Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kira sallah,

Anty tace' kijimu da 'ya da wanka kike?

Yaseer yace' haba shiyasa tunda nazo naji wani bashi bashi haka Ashe Ashe de,

Yusuf yace' Nima naji Ashe de da walakin gyada a miya,

Remote din kusa da ita ta dauka zata wurga masu,

Umma tace' a,a ajje min bazaki lalata min ba kunsa Saba bata na gidan uwarki ajje min,

Tura Baki tayi, tace' daman ni an tsaneni a gidan nan haka kawa suke tsokana ta harda cewa wai da walakin goro a miya,

Yusuf yace' a,a gyada a miya fa nace,

Yaseer yace' yaushe kika gyara kuma?

Dariya tayi tace' ina ruwanku kuma da yaushe na gyara ba fa nasan sa Ido,

Baba yace' ku tashi mu tafi masallaci kar a Shiga muna nan, dukan su tashi sukayi kowa yayi nasa wuri Baba ya nuna masu wani daki suka Shiga, ita kuma ta shiga dakin Anty wanka tashiga tayi ta fito bata da Kaya daman kayan Kala biyu ne Basu San zasu jima haka ba, da sukaje siyo kayan ma ca tace baza ta jeba, babu Wanda yabi ta kanta kuwa sukayi tafiyar su, akwatin Anty ta buda luckily kuwa taga Kaya size dinta harda inner wears dogayen riguna guda uku kowanne da mayafinsu sai atampa guda hudu da takalimi Bama tabi ba'asi ba ta yanke hukunci nata ne, takuwa sa tayi sallah ta fito har lokacin Basu dawo ba kallo takunna ta fara yi yaushe rabon da tayi kallo yau wani shadi takeji ita kanta ta yarda soyayyar su daga Allah ne ahaka suka dawo suka sameta tare da kayan su suka shigo suka Kai daki sannan suka dawo suka zauna,

Ummu tace' ku kunga yarda kuka rame kuwa? Yarda kuka San tsinke haka kukayi,kamar na ture tsinke da Dan tsaya na guda daya haka kuka koma,

Yaseer yace' lalle yarinyar ke Baki ga kanki ba ?

Yusuf yace' kyaleta ita bacin Rama harda Baki,bakin kuwa irin wani shuni shuni takeyi,

Wallahi kun rena min hankali ma kunsan de na fiku fari tunda kufa farin Rama kukayi inaga ma ba jini ajikin ku,

Shiru sukayi babu Wanda yayi magana sun Rasa meza suce Mata ne kawai,
yusuf yace' a kaima Wrestling ko kuma jikin wata ya fada Mata,

Gaskiya wani yayi formatting ina aka taba ganin wrestling da Rana tsaka haka?

Yaseer yace' to a canza mana wannan aljanun akai mana Bollywood,

Tace' yawwa wannan kuwa,

Bollywood ta Kai sai dai Fan akeyi sukuma su dukan su sun tsani film din aikuwa,

tace' wowww my best film ever,
Harda Dan tsallenta,

Yusuf yace' kinawa Allah ki canza mana kinsan munsan bakya so ko?

Tace' ohh sorry lokacin da aka sace ku shine fa nayi ta kalla Nayi ta kalla shine naji insa Shi ai,

Anty da ta shigo tace' ke wai dan Allah ko kunyar Karya bakya ji ne?

Yaseer yace' yawwa Anty fada Mata de nikuwa kinga ba ruwan ai,

Anty tace' da ban San asalin barbela ba sai na..

Ummu ce ta katseta tace' sai kice daga Ghana tazo ta ko?

Dariya yusuf da yaseer sukayi Anty kuwa tashi tayi ta wuce kitchen bazata iya wannan kayan abun haushin ba,

Yusuf yace' kasan yaseer yanayi missing moment din nan dayawa?

