Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiya bama Hajiya kadai ba duka yan gidan basu da mutunci ko kadan har abokiyar zamanta kuwa.
A zaman ta da Hajiya da kuma kishiyarta yarda suke abunsu babu kishi ko kadan na zahiri, ga kuma duk lokacin da suke zance suna ganinta zasuyi shiru,ranar da sukayi Baki taje kaima su lemo sunayin zance tana shigowa,sukayi shiru, bakin ne suka ce ita wannan bata sallama idan zata shigo wuri ne ko yaya? Hajiyar ce tace' ai kurma ce bata magana,
Dayar bakuwar tace ai irinsh ake so a masu aiki,kinga ba Wanda zaiji sirrin ki,tana fita kuwa ta labe, taji abinda suke cewa,tundaga ranar take yawan Shiga dakin Hajiyar,itama Hajiya tadena wani boye boye ko ta ganta,sai wani yare da takeyi abinta, hankali kwance.

Yau aiki take Amma ba kamar kullum ba bayanta ke ciwo sosai,alamun period dinga na gab,babban tashin hankalin ta be wuce yarda bata da pad ba,kuma ita ba magana ba, kuma bata Jin akwai wani shago a kusa,dauriya kawai takeyi, yau ko turaren da take sawa ma bata saba,so kawai take taje ta kwanta,ko zata ji saukin abinda take ji, saukowa takeyi ahankali hannunta rike da bucket din da tayi mopping, sai da taje tsakiyar steps din ta rike bayanta da dayan hannunta dayan kuma tana rike da bucket din tana cikin tafiya sai ji tayi tayi tuntube da bucket rufe ido kawai tayi tana jinran taji zafin fadowar da zatayi,Amma Jin kamar an riketa kuma ga wani sanyayyen turare da take ji yasata bude ido fes ta sauke idan ta cikin nasa, dukda ba rokota yayi ba,tokareta yayi da hannunsa Duka biyu,
Kallanshi kawai take kamar yarda shima ita yake kallo, babban abinda yasa bata fita kenan bata so su hadu,dukda ita tana yawan ganinshi a garden , shikuma tunani yake me yakawota gidan su,mekuma takeyi? Dukda kallan da sukeyiwa juna hakan be Hana su wannan tunanin ba, yayinda zuciyar ta ta fara abnormal bugawa sakamakon wani yanayi da ta tsinci kanta aciki,shima hakanne a wurinsa, sun jima suna kallan juna yayin da idan ta kifta ido sai yaji an tafi da numfashin sau dubu, Baiki su dawwama a haka ba,

Hajiya ce fa fito don zuwa kitchen ta hado Breakfast ganin su ahaka yasata ta saki wani ihu tare da salati,

tace' na Shiga uku ni Hafsatu mezan gani??
Banaifu Kaine rungume da mace haka a kirjinka, lahawwala wala quwwata, jama'a ku fito kuga abinda idona yake gane min,

Shikuwa bema San sanda ya rungumo ta din ba abinda yasani kawai yasa hannu ya tokareta kar ta fadi Amma yanzu sai ganinta yayi a Kan kirginsa, ganin da Hajiya tamasa baisa yasaketa ba,kuma be kalli hajiyan ba sabida wani irin haushi da yaji ,ta katse masa Jin dadin sa,ita kuwa Ummusalma kunyan duniya ce ta rufe ta,tunda tazo duniya wannan kadan ne zatace taji kunya,Amma bata wani nuna ba a fuska, expression din be nuna ba, sai motsi take alamar yasake ta,Amma ko gezau beyi ba sai ma Kara kallan ta yake yarda take motsi da baki,da kuma kifkifta ido sai abin ya bashi dariya, kawai yayi murmushi.

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt=: _Akanji magana_


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023




13

Ihun da tayi ne da kuma salati yasa kowa fitowa daga daki,suka fito Suma cirko cirko sukayi suna kallan ikon Allah,

Hajiya tace' Alhaji nasha fada maka daman yaran nan ga abinda yakeyi,to har masu aiki ma be ragaw ba,bin matan ma shi har cikin gidan ma zai zo ya maka Shi,
Anty(kishiyarta) ta karbe da

cewa' indai sune na Saba kamasu da wannan shegiyar ifrituwar kazama kurma kawai,

Wani irin tafasa zuciyar Daddy keyi,wai dansa? Shi mamaki yake,gashi kuma yau har cikin gidan sa, yana rungume da yarinya,kuma ganinsu besa yasake ta ba,
Cikin wata irin murya ta bacin rai Daddy

yace' sai nace kasaketa zaka sake ta ne?

