Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu hakuri"

Ni'ima ta ruga ciki da gudu tace"wallahi saidai ki kasheni Amma bazan Basu hakuri ba"

Ummi na ganin ta shige ta kwashi ledar da ta dawo dashi tace"Dan girman Allah kuyi hakuri yariya ce"

Ladidi tace"munafuka ai duk ke kike koya Mata"

Tsaki saude tayi tace"yariya da nono a kirji wacce tasan hanyar niman maza za a Kira da yariya,gaskiya kiyiwa kanki fad'a ki daina tura yariyar nan karuwanci"

Ummi Bata kulasu ba ta shige d'akinta ta fara yiwa Ni'ima fad'a

Ni'ima dai amsar ledar tayi ta fito da karamin cylinder 3kg ta aza ruwan tuwo

______________

Aslim na barin shagon gida yayi driver na parking ya fito,be zarce ko Ina ba sai part din mummy Dake d'an nisa da nashi

Yana zuwa ya tarar ba kowa a falo sai tv dake aiki Zama yayi a kujera Yana cewa mum iam home"

Wata kyakyawar matace ta sauko cikin shiga ta alfarma Fara ce sol tana da jiki Amma Bata da tsayi da fara'a ta sauko

Tashi yayi ya Karasa yayi mata side hug yayi pecking dinta yace"mum a gajiye na dawo wallahi"

Murmushi tayi tace"Sannu da kokari my son ai Ina alfari da kai,so ya aikin kana dai ganewa ko?"

Yace"yes mum"

Zama yayi ta d'auko me drinks can sai ga likita ya sauko ta kalleshi tace"ka dai Yi mata allura ko?"

Yace"eh"

Kawai ji sukayi ta fito da gudu tana kokarin zuwa wurin Aslim,tsayawa yayi Yana kallon hajiya mariya da ta rungumeshi tana kokarin yin maganan Amma ta kasa ga jikinta rawa yakeyi

Kallon mum yayi cikin sanyin jiki yace"mum mu fitar da Anty waje Mana she is suffering"

Mum ta kalli dr shima ita yake kallo tayi me signal da Ido sai kawai ya fito da allura a jakarshi ya fara had'awa

Mum ta Karasa inda suke hajiya mariya na ganin Haka ta b'oye bΓ yan Aslim da tausayi ya Gama cika shi

Dr ko hanunta ya Kama yayi mata allura

Aslim yace"mum please mu fitar da ita waje tunda na taso fa na ganta a Haka ana fama"

Mum tace"ai Babu kasar da ba zaga da ita ba Amma Allah besa an dace ba Saidai mu cigaba da Yi mata addu'a kawai"

Cikin damuwa ya zauna kawai sai ya ji ta fad'o jikinshi

Dr ya fara kokarin d'aukarta sai yace"Dr tafi kawai zan shigar da ita tunda ta samu bacci"

Dr yace"ok hajiya sai gobe kenan"

Mummy tace"muje in raka ka"

Suna fitowa mummy tace"gobe ka zo da allurar da zai Kara daburce da kwakwalwar gabad'aya bana son ya fara zargin wani abu,domin za a iya samun matsala in ya gano gaskiya"

Dr yace"karki damu nasa a nimo min allurar Kuma an tabbatar min gobe za a kawu min"

Tace"ok sai na gan ka"

Koda ta koma ta gan har ya kaita d'aki Ya sauko tace"son je ka huta"

Cikin sanyi jiki yace"toh"sanan ya fita ta bishi da kallo

Zaune Fatima take a falo ita da kawarta

Fatima tace"ance Miki in badan abinda Zan samu ba Zan zauna a Nan ne ai da mun cima burin mu Zan bar kasar"

Salma tace"toh me zai hana kiyi beating hajiya a game din da ta had'a

Fatima tace"ban fahimta ba"

Salma zatayi magana sai ga Aslim ya shigo kallo d'aya Fatima tayi me ta d'auke kai,murmushi yayi yace"


Maman Nur
9/10/20, 6:31 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

My paid books
Nida mijina 200
Kaunace 200
Mai mata biyu 200
Nida Yaya hydar 200
So makaho ne 200
Habib Mr neat 200
Mu kawaye ne 300
Zo kiji 300
Yarima annur 300
And now NI'IMATULAH 300
Gaskiya in baki karanta wa'yan nan littatfan ba an sha dake ga me bukata sai a min magana ta wanan layin 09090112846

πŸ…Ώ2️⃣5βƒ?-2️⃣6βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"au yau su Salma ne a gidan namu?"

