Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke ba. Wata ajiyar zuciyar ta sake saki ganin ya nufi hanyar bedroom ɗin da suka kwana. Badan yace idan ta ƙiyi bazai kaita wajen Ummi ba da tabbas bazatayi ɗin ba, amma tana buƙatar ganin ahalinta zata iya komai dominsu. Kusan mintuna goma sha uku da shigarsa sai gashi ya fito. Badan ta tabbatar da bayan shi ɗin babu wanda ya shiga ɗakin ba da babu yanda za'ai ta yarda shine. Ya canja kayansa zuwa manyan kaya irin na tsoffin dattijan Alhazan kauyen nan harda rawani, ga uban farin sajen da ke akan sabuwar fuskar daya canzo sak wani dattijon ƙwarai irin wanda basuko damu da duniya ba. Sai sanda a hannunsa da dogon carbi. Hannunsa kansa sun canja da ga nasa zuwa kalar fuskar zam. Ya zaro ƴar karamar wayar nokia ɗin data sha wani shegen farin salatap da har ya fara komawa brown dan tsufa. Kunnensa ya kai alamar kira ya amsa. Yana sauke wayar a kunne yana duban su Adam da suka mike.
      “Done”.
Suka faɗa a tare shi da Zaidu. Kai ya jinjina musu yana maida dubansa ga Habib. “Ka kula da komai, abinda bata gane ba ka nuna mata, aikinta ne na tsakkiya samun matsala daga gareta yana nufin komai zai ɓaci”.
      Kai Habib ya jinjina masa da faɗin, “Insha ALLAH mune da nasara. ALLAH ya dawo daku lafiya”.
     Amin ya faɗa yana duban ɗakin da su Zaidu suka nufa, sai kuma ya kalli agogon hanunsa irin na sarƙa ɗin nan da yaci duniya ya koɗe matuƙa duk da Silver ne dama. Dai-dai nan su Zaidu suka fito da sauri cikin sabuwar shiga suma. Daka kalli Adam bashi da maraba da driver. Zaidu kam tamkar irin yaran alhazan kauyen nan da bakinsu bai rabo da tsugudidi. Ga jikka ya riƙe wadda ko ba'a faɗaba kasan ta alaramma Muhammad Shuraim Master ce dai.
     “Ga kuɗin an shirya Master”.
Zaidu ya faɗa yana buɗe jakkar hannun nasa mai kama da karamin akwatin maza na tafiya. Shiryayyun kuɗi ne a ciki ƴan ɗari biyar-biyar da ɗari bibbiyu. Kai ya jinjina masa kawai alamar komai yayi.
      Inhar ana mutuwa a zaune to yau dai da alama Hibbah ta mutu. Dan harsu Master suka fice a falon bata gama dawowa hayyacinta ba sai da Habib ya fargar da ita. Cikin alamar ruɗani tace, “Ina zasuje wai?”.
    Murmushi Habib yayi yana ɗan matso da kujerarsa kusa da tata kaɗan. “Aiki zasuje mana.”
      “Aiki?”.
Hibbah ta faɗa cikin sigar tambaya. “Babu lokacin tambaya aunty Queen mu cigaba da namu aikin dan mune tamkar ƴan jagorarsu. “Gaskiya indai satar kudaɗen mutanene bazanyi ba”.
    Tai maganar tana ƙoƙarin mikewa. Kamar daga sama taji muryarsa yana faɗin, “Ashe kuwa ke da Ummi har abada. Na kuma gama aiki nace yayunki sukayisa”.
    Waige-waige ta shigayi cikin falon sai dai babu alamarsa. Sautin muryar tasane kawai data kasa fahimtar da ga ina yake fitowa. Kuka ta fashe dashi tana komawa ta zauna a kujerar. Lallai ta tabbatar yau tana a tsaka mai wuya. Abinda takeji a labari yau shi hannunta zai aikata.
      “Kuka bazaiyi magani ba aunty Queen, duk wani motsinki dake anan tamkar akan idonsa ne garama kiyi kawai".
     Habib yay maganar cike da lallashi. Kamar ta makesa shima takeji, shiyyasa taki tanka masa ta cigaba da abinda takeyi zuciyarta na kawo mata wani shawara acan gefe. Yarda da shawaran yasata share hawayenta ta maida hankalinta ga aiki kamar yanda Habib ke nuna mata shima yanayi.

