Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine ki ajiye aikin ki"

Hade rai tayi,yana ganin ba fuska yace"Yi hakuri toh"

Cikin dare ya fara kokarin janta jikinshi tace"likita fa tace"naji ciwo sosai sai nan da wata d'aya,please ka kyaleni"

Bayan sati d'aya duk inda Aslim ya so ya kara Ni'ima rufe idonta tayi ta hanashi in ya matsa ta sashi gaba tana kuka haka ya hakura har ya daina magana da ita

Yau da safe ta tashi ta fara Shirin zuwa aiki,kallonta yayi fuska d'aure yace"kin ji saukin da har Zaki iya zuwa office?"

Ba tare da ta kalleshi ba tana sa hijab tace"sure"

Yace"I see,saura ki dawo da daddare ki zo ki cemin kin gaji wallahi yau zan baki mamaki domin bazanyi tolerating nonsense ba bar ganin ina binki a hankali"

Juyawa tayi zata me magana ta gan fuskarshi a d'aure sai tayi shiru

Zata fita yace"ki jira In sauke ki bana son yawu a Tasha"

Ganin ba fuska yasa ta yin shiru ta zauna tana jiranshi har ya gama shiri suka fita tare ko a mota d'aure fuska yayi yace"Ina wajen aikin ku?"

Shiru tayi"a fusace yace"tambayarki Nike"

Tace"a mobil zaka ajiyeni zan karasa da kafa"

Yace"ba inda Zan ajiye ki na tambayeki ba Ina ne wajen aikin ku?"

Tace"mtn partners"a gefen titi ya ajiyeta sanda ya gan ta shiga ya ja mota

Tana ganin ya wuce ta fito ta tare abin hawa ya kaita shagon zee ta canja Kaya

Tana zuwa direct office dinshi yayi ya gaishe shi"

Aslim Yace"ishaq ya jikin umma naka?"

Ishaq yace"alhamdullilah"

Yace"toh Allah ya Bata lafiya ka gan alert dinka jiya ko?"

Yace"eh jiya salary ya shigo"

Yace"ok"

Har ishaq zai fita yace"ishaq"

Ishaq ya juyo yace"kun had'a dangin ne dasu Ni'ima?"

Ishaq yace"me ka gani?"

Yace"your eyes?"

Ishaq yace"no bamu da dangin we are just friends"

Yace"tularen jikin ka fa"

Yace"oh oga Ni'ima ce ta bani da bikinta humra ne ta d'iba min"

Aslim yace"ok please if possible ka daina sawa Yana sani shiga yanayi,in Banda abinka me zakayi da tuleran Mata"

Ishaq yace"cikinsu na girma duk friends dina mata ne shiyasa ake kirana na Mata"

Aslim yace"I see"

Ishaq na komawa ko minti talatin ba ayi ba sai ga police sun shigo company

Manager yace"waye kuke Nima"

Security da ishaq yasawa hoda ne ya nuna ishaq yace"officer shine wanan Amma bazan gane d'ayan ba "

Ishaq ya zaro ido,Aslim ya fito zaiyi magana police din yace"in kana da abin cewa ka biyo mu office"

Haka aka tasa keyar ishaq gaba sai station Aslim yabi bayansu

Suna kaiwa station Aslim ya nimi ya kebe da ishaq yace"ko ya zasu Yi da Kai karka Yarda ka amshi laifin ka ce sharri ne in Kuma Basu yarda ba su jira lawyer ka,zanyi kokarin ganin ba a duke ka ba"

Ishaq cikin tashin hankali yace toh "

Aslim yace"don't worried Zan fitar da kai yau Ina kiran lawyer na baya d'agawa"

Ishaq ya rike kukanshi,Aslim yace"karka damu yanzu zanje office din lawyer na "

Ishaq yace"ok sir"

Aslim yaje chamber din lawyer shi ance yana court sai karfe biyar,in takaice muku duk inda Aslim ya so a fitar da ishaq ranan abin gagara yayi Wai yamma yayi sai gobe da safe,

Ishaq na Jin sai gobe hankalinshi ya tashi,a ranta tace"na shiga uku in ban koma gida yau ba gobe Ina zance me naje?"

