Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya Zane sosai da sosai yaseer ma ya taba kwatan tamata mutumi kuma ta zana shikenan infada maki mukayi fada,daman lokacin munyi candy aka bani labarin kuma Zan taho London hutu, ranar da Zan taho naje gidan su,ko kallo na ma basuyi ba ,daga karshe ma Yusuf ne ya hankado ni daga parlourn su ya kulle,na Basu hakuri sunki hakura,suka sani a blacklist,tunda na taho nake kiransu Amma babu,wani lokacin fa idan mukayi fada suke fara nemana,gashi yanzu nayi hutun nagama saidai ni nakirasu Amma kullum user busy ake cemin. Yanzu kuma nasan kona koma tunda Basu Kirani ba shikenan baza su hakura ba, gashi nayi missing dinsu sosai,
Kallanta tayi

tace' kina San su yafe miki?
Dasauri ta tace ehhh mana inaso sosai don bazan Kara karyata su ba wallahi,

Idan kinje kice yaya na gaida su, sannan kice masu yaya tace zata dawo very soon kuma ta karbi numbers dinsu zata kirasu sannan ki Basu wannan kice inji yaya photon tane Wanda sahr ta dage sai anyi Mata da graduation gown  ajikinta,sai kuma Wanda babu harda Wanda suka je park suna Shan ice cream,kala kala wasu ita daya wasu kuma su biyu,Duka ta basu envelope din,
Karba tayi  budewa tayi ta kalli hoton ta kalleta,

tace'  kecen yaya salama daman?
Daga Mata kai tayi

tace' kiyi hakuri don Allah wallahi bansan ke bace,kinji?
Bakomai tace mata.

tace aikuwa zan fada masu, Amma ai Naga gidan zaki je,
Girgiza Mata Kai tayi

Tace' karki fada masu mun taho tare dake,ki fada masu a London muka hadu,kinji?

To shikenan Insha Allah Zan fada masu, shikenan mun shirya,cigaba tayi tace suna sanki,Basu da labari sai naki,tun muna js1 aka kawosu makarantar mu,to Yan unguwar mune shikenan muka Saba dasu tare ake kaimu a dauko mu,wasu ma sun zaci ni yargidan suce, yaseer yanzu  yaya yake cewa Yusuf shikuma yace masa kanina a haka suke,kuma sundena fada,wai kince masu sudena fada Basu dena ba saida kika tafi sunyi mugun missing dinki.
Jinta kawai takeyi daman tasan bazasu manta da ita ba
A haka ummu tayi ta bata labari daga nan har sukayi bacci suka tashi,idan sunyi bacci antashi sai a daura daga inda aka tsaya a haka har suka sauka lokacin dare yayi karfe 10pm,ba'azo daukan suba son haka zama sukayi a waiting suna cigaba da hira anan ta karbi numbers dinsu da   address dinsu,daga nan aka zu daukan su har ya Shiga sai kuma ya fito

yace' student ba magana ?
Sosai taji kunya ya kamata, batayi maganaba

yace' Nima Zan iya zama friend din? Kamar yarda yata ta Zama? Friend or sister?
Sister tace, om thanks yace shima Yana barin wurin,suna tafiya itama taja trolley dinta ta fito Allah ya taimaketa ta ga mai adaidaita ta hau,sunan unguwar ta fada masa suna tafiyar taga anyi sauye sauye sosai wasu wuraren an same wasu kuma sunanan an gyarasu,taga sauyi bakadan ba shekara shida ai ba wasa ba ne,tana masa kwatance har suka iso kofar gidan,don dakyar ma ta gane Saida suka tambaya sannan ta gane, suka sauka ta fito da kudinshi ta bashi har ya amsa

yace' Hajiya fa wanann ba kudin mu bane kalla tayi taga dollar ce ita ta manta shaf da tayi canji a airport ai, numfashi taja,

tace' to gobe ka dawo zaka kaini wani wurin inba damuwa, badamuwa yace
Trolley dinta ta dauka tayi hanyar wani gida gidan ta kalla sannan tayi knocking.......