      A ɓangaren Master kuwa sun isa banki a tsohuwar motar da Adam ya tuƙasu. Adam ne ya taimaka masa ya fito a motar shi a dole ga dattijon da yaci duniya jiki yay laushi. Yana gaba Zaidu na biye da shi yana zuga surutu da kyalƙyala dariya irin dai garorin nan yan bani na iya na gefen alhaji. Shiko Master sai wani gaftarar goro yake yana ƴar dariya da bama Zaidun amsar wasu zantukan nasa.
     Gaba ɗaya kallon garori securitys ɗin bank ɗin sukai musu. Bayan an dubasu babu alamar wani abun ashha tare da su aka basu damar shiga. Yanda Zaidu ke zabga surutu Master na dariya yasa mafi yawan mutanen dake akan layin tura kuɗi da amsa kallonsu, wasu na musu dariya wasu na musu kallon ƙauyawa ne. Master dake lure da motsin kowa ya yafito wani gaye da ya tsuƙe cikin shigar manyan yara yanata bada iska. “Yaro yaka nan ka taimakeni, dan wannan mai bakin kamar bututun mai yanda bansan a ba shima ba bihim ya sani ba. Garama ni nayi yaki da jahilci lokacin da nake zuwa sarin atamfofi na manta wasu abubuwanne kawai.
     Gayen da gaba ɗaya ya gama ƙiyastama ransa tsuntsu da ga sama gasashshe ya karaso yana wani taɓe baki. Wata cimirmiɗaɗɗiyar takarda Master ya fiddo a aljihu ya mikama gayen. “Yarona duba mini nan, ƴan kuɗaɗena na kayan amfanin gona dana noma na sayar zan buɗe akawun na zuba. Nima jikana dake can kudu ya bani shawara amma yace na nema wannan daya rubuta min anan zai taimaka mini aimin komai na buɗe akawun din na zuba kuɗaɗena a ciki naje gida nai barci babu ruwana da takadarai”.
     A karon farko gayen ya dashare baki da faɗin, “Ai babu damuwa baba koni ma na maka. Kaga zomuje can sama acan ake buɗewa.”
    Babu musu Master ya amince. Suka nufi saman bene Zaidu na biye da su. Gaye da gaba ɗaya hankalinsa nakan jakar hannun Zaidu ya sami ma'aikaci guda sukayi magana. Form aka basu da zasu cike suka koma can gefe inda babu yawan mutane.
     A ɓangaren master tun shigowarsu wajen yaga Musbahu, shima kuma ya gansa dan cike da ƙwarewa sukaima juna alama da ido. Kafin Master ya ɗauka ƴar nokia ɗinsa ya fara magana da ƙarfi har hankalin mutane na dawowa kansa. Wasu na dariya wasu na tsaki wasu taɓe baki. Dan kuwa dai garanci zam Master ke zubawa abinsa Zaidu na tayasa cikin kwakwazo shima.
     Da wannan damar gaye yay amfani wajen saƙala hannunsa a hankali ta ƙasan teble ya zuge jakkar hannun Zaidu. Rafar yan dari biyar ya jawo har sau uku ya tura aljihu, yayinda a gefe tuni Zaidu ya sane wayar gaye daya ajiye akan table shi kuma. A dai-dai nan Musbahu yazo a ɗan fusace yana faɗin, “Haba baba dan ALLAH kake magana a hankali mana. Nan fa ba ƙauye bane ko gida cikin banki ne”.
      Cire wayar Master yay a kunne yana zabgama Musbahu dakuwa. “Kaci gidanku dan bantan ubanka. Anki ayi a hankalin idan lahirace nan ɗin jefani a wuta. Mara mutunci takadarin banza.”
     Yanda Master ke masifar yasa mutane fara bashi hakuri da nunama Musbahu kuskurensa na kodan furfurar Master ɗin ya kamata ai ya tauna harshensa yay masa magana ta hankali. Yayinda wasu kejin daɗin abinda Musbahun yayi. Ga Zaidu da tuni ya zurama Musbahu wayar gayen nan a aljihu yana nunashi da dan yatsa alamar bama ogansa kariya. Yanda suke abun baka isa tunanin suna da wata alaƙa ba. Musbahu ya fice a wajen a fusace saboda securitys da sukazo suka tasashi gaba. Yayinda suke bama Master dake matsar kwalla haƙuri.
     Sai da wajen ya samu nutsuwa Gayen nan ya cigaba da cikema Master form yana tambayarsa. Yayinda Master ke amsa masa cikin raba hankalinsa. Dan nokia ɗinsa yake ta dannawa wai yana neman lambar jikansa daya sakashi zuwa ya buɗe akawun..........

