Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsakkiyar p.o.p ɗin kicin ɗin ya burma sai ga ƙofa. Ya ɗan daka tsalle ya fisgo wani zare mai kama da tsani. Hannu ya miƙa mata ta ɗora nata sai faman wai-waige take jin ƴan sandan nata ƙoƙarin buɗe kofar falon. Ta tabbatar suka shigo kuwa sun gama yawone. Cak ya ɗagota duk da tanada nauyi.
        Da taimakonsa ta fara hawan zaren tsanin harta shige. Kafin shima ya fara hawa. Yana gab da shigewa suka sami nasarrar ɓalla ƙofar falon. Cikin sa'a ya ida shigewa da jan tsanin ya maido ƙofar ya rufo. Karan farko a tarihin rayuwa Hibbah a cikin zinc bisa gangancin da taso tafkama rayuwarsu. Wani ƙaton bututu kamar na ruwa suka samu cikin zinc ɗin, Master da ya fara ɗan galabaita saboda jinin dake fita a jikinsa dama ba isashen lafiyane da shi ba ya nuna mata cikin bututun da bata fitila ƴar karama mai shegen haske.
      Ɗan kwalin kanta ta cire tana kuka ta yagashi biyu, ƙafarsa ta ɗaure masa dai-dai wajen da bullet ɗin ya shiga. Sauran rabin ta ɗaure masa hannunsa. Cikin taune lips ya turata cikin bututun shima yabi bayanta dan yasan jinin da yake zubarwane zai nunama su A.G inda sukabi.
     Da rarrafe suka dinga kutsa kai cikin bututun batare da Hibbah tasan ƙarshemsa ba, balle inda suka dosa. Sunyi tafiyar da har sai da ta fara galabaita saboda ƙura sannan ta fara hango haske alamar karshensa kenan. Koda suka fito batasan inane nan ɗin ba. Amma dai gidane a wajen shima mai kyawun gaske. Ya fisgi hannunta ya danna cikin motar dake fake a wajen bayan ya yaye tanfol ɗin da aka rufeta da shi. Shima shiga yay yana jan numfashi da ƙyar dan idanunsa sun fara ganin jigari-jigari. A mamakinta sai gani tai ya danna wani abu gate ɗin ya buɗe kansa. Ya fita da motar da gudu daga gidan. Har daga nan tana iya jiyo jiniyar motocin yan sanda da karar harbe-harbe alamar gidan da suka baro kusa yake da wannan. Gudu yake tsulawa na fitar hankali wanda dole motoci da napep ke basa hanya. Masu zagi nayi masu kiransa ɗan giya nayi. Baimasan sunai ba. Dan bai tsaya ba sai a wata anguwa. Motar taga ya faka a wani dan lungu ya fita. Batare da yayi magana ba itama ya zagayo ya fisgota. Key wani mai shushaina dake a lungun zaune shi kaɗai yana gugar takalma ya jeho masa. Ya cafe dajan hannunta suka sake shiga wata motar, yayinda tunkan su fice a lungun ta hango mai shushaina ɗin nan na rufe waccan motar da tamfol.
         Wani irin tsoransa ne ya tsargama Hibbah. Ta kafesa da ido cike da alamar tambayoyi sai dai babu damar yinsu. Yanzu kam ta cikin anguwanni ya dinga bi da su har suka sake zuwa wani layi sukai canjin mota, anan ko motar kawai suka samu sai mai tallan rake a gefe can shi kaɗai. Sai da ya shiga motar ne ya yafito mai tallan raken yana cizar leɓe. da gudu mai rake ya turo Wheelbarrow ɗinsa zuwa inda suke. “Rake na ɗari uku”.
    Master ya faɗa da ƙyar yana lumshe ido.
      Raken mai rake ya ɗebo ya zuba a leda. Ya turo kansa ta Window ɗin motar yana ajiye keys a cinyar master. “Gida mai lamba takwas, anguwar bauranya”.
     Komai masbaiceba yaja motar suka bar wajen. Gaba ɗaya hibbah ta mutu a zaune a karo na biyu, kallonsa kawai take kamar gunkiya har suka iso anguwar da mai raken taji ya faɗa. horn yayi maigadi yay saurin wangale masa gate ya danna hancin motar. Gaba ɗaya su Salis dake tsaye sunata faman kaikawo a compound gidan mai sashe biyu sukayo inda yay fakin. Hakama baba saude dake can zaune goye da Sharifat ta mike da sauri duk da batasan ainahin abinda ke faruwa ba. Kawai dai su Habib sunje sun taho da itane acan L.E street batare da sun mata bayanin komai ba.
     Kusan gaba dayansu suka rufu akansa. Yayinda wasu a cikinsu harsun fara kuka ganin yanda ya samu harbi. Ga jikinsa harya fara saki saboda jinin da ya zubar. Da taimakonsu suka nufi sashen da ke a hannun dama suna shartar hawaye. Yayinda Hibbah wani irin nadama ke sake shiga bargonta, dan itama kukan da taga su Habib nayine ya sake tayar mata da hankali.
     Kanta baba saude tayo ta kamata itama tana tambayarta miya faru?  Jikin baba saude ta faɗa tana girgiza kanta hawaye na kwarara mata. Sai kuma tai saurin barin jikin baba sauden tabi bayan su Adam. Itama Baba sauden bayansu tabi jikinta sai rawa yake ganin jikin Master duk jini.

