Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeyi irin ita tace tana Jin nan yazage yana surutu,ita ta tambayeshi me yakawo shine ko kuma de kawai San asani wai gaida uwar miji a kasuwa,saida ta tattara kayanta na wurin, jakarta ta bude ta ciro wata leda,sai da ta tashi ta Dora masa a kan ciyarsa,har tayi gaba sai kuma ta dawo

tace' bakai na bawa ba Dan uwanka na bawa.
Kawao tai gaba ta barshi a wurin,Baki a sake yake binta da kallo bai taba tunanin ta iya Hausa ba kuma daga ji ba wai koya tayi ba can dama ta iya,baid daina kallansa ba har ta hau sama ta Shiga dakinta sannan ya saki wata ajiyar zuciya,
yace' Ashe ba kurma bace, Kenan taji duk abinda nace taaab,kawai sai yasaki wata dariya,

yace' Allah sarki ohhh wataran tabbas Zan sha Duka idan na cigaba dayin abinda nake,
Ya jima a wurin Yana yiwa kansa dariya,daga nan kuma ya tashi ya tafi.
Tana kallansa yana magana Shi kaidai Yana dariya, dariyarsa iri daya da Neeena,ita mamaki ma abin yabata duk abinda ya fada akanta bata ji wani haushi ba. Koda ya tafi tajima a tsaye a wurin, balcony ta nufa ko zata sha iska,Zama tayi ta rufe idonta tana hango abinda ya faru tsakaninta dashi,tashi tayi ta zauna sannan ta kalli kayan Zane jitayi tana sha'awar zana shi,tashi kuwa tayi dauko kayan ta fara zane,mutane Biyar ta zana, kuma duk sai taga suna kama da juna, sunaye ta saka asaman kowanne,Neena ce ta farko sai Baba sai AA da Chatty(Wanda suka hadu) sai ita kuma a karshe,kallan Zane ta tsaya yi,tabbas sai yanzu taga kamar su suna kama da AA sosai haka nan da Baba Neena kuma nakama da Chatty,ta jima tana kallan wa'yanna fuskokin, zuciyar tace ta fara saka bata wani abu da sauri ta kauda tunanin tana girgiza kai,tana cewa bazai mata ba iyuwa ba hakan baza faru ba. Tana zaune a wurin har lokacin magriba, tashi tayi tai sallah tayi karatun Qur'ani, har lokacin Isha, fridge dinsu ta duba ganin bakomai lemo yasata Jan tsaki,kuma ita yunwa takeji gashi tayi burgar aiki ta bayar da nata, da hijabin jikinta har kasa ta ta fita Wanda tayi sallah dashi, tafiya take a hankali harta iso cafeteria, tagama siyan abinda zata siya juyowar da zatayi kuwa sukayi Karo da Chatty lemon dake hannunshi ya zubar Mata a hijabi shi besan ita bace kawai ya dago zai bada hakuri har ya bude baki sai kuma yayi shiru ya tsaya kallanta

yace' Baki iya bada hakuri bane ?
Gani take idan ta kuma dagowa ta kalleshi to ai matsayi yasamu,ko kallo bai isheta ba,ta sa Kai tazo zata fita,ji tayi an riko hannunta, a masifen ce zata masa magana saidai ganin Wanda ke rike da hannunta yasa gabanta faduwa,ta zuba masa na mujiya kawai tana kallansa,shima ita yake tabbas wannan badan ita kadai taji an Haifa ba zata iya cewa dan biyunta ne sabida kamar su ta baci ba kadan ba,komai nasu iri daya banbamcin sa da ita kawai tana da tusar jaki shikima bai daita ta fishi karamin baki,ta kuma fishi eyelashes,wata zuciyar ce tace Mata kawai kama ce bakomai ba,sannan ta sauke wata Ajiyar zuciya,shima kallanta take kuma besaki hannunta ba,

yace' Ina mai baki hakuri da abinda fav bro ya maki dazu da kuma yanzu kinji?
Yarda yake magana zaka san baida lafiya,gakuma hannnun Shi da ya riketa,zafi kau dashi,ganin tana kallansa yasa dayan

