Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Karo masu fruit dayawa, ya taho da Kaya Niki Niki, ya bude boot yasa,
ya zauna yace'' bb nagaji wannan matar akwai sa aiki"

Banza yayi dashi ya yaja motat suka tafi, a wani shagon Sai da ice cream ya tsaya yace'' fita"

" Nayi me fa?

" Ice cream zaka siyo Mata"

Wani idi turo Baki yayi ya fara gunguni sannan ya bude motar ya fita, ya siyo ya dawo, Yana dawowa kafin ma ya Shiga motar yasa Shi a seat din baya, sannan ya zauna, be Kara magana ba har suka iso gida.


Tana nan kwance shiru sai kallo da ta kunna tana yi,da sallama suka shigo tashi tayi taje ta tarbe shi ta ansa kayan hannun sa,

Mas'ud yace'' ni kuma fah?

Wata hararan ta wurga masa, tayi gaba, abinta yayi shima da kayan Yana mata magana tayi banza dashi, sai da ta ajje ta fitar Dana fitar wa tasa a fridge ta dauki Wanda zatayi amfani dashi kawai, Shi kuma ya samu waje ya zaune Yana zuba, yana kuma cin guava,

tace'' Ka wanke kazar Ka gyara Ka daura, a takaice de kayi miya, na wuce ni"

A sukwane a sauko daga inda ya zauna yace'' ke kuma meye aikin ki? Ina zakije?''

" Zanje na Kula da Mai house ne"

Ta wuce ta barshi a wurin ya saki Baki Yana binta da kallo sai da ta fita daga kitchen din yace'' marar kunyar banza mijin da ba'a San Shi,Kode tana san shi? Oho de su suka sani"


Koda taje dakin sa yana wanka shiyasa ta fito parlour ta zauna ta kunna kallo tana yi,

Jitayi ya daura kanta a kafadar sa, yace'' me kike tunani haka?

Kallansa tayi tace'' ina tunanin sameera ne"

" Me tayi?''

Gyara kwanciyar ta yai sosai tace'' she's fall for mas'ud"

Ajiyar zuciya ya sauke, yace'' then?

" Gashi ya rabu da ita, yama yi blocking sim dinshi"

" Rabu dashi akwai lokaci"

Shiru sukayi suna kallo babu Wanda yayi magana, sai can ya bata labari abinda ya faru a kotu sai da ya gama,

tace'' Kar Abba yayi wa PA wani abu, ya kamata a buya har zuwa gobe"

" Good idea"


<<<<<<<<<<<<

Ana zuwa ko parking ba'a Gama ba, ya fita ya Shiga cikin gida, Mama na zaune tana kallan TV ga ganshi ya fado kamar Wanda aka jefo Shi Yana neman faduwa,da sauri ta taro Shi tana tambayar sa lafiya?

Babu abinda yake cewa sai ya cuce ni,ya ci amanata, ya ha'ince ni,haka kawai yake cewa, yana girgiza kai.

Mama tace'' wai Alhaji waye haka? Waye ya cuce Ka ne?"

Cikin wata masifa yace'' waye kuwa idan ba Inuwa ba, Inuwa PA da kika sani, shine yaja min komai, shine ma inaga yayi komai, ke shine ma"

" Haba Alhaji wanne Abu ne haka kami biyani dalla dalla mana,sai nafi ganewa ai"

Numfashi yaja sannan kuma ya koma ya jingina da kujera sannan ya bata bayani abinda ya faru kaf a kotu,

Huci ta fara, zuciyar ta wani irin tafasa take yi, tashi tayi ta goya hannun ta a Baya ta shiga zagaya wurin da suke,

tace'' almajirin yaran? Yaran da beda cin yau balle na gobe? Yaran da ko karatu be iya ba? Amma yanzu shine yayi wannan aikin, tabbas ya zama mutum ya gina kansa, wannan Shi ake Kira da daga taimako!

Wuri ta samu ta zauna tace'' Bari muga? Waye zai yi nasara mu ko su?"