By : '''Hijjart Abdoul'''
      Cwthrt=ØÞ<ØBß *A BAKIN WAWA* <ØBß
     _Akanji magana_

   

 
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023


       11

Tasan dai by this time watakila ma sun rufe gidansu,agogon hannunta ta kalla,taga lokaci zata Kara knocking taji an bude kofar,matar ta da ta bude kofar tace' wacece?

tace' Ummusalma ce,
Saida ta maimaita sunan sannan tace shigo mana kya tsaya daga nan kuma,
Shigowa sukayi,sosai taga canji daga gidan,ansake ma fasalin gidan anyi parlour sabanin da,da dakuna ne a jere (sai kace islamiyya), trolley din matar ta ja Mata suka Shiga parlourn nasu,Zama tayi Akan kujera,

Tace' ina yini,
Da lafiya matar ta amsa mata sannan

tace' lafiya kuwa?  Na ganki acikin dare haka?
Ya zamana dole ta canza ta dawo Ummusalma ta tada, idan har tana so ta cimma burinta,kowanne Saida bayani yake iyiwa. Numfasawa tayi

tace' yanzu na dawo daga karatu,kuma naji babu Wanda nake san ji irin labarin su Neena I mean Amina,
Matar( makwabciyar su Amina)

tace' Ummusalma su Amina fa tashi sukayi daga garin nan a yarda suka ce min kenan,don kinga a lokacin ma da suka tashi kudin haya ne Basu dashi,shikuma mai gidan yace bazai daga masu kafa ba,shine ya kwashe kayan su masu amfani zai siyar a lokacin ne Amina tazo da kudi,ta bashi sannan ya hakura ganin kudinsa, yace Amma dole sai sun tashin masa daga gida,kinji yarda akayi,shine ma sanadin tafiyar su,
Lumshe ido tayi ta jingina da kujeran,tana cigaba da ji,
Itama matar cigaba tayi,

tace' tunda suke da mai gidan hayar Basu taba Jin kansa ba da Abban Amina Yana kokari sosai ganin ya bashi kudinsa,to tunda Inni ta fara rashin lafiya shikenan kuma komai ya canja bansan meke damunta ba Kona tambayi Amina bata fada min sai dai ta shashantar da zancen ma, kamar basa so mutane su San meke damunta haka na dauka de, koda zasu tashi Basu fada min inda zasu je ba saidai tace garin zasu bari,
Bude idan ta tayi ta tashi

tace' Bata da yaya? Ko kani haka de?

Gaskiya nidai tunda nazo unguwar nan ita kadai nake gani, kuma ita kadai ce a wurinsu,kuma ban taba Jin ta bani labarin yayun ta ba.
Numfashi ta kuma ja

tace' to yau uwa fah? Wakika sani?

Bansan Yan uwansu ba Gaskiya,sai dai abokan arziki,don munyi rashin mutane kamar su,daga Abban har Inni dukan su mutanen kwarai ga kuma Amina Wanda kowa yake Santa,ta kasance mutum mai shiga Rai,kuma duk wanda yasanta to tabbas ya sanki,wani irin kauna take miki,idan kana San faranta Mata to Ka ambaci sunanki, bansan ya Zan kwatanta maki yarda take sanki ba.

Amma suna cikin wannan halin taya Baffa ke biya Mata kudin makaranta?

Yana aiki ai,yana gadi a wata makarantar primary private ce school din sannan kuma yana Saida fruit kuma yana aikin kafinta bansan ya yake yi ba Yana biya mata kudin makaranta amma de wannan aikin yakeyi,

Ya sunan makarantar?

Bansani ba Gaskiya wannan Abban su Sadiq ne ya fada min(mijinta) Amma idan ya dawo Zan tambayeshi Insha Allah yanzu baya nan.
Shiru sukayi sannan

tace' Amma Ummusalma bakya ganin idan neman su zamuyi ai ya bar makarantar tunda tashi sukayi ko?

