Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewarta ba ya Kama hanun umma Suka fito har d'anki ya Kai umma tana hango Ni'ima ta fara tafi tana dariya Ni'ima ta d'ago ta kallesu,umma na ganin Hawaye a idon Ni'ima ta kalleshi kafin taje da gudu ta rungume Ni'ima

Ni'ima tace"umma ta kara dukarki ko?"
Kama hanunta tayi suka sauka kicin Ni'ima ta dafa musu indomie,suna ci tare babu ko kyama domin umma da hannu biyu take ci"har suka cinye

Saukowa yayi ya zauna a dining yace"Ina abincina?"

Ni'ima batayi magana ba ta haura ya bita da kallo,Kama hanun umma yayi ya maida ita har d'ankinta ya kaita ya kwantar da ita sanan ya fito

Yana komawa d'anki dai-dai Ni'ima na fitowa daga toilet tayi alwala

Kallonta yayi yace

Maman Nur
9/13/20, 11:28 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ8βƒ?5βƒ?-8βƒ?6βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"Wai wanan wani salon wulakanci ne ?"

Dadduma ta d'auka zata shimfide ya kwace yace"kin Fara kaini bango fa wanan ai ranin hankaline kina gama sallah kije kicin ki dafa min abinda zanci"

Ji yayi tace"bazan Yi ba"

Yace"ni kike fadawa bazakiyi ba?"

A fusace tace"toh Kai waye da bazan ce maka bazanyi ba ni baiwar ka ce ko a baya danayi na ga dama ne,Amma bazanyi ba Kuma wallahi the next time ka Kara d'aga hanun ka mareni a gaban mutane Nima ramawa zanyi yau kara nayi maka Amma in ka karayi Zan baka mamaki,maganar abinci kuma in matarka bazata shiga kicin ta dafa maka ba toh ka d'auko househelp ko ka cigana da cin take away Amma karka Kara shiga harkarta domin bani da had'in da Kai in Kuma ka cigaba da matsamin toh wallahi Zan bar maka gidanka tunda ba Dole bane inda baka Sona haka Nima bana sonka"

Shiru yayi zuciyarshi na bugawa,dadduma ta d'auka ta shinfid'e ta tada sallah

Gajiya yayi da tsayuwa shima ya fita massalaci sai bΓ yan isha ya dawo harta kwanta,kasa ya koma ya soya kwai ya Sha tea komawa yayi ya tura Kofa ya ji shi a rufe
Da karfin tsiya yake jijjiga kofar yace"ki taso ki bude kofar nan kan ranki ya b'ace"

Banza dashi tayi har ya gaji ya bar wurin sai kwafa yakeyi ya koma d'ankinshi ya kwanta

Fatima dake jinsu ta tabe baki ta Kwanta tace"jararbabe"

Ji yake kamar yaje d'ankin Fatima ya kwanta Amma besan meyasa zuciyarshi ke hasko me Ni'ima ba tsaki yayi tunawa da yayi Fatima tace"ta Basu wata uku kafin a fara raba kwana


A haka ya kwana ranan ba bacci kirki sai juye-juye

Sallah asuba ne ya tadashi yaje massalaci yana dawowa ya Kara zuwa kofar d'ankin fatima sai ya ji shi a bude ajiyar zuciya ya sauke ya shiga ciki amma bata ciki"

Ya duba toilet bata ciki da gudu ya sauka motsi ya ji a kicin sai ya shiga ya rungumeta ta baya

Juyawa tayi tace"miye Haka?"

