Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda take ba. Musamman anan da take ganin sabon gida tunda ba'a taɓa zuwa da ita ta gani ba sanda ake ginin. Hasalima babu wanda ya taɓa sanar mata ita da Ammar. Sai da ga baya ne Ammar ɗin ya sani, suka kuma gargaɗesa da kar ya faɗama Hibbah.
          Shigowar Isma'il gidan kusan sha ɗaya na safe ne ya ɗan rage mata ƙulafucin son ganin Hibbahn. Bayan sun gaisa cike da girmamawa yay mata bangajiyar biki tare da yima anguna addu'ar zaman lafiya.
       Cike da kulawa a garesa Ummi da ke murmushi ta ce, “Saura kai Isma'il. Ya kamata ka nemo matar aure haka nan, dan shi aure cikar kamalace ta ɗan adam koda ace ya kasance mutumin banza ne. Idan kuma kaima irin nasu Usman ɗin zan maka to”.
       “Ƙayataccen murmushi ya saki da sake duƙar da kansa yana shafa ƙeya. Ummi karki damu kiyimin addu'a kawai”. Ya faɗa murya a tausashe saboda yanda yake jin Ummi matuƙa a rai kodan yana ƙishirwar mahaifiya.
        “Kullum addu'ar nan ita muke muku Isma'il. ALLAH ya cigaba da tsareku a duk inda kuke. Ya baku kariya da ga dukkan abun ƙi. Yay muku albarka ya baku ƴaƴa nagari da zasu kwatanta muku ƙyautatawar da kuke mana da biyayya”.
        Tasowa yay ya durƙusa gaban Ummi hawaye na ciko idanunsa, yay haɗiyesu da ƙyar yana faɗin, “Amin ya rabbi Ummi nagode”.
       Hannunta ta ɗora saman kansa ta shafa dan tsaf ta fahimci abinda yake buƙata kenan. Tausayi yake bata yaron har cikin rai, dan ta jima da nazartar yana matuƙar bege da ƙishirwar mahaifiya ne.
          “ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai albarka Ummi”.
      “Amin Isma'il”. Ta faɗa tana murmushi da sake shafa kansa har fararen haƙwaranta na bayyana.
           “Uhmm kaga ɗan gatan Ummi, ashe kana nan?”. Su yaya Abubakar da ke shigowa suka haɗa baki wajen faɗa suna kallon Isma'il ɗin. Ƙaramar dariya yayi da miƙewa da ga gaban Ummin ya koma inda ya taso. “Gara nai sauri na kwashi rabona kafin kuzo ai mana raba dai-dai.
       Usman da ke dariya ya ce, “Gaskiya Yaya Isma'il i'm jealous”.
       Dariya suka sanya gaba ɗayansu harda Ummi. Kafin su ƙaraso cikin ɗaki su mimmiƙa masa hannu har Yaya Muhammad. Da ga haka suka zauna aka dasa sabuwar hirar da ta sake ɗauke hankalin Ummi duk da kuwa zuciyar tata naga son ganin Hibbah ta shigo. Dan a cikin firarma sunayi suna sakko sunanta da rashin jinta suna dariya. Basu taso gaban Ummi ba sai ƙarfe ɗaya suka fita massallaci. Da ga nan Isma'il yay gaba su kuma suka koma cikin gidan da yake ya ƙara cika da dangin amare ƴan buɗar kai dan yau anguna zasu shiga ɗakunansu.