Bana ganin sun bar garin nan,kece ta fadawa haka,Amma dole suna garin nan,kuma zai ci gaba da sana'arsa ko kuma ya sake wata,dole cikin biyu za'ayi daya.
Tashi tayi

tace' kinga ko sallah banyi ba,Bari kiga na tashi na tafi,

Yan gidan ku Amma Basu San zaki dawo ba ko?
Ta tambaya tana tashi don ta rakata,ta fara Jan akwatinta

tace' ba gida ba zani,hotel zanje na kwana gobe Insha Allah Zan dawo,
Ta fara  tafiya tana Shirin barin bude kofar  parlourn,da sauri matar

tace' wanne irin hotel kuma?
Don Allah kizo mu zauna anan tunda kinga mijina baya nan? Daga ni sai yara kuma ba yau zai dawo ba, tana fada tana rike da akwatinta don karma ta fita, kallan matar tayi taga har zuciyar take maganar,Amma sai

tace' ki barshi kawai zanje na kwana a can din,karki damu,

Yazaki ce Karna damu,kinga Don Allah ki dawo mu zauna kinji ko?
Bayarda ta iya don itama ba San kwannan hotel din take ba,suna cikin haka aka dauke nepa, matar taja Mata akwatinta ta kunna masu bulb din DC, ta Kai akwatin ta dawo taja hannunta ta kaita daki,

tace' dakin yara na ne mata,sun tafi hutu,sai Maza ki zauna anan ki huta ai yafi de,yanzu kiyi wanka sai kiyi sallahn naki,
Da kallo ta bita har ta fice a zuciyar ta tace'"daman akwai mutanen kirki a duniya haka? A gogon dakin ta kalla taga 11:50,bata zaci lokacin ya kure haka ba, agurguje ta fada bayin,Dan karami ne toilet din babu bathtub sai makwarara kawai,kuma ba ruwa don ga containern ruwa nan,a hakan de tayi wanka ta ta daura towel din data gani,tana fitowa kawai ta bude akwatinta ta dauko rigar bacci tasa,tasa hijabi tayi sallah,tana cikin sallah matar ta shigo ta kawo Mata abinci, tana idar wa kuwa ta zanjo tray din abincin,tuwon semo miyar kubewa bushashiya da Banda Tasha manja,harda man shanu da yajin kalwa acikin wani da bowl wato ko tana ci sai tasaka, zubuwa kuwa tayi,tunkafin tafara ci yawunta ya tsinke,irin dadin nan=Ø Þ
Aikuwa taci sosai don kulli biyu taci,ga kuma wani lafiyayyen ginger taci tayi nak da ita, wani dadi takeji Kanta ita zata iya cewa ma tunda kafin ta tafi bata ci ta koshi kamar na yau ba.
Tattara komai tayi ta nufi parlourn duhu tagani ba haske dawowa tayi tadau wayarta sannan ta fito, kofar data gani ya Mata kama da ta kitchen ta nufa,ta ajje kayan sannan ta koma ta zauna, Qur'anin tagani ta dauko ta Karanta daga bisani kuma ta fada duniyar tunanin yarda za'ayi ta Gama abinta cikin kwarewa, tana zaune Jin tafara bacci yasata kashe bulb din ta kwanta, addu'ah tayi sannan sai bacci.
('('('('('('('
Da Asuba Saida maman Sadiq ta tasheta sannan, tsabar gajiya,bayan tayi sallah komawa tayu ta kwanta,sai bacci batawani yi bacci dayawa ba ta tashi ta gyara dakin ta wanke toilet,ta fito bakowa a parlour alama de Basu tashi ba,shima gyarawa tayi, tayi wanke wanke ta bude parlour ta fito ta share tsakar gidan ta wanke Shi tas kasancewar tiles ne kuma Dan karamin ne tsakar gidan,bayan ta gama ta dawo parlourn ganin nepa yasa ta daukan Burnern da ta gani ta kunna sannan tasa turaren wuta,iya parlour tasaka,ta Shiga daki tayi wanka ta shirya cikin doguwar Riga sannan ta fito lokacin yaran ma sun tashi an masu wanka,su biyu Maza gaidata sukayi suna cigaba da kallansu,itama Zama tayi suna kallan tare,tama manta yaushe rabonta da kallo cartoon akeyi kuma mai kyau cartoon itama ya Mata kyau bare kuma yara,suna cikin haka saiga maman Sadiq ta fito daga kitchen gaisawa sukayi,maman Sadiq

tace' ohh sannu da kokari,muna ta bacci har kin tashi kin gyara ko 'ina bamu saniba,na gode sosai,
Batayi magana ba don batasan mezatace ba shiyasa kawai tayi shiru abinta,itama maman Sadiq din wucewa tayi ta Shiga kitchen ta cigaba da abinda takeyi.
    Breakfast ta kawo masu su Duka bata ware ba,a plate daya sai cups, dumamen tuwo ne sai bread da kwai sai tea,maman Sadiq

