Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karanta wata paper kafin tayi bacci haka idan tayi bacci ta tashi sai ta karanta ta,ko karatu zatayi tana karanta papern,ita kanta ta karanta papern ya kai sau ba adadi ita bataga amfanin karantawa ba,tunda indai haddacewa ne to ta tabbata ta haddace ta. Kuma tasan dole wata Rana zata bata labarin ta kamar yarda itama ta bata labarin ta ahaka.

<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß 

   _~Nigeria~_

Tunda suka dawo daga raka Ummusalma su yusseer suke kuka,sunki suci abinci,sunki cin komai, suna ma dakin ta Akan gadanta sun rungume juna sun tukuikuye wuri daya suna razgar kuka,mama tayi fadan tayi fadan ta gaji,Basu taba rabuwa da ita koda na kwana daya bane, da can ma dakin ta suke kwana daga baya ne da tayi rashin lafiya suka dena kwana,har dare suna dakin ko sallah basuyi ba bare su tashi suci abinci ,haka har bacci ya dauke su,idan sun farka suyi kukan su suyi bacci,ga yunwa na cinsu Amma inaaa baza su iya ci ba.
Bayan anyi Isha Mama ta fadawa Abba abinda ke faruwa,idan ransa yayi dubu to yabaci sosai ya fusata ya dau charger ya fita da ita sai dakin Ummusalma Yana zuwa lokacin bacci ya dauke su gashi daman sun galabaita,baiyi wata wata ba ya zula musu,wata rin zabura sukayi suka Kara rungeme juna maimakon su gudu inaaa sai suka Kara tukuikuyewa wuri guda takaici ya Kara kama Abba baisan sanda yayi ya tafakar suba suna ihu suna kuka,Mama na gefe don itakam daman abin nasu ya isheta,ahaka yayi ya gaji ya fita,mama ma ta bishi, dakyar Yusuf daman shine mai Dan wayo ya tashi ya tashi ya zauna ya janyo yaseer Yana rarrashinsa lemo ya tashi ya dauko masu da cake da Chocolate,yanaci yana bashi ahaka suka ci dayawa idan suncinye sai ya Kara masu har suka koshi,tashi yayi ya daura kan yaseer a cinyarsa

yace, "Yaya bazata taba dawowa ba".

Kallansa yaseer yayi

yace, "a,ah zata dawo dazu ta fada min cewar kar na fadawa kowa zata dawo ai".

"A,ah bazata dawo ba ta fada maka zata dawo ne Amma ba dawowa zatayi ba".

Cike da tausayi yake maganar kana ji kasan Yana cikin kunci ne,

"Taya kasan bazata dawo ba ita ta fada maka ne???

"Ba ita bace mama naji tanan fada".

"Yaushe?? 

Ya tambaya cike da zakuwa

"Dazu ta shigo kana bacci lokacin ta shigo tace, indai Ummusalma ce bazata taba dawowa garemu ba har abada kuma sai mun manta da ita a kwakwalwar mu".

Ya karashe da kwalla na zuba daga idonsa, yaseer ma kukan yake,

"shikenan yanzu bazata dawo ba?? Kana ganin zamu manta da ita ne?

Zamu manta da ita idan ta mana wani abun.

"Mezata mana to?

Kallanshi yayi yace, "ina abokin mu da ya manta da mamanshi? Ka tuna Shi?

Šaga masa Kai yayi yaci gaba yace, "to da ya faWa min abinda yasa ya manta da shima lokacin da ta tafi ta barshi kuka yayi tayi shine antyn Shi(matar babanshi) taba Shi wani abu yasha tace inji mamanshi tace a bashi yace tunda yasha shikenan be Kara tunawa da ita ba sai da ya gan maman tasa. To itama mama Shi zata bamu bazamu Kara tunawa da yaya ba".

Kuka yaseer yasa don ya tuna wahalar da abokin su yasha kafin yaga mamanshi kulluma idan suka biya islamiyya zasuga Yana aiki idan suka tambayeshi ina mamanshi sai yace' Shi baida mama.kuka sosai suka Kara sakawa daga karshe, Yusuf

yace, "idan mama ta bamu Abu kar mu karba kuma kar musha,idan ta bamu muce munsha,kuma mudena Zan can Yaya a gabansu ko???