    Anan bangaren Hibbah kam aiki take yanda Habib ya nuna mata hankalinta na ga ɗakin da suka kwana. Habib na cewa su ɗan dakata ta miƙe wai zatayo fitsari. Ɗakin ta shiga ta maida key ta kulle ranta fal farin ciki, dan tayi alƙawarin saita buɗema su Master aikin da suka tafi yi. Wadrobe ta nufa ta fiddo wayar da taga ya ajiye a ciki yau da safe, cikin sa'a kuwa ta ganta. Koda ta ɗakko a kashe take, cikin rawar jiki ta kunnata sai ko gata ta kawo. Wani ɗan tsalle ta buga zuciyarta na mata canki in canka akan wayarwa zata fara kira ne. (Ta yan sanda) zuciyarta ta bata tabbaci. lambobi da yaya Abubakar ya taɓa sanar mata cewar na taimakon gaggawane da ga hukumarsu ta loda a wayar, cikin sa'a tanayin dialing kuwa ta shiga😱..............✍


(Hibbah😬😬😬🙆🏻🤦🏻).

        *_Kuyi haƙuri na zama sai a hankali sa kun haɗa da addu"a_*




TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI......_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*

*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 



*_Typing📲_*




*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


______________________


*_Chapter Thirty Four_*

...........Harta yanke ba'a ɗaga ba, sai dai da ga ƙarshe ake sanar mata ta dakata ana amsa wasu kiraye-kirayen ne. Bakin gado taje ta zauna tana sauraren a ɗaga ɗin, dan an saka taken ƙasa ne domin kar a bar mai jira shiru. Kusan mintuna uku ba'a amsa mata ba taji haushi ta yanke. Tagumi ta rafka ranta zattakaici, taci alwashi duk ma yanda za'ai a yau ɗin nan sai tayi sanadin da za'a kama Master da su Halilu. Bazata yarda ta kira yaya Abubakar ba dan gudun kar'a sake irin na farkon kaita wajen ƴan sanda.
 