tace' bansani ba ko kina cin dumamen tuwo,
Ita mamaki ma taji,tana San tuwo ai ita,ca

tace' bakomai ina cin tuwo ai,kuma ma rabona dashi tun kafin na tafi makaranta,
Daga nan ba Wanda yasake magana suna ci suna kallo,abinsu tare da yaran,sosai abin ya burgeta tana so taga family a haka bakamar gidan da ta taso ba kowa nashi yake zubawa kuma a dining suke ci.
Suna gamawa kuwa ta dauki plate din ta Kai kitchen tare da cups din,tana Shirin wankewa saiga maman nan tazo

tace' kingan ki ko? Duk uban aikin da kika sha,bai isheki ba sai kin wanke wanna ko?
Ta karasa tana karban sponge din daga hannunta, bata tayi amma bata fita ba tsayawa tayi tana wankewa tana daurayewa,suka Gama Suka  fito,yaran ta kalla

tace' kuje ku dau ruwa kafin a dauke yau mun makara,
Tashi sukayi suna cuno Baki da'alama basa son tashi daga kallan,bayan sun tafi Ummusalma ta kalli maman Sadiq

tace' ina San na nemi aiki a wani gida, ya zanyi?
Kallanta tayi kallan kina da wayo kuwa?

tace' bangane ba?

I mean aikin gida kamar Shara wanke wanke haka da sauran su,

To ke me zakiyi haka da irin wannan aikin?

Wani aiki nake so na gudanar kuma dole sai tanan ne nake ganin zaiyi,

To shikenan ba damuwa Zan tambaya maki anan makociyar mu itama tana kaiwa masu aiki, kuma naji tana cigiyar idan ansamu.

Hamdala tayi tayi a zuciyar ta fatanta Allah yasa a dace,

Kallanta tayi tace' Amma ba'a haka zaki tafi ba? Kinga gidan aiki ne dole zani zaki kesawa kuma dabam dabam,sannan kar ki nuna ke yar boko ce,idan ba haka ba za'a samu mutsala,

Kallanta tayi tace' ya kike ganin idan naje masu a marar magana? Zasu karbeni?

Good idea,hakan yayi ma,du abinda ake ciki sai ki fada min idan kinje.
Bari ma na kirata sai tazo muyi maganar zuwa yamma sai a kaiki,
Daga Kai tayi kawai daganan ta tashi ta dauko hand bag dinta tayi rolling ta fito, sallama ta mata ta fito,tana fitowa tana hano mai adaidaita Yana shigowa layin,ita Sam Tama manta dawani mai adaidaita,tsayawa tayi kuwa taga shine ko bashi bane,aikuwa shine,tana Shiga tace' ya kaita banki access bank,kaita yayi ta fito tace ya jirata, atm ta sake don yayi expired,kuma tana bukatar kudin, sannan ta canza dollars dinta Amma ba Duka ba, sannan ta fito gobe zata dawo ta amsa atm din,Shiga tayi suka tafi daga nan ta sai simcard ta saka a wayanta,sai bata cire dayan ba ganin kamar Yana amfanin dukda bawanda ya kirata, Amma taga akwai network..

    <Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß<Ø<ß
Suna sauka ta nufi gate zata fita har wani sauri sauri takeyi don ta fice,sai dai kafin taje taji an damko hannunta,ya tsine fuska tayi don tasan waye,juyowa tayi

tace' haba uncle gidan su besties zani fah,
Wani irin kallo ya Mata me cike da gargadi sannan

Yace' inba de dusa ce taya zaki fita gidan mutane da wannan dare? Daga dawowa ko sallah bakiya ba?