Waya ta dauka ta kira Amma bata Shiga ba, dayar kuma ba'a daga ba, ajjewa tayi tana Kara Jin mamaki gami da jimama min wannan abu,

Dun kule hannun ta tayi tana jinjina Kai tare da bubbga kafa daya tace'' sai na koya maka hankali, sai na koya maka hankalin da ko masu kudi Ka gani zaka gudu, sai na sa maka tsoron mu a cikin zuciyar Ka yarda ko maka mantan sunan mu aka an bata sai Ka razana, ba'a taba ba,kuma baza'a fara ba"

Tashi tayi ta wuce Sama ta dauko wata wayar ta, ta Dan jima tana yi sannan ta ajjeta ta fito, kana gani zaka san abun ya Mata zafi sosai.



<<<<<<<<<<<<<<


"Ina taya ki murna kin samu transfern lettern ki, kije ki karba a wurin barrister Ibrahim,

Amina da taji dadi sosai tace'" Nagode sosai yanzu Insha Allah zanje na karba"

Yace'' bakomai haka zaman taren yake ai, Kar a yar da zumunci de"

Murmushi tayi sosai tace'' Insha Allah baza'a yar ba, Ka gaida min da ummu"

Dariya yayi yace'' ohh Ummu de zata ji,amma tana 9ja sai dai na gaida Madam"

" To Ka gaida ta nagode"

Ajiyar zuciya ta sauke Bayan ta kashe wayar ta, tattara abinta ta fara yi masu amfani sai da ta gama sannan ta fito ta Shiga office din barrister Ibrahim suka gaisa sannan ya bata ta fito.

Tana zuwa gidan kamar kullum suna zaune Yana de bewa Inni kewa Yana bata labari masu dadi yana kuma taya ta aikace-aikace, sallama tayi ta karasa shigowa,

Baffa yace'' Amina lafiya kuwa? Kin dawo da wuri yau"

Inni tace'' gashi kuma Yana yinki ya canza"

Ajje kayan hannun ta,tayi da ragar ta, ta karayin wata Kalar tausay, tace'' a wurin aikin mu ne, aka min transfer, saboda wani case da muka fara ba'a so muyi nasara shine aka min transfer"

Inni tace'' aka maki transfer ko kuma kika yiwa kanki ba?

Baffa yace'' Haba de, kin taba gani mutum yayi wa kansa transfer, kinsan fah aikin yanzu, zai iya iyuwa ma wani Mai kudin ne yace a mata"

Wani kallo Inni fa watsa mata, tace'' ina aka maida ki?

Jakar ta dauka ta dauko papern ta bude tace'' Gumel"

" Mtsww bansan kina fushi ba ai sai kin bar kasar shine zai nuna hakan"

Ta tashi tayi shigewarta daki, Baffa yace'' rabu da ita, bata San duk a cikin iya aiki bane, yaushe ne tafiyar?

Tace'' ko yaushe Baffa"

Yace'' to shikenan jeki huta"

Da Rana suna cin abinci ita de kawai cakulawa take, Baffa yace'' wai meye ne?

Tace'' Baffa inajin haushi ne,yanzu shikenan..."

Sai hawaye, rarrashin ta Baffa yayi yace'' shikenan kiyi hakuri haka Allah ya kaddara,banso ki sawa kanki damuwa"
Abincin ya dibo ya bata ya Kai bakin ta yace'' haaa"

Dan murmushi tayi ta bude bakin, daga nan fah yar Mata aka war tsake,daman tayi hakan Dan Inni ta yarda,Inni kuwa ci kanki bata ce, ko kallan su ma batayi bare ta sa musu baki.


