Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

family na a hade Dan Allah".

Kowa rike hannun sa yayi.
Binaif yace, "haba Baffa babu zancen hada mu da Allah kaifa babammu ne umarni kawai zaka bamu mubi".

Uncle yace, "haka ne Baffa Kai da su Baba duk Daya ne Kaine de Ka haife mu su kuma suka Rene mu ko cawa kayi su bar maka 'ya'yan Ka zasu barma".

Murmushi yayi Mai kyau yace, "kuma bazan ma ce ba har abada yarda duniya tasan Kai Dan sa ne haka zata cigaba da daukan".

Tare suka fito suka tafi gidan Baba sukayi Baffa ya ruki alfarmar a bashi su Baba.

Baba yace, "ni yanzu Banda iko Akan su ai sunyi aure fa ko Ka manta? Suna da ikon kansu mu namu idan sunyi ba dai-dai ba shine zamu musu fada".

Baffa yace, "nagode sosai de har yau ina godiya".

Baba yace, "ai bikin ma ayi acan a gidan naka shikenan ma kawai sun huta zirga zirga".

Baffa yace, "to shikenan Allah ya nuna mana".



('('('('('('


Sun tare a gidan su kowa Yana nan amma Binaif da su Mas'ud ba'anan suke kwana ba a gidan Binaif suke kwana da safe kuma sai su zo suci abinci anan.

Ummusalma kuwa da 'yar ta wacce suke ce Mata pretty Mas'ud kuma yace Mata genios  babu Wanda yake Kula Shi bare ma ayi dashi sosai suke samun kulawa wurin jegon su bata musu idan aka ce tayi yi take yi.

Suna zaune a parlourn kasa iya su ya su yau sati biyu Kenan dayin suna Pretty tana hannun Ummu Dan ita Dan tazo babu Wanda yake daukan ta ko Inni ce ta dauke ta a wurin zata zauna har sai an bata ita.

Mas'ud yace, "Biki saura kwana 10 hehehe waya ganni a babbar riga".

Ya fada Yana washe baki yana wani kwalalo Ido.

Ummusalma tace, "taaab waya ga Aljani a kwabet".

Dariya su Ka saka masa shikuma ya daure fuska.

Yace, "nifa da kika haihu kin ma fi surutu wallahi ko mutum be maki magana ba sai kin masa ni daman a rashin maganar ki Kian zauna har yanzu Dani ji dadi".

"Chatty kake Jin tsoron Allah Naga sanda bana maganar kafi kowa Jin haushi na yanzu ma?"

Neena tace, "taaab inaga Ya mas'ud sanda kuka hadu yarda kake bada labarin nan de lokacin tana magana".

Mus'ab yace, "Neena kin kuwa Santa a lokacin?"

Mas'ud yace, Kai kyaleta wani irin ta fimu sanin ta din nan".

"Shekara nawa kuka yi da ita ne?"

"Shekara har biyu mukayi da ita".

"Nima kusan hakanne ai amma nidai nasan tana magana in fada maka wataran har tazo ta tafi daga school bazata ce uffan ba".

"Caab Dani ne ai ko taab ai sai tayi".

Haka suka ci gaba dayi wannan yayi wannan yayi can kuma akayi shiru kowa yayi shiru.
Kallan su tayi taga kowa hankalin sa na kan waya kawai ta tuntsire da dariya kallan ta kowa ya dawo dashi gare ta da'alamar tambaya.

Binaif yace, "Mi Amor what's?"

Tsagaita dariyan tayi tace, "wallahi Chatty na tuna".

"Dana yi me?"

"Dan Allah karki tafi wallahi ina sanki nama fi Binaif san ki kinga nadena ce maki aljana na dena ce maki komai na dena tsokanar ki nadena fada da dake nidai Kar ki mutu kinga har Anty Ummusalma Zan ke ce miki karki tafi ki barni Dan Allah kinji I love you so much Walidan Inni kinga ma ko..."

Wurga Mata pillow yayi yace, "kuji sharri fa kida kina cikin halin wuya taya ma kika San wannan nifa bansan sharri nidama idan nayi aure ..."

