Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

birgeta don a yarda umsalma ta fada mata Yan uwanta tace mata.
Bangaren su kuwa,sun kasa sanar da ita cewa zasu saura wata daya su koma,sun kasa tunkararta da zance tafiyar su ya kamata ace tasani tun yanzu amma kuma a duk sanda zasu sanar da ita basa iya wa ahaka suka fara exams daga su har ita, su suna zana final exam ita kuma tana zana ta first semester na year four, sun rigata gamawa kasancewar su masters ne,kuma ita tana course biyu ne. A ranar da suka Gama a ranar sahr ta tafi.
Ta shirya don taje wurin aikinta ta fito ta gansu bakin campus fuskar su kawai ta kalla tasan akwai damuwa, Bama su lura da ita ba kowa Yana sakawa da kwancewa a zuciyar Shi,zuwa tayi ta zauna kujeran dake facing din juna,kallansu tayi

tace' inaji,
Sai anan ma suka lura da ita,har tazo ta zauna amma Basu sani ba,
Numfasawa mus'ab yayi

yace' gobe zamu tafi,
Jin maganar tayi wani iri a bakin shi, maimaita maganar tayi

tace' go..be,zaku ta...fi?
Gyada Mata kai sukayi,gani sukayi ta tashi zata tafi da sauri mas'ud ya riko hannunta

yace' bamusan yazaki dauki maganar ba shiyasa,Amma kiyi hakuri don Allah,ya fada kamar yayi kuka,
Juyowa tayi ta kallesu taga mus'ab har ya fara kuka shikuma chatty hawaye me fal a idonsa, komawa tayi ta zauna jikinta sai yayi sanyi,
Mas'ud ne
yace' zamu tafi,amma bamusan komai game da juna ba,ina ji a jikina kedin yar uwar muce,amma munkasa nasanar dake hakan,ki gafar cemu ki sanar da mu wani abu daga cikin labarin ki ko zamuyi dace da samun iyayen mu.
Kallansa tayi hawaye na neman zubowa daga idanta

tace' mekuke san sani a labarina?
share hawayen da ya zubo Mata tayi taci gaba"' labari babu irinshi a labaran duniya, babu kuma film din da yake kama da labarina bare kuma a samu yayi kama dashi,Jin labarina tamkar ruguza sauran farin cikina ne, ina rokon ku don Allah kar ku Kara cewa na baku labarina don Allah,
Takare da kuka sosai tare da hada hannayenta alamar ruko.
Mus'ab ne ya sunkuyo ya goge Mata hawayen fuskar Shi

yace' Baza mu Kara tambayar ki ba amma watakila idan kika ji namu kalar labarin ki tausayawa rayuwar mu ki bamu taki,hannunta ya rike gam cikin nasa

yace'' Wasu yara ne Yan shekaru shida suka tashi daga bacci suka gansu a cikin wani kango,suna sanye cikin uniform na makaranta da lunch box a wurin da'alama ta yaran ce,suna tashi dayan

