fatima kad'an zanyi please"

Tace"gaskiya ni bazan iya ba na gaji"duk inda ya so ta Yarda ki tayi karshe ma ta wuce d'akinta ta kwanta tana latsa waya ta Kira ishaq

Ni'ima dake zaune ta gan Kira a babba wayar tasan daga gun aiki ne canja murya tayi ta d'aga

Fatima tace"

Maman nur
9/10/20, 6:32 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ4️⃣1βƒ?-4️⃣2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Sanda ya fara sa musu videon da Dr yayi tukkuna sanan yace"Babu wanda za a bawa dukiyar har sai Aslim yayi girma yayi aure sanan a bashi dukiyarshi saidai ya bar wassiyar in har Aslim ya mutu toh a bawa marayu dukiyarshi,wasu kamfanonin ma sunan Mariya ce akai be barwa hajiya wani abin kirki ba sai miliyan ashirin"

Ba karamin hauka tayi ba da barrister ya Gama bayani tace"wallahi karya kukeyi mijina bazai min Haka ba wallahi ya aureni tun Ina kuruciya tun ban San kaina ba farar d'aya ya barwa wasu dukiyar shi wallahi be isa ba

Tashi barrister yayi yace"ai kin dai kalla a video Babu wanda za a bawa dukiyar sai yaro ya girma in shi ya gan damar baki sai ya baki"

Tashi tayi a fusace ta haura sama tana Jin zafi a ranta bata tab'a tunanin bazata samu dukiyar cikin sauki ba

Har gida ta bi barrister

Please Login or Register in order to submit comment