"Babu Wanda zaije gidan Ka idan kuma Ka haihu babu Mai daukar maka yaran Ka".

Mus'ab ya Kara sa.

Uncle yace, "kasan Mas'ud har mamaki kake Bani? Ace Sam Baka da kunya ko kadan".

Turo Baki yayi yace, "Ku ai kunyi auren shiyasa amma zaku gani ai babu Mai zuwa min gida Umma ce kawai bata min fada har Inni da Baffa ma duk ba zuwa zasu yi ba".

"Da wa zaizo muzo aka koyawa 'yar yarinya ta surutu da Mita da fada da tsoro ko me?"

Tashi yayi ya yo kan ta  tana ganin haka ta mike tayi Baya kujera suka fara Binaif kawai kallan su yayi ya girgiza Kai ya cigaba da Danna wayar sa.

"La'ilaha illallahu Muhammadur rasulullah yanzu Dan lalace wa mai jegon ce take gudu? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un yau ni Zainabu Naga abinda ya fi karfina jego da gudu? Kaii abun nan da ake anya ke kika haihu kuwa? Waima ina su Iyayen naki ne ma wai? Yanzu Maryma din barin ki tayi kina dididar gudu haka?"

Binaif yace, "me kika zo yi mana? Kinzo kisa yarinya ta ta firgita ne ko?"

Kallan sa tayi da ranta da baci tace, "Dan zo Naga yarinyar da Baka fada min ba ko? Sai da ka fadawa duniya karewa ma sai da ta kwana sannan Ubanka ya fada min haushin da naji shine naki zuwa suna sai yau uban Ka ya kaga dama shima ya kawo ni".

Inni ce ta sauko tace, "Umma kece kika zo ashe  kuma shine suka barki a bakin kofa kina ta tsaye tun dazu aka ce gaki nan sai yanzu Kenan Kara so Umma".

Umma tace, "Alhamdulillahi sai yanzu na samu sirika 'yar arziki ai Bari na suka yi a tsaye ina ya rafka sallama amma a banza suna nan suna faman guje guje da danyen jego".

Murmushi kawai Inni tayi ta amsa jakar hannun ta tare da kama hannun ta tama ta wuri ta zauna ita kuma ta zauna a dan nesa da ita.

Tace, "Amma Inni anan zaki kwana tunda Baki zo da wuri ba".

Sude tashi sukayi Baya sun gaida ta suka hau Sama Binaif kuwa ko kallan ta be kara yi ba, Ummusalma ta kalli Ummu.

Tace, "wai ina su yusseer ne kusan Sati fa Kenan".

Ummu da gowa tayi ta kalle ta sannan ta sunkuyar da kanta.

Tace, "imm sun tafi fa wannan Kaduna wurin shiyasa kika ji su shiru".

Murmushin geden baki tayi tace, "ki Ramin su kice suzo nan dan 20 minutes".

Binaif yace, "Baki me tace bane ba suna Kaduna".

Bata kalle Shi bama bare yasa ran amsa ta ummu kawai take kallo ita kuma ummu taki kallan su tana kallan pretty.

Tace, "Kin Kira su ko kuwa?"

Wayar ta ta karba a hannun uncle sannan ta Kira su
Yusuf yace, "Hello ykk ya pretty".

"Lafiya qalau take zaku zo yau?"

"Ehh zamu zo Insha Allah".

"Kuzo yanzu".

"To shikenan gamu nan zuwa".

Kashe wayar tayi taki kallan kowa Ummusalma kuwa kallan ta kawai har ya Gama.

Tace, "meke faruwa".

Cikin sanyin murya tace, "Abba ne beda lafiya kuma sunce Kar na fada wa kowa shiyasa kiyi hakuri".

Bata ce komai ba ta kyale ta, Jin pretty ta fara kuka yasa ta dauko ta ta kawo mata ita Bata fara yi tana kallan ta.

Mas'ud yace, "saikin koya Mata kiwa ko? Kike wani kallan ta wai ke Uwar ta".

