Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta goce, kwafa yayi irin zamu hadu,

Binaif yace' sai ku karasa komai,

Daga nan aka cigaba da magana ba su suka tashi ba sai Azahar kitchen ta Shiga ta daura abinci sannan taje tayi sallama. Ta idar zata fito taga Ummu na Mata waya dauka tayi,

tace' ummu ya akayi?

Daga can ummu,
tace' Yaya me zan fada Mata kuma?

Ummusalma tace' abinda ya dace Shi zaki fada Mata,

Me Kenan?

Ya ilahi, ummu this time around you have do it by yourself,

Yaya bansan fah mezance ba,ni ba irin wannan abun na iya ba, kuma ni Banda kawa sai besties,

To ki tsaya da kyau Kiji, daga nan ya shiga fada Mata abinda ya dace,

Sannan sukayi sallama, Ummu tace' yawwa Bari naje na Mata dadin bakina, hahaha ho ni Ummusalma 'ya ga Faisal jikar Adamu, hehehe,

Yaseer dake zaune a kusa da ita yaja tsaki yace' mutum sai hauka,

Pillow ta dauka ta wurga masa,
tace' Wallahi Ka kiyaye ni, am I your mate? Ehh? Ina wasa dakai?

Hada hannunsa yayi yace' Ana aasfi ya Ummusalma,

Daure fuska tayi tace' dade ya fi, Ku tashi mu tafi,

Yusuf yace' yaushe su Anty zasu tafi ?

Tace' gobe zasu wuce,

Yace' gidan Antyn Ring road zaki koma?

Nima bansani ba,Amma de Zan tambayi Anty idan ta barni sai nadawo gidanku,tunda kace an sallamu Abba kaga Mama Kenan tana na sai Muke kwana da Yaya Sameera, Amma fah sai kun tayani tambayar ta,

Yaseer yace' zata ma Bari Insha Allah,

Tace' to ku tashi de mu tafi,

Tashi sukayi ta suka fita, gidana su yusuf suka tafi, tana zuwa taje ta Kara yiwa Abba sannu da jiki sannan ta wuce dakin Sameera, a kwance ta Ganta tayi rufda ciki idanta a rufe,
Ajiyar zuciya, ta sauke ta karasa Shiga dakin Bayan ta rufe, a bakin gado ta zauna,

tace' Ya Sameera Lafiya ?

Juyowa tayi ta gyara kwanciyar ta tace' ummu bansan ya zanyi ba? Nakasa samuwa kaina mafita,

Ummu tace' mafita Daya ce, ki canza SIM, ki watsar da duk wasu kawayen ki, ki fara sabuwar rayuwa kamar kowa,

Tashi zaune tayi tare da yin wani murmushi takaici,
tace' kina ganin Zan iya rayuwa kamar kowa? Bacin yanzu ma ya dena Kirana? Daman nike kiransa wani sa'ilin, to yanzu Nima nadena ganin ni Daya nake kidana, soyayyar sa kullum karuwa take yi a cikin zuciya ta, Ummu zuciya ta nauyi take min,

Ummu tace' kiyi hakuri Insha Allah komai zaiyi sauki kuma komai zai tafi daidai, trust me,

Tace' I should trust you?

Daga Mata Kai tayi alamar tabbatar wa, tace' Amma farko dole sai kin danni San da kike masa, kin fara sabuwar rayuwa hakan shine hanya mafi sauki da zamu cimma,

Zan gwada hakan,

Fatana kiyi yarda zuciyar ki ta fada maki,ba yarda kawaye suka fada maki ba,

Shiru tayi tana sauraren ta, tana kuma kallanta, ita kuma ummu tayi ta fada Mata kurarenta data yi a baya.


Washegari Binaif Yana zaune a office aka kawo masa sammaci ana neman sa a koto, dayake yasani kuma shima ya shirya sai kawai ya Kira lawyers dinsa guda biyu, Barrister Ibrahim da kuma Barrister Aliyu ya fada masu, sannan ya fito ya shiga motar sa ya wuce,

A kusan tare suka isa kotun sai Basu Shiga ba,Shi yashiga shima akayi komai da komai da ya kama ta sannan aka sa nan da Wednesday za'ayi Zama, zaman iya su ya su, daga su sai alkali da lauyoyin su sai su kuma su kadai za'ayi hakan,bayan sun fito,

Binaif ya dubi Abba yace' yanzu Alhaji haka ne daman abun? Me kake nufi Kenan ?