Murmushin dake Kan fuskar sa be bace ba,don maganar ma da sukayi zai iya cewa beji ba,sai da daddy yayi magana, ita kuwa taji komai,kuma tayi mamaki furucin Anty akanta, Ashe itama ta tsane ta haka?
Ahankali ya saketa Yana cigaba da kallanta,kamar jira take kuwa yana sakinta tana fara tafiya sai dai ko taku daya batayi ba,santsin ruwan da tayi tuntube da bucket din ya zube, ya debe ta zata fadi don saura kiris taje kasa yai sauri ya tarota wannan Karon har sai da ya tsugunna kadan,
Sakinta yayi ya gyara Mata tsayuwa,Tana Shirin tafiya Hajiya ta Kira

tace' ina kuma zakije,kurmar yar iska,shegiya munafika, kina kurma kina iskanci,.dawo nan bangama dake ba
Daddy yace' ke tsaya zuciyar Shi kawai tafasa take,duk abinda ake fada masa Akan dansa yau ya Kara tabbatar wa dakansa hakanne.
Bema iya magana ba tsabar takaici kawai ya juya ya koma ciki,
Ummusalma kanta a kasa ta dawo ta tsugunna ,Anty

tace' wannan yarinyar mekama da wancan Dan karuwar( Mus'ab) dole daman ai halinsu ya zo daya ai,
Dago Kai tayi ta kalleta sai kuma taji Aneesa na cewa ai itace babbar yar iska ba'a yar iska mace sai namiji, idan bakiyi wasaba wallahi zai Kai ya baro musha suna abin mu, yafada tana shigewa,
Tasan inda maganar su ta dosa,maimakon ma taji haushi,sai wani murmushi takaici da tayi,iya zuciyar ta,abinda yake damun Tama kadai ya isheta, Abu kadai ne ya bata haushi a zaginsu cewa glip( mus'ab) Dan karuwa, ahaka suka kare Mata zagin kare dangi,suka koma daki,itama tashi tayi, ahankali ta juyo don tafiya sai dai kuma ganinshi da tayi rike da moper Yana mopping wurin don har ya goge Kan step din Yana goge kasan parlourn abin ya bata mamaki,saukowa tayi ta nufi inda yake,ta Mika hannu don ta karba,maimakon ya bata Saima jeho Mata tambaya da yayi

yace' me yasa kika Zama kurma? Bayan nasan ba haka bane?
Kallo daya tamasa ta dauke Kai,takara kawo hannunta zata amsa mopper ya kauda ita daga wurin,

Yace' tambayanki nake, ko sai na Kara maimaita wa?
Gani kawai yayi tayi hanyar kitchen don tafiya dakinta, sororo ya tsaya Yana kallanta, har ta shige kitchen Sannan ya bi bayanta, Amma be ganta ba,ta fice ta Shiga dakinta, iska ya fesar tare da shapo kansa daya cika da suma. Kawai yabi ta kitchen din shima don komawa dakin Shi,
Tana Shiga ta ji wayanta Yana vibrating,maman Sadiq ce, Kara daurewa tayi ta dauka, suka gaisa sannan maman Sadiq

tace' Wai sai yaushe zaki zo ne?

Tace' Nima bansan ranar zuwa na ba?

To yanzu ya za'ayi da furnitures din gidan?

Nima bansan yaza'ayi ba kawai abinda yadace kiyi,Zan turo maki kudin,in yaso sai ki bayar a sayo,

Ba sai na bayar ba,daman zamuje siyan kayan kanwata dake jigawa kuma gobe zata zo sai muje tare da ita,a hada da nakin kawai,

To shikenan hakan ma yayi daidai, Amma yaushe ne tafiyar taki?