Kara marairaice wa tayi,wai ko zaiji tausayinta yace taje,

Tace' kaga ko minti daya bazanyi ba zandawo kaji ko?naje?
Maimakon taji amsar sai ji tayi an fara janta,wani takaici ne ya kamata,ta kumbura baki ta fara gunguni ciki ciki, don tasan idan yajita to Saidai wata Ummu badai ita ba, Yana rike da hannunta har suka isa cikin parlourn,suna Shiga kuwa mamanta na parlour da'alama su take jira, da sallama ya shigo,cike da fara'a ta tashi ta tarbe shi

tace' ya hanya,?
Lafiya qalau ya amsa Mata,
Kallan ummu tayi Wanda sai a sannan ya saki hannunta,

tace' ita kuma lafiya?? Me aka Mata haka?
Yana wuce yace wai sai taje gidan wa'ancan  yaran. Shine na hanata take wanann cikar tana batsewa jira nake Naga zata fashe ko kuwa,
Kamar tayi kuka

tace' wallahi mama sako Zan Kai masu fah, shine uncle ya hanani.
Maman ce ta kalleta

tace' rabun kar ku hadu yanzun nan suka fita,don sai da driver ma ya fita dauko ku da jimawa sannan suka fita, na ma ji mamaki da basuje tare an dauko kuba.
Batajira me zatace ba ta dawo ta zauna,daman uncle ya Shiga ciki,itama tana tura Baki ta Shiga dakinta,dukda yunwan da take ji sallah kawai tayi ta kwanta, ko abincin ma bazata ci ba,ai taci a jirgi a haka bacci ya kwasheta.

      Karfe shida,ta fito takalmi a hannu  tana sanda zata fice Dukda ba Wanda zai jita,kowa na dakin Shi,Amma haka ta fito sai sanda take abinta har ta fice daga gidan, gate ma ba kowa mai gadi Yana dakinsa, bude kofa tayi ta fice abinta sannan tasa takalmin ta, gidan su tayi knocking a hankali,Jin shiru yasata tayi da Dan karfi, ta Dan jima ba'a zoba ta Kara yin wani knocking da karfi,kawo yanzu kuwa zuciya ta ciyota zata kuma taji ana Shirin budewa,ita kadai takama Mita,Yana bude Mata ko gaisuwa da ta Saba yimasa ma batayi ba ta shige kamar zata tashi Sama Dan sauri, Saida taje kofar parlourn ta ja ta tsaya watakila ma kofar bude take,zagawa tayi ta kitchen tana addu'ah Allah yasa a bude kodan saboda masu aiki ma tasan ai a bude ne,aikuwa tana zuwa ta murda taji a bude,hamdala tayi ta Shiga,sai da ta cire takalim tukunna, sannan ta Shiga, direct part dinsu ta nufa,tana zuwa ta bude kofar parlourn Allah yasota a bude take kodan ai anyi sallahn asuba shiyasa,ta raya ranta,.
  Tsayawa tayi tana doubting ta Shiga ko kar ta Shiga,tunda suke sai dai ta tsaya a iya parlourn su tun suna yara,bata taba Shiga ba,tana nan tsaye kawai ta yanke shawaran shiga, nufar bedroom din da suke kwana tayi,tasan tare suke kwana tun suna yara har yanzu. A hankali ta bude kofar dakin ta leka kanta ciki suna kwance cikin bargo suna bacci ga wani irin sanyi da dakin ya dauka saboda acn da suka kwana, Shiga tayi taje ta kashe acn ta dawo ta tsaya akansu,taya zata tashesu yanzu? Tasan ko ta Kira sunan su indai sunji itace to baza su tashiba, bottle water tagani akan center table din gabanta,dauka kuwa tayi ta je ta yayyafa masu, aikuwa a tare suka tashi don yin masifa a tunanin su sun zata Sameera ce,ganinta a tsaye yasa su Kara Shan kunu,
Basuyi mamakin ganinta don ta Riga da ta saba,indai da labari kuwa,Suma kuma suna zuwa gidan su, yaseer ne,

yace' fice mana a daki,
Ganin ta tsaya tayi folding hannayenta ta tsaya tana kallansu yasa Yusuf

yace' Baki ji abinda aka ce maki ba?
Sai gani sukayi ma tasamu  wuri ta zauna a bakin gadan,