Tayi murmushi tace"eh ya aiki ai tun safe na zo aka ce ka tafi aiki"

Yace"eh wallahi"kallon Fatima yayi da ta hade rai yace"haba sweetheart bazakiyi welcoming Dina ba me nayi Miki?"

Tsaki tayi ta juya me baya,Salma ta mike tace"haba ke ko kiyi me sannu da zuwa Mana"

Kallon Salma tayi tace"muje in raka ki"daga haka Suka fita ya bisu da kallo

Suna fitowa Salma tace"ke miye haka kike basar dashi?"

Fatima ta yatmusa fuska tace"nifa haushi yake bani ke kanki kin San ni bana yin maza,Kuma in ban Fara hade rai tun yanzu ba ba in na sakar me fuska sai ya takura min,gashi da shegen naci kamar cingum baya gajiya,ni fa harna Fara gajiya domin nidai saboda kudin na aureshi amma ke kanki kin San ko u's da Mata Nike harkata na fi Jin dadin su,Amma an wani takurani a gida da sunan aure"

Salma tace"ai shine Nike fad'a Miki kiyi beating hajiya a game dinta"

Fatima tace"how?"

Tace"why not tunda ke likita yace bazaki iya haihuwa ba,kuma haihuwar ne ake jira a kau dashi ku kwashi dukiyar,me zai hana ki b'ollo ta bayan gida domin in baki riga hajiya ba zata Riga ki we all know how curning and selfish that woman is,she can do anything Kuma zata iya Kau da kowa akan dukiyar Nan ciki harda ke da kike Yar sister ta balle ita da mum dinki step sisters ne,yanzu da baki haihu ba zata iya sawa Aslim din ya Kara aure Kuma kin San Yana jin maganarta Kuma Ina fad'a Miki da Haka ya faru Zaki tashi a tutar babu domin zata iya sawa ya sake ki ko Kuma ma ta kashe ki tunda kin san sirrinta"

Fatima dake gyada Kai alamun kin kawo point tace"Kuma hakane nama ji ta fara zancen"

Salma tace"atoh,yanzu dai me zai hana tunda yana sonki kuma kina lokacinki me zai hana ki ce me kin amince yayi secret wedding ya auro Wanda zata haifa muku yara in aka kawu ta ta samu ciki sai kema ki Fara laulayin karya in cikin ya girma sai ki Fara saka cikin karya ita kuma yariyar da zai auro in ta haihu sai ku kasheta harda shi dama duniya zata d'au yar'ki ne ko d'anki kin gan kafin hajiya ta gane sai ki tattara komai nashi ki bar kasar Amma tun kan ta haihu Zaki Fara Shirin barin kasar da lauyer ya zo ya saki dukiyar kawai sai ki Kai yaron gidan marayu ki tafi inda kike so"

Dariya Fatima tayi tace"Kai kanki naja Amma saidai wanan plan din da hajiyar za ayi shi kin San tsinanniyar wayau ne da ita zata gane da wuri zan fad'a mata komai amma da haihuwar ya zo kawai Zan canja wasan"

Salma tace"Kuma Haka fa yayi duk inda akayi ki min waya"

Tace"Yanzu ko zani in fad'a Mata"

Jan mota Salma tayi ta bar gidan itako Fatima tayi b'angaren hajiya a falo ta sameta tana waya

Zama tayi ta jira ta gama waya,mummy ta kalleta tace"Lafiya dai ko?'

