Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jal, ta rufe Coolern ta Mika masa,
tace'' kaina bawa ba kowa ba"

Karba yayi Yana wani dar waje baki,

yace'' sai na tuna sanda kika bawa Fav..."

Maganar ce ta makale ganin guda Daya jal a ciki, ya dago yace'' wannan ai rashin mutun ci ne meya hakan?"

Batayi magana ba, ta tashi taje ta wanke hannun ta, tazo ta zauna, tayi refilling,kome za'ayi ayi.

<<<<<<<<<<<<

Babu kowa a gidan suna zaune a daki suna tattauna magana iya su uku ne kawai,
Cikin wata irin fusata,

tace'' Wannan zancen banza ne, wanne irin Abu ne hakan? Ace ta gudu, ta balle kofa? Kai bazai faru ba inaaaa"

Tashi tsaye Anty tayi tana zagaye tace'" shekara talatin bata taba guduwa ba sai yanzu? Me take shirya wa kenan?"

Dayar matar tace'' Dana tambaya ance min batayi ne suka shigo unguwar suka dirar wa gidan"

" Barayin su mahaukata ne da zasu Shiga wannan ribabban gidan?"

Shiru sukayi babu abinda suke sai zagaye a dakin, kowa da abinda yake tunanin can,

Anty tace'' nikam nagaji da zaman jiran haushe Alhaji zai mutu na kwashi dukiya nayi ta kaina, ina so fa na ganni cikin daular da tafi wannan, insan naganni ina juyawa ina fanjama cikin manyan mutanen Mata, Amma Shi Naga besan wannan ba, ina dalili kawai mutun yayi ta zaune a gida kamar jakin jahili? Nagaji daman can ba San Shi nake ba"

Matar tace'' Hajiya bamu taba boyewa juna sirrin mu ba, ya kamata ace ki fada min yau dalilin ki na yin haka"

Zama Hajiya tayi tace'' Ban taba tunanin Alhaji zai so wata Mata ba Sama Dani, sai gashi yaso wannan 'yar fulanin, be fada min ba, amma ni nagane hakan, Yana San ta fiye da tunanin ki, tun daga nan na fara azabtar ta, sai na samu Allah ya zuba mata zurfin cikin mala'i tayi ciki har sau Uku ina barar Shi, wani zuwa da Zuwaira tayi Anty Kenan, kawai ta Bani shawarar na barta ta haihu da kanta zafa gudu tabar min gidan, daga nan sai kika bada shawarar a kashe dan kawai tunda shine zai Bani ciwon kai, sai kuma Zuwaira ta bada shawarar da wata shawarar sanini zata amfani yasa na bi Tata shawarar shine kuma data gudu aka kama ta aka Kai ta wannan ribabban gidan aka sa ta, kinji yarda akayi shine kike zuwa duk wata kike kai mata dan abinci naso ace wahala ta kashe ta da yunwa amma har yanzu bata mutu ba"

" Kuma bakwa tunanin wani yasan wannan zancen naku?"

" Sam Bama yi, tunda babu Wanda yasani sai ke"

Anty tace'' lokaci yayi da zamu kama gaba mu, tun kafin ma asirin mu ya tuno tunda ta gudu waya San inda zata tafi"

Hajiya tace'' shiyasa yanzu Nima nake so dukiyar sa"

" Idan kuka jira sai ya mutu to har asirin Ku zai tuno Amma Idan kuka kashe Shi fah"

Anty tace'' tabbas haka ne kisa ce ta kama ce Shi"

" Idan ya mutu kuma dansa bashi ba gadan sa, haka uwar sa ma"

Zama Anty tayi ta kalli Hajiya a tare suka furta" A kashe Shi kawai..."



By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt =: _Akanji magana_



```When life gives you a hundred reasons to break down and cry,show life that u have a million reasons to smile and laugh.
Stay strong.```

54



Wani makirin murmushi,Ya jima da sanin hadin da hadin bakin su, ya jima ya zargin su, Shifa ya auri Zuwaira ne dan ya kunta tawa Hajiya, Yana gani ai kawar tace zata ji zafin abun,ashe bakin su a hade yake wai yau Shi za'a kashe, murmushi yayi Mai sauti, yana tuna shawarar Yayan sa, dan wayar da yayi dashi ne yasa yaji komai ya tafi, ga kuma abin farin ciki da ya samu su Mas'ud, bezai bata komai ba,dukda ya tuno masa babban ciwon abun kaunar sa, a hankali ya wani runtse Ido ya bude Yana tuno duk wani moment nasu, yau ya hadu da yayan ta, bema san yarda akayi ya yarda zumunci haka ba,dole gobe yaje ya Kai gaisuwa.

Tashi yayi ya fita yarda babu Wanda yaji shigowar sa haka ya fita babu Wanda yasani sai dai yanzu Shi kadai ne, ya ansa key a wurin driver sannan ya yace yaje gida yau,

Wayar Binaif yake kira, a lokacin Binaif suna zaune suna cin abinci yaga Kiran Daddy, daga can,
Daddy yace ''Binaif Umma tana gidan Ka ko gidan ta ne?"

Binaif yace ''tana gidan na"

Daddy yace ''kai kana ina?''

"Ina gidan Baffa"

"To shikenan"

Kashe wayar yayi ya dauki hanyar gidan Binaif, koda yaje a zaune ya ganta tana cin abinci tana kallo, da'alama kawo mata akayi Dan yaga cooler a gaban ta,
Da sallama ya shiga, ta amsa ta ciga da abinda take yi,

A kasa ya zauna,
yace ''Umma ina wuni"

" Lafiya, ina ce kaman ta hanyar gidan dan naka"

" Umma ya za'ayi na manta kuma"

" Yoo naga tunda nazo ba'azo an gaida ni ba shiyasa ai"

" Umma jiya fa kika zo"

"Ai yanzu naga rana ta fito"

Shiru yayi ganin yau a Sama take, sai da ta Gama cin abincin ta,
tace'' Yanzu ma ba zuwan Allah da Annabi bane, kafin ka zo Dan uwan Ka ya sanar min komai da komai, kuma abinda ya yanke yayi daidai kaji ai"

Sunkuyar da Kai yayi bece komai ba sai
yace "amma Umma zaki koma gidan ki ko?"

" Bazan koma ba"

"Umma ya kamata ki koma, namma fa gidan jikane ba gidan danki ba"

" Ohh! Bukulu zaka min, idan Baka sani ba, kasani gidan nan wani abincin suke ci Mai dadi yauma wata Kala Kala aka mana,irin 'yan can Mai dadi, shayi ma kadai dadi ne dashi bare abincin su, aitun tana can take mana abin dadi"

"Umma kinga be kama ta ace ni Ida zan gaida ke ba,kullum sai nazo Haba Umma Dan Allah kuma kinsan shima yaya Baya zuwa gidan 'ya'yan sa yanzu idan yazo shima nan zai zo?"

"Da wannan naji zan koma, dan kace baban su amma da Kai ne bazan koma ba"

"Nagode"

"Gode wa Allah"

Be wani jima ba ya tafi suna gama hira ya wuce.


('('('('('('('

Suna zaune a tsakar gidan bayan sun gama cin abincin su, sai hira ake da raha,

Mus'ab yace ''wai taya kika hadu da ita?"

"Kawai haduwa mukayi a asibiti shikenan muka kulla kawance shine kuma take fada min tayi zaman Abuja kaza da kaza waye da waye shine fa kawai na tambaye ka unguwar daka zauna shine Ka fada, Ka wani kwafsa"

"Dana yi me?"

"Mtsww tace kamar na sanka din nan ai sai kaja ta da hira ehh wallahi nima ganin sani nake maki waye waye amma sai kayi shiru"

"Banni kawai am speechless"

Mas'ud yace'' wai daman wannan yarinyar 'yar renin hankali wani ta kalle mu ta kallli wannan yarinyar tace kannai, ta ban haushi"

Amina tace ''ya Mas'ud tambaya fa tayi"

Binaif yace '' kaci sa'a da bata ce Kannan bane danine haka zance ehh kannai na ne sai me aciki"

Mas'ud yace ''tab da anyi ruwa da kankara kuwa, bawannan ba Fav yaushe zamu je mu Hira ne wai?"

" Twinny baza ni da Kai ba"

"Kar Allah yasa aje din, ya sunan ta?"

Ummusalma tace ''sunan Inni ne da ita fah"

Amina tace'' tab akwai girmama wa Kenan ko, sunan uwa guda?"

Shiru mas'ud yayi Dan beza ci haka ba, Sam yaso ace ba haka bane da sai tayi kuka idan suka hadu,dukd hakan ma ba kyale ta ba zaiyi,

Ummusalma tace ''Zafa kaje dubiya Abban na beda lafiya"

"Abban ki kuma?"

"Haka take fada,Abba na, Abba na, komai Abba na, kaga Kenan ya dawo Abban ku"

Mus'ab yace ''yes of course Abban mu"

Tashi Binaif yayi yace '' ga me tafiya"

Kallan Ummusalma yayi Yama ta alamar ta same Shi a mota

Mas'ud yace'' zaka tafi baka yiwa Baffa da Inni sallama ba"

Har ya kusa zuwa kofar fita yace'' ina ruwan ka ne"

Bakin sa yayi yayi alamar zip, yace'' babu water na a ciki"

Mus'ab yace'' Kai Kam baza Ka taba dena magana a cikin hurumin da babu ruwan Ka"

Ummusalma tashi tayi ta fita,

" Sai lokacin daka dena munfirci Zan dena"

"Waye munafikin"

"Wanda ya tsargu Ida Ka tsargu kuma tou, amma ni bance munafiki ba"

Kwafa yayi yace'' kama ce,wallahi yanzu nan nace a fasa bikin, daman ba zuwa wurin budurwa kake ba,naje na hada maka bomb din da zata ji Baya san Ka, sai anzo biki tace ta fasa"

"Zafa Ka iya ko"

"Sosai ma"

Ganin Shi a baya yasa itama Shiga bayan ta zauna, ganin tazarar dake tsakanin su yasa ya kalle ta ya kalli space din,

yace ''ni zan matso ko ke zaki matso"

Turo baki tayi gaba, sannan ta matso daf dashi, be ishe Shi ba sai ya kuma janyo ta jikin Shi,luf tayi a jikin sa Yana daga ta yayi ya cire mata hijabin ta ya kuka rungume ta yana shafa Mata baya, cikin irin muryan nan Mai kama data Yana Jin bacci

yace ''sai yaushe?"

Rufe idan ta Dan kwanciyar tayi Mata dadi sosai har wani bacci bacci take ji, bude idan ta tayi ya fara wasa bottle din rigar sa,
tace'' duk sanda ka ga dama"

Rike hannun ta yayi yace'' baza ba ki daga min hankali ba, kuma ki tafi ki bar ni yau zanyi missing"

Shiru tayi bata ce komai ba yace'' mi amor"

Tace "yau meye fassaran Shi please"

" My love"

Kallan shi, tace'' my love?"

"Ehh"

Tana kallan Shi shima kallan ta tace ''tun yaushe Kenan?"

"I don't know,kawai ji nayi na kamu, kefa?"

Kwanciyar ta tayi tace'' ba kamu wa mayi ba,harbu wa nayi"

"Really?''

"A'ina na harbe ki"

Shiru tayi ya matse ta, tace'' baby na Yana kuka fa"

Sakin ta yayi yace ''kin ma fini san wannan babyn"

"To kar naso Kaya na?"

"A'a so abin ki,wata nawa ne"

"Uku"

"Laa tab kice wata ba'ita ba biki"

"Hmmm bari za'ayi sai an gama suna sannan ayi bikin"

"Wacce yarinya ce yake nema?"

"Sameera ce"

"Mas'ud"

"Please Baby idan kaje gida kaje gidan su ummu idan kaje please Ka neme wa Yaya auren ta nasan Baban ta zai ba shi"

"Meyasa kika ce haka, ummu she's just 17"

"Amma zata iya zaman aure ba"

"Please kidena it can't be possible"

"Ummu na san uncle din ta,shima uncle din ta nasan ta, yusuf ada Yana San ummu but lokacin da yaji komai lokacin ya yanke shawarar bazai bar ummu tayi saurayi ta ba kodan uncle, kaji yarda abin yake, Shi Yusuf ya Riga su Jin komai daga wurin Antyn Ummu"

"Shikenan yarda kika ce"

"Yawwa fa yarda akayi bikin mu Suma haka za'ayi nasu,a daura aure take Kula da mijin ta that's all"

"Mus'ab fa"

"Wannan rabu dashi zan San yarda akayi"

"Baby please Ka bar wannan shafa bayan babu dadi"

"Bari to na zuke zip din sai nayi dakyau"

Fara wa zugewa yayi kafin ta farga har zuge mata zip din, a sukwane ta tashi tace'' haba Dan Allah baby na tace bata so fa kabari nikam"

Janyota yace'' idan to zo muga babyn, wannan babyn tafi ye cin"

"Yanzu ma yunwa nake ji"

Ware ido yayi yace'' yaushe yaushe muka gama cin abinci"

Turo baki tayi tace"Sake ni nikam, tafiya zanyi"

Hade bakin nasu yayi,tuni itama tafara kawo charge sai da ya kashe Mata jiki bata da ko digon karfi,
yace'' mu tafi gida?"

Shiru tayi tana sauke numfashi,bata da muryan ma da zata bashi amsa sai girgiza masa Kai da tayi alamar a'a,

Ajiyar zuciya ya sauke Yana cigaba da shafa ta, shine harda su balle bra, kasa Hana Shi tayi,don bata da karfi ko digo a jikin ta,

Sunkuya wa yayi yace'' nayi?"

Ganin idan ta a rufe yasa yayi wani munafikin murmushi, ya cigaba da abinda yake,

Mas'ud ne ya kwankwasa glass din motar, tsaki yaja,ya Dan yi kasa da Shi glass din kadan ,

yace ''meye?"

Mas'ud yace "bakomai kawai de naga lokaci yana tafiya"

Tsaki yaja ya mayar da glass din ya zuge, yasa mata hijabin ta, sannan suka fito, ko kallan Mas'ud beyi ba ya wuce Shi, suka shi,

Mas'ud kuwa yace'' oho de koma meye"

Shima ya Shiga, a waje ta tsaya shikuma ya wuce ciki ya masu sallama zasu wuce,

Baffa yace ''ka dauki matar ka Ku wuce"

Murmushi yayi yace'' a'a Baffa zata zauna anan ko zuwa gobe ne ma"

Baffa yace'' ai muma goben zamu wuce Gumel daman rashin lafiya Innin kuce shiyasa muka zo nan din Amma Insha Allah gobe zamu wuce"

Binaif yace'' to goben idan Allah ya yarda sai nazo na dauke ta,amma zamu wuce da su Mus'ab"

Baffa yace'' to shikenan hakan ma yayi daidai"

<<<<<<<<<<<<<<


Suna zaune harabar gidan, suna Shan iska, Dan babu batun nepa jiya aka zo aka tsige ta, Sameera dasu Yusuf suna zaune kowa da abinda yake,

Mama tace'' kudin masu aiki"

Numfashi yaja ya ajje, yace'' zan bayar ko zuwa gobe ne"

"Ina kudin da ka Ka Ciro jiya Mai uban yawan nan"

"Ya ilahi! Kin manta da Shi na biya masu nepa?"

"Duka uban kudin nan ka basu? Zaiyi kusan dari biyu"

" Na bawa su Yusuf Arba'in, na bawa Sameera goma, na basu dari da talatin,ashrin din na bawa mai gadi"

"Gaskiya Kam"

Jinjina kai,kawa tayi,

Yace'' idan an sallame su, shikenan sai su tafi, dan bazan iya ba duk wata ana basu kudi"

"Suna tafiya ina tafiya ta, wallahi bazan iya ba, me kake nufi? Cab! Nifa Kenan zanyi aikin gidan nan"

Be kula ta ba, ya kalli Sameera da take rubuta project,
yace ''Kina da Wanda kike so?"

Gaban taji ya fadi, tazaci zai nemeta Ashe ba zuwa zai yi ba, a hankali ta girgiza kanta hawaye na nema zubo mata,

yace'' wani zaizo yayi maganar zuwa gobe, kira na de yayi a waya daman idan kina so wani ne tunda bakya San wani kuma to falillahil hamd"

Wani siririn hawaye ne ya zubo mata, haka nan taji gaban ta ya Shiga faduwa, ambatan Allah kawai ta fara yi, daga karshe ma tashi tayi ta koma daki,suna su yusuf kwashe kayan ta sukayi suka Shiga dakin, babu Wanda ya iya ce Mata uffan kawai tagumi sukayi suka zuba Mata Ido.

Har akayi magariba akayi isha suna nan Basu tafi sai dai idan lokaci yayi suyi sallah su dawo basa ce mata komai sai kallo, sun dawo daga sallahn Isha Kenan sun koma dakin Sameera sai ga ummu nan,

Yusuf Yana kallan ta yasab taci kuka ta gode Allah,
yace'' mene ya faru?"

Zama tayi tana kara goge hawayen ta,
tace'' aure za'a min"

" Then what?"

Yaseer yace'' dawa?"

Tace''da uncle fa"

Murmushi Yusuf yayi kawai, yace'' to sai me kuma? Dan za'a maki aure da Yaya bakomai bane ba, kawai ki yarda ki gode wa Allah kin san da Wanda za'a hada ki, look at Yay Sameera bata san da wanda za'a hada ta ba, bata San sunan sa ba, bata taba ganin Shi ba, kuma za'ayi auren"

Yaseer yace'' ehh gwara ke sau dubu tunda he's your favourite, you loves him and he loves you too,mene na kuka banga abin zubda hawaye anan ba"

Yusuf yace'' haka ne,ummu karma ki wani ce bazaki yarda ba,ko kiyi musu dasu kawai ki yarda tunda kinsan Shi idan kince bakya San Shi na soyayya San dakike masa daga yanzu kike kallan Shi ahakan"

Shiru ummi tayi tana Jin su, a hankali ta sa hannu ta goge kwallan ta,
tace ''thank you"

A tare suka hada baki wajen cewa'' first time in history"

Duka ta kai musu suna dariya, tace'' ku tashi Ku fita"

Yaseer yace'' angama matar big bro"

Yusuf yace'' ai yanzu kin koma Anty,ko yaya?"

Tasowa tayi tace ''Allah Bana so ku fita Ku ban wuri,sanda nace ina so ai ba fada ba kuka yi"

Fita sukayi suna tsokanar ta, kusa da Sameera tazo ta daga ta,
tace'' yaya sameera, ki dauka kece a matsayin ni, ki dauka kinsan wanda Abba zai hada ki dashi, Ka dauka kinsan n halin shi, you told me Wanda kike so sau biyu kacal kika taba ganin sa, sai haduwar da kuka yi a Sahad, uku Kenan, taya kuma zaki so Shi? Mutumin da Baki San halin shi ba"

Tashi Sameera tayi, cikin sanyin murya tace'' ummu sau uku muka taba haduwa, amma muna waya, Yana da kyan hali na lura da hakan, beda wata matsala yana da abindm dariya barkwan ci gashi da mita duk nasan hakan, Amma bansan ya akayi zuciya ta, ta kamu da San Wanda be Sona ba, Mai son Wanda be San inayi ba, mesan wanda be damu Dani ba"

"Kide fadar haka"

"Ummu kenan na fada masa fa, Nan da wata hudu aure na amma ko magana ya kasa min, bare ..."

Kuka ne yaci karfin ta, ta kasa fadar sauran abin da zata ce, girgiza Kai ummu tayi,

tace'' gobe za'a daura aure na,ki fadawa su yusuf Bari na tafi"

Fitowa tayi tagan su a parlour,suna ganin ta, Yusuf yace'' da girman kujeran ki"

Harara ta Galla musu tace'' azo a rakani''

Yaseer yace'' ko Baki fada, idan daukan ki ma kika ce ayi sai ayi ai"

Sun rakata sun dawo yaseer, yace'' Allah sarki an maka kwace"

Banzan kallo ya watsa masa, yace'' Bana San munafinci, san nata da nace ina yi da ne, sai kuma she's not my mate"

Yaseer yace'' wai aure tab Allah sarki yanzu sai a school zamu ke hadu wa fa ko?"

"To Dan gidan ku a gidan ta zaka ke zuwa kome?"

"Wallahi daza'a barni gidan Zan koma da Zama kasan Allah''

"Kaima san Ya mas'ud ba bare zaiyi"

"Ai wannan Dan hana rawar gaban hantsi ne"

"Abokin nawa"

"Shidin"

"Aikuwa zai na sanar dashi"

"To meye ne ina ruwana"



Sai bayan Isha suka tafi gida, suna Shiga Kenan suka wasu hadaddun motoci guda uku iri daya gasu bakake har wani sheki suke yi dukda dare ne amma fitilun wurin sun haska su,

Mas'ud yace'' woww bb wannan fa"

Sai da suka fita sukaje wurin motar Binaif yace'' biyu nawa daya na Mi Amor"

Mas'ud yace'' wacce mi amor din? Tama isa?"

Murmushi kawai yayi ya zaro key din guda biyu ya Mika masu yace'' Happy birthday"

Ya wuce ya barsu a wurin, sanda rewa sukayi suka kasa motsi sai yayi nisa Yama kua Shiga parlour suka taho da gudu suka rungume Shi,

Mas'ud yace'' amma shine Ka..."

"Shishish, bansan Jin komai"

Mus'ab yace'' bb mun gode sosai mun..."

"Haka ma godiya ce, farin cikin K 
u har yau har gobe shine nawa.

Zansu yayi suka Shiga ciki, Umma na zaune ita kadai tana kallo, abin ta,

Tace'' sai yanzu zaku dawo?"

Binaif yace'' wani abun farin ciki ne ya same mu Dan Allah yau karki yi fada kinji Umma"

"Jarababbiya Ka maida ni Ashe bansani ba Ka kyauta"

Binaif yace'' ai idan ana neman masiffiya an same ki"

Cokalin abinci ta dauka ta wurga masa tace'' Dan zakaraw'a kai yanzu zaka cewa Safiya jarababbiya ne? Ka rena ni, gidan nan Zan Bari bazan zauna ba"

Tabe Baki yayi yace'' Dade yafi dan Bana so daman ki zauna yaran su koyi fadan ki, kinga Baban su Mas'ud yau muka hadu da su da maman su"

"Alhamdulilla, Alhamdulilla, Alhamdulilla, Allah Kaine abin godiya, taya hakan ta faru?"

Binaif tsab ya bata labari, Umma tace'' Kai kaga, Abu sai kace almara, Ikon Allah Kenan, azo a kaini Naga Iyayen 'yan albarka"

"Haba Umma da Daren nan? Ai sun rufe gida yanzu"

"Allah ya kaimu gobe"

Mas'ud yace'' bb banga Ka Shiga daki ba"

Mus'ab yace'' bafa ta nan"

Umma tace'' ahaf ina zai Shiga daki ba mata Ashe shiyasa bata dawo ba tana nac wurin Iyayen ta hakan ma yayi kyau ai"

Banza yayi dasu ya koma doguwar kujera ya kwanta ya rufe idan sa, Yana Jin su suna masa tsiya ya kyale su, a haka bacci ya dauke Shi yasan idan yaje daki ma ba bacci zaiyi ba, har suka Yana kwance a parlour ranar nan yayi bacci.


Washegari da safe suka tafi gidan Baffa har Umma sai da aka daura auren ummu sannan su Baffa suka wuce Umma ta koma gidan ta, Daddy kuma ana daura aure ya wuce airport ya tafi Adamawa sunyi murbab zuwan sa sosai shine yake fada masu auren da aka yi da kuma samun Iyayen su sosai hakan yasa su murna,be wani jima ba ya dawo, kasancewar tafiyar jirgi ce befi mintoci ba yasa yayi sauri,

Matan sa ya gani a zaune suna hira tare da 'ya'yan su guda hudu, ya kallo yaran kawai girgiza Kai,

yace'' Ku same ni a Sama"

Ya wuce dakin sa, sai da yayi wanka ya shirya ya fito ganin su da yayi a parlourn sa ga kuma abinci, ya zauna ya dauki remote ya fara zanja channel sai da ya Kai labarai tukun,

yace'' Mas'ud da Mus'ab Wanda suke gida nan ada kafin su koma gidan Umma nasan da cewa kune kuke aika ta komai..."


By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt = _Akanji magana_



55

Shiru yayi tunawa da wani abu da yayi mafu soyuwa a zuciyar Shi, kafin ya lumshe Ido ya bude.