Murmushi yayi sosai mai kama dana dariya, sannan ya dafa Binaif, yace' yaro Kenan haka abin yake, sai mun hado ranar laraba,

Sannan yayi gaba zai tafi, dasauri Binaif ya sha gabansa ya Dan bubbuga kafadar Shi tare da yin wani murmushin da kana gani kasan na renin hankali ne,
yace' to what's done, chest.
Yayi gaba ya barshi ya wurin ya daskare, ya maimaita To what's done,chest.
Kenna Yana nufin what's done is done, you've made your bed, now lie in it. Mekenan?
Jiyayi zuciyar Shi tana bugawa da sauri, lawyern sa ne ya masa magana sannan suka tafi,

Binaif kuwa Yana zuwa ya Sanar da lawyers Dina da yarda akayi,
Barrister Ibrahim yace' Binaif inaga Zan Mika komai hannun Wani barrister Faisal, Dan lokacin nan Bana nan natafi umara, kuma bansan wannan casa din yasha ruwa dukda de muna da muhimman shaidu kuma mune zamuyi nasara Insha Allah, yau din nan Zan Kai masa komai,

Binaif yace' to shikenan Allah ya dawo da Kai lafiya, duk yarda kayi daidai ne,

Barrister Aliyu yace' Ashe shiyasa tun farko be bamu ba, Amma bakomai Allah ya Shiga tsananin mugu Dana gari, sun jima suna tattaunawa daga nan sukayi sallama har zai koma office sai kuma ya koma gida,

Yana zuwa yaga su mas'ud suna nan basu tafi ba.....



Page 47 yayi missing kuyi hakuri sai a hankali daman. Ina godiya sosai da yarda kuke nuna jin dadin ku Nagode kwarai >>>>>>>

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt =: _Akanji magana_

48


Suna parlour suna game ita wucewa yayi ya Shiga dakin ta ganin bata nan ya kwankwasa toilet namma shiru ya bude yaga bata nan, ya fito kallansu yayi,

yace'' ina take?

Mas'ud yayi saurin cewa'' ita wa?

" Mtsww ita mana"

Mus'ab yace'' tana can parlour"

Wucewa yayi tare da Galla masu harara, tana kwance tana latsa waya Akan kujera, kafar ta ya sauke ya zauna ya daura kafar aka cinyarsa, tashi zaune tayi,

tace'' yau ka dawo wuri'

Balla mata harara yayi yace'' ba sannu da zuwa fah''

Murmu      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  shi tayi tace'' Haba Mai gidana yi hakuri tou''

Dan yatsar kafarta yaja,tayi Kara, tace'' da zafi Mai gida"

Zai Kara ja,tayi sauri ta janye kafar ta, tana dariya,

Kumbura fuska yayi yace'' yau...

" Laifi nawa nayi?

Murmushi yayi sosai yace'' Ashe kin San laifin ki"

Tace'' amma Yana ganka kamar kana cikin farin ciki"

Gyarawa yayi ya zame ya kwanta ya daura kansa a cinyarta Yana kallanta, ita Shi take kallo, hannu tasa tafara shafa masa Sumar sa,Yana kallanta, tare da kamo hannun ta guda Daya ya rike, Yana wasa da hannun ya fada Mata yarda akayi, sai da ya gama,

Tace'' amma fah Faisal Adam sunan Baban Ummu ne"

Zaiyi magana wayar sa tayi Kara ganin barrister Ibrahim yasa Shi tashi zaune sannan ya daga,

Barrister yace'' kaga ma yanzu nan na Kira shi dayan barristern yake cemun zaiyi tafiya, kawai inaga Zan zauna,

Binaif yace'' kana ganin ba matsala?

Barrister yace'' babu Insha Allah shikenan sai anjima"

Komawa yayi ya kwanta yace'' yace ma barristern zaiyi tafiya"

" Zuwa dubo uncle a asibiti"

Yace'' sai yaushe mu zamuje?