        A falon suka zaunar da shi bisa wata kujera mara tudu mai laushin tsiya. Cikin sauri Musbahu ya dakko First aid box ɗin daya hango can gefe. Cikin sauri Khalid ya kai tsugunne ya fara warware dan kwalin hibbah data daura masa. Yayinda Idris ke kwance na hannun shi kuma. Cikin rumtse ido Khalid ya zuba masa ruwan magani akan wajen. Wata wahalalliyar ƙara Master ya saki yana sake damƙe hannun Zaidu dake gefensa. Khalid na kuka yasa wani ƙarfe cikin ramin ya fisgo bullet ɗin. Baki kawai Master ya datse da azabar ƙarfi. Tashi Khalid yay ya koma wajen hanun, yayinda Habib ya duka gaban kafar ya cigaba da treating ɗinta. Acan ma Khalid ya cire bullet ɗin hannun, ganin Habib bai gama treating ƙafar ba sai shi ya cigaba dana hannun.
         Tunda aka cire bullets ɗin wani irin zufa ke ketoma Master akowacce hudar gashinsa. Yayinda yaketa faman sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da suka kammala tsaf suka goge jinin da duk ya bata ko'ina sannan ya buɗe idanunsa da sauri saboda abinda yazo masa a rai yanzun nan.
          “Ya ALLAH! Akwai matsala, akwai matsala!!”.
     Ya shiga faɗa yana jujjuya kansa. Hankali tashe su Salis ke tambayarsa wace irin matsala kuma?.   
        Bai iya basu amsa ba, sai wayar da ke a jikinsa ya laluba da sauri yana duban su Adam. Cikin wani yare da ko Baba saude bata taɓa ji Mastern yayi ba yayma su Adam magana. Cikin sauri suka nufi hanyar fita a falon suna amsa masa da girmamawa. Su biyar suka fice aka bar Idris da Khalid kawai.
         Da ido yayma Idris maganar da su kaɗai suke fahimtar yarensa ta hakan. Idris ya jinjina masa kai da duban baba Saude da har yanzu take sharar hawaye.
         “Baba muje na kaiki ki huta ko? Karki damu komai yayi dai-dai insha ALLAHU ”.
     Badan baba Saude taso ba tabisa ɗauke da Sharifat dake barci a bayanta. Dan tunda ta fasa kuka sanda su Habib ke shiga gida suna ce mata tafito saita lallaɓata tai barci lokacin da suka shigo mota, koda suka iso gidan kuma saita goyata da gyalenta.
        Kuka sosai Hibbah keyi wanda ke sake hasala zuciyar Master. Sai dai da yake yanzu hankalinsa nakan wani abu daban yasa ya shareta. Sai da yaji ta cigaba da cika masa kunne ne ya daka matsawar da ba ita kadai ba hatta da Khalid sai da ya zabura.
      Idan baki bar min wannan garshekan kukan ba saina daddage kanki da bullets a gidan nan!!. Kuma ki tashi min anan kafin na hambaraki a ƙasa kanki ya bugi tiles ɗin nan!!”.
        Da gudu ta miƙe tabi bayan su baba saude. Dan yanzu kam ta tabbatar ada ba Master ta sani ba yanzu ne taga ainahin Master ganin idonta ba labari ba. Gaba ɗaya idanunsa sun koma na ainahin tsohon bahagon zaki da babu abinda ya sani sai farauta. Idanunsa kai kace aman wuta zasuyi saboda tsabar jan da suka koma.
             Kansa ya dafe da faɗin, “Ina ji kamar na kashe yarinyar nan a yau na manta da shafin rayuwarta a tarihina.”
        Sosai tausayinsa ya sake ɗarsuwa a zuciyar Khalid. Ya tabbatar yau Hibbah ta ballo ruwa na gaske wanda batasan harda aikin taimakon ahalinta suka fita ba. Mastern su baya kuka sai domin tausayin al'umma. duk haɗarin da zakaga ya jefa kansa a cikin domin taimakon wanine. Kullum wahala yake da mutane batare da sun san manufarsa ba. Kowa kallon ɗan ta'adda takadari yake masa. Hatsabibi shu'umi ɓarawo. Amma hakan bayasa ya sare daga aikinsa duk da waɗanda yake dan su ɗin ko 1% basu fahimcesa ba.............✍