<<<<<<<<<<<<

_London_


Tana kusa dashi tana kallan Uncle da shida gawa babu banbanci a wurin motsi, tana kallan Shi, kawai, yarda yake wani iske, Kai kace lafiyar sa qalau, kafar sa duk ta warke sai abinda ba'a Rasa ba,

Baba yace'' ya kama ta ku koma, ga aiki Ka baro a office"

Abie yace'' ai Baba bakomai"

Umma tace'' gaskiya ya kamata,kunga de jiki gashi nan, de sai dai saukin karaya"

Anty tace'' shikenan zamu tafi tunda korar mu kuke"

Abie yace'' wai da sati zamuyi"

" A,ah Ku tafi kawai, Allah ya bada lada"



('('('('('('('

Washegari a kotu, kowa ya zo karfe takwas kamar yarda akayi ta jiya babu mutane sai su kadai, kowa ya zaune sai anan Abba yaga PA jinya sunne me shi kamar ba gobe, sai gashi yanzu ya ganshi, kwafa kawai yayi inda aka fara shari'a cikin kware wa da iyawa da ga kuma shaidu sun shaaida hakan ga kuma kwararn takardun gaskiya a hannun su, sai da aka gama Jin da kudin da suka zuba duka.

Alkali yace'' Mahmoud zai biyasu dukkan kudin da suka kashe da kuma kazafin da ya masu shima dole zai biya. Zai ba kowannen su a kalla miliyan daya da rabi, rabi sabida Kaya sun tashi, sannan ya bisu da kudin kazafin da ya musu dubu dari dari, shima Wanda aka kawo kararsa zaka bashi Daidai ga abinda Ka basu wannan shine, nanna da zuwa gobe zaka sallami kowa wannan shine"

Sannan alkali ya hada Shi da police akan lalle lalle ya biya su kudin su,

( Ban iya shari'a ba, abinda yayi ne yaci ace ya biya kudin, ina neman afuwa idan banyi dai-dai ba, nagode)

Tashi yayi ya fita sannan Suma suka fara tashi suna fita, haka police din nan suka tusa kyeyar Abba, a mota ya dauko check yayi ta cikewa Yana Basu, su goma sha biyar ne,sai da ya bada kudi da yawa kowa ya sallame Shi takun ya Shiga mota ji yake kamar ya bada gaba kidaya dukiyar sa, Yana mota yaji ana masa waya, daga wa yayi masu aiki ne sukace sun Gama yazo ya sallame su, kashe wayar yayi batare da ya ji karshen zancen ba, jinshi yake duk wani irin, bema mara sarewa ba sai da yaga ana ta masa debit alert, kawai kashe wayar yayi tsabar takaici Yana sauke numfashi Kai kace gudun tsare yayi.








Bayan wata uku ...



By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt = _Akanji magana_



50



"Alhaji yanzu haka zamuyi ta cigaba da rayuwa? Babu aikin yi? Sai kudi da yake ta tafiya babu aikin yi? Ga rashin lafiyar ka kuma da wanne zamuji?"


Ajiyar zuciya ya sauke yace'' Saratu kina gani duk sana'ar dana fara sai dai muyi asara babba ma kuwa, kuma yanzu kike kawo min wani zancen ki"

Tace'' to mezai Hana mu Saida wannan gidan mu koma karami Mai three bedroom ya ishe mu a wadace de"

" Hakan bazai taba iyuwa ba kuwa"

" Aikuwa hakan shine daidain da zai iyu, sabida ga su yaseer nan suna makaranta, Ka Saida motar su Duka biyun,ga kudin transport shima wani abunne ga kudin abincin su, Haba de ayi tunanin ma, gashi duk wata ana bawa masu aiki kudin su, mu ba kudi ba sai kashe kudi wallahi bazai iyu ba"

" Saratu bansan a kara maimaita min abinda ya faru game da asibitin can,kina kallo har gida aka zo akace ba mallaki na bane, Wanda ya Saida min ba nashi bane,irin masu zuwa a siyar da filin karyar nanne, haka inaji ina kallo basu Bani ko Sisi ba, kudin magada ne shiyasa ba'a Bani ba, sannan kuma zasuyi aijin ruguza ginin da aka far, yanzu idan ba kina so a Kara cutar mu ba, me kike kiyi Kenan? Wannan gidan nawa Shikadai na mallaka,kuma a cikin sa Zan rayu har Allah ya dauki raina, abinda yake cikin zuciya ta ma kadai ya isheni, radadin da nake ji ba? Ciwon abinda nayi nake ji, kunyar kaina nake ji, nasan 'ya'yana idan suka ji wannan labarin har su mutu baza su taba yafe min ba"
Shiru yayi Jin wata, irin kuna da yake ji, a cikin kirgin sa, ji yake tamkar ana hura masa wuta a ciki, babu abinda zai sha ya rage masa wannan radadin, cikin wata murya mai rauni,

yace'' a watan nan zan aurar da Sameera koda kuwa bata da Mai sonta Zan hada ta da wani"

mama tace'' 'ya'ya sani zasu yi? Waye ma zai fada masu to?''