Fatima ta harareta tace"miye Kuma na b'ata rai Ali ne fa ya ga Ali "

Hajiya ta mike ta jawo Fatima ta murd'a Mata hanun baya tace"na fara ganin alamun kin fara growing wings har kike tunanin zaki sa Aslim ya juya min baya"

Fatima tayi murmushi tace"kila saboda abinda Nike bashi ke Baki bashi shiyasa ya fara fifitani a kanki,yanzu ki sakeni na kawo plan din da za ayi ta ta Kare kowa ya huta"ta Kare magana da kwace kanta

Mummy ta koma ta zauna,Nan ta zayyana mata komai amma karki nuna me kin San da plan din"

Mummy ta kalleta tace"ke kanki kin San ba a playing dina in wanan hanya ne da kike tunanin zakiyi beating Dina a game Dina toh ki canja shawara domin Zan manta ke Yar kanwata ce Wallahi akan dukiyar nan zan iya kawar da ko waye na d'au shekaru Ina wanan Shirin "

Fatima tayi murmushi tace"hmmm ke bansan meyasa baki da yarda ba auren Nan fa shine zai kawo karshen komai da ta haihu kin gan sai muyi amfani da d'an mu mallaki dukiyar a bawa kowa kasonshi ya kara gaba ita yariyar ai tana Gama haihuwa sai mu kasheta kowa ya huta kin gan ai duniya bazata San waye mahaifiyar d'an ba a cikin sirri za ayi auren'"

(Niko nace lallai wanan auren shi zai kawo karshen komai)

Mummy tayi shiru tana nazarinta tace"ok convince him"

Fatima ta mike tace"ok inshaallah zai amince I will shade crocodile tears"

Komawa tayi ta tarar dashi zaune a dining Yana Shan tea,karasawa tayi ta rungumeshi ta baya tana shagwab'a tana kukan karya

Cikin damuwa ya juya yace"dear meya same ki"

Cikin kuka tace

Maman nur
9/10/20, 6:31 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

Free page

πŸ…Ώ2️⃣7βƒ?-2️⃣8βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim

Cikin kuka ta Kara rungumeshi tace"kayi hakuri kullum Ina maka laifi wallahi haushin kaina Nike ji in na tuna cewa"bazan iya haihuwa ba,Aslim bazan haihu maka ba wallahi hakan na kasheni"

Yace"but na fad'a Miki ko a Yaya kike Zan rayu dake ina sonki matata"

Juya me baya tayi tace"that the problem,wallahi my conscience is Killing me in na tuna saboda ni bazaka gan jinin ka a duniya ba kullum da abin Nike kwana dashi Nike tashi wallahi mijina Ina son koni bazan haihu ba Kai ka gan jinin ka zanfi samun kwanciyar hankali tunda Dr yace"you are ok"

Yace"Fatima what are you saying kema kin san bazan iya Miki kishiya ba Allah ya jarrabce ni da sonki"

Tace"mijina Ina son ka,me zai hana ka Kara aure wacce zata haihu maka Koda d'aya ne ka gan Nima Zan huta da takaicin rashin haihuwa"

Wani kallon rashin fahimta yayi mata yace"ban fahimce ki ba,saboda Baki Sona kike son in Miki kishiya Fatima ko kishina bakiyi,ni bance Zan Kara aure ba sai kece Zaki ce in Kara aure hanya Fatima kina Sona kuwa?"

Kuka ta fashe dashi tace"you think is easy for me in ce maka ka Kara aure?duk duniya Nan Babu macen da zata so mijin ta ya Kara aure balle har tace yayi,ka taimakeni Kuma ba Ina nufin ka zauna da ita bane na din-din data haihu sai ka sallameta ta bar Mana yaron ko yariya Kuma ai zaka nima Yar talakawa ne ka aura Wanda ko daga baya ta zo claiming abinda ta Haifa zamu iya fighting dinta"

Yace"no gaskiya bazan iya ba ai wanan ya zama wickedness ne ita wacce za a auron Bata da gata ne?"

Kuka Fatima ta fashe dashi ta mike ta shige d'anki ya bita da kallo,d'auka biredi yayi da niyyar cigaba da Shan tea dinshi sai ya tsinci kanshi da rashin Jin dadin tashi yayi ya bita tana Jin ya bude kofa ta Kara karfin kukan nata,karasawa yayi gado ya rungumeta ya fara lallashinta cikin shashasheka tace"bafa Zama zakuyi na dindin ba,da ta haihu zaka sallameta,gaya me tayi inda komai zai kasance yace'kina ganin haka bazai Zama matsala nan gaba ba?"

Shafa fuskarshi tayi tace"kaidai ka Amince Kuma bazamu fad'a mata amfani da ita zamuyi ba infact karka fad'a mata kana da Mata sai anyi auren"

Yace"toh Ina zamu samu yariyar?"

Tace"ai kai zaka samu me kwad'ayi da son abin duniya ka kashe mata kudi da ita da iyayenta "

Zaiyi magana ta hade bakinsu dama abinda yake so kenan domin yayi Kwana biyu,dukda ba so take ba haka ta hakura ta bashi hadin kai hakan ya bala'in tafiya dashi bΓ yan komai ya lafa ya rungumeta yace"I love you my wiffy"

Tana shafa suman kirjinshi tace"Mee too please ka amince"

Murmushi yayi yace"in Zaki dinga min irin Haka zan amince,Fatima Ina sonki please ki daina hanani kanki please"

Tace"Nima in ka Amince Zan dinga Yi maka inda kake so"

Yayi murmushi yace"toh tashi muje muyi wanka sai muyi sallah magrib ta gabato"

Suna tashi ya Kuma jawota ta tureshi tace"nifa yunwa Nike ji"

Yace"alright Bari in nayi sallah sai in fita in samo Mana abinci"

A tare sukayi wanka suna fitowa yasa jallabiya ya feshe jikinshi da tularai yace"na tafi massalaci sai bΓ yan Isha Zan dawo"

Tace"ok'yana fita tayi tsaki tace"nifa bani da fellings wa namiji"

_____________
A gurguje ni'ima ta tuka tuwon wheat ta kwashe Sanan ta kashe gas taje tayi sallah magib Bata tashi ba sanda tayi Isha

Ummi tace"Amma sai kin siyo maganin zakiyi Miya ko?"

Tace"bana son dare yayi min domin sai na je mudus zan samu da sauki"

Ummi tace"toh kije kawai zan lallab'a inyi miyar kafin ki dawo*

Tace"in bazaki iya ba ki Bari in na dawo sai in yi kin ji umminta"

Ummi tayi murmushi ta shafa kumatun ta tace"Yar ummi ki daina kula Yan gidan Nan kin ji"

Tace"toh"

Ummi tace"ki dawo da wuri bana son ki tsaya fad'a da kowa"

Tace"toh"

Da sauri ta fita da kafa ta taka da yike Basu da nisa domin a Baki general hospital yake Minna

Tana zuwa ta Basu paper maganin Suka Bata juyowa tayi tana tafiya harta zo junction din gidansu zata tsallake titi sai ga wani mota ya zo a guje sake ledar maganin tayi har ta runtse ido sai taji ya ja birki

A ranta tace"wallahi baka Isa ba tunda har ka kusan bigeni ka shiga uku,fad'awa tayi saman mota ta kwanta

Aslim ya tsaya Yana kallon ikon Allah shidai yasan be tab'a ta ba fitowa yayi kafin a taro Yana zuwa ya

Maman nur
9/10/20, 6:31 AM - Ummi Tandama: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*NI'IMATULAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

Wanan littafin na kudi ne 300 me bukatar karantasa har karshen a tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed 0092544083
Access bank ko Kuma Kati mtn vtu ta wanan layin 08148088368 me niman Karin bayani sai a min magana ta wanan layin 09090112846 sai na ji ku

πŸ…Ώ2️⃣9βƒ?

Bismillahir Rahmanir Rahim

Fita yayi ya leka fuskarta Amma be samu ganin ko waye ba

Jijjigata ya farayi yace"malama meya sameki ina fatan dai baki ji ciwo bako?"

Banza tayi me,ganin dai Bata da niyyar magana yasa shi d'aukarta ya Shigar mota sanan ya ja motar gefe

D'aga fuskarta yayi bΓ yan ya gama parking Yana ganin fuskarta yace"not again"

Bude ido d'aya tayi aiko sai ya ganta turo baki tayi ta wayance tace"a duniya nike ko a lahira"

A fusace yace"meyasa kike damuna ne?"

