Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiyo ganinta da shirin fita sunsan metake nufi, a gurguje suka fara cire kayansu zasu canja, itakuma fita tayi Wakin Abba knocking tayi, taji ba'a amsa ba tasan baya nan shiga tayi taje taWau kuWi, ta fito ta sauka asa, Sameera tagani zata fita itama taci kwalliya kuma tasan be wuce gidan su awaye ba a yarda take cewa mamannasu, amma itakam tana tantama qkan fitan ta kwanannan, ace duk Thursday, Friday dakuma weekend mutum bayayi a gidan su, taSe baki tayi kawai, tasa kai zata fice Mama dake kallanta cikin kakkausar murya.

Tace, "Ina zakije baza ki faWa min ba ehh?

Shiru tayi bata tanka ba amma de bata fita ba.

"Wai ba magana nake maki ba iyye?nace ina zaki je?

Namma shiru

"At least kya faWi inda zakije ai gudun samun matsala ko kuwade".

Ta faWa a Wan raunane,
Namma bata tanka ba kuma ba ita take kallo ba juyawa tayi tana kallan ofa kamar ba da ita ake ba dai-dai nan su yuysseer suka sauko da gudunsu sukayo wurinta ganin da tayi yasa ta bude ofa suka fita.
Mama kuwa ta buWe baki zatayi magana kenan sai ji tayi an rufe ofa baki a sake.

"Tabdijam dole ma nayi maganin yarinyar nan don wallahi bazan yarda ba taabb kaji yarinyar,inaaaaa bazan yarda ba ai"

Komawa tayi ta zauna ta Wauki waya ta Kira yayarta.

<<<<<<<<<<
Driver na hango ta fito ya taho da saurinsa, durusawa yayi zai gaida ta ta mia masa hannu, alamar ya bata key Win bata yayi ta tafi ta barshi a wurin, tashiga ta kunna motar alamar tana jiran su, sukuwa faWa suka fara kowa nacewa shine a gaba ganin haka yasa driver tashi da sauri yazo

Yace, "Kaga kai Yusuf shiga baya kai kuma Yaseer shiga gaba, Idan zaku dawo sai daya ya dawo gaba daya ya koma baya, ba shikenan ba?Amma kuzo kuyi tafaWa de".

Shiga sukayi kuwa don sun yarda da wannan shawarar, suna shiga kuwa taja suka fita, a motar sukadai suke rawar su kuma suke kidansu agogon motar ta kalla taga 5:30 tasan kafin su dawo magriba yayi, wani store ta shigo tayi parking inda ake parking mota.
Jerawa sukayi suna tafiya sun sata a tsakiya,sun birge na birgewa wasu kuma suce ko kyau(daman dole ba kowa ne zaka masa ba Idan kana da masoya dole daman kana da makiya haka nan rayuwar take).
Siyyaya sosai tayi na kayan da bata dashi,ta siyowa Neena chocolate dayawa itakuma ta siyo biscuits
Yusseer kuwa ai anjida Kaya harda na wasa kayan zaki kuwa ba,acewa komai haka suka gama aka masu total,ta biya suka fita,dagannan sukaje suka sha ice cream sanann suka nufo gida, lokacin da sukazo masallatai dayawa sun idar kasancewar a hankali take tafiya kamar mai tausayin kasa.
Bakowa a parlourn da suka shigo,su suka baje anan ita kuma tayi dakinta sannan taje ta kuma daukowa Sauran kayan,sallah tayi,ta cire kayanta tasa na bacci tadauko Qur'an ta karanta sosai,kuma tayi hadda har Akayi Isha tayi sannan ta kwanta,ta Lula cikin tunanin neman mafita,yau ko adduar ma batayi ba tayi bacci.

Asuba tagari

<<<<<<<<<<

"Alhaji lamarin yarinyar gaba yake yi ba baya".

Kallanta tayi

yace, "meyafaru kuma".

"Wai yau ina Mata magana yarinyar nan don ta renani nizata yiwa shiru ina Mata magana? To infaWa maka yau ko daga kamma da ta saba batayi ba, bifa gaskiya nagaji wallahi a toh a San yarda za'ayi atoh".