Kankameta yayi yace"iam sorry in maganar jiya ne ya b'ata miki rai kiyi hakuri please"

Tureshi take sonyi Amma ya kankameta

A fusace tace"ka sakeni bana son kana tab'ani"

Yace"ai babu ruwan fad'an mu da tab'a jiki fadar mu daban tab'a jiki daban"

Tsaki tayi ta janye jikinta ta juye indomie ta tasa cokali d'aya yace"ai biyu zaki sa"

Kafin tayi magana ya d'auki wani cokalin ya bita,duk inda ta so ta hanashi sanda ya cishi sanan ya Kama hanunta ya kaita d'anki yace"oya mu koma bacci"

Tace"ni bana jin bacci,Shirin aiki zanyi"

Yace"Ina mun Gama magana akan wikin nan"

Tace"ah'ah ka Fara wining challenge din tukkuna sai in gan abinyi,karka manta yau day2 "

Yace"ba dai kin ce in naci kome nace kiyi zakiyi ba?"

Tace"eh,Nima in na ci komai nace kayi zakayi"

Ya tashi ya dawo kusa da ita ya jawo ta jikinshi kokuwa take dashi Amma ya rike ta Gam had'e bakinsu yayi sanda yayi son ranshi ya barta yace"Zan baki mamaki
Tsaki tayi ta shige toilet yace"ko in raka ki ne?"

Ya ji ta banko kofa yayi dariya ya koma ya kwanta

Da misalin karfe 8:30 ta Isa office ta fara duk wani aiki daya kamata tayi

Shiko sai 10:30 ya shigo

Misalin 11:30 Fahad ya zo office din

Had'e rai yayi, Fahad yayi murmushi yace"hakuri na zo baka"

Yace"karka kara yi min irin wasan Nan"

Fahad yace"ok,ya su Madam's me Mata biyu"

Yayi murmushi yace"wallahi ko kai me mata d'aya ka fini jin dadi ita Fatima dama ba wife material bace,ita kuma ta biyu sanda ta latsa min zumq a baki sanan ta yadani,yanzu abincinan ba samu nike in ci ba,wallahi Fahad rabon da in kwanta da mace nafi wata daya da wasu kwanaki"

Fahad ya zaro Ido yace"ita amaryar fa?"

Yace"ai ita in Banda fitina da ruwan matsifa babu abinda ta iya,Amma da farko baka gan abubuwan da take min bane har cewa nike na auro Wanda idonta ya bude yanzu zero wai ta daina sona,ka ji raini hankali"

Fahad yace"Kai sonta kake?"

Yatmusa fuska yayi yace"so kuma?"

Fahad yace"cikinsu da Fatima yanzu dawa kafi Jin dadin kasancewa da ita?"

Yace"Ni'ima ofcause"

Fahad yayi murmushi,Aslim yace"yanzu fa Wai sai na ci challenge before I sleep with my own wife"

Dariya Fahad yayi yace"challenge kum"labarin komai ya bashi

Fahad yace"yanzu ya zakayi?"

Yace"nidai sai nayi wining challenge din nan at all cost"

Fahad ya mike yace"toh Allah ya bada sa'a ni na wuce"Amma ya d'au aniyar sai ya nimo ni'ima sunyi magana

Yace"yau in na tashi a office zani gidan ku in gaida daddy munyi kwana biyu"

Fahad yace"ai ka guje mu'

Yace"zanzo"

Da misalin karfe 4:30 ishaq ya bar office shagon zee taje bayan ta canja shiga "

Zee ta kalleta tace*challenge fa Kika ce?toh in yayi wining fa?"

Ni'ima tace"bama Zan Bari yayi wining ba"

Zee tace"Allah yasa bakiyi kuskuren accepting wanan challenge din ba,ni tsorona ki samu ciki"

Ni'ima tace"karki damu Zan kula"

A gaban shago ni'ima ta tare Keke sai gida tayi mamakin ganin ta rigashi ta shiga d'anki ta tube atamfar jikinta tasa dogon riga taje kicin ta fara had'a kus-kus

Tana dining tana ci sai gashi ya shigo,satar kallonta yayi ya ajiye jaka a kujera sai ga Fatima ta shigo itama alamun anguwa taje