★★★★★

          A ɓangaren Abba kam barazanar rashin barci da ya fuskanta a daren jiya ce ta kaisa ga makara sai kusan takwas ya farka. Farkawar ma ba kaitsaye yayita ba masifar Momy ce da ta dawo asibiti ta gansa yana barci ta farkar da shi.
       “Yanzu wannan wane kalar rashin mutunci ne haka Hadiza? Ina tsaka da barci kizo ki tadani saboda rashin mutunci”.
        “Ni da kai a tantance mara mutuncin Abban Junaid. Yanzu dan ALLAH ko kunya bakaji ba ɗan ka namiji tilo na asibiti rai a hannun ALLAH amma kai kana nan kana barci hankali kwance. Bakaje kaga halin da yake a ciki ba baka ɗauki wani matakiba kuma ga wanda ya aikata masa. To sai ka miƙe dan Asiya da yaranta duk basa gidan nan. Yanda alamu ma suka nuna basu kwana ba a cikinsa”.
       “What?!”
Ya faɗa yana wantsalowa da ga gadon ƙirjinsa na wani irin bugawa. “Hadiza wace maganar banza ce wannan. Ita Asiyan idan ta fita anan gidan ubanwa zataje tunda bata ajiye kowa ba bayanan nan ɗin?”.
       “To waya san ko tana da wajen zuwan abu a duhu. Ga dai Hajiya mama can ta gama bincike ko ina na gidan nan ita da su Garba amma babu komai kama da su. Alamuma sun nuna dama da shirin hakan tare da su dan duk sun tattare kayansu masu muhimmanci da ga sashen”.
      “Kutuman bura'uban nan kayyasa”. Abba ya danna ashariya tamkar ɗan gidan maguzawa. Ita kanta Momy jin ashariyar tasa sai da ta zaro idanu waje. Hannu yasa ya ingijeta tare da fisgar sandarsa ya yo waje. Tun daga sama yake hango su kawu bello tsaye cirko-cirko a falo cike da tararrabi.
       Bai iya tanka musu ba tsabar rikicewar da yay ya fice da sassarfa duk da azabar da yakeji sabuwa ƙafarsa na masa.

      Tabbas babu alamar Ummi da ƴaƴanta a gidan. Wannan al'amari ya matuƙar hautsina kan Abba. Babu shiri ya shiga bige-bigen waya. Kafin ya tattara yabar gidan batare da ya tuna da ƙarin sallar asuba da ke a kansa ba bayan sallolin jiya da bai sauke ba har yanzun.
       Yayinda ya bar ƴan biki nata kace nace akan wannan al'amari. Harda masu yima ƴaƴan Ummi da ita kanta addu'ar tsiya suna mai goranta mata asalinta. Oho bama tasan sunai ba, su aiki ya sama😜👎🏻.