Yaseer yace' ai bros ni Zan fada maka,su oo ana so ayi haua proverbs ba'a iya ba,

Yusuf yace' ahakan har littafin su aka suyo aka Hana mu kar mugani,

Yaseer yace' ehh mana kaidai Bari idan ma mutum zai koma English dinshi ya koma Dan yafi masa,

Yusuf yace' sosai ma karma muje a kwafasa mana idan munje wani waje,

Tana jinsu tayi banza dasu ta mayar da cartoon dinta tacigaba da kallo bata tanka masu ba,tasan zata fanshe ko bakwai ai ana tare, har aka Kira la'asar sunan daga wannan hiran su dauko Wanana har lokacin Baba bedawo ba itama Umma ta tafi gidan su sai rage sai su kadai ne sai Anty, bayan sundawo sannan sukaci abinci,

Anty tace' waya Baki kayan jikinki?

Sosai Kai tayi tace' dauka Nayi Naga kamar nawa shine yasa,

Anty tace' baca kikace bazaki ba?

To mama kiyi hakuri kinji,? Ki Bani yanzu na siyo kinga drivers Dina sun dawo,
Ta karashe da dariya a fuskarta,

Anty tace' kudin Bana banza bane bazan bayar ba aje a siyo min kayan shirme kizo ke ba kwalliya ba bakomai ba da tarin ajiya,

Haba Mama kayan Amfani Zan siyo fa, idan na hauka na siyo kawai ki bayar kinji my sweetheart mom,

Anty tace' naji Zan Baki,
Tace Yusuf idan ta siyo kayan shirme karka biya kudin Kai zanbawa kuma sai ku siyo abinda Baku da Shi,

Tura Baki tayi tace' haba Anty kibawa Yaseer mana yaza'ayi ki bawa yusuf,

Tace' daga ke har yaseer banga me hankali ba shiyasa,

Sun Shaka shiyasa ma Basu tanka ba.


('('('('('('('


Su Duka suna zaune a park wurin kujerun hutawa sai table a tsakiyar su ita tana Shan ice cream gefenta Binaif ne sai kujeran dake facing dinsu su uku ne akai Mus'ab da Mas'ud sai Uncle bayan sun Gama bashi labari da abinda zasuyi shima ya jinjinawa lamarin beyi tunanin abun zai zo cikin sauki ba haka a yanzu da yake Jin 'yan uwansa a jikin sa damuwar Shi ta raguwa zai iya cewa beda damuwa ko daya a halin yanzu kuma ya yarda ya gamsu Yan uwansa ne koba ma Yan uwansa bane zai karbe su hannu bibbiyo ko matsanan ciyar kamar da suke shida Ummusalma da Mus'ab, sai yanzu yake ganin kamar su sosai da sosai, zai tambayi kuma Bab yaji shaidar wanne asibiti ce aka cince Shi a hannun sa, indai akwai number to akwa shaida, daga nan kuma sukaci gaba da tattauna yarda Abu zai tafi.

Ummusalma ce ta hango wata kusa da daga nesa kadan ita da wani saurayi harda su tafawa kuma suna hira suna dariya, kamar ancewa yarinyar ta juyo kuwa, afili Ummusalma ta furta"' Sameera???

Kallanta sukayi sukace lafiya,
Nuna musu ita tayi,

Mas'ud yace' itace wacce zanyi dating? Naji kince Sameera?
Daga masa Kai tayi,

yace' yanzu wannan abar zanyi dating? Gaskiya bazan iya ba,

Tace' dole kuwa kayi,idan akace mus'ab ne zaiyi to zata kamar da muke dashi,

Yace' to Abu mai sauki kisa mijinki Yayi kawai,

Kara tamke fuska tayi,
tace' Kai nace kuma Kai zakayi nagama magana,

Dariya ce ta ciwo Mas'ud,
yace' ohh jealousy, ko?