Aslim na komawa gida

Maman nur
9/15/20, 2:24 PM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

9βƒ?9βƒ?-1βƒ?0️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Aslim na komawa gida ya duba d'akin ko ta dawo wayam,saukowa yayi ya gan Fatima da wata kawarta,mikewa tayi tace"baby ya aiki"

Ba tare da ya kalleta ba yace"alhamdullila "kicin ya Shiga ya dafawa kanshi indomie ya fito ya zauna a dining

Yana ci yana kallon agogo yace"this is after 6 and Bata dawo ba"Yana gamawa yaje d'akin yayi wanka still bata dawo ba, jallabiya yasa domin an Fara kiran sallah magrib as usual be dawo ba sanda akayi isha ya dawo rashi b'ace yace"yariyar nan ta raini ni Bari ta dawo"

9:pm nayi hankalinshi ya tashi yace"meke faruwa?ko fushi tayi ne,kila ta tafi gidansu ne"

Kiran numberta ya farayi amma sai yaji ringing a d'anki

Ya kalli gaban mirror da mamaki ya gan misssedcalls harda na ummita kwashe number yayi a wayarshi ya Kira ummi Amma Bata d'auka ba,Safa da marwa ya farayi a d'akin Yana kallon agogo

Yana ganin to 10: ya kwashi makkulin mota ya fita,gidansu yaje ya paka ya shiga da sallama

Ramlat ya gani tana wanki,gaisawa sukayi yace"Ni'ima ta zo?'

Tace"ah'ah Bata zo ba"

Yace"ummi fa?"

Tace"tana ciki"

Yace"please ki sanar da ita na zo"

Ramlat ta shiga ta tashe ummi Dan hartayi barci ummi ta fito tana goge idanunta,shiga yayi ya gaisheta cikin ladabi ta amsa tace"Lafiya da daddaren Nan?"

Yace"ummi ba Lafiya Ni'ima ce har yanzu Bata dawo ba na zo ne in duba ko ta zo Nan ashe bata zo ba"

Ummi ta zare ido tace"Bata dawo ba?"

Cikin damuwa yace"eh"

Ummi tace"toh Bari in sa hijab kuje gidansu zainab ko tasan inda take"

A tare suka je gidansu zainab suka buga musu kofa,maman zainab ta taso da a barci suka tambayeta tace"ah'ah Ni'ima bata fad'a Mata inda zata ba"

Ummi ta fashe da kuka,tace"goma fa ta wuce"

Tare da zainab suka tafi gidansu ishaq Amma a Ranan be kwana gida ba

Jikin Aslim ya fara rawa yace"zee please ko kin san wasu kawayenta?"

Ummi cikin kuka tace"tunda ka gan bata dawo ba toh akwai matsala ni'ima bata yawu"

Yace"ok ummi karki damu kije ki kwanta zanje wurin aikin nata in duba"

Tace"muje tare"

Yace"ah'ah duk inda akayi Zan Kira ki"

Ummi tace"toh sanam ta koma gida ya shiga mota

Gaban mtn partners ya paka ya gan wurin a kulle ya shafa Kai yace"ya Allah ka bayyana min matata"

Har zai koma gida sai ya gan exther resturant tsayawa yayi yace"Bari in kaiwa ishaq abinci maganar Ni'ima yasa na manta shi"

Zuwa yayi ya siyo take away din abinci sanan ya tafi police station yana zuwa ya nimi izinin ganin ishaq sai gashi a fito dashi

Murmushi yake yayi yace"sorry ban zo da wuri ba ga abinci

Ni'ima da ta ci kuka ta gaji tace"me ke damun ka na ganka a cikin damuwa?"

Yace"ishaq ban gan Ni'ima ba,ko fad'an da nayi mata da safe ne ya sata guduwa oho,tun d'azu Nike nimanta naje gidansu bata nan,naje gidan su zee nan ma bata Nan munje gidan wani wai shima ishaq baya Nan,ishaq please ko kasan inda take zuwa"

Ni'ima a ranta tace"iam doomed na shiga uku,a fili tace"ah'ah "

Aslim ya rike kai hawaye na sauko me yace"meyasa Ni'ima zatayi min haka?"

Ishaq yace*ka kwantar da hankalin inshaallah zaku ganta"

Aslim ya mike yace"meyasa d'azu kayiwa police taurin kai kaki cire Kaya?"