Šaga masa Kai yaseer yayi ya rungume Shi,shima rungume Shi yayi

yace, "kanina yau bamuyi sallah ba,
Dago yayi ya kalle Shi kawai sai yayi dariya

yace,"Yayanah ehh haka nefah".

Dariya suka tuntsire da ita, yaseer

yace, "taabbb wai Kaine yaya taaab ko a mafarki bazance ma ba,
Yusuf shima dariyan yake yace,"Ka tuna sanda Yaya tace kana cemun yaya ??

"Ai naga baka girmen ba da zance maka wani yaya,tsayinmu Waya dai".

"Amma ai na girmeka a shekaru ko ?

"Laaaaaa shekara dayan? Dayace fa kuma Zan biya Ka kadena cewa Ka girmen".

daga haka suka tashi sukayi sallah tun Azahar har la'asar kayansu suka je suka cire sannan suka dawo suka kwanta sunayi auna hiran yayar su,
    Washegari kamar ba abinda ya damesu suka tashi sukayi wanka,wai su yanzu andena masu wanka,suka sa Kaya iri daya abinsu sunyi kyau kallo suka kunna yaseer yaje ya karbo masu abinci sukaci suka koshi,suka fita wasa,koda mama tace masu abinci fa, sukace sun koshi,
Washegari Monday ma zuwa sukayi suka ci abincin su sukace sun wuce,
Haka rayuwar su tacigaba da tafiya ko mama ta tambayesu yaya cewa suke babu wata yaya  agidan idan ba sameera ba a tunaninta abinta yaci saidai kuma ba haka bane Sam don Basu manta da yayar suba.......


By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
      Cwthrt=ØÞ<ØBß *A BAKIN WAWA* <ØBß
    _Akanji magana_

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023


      7

  
  A bangaren Abba kuwa,yaji takaicin bada motar da tayi,Amma ba yarda zaiyi tunda ta Riga da ta bayar.
Yana Wakinsa  Yana zirga zirga yaje ya dawo ya yaje ya komo,ahaka mama ta shigo ta sameshi,tsabar tunaninsa ma yayi nisa baisan da zuwanta ba,sai da ta zauna

tace, "Alhaji lafiya kuwa?? Naga kana ta yawo a tsakar Waki meke faruwa?

Kallanta ya yayi ya dawo kusa da ita ya zauna ya ja doguwar a jiyar zuciya

yace, "Bakomai ke damuna face rashin sanin menene acikin safe din Wakin can,bansan ya zanyi ba".

Numfasawa tayi

tace, "Alhaji mezai hana mu chanza pin Win".

"Ba pin bane, password ne kuma ma password ba iya adadin letters Win bane kullum sai na gwada Amma ina,kuma dole sai an buWe za'a iya canzawa,yanzu ya zamuyi?

"Haka zamuyi ta kallanta muna adana Amma munkasa buWewa? Bama wannan ba na tabbata duk wani takardu masu amfani Yana cikin su".

Shiru tayi don itama bata da mafita Akan haka,su bawani iya Abu sukayi ba,kuma ba Wanda zasu yarda dashi su fada masa damuwarsu. Lallaba Shi tayi Akan kar ya kadamu sunsan zasu bude duk Daren dadadewa kuwa. Daga haka suka dauko maganar Ummusalma, mama

tace, "Nifa Alhaji yarinyar ince de baka bata wani kudi da yawa ba?
Kallanta yayi irin bangane ba, tace ehh ina nufin baka bata kudi da yawa ba kasan de dole zata bukaci kudi ai".

Yace, "koma nawa na bata ina ruwanki a ciki, tunda de ko ta neme mu sauya layi zamuyi,bare kuma tunda taje bata neme mu ba,tunda kikaga haka watakil ma an sace ta".

"Allah yasa ma ni an sace ta din,don kwata kwata banasan Kara ganinta".

Ameen yace kawai ya jawo system ya  fara aiki ita kuma ta fita.