yace' ya Muka gammu anan,dayan yace'' bacci mukayi muka gammu anan mu tafi gida,
Sun fito don su tafi sai Kash sun kasa neman hanya,suka karasa karshe de suka fara tafiya har suka shigo cikin gari,kayan jikin yaren kawai za'a kalla asan yayi datti, kowa sai ya kalle su ida n suka wuce, haka suka Gama zaga gari Amma babu alamar ma garin da suka sani,duk Wanda suka hadu dashi suna tambayarsa ya kaisu gida,kowa kallan mahaukata ya fara yiwa yaran,a haka suka kare suna kuka suna tambayar mutane gidan su, har dare yayi gashi sun fara Jin yunwa, lunch box din hannunsu suka bude suka ga abinci,ci sukayi tas suka cinye Amma kuma babu ruwan sha,inda suka zauna gefen masallaci ne hakan yasa su zuwa suka sha ruwan, suka koshi,daga nan kuma sai bacci neman inda zasu kwanta suke Amma babu wurin kwanciya daga karshe de cikin masallacin suka kwana a takure sakamakon sanyin da ake yi, lokacin sallah akazo aka tashesu dole suka tashi sukayi sallah,Basu iya komawa saboda sanyin da ake yi duk da rigar sanyi a jikin su Amma ta makaranta ce,sai da gari ya waye suka fito suka tsare mai abin hawa suka ce ya kaisu makarantar su, tambayar sunan makarantar yayi sukace Basu sani ba,mai irin wannan uniform din, yace kaf garin nan babu mai irin uniform dinsu, a haka ya wuce ya barsu,ganin haka yasa su sukayi ta tafiya,suka ga sunzo wani wuri,Basu San ko ina bane,don Basu taba zuwa ba Ashe wai Tasha sukaje,ganin mai abinci tana bada abinci kowa yazo ta bashi yasa su zuwa wurin suka ce tabasu,sai tace' na nawa zata Basu,anan suka San biya ake a bayar, ganin sun tsaya suna kallanta yasa tace' idan baku da kudi,kuzo kumin wanke wanke sainna Baku sauran abincin, kallanta sukayi sannan dayan yace'' taimaka mana zakiyi bamu iya ba,ca tace idan baza suyi ba Tou su tafi kar su tsaya bata Mata lokaci,dayan ne yace zasuyi,hakan kuwa akayi suna wanke kayan ma sunayi tana cewa sai sun sake ahaka suka Gama Mata wanke kayan,abincin kuwa dan kadan ta basu,sai daya ne ya hakura ya barwa daya,suna nan har Rana tayi tace suzo suyi Mata wanke wanke,suka kuma yi Mata shima de Saida suka sake, ta Basu abinci Wanda beci bane da safe ya yaci shikuma dayan ya hakura,har dare muna tare da mai abinci,itace ta bamu wurin kwana inda take sa kwanikanta,anan suka kwana,gari na wayewa ma hakan ce ta faru sai da suka Mata wanke wanke wannan Karon harda Shara sanan ta basu abinci,suna cin abincin take tambayar su,
Ku yaran nan ina de ku ba almajirai bane,kuma de naga kamar daga makaranta kuke ina iyayen ku,daya ne ya bata amsa yace'' muma bamu sani ba,kuma mu bamu san kowa ba,
Tace' to zaku ke kwana anan kuna min Shara da wanke wanke zanke Baku abinci,Tou suka ce,tunda ganan suke shara da wanke wanke,saidai dayan akwai tsokana duk Wanda ya gani indai bai fishi ba to sai ya tsokana shi,ahaka take daura mana talla kullum muna siyarwa wataran kuma ba ciniki, ahaka munkai wata uku a wurinta,Amma bata taba sai musu kayan sawa ba da wannan uniform din dashi suke zama saidai ta bamu sabulu tace suyi wanki,duk ranar da zasuyi wanki to da gajeren wando suke zama,Ashe tana da yarinya yar boarding tana zuwa kuwa komai ya fara canzawa don ta tsane mu sosai wanki ma muke Mata idan be fita ba Duka ne zasusha haka zasuyi tayi suna sakewa,
watarana aka daukewa mama mai abinci(sunan da suke kiranta) kudinta ,a gaban su yarinyar ta dauka kudin,amma yar sai tace' sune suka dauka,haka ta kamasu tayi ta jibga kuma ta koresu, gashi dare ne Amma a hakan ta koresu, sunyi kuka sun gode Allah,suna cikin tafiya Basu lura ba zasu tsallaka titi daya ne ya fara tsallkawa mota ta bigeshi,dagudu dayan yaje Yana Kiran sunan mus'ab,
Kallanta yayi yace kina ganewa ko? Kin kuma gane suwaye yaran?