★★★★★

        A ɓangaren Hibbah kam Master na fita babu jimawa taji sallama a ƙofar ɗakin tare da knocking. Sam jikinta babu wani ƙarfi dan yunwa takeji matuƙa ga rashin ƙarfi. Hakan yasa tun bayan fitarsa bata motsa da ga inda take ba. Tunanin shine ya sake dawowa ya sakata harar ƙofar tamkar idanunta zasu faɗo. Ta kuma ƙiyin magana.
    Baba Saude dake tsaye ta sake ɗan buga ƙofar da ɗaga murya sosai wajen sallamar. Ɗan zabura Hibbah tayi jin muryar mace. Ta amsa da ƙoƙarin son tashi, sai dai kafinma ta tashin Baba Saude da taji an amsa mata harta shigo abinta ɗauke da tray.
     Wani irin daɗi ne ya tsarga zuciyar Hibbah ganin mace. Macen ma babba da zata iya kira uwa ko kaka. “Sannu mama” ta faɗa cikin girmamawa. Murmushi baba Saude tai mata tana ajiye trayn.
       “Yauwa ɗiyata sannu kinji. Yaya ƙarfin jikin naki?”.
       Da ɗan mamakin jin abinda tace Hibbah ta dubeta. Har zatai magana sai kuma ta fasa ta amsa da “Alhmdllh mama”.
     Baba Saude ta ce, “Masha ALLAH. ALLAH ya ƙara afuwa kinji. Babana yace ga abinci kici”.
      (Babana) Hibbah ta maimaita sunan a zuciyarta tana gyaɗama baba Saude kai batare data sani ba. Baba Saude da har cikin ranta kallon mara lafiya take ma Hibbah saboda yanayinta ta fice abinta ganin kamar batason hayaniyar.
     Jin ƙarar rufe ƙofar yasa Hibbah ɗan zabura tana ƙoƙarin dakatar da ita. Sai dai harta fice abinta. Kanta ta dafe tana cije lips nata dan takaici. Sai kuma ta duba trayn abincin da ƙamshinsa ya gauraye ɗakin tunkan ma ta buɗe. Cikinta ta shafa dan babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar abincin. Hakan yasata miƙewa ta nufi trayn da tunanin abincin kawai zataci ta samu ƙarfin yin tunani akan halin da take ciki a yanzun.
       Lafiyayyen abincine da ƙamshinsa kawai ya isa saka ma'abocin ganinsa kwaɗayin fara ci. Duk da zuciyarta na gargaɗarta da cewar kartaci na ɗan homo ne sai ta kasan daurewa saboda yunwa. Jikinta har ɓari yake ta haɗa ruwan tea duk da bai wani dameta ba ta fara sha. Dan tasan yanda yunwar nan ta cita shine kawai zata fara sha ta samu nutsuwa. Ai ko cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala wata irin zufa ta fara karyo mata. Yanda yake ratsa jijiyarta yasa dole sai da takai kwance na wasu ƴan mintuna. Sai da ya nutsu a cikin jikinta sannan ta sake miƙewa ta hau cin lafiyayyen breakfast ɗin shima. “Alhamdulillahi” ta faɗa a hankali jin uwar hanjinta ta ɗauka. Hakan ya sata miƙewa zuwa saman gadon ta sake kwanciya ƙananun zufa na cigaba da tsatstsafo mata.