<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß

    ~_London_~

  Ummusalma har tayi wata hudu da tafiya,  a bangarenta kuwa bata wani tunawa da  wasu Marika don marikanta zata kirasu ba iyaye ba, bazata kirasu da iyayenta ba, bata tunawa da su sai akai akai,karatun gaban tama ya ishe ta. Tana yawan tuna su yusseer,musamman idan ta tuna rayuwar ta tada. Kamar kullum Karatu suke ita da sahr,sun kusa fara exams sosai suke karatun su,Bama kamar ita da bata so su kwace course dayan don Duka tana San abinta,sungama karatun suna Dan hira sama sama sahr ta kalli umsalma don yanzu kusan kowa a department din su yasan umsalma Indai kana tare da sahr to sai Ka santa,ta kalleta ganin wannan papern da take karantawa

tace,"wai meyasa kike karanta wannan papern ne?

Ummusalma ta kalleta

tace, "ba papern nake San karantawa wacce ta Bani nake so".

"Wacece ita?

sahr ta tambaya
Kwallace ta zubo Mata ta share sannan

  Tace' I love her, she's my friend, but for me she's my blood sister, and she she ran away from me".

Muryan ta ne yafara rawa kuma batasan  yarda zatayi  Mata bayani ba ta gane shiyasa ta faWa Mata wannan kalmomin maybe zata iya ganewa,sahr kallanta kawai take tana San Mata tambayoyi Amma tasan she's not ready to answer all her questions,is better for her tayi shiru, numfasawa tayi ta dafa ta

tace, "sorry".

abinda zata iya faWa mata kawai Kenan ta tashi ta barta. Binta da kallo tayi har ta kulewa ganinta itama tashi tayi ta tattara masu materials dinsu ta fara tafiya kanta a kasa tana tunanin bata an karaba taji tayi karo da wani abu materials dinsu gaba daya suka zube daga hannunta dagowar da zatayi kirjinta ne buga lokaci daya, hawayen da take makalewa tun dazu ne suka sauka Saman kumatunta rufe idanta tayi ta bude sai ganinsa tayi Yana tattare kayansa tare da nata gaba daya,dagowa yayi yasa hannu ya share Mata hawayen cikin wata irin murya mai sanya

yace, "kidinga kallan gaban ki idan kina tafiya kinji ko?

Daman yasan ba magana zatayi ba don Shi duk a zatonsa kurmance da gaske, Mika Mata kayanta yayi

yace, "don't repeat it ok?

Ita de tasan ta karba Abu Amma batasan meye ba,tana kallan Shi har ya kule sannan ta maida kallanta ga abinda yabata kayan sune ai,ta sa hannu ta ida share hawenta tayi gaba abinta amma wannan Karon nrml tafiya takeyi, tana Shiga taga sahr ta barbaje tana video call da yan gidan su,yau birthday dinta kuma ta manta shine suka Kira ta,ita tasan sahr ta manta ranar birthday dinta don tasan yarda taci buri a wannan birthday din,ajje kayan hannunta tayi ta Shiga wanka,har lokacin waya take da yan gidan su shiryawa tayi tafita balcony tafara zane,har tagama tana jiwo muryan sahr na waya da yan gidan su, lokacin magriba ne yayi zuwa tayi ta alwala data fito wannan Karon ta gama, wanka zatayi.
Bayan sunyi sallah sahr

tace, "yau birthday Wina Amma Baki tuna min ba ko? Kallanta tayi batace komai ba.

cigaba tayi

tace, "yau tunda bamuyi abinci ba mu fita restaurant muje muci abinci Kala da Kala".

Tana faWa tana daga Yan yatsu tana fari da ido, Kallanta kawai Ummusalma keyi amma batayi magana ba,tashi tayi tafara shiryawa don idan ba haka ba sai su ja lokaci suna zaune tana shirga masu wani shirmen,ita ma sahr tashin tayi tana shiryawa tana zabga magana ita kadai,    doguwar Riga ta zaro guda biyu a kayanta kusan kusan iri daya ce rigar kallan ce kawai ta bambanta,Mika Mata tayi tace tasa,sahr zata iya cewa bata taba sa irin wannan ba kullum cikin Riga da wando take sai Veil kuma Veil din ma a wuya take rataya,sai kuma skirt,karba tayi tace" thank you".