Hajiya kuwa da Anty Rasa abin fada suka yi ji kawai suji ya gama abinda zai fada su fadi nasu.

Yace ''Hafsat, Zuwaira nasan duk wani kallu kullan Ku, a yanzu ni tsoro kuke Bani, sabida haka ga wannan kowa yaje yayi business din sa da yake so kowa ya kama gaban sa".

Ya fada Yana Mika masu wata envelope mai kyau da ita, har zuciyar su suka ji wannan Batu jiki na rawa Hajiya ta amsa ta dauki nata ta bawa Anty.
Anty harda durkusa wa ta fara godiya itama Hajiya haka.

Hajiya tace ''Alhaji mun gode sosai Allah ya Kara budu".

Anty tace "Allah yasa kaci wannan takarar deputy governor din da kake nema".

Dariya suke bashi sosai, dukda Baya san yayi amma sai da yayi murmushi ya.

Yace ''Idan zaku tafi, ku tafi Ku kadai kubar min yara na".

Hajiya tace ''Haba Alhaji Muda zamu tafi business wasu kasashen saro Kaya taya zamu tafi da yara kuma?"

Anty tace ''su mana me? Su ba Yara ba ba komai ba?"

Murmushi kawai yayi ya Basu wurin ya tashi ya fita yana Dariyan shi shika dai.

Anty tace ''kinga Bari naje yanzu yanzu na duba Naga wanne jirgi ne zai tashi da kudin wuri na nayi booking".

Hajiya tace "tuni ma da me zamu kira kuma tashi zamuyi ai da kudin mu zamu saro kayan ma wannan kuma sai mu ajje sai mun dawo".

Anty tace ''china zani nikam".

"Ahh ni Dubai zani".

Fitowa sukayi kowa ya Shiga daki yayi booking flight Hajiya ita da yamma ta samu,ita kuma Anty sai gobe shima sai taje Abuja. Dayake Hajiya sai sunje Abuja sai kawai Anty tace zata bita.

('('('('('('('


Suna zaune su Duka a gidan Umma, bayan sun dawo daga daurin auren Ummu,

Ummusalma tace ''yanzu Umma ai da kin koma mun tafi tare".

Umma tace ''ke rabani da gidan da babu rahama babu iska ko kadan, babu wurin shakar numfashi window an kama an garke, labule an sake Shi daki ba Hasken Rana sai na lantar ki, bazan iya ba ga gida na kana waiga wa zaka ji iska, ka fita waje Ka bishoyo nan, idan naci gaba da Zama a can gawa ta kawai za'a dauko".

Mas'ud yace ''hmmm Umma Kenan ai kinga gidan nan takaici ne a cikin Shi fal, damma ba'ayi haki ba kinan nida da nake da Asthma kullum sai ta tashi".

Binaif yace ''kun dame ni fa".

"A tashi a tafi daman banne mi mutum ba sai da aka ga na gyara gidan nawa sannan za'a ce wani abu".

"Matata ta gyara de".

"Muna Mata de, ai wannan ba matar arziki bace".

"Matar tsiya ce Kenan ko?''

"Oho de, ace har yanzu ba amo ba labarin samun ciki yanzu da a watan da akayi aure a watan ake samun ciki amma banda ita ko nace banda ku ehh nannan wata wacce akayi auren Ku tare a kauye ciki ne da ita wata hudu zuwa biyar har ya dan tasa abin ta abin sha'awa da ita baku ganta ba wallahi".

Mas'ud yayi karaf yace ''zaki sha mamaki Hajjaju idan nayi aure, ke dai bari sai 'ya'ya sun yi wayo sun girma da wayon sa tukun zasu haifi na fari ai idan nayi aure za'a..."

A tare Mus'ab da Binaif suka jefe Shi Mus'ab da pillow Binaif da remote.

Mus'ab yace ''wai sai yaushe kunya zata ishe Ka ne? Ayi yaro bashi da kunya Sam, Kai da ko nema auren har yanzu ba'aje ba kayi ta cika Baki".

Umma tace "ohh! Dan ya Fadi gaskiya? Shine abu? Gaskiya ya fada ai idan bata yi

Please Login or Register in order to submit comment