cewa' in fada maka bazata maka magana ba ai,wannan da Ka ganta tafi BB miskilaci wallahi gwara ma ka kyaleta Ka barta,kar Allah yasa ta hakura din,daman bani na Baki hakuri ba shine ,
Kallanshi tayi bata ce komai ta ajje ledar hannunta ta sa hannun ta cire hannunsa batare da tayi magana ba tayi gaba ta kyalesu,tabe baki Chatty yayi

yace' dakai daga fada maka kamanninta shikenan sai Ka gane ta kallansa yayi

yace' yarda kabani labarinta,yarda kayi ta fada Mata magana bata tanka ba nasan itace wannan ganin yarda ka bata Mata hajibi kuma kayi magana Amma bata tanka ba.
Dariya yayi Yana Zama

yace' Kai mai tsoron Mata ne fa da ace ta tanka maka akan abinda Ka Mata dazu,to yanzu idan hakan ta faru nasan da da gudu zaka bar nan wurin,ya karashe da dariya sosai Duka ya kai masa ya goce

yace' Kai kuma fa? Har gwara ni ai Akan Kai,ya karashe yana bata fuska,tashi yayi ya fita wai ko zai ganta,Amma bai ganta ba shima fitowa yayi daga nan suka fita.

Tana zuwa daki ko hijabi bata cire ba ta dauko zanen ta ta zana dayan tasa masa glip a sama sunansa. Sannn ta ajje tazo taci abinci tayi shirin bacci ta hau tunanin,ita Allah yasa ma kar su Kara haduwa da su.
*********
Washegari da wuri ta shirya ta fice wurin aiki,wanke wanke ta farayi sannan ta fara taimakawa ana yin abinci, haka sukayi har lokacin tashin su yayi,tana fitowa tagansu zasu shigo,ko kallan inda suke bata kallaba bare su hada ido tayi masu magana, Chatty ne ya hangota zata wuce da sauri yasha gabanta

yace' yawwa wana kama? Dabaki fada min wurinba na Allah basa karewa sun fada min? Glip ne ya karaso

yace' haba mas'ud meye hakan wai?
Kaga mus'ab kyaleni,ni zatayi ma banza ina Mata magana ?
Kallansu kawai take yi,yo ita badan duniya bama da ta sauya mata akwai Wanda ya isa yadaga Mata murya ne bare kuma har ya tsereta Yana fada Mata magana?
Wani banzan kallo tamasa tare da Jan wani wawan tsaki,ta wuce bata tanka masa ba,ai daga mus'ab din har mas'ud cikinsu ne ya duri ruwa Basu iya tankawa ba,dakyar mus'ab

yace' kaga ni ko?kaga abinda Ka janyo mana,to wallahi nikam ba ruwana bazan Kara Shiga sabgar taba ato.
Ya wuce Shi ya barshi a wurin,ai kuwa de yasha jinin jikinsa ai,jiki a sanyaye ya Shiga ciki shima,mus'ab sai ya kalleshi sai ya kwashe da dariya,

yace' kaga wata yarinya can jeka ka tambaye ta inda ake Shan ice cream kaji fav bro,
Ya karshe cike da zolaya, lokacin an kawo masu abinda suka bukata,don haka Saida ya fara ci,sanna ya kalleshi ya kalli yarinyar da aka nuna masa sannan

yace' hmmm kai ai Dan bakaraba wallahi,taab nifa nazaci baza iya yin komai ba.
Wai kaga ma kuwa wani kallo da tayi minne?

Awww Kai kadai tayi wa?tayi mana de zaka ce,
Kasan wani abu lokacin da BB yake cewa shiru shiru va tsoro bane gudun magana ne ban taba yarda ba sai yau,

Jibi ita ba magana tayi mana ba amma gaba daya kallan da tamana yasani Jin Kara tsoron Mata wallahi,

Kai ta kallo take tsakin da taja Kai,

Ni wannan bai dameni ba,wannan kallan,kallo ne na irin gargadin kar ka Kara Shiga harkata,
Dariyan mus'ab yayi

yace' to yanzu fav bro mas'ud dafatan Ka dauki darasi ko?
Shima dariyan yayi

yace' darrussa na dauka,ai

Nikam idan mun hadu Zan bata hakuri daga nan sai mu kulla zumunci tunda da 'alma yar 9ja ce kaga shikenan munyi friend mace de ko?
Tunda yafara zancen zuwa da bata hakuri yake kallanshi tou Shi yanzu ko haduwa yayi da ita ai baya jeba taab.
daga nan yace' Kai kadai zaka kulla zumunci ka Amma Banda ni,

To naji nima Banda ni kadai shikenan?
Ehh shikenan ya bashi amsa,sanna yaci gaba

Amma nifa twiny wannan yarinyace bata fi bama tafi 17-18 bako?