Kai ta daga masa, mas'ud ne ya cigaba,

yace'' bayan an Kai mus'ab asibiti anyi mai treatment mutumin yace mu fada masa inda iyayen mu suke, fada masa komai nayi yarda muka tsinci kanmu da kuma yarda matar nan tayi masa sharrin sata,baice komai ba, yayi shiru yace' Yana zuwa, baidawo ba sai washegari har lokacin kuma mus'ab bai far fado ba, sai kusan Azahar sannan ya farfado mutumin ne ya siyo mana abinci muka ci muka koshi sannan aka sallamemu, mutumin ne ya dauke mukaje hotel din da ya sauka shine yamana wanka yasama sabbin kayan sannan yace' mujira Shi zai je ya dawo zamu tafi gidan Shi,muna zaune kuwa yaje ya dawo,
Tambayar sunan mu yayi muka fada masa,Amma duk yarda Akayi mu tuna sunan babanmu mun kasa,daga karshe ma kusan haukace masa mukayi ganin haka yasa Shi yin shiru,har mukayi bacci, bamusan mun iso ba ji mukayi ana tsashin mu,dare lokacin yayi,gida babba, part uku ne a gidan sai kuma wani Katon parlour, parlourn muka Shiga,ganin mukayi kowa Yana zaune yana kallo,ga kuma yara da manya,tasowa sukayi suka masa sannu da zuwa zuwa yayi ya zauna,mudai munja mun tsaya ganin babu Wanda ma ya Kula damu,sai da suka natsu sannan ya kalle mu yace' mus'ab da mas'ud ku karaso ciki mana,karasowa mukayi muka gaida wasu Mata guda biyu,Amma ko amsawa Basu yi ba,dayar ce ma ta amsa dakyar,a haka ya gabatar damu a wurin yayansa manya daga nan kuma ya bayar da labarin mu, sannan kuma yace'zamu zauna a wurin Hajiya itace babba ba yarda ta iya ta amsa da tou.
Tundaga nan rayuwar mu ta kuma sauyawa don wata irin ukuba ake mana a gidan bamu da gata sai idan Daddy yana nan Wanda ya dauko mu Kenan,ko wanne irin aiki da kika sani munayi yaran gidan ma sun tsane mu har ta Kai ta kawo duk wani abun laifi Akayi a gidan mu ake cewa munayishi, dukda muna makaranta amma a kafa muke zuwa mu dawo a kafa gashi gidan Duka Matane yaran da manya ba maza, Mata shida yayan Hajiya babba sai kuma guda hudu yayan Anty, yayan Hajiya guda uku sun girmemu biyu kuma kusan sa'anin ne sai guda daya shekara hudu, yayan Anty kuma daya shekara hudu dayar kuma yar karama ce shekara daya,sai biyun kuma sa'annin ne da sa'ar mu dayar kuma ta Dan girme mu,Amma kaf cikinsu babu wacce bata Rena mu ba,da zaran mundawo a makaranta to mune komai na gidan kafin mu tafi islamiyya sai mun wanke uniform kaf,idan mundawo kuma mi goge,idan akace weekend yayi Bama Zama sai munyi wankin gida
gidan babba ne sosai Amma sai mun wanke Shi tas,kuma babu Wanda ke raga mana,abinci wataran sai magen su taci ta rage zamu ci,a haka mukayi shekara daya cib a gidan.
Watarana muna aikin wanke gida mun zuba klin dayawa a tsakar gidan muna wankewa babbar yar tazo wuce wa santsin ya debeta ta fadi, aikuwa mezanyi Banda dariya nayi ta dariya abina, aikuwa tana tashi ta wanke ni da mari,zata Kara taji an rike hannun,a fusace ta juyo wani yaro ta gani befi shekara 11 ba amma Yana da tsayi don zai kusa kamota,kallanshi takeyi

tace' yaushe kazo ko kallanta beyi ya zo ya daga ni ya kama hannun mus'ab muka tafi,Ashe shima Dan gidan ne ba anan yake da Zama ba a Spain yake, tunda yazo ko ansamu aiki bamayi,sai dai masu aiki suyi, ahaka yagama hutun Shi ya koma, yana barin gidan shikenan kuma komai ya dawo ma,bautar tafi ma ta baya kullum ana kakaro mana aikin yi,sharri kam mun sha Shi ba laifi.
Ahaka muka gama secondary school lokacin muna da shekara 16 a lokacin anyi auran wasu daga cikin matan duk manya basa nan sai shida dasuka rage,aiki ya Dan ragu Amma de dukda hakan muke yin komai a gidan Banda girki, shikuwa Abdulshakur Wanda ake kiransa da binaif mukuma muke cewa BB big bro,mamansa bata gidan har yau kuma bamusan inda inda take ba kuma shima bai fada mana ba........