           Idanu ta lumshe dan zuwa yanzun hankalinta ya fara dawowa jikinta. Sai kuma ƙwaƙwalwarta ta shiga kai kawon lissafi da tariyo abinda ya faru jiya akan bin bayan Abba da tayi. (Idan har lissafinta yayi dai-dai tun farko dama A.G da Abba tare suke. Da farko ta shiga rayuwar ƴan sanda a dalilin jefama masu power rider na'urar bibiya. A dalilin bincike da sukayi akanta suka gano ita ɗin wacece kuma ɗiyar wanene?. Ta wanann hanyar A.G yasan tana da alaƙa da Abba abokin shaiɗancinsa. Zata iya yuwuwa ya sanar masa komai da ya faru shine shi kuma yay amfani da wannan damar wajen saka A.G ya cigaba da amfani da ita wajen bata ayyukan Master da sukace yaronsu ne. Su kuma zasu dinga samun sirrin ƴan uwanta da Umminsu ta wanann hanyar suna musu illa da sunan suna bata kariya batare da sun fargaba.) “Tabbas babu tantama wannan lissafin nawa haka yake. Dan alamu ya nuna lokacin danai tracing wanann shu'umin shegen jami'in can ne ya sanar masa shiyyasa ya gudu. Shi kansa sun maidashi wawa suna amfani da shi da ƙuruciyarsa wajen gina kansu da wargazashi batare da ya sani ba. Wannan itace matsalar da *_MATASANMU_* suke fuskanta a wannan lokacin. Kuɗi da rashin aikinyine rauninsu. Azzaluman kuma sunda kuɗi da faɗa aji a hannunsu. Sai suke amfani da wannan faɗa ajin da kuɗin da matasan ke ƙishirwa su jawosu a jiki suna amfani da ƙuruciyarsu wajen sakasu zama ƴan ta'adda. Shima da alama wannan tarkon ya faɗa. Ya ALLAH!”. Ta kare maganar da dafe kanta da ya sara mata. Duk da sunce amfani suke da shi su gama mora su yadda dolene ta tonama guy ɗin nan asiri ma duniya shi da ubannin gidan nasa. Hakan na nufin kuma zata cigaba da zama a wajensa kafin burinta ya cika. Idan kuma ta zauna Yayunta da Umminta da ke a cikin tarkon su Abba fa?. Kuma hakan bazai yuwu ba sai ta kasance da su suma ta sanar musu gaskiyar shirinsa. Amma kuma wannan mutumin bazai bar hakan ta faru ba. Dan bai sato ta nan danta kuɓuta ba, saboda duk yana cikin shirin Abba na wargaza rayuwar ahalinta.
     Hannu ta kai ta share hawayen da suka silalo mata. Sai kuma ta tashi zaune tare da mikewa ta hau safa da marwa a cikin ɗakin. Lissafin Abba shine sai ƴaƴansa sun sami ciki zai fara salwantar da rayuwar yayyunta. Hakan na nufin dole tayi wani abu kafin nan da wata guda kenan. Babban abinda zatai kuma shine nutsuwa ta fahimci nan ɗin da aka kawota. Na biyu tai iya ƙoƙarinta na tattara bayanai akan wannan mutumin acikin wata guda ɗin nan shi da iyayen gidansa. Na uku duk tsanani karta bama kowa wannan binciken idan ta kammala sai Yaya Abubakar. Na huɗu duk yanda za'ai tayi ƙoƙarin yin magana da ko ɗaya da ga cikin ƴan uwanta ne. To amma ta yaya? Tunda shi da kansa ya tabbatar mata kozata shekara nemansu bazata samu ba.
    “Ya rabbi ka agajeni”. Ta faɗa tana dafe kanta. Cikin sauri ta ɗan zabura sai kuma ta saki murmushi saboda tuno wannan dattijuwar data kawo mata abinci. Tabbas inhar tana da waya da ita ya kamata tayi kiran. A kuma sirrance batare da tsohuwar ta sani ba.
       “Kenan zan sato wayar”. Ta faɗa a fili tana ƴar dariyar farin cikin zuwan mafita ta farko a gareta............✍