Maybe Nanda sati,kuma idan naje gaskiya Zan jima don na Dade banje gida don zanfi wata daya de,abubuwa dayawa banana duk anyi su.

Daga Mata Kai kawai tayi,sai kace Wanda ta tambaya, daga haka sukayi sallama ta takashe wayanta,
Jakarta ta duba ta dauko numbern mai adaidaita tasaka,ta Danna Kira,

Da sallama yadaga, tafada masa itace, sannan,

tace' akan aikin Dana baka ne, ina so Ka Zama shiri koda yaushe,nanda kwana uku nake so a kammala komai, kaji ai?

Angama Hajiya yarda kika ce hakan za'ayi, amma Hajiya don Allah karki cutar dasu, kinga......

Cikin sauri da masifa ta katseshi tace' sau nawa Zan fada maka, nace Zan cutar da sune? Bade na baka kudin ka ba? Kuma lokacin kana San kudin ai,Ka amsa yanzu nasan har anyi aikin da za'ayiwa mahaifiyar taka,
Hajiya kiyi hakuri ya kashe wayar,
Wayar tabi da kallo tana Jan tsaki, kudi ta dauko tayi rubutu a takarda ta zura hijab ta fita, tana bude kofar taji zata fita taji an wani irin fusgota, an jata zuwa can cikin garden,bayan bishiyar mangwaro, dukda ta tsorata bakadan ba da irin fizgar da aka Mata Amma bata nuna ba ko kadan, gaban tane yake faduwa bakan ba, Amma ko kadan hakan be nuna ba ajikinta bare kuma fuskar ta ba, ganin shine ma yasata Dan samun relief, Amma mamaki fuzgar da yamata take,me tayi masa, bata Gama tunanin ba taji

yace' Wacece ke? Mekika zo kiyi gidan nan?

Kallan Shi kawai take tana karantar yanayinsa,har zuciyar shi yake maganar,kuma yarda yake maganar zakasan zuciyar Shi a tafashe take, ganin iri kallan da take masa yasashi,

cewa' ohh nima pretending din zaki min??
Murmushin takaicin gefen Baki yayi, ya dafa hannun sa a gefen bishiyar ya matso daf da ita,

yace' Wacece ke???
Shiru tamasa ba amsa, wani iri haushi ne ya Kara kamashi babu abinda yake bashi haushi irin kayiwa mutum magana kuma yana jinka yayi maka shiru,dukda shima Yana share mutane bai zaci hakan suke ji ba sai yau, cikin wata irin muryan bacin rai da kuma tsawa,

yace' nace Wacece ke??

Dukda ta tsorata da tsawan da yayi Mata hakan be sa tsoro bayyana a tattare da ita ba, ganin zai Kara wata maganar yasata buge hannun sa da ya dafe bishaya dashi ta ture Shi daga gabanta,yayi baya kadan,Yana kallanta itama Shi take kallo,cikin muryan bacin rai itama tayi magana,

tace' mutumin da besan Wanene shiba,shine yake tambayar wani wanene Shi. Kallanta yayi na irin kina da hankali kuwa?
Tayi folding hannayenta a kirjinta ta Jingina da bishiyar taci gaba da cewa' ehh baka San wanene Kai ba,nasan koda an tambayeka wanene kai,zaka ce Kai Dane ga Adam Dan Lami na taso a Spain wurin Kanwar mahaifina, nayi karatuna tundaga kan primary har zuwa masters, duk shekara ina zuwa gida don yin hutun karshen shekara, ina yayu biyu Wanda muke sa'anni dasu biyu sai kannai shida, sannan zaka ce duk shekara idan na dawo gida babu me nuna min so da kauna hakan yasa Nima bana San su, Bama jituwa da su kokadan,daga nan kuma kace Ina da Kannan da nake so Mus'ab da Mas'ud,bazaka ce ba yan gida ku bane, sannan sai kace,watarana kwatsam Anty ummi ta rasu sanadin ciwon zuciyan da ba'a San dashiba, daga nan sai kace na koma na karasa masters dina sannan na dawo ban Kara komawa ba, koda nazo daman ina aiki da wani campany sai na nemi da na bude nawa,har na sai fili Amma Mahaifina ya siyar dashi daga karshe,baka damu ba,kacigaba da aikinka, daga nan kuma Ka koma Abuja saboda tsabar gaskiyar ka a wurin aiki yasa aka shirya maka makirci shugaban aikin ya koreka,daga nan baka Kara samun aiki ba, kana zaune a gida ko Ka fita don samuwa saboda bakasan zaman gida,idan kafita baka dawowa sai dare daga nan kuma bakasan me aka shirya maka ba, mahaifinka yace kar Ka Kara fita idan ba masallaci ba,baka iya musu ba Ka hakura, daga nan kuma zakace sai wata yarinyar yar Kanwar Hajiya sa'ar Saima ta saka a gaba da cewan tana sanka. Sai Ka fara aikin gida, Amma ko abincin ci baka samu,Kai kuma ba gwanin girki ba bare Ka girka, dukda Daddy yana da Arziki sosai don siyasa ta karbeshi Yana Shirin Zama takaran deputy governor.