Yace'' ni Zan fada masu, irin abinda nayi,kada suyi koyi da halina"

Tace'' wasa kake, wallahi wasa kake, nidai bazan iya ba ato na fada maka, batun aure kuma zaka iya Mata, wannan kuwa na goyi baya dari bisa bisa, Amma batun wannan kin Saida gida da na kuma fada masu wannan sirrin namu ba Dani ba"

Daga haka ta tashi ta koma Sama runtse idan sa Abba yayi tun sanda Inuwa PA ya aci amanar sa, tun daga nan ya dawo cikin hankalin sa be Ankara ba yaji wani ruwa ruwa na bin kumatun sa Yana gangarowa wuyan sa,hannu yasa ya taba Jin daga kumatun sa yake ya tabbatar masa da hawaye ne ba komai ba, beyi mamaki Dan yanzu ya koma tamkar raguwar mace, tambayar Daya ina zai samu Ummusalma ya bata hakuri?

Da yake a parlour suke, Sameera data shigo gidan Jin suna wannan zancen yasa ta tsaya taji komai, a hankali ya karasa hawa Sama hat ta Shiga dakin ta, wayar ta, ta dauko ta sa numbern sa Wanda ta Riga da ta hadda ce ta a kanta, hawaye ne ya fara zurya a fuskar ta, bata damu ta goge ba,

tace'' kana ina yanzu gashi Abba zaimin aure da wani ba Kai ba, Kai nake so ..."

Sai hawaye ta kifa kanta tayi ta cigaba da kuka, babu Mai rarrashin ta sai ummu yau kuma ummu bata zo ba,da taje ma ta gidan su Basu dawo daga school ba, kukan ta, tayi tayi daga nan bacci ya dauketa.





('('('('('('('



Suna zaune su hudu suna cin abincin su hankali kwance sunayi suna hira abinsu duk da Rabin hirar su kadai sukeyi Banda ita.

Tace'' gaskiya Chattu Ka dameni,kabar ni naji da yajin da kuka cika mana a abinci mana,Amma sai zuba kake kamar me ma zance da, Haba Ka rabu da mu mana dame zamuji?


Yace'' to Allah yasa ma ba Mas'ud bane yayi abincin Mus'ab ne yayi a to bani ba"

" Fav kake Jin tsoron Allah, sai da nace wannan yajin yayi yawa yace wani ai kin fi San yaji, kema haka kike maku a spain"

Binaif yace'' kunsan Allah zan kora ku,Ku tafi part din ku, kunda meni"

Mas'ud yace'' yi hakuri kaji bb, wannan aljanar matar taka ce ai mai kama da jannu"

Tace'' sannu to, malamin Aljanun duniya, ya mu'allim din jinnu sannu ko?"

" Jiya tsabar daudewa bata San meye Malam da mu'allim ba"

" Shi yasa Naga Kai kasan aljana da jinnu ai''

Ta maka masa harara ta janyo plate din gaban ta, ganin duk sun ajje spoon din su, daman ita da hannu take ci,

" Ci ba kiba, sai kace gara, mutum yayi ta ci,yayi ta ci,yayi ta fama ko gajiya bayayi"

Mas'ud yace'' Fav kafiye sa Ido ina ruwan Ka"

" Bakasan wannan yarinyar bane ba, taaab Kai kasanta kuwa?cabb bb bashi labari da azumi"

Binaif yace'' wa? Bade ni ba, Kai de zaka iya amma nikam kunga nama yi nan"

Ya fada tare da tashi ya mata peck ya fice, mas'ud yace'' me ya faru da azumin? "


" Kai Kar kaso na baka labarin cin abincin ta, daman kullum wani katan bread sai ta cinye Shi tas da asuba kafin mu ya dafa abinci, befi tabar kadan ba, wannan sumun tabi kenan sai nan kuma..."