*_Alhamdulillahi na biya bashin wanann satin duka harma da ɗaya na wancan week ɗin. Asha hutun lahadi lahiya guys. Dangin su Master kuma zamu dawo da hirinmu ne ku kiyayemu😎😖😏🚶🏻_*


  
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI......_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*

*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*




*_Typing📲_*




*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_Chapter Twenty Six_*

...........Kai tsaye gidan A.G Abba ya nufa. Dan yasan yau ranar hutu ce baya a Station. Kasancewar basu cika haɗuwa a gidajensu ba yasa da ƙyar maigadin gidan A.G ya yarda yay masa sallama da shi. Dan ya kira wayarsa yafi a ƙirga amma bata shiga.
      Cikin takaici A.G ya fito, dan yayi zaman yin breakfast ne maigadi ya sanar masa zuwan baƙo. Turus yayi na ganin Abba. Sai dai tunda ya gansa babu damar komawa. Dole ya karaso inda yake yana faɗin, “Alhaji Halilu wai dama kai ne?”.
        Kai kawai Abba ya iya kaɗa masa. Kafin ya ce, “A.G akwai babbar matsala fa”.
     Saurin dakatar da shi A.G yay yana ɗan waige-waige. “Alhaji Halilu kayi haƙuri maganar nan bata nan bace. Inaga shigo ciki har motarka”.
    Babu musu Abba ya koma mota. Maigadi ya wangale masa gate bisa umarnin uban gidansa. Koda yay fakin ciki suka shige babban falon baƙi na gidan. A.G na niyyar fita domin kawo masa wani abin taɓawa Abban ya dakatar da shi.
        “A.G ci ko sha duk bashi bane a gabana yanzu, zo muyi magana.”
        “Humm Alhaji Halilu kanada ruɗani kai dai. Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka dan nasan tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi dai”.
      “A.G bazaka gane ba. Kai dai zauna kaji mike tafe da ni kawai.”
     Babu musu A.G ya koma ya zauna. Abba da ke a firgice ya fara masa bayani muryarsa har rawa take. “Asiya da ƴaƴanta sunbar gidan a daren jiya. Zuwa yanzu kuma bamusan ina suke ba. Hakan ya sake tabbatarmin yaron nan Master ne ya taimaka musu.......”
        Katsesa A.G yay da faɗin, “Master kuma Alhaji Halilu? Wai nikam miyasa duk kake zargin Master ne? Tayaya zai taimakesu miye ribarsa? Bayan kasani na sani akwai jiƙaƙiyar TAKUN SAƘA tsakaninsa da ƴarsu ma. To kai miye ma na damuwa da tafiyar tasu ne? Ba dama ta samu ba na hawa kan dukiyar da kake dako tsahon shekaru kaci karenka babu babbaka”.
         “A tunaninka kenan. Amma da ga abinda ya faru zuwa yau ka auna da hankalinka da ka fahimci inda alkiblar yaron nan ta dosa mana. A wannan karon da alama burgar banza kakeyi baya tare da kai. Dukiyar nan kuma da kake ganin zan cita cikin sauƙi bazata ciyu ba, koka manta duk kaddarorinsa sunayen ƴaƴansa ya sa matsayin next of kings. Wasu kuma sunan Asiyar ne ma”.
      “Hhhh wannan ganganne Halilu. A yanda na raini Master ni da abokan aikina bai isa zillemana ba ya maidamu abokan TAKUN SAƘAr sa. ai kaima kasan ko a gidan giya akwai babba. Maganar dukiya kuwa shi da kansa ma zai mana aikin”.
       “Ni duk ban musa maka kun raini master da wani blaa blaa ɗin zancenka ba. Yanzu so nake ka kirasa ka bigi cikinsa ko zamu san inda su Asiya suke. Sannan duk yanda za'ai inason ka samamin ma'aikacin banki da zaimin aikin sirri kuɗaɗen dake a accaunt ɗin Aliyu su dawo accaunt ɗina baki ɗaya, ka kuma saka shi Master ɗin nemo mana lauyan Aliyu duk inda yake”.
        “Maganar kiran Master ba damuwa bane, hakama zancen canja kuɗi zuwa accaunt ɗinka koshi zai iya mana wannan aikin.  Matsalar ɗaya ce ka yarda Master bazai zama shashasha akan mace ba. Macen ma ƙaramar yarinya kamar ɗiyar ɗan uwanka”.
         “To naji na yarda kirashi”. Abba ya faɗa badan ya yarda ɗin ba har cikin rai. Dan yanaji a jikinsa Hibbah tayi shu'umcin na mata akan Master. Sai dai shi A.G tsananin yardar da ya bama Master ɗinne yasa bai fahimtaba.
        “Kiran Master bazai yuwuba a yanzu. Amma zan tura masa saƙo da kansa zai biyo lokacin da yaga ya dace”.
     “To ashe kuwa yau a gidanka zan kwana”. Abba ya faɗa kansa tsaye.
     “Gidana kuma?”.
“Ƙwarai kuwa. Dan babu inda zanje saina tattauna da Master.
       “Humm Alhaji Halilu kai fa sam baka da haƙuri. Maganar zama anan bazai yuwuba. Kaje zan sameka gidan hutawarka. Kokuma mu haɗu wajen su Alhaji Alu”.
      “Kawai jeka shirya ina jiranka mu tafi tare”.
             Ɗan tsaki A.G yaja dan Abbah ya takura masa. sai dai babu yanda ya iya dole yace ya jirasan to.