Ta sauke ajiyar zuciya ta gyara tsayuwarta ta kalle Shi tace' haka zaka ce ko ba haka ba??
Bata jira amsar Saba taci gaba dacewa", Ka taba tambayar Wacece mahaifiyar Ka? Ka taba tambayar ina mahaifiyarka? Kasan inda mahaifiyarka take??? Ko kuma ka taba tunanin mahaifiyarka?? Ka taba tambayar dangin mahaifiyarka?? Ko ance ta rasu ai tana da Yan uwa,idan batasan Yan uwanta ba, haka ta taso ta ganta ai tana da Marika,idan marikanta sun rasu ai tana da Yan uwan Marika,idan Suma Basu da Yan uwa suna da abokai idan masu da abokai suna da makwabta. Wannan kuma kasan bazai taba yi wuwa ba ace babu ko daya daga ciki. Bama wannan ba Ka taba tunanin Mene yayi sanadiyar ciwon zuciyan Anty ummi?? Ka taba tunani? The answer is capital NO,u don't know anything about your life,you don't know everything about your life!. U have to start thinking, before you start asking, u have to do so.

Kallanshi tayi tace' Idan ka samu cikakken wanene Kai inaga kana shirye ne da kasan Wacece Ummusalma Muhammad.

A Hannunshi ta soka papern tare da kudin tace' Ka siyo min, ka ajje min ta window,
Ta juya ta tafi.

Tunda ta fara zancen Shi ya Zama statue bambancin Shi da statue Shi Yana ji, zai iya cewa ma numfashin sa daukewa yayi,kunnensa ne kawai yake aiki ganinsa ma besan sanda ya dawo ba,sai da ganinsa ya dawo numfashin sa ma ya samu fitarwa, sai kuma ya rufe ido ya bude,ya kuma rufewa ya bude, jirin da yaji yana neman debansa yasa Shi Jan kafa Yana tafiya dakyar yazo dakin Shi yana zuwa kuwa ya zube a gado ya kulle idan Shi duk abinda ya faru ya fara masa yawo akansa ahankali yafara bin komai daki daki har sanda ta sakala masa kudi a hannunsa, bude idansa yayi da ya koma ja, wannan shine tashin hankali na biyu da ya taba Shiga sanadin wani.
A hankali ya fara tunanin rayuwar sa sanda ya bude ido ya ganshi tare da Anty ummi tana kuladashi, tun Yana karami shekara shida ya fara zuwa hutu Nigeria Amma Anty ummi bata zuwa, sai dai Shi yazo tare da mijinta, ko a lokacin idan yazo Daddyn Shi ke masa wanka ya shiryashi Hajiya bata kulashi, ba abinda take masa sai zagi, da bakar magana,Yana komawa Spain kuwa ya tambayi Anty ummi dama ba ita ta haifeshi ba? Alokacin tace masa mahaifiyarsa ta rasu,da rasuwar mahaifiyarsa ya taso a ransa, Amma kuma be taba mata addu'ah ba betaba neman hotanta ha ,besan ya 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ kamanin ta suke ba, be kuma taba tambayar Yan uwanta ba, To Meyasa???

Kulle Ido yayi ya bude,ya gyara kwanciyar sa, bashi da wata tambayar kuma,yasan da'ace Anty ummi na raye yasan tasan duk wannan tambayar idan ma bata San Duka ba to zatasan rabi da kwata. Besan sanda bacci ya dauke Shi ba a wurin. Be wani jima ba ya tashi saboda be Saba ba,Yana tashi yaga kudi da papern a wurin,har ya fara tambayar kansa na waye,sai kuma ya tuna, Kansa yaji ya Kara Sara masa tunawa da abinda ya faru dazu dazun nan,ajiyewa yayi yashiga toilet yayi wanka,ya Shirya cikin kananun Kaya sai sumar sa da ya taje Sam bayasan tara suma . Yana fita kuwa zaije a aske masa ita a masa gyaran fuska,amma yanzu bashi da wannan lokacin, har zai fita sai kuma ya dawo ganin kudin da ya ajiye akan mirror da zai Shiga wanka,dubu biyu ne sai kuma papern da ya ware ganin abinda ke jiki yasashi dafe Kai yasan zata bukata da gaggawa, da sauri ya fita, yaje wurin drivern gidan,yace ya bashi key, shagon kasan layinsu ya tsaya ya siya ya koma.


('('('('('('('('('
Ummusalma kuwa data tafi har zata Shiga daki sai kuma ta fasa ta shigo parlour ta dauko bucket din da mopper ta fita dashi waje sannan ta Shiga daki ko hijabin jikinta bata cire ba ta fada Kan katifa ta kwanta rufda ciki,Jin dadin kwanciyar dataji yasata rufe Ido,batasan lokacin da bacci yadauke taba, koda yazo Rasa hanyar da zai bata yayi kawai ya zuge windown dakinta,"wato bata rufe window" abinda yace Kenan, ya saka mata,hangota yayi tana bacci akan katifar ta,da'alama kuma baccin ya Mata dadi, har zai jefa ledar sai kuma yayi tunanin kar ya sameta ya katse mata baccinta,dawowa yayi ta kofar ya bude yashiga ya ajiye mata ledar a kusa da ita daga ganin tana gumi yasa Shi kallan fankar dakin,a kashe take,hakan yasa da zai fita ya kunna mata ya fice, Sai dai kuma Daddy da Hajiya dake zaune a garden sun hango Shi tun lokacin da yazo Amma Shi be lura da suba hankalin shi yayi gaba.

<<<<<<<<<<

Kimanin wata guda Kenan suna Kiran numbern Isiya driver Amma a kashe kuma gashi babu Wanda yasan gidan Shi bare ya kaisu,tun suna damuwa har suka zo suka saba, kullum suka Kira a kashe, bangaren Anty kuwa koda su Umma suka zo tas ta zayyane masu abinda ya faru, da kuma yarda zasu fara nemanta,sosai hankali su ya kwanta tawani bangaren, ahaka Suka bada goyon baya dari bisa dari, na ganin an nemota sai dai kuma rashin jin drivern yasa su yin jinkirtawa,amma babu Shi babu labarin sa, yau su yusseer suna gidan tun safe sun fara zuwa makaranta kuma dukan su course daya suke karanta mass comm, suna gidan su Ummu suna assignment kasancewar weekend ne lokacin, kowa da system agabansa Yana Mita musamman ummu da yaseer sun fi kowa mita shidai Yusuf sai dai kawai ya kallesu ya hararesu, Ummu ce

tace' yaya Yusuf don Allah dan bani hint yanda zanyi nawa assignment din ta fada tana masa murmushi yanda wai zai bata,
Ko kallo ma bata isheshiba yaseer

yace' indai yabaki nima sai yabani,ko kuma na kwafe naki na boye nakai nawa kinga ke sai dai ki samu katuwar CO kinsan beda mutunci malamin,yakarashe da dariya aikuwa kamar jira take yagama ta dauki pillown kujera ta maka masa,aikuwa shima ya dauka ya maka Mata daga nan kuwa aka suka tashi suka fara yar make make Kan kace me sun hargitsa parlourn sun ma ture center table din da center carpet wasu pillows din ma zip din ya bude duk sun zuzzube,
Yusuf ne ya kallesu ya cigaba da aikinsa, kwanan nan ya dena Shiga harkarsu, idan suna shirme ganin yake shi yanzu ya girma ya wuce wurin, daga karshe ma tashi yayi ya koma dining tare da kwashe masu system dinsu gudun kar su fasa suna hauka,

yaseer yace'wai bazaki dena ba? Naga ke kika fara kwada min kuma don na Rama?

Tace' ai Kai kayi lefi,kace wai sai zanci co sai dai Kai,kaban hakuri Zan dena kuma kace min Anty ummu kiyi hakuri tukun Zan dena...
Ai bata rufe Baki ba taji ya kwade mata Baki da remote,bai Kai ga magana ba itama ta dauki remote ta kwade masa kai,ai kuwa Shima ya dauka ya jefa Mata sai Akan uncle da yake shigowa ita kuma ta sun kuya,daga Shi har ita kamewa sukayi, ga remote din ya bare saboda Yana faduwa a kasa
AA kuwa da ya shigo da sallama yanajin Abu ya bigeshi yasa Shi yin shiru ya dafe goshin sa, da zafi amma ba can sosai ba remote ne bawani Abu ba dazai ji masa ciwo sosai, takaici ma yasa Shi kin yin magana kawai ya wuce ciki,suna ganin ya wuce ta kalle Shi

tace' kaga abinda ka ja ko?
Kinga abinda kika ja de,aike kika fara,zata Kara magana taji uncle yace' your knees on the ground,
Kallan kallo sukayi,rabansu da kneel down sun manta, sai yanzu za'ace suyi wani kneel down,
" Sai na Kara maimaitawa ne?
Kafin ma ya rufe baki suka durkusa kowa Yana hararen kowa,irin ai kai ka ja, suna nan har karfe tara, daman dare ne,gashi Basu ci abinci ba, sun zaci idan akayi Isha shikenan amma ganin anyi Isha andawo yace' su cigaba, Yaseer

yace' yaya,
Shiru ba amsa,kuma cewa yayi ,yaya, uncle? Uncle?
Namma shiru ganin anyi shuru aN kyaleshi yasa Shi yin shiru, itama,

tace' uncl, uncle, uncle,yaya?yaya?yaya de? Kaga fa dama shine yamin addu'ah wai sai na samu CO,shine fa kuma ya jefe ni da pillow daga nan kuma ya dauki remote ya wurgomin abaki dan nace ya bani hakuri, kuma shine fa da laifi.
Tana rufe Baki taji yace'" rest up your hands and close your eyes open your mouth,
Kallan juna sukayi cikin rada yaseer,

yace' kece kadai zakiyi,ai ke kikayi magana kika ja wa kanki,
Batayi magana ba tayi yarda aka ce Mata,Anty da ta fito tagansu

tace' tun kuna yara kuke bata min parlour yanzu ma kun girma baza ku barshi ba, wataran sai na sa dorina na Zane ku,bar ganin haka,tana me zama a kujera tana karewa parlournta kallo remote take nema don canza channel sai dai hango Shi da tayi a kasa wurin kofa kuma a bare yasata girgiza Kai kurum, taci gaba da kallan Indian ba wai don tana soba, Basu suka tashi ba sai goma kuma sai da suka gyara parlourn tas,har remote din sai da suka nade Shi da zare suka kulle wai sunyi gyara, yusuf kuwa yana zaune Yana dariyan sa kasa kasa Allah ya kaisu gobe zaiyi tsokana. Sai da suka ci abinci tukunna suka tafi gidan su.......

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt= _Akanji magana_



Not Edited
POST 2020
REPOST 2023



14

Washegari Monday da wuri suka biya suka dauki ummu sannan suka fita,suna tafiya,

tace' wani ba wanda zai koya min mota ne? Shikenan sai de na zuba ido kuna Jan mota nikuma ina kallo ko?

Yaseer yace' to da me zakiyi? baki Kai matsayin koyan mota ba sai kin cika 18,

Tace' ehhh Masha Allah imagine Kai Naga ka iya,kana 16 nikuma da nake 17 ban iya bako?

Yusuf dake driving yace' yarinya mu ai koya mukayi da Karan bani,idan kema zaki koya Tou,Amma da sharadin ke kadai zaki Shiga ki ja,ko yakace?