Mus'ab yace' to kar tayi? Abinda ake shi akewa kishi ai,

Murmushi kawai uncle yayi wannan yara bade surutu ba Shi haka yake beda magana sosai Ummu ce ma take sa Shi magana,

Shima binaif murmushi kawai yayi, na irin ana kishi nan nawa,

Ummusalma tace' Chatty ina so kadawo da Sameera yarda take a da,nasan hakkina ne zai bisu Akan 'yar su Amma ni Bana so ina ganin Sameera tamkar su yusseer ne,ina kaunar Sameera kamar yarda nake kaunar su bana San wani Abu ya faru da ita, a yanzu tana zuwa duk wani night event tana zuwa duk wani party koba ba a garin nan ba, Bana so ta fara kwana a waje idan ba gida ba,dukda wani lokacin tana kwana a gidan su kawayenta wani lokacin kuma a gida take kwana to Bana San tafara kwana a wani wurin, gwara komai ya tsaya daga haka, help me please,

Gaba dayansu kallan ga suke what's kind of heart she's have,she have a pure heart, kallansa ya Kai wurin Sameera yaga yanzu ma a wuri daya suke dayake a nesa yake bega wani gap dake tsakanin suba,
Rufe Ido yayi ya jingina zuciyar sa bugawa take be taba zuwa yacewa wata Yana Santa Bata duk iskancinsa Akan Maza yake karewa koda kwa tsokana ce da hausa lokacin Yana Spain sanda suke karatu,

Tace' ka dauke Sameera kasa sunana Ka dauke kammar ta kasa kamata Ka dauki matsayin nice ita, zaka so ka ganni ahaka? Ko kuma zaka so kaga ina yawon zuwa club,party gari da gari? Zuwa night dinner? Zaka so na kwana a wani wurin koda kuwa gidan wasune ba namu ba?
Yanzu kayi imaging nice waccar a zaune ya zakaji? Please Ka taimaka Mata badanni ba Dan Allah zakayi baya ga haka zata taimaka mana sosai idan ta kware maka zata taimaka mana sannin yau Yana ina,gobe Yana ina,jibi Ina zaije?

Tace' nasan cewan it is not always easy to gather the courage to speak to a woman. But chances to make a good impression are often limited,so saying the right thing from first moment is important. I want you yanzu kaje kayi Mata magana tuna Allah yasa mum hadu kaji? Please,

A hankali ya bude idonsa da yayi ja, ji yayi bazai iya barinta ba kamr yarda tace yayi imaging itace hakan yayi, kallan mus'ab yayi mus'ab ya daga masa kai ya kalli uncle,

Uncle yace' babu abinda yafi karfin Dan Adam sai Wanda yace bazai iya ba I want to you to put it on your mind cewan u can do it,u can do it, u can don't ever Star saying u can't I know u can, Ummusalma my daughter ko bata iya Abu ba tana gwadawa, Ummusalma kanwata kuwa she's heroine,bare kuma Kai Namiji,

Kallan Binaif yayi,wani murmushi yayi masa, yace' bansan me wannan me wannan chatty din ba yake so nace, me zance,
Shiru yayi alamar tunanin, yace' bb naganni nan ko? Umm wallahi Zan iya komai amma kaga fav bro babu abinda zai iya ya cika tsorom tsiya kamar farar kura,
Murmushi yayi sosai yace' is now a time that u will show me u can do it, shine kuma Zan yarda oya move on,

Numfashi ya ajje ya tattaro duk maganar su, sannan,
yace' me zanje nace Mata yanzu?

Gaba dayansu Ido suka zuba Mata,
tace' a,a lafiya kufa ya tambaya kune maza yaza'ayi ki zuba min Ido,?

Mus'ab yace' ai tunda kikaga haka to babu Wanda ya taba zuwa wurin budurwa,

Tace' ni ai na taba zuwa wurin saurayi,
Da zakuce min wani Abu,

Binaif yace' kifada komai b, yanzu de me zaice,

Tace' kaje kawai,

Yace' naje na masu me wai? Nace me? Nace' mai da yaji kome,

Tace' idan kaje kayi musu sallama kar kad hi ko Hello Ka kagane?

Yace' sosai ma sai me kuma,

Sai Mika masa hannun ku gaisa, Ka nuna Ka Santa a wani wurin haka,

Yace' gaskiya bangane wannan ba, a,ina nasanta?

Daure fuskayi tace' gaskiya Kai kana da matsala wallahi ahaka Zan koya ma ?