Sosai sukayi kyau ba kadan  ba damma sahr ce kawai tasa jambaki, umsalma kuwa ko powder batasa ba,takalmi suka sa iri daya Wanda yanzu kusan komai zasu siya to iri daya zasu saya,Amma Banda kayan sawa,fitowa sukayi suka hau taxi suka fada masa inda zai kaisu.
Bàyan ya sauke su suka shiga cikin restaurant din Sahr ce taje ta fada musu abinda suke so, bayan ta koma kuwa hotuna kawai take daukansu, sahr tayi tayi da ita tayi ko Dan murmushi ne Amma ina haka ta hakura ta kyaleta,Amma kuma tayi kyau sosai, suna cikin hotuna ne aka kawo masu abincin su Basu ankaraba taga ancika masu table da abinci,kallan sahr tayi kallan irin wazai ci??
Sahr da tasan zancen taki kallanta.tashi ma tayi ganin Basu kawo Mata cake ba,zuwa yayi

yace, "can I ?

Kamar daga sama taji maganar shi,juyowa tayi ta kalleshi yana tare da yarinya bata fi sa'ar su yusseer ba,duk da gabanta ya Wan faWi,Amma ta Waga masa Kai, yarinyar ya fara jawa kujera ta zauna shima ya zauna,sahr tana zuwa bata lura da su Bama

tace, "Yau sai kin ci komai anan wurin sabida yau birthday nane".

Tana Waukar ta hoto,sai da ta zauna sannan ta lura da su gaisawa sukayi don ita sahr Bama ta taSa ganinshi ba tunda bata business bare tasanshi, cake aka kawo musu tace su fara ci, baiji komai ba kuwa ya fara ci,itama Ummusalma ci ta farayi a hankali a hankali kamar bata so, AA da sahr kuwa surutu suke kamar da can sun San juna,ita dai kallansu take, kallanta ta Kai Jan yarinyar taga idonta na kan cake din da'alama Shi take son ci don ba abinda taci,batayi magana ba taci gaba da cin abincinta.

"Uncle cake zanci  ni bazanci abinci ba".

lomar dazata Kai ce ta ma™ale a hannunta ita bata Kai bakin ba ita bata rufe sakamakon Jin abinda yarinyar ta fada . Bata Ankara ba taji 

yace, "bazaki ci ba tunda naki ne".

Ya maka mata wata harara  ba shiri  yarinyar tayi kasa da kanta,
Kallansu Ummusalma tayi daman ya iya Hausa?ita tunda tazo ba taji anyi Hausa dukda tana ganin hausawa Amma Basu fiye yin hausar ba. Sauke cokalin tayi ta ajje sannan ta jawo cake Win ta yanka,ta fara sawa sahr sai Shi ita ma tasa tasawa yarinyar,har aka gama babu Wanda yake magana sai sahr da ke daukan hotuna ko gajiya batayi.sunje zasu biya sukaji wai ya biya kudin,sosai sahr tamasa godiya ita kuwa Umsalma kuwa ko kallanshi bata Kara yiba kawai mamaki take daman Dan Nigeria ne? Har cikin school yakaisu sukayi sallama ya wuce,suna Shiga kuwa sahr ta adda beta da tambayarta waye Shi?

Tace,"kinga nasan de ba saurayi bane don kina mugum kama dashi daman kina da yaya anan bansani ba?

"Kama?

ta maimaita.

tace, "ehh mana ,sosai kuke kama dashi".

"Kinga bama kama dashi please kidena wannan maganar ma,
Ganin batasan zancen yasa sahr cewa Naji na daina to ina gift dina kinsan de zaki Bani gift ko?

Šauko wata takarda tayi da tayi ta Mika mata,ta tashi ta wuce toilet, BuWewa tayi taga mene aciki,ganinta tayi a tsaye cikin Riga da wando sai Vail Win da take sawa a wuyanta hannunta kuma rike da takardu ta na murmushi,sosai abin ya burgeta,ta jima tana kallan zanen sosai ya kayatar ta,wai yau ita aka zana sai ta kwashe da dariya, Ummusalma na fitowa ta rungume ta tana Dariya,

tace, "waye ya zana yayi kyau kuma na gode".

Bata kula taba ta shirya tayi sallah tajanyo books tafara karatu,itama haka ta gama santin zanenta tayi wanka tay sallah.

