Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin kunya

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Aslim ke nunawa ni'ima so baya son b'acin ranta duk dukiyarshi ya dawo hanunshi,inda Ni'ima ta kira duk matar da tasan mahaifinta ya tab'a aure kuma sun bar ya'ya a gidan suka zo ta Basu kyauta sanan tace"su yafe me ta rokesu da ko wacce ta d'auki yaranta

Suma su ladidi ta basu babba kyauta sanan ta koma gida

Bàyan wata d'aya yau gidan cike yake domin har gida umma taje ta d'auki zee aka had'a su da Ramlat ana musu gyran jiki harda ni'ima aiko Aslim ya yaba kudi sosai ya kashe wurin yiwa zee kayan d'anki komai iri d'aya da Ramlat sanan ya bawa ishaq kyautan gida da mota sanan ya d'auke shi a matsayin manager domin ya Yarda dashi"

Ni'ima tayi me nasiha akan ya daina shaye-shaye kuma ya d'auka yace"tayi me addu'a domin Saida addu'a"

Ba karamin biki akayi ba an kashe kudi da programs sanan aka d'aura aure aka Kai zee gidan Fahad itakuma Ramlat sabon gidan da Aslim ya bawa ishaq saidai muyi musu fatar alkhari

Bayan wasu shekaru sosai Ni'ima ta Zama babban mace yaranta hud'u yanzu baka tab'a sanin ba umma ta haifeta ba lokaci-lokaci tana bin gidan Yan uwanta tana dubasu Ramlat ta canja yanzu tana da shago Kaya take sayarwa yaranta biyu zee ce me Yara uku sun kulla zumunci Mai karfi

Soyyaya tsakanin Aslim da ni'ima kullum karuwa yake

Zaune Suka da yara tanayiwa Abba watoh Kabir home work sai ga Aslim ya shigo dukansu Suka tashi gabad'aya Suka rungumeshi ummi ce taki tashi

Yace"waye ya tab'a min ummi?"

Ni'ima ta tab'e baki ta amshi jaka ta haura

Abba yace"abinci aka bamu shine Wai ita Saida akara mata nama mummy tace bazata bata ba shine taki cin abinci mummy ta zaneta tasa ta Dole sai ta ci shine take fushi

Zuwa yayi ya d'auketa ta fashe da kuka lallashinta yayi ya Basu sweet yace"kuje wurin Gramma"

Da gudu suka ruga shikuma yayi d'aki yana shiga ni'ima na fitowa daga toilet ta had'a me ruwa wanka

Fuska d'aure yace"meyasa Zaki duke ummi?"

Tace"laifi tayi"

A fusace yace"Naman ne babu da baza a Kara mata ba?*

Itama fuska d'aure tace"bazan bata ba,domin wanan ba so bane kake nuna mata"

Ganin ta d'aure fuska ya jawota yace"haba baby ai ba fad'a mukeyi ba yau bazaki tayani wanka bane?"

Cikin shagwab'a tace"toh ba Kai bane kullum kayi tayiwa mutum fad'a akan ummi"

Had'a bakinsu yayi tuni komai ya canja bayan ya samu natsuwa yace"baby yau aka kirani Wai Fatima ta rasu a prison"

Ni'ima tace"Allah sarki Allah ya jikanta "

Yace"nidai nace su nimi Yan uwanta bamu da alaka,kinsan dama walida ta shiga duniya"

Ni'ima tace"Allah ya kyauta tashi muyi wanka dan yanzu autan mama zai dawo Yana Nima na"

Yace"ni nace Miki Fahad ne auta?"

Tace"haba dai ai sun ishemu"

Yace"toh tunanin ki ya fad'a Miki karya domin sai munyi dozen ke fa kadai ce gun ummi Nima Haka"

Ni'ima tayi kissing dinshi tace"as you wish my husband "

*The end*
____________
Toh jama'a nan na kawo karshen littafin Ni'imatullah inda nayi kuskure Allah ya yafe min

Godiya ta musamman ga ni'imatullah paid group da Kuma VIPs

Godiya gare ku masoyana Allah ya bar kauna nagode da kaunar ku

Wa'yanda suka karanta free kuma Ina Mai shawarta ku da kuyi settling debt dinku domin kayane🤷‍♀?


maman Nur na muku fatan al'khari

Maman Nur
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment