Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin tausayinta ya kamasu. Suka shiga jera mata sannu cike da damuwa. Bata iya ta amsa musu ba, dan gaba ɗaya a yanda Hibbahn take ta fita hayyacinta ba lallaine ma tana fahimtarsu ba.
      Shi kansa master tunda baba Saude ta zaunar da ita gefensa ya buɗe idanu ya kalleta sai da tsigar jikinsa ya tashi. Yaja numfashi batare da ya ce komai ba ya maida dubansa ga baba Saude. “Baba kije abinki kawai”.
      “To babana, amma babu wani abinda kuke buƙata?”.
     Kansa ya jinjina mata kawai. Sai kuma ya maida dubansa ga su Khalid.  “Tea da bargo”. Ya faɗa a taƙaice dan baya son yawan maganar.
     Cikin sauri Khalid ya nufi inda yake tunanin kitchen ne. Idris kuma ya nufi bedroom. Sai da duk suka shige ya maido dubansa gareta, batare da yace mata komai ba ya ɗaura hannunsa mara ciwon saman goshinta. Zafin da ya ratsa masa hannu ne ya sashi cije lip yana janyewa ya maida kan wuyanta. Ɗan zabura tai dan abin yazo mata a bazata duk da taji sanda ya taɓa goshin. Baice komai ba ya janye hannun. Hakan yayi dai-dai da fitowar Khalid ɗauke da babban bargo mai laushi. Zai warwaresa Master ɗin ya girgiza masa kai. Dai-dai nan shima Idris ya dawo ɗauke da shayin. Saman table ɗin ya ajiye yana jawosa gaban master ɗin duk da ya fahimci na Hibbah ne.
         Zamansa ya ɗan gyara yana riƙo hannunta, a ɗan zabure ta buɗe idanunta, kallon cikin idonsa da tai a mistake ya sakata saurin maida idanun ta rumtse hawaye masu zafi na silalo mata. Ɗan jawo hannunta da yay ne ya sata matsowa jikinsa dan gaba ɗaya a firgice take da shi da komai ma. Fahimtar hakan da yay ne ya sakashi kwantar da kanta a kafaɗarsa. Ta ja wata nannauyar ajiyar zuciya na tabbacin babu abinda tafi buƙata kamar ɗumin jikin uwa. Ganin haka yasa su Khalid barin wajen.
        “Bana son kuka”.
Ya faɗa acan ƙasan maƙoshin da yasa ita kaɗai ta jisa. Haɗiye kuka ta shigayi tana jan tagwayen ajiyar zuciya. Dan tunda ya ɗan jinginata da jikinsa tsinkewar da zuciyarta ke mata ya ɗan fara sassautawa. Hannu ya kai bisa fuskarta ya share mata hawayen yana faɗin, “Kinsan zuciyarki bazata iya ɗaukar duk wannan ba miyasa kika ƙirƙira?.”
      “Dan ALLAH kayi haƙuri”.
Ta faɗa tana fashewa da sabon kuka. Komai baice mata ba, sai kofi tea ɗin da ya ɗakko ya miƙa mata. Babu musu ta amsa ta hau sha, dan yau babu wata ƙofar samun damar masa gardama. Taso mata yake amma haka ta danne taita sha. Tana ajiye kofin tamkar jira sai ga amai. Ƙoƙarin barin jikimsa tai amma ya riƙeta. Tanata jujjuya masa kai alamar ya barta shi kuma bai fahimta ba. Sai kawai ta saki aman ya wanke musu jiki baki ɗaya.
         Da sauri su Khalid suka miƙe zuwa garesu. Hakan kuma yayi dai-dai da fitowar baba saude itama a firgice.
        “Dan ALLAH kayi haƙuri”. Tai maganar wani aman na yunƙuro mata, duk ta sake firgicewa, ta cire hijjab ɗin jikinta ta fara goge masa aman daya ɓatasa. Komai baice mata ba, sai riƙeta da yay ganin kamarma jiri na neman ɗibarta ta faɗi. Sai da ya tabbatar ta gama ya maida kanta kan kafaɗarsa ya kwantar.
     Duban su Idris da ke ta faman jera mata sannu yayi, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Mikewa yay riƙe da ita suka nufi bedroom duk da bayajin daɗi da ƙarfin nasa jikin shima. Har cikin bathroom ya rakata, bayan ya zaunar da ita ya haɗa mata ruwan ɗumi. Batare da yace mata komai ba ya fito ya barta.
      Da kallo tabisa wasu hawaye masu zafi na sake silalo mata. A ranta tana mamaki da tambayar kanta shi ɗin wanene shi?. Rashin mai bata amsa ya sakata fara zame kayan jikinta ta fara wankan batare da tunanin zai iya sake dawowa ba. A kiɗime ta waro idanu da saurin saka hannu ta kare jikinta tare da kaiwa tsugunne ganin ya turo ƙofar ya shigo kansa tsaye, shima da ga shi sai guntun towel.
Ɗauke idanunsa yay da ga kallon da yay mata shima, kayan da ya cire na jikinsa data ɓata da amai ya ajiye yana ɗan jan numfashi a sarƙe.............✍



*_Kuyi manage da wannan, da hanau gara mannau😬🚶🏻_*


    

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI......_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*

*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 
 

*_Chapter Thirty Six_*

...........(Kura ga tsoro ga ban tsoro) ya faɗa a ransa ganin yanda jikinta keta uban tsuma tama rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi. Kansa ya sake ɗaukewa tamkar baiga halin da take a cikin ba ya ƙaraso gareta bayan ya ajiye kayan. Kuka ta fashe masa da shi tana girgiza kai, dan a duniya bata taɓa shiga cikin tsananin kunya da firgici kamar na yau ba. Tayi matuƙar daburcewa, wajen ɓuya kawai take nema amma babu.
         Hannusa mai lafiya yasa ya zame hannayenta duka da take faman rufe jiki, duk ƙoƙarinta na son ganin ta faɗa jikinsa ta ɓuya kuma yaƙi bata daman hakan, sai ma sake mannata da yay da bango ya tokare ta da hannunsa mai ciwo duk da zogin da yake masa har zuwa yanzun. Cikin tsareta da idanu babu ko kunya ya fara magana cikin izza da ƙasaitar fushin da yake ciki har zuwa yanzun, “Nuna tsoro anan gazawace ga wadda ta nunama duniya ta girma, tunda har kika iya ɗaukar wancan da kika ƙulla, wannan ma dole ki ɗauka. Lokaci yayi daya kamata nima naga little Master a duniya, kafin ki ɗanamin tarkon da bazan tsallake ba Hibbaty”.
       Duk da ba komai ta fahimta a maganganunsa ba saboda ruɗanin da take a ciki, kanta ta shiga girgiza masa. Cikin rawar harshe da son ɓoye kanta tace, “Dan......”
        “Shiiii!!.” Ya faɗa yana ɗaura yatsansa bisa leɓenta.
       “Karma ki roƙeni dan zugani kike. Barinki a haka gareni haɗarine, saboda wannan kan naki ba kowane yare yake ganewa a cikin baƙi. Kinfi buƙatar dalla-dalla. Gara na tabbatar da kaina a gareki, kafin lokaci ya ƙuremin na ajiye jini na a jikin ki, maybe ki fara nazari kafin kiyi abu” .
    Baki ta buɗe zata sake yin magana ya rufe bakin da yatsunsa yanda har sai da azaba ta sakata cire hannuwanta da take kare jikinta da shi ta riƙe nasa hawaye na rige-rigen sakkowa a kumatunta.
       A karon farko ya saki wani lalataccen murmushi mai bayyana ƙunar zuciya, “K tsoro ce mai ban tsoro Muhibbat. Da yaren tsoro kawai ake fahimtar da ke karatun duniya. Tunda haka kikafi buƙata kuwa, sai ki shirya zaman jira da rainon ƴata ko ɗana har na fito a gidan yari tunda a can kikafi buƙatar ganina”. 