By: '''Hijjart Abdoul'''
Cwthrt=
_Akanji magana_


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023


10

Mus'ab ne ya share Mata hawayenta sannan yaci Gaba,
Shekarar mu daya da yin candy bamu ci gaba ba bama ma fita sakamakon Daddy yayi tafiya tsawon shekara daya,
Ana ya gobe bb zaidawo ina gyara masa dakinsa,shikuma twiny Yana waje kasancewar babu kowa a gidan daga Hajiya sai Saima yar Hajiya kenan Wanda take sa'ar muce ita,ina cikin gyarawa ya shigo dakin yana Mita,ban Kula shiba donni nazata da Yan unguwa yake fada, ganin mitar taki karewa nasa nace' me ya faru zaka shigo kana yiwa mutane Mita haka,kana wani hade Rai,
Sai

yace' Saima ce tazo ta sameni tace wai mu yafe mata,ta tuba meye da meye haukarta de,wai kasan me tace daga karshe?
Girgiza masa Kai nayi yace' ca tace tana sanka,nazo na fada maka,

Kai kuma me Kace Mata,

Kasan de bazan ce mata a,a don ko kallanta ma banyi ba, bare kuma a samu matsla,to kawai nace Mata.

Ni Gaskiya Bana Santa,taya za'ayi ace yarinyar da ta wulakanta mu,tun muna yara kuma yanzu tazo tawani ce tana San dayan mu,Kai ina bazai yiwu ba,
Baka ganin tarko aka Dana mana?

Abinda bansani ba de,Amma tunda gobe BB zai dawo ai sai mu fada masa ko?
A haka muka yanke shawaran fadawa BB ,daddare muna zaune a part dimmu muna game,ta shigo cikin wasu arnan kaya, masu bayyana tsiraici,ko sallama babu bare kuma mu bada izinin Shiga,Bama mu lura da ita ba muna game dimmu, tazo kanmmu ta tsaya

tace' mus'ab kaji abinda mas'ud ya fada maka ?
Sai da tayi magana sannan muka lura da ita ganin irin Shigar dake jikinta yasa muka kalli juna,bamu Kara kallanta ba Saida ta Kara maimaita wa, cikin wata jarumta