       ★★★★

     A ɓangaren su Master kuwa koda Musbahu ya fita sai ya koma can gefe. Da wayar gayen nan da Zaidu ya sano musu yay amfani, sai da ya tabbatar yayi duk wani abunda bazai saka rayuwar gayen a haɗari ba sannan ya ƙaddamar da shirinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci shi da Master dake can ana cike masa form yana danna waya da subaɗi suka shiga wawasar kuɗaɗe. Yayinda acan kuma su Salis suma suke kaddamar da nasu shirin akan sauran asusan. Dan yau aikine ba'akan mutum ɗaya ba. Kusan asusu goma sha zasu yashe a ƙiyasi.
          Master na gab da tatse kuɗaɗen asusai uku daya haɗa gabansa yay wata irin faɗuwa. Addu'a yay saurin karantowa zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Cikin sauri ya dubi Zaidu.
      “Ba'are anya kuwa baƙaƙen shanun gidan ɗan sandamu basu shirin kaima gonata ta yammaci hari? Inaji a jikina maƙwafcina ya samu damar yimin ƙafar angulu kuwa”.
        Kai tsaye Zaidu ya fahimci zaurencen, dan haka ya ɗan kallesa a ɗan firgice. “Alhaji Baba wanne maƙwafcin a ciki? Mati mai igiya ko sambo?”.
       “Bansan waye a cikiba ba'are, sai dai zuciyata na min zargin Mati mai igiya ne dan nayi kuskuren ajiye wayar lantarkin nan da za'aimin wayarin wuta a kogon ɓaure. A lokacin Kuma Mati na cikin gonata zai bani taimakon ruwa saboda zafin ranar da akai jiya. Inhar hasashena yayi dai-dai akan idonsa na ajiye wayar lantarkinnan. Ɗakko tarho ɗinka ka kira min ɗan ƙane ka shaida masa ya leƙa gonata ya bincikamin waya a cikin kogon ɓaure, sannan ya sanar maka Mati mai igiya yana kan tudune koya tashi?”.
       “An gama alhajin ALLAH”.
Zaidu da duk jikinsa ke tsuma ya faɗa yana nufar hanyar fita daga cikin bankin. Waya master ya ɗaga yay kira. Ana dagawa ya fara magana cikin wani zaurancen. “Sallau kun gama tattare harawar nan kuwa?”.
       Gaban Salis dake gab da kammala nasa aikin ya faɗi. Cikin ɗan waige-waige ya bashi amsa da faɗin, “Muna gab dai”.
       “To maza kuwa ku tattare dan Mati mai igiya ina tabbatar da ya turo baƙaƙen shanun ɗan sandamu cikin gonar yamma. Da alama kuma zasuyi ɓarna bawai a gonata kawai ba harda ta maƙota. Kuyi himmar tafiya gonar yamman harda su Kalla ku tasamin ƙeyar mati kafin shanunsa su iso ya koma gabashi. Ni kuma zan kira maigari na tabbatar masa tsiyar da matin ke shirin tafkawa”.

     Lokacin da Master ke wannan ƙoƙarin na fargar da yaransa halin da ake ciki a dai-dai lokacin Hibbah ta sake kiran wayar. Kuma cikin sa'a aka dauka mata. Jikinta har rawa yake jin an amsa. Daga can aka tabbatar mata ta kira wayar taimakon gaggawane daga police station mai lamba talatin da uku a anguwar andu dake jihar. Wane taimako take buƙata.
       “Babu taimakon da nake bukata, ina dai tabbatar muku a yanzu haka gawurtaccen barawon nan da yaransa na kan hanyarsu ta wawasar kuɗaɗen wasu mutane ta banki. Nima satoni yayi yanzu haka sun barni anan gidanne sun wuce”.
      “What!?”.
Aka faɗa daga can ana mikewa. “Ƴammata minene sunan anguwar da kike yanzu haka?”.
       “Nima ban sani ba yallabai. sai dai ku bibiyi wannan kiran nasan zaku dace. Dan a yanzu haka suna gab da dawowa na tabbatar”.
     