"Sai ranar da kasa rana"

" Shikenan ba rana kenan"

" Um,um''

" Ina so zanje Spain daga can sai mu wuce mu dubo Shi"

" Kana so zaka je Spain, daga can sai mu wuce mu dubo Shi, damu Kenan za'aje kodani ni kadai"

Hancin yaja, yace'' kekam ko? Sai kace Wanda kika yi psychology"

Murmushi kawai tayi batayi magana ba, ganin Yana neman rufe Ido alamar Yana Jin dadin yarda take shafa masa Kai, ga kuma hannun ta da ya rike shima,

tace'' ita wannan Sumar ba'a askewa ne?

Buda idan yayi yace'' so nake na tara irin taki, Mai yawa, tama fita tsayi"

Ware ido tayi irin really, sai kuma abin ya bata dariya tace'' ina bazai yi ba ma"

" To kisa wasa ki gani"

"Haka kace"
Tace'' ina San fita makota mu gaisa da su"

Juyawa yayi daga kwanciyar yace'' to na hanane? Zaki iya zuwa ko yaushe ma idan Bana gida"

Tace'' Amma gaskiya ya kamata a cire wannu sumar, idan ba haka ba Zan Kai karar Ka wajen Umma"

Juyowa tare yin 'yar Dariya yace'' so kike kawai ki tada min rigima de, Umma bala'i ce"

"Umman kake cewa bala'i?

"Kina wasa da Umma, wannan tsohuwar idan ta kara girma da matsala''

Dariya tayi tace'' to nidai badani ba,Kai da ita kuma Zan fada Mata"

"Kiyi ta fada indai nine, daman tace na tsaneta, sanda taje spain"

"Taje spain?

"Kai tab sanda ciwon kafar ta yayi tsanani wani zuwa da Mijin Anty Ummi yayi gaida ita kawai suka taho tare sai ganinta mukayi, in fada maki, daga nan Ranar da tazo ranar ta fara yi mana jaraba,Anty ummi tace na zubo mata abinci, shikenan ta fara masifa wai Dan ta rena ta yaro ne zai zubo mata abinci eh,eh wannan ai reni ne, eh, bata da kunya, ehh rashin kunyar da takeyi ashe be barta ba, eh"

Dariya tayi Sosai tace" to meye na cewa eh din"

Yace'' Rasa abin fada tayi kuma tana San yin fadan, harda cewa nima na koma dangin nasara, ai Umma Idan tana fada kawai Kar ki kulata, Shikuma Mas'ud sunfi shiri da ita shine me fassara abinda nake cewa da Spainish, sabida wani abun Yana kari"

Tace'' indai chatty ne zai aikata abinda yafi haka ma"

" Meye naji ana cewa chatty me yayi? Wato gulma ta kuke me kuke cewa?

Karasa shigowa yayi ya zauna, a kujeran kusa da ita yace'' kina jin ina maki magana ko?

Tace'' labe Ka koma Kenan?

"Kin manta abinda yafi labe na koma ba labe ba"

" To meya kawo Ka?

" Daman maganar Sameera ce, nace kawai tunda ga su Yusuf nan suma zasu abinda zata yi,ko fiye ma da yarda zatayi, shine nace kawai a bar zancen ta hakan zaifi"

Za tayi magana Binaif ya matse hannunta dake cikin nasa kallan Shi tayi ya girgiza Mata Kai, alamar tayi shiru.

Tace'' to shikenan hakan ma zai yi,Ka barshi kawai"

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da fezar da iskar bakin sa, kallan sa kawai tayi ta girgiza kai,

Binaif yace'' sai me kuma,ina mus'ab"

" Gashi can Yana shiryawa wai zai tafi"

"Ina"

"Abuja"

Tace'' okay, sai yaushe kuma?

" Oho masa, idan yazo ki tambaye shi"

Binaif yace'' Kai kuma fah?

" Ni Spain nake so na koma,akwai aikin da zanyi Dana wa dana twinny idan na tafi Zan jima gaskiya"

" Yaushe zaka tafi?

" Nanda sati daya"

" Ka Gama aikin da aka saka?