Uncle yace' idan fada zakuyi bazaku tsaya yi abinda ya kamata lokaci fa jiran ku zaiyi ba,munan za'ayi magriba su tashi muma mu tashi,

Yace' to ai itace bani ba,

Tace' Kaine de,

Mus'ab yace' kunga wannan haka suke basa jituwa,

Tace' kaje kuma karyi masu surutu Ka ja ajinka,Banda rawar Kai da kafa,Ka zauna a kusa da ita kaji ai? Sannan kace Ka santa Ka taba ganin ta a Kaduna da taje partyn wani saurayin ta,

Samarin mata Har nawa e haka?

Kai zaka Nemo wannan kuma, yanzu tashi Ka tafi,

Tashi yayi a hankali Yana tafiya yana juyowa Yana kallansu kamar yarda suke kallanshi sai ya tafi sai ya dawo sai ya tafi dawo idan zai dawo harda gudu yake hadawa a na karshe ne yadawo ya,

tace' danzo na fada maka wani Abu,

Zuwa yayi harda su sunkuya daidai kunnasa, kunnan ta kama,

tace' karka manta wallahi,taam,
Ta dauki lemo ta Mika masa tace' ungo wannan Ka rike a hannun Ka kar Ka dawo har sai sun lura ma damu,
Karba yayi yayi gaba sai da yakusa zuwaya juyo alamar zai dawo ai gaba dayansu rufdugu suka masa na Harare ba shiri ya juya ya bude lemon sa yaje wurin, zuciyar sa bugawa take shidai besan ya zaice,yama Mata abinda tace masa yace sallamar kadai ya rike,

Cikin wata irin voice mai cike da sanyi da fargaba sai dai bazaka ce yana cikin fargaba ba,

yace' Assalamu Alaikum........


Comments
'
'
'
'
'

By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
Cwthrt=BAKIN WAWA*
_Akanji magana_

30

Dagowa sukayi suka kalle Shi Dan murmushi yayi Wanda iya fatar bakin ya tsaya beje ko ina sannan ya samu wuri ya zauna ya Dan kurbi lemu, gaban Shi faduwa kawai yake,

yace' sannu fa,

Namijin yace' Hi,

Karar wayar Shi yaji yasa Shi daga wa ganin ita ce,

Tace' banga kana wani abuba sai San lemu Allah zamu tafi mu barka,

Adan wayince ya juyo ya kallesu,ya juyar da kansa,

yace' sannu fah,

Namijin yace' ina de lafiya?

Sameera tace' Kawai kazo Ka samu a gaba?

Tace' baeb mu tafi abimmu,

tashi sukayi zasu tafi Yana rike da hannunta ta gaban Shi suka zo zasu wuce mesan what comes his mind ba yade ba daga zuciyar Shi shawarar ta fito sai gani yayi ya rike hannunta, juyowa tayi ta kalle shi,

tace' wai Kai lafiya?

Namma shiru yayi Shi kawai hannunsa yake kallo da ya rike Yama kasa magana,dakyar ya samu kalma biyu,

yace' yi hakuri,

Cikin fasifa tace' sake min hannu ko na zabga maka Mari a nan wurin mu jawo 'yan kallo,

Sakinta yayi
yace' am daman a wannan Kaduna,

Wayarsa dake hannunsa tayi kara message ne ya shigo kafin ya dago ya gansu sun gifta Shi, binsu yayi Yana Kara Karanta abinda ke ciki, ta kusanta ya je,

yace' am daman fa a Kaduna na sanki,nazaci wacce nasani ce shiyasa ma har na rike Mata hannu,kiyi hakuri fah,

Namjin yace' Kai tafi a anan wurin ba ita bace,

Besaurare Shi ba don beda abinda zai fada masa, shiyasa yayi shiru sai,,
yace' kiyi magana mana koba Sameera bace?

Ja tayi ta tsaya tabbas kuwa ya Santa Amma ita batasan Shi ba ai, shima tsayawa yayi ya Dan kalli wayarsa,

yace' Nasan kece wacce nasani ai, bazaki tuna ni ba ai, Amma ni nasanki,

Namijin yace'kar ki Rena min wayo mana, Sarai kin San Shi Ashe daman bani daya kike kulawa ba ko?