*_Asirin da xoxo taimin yau ya warware🙄😏🚶🏻😖_*



TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI......_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*

*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 *_Typing📲_*




*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_Chapter Thirty Five_*

..........Yaran A.G sun gama bincike ko ina babu Master da Hibbah a gidan. Sai da ga ƙarshe A.G ya farga da bin jinin da Master ya dinga zubarwa har cikin kitchen. Yay tsam yana auna inda jinin ya tsaya ya kuma zuba da yawa.
     “John!”.
Ya kira sunan ɗaya da ga cikin yaran nasa cikin da ka tsawa. A guje sukazo. Batare da yayi magana ba ya nuna musu p.o.p yana zaro waya aljihu. Cikin ƙanƙanin lokaci suma suka shige cikin p.o.p ɗin. Koda suka shiga suma ta cikin bututun sukabi suna sanar masa abinda suka fahimta. Sai da suka ɓilla har ta wancan gidan sannan suka sanar masa ta waya.
        Wasu yaran ya bari anan ya fito ta cikin layin, gida uku ne tsakanin gidan da inda su Master suka zauna.
       “Lallai guy ɗin nan ya cika matsiyaci shu'umi. Kaga shege kamar wani kurege ta ko'ina fasa hanyoyi yake.”
      Ɗaya da ga cikin yaran A.G ya faɗa rai a ɓace. Komai A.G bai iya cewa ba. Dan zuciyarsa tabbas tana gab da fashewa a cikin ƙirjinsa. Jin shigowar wasu ɓangarori na jami'an tsaro cikin layin ya sakashi fita. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ma baki ɗaya ta gama hargitsewa. Bakaji da ganin komai sai jami'an tsaro da ƴan jaridu. Kowa burinsa yaji wani abu da ga bakin su A.G da suka fara zuwa wajen. Sai dai ina komai ya kasa fita da ga bakin A.G. da ga ƙarshe ma zare jikinsa yay ya baro anguwar saboda kiran da Alhajin Mande yay masa akan ya maza yazo inda suke tunda zancen guduwar master harta sake bazuwa cikin ƙanƙanin lokaci.