Kallanta kawai yake,don zai iya cewa shikam ya gaji da ita ya kagu ta kawar da kanta daga garesu.
Numfasawa yayi sannan

yace, " wato saratu ke naki duk mai sauki ne ni abin dake daga min hankali karatun ta, wanne course zamu turata ta karanta?

"To wezai hana karanci bagaran lafiya kaga tunda bawani kokari ne da ita ba bazata fito da result me kyau ba kuma ba asibitin da zai dauke ta aiki".

"Hakan yayi idan lokacin yayi sai a nema Mata Oxford university ko?

"Amma de kinsani da sauran lokaci tunda befi sauran one month ba su fara exams ba".

"To shikenan Allah ya kaimu".

"Ameen" ya furta sukaci gaba da kulla kullansu

Washagari da wuri tayi Shirin makarantar ta fito lokacin 7:10 bakowa a parlourn sai mai aiki datake gyara parlourn,ta fita
Drivern tane ya taso suka tafi,
Bakowa a class din sai ita tazauna a seat dinta ta fara karatu kamar kullum har aka fara shigowa Amma ba Neena ba labarinta,abun ya bata mamaki ta kalli agogo taga 7:45 Amma bata zoba ahaka de har teacher ya shigo ya fita bata zoba har akayo Break fitowa tayi ko zata ganta tunda jiya tace tazo late bata Shiga class ba haka ta gama zagayen ta tadawo ta zauna a class, biscuit dinta ta dauko ta fara ci ta kalli ledan chocolate din Neena a zuciyar ta

Tace, "yau ma ina kika zauna, jiya kin faWa min karya yau kuma mezaki faWa min ?

Kallan ta gabanta tayi ta Kai hannu ta tabo juyowa tayi ta takalleta alamar Mene? A hankali

tace' Don Allah kinsan gidan su Neena?
Neena? Ta maimata sunan
Ganin bata gane ba yasa

tace' i mean Amina

Ca tace' Mata ehh nasani menene?

"Idan an tashi zaki raka ni Don Allah".

"Da wuri ake zuwa Waukana saidai ki jira idan anzo Wauka na faWa".

Nodding kawai tayi.

Ana tashi kuwa suka fita basu jima ba aka zo Waukar Wayar ta faWa to kawai drivern yace.
Basu jimaba drivernta yazo suka shiga suka tafi Wayar ce tafaWa masa inda zasu,ya kaisu unguwar tana masa kwatance har suka iso kofar gidan.


tace, "kinga gidan munzo",kallan gidan takeyi sosai gidane gidan rufin asiri Amma kuma duk a kwarkwarje gidan yake,duk da Neena bata bata fada Mata ko ita Wace ba Amma kuma a yarda take bata labari tasan bamasu kudi bane Amma batayi tunanin haka gidan yake ba ai,fitowa sukayi suka nufi gidan koda suka karaso sai suka ga Dan karamin padlock a jikin kofar katakon.

Tace, "kinga Ummusalma basa nan yanzu yaza'ayi? Kode muje mukwabtansu muji?

Kai ta Waga mata,suka nufi gidan kusa dasu, sallama Wayar tayi aka amsa masu suka shiga,wata Mata suka gani da yara huWu anana suna cin Abinci,matar da yar fara'arta ta amsa tana tashi.

Tace,''ku shigo kwa tsaya daga nan?

Shiga sukayi amma basu zauna ba.
Matar
Dayar ce ta gaida ta suka gaisa Ummusalma kuwa kawai kallo take binsu dashi musamman ma yaran.

"Daga ina?matar tace

"Ni suna na Aisha wannan kuma Ummusalma mu an makarantar su Amina ne munga jiya da yau bata zo ba shine muka zo muji ko lafiya kuma kinga munzo gidan a rufe?

Tunda tafara matar take kallan ta da tace Ummusalma kuwa Ummusalman take kallo don tanajin labarinta sosai da sosai a wurin Amina,
Ajiyar zuciya ta sauke badan Amina ta gargaWeta kada ta faWa ba mata ba da ta faWa mata komai, Amma kuma tayi alawarin bazata faWa mata ba, Cikin yake da kauda damuwa matar

tace, "ai sun tashi jiya jiya suka tashi wallahi kuma ma garin suka bari kunji ko".
Aisha ce tace to shikenan mun gode sosai juyawa suka yi zasu tafi da sauri matar

tace, "Ummusalma tsaya tabada sako a baki".