       Yana gama faɗa ya ɗan lakaci hancinta da janye jikinsa a nata, tana son yin magana yay mata alamar gargaɗi, idanunsa tamkar zasuyo aman bala'in da ke a zuciyarsa. Bai sake ce mata uffan ba ya juya mata baya ya sakarma kansa ruwa tare da cire towel ɗin jikinsa kansa tsaye tamkar yama manta da ita a wajen. Da sauri ta zame tai ƙasa jikinta na matuƙar rawa ta ɓoye fuskarta. Jin kamar ya kashe ruwan ya sata sake rumtse ido da ƙarfi kamar zatai kuka. Dan ita duk tunaninta tsayawa yay kallonta, duk da tanajin motsin da yakeyi alamar yin wani abu. Kaɗan ta buɗe idanunta sai taga har yanzu yana a yanda ya juya mata bayan. Ta ja ɓoyayyar ajiyar zuciya da fara ɗauraye jikinta da sauri-sauri. Duk da yanajin yanda take facal-facal da ruwa har yana fallatso masa a jiki bai juyoba, sai da ya kammala abinda yake a wajen sannan.
      Juyowar tasa tayi dai-dai da fisgar towel ɗin daya ajiye ta ɗaura. Duk da bai gama rufe mata jikin ba dai taji ƴar nutsuwa fiye da ɗazun da take a sule. Ya ɗan bita da kallo ganin yanda ta nufi hanyar fita da sauri har tanayi kamar zata faɗi, ga santsin ruwa da tiles ga na rashin ƙarfin jiki.
       Ya ɗan girgiza kansa da sakar ma kansa ruwan shower tausayinta na ratsashi. Tabbas yasan abinda ya faru a yau ɗin rubutaccene da ga alƙalamin ƙaddarar Sa. Ko babu ita sai hakan ta faru, tana da laifi yanada laifi. yasanma yafi yawa fiye da natan, sai dai yanda ya santa inhar ya nuna mata sassauci sake birkice masa zatayi, a yanzu kuma rayuwarta tafi ta kowa haɗari dan ita kowa kema kallon lagonsa. Haka dai ya kammala wankan cikin dabara da tunane-tunane. Bathrobe ya saka maimakon towel ɗin da ya shigo da shi tunda ta ɗauke. dan ya fahimci gaba ɗaya tsurewa take idan ta gansa babu rigan. Koda ya fito kwance ya sameta a kan gado ta kudindine da bargo. Komai baice mataba ya ƙarasa ga mirror yana ɗan duban kansa zuwa real face nasa na Isma'il da ya fito da shi. Jakar kaya daya gani ajiye a gefe ya sashi fahimtar su Habib sun dawo kenan. Koda ya buɗe kayansa ne a ciki da dukkan abin buƙatarsa na yau da kullum irinsu mai, turare da makamantansu. Ya ciri abinda zai buƙata ya ajiye gefe da wanda itama zata buƙata ɗin. Harya gama kintsawa Hibbah na cikuykuye abinta a bargo duk da tana jin motsinsa. Amma tsananin kunya da zazzaɓi sun hanata ƙwaƙwaran motsi.
        Shima duk da yasan idonta biyu komai baice mata ba, sai ma salla da ya tayar ta azhar. Sai da ya idar ya miƙe ya saka sabon mask sannan ya karasa saitin inda take a gadon. Hanunsa dafe da kansa dake sara masa ya kai zaune. Batare da yace komaiba ya yaye bargon da ɗaura hanunsa saman goshinta. Sosai jikin ya ƙara zafi, dan haka ya ɗan tsura mata jajayen idanunsa da ke sake tabbatarma mai kallonsa baida lafiya. “Ki tashi kiyi salla, sai ki sha magani ki kwanta”. Yay maganar har yanzu muryarsa bata fita da ƙyau.
         Sarai Hibbah tajisa. sai dai ta kasa koda motsawa harya tashi. Sai da taji ya fita a ɗakin gaba ɗaya sannan taja numfashi tare da miƙewa zaune tana share hawayen da ke ziraro mata wanda ba komai ya kawosu ba sai tsananin kunya da nadamar abinda ya faru. Ga kewa da ƙulafucin son ganin ƴan uwanta da Umminta da ke cike da zuciyarta.

    ★★
  
      Sosai su Habib sukaji daɗin ganin yay wanka ya sauya kaya. Sai dai tsananin tausayinsa na nan shimfiɗe akan fuskokinsu. Dan a kallo ɗaya da zaka masa zaka iya fahimtar rashin jin daɗin jiki dana zuciya dake tattare da shi. Kawai dai ƙarfin hali ne da juriya irin tasa.
       Sannu da tambayar yaya jikinsa suka shiga jera masa. Batare da ya iya buɗe bakin yayi magana ba ya shiga ɗaga musu kai kawai alamar amsawa. Basu damu ba, dan su kansu idan yana cikin irin wannan yanayin sunajin tsananin shakkarsa. Yanayine da yake a cikin fushi da zafin zuciya. Ƙiris yake jira wani ya shiga gonarsa ya tabbatar da fushin a kansa.
         “Ga magani ko a kawo tea sai ka sha?”.
    Musbahu ya faɗa cikin girmamawa. Master da ke kallonsu na tabbatar da suna a cikin ƙoshin lafiya ya jinjina kansa kawai yana rufe idanu. Sai kuma ya motsa laɓɓansa a hankali ya ce. “Kunyi salla?”.
       “Eh”
  Suka faɗa kusan a tare.
Komai bai sake cewa ba da ga hakan sai da Adam ya gabatar masa da magungunan da suka shigo da shi. Khalid kuma yay saurin nufar kitchen ya ɗakko ruwa tare da tea da ya haɗo masa. Batare da yayi magana ba ya ɗauka tea ɗin yasha kusan rabin cup. Shima maganin yasha.
        Fahimtar ya kammala ya saka Habib fara masa bayani a nutse game da aikin daya turasu. “Alhmdllh Master anyi bani gishiri in baka manda. A yanzu haka dukkanin iyalansu suna a hannumu”.
       Kansa ya jinjina fuskarsa har tana nuna alamun jin daɗin yanda sukai aikin cikin sauƙi da sauri babu wani mishkila. Musbahu ya dire jakkar da suka shigo da ita shima yana faɗin. “Wannan wayoyinsu ne duka anan. Duk da mun yanke network ɗin gidan gaba ɗaya saboda tsaro dai sai muka taho da su. Kayi haƙuri munyi abinda baka saka mu ba. A cikin yaran akwai wani mai taurin kai ya nema mana gardama muka bibbigesa, dan mun nunama mamansa ta tsawatar masa amma taƙi”.
         “Yaron waye?”.
Master ya tambaya yana kafe Musbahu da ido. Adam ne ya bashi amsa da cewar, “Kamar dai yaron Engineer ne”.
        Komai Master bai sake cewa ba, sai hannu da ya miƙama Habib da ke riƙe da lap-top ɗinsa. Cikin sauri Habib ya buɗe lap-top ɗin ya kunna ya miƙa masa. Filo ya sa a cinyarsa sannan ya ɗaura system ɗin. Sai kuma yay ma Adam nuni da jakkar da sukazo da ita na wayoyi. Jakar ya zuge ya zazzage wayoyin a saman table ɗin. Komai Master bai ce ba ya miƙa hannu ya ɗauka ɗaya da ga cikin wayoyin ya jujjuya a hannunsa. Kamar zai kunna sai kuma ya fasa ya ajiyeta. Wayarsa da ke a gefen damarsa ya ɗauka, ya ɗanyi danne-danne tare da kaiwa kunnensa ya lumshe ido da kwantar da bayansa jikin kujera jin ta shiga.