Kaga fav bro idan kun hadu sai Ka tambaye ta shekarunta inaga hakan yafi ai ko?
Ganin maganar yakeso yasa shi yin shiru Yana cin abincinsa,shima mus'ab din shiru yayi ganin ba'a tanka masa ba.

<<<<<<<<<<

Aikin banza suzo su addabi mutane kawai idan ya kuskura ya Kara Shiga harkata sai na nuna masa true colour Dina tunda Shi beda mutunci,
Ita kadai take mitar ta tana juyi Akan gado,zaman dakin ne ya isheta yasa ta fitowa fita wurin dayan aikinnata,sai bayan magriba ta dawo, wanka tayi,tay sallah sannan taci abinci ta dau Qurani ta karanta, lokacin Isha nayi,tayi ta kwanta.
Washegari ta makara sakamakon ciwon bayan da ta tashi dashi, gashi batayi wani baccin kirki ba,haka de ta shirya ta fito, fuskar nan kamar kullum,tana tafiya taji tayi kicibus da abu dagowa tayi don ganin da me tayi gware,shima ita yake kallo, hada ido sukayi babu Wanda yayi tunanin dauke idon sa, fuskar juna suke karewa kallo,tunanin inda yasan fuskar take Amma yakasa ,itama tunanin inda tasan Shi takeyi Amma kuma ta kasa tunowa,
ahankali ta fara janye idonta tayi kasa dashi,bahaka yasoba yaso ace sun cigaba da kallan juna wani irin yanayi ya tsinci kansa mai wuyar fassarawa,ganin tana shirun wucewa yasa ya riko hannunta,sai da gaban ta yafadi,Amma bata juyo ba shima bai juyo ba

yace' can't you apologize?? U don't know how to apologize right????
Tabbas tasan muryan nan kuma yarda ya fada haka aka taba fada Mata,Amma a'ina ???
Batare da ya saki hannunta ba taji yace' maybe ma
Kurma ce, da fillanci yayi maganar,kuma taji abinda yace bataji mamaki ba kasancewar Shigar hausawace tagani a jikin Shi harda hula kuma yayi Kala da Fulanin,
Hannunta tasa ta tacire hannunsa tayi gaba ta barshi Yana binta da Ido,taxi ta Shiga ta barshi a wurin.
Koda taje wurin aikinta dauriya kawai take yi sosai bayan ta ke Mata ciwo indai zatayi period haka takeji,a daddafe ta Gama aikinta har lokacin tashinta yayi,ta dawo hanya,nufar dayan wurin tayi namma yau akwai aiki,Basu Gama sai dare kusan 9pm sannan ta samu kanta shima a hakan sararawa ce Akayi give zasu ci gaba,tafiya kawai take batare da tasan ina zata dosa ba tasan dw tadau hanyar school dinsu,sai ogan su yace zai sauketa tace a'a, tsayawa tayi tana jiran me taxi ganin tafiyar ta gagareta,mota ta gani ta tsayar Shiga kawai tayi ta Fadi inda zataje, har jikin campus ya Shigar da sai da tafito sannan ta fito da kudin Shi zata bashi hannunta ne ya makale ita bata Mika masa ita bata mayar ba,kawai ta tsaya take kallanshi,mutumin dazu ne da sukayi Karo,fitowa yayi ya zagoyo inda take cikin harshen turanci

yace' da sace mutane nake saidai na sace ki ko? Meke damunki haka?
Ganin bata da niyyar magana yace' wannan motar ta maki kama da taxi ne ?
Bata kulashi ba sai maida kudinta tayi jaka tana neman tafiya da sauri ya riko hannunta

yace' sunana Abdulshakur,ana Kirana da Binaif,sai Naga kamar na taba ganinki Amma ba anan ba zan iya sani?
Hannunta ta cire daga hannushi cikin Hausa

tace' kar Ka Kara tabani,
Ta juya ta barshi a wurin, tabbas ya Santa kuma ya tuno inda yasanta,Amma abin mamakin da ai bahaka take ba meya faru ta dawo shiru shiru haka??
Yana nan tsaye ya daga waya yayi kira, fitowa yayi daga cikin campus din ya samu wuri ya zauna ya Dan jima a zaune sai ga su mus'ab nan sunzo,sun jima kuwa suna bashi labarin abinda ya faru bai nuna musu ya Santa ba har suka gama bai kuma yi magana ba.