Harara ta Galla masa tace, "ina ruwan ka tunda Kai ba dauka zaka yi ba sai kayi shiru".

"Danna fada maki?"

"Bana so".

"Masifaffiya".

Banza tayi dashi ita kadai tasan halin da take ciki dan babu wata alama da ta nuna hakan. Basu wani Dade ba sai gasu nan sun zo da sallama suka shigo wani kallo da ta  musu yasa su tsaya wa a bakin kofa Basu Kara ba sun rigada sun san halin ta tun kuwa suna yara sun jima basu ga wannan bacin ran dake tattare da ita ba, Binaif ta mikawa 'yar ta tashi kowa kallan ta yake tana zuwa batayi aune ba ta kifa wa yusuf mari.

Yaseer yace, "ya..."

Shima nasan raban ya samu tana cigaba da kallan su, Dafe kunci sukayi suka sunkuyar da Kai".

Cikin tsananin bata rai tace, "Abban ku Kenan ba Abban Ummun ne ita Daya ko? Baza Ku iya fadan cewan Abba beda lafiya ba ko? Sai kawar Ku da Zama dolen Ku ko? Okay ko Dan abun da ya min ne yasa aka ki fada min".

dagowa Yusuf yayi yace, "dalilin Kenan yaya kiyi hakuri".

"To najima da yafe masa abinda ya min Ida ma shine saime kuma?"

Yaseer dagowa yayi ya kalle ta yace, "Anya yaya kina da zuciya kuwa? Anya zuciyar ki tana aiki? Kinsan me kike kuwa? Kin ma jima wato da yafe masa".

Wani banzan kallo ta wurga musu tayi tafiyar ta ya wuce daki tayi kwanciyar ta tana maida numfashi ta jima a haka  Binaif ne ya shigo ya rufe kofar ya zauna a kusa da ita.

Yace, "meyasa kika yi haka?"

"To su abinda sukayi yayi daidai Kenan Yusuf fa yaseer? Me zamu boye wa juna? Just because of ..."

Hade bakin su da yayi yasa ta tayi shiru bata Kara ba, Sai da ya nemi wuce gona da iri sannan suka sarara ya kwanta akan ta Yana sauke numfashi shafa kansa tayi ta fara yi sai da ya dawo normal.

Yace, "yaushe zamu koma ne wai nifa nagaji sati biyu fa ai ba wasa ba nayi kokari ko dan hug din nan ba min ba kike".

"Hmmm".

"Daya Kenan".

"Uhm hum".

"Biyu".

"Wai meye kake wani kirga abu".

"Babu komai kawai ina ga de rashin ki a kusa ni ya fara yasawa kin manta ni ne Amma bakomai karki damu Zan fanshe".

"To kayi hakuri".

"Meyasa aka Sawa pretty zulaihat".

"Kawai insan suna nan ne sosai da sosai shiyasa tun ina karama kuwa".

Murmushi kawai yayi ya rabo da ita badan ya gamsu ba sai Dan besan bata moment din su Yana Jin dadin haka.



Ana gobe bikin su ta shirya tsab suka fita ita dasu Neena da Ummu.


BY: ```Hijjart Abdoul```
       Cwthrt =ØÞ*<ØBßA BAKIN WAWA<ØBß*
   _Akanji magana_


  
     60



Basu dauki mota ba haka suka tafi direct gidan Maman Sadiq suka nufa.

Tayi mamakin ganin su ba kadan musamman Neena da taje suna bata ganta bata ga Inni ba da yake Sunan yayi jama'a kuma da wuri ya dawo sosai suka sha hira, suna cikin hira Ummusalma ta dauki pretty tace tana zuwa.

Gidan kusa da Maman Sadiq ta kwankwasa shiru babu amsa kara Knocking tayi namma babu amsa sai da tayi da Dan karfi sannan taji anyi magana, ita kuwa matar gidan gani tayi tunda wannan din nan ya tafi shikenan babu Wanda ya kuma zuwa sai Shi kuma idan zaizo waya yake mata ta bude ya bata abinda zai bata ya tafi.
Shiru tayi har aka zo aka bude.