       
★★★★★

            A ɓangaren Hibbah kam Shawarar data yankema zuciyarta ne ya sata sauka a gadon ta nufi toilet. Fuskarta ta wanko ta fito. ɗaukar tray ɗin kwanikan da tai breakfast tai ta fita da addu'ar ALLAH yasa yabar gidan. Babu inda ta sani amma tsabar ƙarfin hali yasata yarda zata gane. Taji matuƙar daɗin ganin baya falon, taɗan tsaya yima falon saman kallon tsaf. Sosai tsarinsa ya mata ƙyau. Ga wani ƙamshi mai daɗi da sanya zuciya nutsuwa na tashi duk da mayataccen ƙamshin turarensa na neman dannewa. Tunaninta ya bata baza'a samu kitchen anan ba, dan haka ta nufi downstairs ɗin kai tsaye.
        Tunda ta fara tako staps ɗin su Adam dake zaune a dining suna breakfast suka ɗago kusan a tare. Hibbah da ke sakkowa tayi ɗan turus ganin matasan samari kusan bakwai. (Su kuma waɗan nan fa?) tai tambayar a zuciyarta. Kai tsaye zuciyarta ta sake ayyana mata (Kin manta minene aikin mai gidan, ba dole kiga maza ba tare da shi). Tsaki taja a ƙasan maƙoshi tana ɓata fuska. Akan laɓɓanta tace, “Asararru”. Tana cigaba da sakkowa.
        Suko su Habib tuni sun maida kawunansu ƙasa tun kallo guda da sukai mata. Tana sakkowa step ɗin ƙarshe suka haɗa baki wajen faɗin, “Barka da safiya aunty”.
       “Aunty?!” ta faɗa tana kallonsu cikin ware idanu. Sai kuma ta turo baki, “Kujimin mutane dan ALLAH. Rusa-rusa daku zaku wani kirani aunty wannan ai zagi ne”.
        “Tofa ga mai gayya mai aiki, Kunga wata zuƙeƙiyar halitta.
Cewar Salis a hankali.
    Zungurinsa Zaidu yayi cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Karkai maganar banza matar babban yaya ce, akwai tazarar taku”.
     “A gafarceni wlhy suɓutar baki ce”.
      Baba Saude da ke zaune da ga can falo tana murmushi ta ce, “Kinga manta da waɗan nan shaƙiyyan ɗiyata. Keda baki da lafiya ai da baki fitoba kinma barsu zanzo na ɗauka.
       Sai da Hibbah ta ɗan harari su Musbahu da murguɗa baki duk da bawai jin mi suke faɗa tayi ba sannan ta maida dubanta ga baba Saude tana sakin murmushi. “A'a babu komai mama. Ai naji sauƙi Alhmdllhi. Inane kitchen ɗin?”
       Cikin jin daɗin wayewar kan yarinyar da ko alamar baƙunta babu tattare da ita ta nuna mata hanyar kitchen. Kan Hibbah tsaye ta nufi kitchen ɗin kuwa. Komai ƙal fes tamkar ba girki aka kammala a cikinsa ba. Ganin hakan yasa Hibbah ajiye kwanikan a wajen wanke-wanke ta fara yunƙurin wankewa.
      Motsin wanke-wanken natane ya saka Baba Saude shigowa. “Ya ALLAHU ƴar nan inake ina wanke-wanke kina fama da kanki. Ki barsa su Habibu zasuzo su wanke idan sun gama shiritar cin abin nasu”.
        (Uhm ai da yake ƴan daudu ne) Hibbah ta ayyana a ranta. A fili kuma sai tai ɗan murmushi. Karki damu mama zan wanke kawai. Ina maza ina wanke-wanke banda dai gidan naku a haguggunce yake”.
      Baba saude da ba fahimtar ina Hibban ta dosa tai ba tai ƴar dariya da faɗin, “Taɓ. Ai indai waɗan canne komai yi suke har girki. Babana ya musu horon tarbiya mai ƙyau ai. Sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi”.
        Ɗan kallonta Hibbah tayi danjin abinda ta faɗa. Sai kuma ta saki guntun murmushi. “Mama iyayensu dai, shi da ya samesu da ga sama ai ba'ace tarbiyyarsa ba”.