      
        Kwanci tashi aka ce  asarar mai rai su Ummusalma sun Gama  jarabawar su sai tafiya gida,Amma banda ita anan zata  zauna bazata je ba,sahr kuwa sai zumudi take na zuwa gida.
Dawowa tayi Wakin su  taga yarda sahr take zumudin tafiya,sai duk taji babu dadi sam,zata tafi ta barta,Amma sai dai kokadan bata San komawa gida, koda kuwa na kwana daya ne, ahaka ta gama shirya kayan ta a trolley,tare sukaje airport din suna zuwa shima Yana tare da wata mata da wani dattijo kana gani zaka ce iyayen  sane  dukda ba kama suke ba Amma yarda yake kaffa kaffa da su zaka tabbatar da hakan sai wata kuma sai yarinyar nan ta rannan, Allah Allah take kawai su sahr su tashi ta bar wuri,don kallo daya tamasa ta dauke kanta,sai satar kallo kuma da takeyi musu ganin irin nishadin dake tare da su,,su sahr k c na tafiya itama ta tafi. Duk wayanci kowa ya tafi sai ™alilan na nesa ,Kayan ta take gyarawa Saida tagama tsab ta share Wakin ta goge ko ina,Zama tayi a bakin gadon ta dauko envelop din da kudinta suke ciki,kirgawa tayi taga saura kaWan kuWin ya ™are,yanzu ya zatayi? Zama tayi tana tunanin yarda zatayi gashi tana bukatar kudi kuwa shekara shida ai bawasa bane,Zama tayi tana  sakawa tana kwancewa, daga bisani ta tashi tayi wanka ta shirya ya fita,tana bin restaurant da store haka ko zata samu aikin da zata iya, dakyar ta samu a restaurant,shima wanke wanke ne daga safe har Azahar sosai hakan ya Mata dadi kuwa, tahowa tayi tana tafiya a kasa taro tagani anyi ita a zatan tama accident Akayi Amma tana Shiga cikin taron Dan ta wuce taga Ashe wai kudi a kasa Wanda zai yi Zane,idan kayi Zane a baka kudi idan bakayi daidai ba Kaine zaka biya,batare da ta yanke shawarata daga hannu,aka ce ta fito kuwa ta fito,aka nuna Mata abinda zata zana,cikin 10 minutes kuma zatayi,takuwa ce zata yi,don ita zanen mutane ne ke bata Mata lokaci tunda kuwa ba na mutum bane alhamdulilla,
Cikin lokaci kankani ta kammala zanen ta 6 minutes ta dauka tanayi ita aganinta ma ta jima tanayi,Amma ga mamakinta sai gani tayi suna cewa tayi sauri,sosai zanen ya samu karbuwa ga jama'ar wurin, ogan ne ya Basu address dinsu incase idan tana da sha'awar aiki tare dasu karba tayi suka bata kudinta dayawa. Cike da annushwa takoma Waki,ta samu aiki biyu Kenan don ba tan Tama sai ta nemi wannan aikin zanen, godiya tayiwa Allah da yabata baiwa wannan zanen,sosai tayi murna da dukda bazaka gani ba a fuskar ta amma Itakam ahakan ji take fuskanta a sake take. Washegari da wuri ta shirya ta fice wurin aikinta tana zuwa ta wuce kitchen sosai tayi wanke wanke,kuma ita kadai,bata Gama ba sai 2 tagaji kam ba laifi kafafuwanta da bayanta sun gaji bakadan ba,koda ta kwanta bacci juyi kowai take dakyar tayi bacci, washegari ma haka tayi aikinta ta gaji sosai ita sai tagama na yau yafi na jiya,dukda ta gaji Amma haka ta wuce wurin address din nan da aka bata tana zuwa kuwa suka ganeta sunyi murna sosai da sosai, da zuwanta,aiki suka bata tana zanen wani nature,karba tayi tace'gobe zata dawo dashi bazatayi anan ba,fadar inda take tayi da komai da komai nata,zasuke nemanta. Kafin ta saba da ayyukanta guda biyu ta wahala bakadan ba kullum kuma take zuwa bata fashi tun kafarta da bayanta na ciwo har ta Riga da ta saba,bata fashi,kuma bata makara Akan lokaci take zuwa ta tashi Akan lokaci,Suma kuma daman sun fi San haka don su basu San wani abu ba wai shi  African time ba.
   