Ishaq yace"sir sanyi Nike ji kuma akwai tsoro a cell din"

Yace"ok inshaallah gobe barrister Yusuf zai zo ya cire ka"

Ishaq yace"ok"

Aslim yace"nayi bribing dinsu akan Kar suyi torturing dinka"

Yace"ok,but sir akwai matsala na ji ance macece Mai company nice builders naji Yan sanda suna Hira Wai tace"bazata bar maganan ba,and ko ma waye me companin Nan da Kai yake da matsala domin so suke suyi tanishing image dinka"

Yace"zamuyi magana yanxu Banda natsuwa"


Tuki yake Yana addu'a Allah yasa in ya Kai gida ya ganta sai dai Yana zuwa wayam dawowa yayi falo ya kwantq sai Kuma ya mike yace"kila tana gun mummy"

Zuwa yayi ya bugawa mummy ya dade tsaye kafin walida ta bude ya shiga mummy dake saukowa tace"Lafiya ?"

Yace"Ni'ima ta zo Nan?"

Tace"Ni'ima Kuma?"

Yace"eh taje aiki bata dawo ba na je gidansu Bata Nan Babu inda ban zaga ba"

Mummy tayi murmushi tace"ai Wanda yaki ji bazaiki gani ba ta fara nuna maka halin nasu na bariki ko,in ba Haka ba wata mayar aure ce zata fita bazata Sanar da mijinta ba?kila tana can tana holewa da samarinta ni Ina ganin yariyar nasan ba son tsakani da Allah bane Amma idonka ya rufe"

Yace"mummy in Bata nan sai da safe ya fita ya barta tsaye Baki tsaye

Komawa yayi ya kwanta a falo yana addu'a Allah yasa Lafiya

A daren ranan Babu Wanda ya runtsa cikin su ummi kwana tayi tana jiran Kiran Aslim yace"ya ganta,zee ma Haka,shima haka,Ni'ima ma Haka"

Washe gari da safe da misalin karfe 8:am

Maman Nur
9/15/20, 2:24 PM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

~Book2~

πŸ…Ώ1βƒ?-2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Da misalin karfe 8:am yayi wanka ko shafa Mai beyi ba yasa jallabiya da short nicker a ciki ko yunwa baya ji ya tafi mtn partners ya tambayesu Ni'ima abubakar suka ce basu da staff me wanan sunan"

Fitowa yayi ya kife Kai a starting mota,Kiran lawyer ne ya dawo dashi daga duniyar tunani ya d'auka

Barrister yace"sir mun samu papers a kotu yanzu Zan je a fito dashi sai dai time-time za ayi ta zuwa dashi station din"

Yace"please barrister kayi duk abinda ya dace yanzu bazan iya zuwa ba banji dadi

Da mugun zazzabi ya koma gida,ana fitar da ishaq ta tare abin hawa sai shagon zee,zee ta rungumeta tace"jiya bamuyi bacci bq,ummi nata kuka

Ni'ima ta shiga ciki ta canja Kaya ta fito tace"a station na kwana zee yau Ina cikin matsala domin duk inda zanyi karyar naje duk kun zaga"

Zee tace"mijinki kamar zaiyi hauka jiya"

Ni'ima tace"na wuce sai munyi waya"

Keke ta tare ta koma gida tana shiga ta had'u da mummy zata fita kallo d'aya tayi mata ta d'auke Kai mummy tace"yar bariki"itadai Bata kulata ba ta wuce ciki abinta"

A hankali ta bude kofar falon din ta shiga da sauri Aslim Dake kan stairs ya d'aga Kai ya kalleta

Mikewa yayi yace"ni'ima Ni'ima da gudu ya karasa ya rungumeta gam yace karki Kara tafiya ki barni please"

Ta janye jikinta domin batayi wanka ba,hade rai yayi yace"daga Ina kike?"
Tayi shiru,a fusace yace"nace daga ina kike?"

Tace"Dan Allah kayi hakuri wallahi.. ..."

Katseta yayi yace"tambayar ki Nike daga Ina kike?"rasa me zata ce me tayi ya fisgo hanunta ya jata d'anki yayi wurgi da ita ta fadi saman gado yace"Ni'ima ki fadamin kafin inyi loosing temper dina"

Tace"kayi hakuri bazan Kara ba"zuciyarshi na rafarfasa yace"Ni'ima ki fad'a min daga Ina kike?"