nace' Gaskiya Bana sanki,Baki min ba kuma.....
Kafin ma nagama fadar abinda Zan fada ta wanka min Mari,daman nasan za'a rina shiyasa ko kallanta banyi ba,a tare muka tashi zamu fita,ta rike rigar mu ta baya,bamu Ankara ba ta saki wani ihu,kamar a mafarki muka ga ta fara yaga kayanta, sannan kuma tana gunjin kuka,tsabar mamaki tsayawa mukayi muna kallanta,bamu Kara tsinkewa da lamarin ba sai ji mukayi ana bubugga kofa,Ashe ta kulle kofar bayan ta shigo,dakyar mas'ud yaje ya bude kofar,Yana budewa kuwa ta fara zabga masa Mari ta ko ina,tana duka Shima Daddy ni ya kama yake zabga Ashe ya dawo bamu sani ba, Saida sukayi Dan kansu suka gaji sannan taja hannun yarta suka fita.
A ranar gani mukayi Ashe da ba kunci muke ciki ba yanzu ne muke cikin kunci Rana daya?tunda muna yara ake kulla mana sharri kuma mace amma gani ma mukayi Ashe ba sharri ake mana ba, yanzu ne aka yi mana shi.
Allah yayi mu da tsoron Mata sai tsoronnasu kuma ya Karo sanna tsana ta biyo baya. A parlour muka kwana ranar bamu rintsa ba, aranar muka fara tunanin iyayen mu.
Daddy kuwa ko a masallaci da muka hadu gaisawa mukayi dashi sosai kamar ba abinda ya faru,amma muna zuwa gida ya daure fuska,
Gari na Gama wayewa aka Kira mu aikin gida,kamar kullum aikin gidan muke gaba dayansa,sannan muka bi dakunan yammatan muka gyara dayake su basa nan,Anty ma bata nan amma haka muka gyara ko ina Banda dakin Saima,
Kamar jira take kuwa takai Karan mu wurin Hajiya, Hajiya kuma tazo ta tasamu a gaba sai mun gyara Mata daki idan bamu gyara ba wazai gyara? Dayake Daddy Yana yace ta gyara da kanta, muna nan zaune kuwa sai ga BB nan yazo. Tashi mukayi muka fita,bamu San me aka fada masa ba sai ganin sa mukayi idan shi yayi jajur tare da tambayar me ya faru,bamu boye masa komai ba muka fada masa abinda ya faru.
Bayan kwana biyu kuwa Daddy yace mu hada kayan mu zamu tafi da BB Spain acan zamuyi karatu,hakan yayi mana dadi bakadan ba.
A wurin kanwar Daddy BB yake acan,Wacce ake Kira da Anty ummi, Anty ummi bata taba haihuwa ba,sai yayan mijinta guda biyu Maza da take rikewa,bata da fara'a sosai sannan kuma tana da taka tsantsan a tarbiyar yara, sannan tana da bin kwakwafi akan yaranta. Rayuwar mu ce sosai ta sauya dukda de baza'ace muna cikin soyyayar uwa ba amma idan mukayi Abu ba daidai ba to zamusha fada sanann kuma daga baya tayi mana nasiha,idan taga dayanmu cikin damuwa to dole sai ya fada Mata mene silar damuwar sa, yaran da take rikewa Duka shekara goma sai kuma shekara takwas,
Mijinta beda matsalar komai don yana Kula da mu daidai iyawarsa. Kasancewar Fulani ce yasa bata mana Hausa sosai,daga mu har yaran,daman Shi BB basa Hausa dashi sai jefi jefi, tunda a wurinta ya taso,sai ya zamana muma mun fara iyawa,
Sannu a hankali muka fara zuwa makaranta physics muke karanta muduka,sosai wata shakuwa ta Shiga tsakaninta damu,bata fiye Zama ayi hira ba kullum tana daki,Amma zuwan mu yasa mas'ud zuwa dakinta ya jawo ta mu zauna ayi hira da ita, a hankali kuma ta fara sakin fuska,idan muna gida kuwa Bama barinta tayi aiki mu mukeyi har dakinta mu gyara komai. Sosai muke Karatun mu hankali kwance bamu da damuwar komai. A school kuwa mas'ud Yana ganin mutum zai fara zagin sa ba gaira ba dalili ko da Hausa ko kuma yayi da fulatanci,nasha hanashi yaki hanuwa, ga shegen fada,ko Dan bige Shi kayi to sai ya rama,dama can Ashe wuri ne baisamu ba.
Shekarar mu hudu cib muka kammala karatunmmu lokacin BB ya samu aiki a Nigeria tare da wani company, Shi architect ya karanta.
Dawowar mu Nigeria munzaci Abu zai lafa Amma babu lafawar da yayi, dukda de yanzu mun rage aiki amma kuma mu muke yiwa kowa wanki a gidan, Duka yanzu saura su hudu a gidan,Saima ce yanzu babba sai Ameera da Aneesa kusan sa'anni sai kuma Fatima wacce ake cemata auta,
Alokacin ne kuma aka tashi daga wanan gidan aka dawo zoo road kasancewar Daddy ya Shiga cikin siyasa sakamakon da dayake aikin governmenti,gidan upstairs ne,kowa na ciki, Amma mu muna boys qrts, sai na masu aiki,
Bayan mundawo daga camp aka tura mu service, kudu amma ba gari daya ba ,mukam mungi son haka dukda bamu taba rabuwa ba ,Amma hakan ya mana dadi,Amma kuma muna fadawa Daddy yasa aka mana transfer muka dawo Kano,bahaka muka soba Amma daddy yafi karfin komai wurin mu,shekarar mu daya munayin service muka Gama,sai zaman gida kuma, lokacin shekarar mu 22,Amma babu abinda ya sauya game da tsanar da Yan gidan suke mana,
Yanzu Daddy kulluma beda lokacin 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ mu tun muna masa uzurin siyasa ce har muka gane Ashe kullaliya ce aka mana, yayin da BB shikuma ya koma Spain Yana yin masters dinshi,mu kuma muna gida,koda mun fita munyi yar buga bugar mu munsami kudi,muna dawo wa za'a kwace yan kudin da mukasa mu,daga baya mu kuma sai muke boyewa abinmu, a lokacin Anty ummi ta fara rashin lafiya ashe tana da ciwon zuciya,kuma taki yarda Amata aiki tace a dawo da ita Nigeria ana dawo da ita kuwa kwana daya ta rasu, wannan mutuwa bakaramin girgiza mu tayiba don mu Bama musan meke damunta ba Saida ta rasu. Zan iya cewa ma BB yafi kowa jin mutuwarta sabida a hannunta ya taso,itace mahaifiyar sa,da zai iya kiranta da shi. Ahaka komai ya wuce mutane aka fara mantawa da ita,saidai mukam har yau mutuwar ta sabuwa ce a garemu,itace mutum na biyu da ta taimake mu,taimakon da zai sa mu taimaki wani muma. Bayan bb ya kammala masters dinshi ya dawo yacigaba da aiki, yasamu aiki a Spain Amma be zauna acan ba ya dawo yacigaba da aikinsa daga nan shima ya fara kokarin ganin ya bude nasa company yasai fili kuma ya bukaci Daddy da ya taimaka masa tunda bazai iya Shi kaidai ba amma haka Daddy ya watsa wa idan sa toka yace bazai yiba daga karshe ma sashi yayi ya saida filin da yasaya kuma maimakon ma a bashi kudin ba'a bashi ba,dukda munsan ya damu amma ko a fuska bema nuna ba,ganin muna fuskantar matsala idan baya nan yasa Shi turo mu masters.