<<<<<<<<<<

Tana Shiga daki wanka tayi taci abinci sannan ta kwanta,sai da ta kwanta tafara tunanin shi,
Abdulshakur tace,meyasa ta manta inda ta sanshi? Tashi tayi ta zauna ji tayi maganar sa tana dawo mata inda yace meke damunki?? Lumshe ido tayi ta bude ba'a taba tambayar abinda yake damun taba,koda can data ke ganiyar kan mulkinta babu Wanda ta taba tambayar damuwarta,haka sahr da suke kwana su tashi tare bata taba ganewa ba sai Shi?? A,ina ta sanshi? Ganin baccin ya gagara yasa ta tashi ta leka window hango su tayi sunsa Shi a tsakiya suna ta maganar su, dariya suke Amma bandashi ga dukkan alamu ya tafi duniyar tunani ne,kallanshi kawai take bako kiftawa, bata San metake ji ba idan tana kallanshi amma koma mene ne hakan Yana Mata dadi sosai. Tashi taga sunyi zasu Shiga mota,kamar yasan ana kallanshi kuwa yatsaya ya kalli saitin windown ta,tasan de baya kallanta sabida filar daki a kashe take, shiyasa ta tsaya,ya Dan jima Yana kallan wurin daga bisani kuma ya tafi.

('('('('('('
Tun daganan bata Kara haduwa da suba hakan ya Mata dadi bakadan ba,bata kuma son Kara ganinsu,musamman Shi da tun sanda ta daura idan ta akanshi take fama da tunanin sa, har aka dawo hutun makaranta wahala ta dawo,dukda wahalar karatu dakuna zirga zirga hakan bai Hana ta yin kyau ba fatarta ta murje,tayi haske da ita,sai dai ba kiba tana nan bata Kara kiba sai abinda ba'a Rasa ba. A haka take samu take biyan kudin makarantar ta kuma tana tara wani tunda shekara shekara,har sun gama year two abinsu,kokari kuwa sai abinda yayi gaba ba baya ba don basa wasa da karatun su ko kadan kuwa. Duk hutu sai sahr tace suje gidan su amma bama ta kallanta bare ta dau zancenta da muhimmanci,har ta hakura ta dena Mata zance.
Shekara daya Kenan Amma kulluma sai tayi tunanin Shi. Gashi yanzu sunyi hutun first semestern na year three,yau weekend tana zaune tana karanta papern Neena mus'ab yazo kusa da ita,daman ta ganshi fuskewa tayi, kuma ya wani zo ya zauna kusa da ita, Amma ganin ya Mata sallama yasa ta ansa,

yace' am kin....ga ...am,da...man. da..da am
Jin Yana in ina yasa ta Kara daure fuska ta dago ta kalleshi tayi shiru

yace' daman hakuri Zan baki
Akan abinda wancan yaran yayi Miki haka yake Shi sai tsokana Amma kiyi hakuri kinji?.
Ya karashe da lagwabar da Kai,kallansa tayi

tace' shikenan?
Gani ta mai magana yasa Shi cewa uhhm

Nafadi dayan?? Ya fada cike da fargaba kar tace a'a
Nodding Kai tamasa kawai tana wani lumshe ido alamar bacci takeji, cigaba yayi

yace' wallahi ina sanki ne daman,gani ta bude ido yashi saurin cewa bafa San soba, so na kawaye dakuma so na Yan uwa musulmai haka nake nufi,amma kiyi hakuri idan bakya so sai na daina sonki shikenan,yafada yana neman tashi ga mamakinshi sai ji yayi

tace' Ummusalma by name,
A sukwane ya dawo ya zauna,wani irin dadi yaji ya kamashi, sai yaji Shi wani irin free lokaci daya ya daina Jin tsoro tsoronta, numfashi yaja,

yace' kinsan nazaci bazaki amsa min ba?
Itadai nata kallo ne,tana jinshi,.baidamuba yaci gaba