Hararanshi tayi tace"oh ni da ka buge da mota banyi magana ba sai Kai ne me bakin magana sai ka biyani asarar da kasa nayi"

Yace"fita ko in yi Miki dukar tsiya"

Tace"al-quranin ubangiji bilahillazi la'ilaha ilahuwa na rantse da Allah in ka gan na fita a motar nan ka dire min dubu goma da a ce na fadi na mutu fa iyayena ne da asara wallahi bazan yarda ba,ni Yar iskace zan Bari ka wuce free wallahi baka isa ba"ta Kare magana da gyra Zama

Wani kallo yayi mata a ranshi yace"yariyar nan akwai son kudi"tsaki yayi a fili yace"ni kuma bazan Baki ko sisi ba,fita ki bar min mota"

Tace"ok ai zamu gani"

Ganin dai da gaske take yasa ya Ciro kudi a inda take ajiyewa ya wasa mata murmushi tayi ta fara sincewa harta gama ta kalleshi da murmushi tace"tun d'azu da haka kayi da an wuce wurin,ledar maganin daya shigo dashi ta d'auka ta kalleshi tace"Ina wuni,ya mutane gidan su umma fa?"

Yace"fita please sauri nikeyi"har zata fita sai ta gan take away guda biyu d'auka d'aya tayi tace"nagode Allah amfana inda kake d'awainiya dani kaima Allah ya biya ka"

Bata jira me zaice ba ta fita ta kama hanyar gida tana sauri

Tana kaiwa ta tarar da abbanta a kofar d'ankinshi ummi harta kad'a busashan kubewa"

Hade rai tayi ba tare data kalle inda yake ta shige ciki,ummi tace"kin samu maganin"

Tace"eh na samu"

Abba ya kalleta yace"ke baki ganni bane?"

Tace"na ganka me zan maka?'

Ummi ta daka mata tsawa tace"ke miye Haka"

Ni'ima bata kulata ta bude kula abinci ta cirewa ummi leda d'aya tasa mata Miya

Ta kwashe ta Kai d'anki ta zauna ta bude take away dinta fried rice ne da chicken ta ajiye kudi gefen ta ta fara ci,ba tare da ta kalli inda yake ba tace"in ma mutum abinci yake jira gwamma ya tashi kafin dare yayi me domin tuwon mu dai-dai mu Muka tuka'

Kallon abincinta Abba yayi ya had'iye miyau ni'ima ta cire kaza saman abincinta ta sawa ummi duk Yana kallo'

Kallon ummi yayi yace"ladidi baki bani abinci ba kuma yau girkin ki"

Wani dariya ni'ima ta kyakyale dashi Amma batayi magana ba

Ummi ko yi tayi kamar bata jishi ba domin duk ranan da yunwa ya kwaso shi sai ya zo ya zauna yace"girkinta ne alhalin tunda ciwon ta ya tashi ya daina kulata Ni'ima ce kawai me fama da ita

Yace"dake Nike ladidi"

A fusace tace"Wanda ka kawo zan baka ko wanda ya'ta ta samo?ka gan mal am na dawo daga wanan rakiya Dan bazai yiwu ya'ta ta fita kullum dan rufan asirin mu kuma in kwashe inyi ta baka ba bazai yiwu ba"

Da mamaki ya kalleta domin zamanshi da ita Bata tab'a yime magana haka' ba lallai tura ta Kai bango,ita kanta Ni'ima tayi mamaki ummi nata yau

Muryar tausayi yayi yace"ladidi Dan Allah kiyi hakuri yunwa Nike ji"

Ummi tace"ka cire kudi cikin wanda ka tara na sadakin da zaka Kai ranan juma'a ka ci abincin dashi "

Yace"ai na aika dashi ko?"

Ni'ima ta d'auki kudinta ta kirga dubu bakwai tace"ummi gashi wanan gobe in kin samu lafiya ki shiga ki yanko Mana kaza ki siyi shinkafa irin Wanda kike ci da tumatu gobe shinkafa da Miya zamu ci ki siyo holandia babban gora da wanan dubu uku nan ki siya atamfar da aka fito dashi na auren zara'u makociyar mu ki bada d'inki"

Ummi tace"kefa bazaki d'inka ba?"