  Ahaka take samu kudinta ba laifi har aka dawo school,sosai result dinta yayi kyai don babu C B dinta ma befi biyu ba zuwa uku sosai hakan yayi Mata dadi Suma kuma school din sunga kokarinta ba kadan ba,tunda suka dawo bata fasa zuwa aikinta ba Amma kuma sai ta koma na dare daga 6pm zuwa 10pm abinta,bangren zanenta kuwa zuwa take ta karbo zanen idan ta dawo komin dare sai tayi,sai ya zamana lokacinta ya ragu batada wani lokaci sai na aiki da karatu,dadinta ma yanzu sunce tadena zuwa da weekend saboda karatunta hakan yayi Mata dadi.
  sahr tayi tayi da ita ta dena taki,ko kallanta ma batayi bare ta tanka Mata ganin haka yasata yin shiru......

<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß

   ~_Nigeria_~

    Yusuf da yaseer ne a dakin Ummusalma suna dauka abinda suke so na Zane da kuma hotunansu sosai suke jidar kayan sunayi suna leka window ahaka suka kwashe suka Kai mota suka dawo suna Zama kuwa mama nashigowa

tace, "yawwa yau zamu tashi daga wannan gidan mukoma wani,ku dau abinda kuke so ku dauka,kunji ko?

Kallan juna sukayi suka ce tou
Sama tahau gani Suma tashi sukayi don su haura Saman gani sukayi tana rufe dakin Ummusalma,dakin su suka Shiga, yaseer

yace,"yanzu dabamu ji zamu tashi daga gidan nan ba shikenan ko?
Yusuf yace, "sai kuma Allah yasa munji".

Zama sukayi suna buga game,abinsu
Mama ce ta leko ta gansu

tace, "au wai daman ba haWa kayan kuke ba?

Kallanta sukayi yaseer

yace, "a Kira Indo ta haWa mana kayan mana,ni banzan iya ba".

Ya faWa ya turo baki.

tace, "ehhh tunda Indo ce tasan abinda kuke so ko? To idan tazo gaba daya kayan zata kwashe ta bayar,na bata kayan duka,shiyasa nace ku debe abinda kuke so,kuma Bana San tarkace kunji ni ai?

tafaWa tana barin wurin,kallan juna sukayi sannan suka dauko school bag dinsu suka sa games dinsu aciki sai abinda ba'a Rasa ba wasu ma a hannu suka riko,suka fito,mota suka Kai kayan suka dawo, kallan su mama tayi

tace, "kuje Driver ya kaiku gidan".

Tashi sukayi suka fita. Gidan ya haWu iya haWuwa zaka iya rantsewa ma ba'a ™asar ya™e ba don haWuwar sa  yayi kyau sosai Saida muce Masha Allah,
Sun yaba tsarin gidan sosai kuma ya musu kyau bakadan ba,don harda wurin buga ball,yayi kyau sosai da sosai. Suna gama zagaye gidan suna parlour suna ™ara ganin gidan, Mama ta shigo wannan karan Wakinsu a kasa yake,da parlour aciki sai Dan karamin kitchen da toilet a parlourn,su kuma kowa da dakin shi,sukam sun Saba da Zama daki daya,tunda Basu taba rabuwa kuma basa Jin zasu rabu,fita sukayi suka dauko kayansu a mota,suka dau daki daya suka zuba kayan da suka dauka a dakin Ummusalma,dayan kuma suka saka kayan su anan zasu zauna acewar su.
   Sosai suke baza hajarsu agidan suna watayawa. Makaranta ma ancanza musu wata sunso ace sai zasu Shiga js2 asake tunda yanzu suna js1 kuma second term Amma a haka aka sake masu,basu so ba,haka sukayi mitar su suka gama,sunyi ™awaye maza da mata abinsu don akwai wata ´ar anguwar su suna cemata Yaya wani sa'in sabida wai sunan Ummusalma ne da ita,ita kuma ba laifi akwai san girma,sosai suka sha™u da ita wataran ma tare ake Waukosu ko akaisu tare,har suka dawo idan aka kaisu agidan wannan to wani satin za'a kaisu a gidan wannan haka suka zama. Kuma hakan bai sa iyayen zumumci ba.........