Tayi shiru,wayarshi ne tayi Kara ya d'aga yace"ummi gata ta dawo"

Ummi tace"toh Ina taje"

Yace"taki magana"

Ummi ta yanke wayar,yace"sanan Kuma sai kin min bayanin karyar da kike min domin naje inda Kika min karya wurin aikin ku ne sunce Basu sanki ban"

Ni'ima ta fara in Ina tace"uhrmm dama dama ehrmmm"

Tsawa ya daka mata yace"dama me?"

Fashewa da kuka tayi jikinta har rawa yakeyi

Tsaki ya ja yace"na baki nan da lokaci ki fad'a min gaskiya in ba Haka Ni'ima zan baki mamaki"Yana Gama magana ya fita ya koma d'akinshi ya kwanta sai a sanan ya samu bacci

Tashi tayi jiki ba kwari ta Shiga tayi wanka ta fito ta saka dogon riga,sanan ta sauka ta Sha tea ba bread ta bishi d'aki,bata tab'a tunanin yana da fushi Haka ba,hayewa tayi ta kwanta bayanshi tace"iam sorry"

Tureta yayi yace"tashi ki fita"zatayi magana yace"tashi ki fita nace"

Fashewa da kuka tayi tace"Dan Allah kayi haku...."

Tsawar da ya daka mata ne yasata fita da gudu

Komawa tayi ta kwanta ta ci kukanta kafin bacci ya d"auketa

Sai 2 ta tashi tayi sallah ta sauka ta dafa jelouf rice Yana dawowa tace"ga abinci"

Ko kallonta beyi ba ya haura,

Da misalin karfe 8:,pm ya bude kofarta tana zaune gaban madubi yace"ki shirya zamu fita"

Hijabi kawai tasa sanan ta fita ta ganshi a falo

Tafiyar shi yayi ta bishi a baya,tuki yake fuska d'aure Ni'ima ta aza hanunta saman nashi tace" baby iam sorry"beyi magana ba saima janye hanunshi da yayi tayi mamakin ganin gidansu ya sukaje

Tace"baby pleas..."

Be jira me zata ce ba ya fita ta bishi a baya jiki ba kwari

Gaisawa sukayi da ummi,sanda ta jira sun gaisa tace"ummi Ina yini"

A fusace ummi tace"ke zanyiwa ina yini Ni'ima "

Ni'ima tace"Dan Allah kuyi hakuri....."

Ummi ta katseta tace,"fad'a mana Inda kikaje jiya zakiyi, ba hakuri zaki bamu ba"

Shiru tayi ummi tace"ko bada ke Nike ba"

Aslim yace"ummi gata nan wallahi ban Isa da ni'ima ba abinda take so shi takeyi,girki sai ta gan dama,ko bacci Muka zo yi sai tayi shimfid'a ta koma kasa,ko kuma ta samin sharadi da in ba cika ba bazata Yi inda Nike so ba,ga karya Ni'ima Bata da gaskiya a baki ta min karyar wurin aikinta,bayan tasan bana son aikin taki ajiyewa tun satin can take min karyar Bata da lafiya,yanzu tun safe nike cewa"ta fad'a min inda taje amma taki fad'a yanzu ummi a ce ban Isa da ni'ima ba"

Ummi tace"Daman iskanci da takeyi kenan shine baka tab'a fad'amin ba?A fusace
Ummi tace"dan gidan ku Ina kikaje?"

Ni'ima tayi shiru,ummi ta rufeta da duka,yace"yi hakuri mu bita a hankali kila zata fadi mana,ummi tace"yariyar nan Yar iskance yariya ce bazata fad'a ba shagen kafiya ce da ita"

Cikin kuka tace"abinda muka Yi shi da wasa shine zaka ce Ina baka sharad'i bayan Kai ka Fara challenging dina nayi accepting yanzu ka zo ka canja magana"

Ummi ta mata kafa tace"karya zai Miki?zaki fad'a Mana inda kika je ko sai na Miki shagen duka"

Tace"ummi kiyi hakuri bazan iya fad'a Miki ba"

Ummi tace"toh ki tashi ki bar min d'anki wallahi ni'ima in ni na haife ki Kika Kara karacea shimfid' mijinki Allah ya Isa ban yafe Miki ba,kuma ko bai ni me ki ba ki nimeshi"