" Wannan ai ya gamu, sai dai wani kuma"

Tashi zaune yayi yace'' inaga tare zamu tafi"

" Kaima zakaje, harda wannan abar za'aje?

Binaif yace'' eh harda Antyn ku zamu tafi"

Bata fuska yayi ya tashi yace'' har nafara Jin wani ama-mai wai Anty, sai anjima"

Ya karasa fita, tace'' kaima kace wata Anty? Taab kasan me kace ai"

Komawa yayi ya kwanta yace'' zamuje zata inga mi amor dinta yayi rayuwa ko?

" Ehh to kusan haka"

" Maybe mubi ta paris"

" Allah sarki sahr idan munje Dan Allah zan je gidan su, ban taba Kiran ta ba, gaskiya Bani da kirki"

" Damma ke kika fada ba wani ba''

" Eh naji din, Kira mana umma mu gaisa Banda numbern ta"

Wayar ya dauko yace'' nasan sai ta Gama zagin baba Usman tukunna"

Dariya kawai Ummusalma tayi, a speaker yasa wayar tana daga wa kuwa tace'' Assalamu Alaikum, nace batan hanya kayi? Ko kuma bashi ake bina aka kira ni a tuna min? Dan uban ka Adamu ba magana nake maka ba?

Yace'' Umma ina wuni?

" Ehh yayi baya da gudu be dawo ba"

" Haba Umma daga gaisu wa kuma?

" Naga na amsa eh? Kai kaji yaro Ka kiyaye ni, meye kuma aka kirani ?

" Daman nace yaushe zaki dawo nayi kewar ki sosai"

Washe Baki tayi tace'' kaji yaran arziki ai kwanan nan zan dawo ina zuwa sitiret sai gidan audushakuru bawan Allah Mai nema na"

Bashiri ya ta Shi zaune yace'' wanne gidan kenan?

" Kaji dan zakaraw'a kuma kake nema na? Baka so na dawo ko? To wallahi daga nan sai gidan ka, kaji dakyau, nace kaji ai"

Bata rai yayi yace'' daman ban Kira ba"

" Ba mutuwa zanyi ba,kuma ba yaushi zanji ba, daman ba Kira kake ba, munafikar matar Ka ce zata ce Ka kirani"

" Haba ummu me Mata ta tayi maki kuma"

" Ai wannan matar taka tayi ta sinne Kai wai ita kunya, idan tana yi sai kace wata tsohuwar munafikan da tayi sata aka kama haka take Kai Saima zatayi dariya a wani noke Kai ana taba abin hannu iwa sai kuma a danyi murmushi ace Kiki hmm hmm, wai dariya ce hakan"

Kallanta yayi da take kunshe dariya yace" umma Zan fada Mata fah"

" Dan uwar Ka safiya ai ba tsoranta nake ji ba"

" Gaskiya Umma kina da matsala"

" Nice gidan haya,nace nice gidan haya a matsala dan zakaraw'a Kai"

Yace'' kinga sai anjima nadena kuma kiranki"

"Hehehe audushakuru Kenan, daman ba Kira kake ba, Ka gaida dunkun Kumar matar ka idan kaga dama"

" Banida dankun Kumar Mata"

" Taje can ta sani maka"

Kashe wayar yayi yana bata fuska, kallanta yayi yaga ma dauriya take, yace'' duk ke kiga bada wannan shawarar ai, gashi nan zata dawo gidan ai"

Tace'' to ni menayi?

Pillow ya dauka ya wurga mata, tashi tayi daga kusa dashi tare da yi masa gwalo ta fita a guje, ya biyota yana kumbura fuska, a parlour taja ta tsaya ganin Mas'ud da Mus'ab yasa ta tsaya tana saisai ta dariyan ta,
Tace'' lafiya? Naga glip da jaka ina zuwa?

Mas'ud yace'' ciwon mantau ya kama ki"

Binaif da ya karaso ko kallan su beyi ba ya samu wuri ya zauna.

Mas'ud yace'' me kika masa?

"Nasani? Daga yin waya da Umma shikenan ya koma haka"

Mus'ab yace'' idan na biye ku baza Ku kaini airport din nan ba, sai nayi missing flight"

Tashi mas'ud yayi yacei kaga tashi na kaika a bamu key"

Tace'' Yana can parlourn"

Zuwa yayi ya dauko yace'' to muje''

Sallama ya masu suka wuce.