       Duk sake nutsiwa su Habib sukai da tunanin wa yake kira a cikin wannan ruguntsumin kuma?. Rashin samun amsa ya sakasu nutsuwa a saurarensa.
       Wayar na gab da tsinkewa aka daga. Shiru baice komaiba. Takaici ya saka A.G dake can faɗin, “Waye ke magana?”.
        Wani lalataccen murmushin gefen baki ya saki, cike da izzarsa da ƙasaita yace, “Master!!”.
       Duk da sunan ya daki zuciyar A.G sai ya dake, harda saki wata dariyar gatsatsa wadda tafi kuka ciwo. “Hhhh karen farauta! kai har kana da zarrar ɗaga waya ka kira wani a cikinmu a wannan lokacin kenan? Kako san su wanene mu kuwa?”.
       Master ya sake sakin murmushi a karo na biyu da gyara zamansa. “Sai da na sanku ma sannan na fara wasan kaima kasan wannan”.
        A.G da kejin zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito ya rumtse idanu da ƙarfi batare da ya tuna a tsakkiyar jami'an tsaro yake ba, dan meeting sukeyi akan Master ɗin ya ce, “Kai kare! Idan damar da ka samu a baya kake tunanin tana hannunka har yanzu to ka sani rayuwarka ta ƙare a wannan gaɓar.”
          A bazata su Habib sukaga Master ya ƙyalƙyale da dariya, sai kuma ya haɗe fuskar cikin kaushi da barazanarsa ya cigaba da magana.
       “A.G! A.G! Na master. Shin ba kune kukace ɓoyayyen wasa bane ba babban jami'i mai gaskiya?. Ya da tada jijiyar wuya tun a farkon karo haka?.........”
        A fusace A.G ya miƙe yana buga table ɗin batare da ya tuna a inda yake ba. “Kai tsinanne, ka sani duk randa kazo hannu ni ɗin nan da hannuna zanyi gunduwa-gunduwa da namanka na bama karnukan farauta da suka fika giyata su cinye namanka a tsakkiyar kasuwa!!”.
       “Tofa babbar magana, wai da wuri haka har ka fara fusata?. Nifa ta ɓangare ɗaya kawai na fara buga wasan a yanzu, amm har kake tada jijiyar wuya da ɗaukar alwashi kamar haka. To kwantar da hankalinka dan bamma fara komai ba, yanzu ma na kiraka ne danna sanar maka tarkacenku na hannuna, a kuma daren yau wasu a ciki zasu iya tsallakawa barzahu, gawawwakinsu kuma zasu iya zuwa maku ƙarfe biyar ɗin asubahi. Ku shirya dakatar da hakan ta dawo min da ahalin MATATA. Sannan ku tabbatar kun lashe aman da kukai na kalamaku daga nan zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu, daga nanne sai ai wasan fili ba TAKUN SAƘA ba. Umarnine ba shawara ko neman alfarma ba..”
      Ya katse kiran da jefar da wayar gefensa yana cija lebensa na ƙasa da haƙori tamkar zai huda shi. Sai kuma ya buɗe jajayen idanunsa dake fusace ya dubi su Salis da sukai tsuru-tsuru.