Ni'ima dai kuka takeyi,ummi tace"maza duka ki bashi hakuri"

Ni'ima ta mike tace"nasan nayi laifi jiya Amma meyasa zai fΓ d'a Miki ba dai-dai ba

Ummi tace"daga yau ya Kara saki abu kika ki har ya zo kunnina Zan mugun sab'a Miki"
Ni'ima ta fita tana kuka su saude suka bita da kallo suna d'aga hanci

Ummi ta kalli Aslim tace"Zama da ni'ima sai hakuri,Dan Allah kayi hakuri Kuma ka kwantar da hankalinki nasan halin Ni'ima Bata da kunya Amma bazatayi abinda ya sab'awa addini ba in ta huce zanzo har gida in lallasheta zata fad'amin inda taje Amma yanzu da ranta ya b'ace ko kasheta za ayi bazata fad'a ba,karka Bari zargi ya shiga zuciyar ka"

Yace"ko kad'an ummi bana zargin Ni'ima nidai Ina son inji inda taje ne ko hankalina zai kwanta"

Tace"karka damu zata fad'a"

Yace"toh nagode"

Sallamarta yayi Yana fitowa ya gan Ni'ima a dakalin kofar gidan ta hade Kai da guiwa tana kuka"

Yace"muje"

Tashi tayi ta shige motar Suka tafi gida

Yana parking yace"Kira min walida ta zo ta d'auki sakon mummy"

Ni'ima ta Kama hanyar part din mummy zata bude kofa taji mummy na cewa"ai so Nike kafin ya gane bani na haifesa ba Zan sa yayi sighning takardun gidan,ita kuma yariyar zan San inda zanyi da ita"

Murd'a kofar tayi mummy tayi saurin sauke waya a fusace tace"ke gidan ku ba a koya Miki sallama bane"

Ni'ima tace"Wai yace walida ta zo ta amshi tsako"tana Gama magana ta juya

Abin mamaki sai ga mummy ta biyota tana cewa"Ashe an ganta,Aslim ina ka ganta?"

Beyi magana ba Dan ya ma rasa me zaice,tace"Kai yaran yanzu in sunyi aure basa manta samarin da'yanzu haka wurin tsohon saurayinta taje,Amma ta fad'a inda taje ko? tun jiya ta hana mu bacci"

Ya Mika mata leda yace"ga maganin da abinda Kika ce in siyo Miki"

Tace"Amma Ina taje?"

Yace"Ashe wajen aunt dinta taje,tunda jiya mun d'a samu sab'ani"

Ni'ima tace"sai ka shigo"sai ya bi bayanta mummy ta bisu da kallo domin ya fara canja mata,inda da ne da bazai bata sako a waje ba

Ni'ima na Shiga ciki ta zauna gefen gado ta rike Kai"

Shigowa yayi,yace"kenan wajen saurayi kikaje ko?"

Ni'ima ta mike ta me wani kallo tace"eh nan na je"

Fisgota yayi da idanunshi da suka canja kala yace"ni zaki kalla ki ce wajen saurayi Kika je eh ni ni'ima

A fusace tace"toh me zance maka tunda zargina kake,kasa yau ummina ta furta min kalma mafi muni,kasa ummina ta gan bakina yau,miye nayi maka?Ashe ko da laifi nayi maka ai Kai me rufa min asiri ne ko?"

Yace"eh Amma Banda wanan laifin"

Tace"ni Ashe da kamin na hakura na shanye ni wawiya ce?wallahi da Ina son ummina ta tsane ka da a take a nan wurin zan tona ma asirin yaudarata da kayi ka aureni,saboda in rufa maka asiri Kuma Ina son ummita ta cigaba da ganin kiman ka shiyasa yau ban sanar da ita kana da wata Mata bayan ni ba,Kuma saboda ta cigaba da ganin girman ka shiyasa ban Sanar da ita mahaifiyar ka ta tsani ba,ko kasan meyasa Randa ka mareni a gaban mummy ban rama ba?saboda nasan ka isa dani ne despite sharri mummy tayi min Amma yau d'aya ka kasa rufamin asiri ko uzuri baka min ba"fashewa da kuka tayi ta koma ta zauna,jikinshi yayi mugun sanyi cikin kuka tace"yanzu kuma zargina kakeyi da Kai da mahaifiyar ka,gaskiya ni bazan cigaba da Zama da Kai ba ka sallame in wuce gida"