         Gaba ɗayansu sun hallara ne a gidan hutun Dr Sufi, duk da kuwa kiraye-kirayen wayoyi da suketa samu daban-daban akan neman tabbacin kuɗaɗen da akace Master ya wawasar musu. R.D na zaune yana rusar kuka kamar ƙaramin yaro shi da Alhaji Sallau. A.G na shigowa R.D ya miƙe ya nufesa cikin rawar jiki.
      “A.G an kamashi?”.
A.G da shima kusan kan nasa so yake ya juye ya girgiza masa kai.
       Kuka R.D ya sake fashewa da shi saboda tsabar tashin hankalin da yake a ciki. “A.G ya nakasta min rayuwa ya yasheni matsiyacin nan. Naira dubu hamsin kawai ya barmin a accaunt tsinannen......”
         “Kowa ma abinda ya bar masa kenan R.D. yanzu ba lokacin zaman kuka bane ko jajantama juna. Lokacine na himmar cimma rayuwarsa dan baiyi nisa ba. A yanzu haka na baro cikin gidan da yake ne saboda kiran da kukaimin. Amma na bar yarana duk da kuwa ya gudu. Yarinyar nan ta wajen Halilu ne ta tona asiri. Amma abinda ya bani mamaki da ga ƙarshe bayan mun tarfasu a cikin gidan duk da abinda tai masa shine ya ringa bata kariya daga harbin dana saka ai musu, sai shi harbin yayta sama shi a dole jarumi”
       “Dan ALLAH da gaske kun harbeshi!!”. Engineer yay maganar tamkar wani zararre. Dan alamu ma sun fara nuna kamar notin kan nasa ya fara kwancewa shima fiye da nasu R.D ɗin”.
      A.G ya kaɗa masa kai cikin tabbatarwa. “Tabbas mun harbesa. Sai dai harbin duk ya samesa inda bazai mutu ba.......”
      Cikin katse A.G Alhajin Mande yace, “Idan matsiyacin yaron nan ya mutu yanzu to ai muma mun mutu A.G. dolene yaƙinmu ya kasance na dawowar dukiyarmu hannunmu harma da wadda muka sakashi ya tara. Kafin mu walakanta rayuwarsa da duk ma wanda ya shafesa. Tunda har ya bama yarinyar kariyar hakan na nufin yana sonta kenan, dan nidai nasan baida imanin da zai kareta batare da soyayya ba.......”
         “So! Kuma? Kai gaskiya bana tunanin haka”.
   Cewar Dr Sufi cikin kokwanto.
           Tsaki Alhaji Sallau yaja da faɗin. “Dr Sufi kana mamakin wacece mace. Duk wani shaiɗanci da kake ganin matsiyacin yaron nan ya iya bazai saka ya kasa shiga kaidin mace ba. Ai ni tun randa akace ya ruguza auren ƴaƴan halilu nakeji a raina akwai wata a ƙasa. Shiyyasa ban zauna ba sai da na gano inda ƴan uwan yarinyar suka koma yanzu haka. Jiya-jiya aka kawomin bayanan dama a meeting na weekend ɗin nan naso kawo zancen dan mu masa tarko da su koda yaso aikata cutarmu, to ashe shaiɗanin ya gama shirya mana tsaf.
      A zabure A.G yace, “Da gaske ka samo inda suke?”.
     “Tabbas kuwa bar kokwanto A.G”.
Alhaji Sallau ya faɗa yana zaro waya a jikinsa.
     Wata shegiyar dariya A.G ya sanya da faɗin, “Tabbas Master kazo hannu dan uban babanka. Dan da yarinyar zamuyi amfani kazo garemu. Yanda take son ahalinta muna damƙesu kaima bazata barka ka shaƙi numfashi lafiya ba”.
     Fahimtar gaskiyar zancen da manufarsa ya sakasu jin wani ɗan karen sanyi na ratsa zukatansu. A take suka gama aminta da zuciyarsu cewar Master yazo hannu ya gama kawai. Dan Alhaji Sallau na gama basu adireshin su Ummi A.G ya kira ya ransa ya basu Umarnin binsu Yaya Umar har wajen ayyukansu a kamo masa. Hakama su Ummi.