★★★

      *_Bank_*

       Cikin jin haushi gaye yace, “Nikam Baba kodai baka shirya buɗe accaunt ɗin nan bane na kama gabana? Inada abunyi fa na zauna taimakonka amma sai wani kiran waya kake akan wata wayar lantarki ɗin banza ne ko harawa ma oho maka”.
         “Kai ja'iri waccan harawar tanada mahimmacin da tafi wannan buɗe akawun ɗin. Kaga nama fasa buɗewar sai wani satin zanzo da jikana muzo tare.”
     Master yay maganar yana mikewa. A take mutane suka shiga bashi haƙuri da wasu ma'aikatan bankin, amma fafir yaƙi dan gab aikinsa yake da kammala shiyyasama ya tsaya yana biye musu. Kuɗin daya wawasa na kammala shiga accaunt ɗinsa wani irin jiniya ya fara a cikin bankin. Yanda abin yazoma mutane a bazatane ya tsoratasu bankin ya hargitse aka fara fita a guje. Tuni master yabi rububi ya fice bayan ya cire babbar rigarsa da mask ɗin fuskarsa ya yarda, da sandarsa da carbi. Securitys da ma'aikatan bank ɗin da sukasan minene ma'anar jiniyar dan an sakatane saboda tsaro dama hankalinsu yay masifar tashi. dan fara ƙaɗawar jiniyar yayi dai-dai da fitar maƙudan kuɗaɗe a cikin wasu asusai biyar na manyan mutane dake bank ɗin. Ƙoƙarin hana mutane ake fita ta ƙarfin tsiya, yayinda daga cikin bank har sun kira jami'an tsaro.
     Master na fitowa ya sake cire dayar mask ɗin face ɗinsa ya yarda, dan zuwa yanzu zuciyarsa ta gama bashi Hibbah ta ɓallo musu ruwan da yafi na bankin tsauri. Sam baiyi tunanin taga sanda ya ajiye wayar nan ba. Babbar damuwar wayace da sam babu wani tsaro tare da ita sai idan tana a kashe. Dan yana amfani da itane wajen yin magana dasu A.G, ya tabbatar inhar ta kunnata ko tai kiran wani cikin sauƙi zasu gano inda take musamman da ya san saƙon da ya aika na wawashe musu kuɗaɗe zuwa yanzu ya isa garesu. Hankulansu yana a tashe ne, tare da tsintar kansu ckin ruɗanin yanda akai reshe ya juye da mujiya.

★★★★

              Kamar yanda Master yay hasashe hakance ta kasance. Dan kuwa aikinsu na cika dukkanin wayoyin su A.G saƙwanin alerts na fitar kuɗi suka fara shiga musu. Duk da a mabanbanta wajeje suke kusan a lokaci ɗaya duk suka miƙe zumbur a cikin matuƙar ruɗani da tashin hankali kowa na tambayar mike faruwa? Yaya haka?. Zukatansu na jera musu waɗan nan tambayoyin suna ƙoƙarin kiran juna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fahimci cewar ɗan zakin da suke tunanin sun raina ya girma. Dama a kwanakin nan babu abinda sukeyi sai zaman meeting akan Master. Dan zukatansu na raya musu lallai akwai abinda yake shiryawa shiyyasa yaƙi basu kuɗaɗen da ake tarawa tsahon shekaru biyu. Sun yankema kansu shawarar yana kammala musu aikin nan da suka bashi zasu ruftashi kawai. Sai gashi shi ya fara rufta rayuwarsu alamar shirinsa daɗaɗɗe ne a kansu.
     A.G ne ya saka bibiyar masa number master ɗin duk da basu da tabbacin samu, ana tsaka da bibiyarne batare da an samu ɗin ba Hibbah ta kunna wayar, cikin hanzari jami'in da ke zaune a computer room ɗin nasu yana aiki akan number ya sanarma A.G. shine ya bashi damar yin azamar saita layin akan duk kiran da za'ai ya shigo wayarsune, sannan ya bibiyi a inda lambar take. Shi kuma ya fita yana bada umarnin a haɗa runduna za'a fita operation na gaggawa. Yana dawowa computers room ɗin ya samu Hibbah na zuba bayani ta waya, kuma komai akan kunnensa shima ta zayyane.
      
         A ɓangaren Abba shi kuwa sai da aka fara lasa masa zumane, dukannin kuɗaɗen dake a asusun mahaifin su Hibbah sai da aka juyesu a asusun sa. Farin ciki ya sakashi kaiwa duƙe yay sujida (irin mufa mun fara tsoron ALLAH ɗin nan). A lokacin duk yaransa na zagaye da shi dan an sallamo Junaid ne yau da ga asibiti duk da bawai ya warke bane ba. Gaba ɗayansu galala sukai suna kallonsa. Ameera tace, “Abbah halan yau wani ya maka kyautane? Dan inba kuɗi ba banga abinda zai sakaka wannan rawar jikin ba harda su salla babu alwala babu kallon gabas?”.
      Farin cikin da yake a cikine ya hanashi tanka mata, sai baki da ya sake washewa yana nufar hanyar bedroom ɗinsa cikin ɗunbin farin ciki. Sai kuma ya dawo da baya domin ɗaukar babbar wayarsa da nufin turama Master kuɗin tukuyci kafin yaji farashin sauran na aiki. Dan ya saka a ransa ko nawane Master ya nema sai ya bashi harma da ƙari. Yana ƙoƙarin ma Master transfer ɗin dubu ɗari biyar na tukuyci wasu sabbin alerts ɗin suka fara rige-rigen shigowa. A zatonsa wasu kuɗinne suka shigo dan haka ya buɗe da zumuɗi.
      “Wayyyyiiiihuuuuuu!!!!! Ni Halilu na mutu!”.
     Ya faɗa a matsanancin firgici har sai da su hajiya mama suka toshe kunnuwa suna miƙewa tsaye a matuƙar firgice ganin Abba ya yanke jiki ya faɗi a wajen wayoyin duk sunyi gefe.