Message yaga ya shigo wayarsa,
yace' ni zan tafi sai wataran Kenan?
Bejira amsar ta ba yayi gaba ina ruwan Shi abinda aka sashi yayi besan cewa fada tasa Shi hadawa ba,

Sameera tace' aww daman kana tunanin Kai daya nake kulawa? Nasan cewan kana da 'yam Mata kalata sunkai goma ko fiye dahaka bakai daya bane,

Yace' Naji karki Kara kulani tunda ke mayaudariya ce kuma zaki sane kinyi Dani,

Tace' nasaba Jin Kalmar nan a bakin mutane da yawa,wato ga banza ko? Kai kuma mene? Har gwara ni Bana lalata da samari Kai fa? Meye bakayi ? Waye besan halin Kaba? Kowa ya kama rabansa medame ni ba, banza kawai shasha,
Tasa Kai tayi gaba abinta,shikuwa Yana tsaye kamar gunki tunda yake da mace sai dai ya gama amfani da ita ya yar a bola bolarma wacce za'a Kona bazata anfanu ba, Amma wannan babu abinda yayi da ita niyyar Shi yau yayi duk abinda yi da it gashi yanzu komai ya wargaje beje ga komai ba, beyi tunanin ma bata sanshi haka ba,tunda suke bata taba daga masa murya ba sai yau, shima tafiya yayi ya bar wurin,

Yana zuwa ya samu waje ya zauna Yana sauke ajiyar zuciya nishi kawai yake Kai kace yayi gudun tsere ne, a zaton Shi zasu haushi da fada shiyasa ma ya kulle idan sa, so bega abinda yake faruwa ba a tsakanin su,sai da suka tafi Ummusalma tace' ya kamata a Nemo wannan mutumin bazai barta haka ba,

Uncle yace' to amasa me kuma? Bacin kina gani de da'alama sun rabo,

Tace' ehh da'alama ba? Amma Shi bazai kyaleta ba ai, idan Ka lura sanda ta tafi kamata yayi acd shima ya tafi amma sai ya tsaya yayi wani Dan tunanin kadan, ayarda suke fadan zaka San beji dadi ba Ka gane?

Yace' na fahimta,

Kallan mas'ud tayi tace' Chatty kafa Kayi kokari fa sosai da sosai Allah ya Kara jarumta,

Ba shiri ya bude ido yace' Kai haba da gaske? Kice nazama expert Kenan ho ni ho hoho, na bar wani a Baya first time in history nayiwa mace magana Bama maganar komai ba maganar soyayya na bar wani wallahi,

Mus'ab yace' ji banza waka Bari din? Ai ni de kasan Zan iya wallahi,

Ummusalma tace' meye maganar soyayyar tukunna ma wai? Kana nufin wannan abun daka fada Mata shine love din?

Dariya suka sa masa,shikuwa kumbura Baki yayi, dayake mus'ab ne marenin wayan sa shi ya tashi zai buga aikuwa suka fara gudu wannan yayi ta nan Wannan yayi tannan,
Murmushi fal fuskar uncle bazai iya fassara yarda yajiba Amma kuma dadi yaji meyasa aka raba su? Kwalla yaji zata fito daga idansa bema sani ba sai Jin hannu yayi Ya share masa kwallar hannun yabi da kallo yaga Binaif Yana masa murmushi,

yace' kayi hakuri kowanne bawa da irin tasa kaddaran ku taku sai tazo da sauki Allah yasa kun hado,amma ni tawa,
Murmushi yayi Mai ciwo,
yace' har yau banyi wani Abu ba,Bm Akan neman mahaifiya taba ( a lokacin da aka bada labarin uncle Yana cikin damuwar labarin da aka bashi to besan sunyi zancen ba kawai jinsu yake bazai ce ga me aka fada ba),

Uncle yace' kayi hakuri komai zai wuce kaji ko?

Murmushi kawai Binaif yayi bece komai ba beda abinda zaice shiyasa ya zabi da yayi shiru,
yace' kalle su Ka gani?