yace' twins ne mu amma ba identical ba,ni mus'ab shikuma wancan yaron mas'ud, munyi karatunmu a spain.amma mu yan Nigeria ne kingane?
Daga masa Kai kawai tayi,

yace' fav bro Yana da tsokana sosai tun muna yara gashi bashi da kunya,bede hakuri,ga Shi da zuciyar masifa, surutu komai ya hada,bejin tsoron komai sai abu daya kinsan menen? Ya tambayeta Yana kallanta, nodding tamasa alamar a,a,cigaba yayi

yace' Yana da tsoron Mata ko kuma nace muna da tsoron Mata don har gwarani ma ni akan Shi, shiru yayi sannan yaci gaba

yace' bamu kadai ba har yayammu shima tsoron matanne dashi Amma ba kamar mu ba, BB ya koma 9ja da na hada ku dashi.
Kallanta yayi yace' kefa fadamin kinsan wani abu a kaina de ko?
Girgiza masa Kai tayi

tace' Akan Chatty, ba Kai ba,
Chatty kuma? Ya maimaita,.
Daga masa Kai tayi a hankali tace mas'ud,
Dariya yayi

yace' shine chatty? Bata daga masa Kai ba amma kuma bata kalleshi ba,
Yace' to ai halin mu daya dashi nikawai Bana da tsokana bana da zuciya kamar tashi shikenan banbamci Amma Duka halinmu iri daya ne kinsan mu twins ne.
Ahaka ya cigaba da bata labarin tsokanar chatty, dayake yi,dukda ba magana take ba Amma tana enjoying jitayi kamar tana tare da Neena,kawai kallanshi take Yana bata labari,sai a labarin bai taba sako iyayen su ba sai dai yace bb.
Suna nan har lokacin magriba sannan ya Mata sallama ya wuce

washegari tare da chatty suka zo amma ko kallansa batayi dukda ya bata hakuri,tun tana shareshi idan Yana sa Baki har take Dan daga masa Kai ko girgiza masa Kai haka suka debe Mata kewa sosai,sukayi exchange number,daga nan kuma Basu sake haduwa ba,sai wani weekend din sosai ta saba dasu tana so ta tambayesu iyayensu fa? Amma kuma batasan mezatace ba tunda ba iya tambayar Abu tayi ba itakam.....

Hope your are enjoying the book =؃=؃

By: '''Hijjart Abdoul'''
Cwthrt=BAKIN WAWA* _Akanji_ _magana_

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023

9

Yau Monday da wuri ta shirya ta fita,tana fitowa ta hango su suna zaune suna hiran su, ko kallan inda suke batayi ba zata wuce da sauri suja tashi suka bita,glip ne

yace' Haba ke kuwa ya zaki wuce ko kallo babu kuma Nasan kin gammu,
Ko kallo be isheta ba taci gaba da tafiyar ta, Chatty

yace' yau yan mutuncin ne kenan ko?
Ya fada Yana Dan Sosa Kai ganin irin kallan da ta watso masa,ganin ma haka yasa shi Jan bakinsa yayi shiru,shima Glip shiru yayi da bakinshi, ahaka suka samu taxi ta Shiga Suma suka Shiga fada masa inda zai kaita,ita da mas'ud a baya mus'ab kuma a gaba, suna baya tafiya tana kallan hanya

tace' meyasa kuka fito da safiya haka?
Kallanta yayi ganin hankalinta a waje yake kuma yasan badan Allah yasa yaji ba to yasan ba zaiji me tace ba,
Kawai mungaji da Zama wuri daya ne, shiyasa muka fito,
Bata kuma maganab har suka iso, suna ta sauka abinta, zata wuce mus'ab

yace' kudin Shiga?
Kallan irin ni nace ku Shiga tayi masa,sannan ta juyo ta kalli Shi

tace' chatty ya bayar,
Ta wuce abinta ko juyowa batayi ba,kallan kallo sukayi sannan mus'ab

yace' chatty kaine fa zaka bayar
Kallanshi yayi

yace' Wallahi yarinyar nan ta rena ni,har wani na bayar,wayace Mata Tou mun fito da kudi, mu Bama mu San zamu fito ba yanzu, yar renin hankali danma ta samu an rakota?
Tunda ya fara ta dawo Amma besani sabida ya juya Mata baya, shikuma mus'ab sai signing yake masa Amma idan sa ya rufe kawai yi yake,bema kula yaci gaba da