Zuwa tayi ta zauna a kusa dashi tace'' Mai gidanaaaaa,
Ta fada tana jingina da hannun sa ta daura kanta a kafadar sa,

Tace'' zo muje muyi girki"

Yace" sabida?

" Kaga wataran idan Bana nan shikuma sai Ka Shiga Ka girka abinka"

" Kuma ni barin ki zanyi kije wani wurin?

" Sosai ma,sai dai idan abu bai taso ba"

"Naji wannan, tashi muje muyi girkin to"

Tare suka Shiga kitchen suka fara aikin su, sunayi suna hira suna dariya abin su.




Yau za'ayi shari'a Dan haka da wuri kowa ya hallara a kotu Inda za'ayi daga su sai su babu wasu mutane,
Sun zauna kowa a zaune har alkali inda ya Gama Jin wannan karar ta Abba.

Alkali ya dubi Binaif yace'' Abdulshakur shin anyi haka?

Binaif cikin nutsuwa yace" anyi haka ya Mai girma Mai shari'a...



By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt =*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_


49


Alkali yace'' kana da ja a cikin?"

Yace'' ya Mai shari'a tabbas nasai company a hannun sa, sai dai kuma ba baka mu kayi dashi ba''

Alkali yace'' to meyasa kace anyi haka?''

Yace'' Nima bansani ba,haka kawai naji na fada Amma shine ya sayar min da companyn a hannun sa"

" Ina shaidu?"

Yace'' ga shaidu nan, barrister Ibrahim da Barrister Aliyu, dayan kuma be samu daman zuwa ba"

Kallan su alkali yayi yace'' a gaban Ku akayi?

Jinjina masa Kai sukayi, sannan barrister Ibrahim ya Dan rissina yace'' Anyi haka, sannan kuma shine yace bezo da takardun ba,sai gobe zai bayar"

Barrister Aliyu yace'' kuma shine ya bamu original din takardun wannan company"

Barrister Ibrahim yace'' kuma yanzu yazo yace besan zance ba? Bacin anyi haka ya bamu ya sallame mu? Akwai alamar tambaya anan ya Mai shari'a''

Shiru Mai Shari'a yayi yana nazarin abinda suka fada, barristern Abba yace'' ya me Shari'a wannan abinda suka fada ba haka bane, tunda sunce haka kawai su bada shida su hakan zai sa a gane waye Mai gaskiya"

Jinjina Kai alkali yayi kafin yace'' masu Kara da Wanda aka kawo karar ko sun zo da shaida?

Barrister Ibrahim yace'' ehh munzo d ita"

Sannan ya Mika masa, karba yayi ya duba, Suma su Abba suka Mika masa ya ansa ya duba, ya sosai, ya dago yace'' wannan takardun duka photocopy ne, kuma Yana yi da tsarin rubutun ba iri daya bane, hatta sighing din ba iri daya bane, ko Zan iya ganin original copy din?

Zufa ce ta fara ketowa Abba,da suka zo ai Basu ce masa su lawyers bane,kawai gaisawa sukayi, da sunce su lauyoyi ne da duk haka bata faru ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, alkali yace'' ina Original din?
Ya tambayi Abba Wanda hankalin sa gaba Daya Baya jikin sa,
Dakyar,

yace'' ya Mai girma Mai shari'a an barsu ai wannan sune original din"

Alkali ya bubi Binaif yace'' Kai fah,kana tare da naka shaidar?

Binaif yace'' eh ina tare da Shi"
Jakar sa ya bude ya dauko original copy din takardun na company ya mikawa alkali,karba yayi ya duba dakyau,

yace'' Zan iya karban wannan a matsayin sune na gaskiya, badan komai ba sai dan wannan takardun babu su yanzu''

Barrister Ibrahim yace'' kuma bugu da Kari ma shine ya bamu Shi"

Barristern Abba yace'' ya Mai shari'a wannan ba haka bane"

PA din Abba yace'' ya Mai shari'a tabbas mune muka basu, wannan takardun, a lokacin bamu taho dasu ba, sai washegari na Kai masa,nine na Bashi da hannun na, ina wurin ma ya bayar aka masa copy din shi"

Wani raza nannen, rikitaccan kallo Abba ya shiga yiwa PA din Shi besan sanda bakinsa ya furta "Inuwa??"