Yaseer yace' haka ne mana yaya, wazai Shiga tukin ganganci,

Yusuf cikin muryan ta idan tana magana

yace' uncle, uncle, uncle, yaya? Yaya? Yaya de? Kaga fa shine daman,

Rankwashin data sakar masa ne yasashi cewa" ouch ke da zafi fah,

Tace' daman ai nayi don kaji zafinne, mtsww
Ashe bakwa Sona daman?

Yaseer yace'laaa ni ina wannan saurayin naki dan level four, kuna waya dashi?

Tayi dariya tace' ni mantawa ma nake dashi wallahi,bafa number ta na bayar ba, numbern Inna na bayar kasan kuma Inna ba turanci take jiba shikuma be iya Hausa ba,kaga shikenan anyi run da come,
Amma Baki da mutunci wallahi,

Yusuf yace' wallahi kar ki bawa kowss numbern ki, taam nidai ba ruwana atoh,

Babu Wanda ya Kara magana har suka je suka je school din, parking sukayi inda suka saba,kamar kulluma yarda suke tafiya yauma hakan ce ummu a tsakiyar su,sukuma a gefen ta, Dukan idan Ka kallesu zaka ce bahaka suke ba,don a school basa magana ma da wasu,Basu da kawaye sai dai course mate, suna tafiya ummu ta matsa kusa da Yaseer,

tace' kaga in-law dinmu,tana jiran mu,
Besamu yayi magana ba amma yayi Mata alamar ya gani,saboda sun karaso,Sarai Yusuf yajita Amma be ko tanka musu ba,idan da sabo ya Saba da wannan yarinyar da ta makale masa dukda bata ce tana sanshi ba Amma alamar hakanne da ita, shikuma sai wani basarwa yake,sabida kwata kwata baya san dizgi ita kuma akwaita da wannan,
Ummu ce tace' Fati, yau ma kin rigamu zuwa Kenan, nikuwa Naga ranar da zamu rigaki zuwa,

Wacca aka Kira da fati tace' aikuwa bazaku taba rigani zuwa ba,kufa komai kukeyi nikuwa yimin ake,tafada suna Shiga lecture theatre din. Sai da suka Shiga suka tuna cewan basuyi assignment ba, shikuwa yusuf Ko a jikinsa, Dan yayi nasa,kuma Yana sane yaki tuna masu,to Allah yasa su lecturer baizo b. Sai 2 suka gama, sun fito don tafiya fati,

tace' idan Baku manta na tuna maku kunce zaku je gidanmu yau,kuma ummu ke kika fada,Dan haka tare zamu tafi,
Yusuf wani irin takaici da haushi suka darsu a zuciyar Shi, Sam bayasan wannan yarinyar amma ummu da Yaseer baza sudena kulata ba,mtswww yaja tsaki a zuciyar shi, badan bayasan karya alkawari ba da babu inda zashi shikam, suna tafiya har suka iso wurin motar tundaga nesa ya budeta suna zuwa kuwa yaga ta shiga gaba su kuma sun Shiga baya, wani murmushin yayi shima ya shiga, yana Shiga kuwa ya yatada motar, sai dai be tafi ba sai ma kifa kansa da yayi,ganin shiru shiru Basu tafi ba yasa Fati cewa Yaya lafiya kuwa?( Yarda suke cemasa a makaranta)
Girgiza Mata Kai yayi yace' kaina ke ciwo kice yaseer yazo ya ja,
Yaseer yaji abinda yace kuma yasan bawani ciwon Kai, kafin ma tayi magana ya fito ya bude kofar ta

yace' ki koma baya Zan ji dashi,
Bata yi musu ba ta koma baya kusa da ummu,itama umma da tasan kwannan zance batayi magana ba, suna Shiga kuwa yaja motar ya suka tafi,zoo road tace,bayan sunje kuwa ita ke nuna masa hanya har suka iso horn yayi aka bude masu gidan, parking yayi suka fito, parlour ta Shigar dasu,ta wuce kitchen ganin Ummusalma a kitchen din yasata cewa ke kurma yau ke kike abincin? Mai abincin? Bata nan ne?
Daga Mata Kai Ummusalma tayi

Please Login or Register in order to submit comment