Yaseer yace' wallahi idan Baki tashi ba Zan turaki ki fada daman ai bamu muka kiraki ba da zaki shigo mana daki ki tashemu a bacci banza kawai?
Daura kafa tayi daya kan daya ta bude envelope din hannunta ta zaro hoton Ummusalma guda daya ta ajje a tsakiyar su tare da cewa" kunsan wannan??
Rige rigen daukan hoton sukayi ganin kamar yaya, kowa ya rike gefen hoton suna kallo, tabbas itace ba abinda ta Kara sai farin sai kuma abinda ba za'a rasa ba.
A tare suka kalli suka furta YAYA?? sannan suka maida kallansu ga ummu da take kallansu tana wani murmushi tana kallansu ai a sukwane suka diro suka dawo gaban ta yaseer da sauri

yace' a'ina kuka hadu?taya kukasan juna? har tabaki hoton ta? Ca kikace kin samu? Fada mana,ki fada mana ya labarin ta yake? Tana nan lafiya? Ba abinda yake damunta? Tana magana kamar da? Kunyi magana sosai da ita ne? Ki fada mana mana,
yafada ya Dan dukan kafar ta irin yi sauri dinnan.
Kallan su tayi

tace' tace tana gaida ku,kuma zata dawo very soon,kuma ta bani wannan ba Baku,ta fada tana Mika masu envelope,
taci gaba dacewa kuma ta karbi numbern ku zata kiraku Sannan tace  ko  munyi fada ku dena yin fushi Dani kuma( Hajiya ummu harda Karin ),
Yusuf ne ya tashi tsaye 

yace' meyasa, meyasa,meyasa Baki karbo numbern ta ba? Ke kika bata tamu ? why,why zakiyi haka ehh?
Itakam Sam tunanin Amsar numbernta bezo mata ba,kawai numbers dinsu ta bayar harda Tata,ai tasan zata kira,

tace' ai tare ma da ita muka........
Sai ta tuna abinda ta fada Mata  tace kar tafada tare suka dawo "ohhh God tafada kasan makoshinta, tana dafe goshi,
Da sauri Yusuf yadawo

yace' tare da ita kuka dawo ko? Fada min ehh? Tare ne ko?
Ganin tayi shiru tana kallansa yasa

yace' nasan tare ne ai,nasani tunda kika ki karasawa nasani,me tace maki?
Yafada kwalla ta cika idansa, shikuwa yaseer hotan kawai yake gani yana kuka,  tuno rayuwar su da ita,
Kallansu tayi ganin halinda suke ciki, don kawai suna son ji labarinta,su Basu da saurin kuka koda kuwa an dakesu Amma,zata iya cewa bata taba gani sunyi kuka haka ba, numfashi taja sannan Ta Basu yarda Akayi suka hadu,da labarin da ta bata da komai da komai har kawo dauko su a airport.

Wani irin kuka suka hade Kai da gwiwa sunayi,ita de kawai kallansu take yi itama ta Dan share hawayen ta, a ganinta farin ciki zasuyi Amma sai akasamu akasin haka,suna kuka to kukanne batasan na meye ba. Bayan ta share hawayen ta

Tace' to wai kukan na meye haka? A ganina na farin ciki ne ai,
Yaseer ne yace'" farin ciki? Kinsan kukan da mukeyi ne? Kuka ne na danasani,kuka ne na danasani,yanzu kinji ?
Danasani kuma? Ta maimaita cike da mamaki,
Yusuf ne ya dago a zuciye

yace' ehh danasani, Shi mukeyi don Allah ki tafi ki barmu mungode,don Allah,.
Yafada yana hade hannayensa wuri daya, ya cigaba da kukan sa,

Tace' nifa ba inda zanje sai kun fada min, danasanin meye kuke kuka haka? Maimakon kuyi farin ciki ta dawo,Amma ku zauna kuna kuka?
Wannan Karan yaseer ne ya hada gumi sharkafi ya dago da kansa Yana jan majina

yace' danasani ne na rashin bin drivern ku dauko ki,da'ace munje mun dauko ki kamar yarda mukeyi kullum da mun hadu da ita ai, da kuma ace munbi maganar Anty( maman ummu). Da duk haka bata faru ba,daman ance binna gaba bin Allah,gashi nan fushi da zuciya ta kaimu ta baro.yaya kiyi hakuri ki dawo don Allah,

Sai yanzu ta gane Inda maganar sa ta dosa tabbas kuwa mama ta fada Mata Amma batace tace su bi driver a dauko suba.