Spoon Daya ta dauka ta kwada masa, tace'' Bana San karya, daman salan rowa ne, wani indomie da rana, kuma baza'a dafa dayawa sai kadan"

Tashi tayi ta bar musu wurin, Mas'ud yace'' bashi sai na rama,

Mus'ab yace'' basa sunan wani film ba"

Mas'ud ya koma kujera yace'' wai me Ka tsaya yi a Abuja kafin Ka tafi wurin Umma Naga de tun kafin azumi ya saida companyn shi "

Mus'ab yace'' bakomai kasan garin akwai dadi,ina san garin sosai"

Tabe Baki Mas'ud yayi yace'' Kai kasani"

" Fav gist me"

" Kaifa gulma ne da Kai me kake San ji?"

" bb da aljanar ka"

" Munafiki Twinny to kuwa baza Ka ji ba"

Matsowa yayi kusa dashi yace kasan de nida kai ba'a Jin Kan mu ko? "

" Me Zan fada maka? Idan suka tun safe to sai yamma zasu dawo, sai ni kadai, Nima wata ran na bisu wata ran kuma na zauna, wai in fada maka, suka tafi suka barni? Ina bacci?

" Ina?"

" Paris, nake fada maka, wai sai da suka je airport aljanar nan ta kirani da wannan muryan ta ta,sai ca tace to idan Ka ga dama Ka tashi mu muna airport, Kai kaga wata mikewa danayi da kayan bacci ajikina kawai ta dauki jaka ta na goya daman na hada komai na, na dauki waya ta da wallet a dari na fito bamma rude gidan sai Mai gadin ne, ya rufe drivern kwa, kawai gudu yake ganin na fito a haukace, ina zuwa kuwa na Shiga, aikuwa nine last a shiga"

" Sun tashe Ka kaki tashi"

" Wai haushi taji na koma bacci Dana dawo sallah shine aka min wannan abu, kasan ta fa, to jarabar yanzu ta linka ta da"

" Amma ta hadu da wannan kawar ta ta ko? Mai shegen surutu kamar loro"

Gyara Zama yayi ya lankwashe kafa daya,Daya kuma a kasa,

yace'' ai in fada maka, muna sauka na hango su, da tafiya zasuyi su barni, aikuwa na gano su, muka tafi, muna zuwa fa da yamma sai ta Kira sahr wannan 'ya de data zo daukan mu muje gidan su, tun a mota ta ringa zuba take yi, takeyi, ko nace suke yi, Ashe ma 'yar uncle Felix ce,Ashe Kai Baka San Shi ba"

" Nasan Shi ban taba ganin saba de''

'' yawwa to 'yar sace''

" Daga nan muka je London zamu gano Bros sai aka ce sun dawo 9ja shikenan sai muka koma Spain, show ya barka"

" Kai dai bari daman naje''

" Sosai ma"

"Sai me kuma?"

" Ande ji wani wuri kude kam, ohh su glip da gulma sannu to"

Ganinta da bowl Mas'ud da yayi yasa Shi yin shiru sai da ta zauna ya koma kusa da ita yace" Zan sha, kinsa de ni dake tamkar hanta da jini haka muke forever and ever ne"

Mas'ud yace'' andeji kunya,kaima kaje Ka hada naka mana"

Pillow ya dauka ya wurga masa yace'' waye yaji kunyar? Reni ko?"