Kallan su yakai wurin da suke guje guje har Ummusalma suna dariya kamar wasu yara tun sunayi su kadai har suka gayyato yaran wurin Suma suka fara dole wai sai Mas'ud ya kama su ya nada sai kace wani ubansu, sukuma sunki shine yara ma akazo,

Binaif yace' Shekaru hudu Baya da muka hadu da su bata magana bare tayi dariya, bacin na taba ganinta tana yin hakan,

Uncle yace' ni Zan fada maka,ko presentation ne fah batayi ance min kurma ce shiyasa sai na bata assignment a maimakon shi,Ashe ba kurma bace tsantsan rashin son magana ne,

Murmushi binaif yayi yace' Ina San farin cikinta ina san ta kasance cikin farin ciki a koda yaushe bansan bacin ranta, bansan tayi ta tunani idan ta zauna ita daya,

Uncle yace' idan haka ne why not ku zauna tare dasu?

Binaif yace' wannan daman shine ra'ayi tun kafin nasan Zan yi aure, ko Dan suji suna rayuwa cikin 'yan ci, suji suna rayuwa acikin gidan su,tunda suka taso suke fuskantar matsala, tafiyar su Spain ya Dan lafa suna dawowa komai ya cigaba, daga karshe suka dawo gidan Kakar mu ananne suka Samu freedom bayan an koresu daga can gida,

Murmushi kawai uncle yayi Yana cigaba da kallan su,
Wani Abu ya fito da Shi a cikin Dan box box din ja ce mai ba'a kuma ganin abinda yake ciki, ya mikawa Binaif

yace' wannan abun shine abinda aka gani acikin towel din da aka yar Dani bayan sun duba sun gani Ka rike Ka hada Shi da takardun wajenka, maybe zaiyi amfani gaba,

Meyasa Kai bazaka rike ba?

Inaji kamar wani Abu zai faru,kamar wani Abu zai sameni, godiya ta ga Allah dayace dayasa na ga 'yan uwana da yasa nasan gaskiyar komai, Ka rike Shi a wurinka abun Yana da mukulli amma babu key din haka suka ga abun, ko ya fadine Basu sani ba, box Mai kyau gashi karami kamar na zobe na zobe ma yafi girma karba yayi yasa a aljihu bekara magana ba daga nan, suka zuba musu Ido suna kallan su. Waya akayiwa ganin Baba yasa Shi dagawa,

yace' Baba an wuni lafiya,

Daga can ummu tawaikwayi muryan Baba irin shine din nan,
tace' Lafiya qalau yarona,

Yace' ummu ranki zai baci, fa

Tace' Uncle saban labari su besties sun dawo fah tunda safe sai ga su sunzo Amma fa Wanda yasa ce su ne ya kawo su sannan kuma Ance kar Abie yaji donmma Kar yayi wani bincike kasan halin Abie da Dan Karan bin kwawwafi daga karshe de yaushe zaka dawo, Amma idan zaka tafi can London tana nan zaka wuce sannan kuma Kai daya zaka koma Allah sarki My Uncle,

Yace' kekam Ummu bazaki canza ba ko? Daga dawowar su har kindawo normal,yanzu bakin Anty zai fara ciwo,

Laaa kaga ni bazan iya Bama kwasar su zanyi inkai su gidan Hajja yalwa itace babu ruwanta ko fada bata maka idan kayi lefi sai dai

tace' yanzu Kaine kayi kaza kayi kaza to kar ka kuma Zan Zane Ka idan kayi,
Cikin sanyi take maganar shiyasa itama tayi magana yarda takeyi,

Murmushi yayi yace' hmmm ba ruwan keda Umma idan taji ki,

Yaushe zaka dawo de,

Gobe Insha Allah zuwa rana haka? Zan dawo

Tace' Haba de Rana ai yayi nisa dayawa ina laifin zuwa safe haka kayi break fast anan dakaina Zan girka maka abinda kake so,

Shikenan Zan duba nagani,idan nazo akwai labari dayawa,

Kai Amma naji dadi sosai sai kazo idan Ka zo kamin waya da wannan wayar Baban, Amma kace ni kake nema Kar Ka Kira Shi ku fara gaisawa kaji ai?