Tace, "sannu da zuwa shigo".

Dan murmushi tayi sannan ta shigo a waje ta zauna ganin tabarma da kayan wanki da'alama wanki take itama Zama tayi suka gaisa sannan matar.

Tace, "kawo yarinyar muganta".

Mika Mata ta ita tayi pretty kuwa idan ta ras a bude take kallan ta itama kallan ta take yi tare da sa Hannu cikin nata babu abinda take hango wa game da yarinyar sai kamar ta da Binaif sanda Yana jariri kwalla taji ta taru a idan ta tana kallan yarinyar tana Mata murmushi da gowa tayi ta kalli Ummusalma dake kallan su.

Tace, "ya sunan ta?"

Murmushi Ummusalma tayi tace, "zulaihat".

Fadada murmushin tayi sosai tace, "kice itiyi nace".

"Itiyi kuma?"

Murmushi tayi dakyau tace, "takwara ta nake nufi".

Itama murmushi tayi tana cigaba da kallan yarinyar sai anan hawayen ya digo daga idan ta tasa hannu ta share tana maida sauran zubowa.

Ummusalma tace, "Mama lafiya?"

"Bakomai kawai ina tuna yaro na ne".

"Ayyyaahhhh sorry, shima Karami ne?"

"Sanda na tafi na barshi Karami ne amma yanzu nasan ya girma dakyar ma idan beyi aure ba".

"Kamar ya Kenan? Kin tafi kin barshi fa kika ce Yana karami mekenan?"

"Amma daga ina kike?"

"Gida nan makwabciyar ki nazo shine nake tambayar ta ta taba Shiga  tace bata taba ba tana de Jin motsin mutum a ciki shine kawai nace Bari nazo".

"Ya sunan ki?"

"Ummusalma tace".

"Suna mai dadi".

Murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta irin kunyar nan sai kuma ta dago.

Tace, "amma Mama meyasa kika bar yaran ki Tou".

"Labari ne Mai tsayi babu kuma Wanda yasan da wannan daga ni sai Hafsa sai kuma kawar ta".

"Wacece Hafsa?"

"Kishiya ta ce".

Irin mamakin nan tace, "kishiyar ki kuma? Shine zata raba ki da yaran ki tun yana Karami?"

"Kamar yarda nace maki labari mai tsayi".

"Amma mama baza ki iya Mai dashi gajere ba? Ina San nasani ko Zan iya taima maki".

"Salma kenan bansan taya Zan Baki labarin ba ban kuma san ya zaki dauki abin ba zurfi ciki na ne ko kuma San yaro na ne ya rufe min Ido bansani ba".

Hawayen ne ya zubo mata ta goge shi, Ummusalma tace, "Mama kome zaki fada min Zan fahim ce ki sosai".

Tsab ta kwashe komai ta fada duk da ta sani amma bata katse ta ba har barin cikin ta da tayi har samun wani cikin da komawan Rukayya gidan ta anan tayi shiru haweye na zuba a idan ta da'alama ta tuna abu mafi girma shiyasa ta zubar hawaye.