Dagowa yayi ya kalleta ganin yarda har yanzu hawayene ke zubowa daga idanta ,goge Mata yayi hawayen yasaki hannunta shima ya goge fuskarshi, mas'ud ne

yace' wannan kadan Kenan daga cikin takaicacan labarin mu,muna so musan ina iyayen mu suke,muna San sani,shin suna raye ? Ko sun mutu?bamu sani ba.
Kallanshi tayi da idanta da ya Riga da ya sauya,cikin wata irin murya da zai nuna tana cikn bacin Rai

tace' wanne gari kuke kafin Daddy ya dauko ya kawuku Kano?
Numfasawa mus'ab yayi

yace' Bama iya tuna sunan garin da muke Amma kuma a Katsina Shi ya dauke mu,

Taya kuka San ku twins ne,ta tambaya,

Bamu manta wannan ba a zuciyar mu,bamu manta sanda mahaifiyar mu ke cewa mu twins bane,bamu manta ba,
Mas'ud

yace' shikadai zamu iya tunawa,harta sunan su har yau mun gagara tunawa.
Tashi tayi ta tsaya

tace' ya sunan Daddy,

Adam Dan Lami,
daya daga cikin su ya fada,bata juyo ba kawai wucewa tayi,da ido suka bita har ta Shiga daki,
Ajiyar zuciya suka sauke a kusan tare,suna wurin suka ga fitowarta ta dawo hannunta rike da wata takarda,Zama tayi ta Mika masu takardar,sannan

tace' ina su idan kunje ku nemin aiki a wannan company din,sannan kuma kuyi binciken sa, sosai.
Daga nan ta tashi ta tafi,kallan takardar da ta miko masu sukayi, address ne na company guda uku da sunan company din daya a Kano dayan Abuja dayan kuma a Lagos yake.
To yanzu ya zasuyi?
Basu da amsan tambayar dole suna bukatar lokaci.

Washegari kashe wayar ta tayi,sunyi Kiran Amma bata Shiga ba,kofarta ma a kulle don a dakinta suka zo sukayi knocking din duniya taki ta bude,bata son Kara saka su a idonta,a yarda take ji. A haka sukayi Mata sallama sannan suka tafi cike da kewarta.


('('('('
_Bayan shekara biyu_

Suna zaune a airport ita da sahr,suna hiran su,don ma sahr ce yawanci meyin hiran ita Ummusalma saidai ta daga Kai tace ehh ko a,ah, kuma hiran tasu ta bankwana ce Duka jiya da daddare basuyi bacci ba, sahr harda kukan ta ajiyan.
Suna nan aka fara Kiran su sahr,sai yanzu taji badadi, shikenan fah tafiya zasuyi, maybe Baza su sake haduwa ba,kawai hawaye taji ya zubowa, sahr juyowar da zatayi ta ganta tana kuka,tasan kukan rabuwa da juna ne,bata iya jurewa ba itakama da gudu ta dawo ta rungumeta, dakyar suka rabu,sahr ta tafi.
Lallashin kanta tayi sannan tayi shiru,ta Lula cikin tunani, acikin zuciyar ta take