(Tabbas Master kayi gaskiya akwai matsala🙆🏻🤦🏻🚶🏻)

__________________________

            Ummi da surukanta gaba ɗaya na a sashenta suna hira kamar yanda suka saba zuwa mata a kowanne safiya su ɗan zauna bayan fitar mazajensu, matar Yaya Umar ta fara ganin abinda ke faruwa awayar hannunta. Cikin waro idanu waje take faɗin, “Tabɗi jan, shahararren ɓarawon nan yau ma ya sake guma uwar satar datafi ta kowanne lokaci a tarihi”.
      Kusan a tare suka haɗa baki wajen tambayar waye?.
     “Master mana. Gashi bbc ma har sun saki”.
     Ta basu amsa kanta tsaye. Gaban Ummi ne ya faɗi dan a saninta dai na yanzu Isma'il shine Master. Kafin ta samu damar cewa wani abu Zahidah tace, “To bara mu kunna television”. Batare da jiran amsaba ta dauka remote ta kunna. Cikin sa'a kuwa ana tsaka da nuna rahoton ne dan kowanne gidan tv da na redio shine latest labarinsu na yanzu-yanzun nan da gaba ɗaya ya hargitsa ƙasar dama duniya. Dan anyi itifaƙin bai taɓa mahaukacin sata makamancin na wannan karon ba ma. Ya yashe asusu goma sha ɗaya a lokaci guda. Asusai kuma masu matuƙar nauyi na kuma manyan mutane da ake matuƙar ganin mutuncinsu cikin dattijan ƙasa. Harda jami'an tsaron da ke farautar rayuwarsa.
       Hankalin Ummi bai gama tashi ba sai da taji sabon rahoton da ɗan jaridar ke faɗa cewar a yanzu haka labari yazo musu wata matashiyar budurwa da Master yay garkuwa da ita  ta samu nasarar tona masa a siri ta hanyar kiran wayar ƴan sanda ta sanar musu a inda ya ɓoyeta. Sun sami labari kuma a majiya mai ƙarfi a yanzu haka ƴan sanda sun zagaye gidan inda suke da tabbacin Master yana ciki shima.
     Karkarwa jikin Ummi ya farayi, ta ɗauka waya da nufin kiran layin yaya Abubakar taji tabbacin zancen, sai ga ƴan sanda sun faɗo musu su huɗu. A razane duk suka miƙe da ɗaga da yin surrender, dan bindigu duk suka nuna musu.
     “Duk ku fita!!”.
Ɗaya da ga cikin ƴan sandan ya faɗa cikin daka tsawa. ALLAH ya taimakesu dukansu akwai hijjabai a jikinsu har Ummin, dan basu iya zuwa su zauna mata babu hijjab ko mayafi. kamar yanda itama idan suka shigo bata taɓa zama cikinsu babu mayafi ko hijjab tare da ita. Haka suka fita cikin matsanancin tashin hankalin rashin sanin laifinsu. Da ga su sai wayoyin hannunsu. A cikin mota guda aka zuba su Ummi. suma ƴan sandan suka shiga tasu.

★★★★

      A ɓangaren su Yaya Muhammad ma suna wajen ayyukansu cikin tashin hankalin abinda suka gani a labaran daketa yawo a wayoyin hannu. Zukatansu sun gama basu Hibbah ce ta tonama Isma'il asiri. Duk da suma har yanzu basu san ainahin gaskiyar dalilinsa na aikata waɗan nan abubuwanba hakan bai musu daɗi ba. A daren shekaran jiya yake sanar musu akwai aikin da yake kanyi yanzu haka, yana kammalawa zai kawo Hibbahr ta gaida Ummi. Sai gashi koma ya hargitse tunda gashi suma ta shafesu.
      Dan batare da sun san nasu laifin ba suma dai sai ga ƴan sanda sunzo kamasu suma. Hatta da Yaya Abubakar da ke matsayin jami'in tsaro suna tsaka da kai kawo akan abinda ke faruwar kawai akazo akai arresting ɗinsa. Ƴan sandan dake station ɗinsu sun so ɗaga hankalinsu Yaya Abubakar ɗin ya kwantar musu da hankali yabi jami'an farin kayan da sukazo kamasan. Dan shima a ransa yanason zuwa kodan wani bincike.

★★★★★

         Kusan awa ɗaya kenan da barin su Habib gidan amma babu su babu labarinsu. Gaba ɗaya su Idris sun kasa zaune sun kasa tsaye. Sai kaiwa da kawowa suke a falon hankalinsu nakan wayoyinsu suna ganin abinda ke faruwa ta yanar gizo. Basu kunna tv bane saboda fahimtar gaba ɗaya Master baya buƙatar wata hayaniya. Dan tun korar Hibbah da yay a wajen ya maida idanunsa ya lumshe kai kace barci yakeyi. Koda Khalid ma ya tambayesa ko zaisha tea bai tanka ba dan yayi zurfi matuƙa a tunani.

       “What!!?”
Khalid dake rike da waya a hannu ya ambata yana mikewa tsaye a zabure cikin alamun gigita. Idris dake zaune gefensa yay saurin dubansa da faɗin. “Lafiya?”.
      “Inafa lafiya!, wai kaji mi matsiyacin A.G ɗin nan ke faɗama ƴan jarida kuwa akan alaƙar Master da aunty queen?!”.
        Hannunsa ya janye a kansa da ke masa tsananin ciyo, tare da buɗe lumsassun idanun ya sauke akan  Khalid da yay maganar. Kafin Idris dake ƙoƙarin buɗe baki yay magana yayi ɗin ya katsesu.
       Cikin muryarsa da ke a shaƙe na mura da tsananin ɓacin rai ya ce, “Television”.
       Kai Khalid ya jinjina masa da ajiye wayar hannunsa ya ɗauka remote ɗin tv ya kuna. Hakan kuwa yayi dai-dai da hasko A.G da ke bayani ga ƴan jarida, da alama yabar wajen su alhajin Mande ya koma office.
            “Tabbas har yanzu babu wanda yasan fuskarsa. Saboda yana amfani da facemasks iri daban-daban idan zai aikata laifinsa. Misali kamar yau an samu fuska biyu da yaje banki da ita, inda mutane da yawa suka tabbatar da sun gansa a matsayin alhajin ƙauye daya shigo bankin tankar baisan komai ba. Sai a yanzu ne kowa ya fahimci shine yay shigar ɓurtu tamkar yanda ya saba. Tabbas mun bibiyesa adalilin yarinyarsa kuma har mun sami nasarar harbinsa. Sai dai yanzu-yanzun nan muke samun labari a majiya mai ƙarfi dangane da ita yarinyar da tai kiran ta sanar da inda yake. matarsa ce, soyayya sukai kuma kafin aure. Hakan na nufin ahalinta sun san wanene shi suka ɗauketa suka bashi. Dan a yanzu haka zancen da nake muku harda ƙanin mahaifin ita yarinyar dake dauke da ɗawainiyarsu tun suna kanana saboda mahaifinsu ya rasu suka yashema asusu. Kenan hakan na nufin harda ita a cikin tawagar tasa.......”
        “Amma yallaɓai idan harda ita mi zaisa ta tona masa asiri?”.
    Wani yayma A.G tambayar cikin katsalandan na ƴan jarida.
        A.G yaja numfashi, “Muma wannan itace tambayar da muke nemawa amsa. Sai dai a ganina kawai sun shirya mana wasa da hankaline kawai sai suka rufta..”
       “Kenan dama kuna bibiyar al'amuransa a koda yaushe?”.
     “Sosai ma kuwa. Dan bamu da burin daya wuce mu kamashi. Shiyyasa dare da rana muke tsaye tuƙuru akan dukkan motsinsa...”
       “Amma yaya akai duk da jajircewar nan taku harya samu nasarar yashe asusan bankunanku kuma a yau?”.
      A.G ya kafe ɗan jaridan da yay tambayar da ido har saurayin ya tsargu. Ganin sauran ƴan jaridar na juyawa suna kallon saurayin saboda kallon da yake masa ya sashi basarwa yana sakin murmushi. “Tambaya mai ƙyau. Sai dai zan bada amsartane anan gaba bawai yanzu ba...”
       “Tabbas zaka amsata kuwa! Koda su sun manta ni Isma'il Aliyu Hikima zan sakaka ka amsata!!”.
      Master ya faɗa cikin wani irin kaushin murya da ɗaci yana sake maida idanunsa ya rufe. A haka ya cigaba da sauraren A.G daya ke tabbatarma da duniya a yanzu haka sun sami nasarar tattaro ahalin Hibbah, dan sune kaɗai zasu iya faɗama duniya a inda master yake a yanzu.
       Cikin tashin hankali su Khalid ke duban Master daya maida idanunsa ya rufe. Sun san sarai yana jin A.G ɗin shima. “Innalillahi.... Boss akwai matsala kenan”.
     Bai motsaba, bai kuma tanka ba duk da yaji abinda Idris ɗin yace. sai dai faman taunar lip ɗinsa yake na kasa alamar zuciyarsa na masa zafi da ciwo. Dan tsabar yanda yake taunar lip ɗin har ya koma jaa sosai.
         Shigowar baba saude da ke faɗa musu Hibbah fa babu lafiya jikinta sai rawa yake ga kuma zazzaɓi ya sakashi buɗe idanu a hankali. Kallon baba Sauden kawai yakeyi yana cizar lip. Su Idris kam duk sun zabura kan baba saude suna tambayarta miya sameta? ba yanzu ta shigaba lafiya lau.
     “Gaskiya inaga firgici ne. Da alama bata taɓa gamo da makamancin wannan tashin hankalin ba. Tunda ta shiga fa sai surutai takeyi. Maida idanun yay ya lumshe, gaba ɗaya kansa ciwo yake masa tamkar zai buga.
       Jin yaƙi cewa komai yasa sukai tsuru-tsuru suna kallonsa. Musamman ma su Khalid. Ganin haka yada Baba Saude takowa ta ƙaraso inda yake. Cikin taushin murya tace, “Babana ko jikin ne?”.
     Idanunsa ya sake buɗewa, yanda suka sake kaɗawa sukai ja har kamar suna ƙyallin ruwa sai ka ɗauka kuka yake. Yay ɗan murmushi mai ciwo yana girgizama baba sauden kansa.
       “Naji sauƙi baba, kice mata tazo nan”. Yay maganar acan ƙasan maƙoshi cikin rauni da ɗacin dake addabar zuciyarsa da maƙoshinsa.
        Baba saude da gaba ɗaya itama zuciyarta ta ƙara raunana. Ta kaɗa masa kai da juyawa ta koma. Babu jimawa kuwa sai gata ta fito riƙe da hannun Hibbah da kallo ɗaya zakai mata ta baka matuƙar tausayi. Duk ta susuce ta firgice. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta sun kumburo matuƙa, jijiyoyin kanta duk sun miƙe ruɗu-ruɗu. Duk da haushinta da su Khalid ke ji sai

Please Login or Register in order to submit comment