"Dawowar Rukayya gidan yasa na dena aiki ita take yi idan kuwa zanyi to tare zamuyi shakuwa Mai karfi ce ta Shiga tsakanin mu harta kai da bama maganar da Hausa sai da fulatanci babu abinda take so irin taga na haifi abin dake cikin na ga wata irin son yayan ta da take yi haka shima Yana san ta wannan abin yasa aka hadawa Rukayya tarkon sata Hajiya kuma ce ta hada wannan abun ba kowa ba hakan ya mugun bata min rai kuma nasan Hadi ne tun daga nan ya dena Kula ta sosai duk wani Abu Idan aka nema aka Rasa sai a zo dakin da take kwana za'a same shi tun yana Mata magana har yazo ya dena ko ta gaishe Shi Baya ansawa bata taba fada ba ta rike abin tsakanin nida ita har ciki na yayi girma yazo watan haihuwa muna zaune kullum da irin abin da ake fada masa muna cikin damuwa sannan ni kuma Bana iya fada masa sabida wannan zurfin cikin nawa da beda amfani ko kadan.
Kwatsam wata Rana da daddare suka zo  lokacin har na fara bacci dayake ba a daki na yake ba ranar suka tashe ni ita da kawar ta Hafsa tace zabi biyu zasu bani na farko idan na haifi yaran nan zan tafi na barshi su zasu Kula dani za'a nemi ni a rasa na biyu kuma idan na haife Shi ban tafi ba zasu yi ajalin abinda na Haifa sannan kuma suyi ajalin Alhaji sannan kuma suce nice nayi wannan abun. Nasan zasu aikata hakan yasa na yanke hukunci tafiya na barshi a ranar da na haife shi ina fito wa da ga asibitin aka dauke ni aka kaini can wani gida Ido na a rufe aka ajje ni gidan gidan kasa ne daki daya ne sai ban daki ba kitchen ma ko baranda babu ga zafi gidan a haka nayi rayuwa ta gidan ya kwarabe musamman da damuna amma sai dai suzo suyi faci facin sa da kasa suyi gaba duk wata suna aiko min da kayan abinci sai dai kadan ne Baya isa na wata dayan sai dai na can cana haka Ida ana ruwa babu inda zanyi girki sai dai nayi daki na sha wahala ni kadai tun ina damuwa har nazo na dena hatta ruwa shima na wata ake kawo min har na wanka da komai da komai fita kuwa kulluma a kulle nake sannan suka ce bani ba fita duk ranar da na fita to nayi ajalin yaro na da hannu na".

Anan ta tsaya ta goge hawayen ta.
tace, "gashi yanzu bansan wanne hali rukayya take ciki ba bansan ko ta shirya da yayan ta Mai son ta ba bansani ba ko yaran ta nawa? Allah sarki Rukayya she did a lot to me, Iyaye na kuma nasani Suma zasu ji haushi na sosai bansan ya zanyi ba ga yaya na".

Shiru sukayi Ummusalma ta Rasa abin fada ta Rasa taya zata ganar da ita cewan ita ce tasa aka dauko ta aka dawo da ita nan, ko kuma tace itace matar yaran ta ba yau ta tsici bakin ta yayi nauyi shikuma Binaif abinda yake tunanin akan ta daban ne dana kowa besan sabida tsananin son datake masa ya rayu bane hakan ta faru, numfashi taja ta ajje sannan.

Tace, "Mama ina ganin Anty ummi taji komai shiyasa ta dauki yaran ki ranar da kika haife Shi ta Hana kowa koda tayi aure tare dashi ta tafi ta bar kasar da shi ita ce ta reni shi har ya girma sai dai Allah be bata yaro ko Daya ba sai yaran da rike sannan kuma sai dai muyi hakuri".

Cikin mamaki take kallan ta kafin.
tace, "taya kika san itace? Bamma fahima ci inda zancen ki ya dosa ba".

"Mama wata Antyn Mijina ta taba bani labari irin yarda kika Bani komai naku shiyasa nasan kece kuma nasa itace yarda na fada maki haka ne naji labarin ta".

"Amma ke to Wacece?"

"Mama zaki san komai, amma Dan Allah kibini mu tafi".

Mama zatayi magana taji wayar Ummusalma na Kara shiyasa tayi shiru bata yi magana ba ga kuma Pretty da ta fara kuka, kawaici tayi ta ta daga wayar ganin Binaif ne".

Yace, "kina ina haka? Baki ce zaki jima ba ya kama ta kidawo fa".

"Nace to ko zaka zo Ka dauke mu, muna gidan Mamaan Sadiq".

"To ganin but wait, ba kukan Pretty nake ji ba bazaki dauke ta ba?"

"Wayar Ka ce tasa ai".

"Irin wannan Marta bawa haka? Zaki biye ni zuwa jibi ai ganin nan".

Murmushi kawai tayi ta kashe wayar mika ita mama tayi ta ansa gaba Daya sai taji kunya ta kama ta takasa shayar da ita a gaban ta. Haka nan Mama taji yarinyar ta burge ta sabida kunyar ta.

Tace, "ki bata mana sai kuka take amma ki Dan rarreshe ta tayi shiru kadan ba'a san shayar da yaro Yana kuka Sosai ki tashi ki Shiga parlour".

Tashi ta wuce Kan ta a kasa sai da dan rarreshen ta sannan ta bata ta koshi sai bacci goya ta tayi ta fito ganin tana wanki yasa ta je ta fara taya ta wanki ba yawa da wuri suka gama.

Mama tace, "gaskiya ba lalle bane na biki Bana san wani abu ya sami yaro na".

Murmushi Ummusalma tayi kawai bata kuma cewa komai ba ta tashi zata tafi Kenan wayar ta tayi Kara ganin shine yasa ta daga.

Yace, "ina kofar gidan Ku fito".

"Ka shigo to ni ina gidan kusa dasu Ka shigo nan din me farar kofa nan please!"

"Ohh! Keko?"

"Please".

"To ganin nan".

Dayake bayan sunyi wankin ciki suka koma ita kuma a waje tayi wayar shiyasa itama ta koma ciki sauko da pretty tayi ta kwantar da ita ita kuma mama kitchen ta shiga ta kawo Mata snacks da lemu.

Tace, "kiyi hakuri ko ruwa ban kawo maki ba".

Murmushi Jin kunya tayi tace, "laa bakomai dayake ai daga gida nake shiyasa".

Mama tace, "nikam ina Shan kunya sai kace wata sirikar ki".

Murmushi ta kuma tayi ta, tace, "Mama inaga gashi nan yazo zaku gaisa".

"Tou! Jeki shigo dashi Bari na dauko mayafi"

Tashi tayi ta fita ita kuma tayi hanyar waje bude masa kofar tayi ya maka harara ita kuma tasa dariya kawai tayi gaba da sauri ya shigo Yana kwafa har parlour ya shiga ya zauna a kusa da pretty sannan ya dauke ta.

Yace, "kawai ki kafa ajje ta a gidan mutane salan ta fado ta fasa Kai".

Waro Ido tayi tace, "yarinyar da ko cikakken juyi bata yi?"

Harara ya balla mata, murmushi tayi murmushi kasa kasa tace, "wallahi zanyi Zama na a gida ko na tafi Adamawa nayi wayon arba'in acan sannan nadawo".

"Naji wannan".

"Yarda fa".

"Banyi ba".

Shiru ganin Mama ta fito da murmushi a fuskar ta ta karaso zata zauna Kenan ya dago dan ya gaita da ta gaisuwar da ba'ayi ba Kenan kowa ya kame ita kuma zaman da batayi ba sai ma Kara Mike wa da tayi.

Kama biyu take hangowa a fuskar Shi Daya kamar ta Daya kuma kamar Wanda ko mutuwa tayi ta dawo zata gane shi shikuma babu abinda yake hangowa sai tsantsan kamar shi ga kirginsa da yaji Yana wani irin dokawa kamar ya fito zuciyar sa wani irin sanyi sanyi yaji tana yi sai faduwar gaba haka nan yaji ya kasa dauke idan sa Akan ta itama haka.

Ummusalma tace, "Mama Zaikai ga Baban Mai sunan ki".

A tare suka maida Idan su Kan ta
kowanne da alamar tambaya a fuskar Shi.

Binaif yace, "mekike nufi Kenan? Wannan ita ce kika Sawa pretty?"

Gingina Kai tayi alamar tabbatar wa.
Lineage Ido yayi ya Bude cikin a kanta.

Yace, "a'ina kika samu ta? Mene hadin mu da ita".

Kanta ta mayar kasa tana wasa da hannun ta.

"She's your mother".


Ba shiri ya mayar da kallan sa ga kanta itama Shi take kallo sun jima a haka babu Wanda ya iya magana daga bisani.

Yace, "Nasan kin san komai kin kuma san dalilin barin ta ta barni bayan Anty ummi tace min ta rasu please tell me everything".