Shima dauka yayi ya wurga masa, yace'' Kai din fav bro twinny"

Aikuwa sai suka fara daga karshe ma tashi sukayi suna zagaye kujeru suna gudu, su Yusuf ne suka shigo da gudu su Duka ukun sukayi kanta suka rungume ta,

Ihun sune yasa su Mas'ud tsayawa yace'' Ku meye haka? Zaku wani zo ku wani rungume ta, sai kace Yaran da aka gudu aka Bari, dalla Ku sake ta"

Ummu ta mararai ce tace'' Haba yayamu, yanzu yaushe ta dawo mu Dade bamu hadu ba fa, shiyasa"

Wani fasa dadi yake ji duk sanda aka ce masa yaya, dawowa yayi ya zauna yace'' aww haka ne fah, Ashe anjima ba'a hadu ba"

Yusuf yace'' wata uku fah, ai ba wasa ba"

Yaseer yace'' to da waya ce wasa ne"

Bige Shi yusuf yayi yace'' Ka kiyaye ni, Naga reni naso ya Shiga tsakani tam,Kai da wannan yarinyar Ku raba kanku dani  "

Hada Baki sukayi shida Ummu suka ce " inyeee sannu babba"

Mus'ab yace'' kude San girman Ku ya maku yawa wallahi,kunji kunya de"

Mas'ud yace'' kasan ance sai Hali yazo Daya ake abota ko?"

Yusuf yace'' shiyasa muke abokan juna ai"

Ummu tace'' yaya salama yunwa nake ji"

Ummusalma tace'' aikuwa ba'ayi abinci ba, Nima na koshi nayi ba, wata indomie aka dafa mana, ba kwai ba komai sai shegen yaji, kuma babu lemun hada wa,sai de kije ki dafa maku wani abun"

Yaseer yace'' daga mana wake da shinkafa yau indomie muka ci fa da safe"

Tashi tayi tace'' haka za'ayi Dan uwa na"

Yusuf banza yayi dasu sunsan Baya son Shinkafa da wake shine zai ce a dafa Dan neman magana,

Yusuf yace'' kasan yayamu ko? Wannan yaran kullum sai sun bata min Rai, narasa me na tsare musu"

"Ai haka Yara suke aboki na, Nima haka nake fama da wannan yaran abin sai addu'ah kawai"

Mus'ab kawai Kai ya girgiza, Mas'ud kuwa yace su fita suyi ball, fita sukayi su duka Banda Ummusalma da tashi ta Shiga kitchen ganin ummu na aikin Dora abincin yasa ta dauko fruit salad tace'' Idan kin daura kizo ki Sha wannan, kafin kuci abinci,ki kuma daura da yawa basai an kuma yin wani abincin ba"

Ummu tace'' to shikenan"

Yoghurt ta dauka ta fito waje, ganin su suna ball amma Banda Mus'ab Shi Yana zaune Yana kallan su.

Zama tayi a kusa dashi, ta taba Shi,sai da ya juyo ya kalleta,

tace'' Wacece ita?"

Kallan ta yayi dakyau ita kuwa bashi take kallo ba, su take kallo,

yace'' banga ne ba?"

" Tunda kaji abinda nace ai shikenan, sunanta?"

Kallan sa ya koma zuwa wurin su, cikin muryan alamar dake nuna tsantsanr damuwa,
yace'' ban san taba, ban san sunan ta ba, ban san gidan su,Dan uwa, kawa, bansan komai ba, kawai ina ganin ta de a unguwar Dana zauna dake Abuja, tana yawan wucewa da yamma, tana cikin damuwa, ina San taimaka Mata,ban san ta inda Zan fara ba, kuma na dena ganin ta, naza ci kawai taimakon ta zanyi, Ashe ba haka bane, Son ta nake ban Sani ba, sai da na dena ganin ta a unguwar kwata kwata,I love her"

Cigaba da sha tayi tace'' da Ka fada Mata tun wuri da duk haka bata faru ba, yan zuma lokaci be Kure ba, Insha Allah za'a samu solution"

"But please don't tell Fav please! Ina san Naga shima ya samu wacce yake so"

Shiru tayu ba tayi magana, sabida ya tuna Mata da Sameera har yanzu tana can tana dankwan san, Wanda yanzu ya tabbata ya manta da ita, ajiyar zuciya ta sauke kawai tana ci gaba da kallan su, ji sukayi an turo gate an shigo da Kaya niki niki an kawo an ajje, drivern gidan Daddy ne,

Mus'ab yace'' Malama Musa kayan waye?"