cewa' sai na seta Mata burki Wallahi idan bata dena cemin wani Chatty ba,Nasan de na girmeta Wallahi,idan auren kauyena ma ai na haifeta,amma tazo take wani yiwa mutane kallan uku saura kwata ake cewa ko,? Koma mene sai na taka Mata burki tukunna zatasan ta takalo masifa,ya kareshe da kwafa Yana jijjiga Kai,
Mai taxi ne ya fito ya zagoyo yace a bashi kudin Shi,ya bude baki zaiyi magana kawai yaga hannu na miko kudin,Baki a bude ya bi hannun da kallo besauki idonsa a ko ina ba sai a fuskar ta,wani irin bugawa kirjinsa yayi,shikuwa mus'ab mezai yi inba dariya ba,
Kallan mus'ab tayi

tace' Kai Shi yaga psychiatrist,
Kawai ta wuce ta barshi a wurin,shikuwa ca

yace' dalla muje Ka bata hakuri kaji ko twiny kaga Kai kuna good time da ita kaji Dan yayana?

Ohhh yau nazama yaya Kenan to babu Inda zani,ba'a cemin yaya sai ana neman abu,kaga ma tafiya ta yunwa nake ji Nasan zata siya min abinci Kai kuma ko oho,ya kareshe da murmushi a fuskarsa Yana tafiya,
Dakyar ya tattaro jarumtar binsu ciki,Yana Shiga yaga mus'ab a tsaye Yana nemanta sai wurga ido yake Amma bai hango ta ba,zuwa yayi ya tsaya wurinsa

yace' Nima ina Jin yunwar please kace ta aramin kudi idan mun koma Zan bata kaji ko?
Kallansa yayi yace' ba sai na ganta ba watakil ma tayi tafiyarta ta barmu,
Tana Shiga taga aiki da yawa mai yin aikin dare namiji ne kuma baizoba sabida haka ayyukan ya taru dayawa ga kuma mai bada coffee shima bai zoba yau kusan ma'aikantan duk Basu zoba,har ta fara ta tuno maybe suna can suna nemanta,tunowa da abinda chatty ya Mata yasata kwafa ta cire apron ta fito,hango su tayi suna baza ido da'alama ita suke nema,daure fuska tayi ta karasa wurin da suke bata kalle suba

tace' follow me,
Ta juya ta wuce,kallan juna sukayi Basu da ta cewa suka bita, kitchen suka nufa,suka uban kayan wanke wanke,kallan kallo aka fara, ita kuwa tasamu kujera tahau ta daura kafa daya kan daya

tace' sai nace a fara za'a fara ne?
Kafin ma ta ida Kai zance chatty ya nufi wurin ya fara,ganin haka yasa shima Glip zuwa zai fara

tace' Glip abinci.
Haka kuwa Akayi sukaje suka ci abincinsu suka koshi sunayi Yana bata labari har suka gama,ita ta biya kudin sannan suka dawo tare da Shi,a mamakinta sai taga ya zage tana tikar uban wanke wanke wurin,ko gajiya kuma baiyi ba,Amma daka ganshi kasan Yana Jin yunwa, tausayinsa ne yadan kamata, tafara mai dauraya,ganin haka yasa Glip zuwa Yana jera inda ya kamata ahaka suka gama,sunayi ana kawo wasu,a hakade suka samu suka gama, lokacin Azahar nayi suka je bayan wurin Inda take sallah tayi alwala ta Ciro daddumar ta sai da ta idar ta Basu sukayi sannan ta fito tayi sallama da masu aikin ta wuce,tafiya suke Amma babu mai bakin magana, Mus'ab ne

yace' meyasa kike aiki a wurin nan?
Bata kalle Shi

tace' ra'ayi,
Ganin ba fuskar sake tambayar yasa Shi yin shiru bai Kara magana ba,gajiya tayi da tafiyar ta tsaida masu taxi,wannan Karon chatty a gaba ya zauna,a zatan su school zasu wuce Amma sai sukaji ta fadi wani wurin daban, suna zuwa aka Mata sannu da zuwa daga Kai tayi,ogan su