Mama kuwa takuwa wurin Shi tayi tana kallan sa hawaye na zuba a idan ta ita de ko ba dan ta bane da gaske zata ke daukan sa yaran ta har ta bar duniya, kawai ta rungume Shi shida pretty dake hannun sa  lumshe Ido yayi ya Bude su akan Ummusalma dake kallan su. Jin yarinyar ta fara motsi alame zata tashi yasa tayi breaking hug din sai anan yani bugun da zuciyar sa take masa yaji ta dena sai wani sanyin dadi Mai kama dana Jin dadi dake ratsa jikin sa.

Ummusalma tace, "a lokacin da su Mas'ud suka bani labarin su tare da naka haka nan naji ban yarda su Hajiya ba hakan yasa na fara aiki a gidan saboda abu biyu na farko sabida Kai na Biyu kuma saboda idan ina aiwatar da komai nawa babu Wanda zaiyi tunanin nice sabida ina aiki a gida.
Zuwa gidan sai ya zama naji abubuwa da yawa Dan game da Kai da Maman ka, sannu a hankali nagane duk wata duk wata suna zuwa wata anguwa duk da wata na Daya a gidan da satittika nagane hakan sabuda zancen da suke yi ga kuma abina suke kulla maka wani zancen ba da Hausa take ba da yaren Bole take kasance war ta yare sai akayi sa'a na iya yaren sanda ina junior sosai kuma Dana ji sai naji ban manta ba duk wani abu da za suyi nasan dashi har business din da Daddy besan sunayi ba nasan suna yi ita da Anty da taimakon kawar su Bari na gidan sai ya Zama na bana Jin komai sai dabara ta fado min na nasa iya ladi aiki a gidan take dauko min maganar su idan da Hausa sukayi zata sanar min idan kuma da yaran su tayi zata yi recording ta kawo min a boye a haka har wata yayi ranar da za'a kai mata nasa Saminu Wanda suka ce su yusseer suka bita har gidan a daren kuwa aka  dauko ta aka kawo ta nan".

Shiru sukayi kowa Yana kallan ta ta dago ta kalli Binaif tace, "Sanka ne yasa ta tafi bar Ka bata a lokacin kana tsananin bukatar ta San ka ne yasa tayi haka bakomai ba babu uwar da zata haifi yaran ta ta tafi ta barshi a ranar Ka godewa Allah Ka samu Anty ummi wacce ta rike ka a matsayin uwa".

Wani hawaye ne ya digo daga cikin sa a diga akan Pretty yarinya sai ta fara kuka irin tana taya Baban ta kukan farin ciki kallan yarinyar yayi ya tashi ya kai mata ita sannan yaje wurin Maman shi ya zauna a kasa ya Dora kansa akan cinyar ta sai kuka kasa jurar kukan sa tayi ta tashi ta fice daga gidan ma gaba Daya ta koma gidan Maman Sadiq tana zuwa Ummu ta karbe ta ta goya ta Zama tayi itama ta fara ci abinci.

Neena tace, "ina kika je?"

Harara ta zabga mata tace, "inda kika aikeni".

"Haba Salma Dan Allah wai tunda muka hadu fa babu wani zancen arziki da ya taba hada mu wai laifin me nayi maki Dan Allah".

"Mtsww tambaya ma kike? Bakiyi komai ba".

"Haba dan Allah idan dande naganki har sau dayawa ban maki magana ba kiyi hakuri komai ya wuce ai yanzu".

Banza tayi mata bata amsa ba wato har sau dayawa ma ta ganta amma ba magana hakan yasa ta Kara kume wa da ita kadai tasan tayi abin ta sai da maman Sadiq tasa Baki sannan tace ta hakura.


Mama kuwa itama kukan take ta kasa hanashi bare itama ta Hana kanta,dakyar ta samu.

tace, "kayi hakuri Abdul am sorry".

Kukan ya tsayar ya dago Yana kallan ta, goge mata hawayen yake yi itama ta fara goge masa a tare suka sakar  wa da juna murmushi.

Tace, "yaro na Ka girma ko?"

Please Login or Register in order to submit comment