      “Kuje ku huta, zuwa dare ku tattara min dukan bayanai akan maganganun su A.G da duk wani mai faɗa aji da ya fito yay magana. Salis ka turama Faisal cewar ya kawo saƙon nan, sannan ya faɗama *_WALƘIYA yayi barci a farkon dare, ya farka a farar asubahi. Kar yay baƙin ciki akan rubutacciyar ƙaddara, farautar *MASTER* ba wawaso akan naman shanu bane. Masu tambari a bayan ƙeya sun tabbatar da shiryawarsu tunda suka bayyana wasan a fili. Ya shirya dan yanzune TAKUN SAƘA zai fara”_*.
        A tare suka ƙame jikinsu da salute nasa. Fuskokinsu washe da fara'a suka hada baki wajen faɗin, “Yes master!!”.
      Wani shegen lalataccen shu'umin murmushi ya saki a karon farko da ɗaga lumsassun idanunsa ya dubesu. Tausayin ƙannen nasa kuma ahalinsa a halin yanzu na ratsashi, a hankali ya buɗe hannayensa ya mika musu alamar suzo garesa saboda yanda duk suka koma kalar tausayi a dalilin halin da yake ciki, baya son ganinsu cikin damuwa sam. Cikin ɗoki da zumuɗi suka nufo jikinsa batare da sun yarda sun fama masa ciwukansaba saboda tsabar taka tsantsan ɗinsu garesa. Ya haɗiye hawayen da suka ciko masa idanu cikin muryarsa da ke bayyana kaushinsa da ƙaunarsu ya furta, “I love you so much my sweet Brothers. ALLAH yay muku albarka.”
        Hawayen dake bin fuskokinsu suka shiga sharewa kamar yanda suka saba a duk lokacin da ya furta tsananin kaunar da yake a garesu. Cikin haɗa baki suma suka shiga sanar masa da ɗunbin ƙauna da soyayyar da suke masa har cikin ruhi da ɓargo. Irin wadda gaba ɗayansu suke jinsa a ransu tamkar mahaifi. Dan ya ɗaukesu lokacin da nasu iyayen suka jefar da su. Ya raineso lokacin da iyayensu suka nisancesu. Ya kaunacesu lokacin da iyayensu suka manta da su. Ya basu tarbiyya lokacin da iyayensu suka toshe idanunsu da kunnuwansu. Ya inganta rayuwarsu lokacin da iyayensu suka nuna gazawa da su. Ya yalwata farin cikinsu tamkar yanda kowaɗannen iyayen ƙwarai suke yalwata na ƴaƴayensu da basu gata. Bai taɓa banbantasu da Habib ba balle nuna ya fisu a gareshi.
      “Bana son kuka”.
  Ya faɗa a hankali yana shafa kawunansu da hanunsa mara ciwo tare da ɗan jan kunen Salis dake gefen damarsa cikin salon da yake musu punishment tun suna yara idan sun masa laifi. Dariya suka sanya dukansu suna share hawayen. Kafin su miƙe kowanne ya manna masa kiss a gefen kumatunsa, dan wannan itace fuskar da suke ɗauka real face ɗinsa saboda ita suka taso suka sanshi da ita. Hakan ya sakashi sakin murmushi ƙarfin hali. Tausayinsu na ratsashi da tarin ƙaunarsu. Sune ahalinsa, sune farin cikinsa, sune raunin sa, sune... Sune... Sunee.... Da yawan da babu adadin kididdiga.