Barin d'akin yayi ba tare da yayi magana ba ya koma d'akin shi,itako wanka ta shiga ta fito tasa dogon rigar bacci ta feshe humra sanan ta bar d'akin,da sallama ta bude d'akinshi ta shiga ta ganshi Jingina da gado Yana latsa laptop

Tace"dama ummi tace"bata yarda mu raba d'anki ba,shiyasa na zo kar tsinuwanta ya bini"

Zagawa tayi ta kwanta nesa dashi ta juya me baya,kallonta yayi sai ya cigaba da yin abinda yake sai 11:40pm ya kulle ya kashe wuta ya kwanta,tuni tayi bacci,ya


Maman nur
9/16/20, 9:30 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ3️⃣-4️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ya jawota jikinshi,kuka ta fashe dashi harda sheshaka

Ya d'ago fuskarta ya kunna wuta yace"nayi laifi da nayi Miki fad'a?ni'ima nayi miki laifi dan na nuna na damu dake,wallahi tunda Fatima ke yawunta ban tab'ajin kwatankwacin abinda naji jiya ba,sai yanzu na gane abinda ishaq ke fad'a gaskiya ne abinda kake so shi kake kishinsa,sai yanzu na gane ashe da can ba son Fatima Nike ba sai hauka kawai nikeyi ,Ni'ima nayi laifi dan kin kwana a waje nayi magana,kina matan aure,kina ganin inda wani namiji ne da bai dade da warware auren ba?baby zaman kanki kike da zaki fita ki ce kar a tambaye ki kwana fa kikayi"

Itadai kuka takeyi,ya kara matseta a jikinshi it ok if baki son ki fadamin inda kika je,but Ina son ki sani shirun ki na nufin bani da muhimancin ne a gunki"Yana gama magana ya kashe wuta ya kwanta

Jikinta ne yayi mugun sanyi tana tunanin ta fad'a me ne ko kuwa,gyra kwanciya tayi ta lumshe Ido amma ba bacci take ba shima haka ya dai juya mata baya ne sun fi minti ashirin babu Wanda yayi magana

Rintse Ido tayi tace"sir Zan fad'a maka....'

Juyowa yayi ya kunna wuta yace"what do you mean by sir?"

Tace"sorry Zan fad'a maka"

Yace"Ina ji"

Tace"please kayi min alkawari bazakayi fushi ba"

Yace"sai kin fad'a"

Tace"dama abinda yasa ban fad'a maka ba shine,wallahi ba wani aiki nikeyi ba illah house help"

Ya maimaita kalman house help,ganin inda ya b'ata rai yasata cewa"Zan fad'a maka komai"

Yace"ok iam listening"

Tace"dama a wani gida Nike aiki tunda dadewa,ummi ma Bata sani ba domin nayi Mata karya a wani company nike aiki toh dama abinda yasa na b'oye mata shine,dama,dama ni ban gama makaranta ba,korata akayi a university munyi fad'a da wata,nasan ban kyauta Mata ba domin tayi sacrificing komai dan in Yi karatu but sanda ta gama wahala na b'ata komai shiyasa ban Sanar da ita ba dan nasan ranan data gane gaskiya sunana sorry,Kuma kasan bata da lafiya,ban samu aiki bane yasani Fara aikin house help kasan inda gidanmu yake ai in banyi aiki ba yunwa zai kashe mu,jiya abinda ya hanani dawowa,shine bayan na gama aiki Ina shirin dawowa,sai hajiyar ta sume Domin tana da hawar jini kuma yaranta basa nan shine nida me gadi Muka kaita asibiti toh nayi ta jiran zuwan babban yar'ta shiru shiyasa na kwana a asibiti Amma in baka Yarda ba gobe sai in kaika"

Wani kallo yayi mata yace"matata ce house help a wani gida?dan tana Jin yunwa ko rashin sutura ko?toh nagode ni'ima inda rashi ne yanzu kuna fa?kin tab'a tambayata abu na had'aki?ni'ima kin..."sai kawai yace"forget it goodnite"

Tace"wanan shine dalilin dayasa ban fad'a maka ba nasan zakayi fushi shiyasa,but iam sorry bazan Kara ba please"