Tace"karki damu in ke kin samu ni ban damu ba bana son ranan tayi ke ki fita daban kin San ina kishin ki,ni Kona d'inka bana Nan ina gun aiki"

Abba yace"nifa Ni'ima"

Ni'ima tace"ni ban tab'a saninka kamar inda baka sanni ba,malam zan baka mamaki nan gaba mu zuba nida Kai tunda har kayi musu na kace Kai ba mahaifina bane Kuma kaki yanka min ragon suna,hmmm malam zan baka mamaki kad'an kenan ka gani"

Yace"Ni'ima ai abinda ya wuce ya Riga ya wuce a baya Kuma karya ake miki,nidai a manta baya kawai,yanzu dai bani dubu a wurin"

Ni'ima zatayi magana ummi tace"ya Isa haka"

Talatu ce ta fito tana marsifa tana zuwa ta shake shi tace"malam in baka so in tara maka jama'a ka fito ka bada kudin abinci domin ni da yarana yunwa muke ji"

Saude ta fita tace"ai yau in be bamu kudin abinci dukan siya zamuyi me"
A fusace yace"ku sakeni ko ku kwana gidanku yau"

Tuni talatuwa ta sakeshi tace"malam Babu abinda zamu ce ma sai Allah ya isa"

Saude tace"ai wallahi sai Allah ya isar mana kuma daga yau sauran ya'yan ka wanda uwayensu basa nan sai ka San inda zakayi dasu tunda manya suna fita wajen samari"

Saude na barin wajen ta aika taliya guda biyu ta dafa ta ci ita da yaranta,itako talatu ta dafa shinkafa Yar Fara da Mai kowa ya ci da yaranshi sauran yaran da ba iyayensu a gidan sukayi tagumi kanana na kuka manya dai sunyi shiru

Babba cikinsu ramlat ta zo tace ummi Dan girman Allah ki tausaya Mana tun safe bamu ci komai ba"

Ummi ta saci kallon Ni'ima, Ni'ima tace"a Basu ragowar tuwon,d'aki ta shiga ta d'auko d'ari biyar ta mikawa Ramla tace"ku Kara dashi

Sosai Ramla tayi godiya Ni'ima tace"ya kamata kema ki fita ki nimi aiki Koda shara ne in ba Haka ba yunwa zata kashe ku"

Ramla tace"toh anty in an samu Ina so"

Ni'ima tace"Zan duba Miki Amma kema kiyi ta tambaya"

Tace"toh"

Suna wucewa ummi tace"Ni'ima Allah yayi Miki albarka ya rufa Miki asiri nagode"

Tace"Amin"

Ummi tace"Amma ki rage wanan tsanan da kikewa mahaifin ki ki Fara kiranshi da sunan abba bawai kiyi ta kiranshi malam ba ya kamata ki gane shi mahaifin ki ne"

Ni'ima ta mike tace"duk Randa ya gane shi mahaifina ne Kuma ya d'aukeni kamar yar'shi Nima Zan Fara bashi muhimmanci

Binta d'anki ummi tayi tana mata nasiha,itadai Ni'ima ta juya mata baya tana kuka,haba ita Bata jin zata iya yafe Masa domin ta sha wuya tun tana yariya har girmanta da a ce shi responsible father ne da yau ba sai tayi shigar maza ba

___________

Aslim na kaiwa gida ya tarar da Fatima zaune tayi tagumi

Rungumeta yayi yace"ai na ce Miki karki damu Kuma ni kaina nayi tunani na gano soyyaya da kike min ne yasa Baki son in mutu ba ya'ya you are Not selfie at all shiyasa nike sonki dan da wata ne sai dai ta hanani aure"


Tace"Ina son ka mijina please ka Fara niman yariya ko cikin staff dinka ne nasan baza'a rasa Yar talakawa ba masu kwad'ayin kudi"

Shiru yayi kamar me tunani ni'ima ce ta fad'o me a Rai yace"it will be easy to use her domin tana da kwad'ayi ga son kudin bala'i sai dai bazan so in had'a zuri'a da ita ba"