Rungumeshi tayi sai ya saci kallon Ni'ima ya gan ta d'auke Kai

Murmushi yayi,Fatima tace"baby Sannu da dawowa"

Murmushi yayi ya Kama hanunta ya yayi kissing,satar kallon ni'ima yayi sai idonsu ya had'u ta kau da nata

Yace"baby da alamu kin gaji"

Zama tayi tace"wallahi yau mun sha harka"

Ni'ima ta harareshi duk Yana kallonta a sace

Zama yayi yace"na gaji wallahi dama zan samu wata yar albarka tamin tausa da girki gaskiya dana gode Mata"

Fatima ta mike tace"baby Nima a gajiye nike Bari inje in huta"

Ni'ima ko kasa cigaba da cin abincin tayi ta tashi ta kai kicin saban b'acin rai ta mance ta juye Wanda zataci anjima a kula balle ta b'oye

Yana ganin ta haura sama yayi murmushi ya bita

Da sallama ya shiga d'ankin Amma Bata amsa ba saima tsaki da ta ja

Ajiye jaka yayi yace"baby what wrong meke damun ki"ya Kare da Kai hanunshi zai tab'ata a fusace tace"karka kuskura ka tab'ani da wanan kazamin hanunka,sai ka je ka Gama kazanta da wasu zaka zo ka tab'ani toh wallahi ina son ka sani ni Ina da kyakyami bazai yiwu a tab'a kazamai a zo a tab'ani ba ehhe"

Murmushi jin dadi yayi yace"waye kuma kazamai badai Fatima ba,baby dole fa kiyi accepting Fatima a matsayin matata,domin zakuyi sharing abu d'aya

A fusace tace"wanan yana d'aya daga cikin abinda yasa baxan tab'a Bari ka tab'ani ba,dan bazai yiwu kaje ka saka jikin ka a wani datti ba ka kwaso cuta ka zo kace zaka sakamin ba bazai yiwu ba Wallahi"

Yace"baby ai ana wankewa bawai daga can za ayi Nan direct ba sai anyi wanka an wanke,ko yanzu kikace inje in wanke sai inje in wanke ko ke ki wanke min in Zaki bani hakkina zan yarda"

A fusace tace"ubanwa za ayiwa tsome?Allah ya kiyaye bancin ka gama tsomawa a wani wuri"da iyakar gaskiyarta take magana

Besan lokacin da ya kyakyale da dariya ba,wani haushi ne ya dibe ta fashe da kuka tace"Allah ya Isa tsakanina da Kai tun farko da na san kana da mata da ban aureka ba "

Jawo ta yayi jikinshi yana lallashinta ta lafe tana sauke ajiyar zuciya,yace"toh sai hakuri tsome ya zama ya Zama dole

Tureshi tayi ta koma ta Haye gado shiko tsintar kanshi yayi cikin farin ciki yaje kicin ya cinye kus-kus din tas

Itako bata kara saukowa ba,yana gamawa ya tafi massalaci sai bΓ yan Isha ya dawo yau bata kulle kofa ba Yana murd'awa kofar ya bude

Ya gan tayi shimfid'a a kasa ta lumshe Ido shi yasan ba bacci take ba

Yace"kinyi bacci ne?"ya ji shiru

Tube jallabiyar jikinshi yayi a ranshi yace"day2 ba abinda nayi karfa yariyar nan tayi wining,Bari dai in Bari tayi nisa a bacci

Kwanciya yayi a gado besan lokacin da bacci ya d'aukeshi ba,sai 2:am ya bude Ido zaro ido yayi ya duba agogo ya gan time yace"perfect yanzu nasan bazata iya kokuwa ba tashi yayi a hankali ya sauka a kasa ya kwanta a bayanta zai Kai hannu ya ji tace"idona biyu"
Tsaki yayi yace"and so in idonki biyu"

Tace"na fad'a maka ne kayi using another trick wanan yayi failing "

jawota yayi ya matseta Suka Fara kokuwa dukda yayi nasarar cire mata riga Amma tasa wando rana nan gajiya yayi ya barta

Ta mike tana numfashi tana dariya tace"Kar Nike malam"

Tsaki yayi ya naushi iska

Itako bayi ta shiga ta d'auro alwala tana fitowa ya fara rokonta wallahi kad'an zanyi please"

Tsaki tayi ta tada sallah nafila,da asuba Yana dawowa daga massalaci ya ganta ta koma gado ya haye ya jawota ya rungume tana jinshi tayi shiru

Yace"baby kiyi hakuri please kin ji?kad'an zanyi"

Murmushi ne ya so sub'uce mata ta gimtse

A fusace yace"ki bani ko inyi Miki allah ya Isa wallahi,in biya sadaki kuma in wahala

Tashi tayi tace"Bari inyi shiri Kar in makara

Day3

Maman Nur
9/14/20, 3:29 PM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ8βƒ?7βƒ?-8βƒ?8βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim

Falo ta sauka ta soya kwai ta had'a tea ta Sha sanan ta koma d'anki ta ganshi kwance ya lumshe ido

Dariya tayi tace"da nine Kai da na dade da accepting defeat ka sani bazakayi wining challenge ba"

Bude ido yayi yace"hell no zanyi wining wait and see"

Tace"good luck then"

Yace"nagode da addu'ar ki"

Shiri tayi ta d'auki jaka tace"na wuce aiki sai na dawo"

Har zata fita yace"a Ina kike aiki?'

Juyowa tayi tace"Ina ruwarka?"

Yace"ok Bari inyi wining challenge zaki Sha mamaki"wucewa tayi ta barshi sai 11:30 ya tashi ya shirya duk baya Jin dadin jikinshi"

A shagon zee ya sauka ya zauna ta gaishe shi"

Ya amsa yace"zee taimakon ki nike nima please ki fada min weakness din kawarki I really want to win this challenge"

Zee tace"wani challenge?"

Yace"kedai ki fad'a min weakness dinta her likes and dislikes inda take aiki da dai sauransu "

Zee tace"bazanyi betraying friend Dina ba but abinda zan fad'a maka shine show her love,ka Kai mata breakfast gado,ka mata girki,kata ririta,nasan in ka mata haka kome kake so zatayi maka"

Yayi shiru,zee tace"Lafiya tunanin me kakeyi?"

Yace"tunani nike kawai farat d'aya ta ganni na fara ririta ta bazatayi zargin wani abu ba kin santa fa wayau ne da ita Kamar b'are"

Zee ta kyakyale da dariya tace"ka jarraba"

Sallamata yayi yau da wuri ya sallami ishaq yace"zai koma gida"

Yana zuwa gida ya tube ya fito ya fara had'a mata abinci sai zufa yakeyi albasa ya Shigame ido yace"duk fa akan a bani hakkina gaskiya ni na Fara gajiya"

Yana cikin aiki yaji shigowarta,fitowa yayi falo yaje zai rungumeta tayi saurin matsawa baya tace"kana lafiya dai ko?miye haka?sabon salo"

Yace"kai baby daga kawai zanyi welcoming matata nayi laifi"

Ratsa gefenshi tayi tace"in plan ne Bari in gaya maka it won't work"

Hayewa tayi ya bita,Fatima da saukowarta kenan tace"ikon Allah shifa akan mace babu abinda bazaiyi ba yanzu haka hanashi tayi"

Suna Shiga dakin yace"baby Bari in had'a miki ruwan wanka sanan in Miki tausa kafin ki ci abinci"

Dariya tayi tace"lallai kai jarrababe ne yanzu duk akan gado kake wanan bautar"

Yace"laifine Dan namiji ya tambayi hakkinshi gun matarshi baby zan Rama fa,Kuma ki da kyale ki kawai nikeyi da Koda karfin tsiya sai bayi"

Tace"Kai ka sani bari inje inyi wanka"

Yace"ok Nima Bari in sauka in duba abinci"

Tana shiga ta kulle kofa"

Tsaki yayi yace"hanya ba Wawa zee ta maidani ba"

Tana fitowa ta zauna a mirror tana tsafe kitson kanta,sai gashi ya shigo da abinci yace"baby sauko mu ci"

Tabe baki tayi tasawa kanta net ta sauka ta d'auki cokali shidai kallonta yake"

Tace"Fara ci"
Yace"Baki yarda dani bane?"

Tace"kaidai Fara ci"

D'iba yayi ya Kai baki"

Sanan itama ta fara ci,tace"wow dama ka iya girki haka gaskiya yayi dadi"

Ci take tana santi murmushi yayi yace"baby ai ni boarding school nayi"

Tana girgiza kai tace"na gan alama gaskiya girkin yayi Dadi"

Tama fishi cin abinci tana koshi tayi gysa ta tashi ta Koma kujera,ya kwashe plate din "

Yana dawowa yaji tana waka tana cewa"Allah bani bani,bani masu sona'tana kaiwa wajen baitin Nan ta d'aga murya tace"dadina da duniyar kowa yace baya sonka kaima ce baka so nai,ba Allah bane ba balle ya kashe ka yanzu"sai a hararanshi take

A ranshi yace"tana hararana bayan ta cinye min abinci ji raini wayau"

Ni'ima ta tashi tana tsifa ta koma ta Jingina da gado ya shiga wanka ya fito

Kallonshi take daga sama zuwa kasa ta tabe baki a ranta tace"useless fellow you think iam a fool da zan bari ka kusance ni duk hanya daka b'ullo Ina dai-dai da Kai"yatmusa fuska tayi ta hura hancin ta leka kirjinshi,tace"ji farfad'a kirjinshi Kamar zai fito,ai wanan b'ukeke in ya afka min mutuwa zanyi jibeshi fa,kazami Yana shiga jikin wanan lesbian din da kowa ya Gama tura hanun da Mata da maza jifa inda take nuna tana son ishaq kenan harda maza take bi"

Shima juyowa yayi ya kalleta suna had'a ido ta harareshi,a ranshi yace"wallahi duk rowarki sai na samo hanya da zan karb'i hakkina at all cost,in na Bari Kikayi wining Zaki Raina ni"

Kara juyawa yayi ya kalleta yace"jibeta kullum kwalele takeyi min dubi kirjinta dukda basu da wani girma suna d'aukar hankali,dubi cinyata very fresh"

Juyawa yayi sai suka Kara had'a ido a tare suka ce what?"harararta yayi yace"bayan kin Gama ci min abinci kina min wulakanci maimakon ki ce in zo mu kwanta

Tace"oh dama badan allah ka dafa ba?"

Tsaki yayi yasa jallabiya ya tafi massalaci sai bΓ yan Isha ya dawo sai tunanin plan yakeyi Amma ba mafita

Yana dawowa ya ganta saman dadduma yace'har kin gama tsifar kenan?"

Tace"eh gobe ma zanje gida tunda Saturday ne ba aiku zanje Ramlat ta min kitso"

Yace"da izinin waye?"

Tace"da izinina Mana da kafar wani zanje"

Yace"shirya in kaiki ki gan ummi gobe ni da kaina Zan kaiki saloon"

Tace"da gaske zaka kaini gida yanzu?"

Yace"eh Mana na tab'a Yi Miki Wasa"

Tsalle tayi ta rungumeshi tace"nagode"tame peck a gefen baki murmushi yayi yace"yi sauri ki shirya Nima bari inje in shirya"

D'akinshi yaje cike da Jin dadi yace"nasan ma da mun dawo zata yarda tunda gashi ta min peck Kuma tana good mood"

Polo da jeans yasa itako tasa jallabiya tayi rolling Yana shigowa yace"baby ki sa hijab zaifi please"

Tace"dare ne fa"

Yace"toh a fasa zuwan,hijabi tasa ya Kama hanunta Suka fito suka shiga mota a mota sai Hira sukeyi kamar Babu komai

Suna kaiwa gida Suka gan Abba kofar gida yayi tagumi yara sun zagaye shi,Yana ganin mota ya mike yana kallon ko waye,Ni'ima ta b'ata rai

Ai baba na hango Ni'ima yaje yace"sannu da zuwa Yar albarka wallahi tun washe garin auren Nike ta jiran kujeran makkah,na d'au tunda me kudi Kika aura duk sati zakiyi ta kawo abinci Ni'ima kanne ki yunwa suke ji,sai gashi allah ya jeho ki,sati biyu kenan ina sa ramlat ta kaini gidan ku Amma masu gadi sun ce baki ciki,turai ya kaiki halan?Amma shi Yana zuwa Kuma Yana d'an yin al'heri Amma da yike kudin yanzu basu da auki in ba Haka ba shekaran jiya ya bani dubu d'ari"

Ni'ima ta kalli Aslim dake murmushi

Aslim yace"ina zuwa Abba bari in Baku na abinci ai yunwa ba dadi"

Ni'ima tayi tsaki ta shige ciki"Abba yace"rokon siriki Kamawa takeyi"

Kudi Aslim ya bashi sanan ya bi bayan Ni'ima

Ramlat na ganin Ni'ima ta rungumeta ta saki ihu dayasa su talatuwa fitowa da fara'a suna Mata sannu da zuwa

Saude tace"Allah ya kawo ki Ni'ima tun safe babu wanda ya ci komai nan gidan"

Ta kalli Aslim hawaye cike da idonta sai yayi murmushi yace"ni Zan shiga d'akin ummi"barin wurin yayi Yana mamakin halin irin nasu jiya nan fa ya raba musu kudi Kuma ya Basu jari yafi a kirga wanan wani irin gidane amma Yana ganin girman ummi domin duk zuwanshi Bata tab'a tambayar shi sisi ba,ko ya Bata,bata amsa saidai ya ajiye Mata"

Tana ganinshi tace'barka da zuwa"

Yayi murmushi ya shiga d'akin saf sai kamshi ke tashi na tularen tsinke"

Ni'ima ce ta shigo ta gan inda suke Hira da ummi abin sai ya Bata mamaki

Rungume ummi tayi tace"nayi kewar ki ummi"

Ummi tace"Nima Haka Bari in Baku tuwo"

Tace"a koshi muke"

Yace"kedai a koshe kike nidai zanci"

Ummi tayi murmushi ta zuba me tuwon wheat da miyar alaihu yaji nama,"

Ci yake yana Santi Ni'ima tace"ummi Nima zanci"

Yace"ummi karki bayar dan gulma tace"bazata ci ba shine dan ta gan zan kara zata ce zata ci salon mu cinye Miki tuwo"

Ummi tayi murmushi tace"karka damu har a kula zan sa maka"

Umma na zuba tuwo sai ga yaran gidan sun Fara buga kofa suna kuka"

Ni'ima ta fito tace"wai miye ba an baku kudin abinci ba"

Cikin kuka suka ce Abba ya gudu dashi wallahi ana bashi ya gudu"

Ni'ima tace"ya miye?"

Suka ce ya gudu tace"muje ku nuna min ta Ina ya bi"

Suna fita ta gan machine dinshi

Ni'ima ta cire hijabi ta d'aura a kugu ta

Maman Nur
9/14/20, 3:29 PM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ8βƒ?9βƒ?-9βƒ?0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ta cire machine din a standard ta fara janshi sai gidansu ishaq

Ta buga me kofar d'anki ya fito Yana ganinta a tsorace yace"Ni'ima lafiya cikin dare Kuma hijabi a kugu dan Allah ki rufa min asiri"

Tace"ga machine din nan ka fitar dashi a unguwanan cikin dare Nan gobe ka sayar ko nawa aka siye ka rike kudin"

Yace"kamar na tsohon ki ko?"

Tace"eh ko baka so?"

Yace"ina so Mana yayi laifi kenan ko?"

Tace"kaidai Yi abinda nace"

Ishaq yace"toh ai babu key"

Ni'ima ta duka ta zaro wani waya guda biyu ta jona tace"ai wanan akwalan machine din ta dade bata da key,watoh mutumin Nan ya amshi kudin sabon machine a wurin mijina yafi so uku Amma be siya ba,ko me yakeyi da kudi oho"

Ishaq yace"ai matan banza yake bi yanzu, Ina karuwanan nan na kasa kwangila?yana da dadiro anan da yike Nan Nike siyo wiwi Ina ganinshi"

Ni'ima tace"no wonder kwana biyu be Kara aure ba"

Ishaq yace"nagode sai munyi waya"

Tace"toh"ta maida hijabinta shiko ya d'ane ya bar wurin

Komawa tayi a kofar gida ta gan Aslim tsaye Yana nimanta

Yana ganinta yace"Ina Kuma kikaje?"

Tace"gidansu zainab shiga muje ka ci abinci ko ka koshi ne"

Yace"ina kuwa ummi tace"in nimo ki dan tasan halinki"

Suna Shiga tace"shiga yanzu Zan biyo ka yace"toh"

D'akin Abba ta shiga ta fara bincike kudi ta gani kasan katifa zai Kai dubu ashirin ta d'auka ta fito ta bawa Ramlat tace"kuyi girki zai kaiku sati biyu in kukayi manaji"

Tace"toh mun gode"

Tana komawa ummi tace"Ni'ima in kin d'auke me abu ki maida bana son fitina"

Tana cin tuwo tace"Babu abinda na d'aukar me"

BΓ yan sun cinye tuwo suka ji ihun Abba a kofar gida ,ummi tace"wanan mutumin Allah ya shirye ka"

Aslim yayi murmushi,shigowa Abba yayi ya kwanta a tsakar gida yana ihu

Ummi ta fita ta gan birgima yakeyi a kasa talatu tace"lafiya?"

Yace"an d'auke machine din"

Aslim dake tsaye nisa dasu ya rungume hannu yana mamakin Abba,Ni'ima ko fitowa Batayi ba yayi ta kuka Yana cewa ga tsantalelen mota Basu d'auke ba sai machine din bawan Allah,Yana hango Aslim yace"dan Allah ka taimaka ko zan rage radadin da nikeji ka bani Koda kudin ne"

Kafin Aslim yayi magana Ni'ima ta fito tace"wallahi sisi bazai baka ba,shi ba d'an iska bane da zaiyi ta baka kudi kana kaiwa dadiron ka"

Talatu tace"Ashe dai abinda ake Fadi gaskiya ne dadiro gareka"

Saude tace"ba na sha fad'a Miki ba Baki yarda ba"

Aslim ya shige ciki Ni'ima ta bishi,ummi tace"toh Allah ya kyauta

Su saude suka rufeshi da fad'a

Suna shiga ummi ta kalli Ni'ima da taki yarda ta kalleta tace"meyasa kika d'auke me machine "

Ni'ima ta mike tana sa hijab tace"ni ban d'auke me machine ba'

Ummi tace"karya kike"shidai Aslim kallonsu yake"

Ni'ima tace"muje dare yayi"

Ummi tace"watoh ko da kikayi aure Baki daina halin naki ba na rashin ji"

Aslim yace"nidai Bata tab'a d'auke min Abu ba"

Ummi tace"abbanta kadai takeyiwa haka in ya b'ata mata rai ta d'auke me abu ta sayar ta bawa yaranshi kudin abinci"

Ni'ima ta fita ta barsu Aslim ya sallami ummi ya bi bayanta Abba nata kallo ko zai bashi kudi yaji shiru

Yana shiga mota ya ganta zaune ta Jingina ta lumshe Ido

Kallonta yayi saita fashe da kuka yace"subhannallah meya faru?"batayi magana ba sai ma cigaba da kukanta da tayi ya jawo ta da hannu d'aya ya rungume yace"I understand karki damu please"

Kullum kenan mutumin Nan yayi ta badani"

Yace"koya yake babanki ne,ki godewa Allah kina ganinshi nifa bansan mahaifina ba sai a hoto tun Ina yaro mahaifina ya rasu"

Ni'ima tace"ai gomma Kai mutuwa yayi Amma ai ba dadi mahaifinka ya zama abin kwantace da mutuwa yayi Dana hut......."

Bige Mata baki yayi yace"ko ya yake don't wish him death"

Shiru tayi tana kallon hanya bΓ yan sunyi nisa yace"Zaki ci kaza in siya Miki"

Tace"ah'ah a koshe Nike"

Yace"ok"

Suna kaiwa gida suka hango mummy zaune a balcony dinta

Tana ganin ya paka ta tashi tana jiran fitowar su domin tunda Fatima ta fad'a mata sun fita tare da ni'ima hankalinta ya tashi

Suna fitowa Ni'ima ta hangonta ta d'auke Kai"

Kama hanunshi tayi Suka Fara jerawa shi be ma Lura da mummy ba

Mummy na ganin zasu shige tace"Mohammed zo nan"

Juyawa yayi yace"toh mummy"

Sake hanun Ni'ima yayi ya juya zaije wajen mummy saidai be Kai wajen mummy ba yaji Ni'ima tace"wayyo kafana baby ka taimaka"

Juyawa yayi ya gan Ni'ima ta lankwasa kafa tace"wallahi baby gurd'ewa nayi ka taimakeni please"

Komawa yayi da sauri,mummy ta zaro ido"

Yace"meya same ki"

Ni'ima tace"ka taimaka ka d'aukeni bazan iya tafiya ba wayyo ummina na mutu wayyo ka taimakeni mijina"

Ai rudewa Aslim yayi ya d'auketa ya ma mance da wata mummy ya d'auki ni'ima jiki na rawa"

Mummy na kallonsu ta cika fam kamar ta fashe

D'aga Kai tayi Suka had'a Ido da ni'ima,Ni'ima ta kashe mata Ido"

Mummy ta shige ciki,cike da haushi da b'acin rai"

Suna shiga ya ajiyeta a gado yace"sorry dai-dai Ina ne in ja Miki"

Tace"Nan ne"

Ja ya farayi tana Jin chakulkuli tana dariya"

Kallonta yayi yace"miye Haka"

Tace"chakulkuli Nike ji"

Murmushi yayi yace"tell me something,da gaske ke Kika d'auke machine din"

Dariyar fuskarta ne ya d'auke ta juya me baya"

Dawowa yayi gadon ya fara mata chakulkuli tana b'ab'aka dariya har ya had'e bakinsu ya fara romancing dinta

Sanda ta Bari yayi nisa ta tureshi da karfi ta sauka gadon da ta shige toilet

Naushi iska yayi yace"me take nufi yauma bazata yarda ba kenan duk irin shiryawa da mukayi

Ta dade kafin ta fito ta zauna a saman mirror tana dariya tace"ya dai malam day3 ya kusan expire "

Tsaki yayi yace"wallahi na kusan yi Miki Allah yasa"

Tace"Allah ko"

Shimfid'a, tayi bΓ yan tasa kayan bacci da wando uku ta Kwanta a kasa,shima kasan ya dawo yace"wallahi Baki Isa ba"

Murmushi tayi ta juya me baya tace"asuba ta gari"

Cikin su biyu Babu Wanda

Please Login or Register in order to submit comment