yace' customers ta kawo masu ne?
Girgiza Kai tayi tace' brothers dinta ne?
Da tace brothers dinta ne su kawai kallanta suke suna mamakinta sosai,Basu karajin mamaki sai ji tayi tana cewa the same father the same mother,abin kam ya Basu mamaki sosai,amma koma meye hakan ya masu dadi, introducing dinsu tayi a wurin ogansu, wani Dan daki ta nuna musu tace su Shiga su sameta tana zuwa, bayan sun tafi take cewa ogan ai Suma suna San yin aikin tare da su Amma su tun safe zasu ke zuwa har dare,kuma bai wuce suyi Shara ce da mopping zasu nayi,sosai yayi na'am da zancen ta, sanadiyar tane suke Kara samun customers Akan me kuma bazai taimaki relative nata ba.
Shiga tayi tagansu kowa ya zauna yana duba zanikan dake Dan karamin office din nata,Zama tayi ta kallesu

tace' zaku ke aiki daga safe har dare anan Shara da mopping idan kuma kun iya computer zaku ke editing,
Kallanta kawai sukeyi ca suka ce suna sanyin aiki ne kome?
Ganin irin kallan da suke binta dashine yasata Kara daure fuska tace' naga ku ba karatu kuke ba zaman banza? Shiyasa na yanke wannan shawaran, weather you like it or not,
Ta juya ta fara zanenta hankali kwance bata ko kallansu,
Sukuma daman gasu da tsoron matan tsiya ga kuma dazu mas'ud yaci Mata mutunci,bayarda suka iya hakan za'ayi ma. Koba komai Suma suna bukatar kudin.
Kallanta sukeyi yarda take zanen ta ahankali kamar ba zata Gama ba, tana cikin zanen aka Kira ta,ta tashi ta fita, tana fita wayarta ta fara ringing kallan juna sukayi sannan mas'ud yace'"Ka daga kace bata nan,
Be kalleshi ba ya Ciro wayar daga cikin jaka ganin suna sahr yayi akai hakan yasa

yace' wallahi wannan kawar ta tace mai surutun nan bazan daga ba taab,har wayar ta katse aka sake Kira Basu dagaba ganin ba'a sake Kiraba yasa Shi daukar wayar bakomai ajikin wayar, contact ya shiga,yaga mutane shida ne kawai aciki,daga sunan su sai na sahr sai kuma inda take aiki, daga wayar yayi ya kalli mas'ud

yace' kaga contact dinta mutune shida kawai ne aciki,
Numfashi mas'ud yaja yaja

yace' lamarinta Yana ban mamaki bakadan ba,
Beyi magana ba ta shigo,hakan yasa Shi yin shiru bai Fadi abinda zai fada ba.
Ajje kayan hannunta tayi sannan ta cigaba da zanenta,zuwa Akayi aka kirasu sannan suka fita.
Sunyi aiki kam ba laifi kuma kokadan Basu nuna gajiyar suba Akan hakan, Itakam tana mamakin su,aiki sai kace da can sun Saba?sai dare sannan suka fita,itace ga biya masu kudin taxi,ana Basu abinci a wurin aikinsu.

Sosai suka shaku da ita dukda bata magana Amma ba laifi,hakan na masu dadi,ga kuma kudin aikinsu da ake biyansu, albashin farko suka bata Amma ko kallansu ma batayi ba bare ta amsa,ahaka sukaci gaba da zuwa abinsu tun safe sai dare,ita kuma daga Azahar zuwa dare tare suke dawowa da su,kowa a wurin yasan su har makwabtan shaguna saboda faran faran din da suke da jama'a ga girmama na gaba,gashi ba ha'inci a aikinsu,hakan ya Mata dadi Itakam,
A haka aka dawo hutu,basa haduwa sai wurin aiki
Shima bawani hiran da sukeyi sai zasu tafi.

('('('('('('('
A haka suka cigaba da Karatun su, bangaren su mus'ab kuwa daman two years zasuyi,yanzu kuma befi sauran watanni, su gama, gabadaya basa San tafiya,wata irin shakuwa sukayi ta ban mamaki Dan tafi ta da ma za'a ce,ita kuma a yanzu suna year four hatta sahr tasan irin shakuwar dake tsakaninta da su,sai dai itakam har ga Allah suna

Please Login or Register in order to submit comment