Fatima da ta ji maganar shi Wanda shi a zatonshi ba a bayyane yayi ba

Tace"baby wacece ita?_

Yace"share kawai"

Tace"fad'a min mijina"labarin komai ya bata tace" wow baby ai itace zamu iya amfani da ita Kuma ai mu zamu bawa d'an tarbiya kawai kasan inda zakayi ka jawo ra'ayinta in zaka tura magabatanka sai mu biya wasu su je niman aurenta bazaka fad'awa kowa ba if possible a d'aura da asuba karka Bari wani ya san da maganar auren sai ku biyu da iyayenta,ko Fahad karka fad'a me ka gan Koda ka saketa in sukayi musu sai mu ce su kawo shaidu"

Yace"ok no prob Allah yasa ta amimce"

Tace"karka yarda tasan manufar mu ka nuna Mata soyyaya"

Yace"hanya kina kishina kuwa?"

Tayi murmushi tace"sosai ma kuwa"

Ajiye abinci yayi yace"ki ci nagode da kokarin ki dan ganin na gan jinina a duniya"

Tace"jinin mu dai "

Yace"eh hakane kam"

Murmushi yayi a ranshi yace"perfect ta wanan hanya Nima Zan Rama iskanci da tayi min"

Jiranta yayi ta gama cin abinci duk inda yaso kusantar ta kin yarda tayi Wai bacci take ji badan yaso ba ya jika tea ya Sha ya kwanta,domin Fatima bata girki

Washe gari da safe ya shirya ya fito falo dama ya rigada ya Saba da rashin breakfast shiyasa be wahala da kanshi ba ya fita aiki

Yana kaiwa kowa ya mike ya gaidashi ya amsa ya shiga office

Ishaq dai na desk dinshi yayi serious Yana aiki

Sadiya ce ta kawu me coffee ta ajiye me godiya yayi mata

Tace"ishaq"

Yace"Wai miye?"

Tace"haba ishaq ka bani dama Mana ka gan nawa kala soyyaya"

Ishaq yace"aiki Nike please don't distract me"

Ta ajiye wani kula tace"ok ga abinci na kawo maka daga gida"

Yace"nagode je kiyi aikin ki zamuyi magana anjima"

Wucewa sadiya tayi badan taso ba tana wucewa ya sauke ajiyar zuciya

Coffee ya d'auka ya fara sha ya bude abincin ya gan lafiyayar jellouf ne da nama tabe baki yayi ya rufe abincin Yana Gama shan coffee ya cigaba da aikin shi"telephone din ne yayi Kara ya d'auka ok sir, s kawai yace"ya mike ya shiga office din a lokacin da suka had'a ido ji yayi Kamar ya fashe da dariya tunawa da abinda ya faru jiya Amma sai ya basar ya karasa yace"sir gani"

Aslim yace"wani time ne meeting din?"

Yace"10:30am sir"

Yace"ka gama aikin ka"

Yace"sir iam still working on that sir"

Yace"ok gobe Ina son ka gama zuwa gobe so that mu duba mu gani kafin mu had'a plan din"

Yace"ok"har zai fita,aslim yace"kasa a kawo min coffee"

Ishaq yace"ok sir"

Yana fita yaje inda zai gan sadiya amma Bata nan duk Babu kowa a wurin,kawai sai ya d'auki cup me kyau ya had'a me coffee ya aza a tray ya kawo me ya ajiye a table"

Har zai wuce ya ji yace"please use my laptop to reply the email din public procurement board

Ishaq yace"nidai na gan jaraba kamar ni kadai ne a office din"kasa-kasa yayi magana inda bazai ji ba Yana zuwa ya fara danne-danne

Ji yayi aslim yace"who made this yayi daban dana jiya"

Ishaq yace"sorry sir dana je ne ban gan kowa ba a kicin din shiyasa na had'a ma da kaina Amma in baka so Bari inje in nimo sadiya ta had'a ma"

Aslim yace"no infact I love it,gaskiya ka iya coffee waya kowa maka domin jiya banji dadin shi ba"

Ishaq yace"thank you sir kawai ginger ne nasa kila shiyasa kaji dadin shi"

Aslim yace"as from today you will be the one

Please Login or Register in order to submit comment