By: '''Hijjart Abdoul'''
     Cwthrt=ØÞ*A BAKIN WAWA*<ØBß
       _Akanji_ _magana_

    
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023


         8

   A bangaren Ummusalma kuwa balaifi don ita yanzu ta saba sosai da hakan da take,kuma bayan wanke wanke da take a restaurant,yanzu har girki takeyi,takan gani wani sa'in yarda sukeyi da haka ta koya,aikim Zane ma ba laifi yanzu takan zana ma takai ko ba'a ce ba tunda sun fi son zanen nature,kudi sosai takeyi abinta.
Gashi yanzu sungama year one zasu Shiga ta biyu,kusan kowa sun tafi gida sai yan kadan kamar wancan lokacin. Ahaka ta cigaba da zuwa aikin ta kasancewar ta dena zuwa da weekend yasa take karatun da za'a masu nan gaba sosai kuma take ganewa.
Yau ma de tana zaune a bakin campus da yamma tana sanye da wando sai jacket datasa da baby hijab,karatu take yau weekend ba taje ko'ina ba,tana nan zaune taga wani ya zauna a kusa da ita,yana waya kuma da Hausa yake wayar wani sa'in Yana hadawa da Spanish,bata kalleshiba kawai taci gaba da abinda take kallanta yayi

yace' Hello,
Bata tanka masa ba ta dan juyo ta kalleshi da sauri ta maida kallanta ga books dinta saidai gabanta da ya fadi,Amma Sam bata nuna ba,meke faruwa da ita ne???abinda tace a zuciyar ta Kenan,mai fuskar Baba ga kuma mai fuskar NEENA mekefaruwa???
Katse Mata tunani yayi ta hanyar

cewa" hey can I ask u?
Shiru tamasa,sai ma Kara Dan kallansa da tayi,zuwa yanzu taji zuciyar ta tadena bugawa shiyasa ma ta Kara kallansa,tabbas sunyi kama da ita sosai,amma Neena farace bata Kai hasken shiba,shikuma ja kuma jikinshi ya samu hutu, sabanin Neena. Ganin ta tafi tunanin ya kuma

cewa" please,
Dauke kanta tayi daga kallansa ganin haka yasa Shi cewa a fili" To ko kurma ce ne bata magana??
Daman tasan za'a rina indai cewa kurma badaga kanshi aka fara ba,sabida ko haushi ma bataji bare kuma tayi magana.
Joyuwar da zatayi taga ya fara Mata zancen kurame ikon Allah haka ake zancen kuramen?
Ganin irin kallan da take masa na irin mekakeyi?
Yasa Shi sararawa ya Ciro wayarsa ya kira wani bata sai ji tayi Yana

cewa" Nidai yunwa nake ji,ni banga kowa ba,sai wata kurma kuma nayi nayi ta gane takasa ganewa Itakam wannan a kurman ma ina ga ajin karshe ce,
Ita dariya yaso bata wai a kurman ajin karshe ce,hmmm kawai tace,batajin me aka fada amma da duk kan alamu lallashinsa ake,ganin yarda yake hade fuska, kallanta yayi,ya dauke yaci gaba da fadin bazaka gane ba ne yarinyar daman tayi kama da ifiritu gata da manyan ido kwala kwala da su irin na twiny gata da dan wani matsitsin bakinta in fada maka wannan badan kurma bace marar kunya za'ayi inaga ma ko a kurman ma bata da kunya,nifa tana min kama da twiny wallahi,Dan kamar ta baci ma,ya kareshe yana wani ya tsine fuska,
Batasan me aka ce Saida ganin yarda ya hade Rai Ya nuna fada ake masa, bayan ya kashe wayar ya juyo ya kalleta,

yace' yunwa nakeji ki taimaka min kifada ko ki nuna min cafeteria ko restaurant ni bako ne masters aka kawo mu yi nida Dan uwa kuma baida lafiya yana can adaki kuma wai shine  aka kawo mu tun yanzu don an tsanemu please ki taimaka kinga ni Yayanki ne ko? Duk maganar da Hausa

Please Login or Register in order to submit comment