Da sauri ta shige dakinta ta dauko Dan box mai kyau ta Mika
Mata.
Tace, "tace a abaki wannan".

Dawowa tayi ta karSa batare da tayi magana ba ta miawa yaran ledar hannunta na chocolate din da tashigo dashi, suka fita.
A mota Aisha ce sai masifa take wai sunje gidan mutane batayi magana ba kuma bata gaida matar ba, da ita ce matar ma wallahi bazata bada sakon ba, ita kadai tayi ta masifar ta takalli driver tace "ring road zaka kaini" sannan tayi shiru.
Kallanta kawai Ummusalma duk abinda ta faWa nakin magana da gaida mutane gaskiya ta fada saidai bata iya ba, batasan ma tana zata fara ba tace wai ina wuni ba'a koya Mata ba gaida babba saidai a gaidata,ba,a koya Mata komai ba na tarbiya tabbas ita an koya Mata kuma tana aiki dashi tunda har zata iya tsayawa drivern gidan su yazo tace ya fada ga inda ta tsaya tasan an koya mata
Tana tunani batasan sunzo gidan su Aisha ba har ta fita sai ji tayi Aishan na cewa

"Godiyar ma Baki iya ba baza kiyi ba,kin bata min lokaci na rakaki Amma ba godiya kekam kinji dadin rayuwar ki wallahi mtsww".

Taja tsaki ta rufe kofar ta wuce,
Runtse ido tayi sabida yarda taji bugun kofar har zuciyarta. Tabbas Bata taba yiwa wani godiya ba,wama zata yiwa godiya bata taba neman alfarma ba a rayuwar ta har da zatayi godiya.yau ta dau karu da Abu biyu gaisuwa da kuma godiya idan an taimake ka.Ahaka suka karaso gidan tana sana'arta.
Yau Friday tasan mutenan gidan basa nan sun tafi gidan kawayen Mama,
Haka ta shige dakinta,wanka ta shiga,koda ta fito bata kalli mirror ba ta wuce tasa kaya ta dawo ta zauna ta jawo jakar ta dauko Dan box din da Amina ta bata, box din ta fara shafawa a hankali bata ankaraba taji hawaye ba ta goge ba,bude din box tayi, zobe ne na silver sai bracelet, da zanen heart a jikin su sai wata yar karamar paper aciki yayi kyau sosai,tana kuka sosai, ta dauko bracelet din tasa a hannunta kamar an gwada cib daidai hannunta,sa zoben tayi sai dai Mata yawa.
Dauko papern tayi ta warware
_TO A YOUNG GIRL WHO WILL GROW TO BE A BEAUTIFUL WOMAN.... JUST REMEMBER BEAUTY IS INSIDE AND OUT, I WISH, ONE DAY U WILL BE ALWAYS SMILING.
HAPPY BIRTHDAY TO YOU......
wani iri kuka ne ya kwace mata tana rike da paper ta karanta ba adadi tanayi tana kuka,tarasa kukan me take,kukan rabuwa da Neena ne ko kuma kukan tunawa da tayi a irin wannan rana ne komai nata ya canja,kuka take sosai mai cike da tausayi,tana har bacci ta dauke rike da papern ta dunkule ta a hannunta.....

By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
Cwthrt= _Akanji magana_


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023


4

Bata farka ba sai 4,da sauri ta tashi tunawa batayi sallah ba,ta shige toilet a gaban sink ta tsaya fuskar ta ta kalla taga yarda tayi wani iri da ita idanta ya kumbura sabida kuka, papern dake hannunta ta kalla ta warwareta ta kuma karantawa taji hawaye ya kuma zubo mata kallan kanta ta kumayi a jikin mirror.