Numfashi yaja yace' Naji second mom din na,
Sannan sukayi sallama murmushi fal fuskar Shi,

Ummusalma ce tazo ta zauna tace' nagaji dayawa,nayi gudu, tana sauke numfashi,

Mus'ab ma zuwa yayi ya zauna shima, mas'ud kuwa wasan sa yayi tayi da yaran sai da Iyayen su suka zo suka dauke su sannan shima ya dawo yana Nishi,

Binaif yace' ku tashi mu tafi gida magariba ta gabato,

Mas'ud yace' sai da kukaga nazo Zan hutar sannan za'ace a tashi a tafi gida?
Wannan in justice ne, daman nasani ba'a Sona ku Duka kuwa,

Babu Wanda ya kula Shi Dan sun San halin sai uncle shikadai ne ya masa magana sannan ya tashi, sai da sukaje inda sukayi parking Binaif ya juyo ya kalle su,

yace' kubi bros ku tafi baza'a takura min ba, a tafiya na rage hanya a komawa kuma bazan rage ba,

Kallan juna sukayi sukace' mekenan?

Ummusalma kuwa bata ma San me yace ba Dan har ya Shiga mota abinta shima shigowa yayi ya kyalesu suna sun hangame baki,

Tace' yanaga Baka shigo da suba?

Yace' kyalesu sun fiye sa Ido ganawa zanyi da mi precioso,

Shiru tayi ta kyale shi bata San mezata ce ba,
yace' Kinyi shiru lafiya?

Tace' uhm

Uhm kadai?

Wasa wasa fah Surutu dakai

Ohh really?

Shiru tayi bata Kara magana ba, itama ta kyale shi kawai,
Har suka zo gida babu maganar arziki a tattare da su.


<<<<<<<<<<<<<<

Sai da ya sauka a airport ya Kira numbern Baba Yana Kira tana dagawa

yace' gani fah nazo nama kusa zuwa gida kinji ?

Tace' Amma ai da nazo na daukeka,

Karki damu nama kusa gani nan,

To shikenan sai Ka Kara so, Allah ya kawo Ka lafiya,
Ta kashe wayar tace' Baba wai har yazo,ina so yaga besties dina sun dawo lafiya sai dai sun rame fah,
Baba yace' hmmm ke bakya gajiya da magana,

Dukansu suna parlourn sunsa abinci a gaba Shi kawai ake jira yazo yaci,ummu ce tayi abincin kuma ta hana kowa ci Baba kuwa ya biye Mata sai yazo din, hira sukeyi mai cike da annashwa babu wata damuwa a wurin su,

Wayar Baba aka Kira ganin sunan Uncle yasa Shi dagawa, beyi magana ba daga can akayi magana,

yace' Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, wanne asibiti aka kaisu?
AAA hospital, ne asibitin Shine,
Yace' gani nan zuwa kuwa yanzu nan, ya kashe wayar,

Dukan su Ido suka zuba masa,suna San Jin ba'asi,
Yace' wai Abokina ne yayi accident Wanda zai so muyi magana dashi yanzu Yana asibiti, Zan Kira yarona sai ya wuce mu hadu acan din,kun gane?

Umma tace' Allah ya kiyaye,
Yana sauri ma be amsa addu'ahr ba, sai dai duk jikin su yayi sanyi qalau a haka suka ci abincin su tunda ba zai zo ba asibiti zai wuce...


<<<<<<<<<<<<<<<<

Sameera ce a zaune a parlour tana kallo babu abinda take tunawa sai abinda ya faru jiya waye Shi? Duk iya tunanin ta takasa samu waye Shi kaf samarinta idan ta hada babu mai kamar shi, bata taba yin mai kalar Saba ma, ya zatayi? Gashi ko sunansa be fada ba, tana zuwa Kaduna suna party amma takasa Nemo Shi, ajiyar zuciya ta sauke,ga kuma wannan yace zata gani mezata gani? Anya ba tarko aka Dana Mata ba kuwa? An rabata da saurayinta daman de bawani San Shi take ba, tanda Wanda take so tana ganin shine daidai da rayuwar ta, shine Wanda zata tsayar a mijin aure

Please Login or Register in order to submit comment