Shareta yayi a fusace tace"ok then sai kowa yayi ta kasan Kuma wallahi anjima mutum ya nuna ya sanni ya gan kafirin wulakaci"

Da sauri ya juyo ya

Maman nur
9/16/20, 9:30 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ5βƒ?-6βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim

Juyowa yayi yace"who cares ba sai inje d'akin uwargidana ba"

Tsaki tayi ta juya baya tace"ka ji na rantse ko? duk randa na gane kaje d'akinta wallahi karshen aurenmu ya zo kenan"

Jawota yayi yace"tana fa da hakki a kaina Kuma tayi kokari bamu wata uku nasan inda kece bazaki Yarda "

Tsaki tayi tace"Dan Bata sonka ne shiyasa so ka daina ganin kokarinta domin a wajenta ta rabu da Kaya ne'

Shiru yayi na d'an lokaci Yana tunanin maganarta tabbas abin hakane domin Fatima bata nuna tayi kewarshi ba

Murmushi yayi ya jawota yace"toh kefa kina sona?'
Ya Kare magana da had'e bakinsu,a wanan Ranan Aslim ji yayi kamar yau ya zo duniya domin Ni'ima Bata me raki ba

Bayan ya samu gamsuwa ya rufesu da duvet yana jan hancinta

Tace"in tambaye ka Mana"

Yana shafa hanunta yace"Ina ji"

Tace"ku nawa mummy ta Haifa?"

Yace"mu biyu nida walida"

Tace"akwai Wanda take riko ne?"

Yace"no mu biyu ne kawai "

Tace"wacece umma a wurinta "

Yace"wacece umma Kuma"

Tace"wanan mahaukaciyar matar Mana"

A fusace yace"waye yace Miki mahaukaciya ce bata dai da lafiya ne amma ba mahaukaciya bace mind your language,Ina Jin anty mariya a Raina fiye da mummy bansan meyasa ba please in kina son mu shirya karki kara ce mata mahaukaciya"

Tace"but meyasa kake jinta fiye da mahaifiyar da ta Haifa?"

Yace"Nima ban sani ba muyi bacci gobe da wuri zan fita"

Tace"ok"

Lumshe Ido yayi bΓ yan minti biyar yace"baby babu maganar aiki fa"

Tace"ok,but muyi wanka ko kafin muyi bacci zaifi"

Yace"ok muje"

A tare sukayi wanka suka kwanta itako NI'IMA tunanin maganar mummy take a ranta tace"Dole akwai wani abu a kasa"

Washe gari kafin ya tashi ta had'a breakfast sanda ya ci ya koshi sanan ya tafi aiki

Yana fita ta d'auki wayar da take amfani dashi a office ta tura me text Kamar Haka good day sir,sir jiya mum dina tayi fushi akan kulleni da akayi a station tace bazan kara aiki a company ba kayi hakuri Zan kawo resignation letter na"tana gamawa ta rungume waya tace"zanyi missing office"

Da misalin 10:30 tana kwance aka kirata Ramlat ce d'agawa tayi Rahmlat tace"Ni'ima ki zo gida please ciwon ummi ya tashi tun jiya muke fama"

Ni'ima ta mike da wuri ta shiga bayi tayi brush ta fito tasa dogon riga sai ta fara kiran aslim be d'agawa text tayi me ta fad'a me,ta saka hijab da wuri ta fito tana sauri sai ta hango wani ya shigo da kafa tun daga nesa take kallonshi domin manager ne,da yike da ishaq ya Santa sai be damu ba ya shiga b'angaren mummy"

Sauri take data bishi tana fitowa tayi ta niman abin hawa babu sai tayi ta takawa a gefen titi

Wani mota ne ya zo ya paka a gabanta kafin tayi wani abu taji an turata mota tana ihu aka rufe mata baki akayi blindfold dinta

Bayan tafiya me tsawo motar ta shiga wani had'eden gida Suka shigar da ita aka d'aureta a kujera sosai take kokuwa,bayan minti talatin taji wani yace"ku bude mata fuska

Suka bude mata fuska ta fara kokuwa tana son yin magana

Dattijon mutumin yace"ku bude mata Baki"

Budewa sukayi ta saki kara,a fusace tace"

Maman nur
9/16/20, 4:23 PM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar

Please Login or Register in order to submit comment