Tace, "a duk sanda nake tare dake inajin wani farin ciki da nishadi marar misultuwa,Amma yanzu nasan bazan kuma samun wannan farin cikin ba,kin kuma sani acikin rudani,meyasa zaki min haka ?dole kina da dalilin ki na boye min koke wacece amma meyasa? Duk Daren dadewa Zaki dawo".

Takarashe tana goge hawayen dake zubo mata, adana papern tayi gudun kar ta jike,zoben ta cire shima ta adana Shi a cikin cupboard, alwala tayi ta dauko papern har ta fito kuma ta koma ta hada papern da zoben ta tafito. Azahar tayi,tayi la'asar tagama azkhar sannan ta fito,bakowa a gidan kamar yarda tayi tsammani, kitchen ta wuce ta tsaya tana tunanin me zata ci, fridge ta bude dauko abarba ta yankata kanana,ta dauko madarar ruwa ta zuba tasa sugar,ta dau teaspoon ta fita garden,kujera tasamu ta zauna tana sha tana tunani,acikin zuciyarta tafara saka abubuwa, daga bisani.

Tace, "yanzu mezanyi?

Wani murmushin takaici tayi ganin tasamu solution cikin sauki,tasan yanzu burunsu akanta ai, wuri dya take kallo ta kai spoon bakinta tayi taji babu komai, bowl din ta kalla taga bakomai ta shanye, tashi tayi ta dawo parlour har yanzu Basu dawo ba ji, agogo ta kalla taga lokaci yaja.dakinta ta hau ta bude balcony ta zauna tana kallon harabar gidan,tana nn har Akayi magriba ta tashi ta koma dakinta,bayan tayi magriba tana azkhar, idon ta ne ya kai kan hannunta,bata ankaraba taji hawaye na zuba da sauri tasa hannu tashare tacigaba da Azhar dinta,kamar kullum ta dauko Quran tayi karatu tayi komai da tasaba har aka kira Isha tayi, tasa kayan bacci ta dauko school bag,karatu tayi sosai wayarta ta jawo ta kalli agogo 11 Amma har yanzu basu dawo ba,kulle kofar tayi ta kwanta.

<<<<<<<<<<

Basu dawoba sai 11:30 yusseer sunyi bacci,dakinsu ta kaisu ta rage masu kayan jikin su ta musu addu'a ta fita wanka tayi itama, coffee ta dafa ta kaiwa Abba Yana zaune Yana aiki da system,a gefenshi ta ajje,

"Thanks". yace sannan ya daura dacewa banga kun dawo da sameera ba,
Kasancewar bada mota daya suka dawo dashi ba,

Tace, "ai sameera tun dazu tamin waya tadawo".

Gyada Kai yayi cike da gamsuwa sabida yasan Sameera nada hankalin uwa uba kuma ga ilimi.
Haka de sukayi tattauna,har sukayi bacci.



Tashi tayi,ta zauna ta jawo wayar taga 1:30am gaban tane ya fadi

tace, "kardai har yanzu Basu dawo ba".

Da sauri ta taso kofar ta bude ta ziro kanta waje ta leka, ahankali ta fito,don ba laifi akwai tsoro, a dakin Sameera ta Shiga dake opposite danata fitila ta kunna Amma bakowa,tsorone ya kamata ta fito, lokaci guda ta tuna sometimes tana kwana a gidan yayar mamansu da gudu ta Shiga dakin su yusseer ganin su da tayi sun dungule suna baccinsu hankali kwance,wata wawar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma dakinta ta kwanta,bata jima da kwanciya ba taji motsi, kasancewar dare kuma ko ina tsit, maimakon ta koma ta kwanta sai ta fito taga waye,a kasan parlour take Jin motsin sbd haka nan ta nufa Sameera tagani a kofar parlourn tana kullewa,mamaki tayi bakadan ba ita bata karasa sauka ba kuma bata komaba ganin zata hawo yasata cigaba da tafiya,maimakon ma ta Mata magana ko kallan ta batayi ba ta wuce kitchen.
Sameera kuwa gaban tane ya fadi Allah yasa bata ganta ba tana rufe kofa ba.Ruwa tasha ta koma dakinta,tana tunanin ko daga ina take Oho?