Ko kallansa PA beyi ba, ya make ya cigaba da bayani Sai da ya gama, Abba zaiyi magana,

Barrister Aliyu yace'' ya Mai shari'a wannan bashine Karo na farko da wannan bawan Allahn ya Saba yiba, ya yiwa mutane da yawa hakan, duk wani Wanda ya siyi kadarar Shi haka yake masa, haka a shaguna da dama dake cikin saban gari, da kuma kwari, du haka yayi musu"

Barrister Ibrahim yace'' sai sun zuba ma kudan kudin su, sun fara kasuwancin su, sai kawai yazo ya kwace, Basu da kudin Kai Kara, duka sun sa Shi a cikin kasuwan ci, kamar yarda Abdulshakur yayi,shima sai da ya bashi kudin companyn sa sannan yaga ya fara bunkasa yayi wannan aika aikar, a duba irin ta'asar da yakeyi da kuma cin zarafi,kazafi, karya, caca, Da yake yi a biwa mutane hakkin su, ya Mai shari'a"

PA yace'' ya Mai shari'a duk abinda suka fada, tare Dani ake aikata wa nine jagora"

Idan aka ce ga tashin hankalin da Abba yake ciki, bata lokaci ne, Dan wata irin bugawa kirgin sa keyi,ya rasa taka mai Mai zuciyar ce ke bugawa ko kuma de kirjinne ke bugawa?

Bekara tsinkewa da lamarin ba, sai da yaji, Barrister Aliyu ya kuma cewa'' sannan kuma ya Mai shari'a takardun gaskiya yake Basu Bana karya ba"

Mai shari'a wannan Abu ya daure masa Kai, Dan ya tabbatar da maganar su,

yace'' mun daga karar nan zuwa gobe, gobe azo min da mutanen da wannan abu ya faru da su"

Sannan ya tashi ya tafi, kowa tashi yayi Yana fitowa Banda Abba da lawyern sa, sai daga karshe suka fito kuma babu kowa, Abba na Shiga mota ya dafe kirjin sa, babu Abinda yafi komai ciwo irin cin amanar za Inuwa ya masa tambayar anan shine haka cin Amana take???

Ikon Allah!




('('('('('('('

Koda suka fito Basu tsaya ko ina ba sai company ana suka tsaya sukayi breakfast Sannan,

Binaif yace'' yanzu de ya kuke ganin za'ayi?''

Barrister Ibrahim yace'' Insha Allah Mune da nasara"

Barrister Aliyu yace'' komai ya kare daga gobe inaga, yanzu zai fara neman mutanen da ya siyarwa ne, yanzu ya za'ayi?"

Binaif yace'' ba damuwa, Allah ya kaimu goben"

Barrister Ibrahim yace'' Bari na wuce, sai dai idan mun hadu goben"

Sallama sukayi shima ya wuce,
Coffee ya hada ya tashi ya koma cikin office ya fara aiki, sannan ya Kira Felix shima sukayi magana Akan zasu wani satin daga nan kuma suka fara tsare tsaren su, Baya sunyi sallama ya jima Yana aiki har lokacin sallah sannan yayi sallah, ya dawo ya zauna zai cigaba kawai Ummusalma ta fado masa,ture aikin yayi ya kwashi kayan sa ya fice zuwa gida.

Ya fito Yana tafiya sukayi gware, dagowa yayi yaga dawa sukayi gware haka? Mas'ud yagani sai mulmula wurin da ya bige yakeyi Yana wani shishi da Baki kamar yasha yaji, besan sanda tsaki yayi escaping daga bakin sa ba,

Yace'' Baka ganin gaban Ka?"