       “To ƴar nan ai shine iyayen nasu. Dan dukansu da kike gani nan shi yay wahala da su tun daga gidan marayu, yawancinsu ma tun suna jarirai. Tarbiyarsa ce, horansa ne. Shine uwa a garesu shine kuma uba. Shine dangi. Ai samun mutum irin babana a wannan zamanin abune mai matuƙar wahalar gaske. ALLAH dai ya saka masa da alkairi ya cigaba da dafama rayuwarsa.”
        Karon farko da Hibbah tai sagade tana kallon Mama Sauden. Dan ba karamin dukan zuciyarta zancen yayi ba. Sai kuma tunawa da fasikancin da su Abba ke aikatawa da shi da tai yasata juyawa tana taɓe baki. A ranta tace (dan ya taimakesu shine kuma ya ajiyesu yana ɓata musu rayuwa kenan. ALLAH ya saka musu).
        Baba Saude da bata fahimci abinda Hibbah tai ba ta cigaba da bata labarin ƙoƙarin Master da jarumtarsa akan su Khalid na tsayama rayuwarsu har suka sami ingantaccen karatu a fanin islama da boko. Hibbah dai gyaɗa kai kawai take, dan zancen wani na shiga wani na fitane kawai. Ita duk wannan tarin alkairin nasa bawai gani take ba sam. Tsiyar da suke aikatawa da su Abba ta goge mata duk wannan farin nasa baƙi ya maye gurbinsa.
      Sai dai cikin son bugar cikin Baba Sauden sai catai “Uhm lallai yaci sunan nasa Muhammad Shuraim”.
         Baba Saude tai ƴar dariya da faɗin, “Wai ƴar nan kinko iya faɗar sunan. Ni wlhy wahala yake min sunan nan nasa na larabawa. Shiyyasa nafi ganema kiransa da baba na saboda asalin sunan sa”.
      Gaban Hibbah ne ya faɗi. Kenan sunansa ne Muhammad Shuraim ɗin? Da sauri ta juyo tana duban baba Saude. “Oh mama bayan Muhammad Shuraim ɗin yana da wani sunan yanka ashe?”.
        Baki Baba Saude ta buɗe zata bama Hibbah amsa Habib ya shigo kitchen ɗin wuff tamkar an jehoshi. Waya ya mikama Baba Sauden. “Baba Master na magana”.
         Cike da farin ciki Baba Saude ta amsa wayar takai kunnenta da faɗin, “Alo babana”.
     Batare da Hibbah tasan mi ake faɗa da ga can ba taga Baba Saude na gyaɗa kai da faɗin, “To to babu matsala babana sai a dafa maka. ALLAH ya dawo dakai lafiya”. Da ga haka ta mikama Habib wayar. A dai-dai nan kuma su Salis suka shigo ɗauke da kwanikan da sukaci abinci.
    Ganin Hibbah ke wanke-wanke suka zaro idanu waje. “Aunty da kanki? Rufa asirinmu kar boss yay mana walmakalufatu”.
     Cikin bata fuskar haushi biyu Hibbah ta juyo tana dubansu. “Malami kubar wani kirana da Aunty niba auntynku bace.”
         Dariya kawai sukayi batare da sunce mata komai ba. Sai ma Habib da ya sake faɗin, “Aunty kibar wanke-wanken zamuyi Please”.
     Harara ta dallara masa. Yay saurin ɗora hanunsa saman baki yana faɗin, “Na tuba”.
     Dauke kanta tai batare data tanka ba. Idris ya matsa tacan gefe yana tattare hanun rigarsa. Bara to na miki ɗauraya kawai. Banza tai masa ta cigaba da wanke kwanikan a cikin kumfar data ƙara ganin sun ƙaro kwanikan. Wannan taruwar tasu a kitchen ɗin ya hanata jin ɗayan sunan na Master. Hakan kuma ba karamin takaici ya sakata ba shiyyasa ta haɗe fuska har suka kammala wanke-wanken bata sake kulasu ba. Sai sauraren hirarsu da Baba Saude da takeyi.

Please Login or Register in order to submit comment