Yace'' na Umman Alhaji ne ai" sannan ya koma, aikuwa sai ga tana ta shigo,

Mas'ud Yana ganin ta ya kwasu da gudu yazo ya rike ta, saura kadan su fadi badan ya rike ta ba da tuni sun hantsila, cikin bala'i,

tace'' Kai kaji yaro ne, yanzu Dana Fadi ba, ai sai dai wata mai tagwayen sunan bade wannan zainabun ba"

Sandar ta ta dauka zata kwala masa ya rike, yace'' Haba Hajjaty murna ce fa hakan, ai kinsa Dan da uwa idan maman Shi ta dawo haka fah yake Mata"

Kwace sandar tayi ta kalli su Ummusalma da mus'ab tace'' ehh gwara Kai ai, Dan albarka akan wasu da ko kallo Basu ishe ni ba, kuma a gidan nan Zan zauna ko ana suna ko ba'a sona, aji ma dakyau yawwa ana nuna min daki na"

Binaif da yazo yanzu dayake ba'a mota ya fita, ganin ta da yayi yasa ya turbune fuska yace'' ai banyi da dakin ki ba, kima koma inda kika fito Dan nidai baza ki zauna ki mayar min da gida gidan jarababbu ba"

Wani salati ta dauko ta rabfa, Kai mace wani ya mutu, tace'' yanzu ni zaka fadawa haka? Au..au..du..audu shakuru ni? Nice fa na haifi babanka,na haifi Ubanka,na haifi babar Ka, sannan nazo na haifi uwar Ka da ta koya maka rashin kunya, Allah ya jikanta, shine zaka ce min jarababbiya ko? Har kace mema yace?

Ya fada tana kallan Mas'ud, Mas'ud yace'' haka yace baza ki maida masa gida gidan....

Karaso wa yayi ya kai masa naushi ya goce yaje ya buya a bayan ta,

tace'' yau a gida nan zan kwana,Kai Bama kwana daya na, anan za'a jana'iza ta, Dan uban Mai gidan da matar mai gidan ko suna so ko basa su"

Takuma cewa'' kaga nuna min daki, a cikin gidan masu gidan nan"

Mas'ud kuwa kayan ta ya dauka ya, yace'' shigo na kaiki dakin ki"

Tana tafiya tana Mita, tsaki Binaif yayi ya zo ya zauna, Yaseer ya Kara so yace'' yaya Wacece?

Mus'ab yace'' kakar muce"

Yusuf yace'' amma tafiye masifa''

Ummusalma tace'' Idan taji ku kuda ita ne,Kar ku sani a ciki"


Suna cin abinci Umma tace'' wai ba ruwa a gidan nan ne?"

Yusuf yace'' jiya suka dawo, inaga yau kuma aikin gida sukayi"

Ummu tace'' ehh inaga yanzu zasu je su siyo"

Umma tace'' ai ni ina San haka, nayi tambaya,ayi farat a fada min amma masu gidan nan hmmm sai addu'ah"

Girgiza kai Binaif yayi, kawai ya tashi ya tafi dayan parlourn ya zauna, Umma kuwa daga murya tayi tace'' azo a siyo min ruwa dan kaniyar mutum"

Mas'ud yace'' Bari mu Gama daman za'a siyo wasu kayan sai muje"

Sai da suka sha fruit salad sannan suka fita Banda su ummu da suka wuce gida, aka bar Mas'ud da Umma kawai sukuma suka fita.


Sun Gama siyayyar su Ummusalma tace'' ina zuwa bari naje na dauko wani Abu"

Mas'ud yace'' so kike mu tafi mu barki,daman kin daddar mu"

Binaif yace'' muna nan kiyi sauri"

Wurin turare tayi, zatayi kwanar da zatayi ta hango Sameera ita da ummu suna zaba, kallo Daya tayi mata ta hango kwantacciyat damuwa a tare da ita, da wani irin speed ta juyo, ta dawo,

mas'ud yace'' ina abinda kika dauko?"

Matsowa tayi kusa dashi tace'' na kasa kuma banga masu aikin ba, zo muje Ka dauko, ina bb?"

" Ya tafi mota, muje ni na dauko maki,gaba yayi

Please Login or Register in order to submit comment