Tace'to yanzu ku daina kuka kunji ko? Tunda tazo basai mu fadawa umma ba(maman su) a bincka ko abada cigiyar ta ba kaga sai a samu ta dawo gida ai ko?
Da wani speed Yusuf ya dago cikin wata irin murya mai Kara

yace' kina hauka zaki fadawa mama? Ida kika fada Mata Tou ko sun samota cazasu ce Basu ganta ba, su turata ga halaka, wannan Karan na tabbata kungurumin daji zasu kaita,damun daji su cinyeta, shikenan mu kuma kin samu a uku ko?
Kanta ne ya wani uba daurewa bata gane Inda zancen ya dosa ba, zasu Kara sa turata ga  halaka??? Mekenan? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un bata gane ba,

Tace' kunga ku ganar Dani mana meke faruwa ? Bangane ba? Naga de sunan baban ku daya,kuma yar gidan ku ce? Ba Abba bane ya haifeta ba?
Yaseer

yace' Yaya itace cikwan farin cikin mu,yaya itace komai namu tun muna kanana,da yaya muka fara bude ido muke gani a matsayi  mai Kula damu,dukda Yusuf ya girmeni da shekara daya,itace ta reneshi har aka haifeni, ta hada Dani dashi ta rena,bata da wani buri Sama data faran tamana koda zata bakan tawa wani ko ita kanta, she's sacrifice alot of things for us, shes can do anything for us,yaya tun muna yara take Kiran mu da Yusseer wato Yusuf and yaseer, yaya ce ta fara koya mana karatu,dukda ita bata maida hankali Akan karatunta amma kome aka yi Mata ta iya,indai har zata tsaya ta koya din,Amma kuma bata tsayawa tanayi ba ruwanta da karatu Bama taso,kuma mama bata Mata fada Amma mu tana mana fada sosai musamman akan karatu. Ada ba abinda ta iya sai mana wanka da shirya mu,suka dai mukasan ta iya don ko  kunna gas da bata iya ba, Akan mu ta iya mota saboda fitar da muke any how,ita zata kaimu school sai ta dawo ta shirya taje Tata,bata damu ba don ta makara,abinda tasani shine karmu makara,daga makarata take wucewa ta dauko mu ,Idan mundawo ta samu muyi sallah tamana wanka, tasa mana kayan islamiyya, sannan ta kaimu,sai ta kaimu islamiyya sannan zata cire uniform dinta, tun muna yara tayi damu mudena fada mukaki jinta , tace nake cewa Yusuf Yaya naki fada, kullum sai tai rabiyar fada idan ba ita ba ba wanda ke iya raba mu, bata da  lokacin kanta sai namu, Yaya taje cell saboda mu,ba Wanda yasani saI mu sai Allah,bata damu ba, yaya ba ruwanta,tana da tausayi,kuma bata da mutunci,don kaf ma'aikatan gidan tsoron ta suke ji.
  Watarana zata kaimu islamiyya har mun Shiga ta manta bata dauko kudi ba kuma bamu dauko abinci ba, wataran muna tafiya dashi sai tabi ta kofan baya don ta dauko abincin,komawan da zatayi bata dawo ba sai gajiya mukayi muka taho don mu ganta,Jin numfashi a garden yasa mukaje wurin,muka Kira mama,tundaga wannan rashin lafiyan ta koma wani rin shiru bata magana,dazaki Mata magana dubu to nodding Kai zata maki sau daya,tun muna damuwa har muka saba, da shirunta,ta kuma rage kaimu park da duk Friday da Thursday idan an dawo daga school Bama Zama muna park,da can ita ma bata San zuwa gidan kawayen Mama, shiyasa wani zabin muke wuni a park wani zubin kuma mu yi a gidan kawayen ta,
Alokacin da zata tafi karatu mama tace mana idan ta tafi bazata dawoba,koda na fada Mata tace min zata dawo,amma kar na fadawa kowa sai Yusuf, munyi kuka har Abba Saida ya zane mu,a lokacin Yusuf ke fada abinda mama tafada lokacin muna bacci tace,wai yaya bazata dawo ba kuma zamu manta da ita a rayuwar, abinda Yusuf yayi tunanin zata mana irin abinda akayiwa wani abokin mu,muka dena yarda tana zuba mana abinci

Please Login or Register in order to submit comment