***********************

Washagari kamar yarda ta Saba duk asabar tana Riga su tashi kafin su tashi tayi wankinta,tayi gyaran dakinta wanke toilet ta gyara duk inda ya dace ta gyara tayi tagama,sai tagama tayi wanka wani sa'in ma sai taci abinci sannan suke tashi wani sa'in kuma ko wanka ma batayi suke tashi.Tana kitchen taji motsin su yusseer suna fada Akan remote. Chips da kwai tayi sai sauce mai kifi aciki, fitowa tayi taga yarda suke fadan wannan na fada dayan ma na fada girgiza Kai tayi baza su canja ba sukam,Wucewa tazoyi.

Tace, "yusseer abinci".

Bada karfi tayi magana ba Amma sunjita. Wucewa tayi dagudu suka bita summa Rigat Shiga dakin balcony suka bude suka zauna itama nan ta nufa, bayan ta dauko masu lemo, Yusuf ne ya dauko masu cup,suna ci suna Santin abinsu
Yaseer

yace, "Yusuf nifa yau bazani tahfeez ba gaskiya nagaji nidai".

Yusuf yace, "bawani ka gaji kawai kace baka iya hadda ba, kuma idan baka jeba amaka duka biyu Dana hadda nakin zuwa".

"Islamiyya kawai zanke zuwa ta yamma ai itama ana hadda".

"Oho de nikuwa dole sai kaje ko nafadawa Abba".

Shiru Yaseer yayi bai Kara maganaba yasan halin Yusuf tsab zai fada,Amma kuma ya kudurta bazai jeba. Ba Wanda ya Kara magana daman shine mai dauko maganar har suka gama suka kwashe kayan suka tafi dashi. Bayan sun fita tunaninta ta fara har ko yaushe ta jima a wurin sannan ta tashi ta fita, tasan yanzu suna parlour su duka saboda haka dakin Abban su ta nufa,safe ta bude taga kudin ba yawa rufewa tayi ta fito har taje bakin kofar parlourn sai kuma ta dawo tunda take bata taba Shiga dakin ba kullum a rufe,yau kam sai ta Shiga tasan yau Yana gida maybe a bude yake , komawa tayi ta murda handle din aikuwa abude yake,Shiga tayi taga wardrobe ne mai kofa uku kawai a dakin sai bedside drawer guda daya, wardrobe din ta bude taga safe guda uku a jere,buder sauran kofar wardrobe din tayi sauran ma haka ne aciki,
Gwada bude daya tayi Amma be budu ba sunnanta tasa namma bai budeba,tasa sunnan kowa a gidan namma haka,kuma password ne ba pin ba,sunaye tayi tasawa be bude ba,gajiya tayi kawai zata rufe wata zuciyar tace kisa ummu,sawa tayi badan tasan zai bude ba,tasawa safe din ya nuna correct,dadine ya kamata,a hankali taga safe din Yana yin kasa Yana budewa kudine aciki dayawa,kudi Bana wasa ba,da sauri ta gwada sauran Suma duk kudi aciki guda daya ce kawai taga takardu rufe me takardar tayi, dankwalinta ta shimfida ta fara jidan kudin a cikin kowanne safe,ita kanta batasan yawan kudin datake jida ba kawai jida take,dayawa ta kwasa sannan ta rufe,ta kulle dankwalin ta fita daga dakin,Jin za,a shigo parlourn yasa ta buya a bayan labile,Abban ne yashigo,zama yayi ya ciro da wayar sa har ya Gama abinda zaiyi sannan ya tashi ya kulle dakin da tafito ya Shiga dakin sa,Yana shiga itakuma tana fita dakinta tashiga ta Adana kudin,ta kwanta.