cewa' ko idannaje ina zani?komawa zanyi? Zasu karbeni? Ya zanyi?
Bracelet din hannunta ta kalla tace' Neena mene mafita? Ajiyar zuciya ta ja sannan ta jingina da kujeran da take Kai tare da lumshe ido,tana neman mafita.
Hausar da taji anayi ne a gefenta da'alama kuma yanzu suka zo, bude ido tayi ta sauke su akan yarinyar da batafi 16-17 ba,sosai ta kallao yarinyar yarda take magana tana ta zuba surutu, maganar ta wayance Akan yara biyu ne take bada labari kuma tana ji tana cewa Yusuf da yaseer,sosai taji wata sabuwar kewarsu ta darsu a zuciyar ta,sosai take karajin labarin yarinyar don kawai sunan su yusseer shiyasa ta bada kaimi wurin jinsa,maida idonta tayi ta rufe tana Jin labarin yarinyar.
Yarinyar ce

tace' kaga fa zanen da suka bani,wai yayar suce takeyinsa, waifa a yarda suka ce tsabar karya wai idan taga Abu komeye tana iya zanawa ko bata zana daidai ba tana iyawa,wai yaseer ma ya taba kwatan tama wani mutum kuma wai ta zana Shi,shine nace karya, shikenan mukayi fada,kuma ko yayar tasu fa Basu San Inda take ba sunce de ta taho London karatu bata dawo ba.
Kuma ko uncle idan muka zauna ba abinda ake min sai labarin yaya kaza yaya kaza,shine da zamuyi candy suka bani wannan zanen nasu suna San zanen wai itace tayi zanen,
Tunda ta fara zancen take jinta bata bude idanta ba sai da taji ance zane,kawai zuciyar ta ce ta bata su yusseer ne,juyowa tayi ta kuma kallan yarinyar dake kusa da ita hannunta ta tabida kallo,aikuwa de zanen su ne lokacin suna yara, a hankali ta Kai hannunta ta dau zanen,tana kallo, yarinyar ce ta juyo tana kallanta kawai, dagowa tayi suka hada ido da ita,kwalla ce taji ta cika Mata ido muryan ta na rawa

tace' waya Baki wannan zanen ?
Yarinyar

tace' laaa kema kina Jin Hausa ?
Sunana Ummusalma,
Kefa ta fada tana miko Mata hannu,Mika Mata hannun tayi

tace' Ummusalma Muhammad,

Kice sunan mu daya ma Ashe Amma fa ni ummu ake cemin, friends Dina kuma guda biyu Yusuf da yaseer suna cemin yaya wani lokacin idan bamuyi fada ba, wannan zanen ma sune suka bani,
Kwalla ce ta zubo,ta share

tace' can u tell me more about them ?

Ummu tace' mezai Hana Nigeria zaki je?
Daga Mata Kai tayi tace' sai nayi ta Baki labarinsu har sai kince ya isheki tukunna,

Tunda tayi maganan yake kallanta yarinyar da akace masa bata magana? To ko yanzu ta fara tunda Shi rabunshi da school din ya jima, maybe ma yanzun tafara,ahaka ya bar maganar,
Jiyayi ummu nacewa kinga uncle dina,sunan sa Abdullah Abdullah,tare zamu tafi grandma Dina kuma ba yanzu ba zasu tafi shiyasa mu zamu tafi am eager to see my mom,
tafada cikin zumudi,dan matsawa tayi kadan sannan ta hango Shi,if she's not mistaken Kenan wannan yarinyar ce suka hadu da ita years ago,batayi maganaba kamar yarda shima beyi magana ba sai ma Danna wayarsa da yakeyi,
Tana rike da zanen suka Shiga jirgi wuri daya suka zauna,ita da ummu,
Ummu ta kalleta

tace' Yusuf da yaseer sune best friends Dina kuma nima nice best friends dinsu,amma yanzu munyi fada kuma sunyi fushi da ni sosai,
Ummusalma ta kalleta

.tace' meya hadaku?

Hmmm ai infada maki bansan abin zaiyi tsamari haka ba,karya tasu nayi Akan sun bani labarin yayarsu ta

Please Login or Register in order to submit comment