★★★★★

     Abinda ke a kunnensa ya danna lokacin da yake shiga motar da sukazo yabar wajen, dan tuni su Zaidu sun ware. “Habib ka ɗauki yarinyarnan yanzun nan kubar gidan nan, ka tabbatar kafin ku wuce ka kashe wayar hannunta ka cire sim card ɗin ciki kayi flushing ɗinsa. Ga su Zaidu nan isowa. Kubi ta cikin store ɗin kitchen akwai hanyar da zata fiddaku ta wancan layin.”
     Sosai hankalin Habib ya tashi, dan yanzun nan dama ya kama Hibbah da waya. Yana tsaka da tambayarta ne kiran master ya shigo masa. Wayar ya fusge daga hanunta a fusace ya takata bayan ya fashe. murfin ya ɓalle da kyar, ɗan pin ɗin dake jikin blackboard ɗin inda computers ɗin suke ya ɗauka ya cire sim card ɗin ya karya. Yay azamar danna wani abu a jikin teble ɗin yay ƙasa.
    Baki Hibbah ta taɓe dan a ganinta kafin ya gama duk wannan abun da master yace ta tabbatar ƴan sanda sunzo. Ranta fes yau ALLAH yayi dubun masu aikata saɓon ALLAH ya cika.
       Dawowar Habib yayi dai-dai da shigowar su Salis kusan a tare. Gaba ɗaya firgice suke. Jakunkunansu suka shiga ɗakin da suke kwana suka tattaro. Habib ya fisgi hanun Hibbah da duk abinda suke tana tsayene kamar dogariya tana kallonsu. Sai faman taɓe baki take irin ko'a jikinta ɗin nan. Hannun ta fige tana ture Habib, a dai-dai na Master ya shigo falon shima.
      “Ku tafii!!!”.
Ya faɗa da ƙarfi jin jiniyar ƴan sanda na gabato anguwar. Yay maganar yana nuna musu hanyar kitchen, kallo ɗaya zakai masa kai kanka ka firgita dan gaba ɗaya ya rikiɗe tamkar wani bajimin zaki. Kobi takan Hibbah da tsawarsa ta firgita baibi ba. Ya nufi ɗakin da suka kwana cikin zafin nama. Mintun uku tsakani ya dawo falon, wanda yay dai-dai da ƙarasowar ƴan sandan ƙofar gidan. Ga kuma Hibbah data nufi hanyar waje da gudu. Baya ya take mata shima. Sabon tashin hankalin daya yunƙuro masa ne yasashi fisgo Hibbah cikin zafin nama ya yarfa mata wani shegen mari mai azabar zafi da saida jinta da ganinta suka gushe na wucin gadi. Ya kama kunnenta ya murɗe da shegen karfi yana magana cikin matuƙar hasala da hargowar da bata taɓa gani tare da shi ba. “Stupid girl!!, idan ni baki kasheni ba, ke da hannunki da wannan shegen taurin kan naki zaki kashe ahalinki”. Wani irin rawa jikinta ya fara hawaye na mata ambaliya akan fuska. Ya turata ta zube ƙasa dan ji yake kamar yay mata bugun mutuwa kozai huce daga abinda yakeji a halin yanzun. Sake miƙewa tai da gudu, Fitowarsu compound ɗin gidan yayi dai-dai da shigowar ƴan sandan cikin gidan.
        “Ku buɗe musu wuta gaba daya!!!”.
     A.G ya faɗa da ƙarfi.
        A razane wani a ciki ya bashi amsa da cewar, “Oga yarinyarfa data bamu information akai gata tare da shi”.
       “Har ita ku haɗa”.
A.G ya faɗa cikin karaji. Ba ƙaramin firgita Hibbah tayi ba. Ta waiga ta dubi Master take biyota ta kalli ƴan sandan da suka saita bindugu akansu da alamun cika umarnin ogansu zasuyi ta rumtse idanu da ƙarfi wasu zafafan hawayen nadama da dana sani na sakko mata. Ita data bada bayani akansa amma jami'in tsaron daya kamata ya bata kariya wajen kubutar da itane ke cewa a harbeta baida matsala. Wace irin ƙasa muke da ita kenan? Ahaka akeson wanda yaga mai laifi ya tona masa asiri.......
           Master da gaba ɗaya kamaninsa sun canja duk da bindugun da aka saitasu da shi ya nufota a guje da alamar son kubutar da ita saboda harsasai guda uku da jami'an suka harbo gaba ɗaya kanta sukayi gadan-gadan, sai ɗaya ne ya nufosa shiko ya saka bullet proof jacket a jikinsa, yasan duk tsiya harbin bazai samu makasrsa ba sai dai idan kwanansa ne ya ƙare yau. Yana gab da isowa gareta bullet ɗin ya shiga cikin kafarsa. Ƙaramar ƙara ya saki yana kaiwa duƙe, hanunsa ɗaya na zaro karamar bindigar jikinsa shima ya fara maida murtani. Wani irin zabura Hibbah tai babu shiri ta nufosa, hakan ya bata damar gocema bullets ɗin da suka nufo kanta har guda biyu ɗaya ya sake samun master a hannu.
        Hankalinta ya ƙara matuƙar tashi ganin shi ƙoƙarinsa ya bata kariya, yayinda waɗanda ya kamata su bata kariyar su son kasheta sukeyi. Sam rikicewa ya hanats gane fuskar dattijo A.G. Shiko Master ya gansa ne duk da yana ƙoƙarin ɓoye fuskarsa garesa. Duk da tasan ya mata nauyi haka ta miƙa hannu ta kamo nasa tana kuka. Haɗin kai ya bata ya miƙe shima da ƙyar cikin dakiya da dauriyarsa duk da tuni jini ya ɓalle masa ta ƙafa da hannu. Kasancewar suna gab da ƙofar falon suka sami nasarar afkawa ciki, Master ya danna security jin A.G ya bama yaransa damar bin bayansu duk da dama ba daina harbin sukaiba ALLAH dai ne ya bama su Master kariya bayan biyun da suka sameshi wasu basu sake taɓasu ba. Jakkarsa daya yasar a falon ya ɗauka, da sauri Hibbah ta amsa ta goya a bayanta. Ya fisgi hannunta cikin bama kansa ƙwarin gwiwa suka afka cikin kitchen ɗin suma. Sai dai su a tsakiyar kicin ɗin ya tsaya ya haye saman table ɗin wajen duk da jini dake kwaranya masa. Hannu ya miƙa ta

Please Login or Register in order to submit comment