<<<<<<<<<<

Ranar Monday ta Gama shirinta tsab, dauko jakarta ta tayi zuba dubu dari dayake ta kirka dari dari ta ajje duka one million ne da duba dari biyu,wayarta ta dauka ta fita,bakowa a parlourn ta sa Kai ta wuce abinta
Banki tace ya kaita,bata fada masa wanne ba kawai taga sunyi parking a access,fitowa tayi ta Shiga kasancewar da wuri tazo yasa aka Mata da wuri account ta bude tabada dudu Dari amata transfer cikin account din,
Gobe kace tazo ta karbi atm card.
Daganan park tace ya kaita ko zata ji dadi don kwata kwata bata ra'ayin zuwa school yanzu sabida ba Neena,
Ahaka ta karashe ranar har yamma yadawo ya dauketa.
Washagari ma haka bataje ba daga karban atm park ta wuce,tayi zamanta har yamma.sai Wednesday ne taje amma badan tasan me ake cewa ba kawai tunani take ahaka de satin ya cinye kullum sai ta ba driver dubu dari ya kai banki an Mata transfer a account dinta.





<<<<<<<<<<

Haka ruyuwa ta cigaba da tafiya a wurin Ummusalma kullum ba dadi,kullum cikin kadaici take duk da su yusseer na debe Mata kewa Amma ita kam bata gani haka,haka idan taje makaranta ji take kamar Neena zata dawo Amma kuma baita ba labarinta kuma bata Saba ba,yanzu abin kadan zata tuno sai tafara kuka, musamman idan Neena ta tuno,abin har mamaki yake bata,tayi bakin kokarinta ta daina kukan Amma inaaa bata iyawa sam. Gashi har sun Gama waec da neco yau watan su 1 da gamawa saboda haka maganar tafiyarta kawai ake tayi. A yanzu tunaninta ya karu kuma kwakwalwar ta takasu kusan uku da tunani na daya neman mafita nabiyu kuma abin da zata karanta na uku kuma Neena,wannan abin yabin yana damunta kwarai da gaske batasan ya zatayi ba.

Fitowa tayi kasancewar yau Friday bakowa a gidan sai ita, parlour ta sauko badan tasan me zatayi ba,idan ta Akan TV ta sauko tamanta yaushe rabon da tayi kallo hakan nan yau taji tana so,kunnawa tayi ta zanja Channel zuwa india,film din dake kallo ne ya fara Jan hankalinta,na shahid Kapoor mamanshi naso yayi police shikuma naso yayi film,wani tunani ne yazo Mata,da sauri ta tashi ta kashe kallon tasami mafita Kenan, Da daddare yaseer ya kirata yace Abba na kiranta,bayan shi ta biyo har parlour inda Abba yake zaune Zama tayi batare da ta kalle shiba,shima Bai damu ba.

yace, "wato Ummusalma kinsan mu muka haifeki,kuma kunfi kowa sanki sabida haka badan bama sanki ba zamu tura ki wani guri mai nisa ba,sai dan muna sanki kiyi karatu mai zurfi,ki taimaki alumma gaba daya kinji ko".
Kallan Shi kawai take bako kiftawa tsayawa tayi kamar statue tana kallon shi,
Mama dake gefenshi tacigaba

Tace, "muna matukar kaunarki kinji ko ata,abinda nake sodake Shine kiyi kokari ki maida hankalinki, kiyi rayuwar ki tamkar da kiyi hulda da jama'a sosai.
Sannan kuma zaki karanci gynecologist kinji ko Shi aka samu,don har babanki ya Gama komai da komai da ya kamata har hostel kinji ko?

By: '''Hijjart''' '''_Abdoul_'''
Cwthrt= _Akanji_ _magana_


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023

5

Kawai kallansu take yi,ba ko kiftawa, idan suka ce suna Santa wani irin bakin ciki takeji,wai suna Santa. Abba ne ya mika Mata envelope

yace, "gashi takardunki ne da komai da komai mun ajiye copy a wurin mu,abinda nake so dake shine kiyi karatu,shine ya kaiki,banasan shirmen banza kina jina ai".
Batasan mezatace ba shiyasa ta zabi da tayi shiru,Amma har yanzu bata dauke idan ta akansu ba kallon su kawai take kallan irin kun tsaneni dinnan

"Tafiyar kuma Nanda sati daya ce kinga saura kwana takwas kenan,sabida haka sai kifara shiri kinji ko".

Muryar Abba taji ya fadi haka,
Ganin sungama magana sun dauko wata yasa ta tashi ta fita,dakinta ta koma ta zauna a balcony, envelope din ta bude ta zaro takardun ciki ta dudduba komai, su biyu ne a dakin,don har sunan dayar akwai saidai ba musulma bace daga ganin sunan,maidawa tayi ciki,ta jingina da kujerar tana tunanin tafiyar kuma da dukkan alamu ita kadai zata tafi ina laifin ma su tafi tare sai su dawo Amma zata tafi ita akadai sai kace wani namiji,kuka takesonyi ko zata ji dadin abinda takeji amma yau taga bata da alamar yin kukan,tana zaune anan bata San iya adadin lokacin da ta dauka ba tana tunani, dayar ta tashi ta rufe kofar, alwala ta dauro ta fara sallah tana rukan Allah yasa da alkhairi a cikin tafiyar ta kuma,tare da shiriya.
Tana kwanciya bata jimaba aka fara Kiran sallah dakyar ta tashi da aka shiga sallah,tana idarwa kuwa ta koma bacci. Ba ita ta farka ba sai shaWaya shima su yusseer ne suka zo suka tasheta zasu wuce tahfeez yau za,ayi hakan yasa akace suje goma Amma sai suka ce sai shadaya akace suje, zuwa sukayi suka tasheta suka Mata sallama sannan suka wuce, tashi tayi ta gyara dakin,yaukam sanyinta ta Kara karowa don Saida takusa awa daya da rabi Dana gyaran dakin tanayi tana tunani,ta wanke toilet tayi wanka,batajin zata iya wanki shiyasa ta hada takai laundry.
Lemo ta dauka da biscuit taci ta koshi, fitowa tayi ta Shiga parlourn Abba bakowa a parlourn sai tv dake aiki,dayan dakin ta shiga kudi ta dauko ta dawo dakinta kirga su tai sannan ta zuba su ajaka key din motar ta dauka guda daya Wanda yake wurinta ,sarkan gold dinta ta dauko da receipt dinsu ta hada ta dauko wani key din motar ta Wanda yake a wurinta guda daya shima ta hada.

Bayan tayi sallahn la'asar ta hada su Duka ta sa acikin jakarta, ta fito sameera kawai tagani a parlourn da'alama yau bata je islamiyya ba,wucewa tayi ta fita harabar gidan, drivern ta na ganinta ya taso da Dan gudunsa,yazo zai gaisheta saidai kafin ma karaso ta karasa wurin motar,budewa tayi ta Shiga, shima Shiga yayi sannan suka fita,inda zai kaita ta fada masa,sarkarta ta siyar,ta dawo kudin ta Mika masa,tace ranar Monday yasa Mata a account,daga nan ya kaita park,ta zauna sai dab da magriba suka dawo gida,har zata fita ta bude jakar ta Ciro mukullin motar

tace, "kasiyar da biyu ka samun kudin account".

Ta juya ta wuce. Kallanta kawai yayi to wacce zai siyar tunda ya gane motar take nufi,Bari kawai ya siyar biyun a ajje Mata sabuwar Amma Allah yasa kar yayi laifi.

<<<<<<<<<<

Washegari da rana gaba daya gidan suka tafi rakata shopping banda Abba,duk wani Abu da zata bukata,kayan sawa kam an jide su ba laifi,ita kawai ido ne kawai nata, daga nan suka wuce yawo Basu suka dawo ba sai tara na dare, don haka kowa dakinsa yayi ya kwanta. Haka Mama tasa drivern gidan yake kaita gidan kawayenta acewarta tayi masu sallama,ita kuwa duk inda taje ko sallama bata masu bare kuma gaisuwar da daman can ba gaida su take ba,ko ruwa batasha bare aje ga abinci,haka zata karaci zamanta ba magana,idan kuwa zata tafi ba sallama take wucewa abinta,Haka kawayen Mama zasuyi ta kiranta suna Mata complain akan Ummusalma,ko mama ta sameta ta mata fada,bazai hana gobe ma idan taje takuma yin shirun ba,tun mama nayi har tagaji tayi shiru.

Ya rage sauran kwana biyu ta tafi ta dena fita ko'ina tana gida abinta, Mama kam ba laifi ta Mata snacks da dambun nama sai yaji dayawa, kasancewar tana San

Please Login or Register in order to submit comment