         ★★★
  
   Gaba ɗaya A.G ya birkice, jiya yake tamkar ya jawo Master ta cikin wayar. Su kansu sauran jami'an kallon mamakin rikicewar tasa suke duk da sun san cewa mastern yay masa illa. Cikin gaggawa aka fara bibiyar lambar da yay kiran. Sai dai kash babu wata hanyar da za'a iya samun sa.
        A.G da gaba ɗaya jikinsa ke matukar rawa ya fice tare da wasu jami'an domin tabbatar da zancen master ɗin. Cikin lokaci ƙanƙani hukumar ƴan sandan ta sake rikicewa. Suma su Alhajin Mande aka fara kiran wayoyinsu domin ji da ga garesu....

★★

     A ɓangaren Abba kam sai da suka zuba masa ruwa sosai ya farfaɗo. Koda ya buɗe ido ya kallesu tsaitsaye a kansa sai ya fashe da kuka. Cikin mamaki da tsoro suke dubansa. Hajiya mama da zuciyarta ke tsitstsinkewa da tunanin waye kuma ya rasu tace, “Halilu kabar mana wannan kukan ka sanar min wanene ya rasu ne?”.
     Sake fashewa yay da wani sabon kuka saboda jin abinda hajiya mama ta faɗa. Sai kuma ya rarumo wayarsa batare da ya bata amsa ba. Number A.G ya shiga nema amma kuma ya gagara samu. Sai busy take nuna masa. Ya maida akalar kiran kan Alhaji Balele. Sai da tana gab da tsinkewa ya ɗaga. Ɗan gidan Alhaji Balele da ya ɗaga wayar cikin kuka da ga can yake sanarma Abba ai suna asibiti, tunda yaga yasar da Master yay masa shima ya yanke jiki ya faɗi. A yanzu haka ma likita ya sanar musu paralysis ta kama shi.
      Rawa jikin Abba ya kamayi, sai kuma ya fashe da sabon kuka yana jeroma Master tagwayen ALLAH ya isa da tsinuwar alkaba'i kala-kala. Takaici yasa Momy fisgar wayar a hannunsa ta fara dubawa. Dan yaki musu bayanin da zasu fahimta gashi yana rusar kuka tamkar wani ƙaramin yaro.
      Komai bata fahimta ba, dan haka ta dangwarar masa da wayar tana jan tsaki tabar wajen, hakan yasa suma su Ameera bin bayan uwarsu suma cikin takaici suka bar Hajiya mama ita kaɗai tsaye akan Abba.
     Sai daga baya suka fahimci abinda ke faruwa ta hanyar kunna tv. Hankalinsu ya tashi suma matuƙa. Dan a take momy ma tai zaman ƴan bori da ƙwala ihu. “Na shiga Uku dadyn Junaid kai ko miya haɗaka da Master har ka shiga lissafinsa?”.
         “Tsautsayi!. Wlhy Tsautsayi ne ni Halilu na shiga uku. A.G ka gama da rayuwata. Nayi dana sanin sanin matsiyacin yaron nan mai kama da bokan tsauni”.
        
    *_________________________*    

            Har zuwa yammaci abu ɗaya ke maimaita kansa a kowacce kafa ta yanar gizo da kafafen yaɗa labarai. Manyan masu fashin baƙi nata famanyi tare da jami'an tsaro da jama'ar gari ƴan bani na iya. Babu wanda yasan da ga ina hoton Hibbah da ahalinta ya fito sai gashi yana yawo. Master dai babu ma wanda ya sansa balle ya fidda hoton nashi. Sai dai hotunansa na ɓadda kama da keta yawo wanda yake a cikin fuskoki kala-kala da ko yatsansa ba'a gani.
       Ana tsaka da wannan kace nace kuma sai ga sabon zance ya fito da ga su A.G cewa anyi kidnapping ahalinsu har gida. Hatta da ma'aikatan gidansu ba'a bari ba sai masu gadi kawai.. Dan shi A.G ma securitys ɗin da ke a gidansa suna bada tsaro saboda kasancewarsa babban jami'i kansu an kwashe harda su.
         Komai ya sake tashi sabo anata kace nace na hasashen dalilin yin hakan da Master yayi, sai dai abinda ke ba mutane mamaki a wannan gaɓar miyasa Master ɗin zaiyi hakan? Tunda kowa yasan a baya iyakarsa satar kuɗi ba'a taɓa jinsa da yin garkuwa da mutane ba.
      A gefe kuma na manya irinsu A.G da wasu kasashen ƙetare na ƴan bani na iya har wasu na iƙirarin saka sunan Master ɗin a jeren ƴan ta'adda na duniya. Sun kawo hujjoji da dama na cewar hakan da hasashensu ya basu. Musamman da a wannan karon al'amarin nasa ya fito fili

Please Login or Register in order to submit comment