Marairaice fuska yayi tare da yin kalar tausayi yace'' Taya Zan gani, waccan aljanar ta Bani sako wajen dubu wai na siyo mata nikuma har ga Allah na manta na farko ma bare na tuna"

Wani tsakin yaja yace'' kuma Ka Kira Ka tambayeta mana"

" Nine nan naki,sai da tace ta maimaita min, nace Allah ya sauwake ai ni din ba na karshe nakeyi a aji ba, ta kuma cewa to tunda sakon dayawa na rubuta maka, nace daman ai ita ta Saba zuwa ta karshe a aji shine na taho kuma wallahi gashi yanzu na manta komai, sakon kuma tun goma ta Bani Shi, yanzu kuma har Azahar tayi, bansan ya zanyi ba, please my sweet bb Ka taimaka min Dan Allah"

Binaif yayi wani murmushi na irin Ka Rena ni, sannan yace'' idan baza ka Kira ta ba, Nima bazan Kira ba,har wani tayi ta bin kanka ma? Kace wani meye meye,harza ce Mata dakikiya har sau biyu kuma kace na taimaka maka, you must be kidding"

Yasa kafa ya fara tafiya wurin motar Shi,bin Shi ya farayi Yana rukonsa,

" bb Haba bb ya zamuyi haka, wallahi bance Mata ba, kasan Allah kuwa, Haba Dan yaya naaa? matar Ka ce,ni kuma kauwata ce, yama za'ayi haka, please mana"

Sai da yaje wurin motar sa ya Shiga shima mas'ud din da sauri yaje ya Shiga ya zauna a gaba, Sai da ya tada motar ya fara tafiya, bedana masa magiya ba, Can,

Binaif yace'' da Sharadi"

" Mene sharadin? Ni indai baza ta Rena ni ba ai shikenan"

" Mtsww, kamin shiru"

" Nayi "

Waya ya dauko yayi dialing numbern ta,

Tana kwance tana tunanin inda Mas'ud ya tsaya gashi Baya picking call dinta, kawai tunanin ya tafi ko wani abun ne ya same Shi, ta dafa farar shinkafa batayi miya ba, tana jiran yadawo tayi miya, har tayi bacci ta farka ta sake wanka shiru, tana cikin tunanin taji karar wayarta ganin sun Binaif yasa ta daga,

tace'' Hello!

Yace'' ya gida?"

" Lafiya ba lafiya ba"

" Me yafaru?"

" Manta kawai,Ka kusa dawowa?"

"Ehh! Mezan taho maki da Shi?"

" Komai ma"

"Kamar me ?"

" Dayawa fa,kaga ko miya banyi na,na aiki Chatty har yanzu be dawo ba"

" Kyale wannan,waya ce maki da ana aikin Shi, sai yamma zaki ga sakon ki idan bakiyi sa'a bama ya manta, ya tafi wurin abokai, ko ya sami majalissa ya zauna kawai kimin message din abinda za'a"

" To shikenan nagode, sai Ka dawo, take care"

Kashewa tayi, Dan kallan mas'ud yayi yace'' sharadin shine zaka Mata hakuri"

A sukwane ya juyo ya kalli Binaif yace'' am..am..daman,shine sharadin? Imagine nine Zan bata hakuri"

Samun gefen hanya yayi yayi parking yace'' then go"

" Haba bb wasa fa nake, ai Zan bata ma, ai kauwata ce,aww yaya ta, Anty Ummusalma Walilin Inni, Zan bata ai"

" Better"

Message din tayi mas'ud yayi sauri ya bude yaga ni sai ca yace'' mtsww Ashe ma wannan abun ne, ai na tuna ma, harda wani ice cream a karshe baza' a siyo din ba "

Kallan Binaif yayi yaga driving kawai yake hankalin sa ma kamar ba a kunsa yake ba, ya kuma hade fuska irin ba wasa nan, yace'' bb to Ka saki fuskar mana,Naga de shan kunun ya kare tunda nace Zan bata hakuri"

Ko ehem bece masa ba, be daddara ba ya kuma cewa'' Haba de mutum sai kace ance gobe zai mutu? Sai cika yake Yana batsewa ai shikenan"

Be tanka Shi ba sai suka je kasuwa,yayi parking ya dauki wayar sa yace'' jeka siyo kayan ina nan ina jiran Ka, idan Ka dade nayi tafiya ta"

" To bani wayar na ga abinda za'a siyo"

" Nazaci Ka tuna,kana bata min lokaci"

Dakyar ya bashi yaje ya siyo abinda tace, sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment