Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaman ya kashe ta.

Manyan kaya ya saka yau,blue shadda dikin half jampa da hula shima blue .cover shoe baki ya saka da da ratsin blue a kan takalmin sai kamshi yake.

Kayan break fast ladi ta dora mishi a katon tray ya shigo da shi dakin ta,ya same ta ta saka rigan da ya ciro mata wani dam karamin gown pink colour.ajiye trayn a tsakiyan rug capet dake tsakiyan dakin,a plate daya ya zuba musu komai sannan ya dauko ta itama ya ajiye ta a gaban abincin sannan yace mata "eat now kisha magani".spoon ta dauka ta fara cin abincin a hankali kaman bata so.ita dai ta banu bata sa wani add uan ya mata ba take shakkan sa yanzu dan ko ido bata iya hadawa dashi tsabanin da da take kallon cikin idon shi ta fada masa magana sin ran ta.

Maganin ya dauko bata shima ba musu ta karba ta sha.hankalin tane ya tashi ganin ya dauko na shafawa.hannu ta fara yarfewa tana hawaye,wani kallo ya bita da shi wanda yasa a take ta natsu.wannan karan a hankali ya shafa mata dan haka bata ji wani zafin kirki ba.

Mikewa yayi yace"zan dan leka office,ba zan dade ba kema ki kwanta ki huta"da kai ta amsa mishi.har ya kai bakin kofa kuma ya dawo cikin,sai da yazo dab da ita sannan ya tsaya.

Zuciyar tane ya fara bugawa da sauri sauri ganin shi a kusa da ita.

Numfashin ta ne ya dauke jin bakin shi kan nata,ya bata light kiss sanna ya fice yana murmushi ba tare da ya juyo ba.

Wani abu taji yana mata yawo a jiki,ji tayi kaman tana yawo a gajmarai.bata taba jin wannan feeling din dan yayi kissing din ta ba kodan da na mugunta yake mata oho.

Ta baya ta fada kan gadon tana murmushi ita kadai kaman sabuwar kamu.
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by Ummee yusuf
(Maman yusuf).


Page 41~42

Baifi awa daya da rabi ba ya dawo gida ya same ta tana bacci,rage kayan jikin sa yayi shima ya hau gadon ya kwanta tare da jawo ta jikin sa ya rungume.ba dadewa bacci yayi awon gaba dashi saboda jiya basu samu isasshen bacci ba.

Karfe daya da minti biyar ya farka but ya kasa tashi daga kwancen da yake'kallon farhat yake wacce ta baje a kan kirjin sa tana bacci hankali kwance gaba daya ta saka shi a wani hali.

Yana ganin alamun zata farka yayi saurin rufe idon shi kaman mai bacci.koda ta bude ido akan fuskan farhan ta sauke su,kallon shi take cike da mamakin yaushe dawo har yayi bacci?


Shagala tayi sosai wajan kallon kyakkyawan fuskan shi,a hankali cikin tsoron kar ya tashi ta kai tana shafa lips din shi da yake matukar burge ta.hakan ma bai ishe ta ba,ta kawo nata lips din tayi brushing kan lips din shi a hankali.kaman dama jira yake taji ya capke ya fara bata hot kiss mai tafiya da zuciya.ko kadan ba tayi yunkuri hana shi ba saima biye shi da tayi,sosai suka shagala farhan sai jujjuya ta ke.

Kiran sallahn azahar ne ya dawo da su hayyacin su,mirginawa gefe yayi yana maida numfashi yayin da farhat kuma a kunya ce ta juya masa baya tana gyara rigan ta da ya zame.

Farhan sai da ya saita breath din shi sannan ya mike ya shiga bathroom ya hada musu ruwan wanka sannan ya dawo ya dauke ta zuwa bathroom din.koda suka shiga wanka ma wajan gasa kafa sai da ya kara dan jagwalgwala ta.alwala tayi sannan ya fito da ita .shi kuma komawa yayi ya kara dana sarki sannan ya fito sukayi sallah.

Yau satin farhat daya da yan kwanaki farhan yana jinyar ta kuma alhmdllh kafafun sunyi sauki har tana takawa da kanta zuwa bathroom ko zuwa palourn ta.a satin nan da sukayi tare yake jin ta a ran shi fiye da tunanin shi.

A bangaren farhat kuma tama manta da duk wani abu da ya faru tsakanin ta da farhan a baya,dan yanzu kullum suna manne da juna wajan bacci,cin abinci ko wanka kuma koda ya fita office ma suna manne a waya dan haka ba kasafai ma yake dadewa a wajan aikin ba burin shi ya dawo gare ta duk da har yanzu basu gama taka matakala na karshe ba a matsayin su na ma aurata.

Yau da wuri farhan ya fita office sakamakon aiki da suka taru mai.

Fitowa tayi palourn sama ta zauna kallo duk kadaici ya ishe ta tana lissafin yaushe farhan zai tashi ya dawo gare ta.tun yanzu she missed him.dan hayaniya ta fara ji a palourn kasa,ynkura tayi dan tashi ta duba ko su waye?sai ganin ladi tayi ta hauro saman,sake baki tayi tana bin ladi da mamaki sannan tace"ke kuma saukan yaushe"ladi da dama haushin ta take ji kuma ta ayyana ta daina daukan cin kashin farhat tunda yanzu ba a karkashin ta take ba.tace"tun ranan da kikaji ciwo farhan ya kawo ni gidan nan amma yace inyi zama na a can kasa,kar in bari kisan ina gidan.yanzu ma shigowa nayi in fada miki kinyi baki".

Daga haka ta juya ta koma inda ta fito ta bar farhat da mamaku ya kusan kashe ta.anya wannan ladi ce,in itace yaushe har raini ya shiga tsakanin su haka,kuma meye ma anan farhan na dauko ladi bada sanin ta ba,kodai da wani abune tsakanin su?a take taji zuciyar ta na mata wsni irin daci da kuna.dayan zuciyar ne ta kwabe ta me farhan zai da mace kaman ladi?a yanda ta fahimta yanzu yayi amfani da hakan ne wajan raina mata hankali.mayb ammi ta turo tane dan kula ita amma ya hana,yake yanda yaga dama da ita da sunan taimako.

Sallaman su ruky ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da ra lula,ganin su yasa ta saki ihun murna suka rumgume juna dan rabon ta dasu tun bayan bikin ta.

Tsokanan ta suka fara wai ta canza tayi fresh ana ganin ta anga wacce take jin dadin rayuwar aure

Cike da shakiyanci ruky ta"hmmm da alamu poor bagger yayi winning game din nan dan naga alamun har ya kwashi gara".shewa suka sa ita da ramlat har suna tafawa.

Tunani ta fara anya kuwa itce? in itace toh me ya same tane?ashe fa da poor bagger take kwana gado daya,wanka tare komai tare,ina alkawarin ta na sai ta kuntata mishi,ko na rama kusan karya ta da yaso yayi?"oh god wat has got into my head"tace tana dafe goshin ta.

Dariyan su ne ya fakar da ita daga tunanin da take,"will u shut up nd stop laughing like fools,taya ma zakuyi tunanin zan iya bawa farhan kaina bayan kusan dalilin da yasa na aure sh.am just waiting 4 d right time ne in nuna masa iyakar sa".dariya ruky tana kara zuga ta,ramlat tana jin su can tace"gaskiya star na dauka by now kun dai dai ta da mijin ki a yanayin dana ganshi so romantic ranan dinnern ku.shiyasa ko rukky tace muzo gidan ki sai ince mata ba yanzu ba dan ku samu good time wit ur hubby but am disappoited in u"

Ruky tace "dont mind this silly gal ba abinda ta sani,how would u even think of that?"haka tayi ta zuga farhat ramlat tana karewa,bata hakura ba saida taga ta dawo asalin unimad star sanban ta kyale ta.

Nan ruky take fada mata she was invited to d birth day party na course mate din su yagana aji.

"Haba ruky ya zaki ce taje birth day party da auran ta?"ramlat tace da alamun damuwa akan fuskan ta.

A kule farhat tace"wai ke din nan me kika mayar dani ne?auran da ban ma san da shi ba kike babatu akai,toh party kaman naje na gama".

"Kyale ta kawai star just ki tabbatar kin haska a wajan su san eh yau star ta fito".ruky tace dariya su kasa ita da farhat."mu zamu wuce soboda mu shirya da wuri kema make sure 4 kina can inji ruky sannan suka tafi.

Suna tafiya ta fada duniyan tunanin ya akayi farhan yaci nasara akan tane?kwata kwata yasa ta manta kan ta"ina ganin wani tsiddabarun su na yan kauye ya min,bari in dawo daga partyn sai yasan nafi karfin bokan sa"tace a sarari tare da tashi zuwa bedroom din ta dan binciko kayan daya dace tasa na zuwa partyn.da kyar ta binciko wata doguwar riga peach colour yar kanti harda dan karamin farmalan shi,veil,poss har da takalmin da zata sa duk ta shirya su ta ajiye shi a gefe.

Zama tayi tana nazarin wani mota ya kamata taje dashi wajan partyn yanda zata haska a matsayin starn ta cos ta san ta samu cars dayawa as wedding gift.mikewa tayi ta duba inda aka aje car keys amma ga mamakin ta babu ko daya.duddubawa take tayi har ta hada gumi can wata zuciyar tace ta duba dakin farhan,tana zuwa shima ta fara bincike can ta hango su cikin wani dan karamin safe din shi mai kama da drower ana ganin komai na ciki dan tinted glass ne.keys ne birjik harda su files.

A zuciye ta koma dakin ta ta dauko waya dan kiran farhan kuma ta nuna mishi ta dawo asalin farhat din ta.ganin tayi sanyi kwana 2 shine ya kwashe mata car keys gaba cewa ma zatayi nashi ne.

Abba ne zaune a office din farhan,saukowan sa kenan daga london .ya shigo su tattauna wani muhimmin issue kamin ya karasa gida amma ya tarar wai ya sauka block 3 duba wata matsala.

Wayan farhan yake ringing a karo na uku kenan har ya kusa katsewa abba ya jawo wayan dan saka ta a silent kamin farhan ya dawo.sunan da ya gani akan screen din ne yasa ya fadada murmushin kan fuskan shi sannan ya daga wayan.

A can bangaren farhat kuma ta cika tayi fam,kaman ita ta kira shi yaki daga mata waya,jin an daga ta fara sauke mishi kwandon bala'i.

A hankali tashin hankali ya maye gurbin murmushin fuskan shi,kasa cewa komai yayi illa gumi da yake tsatsofa masa duk da sanyin ac dake office din.a haka farhan ya shigo yana ganin abba ya karaso cike da farin cikin ganin shi amma yanayin fuskan shi da wayan sa da ya gani a hannun abba yasa yayi turus ya binsa da kallo.

Farhat kuwa tana gama masifan ta tare da bashi umarnin yazo yanzu ya kaita party sannan ta katse.

Sai a likacin abba ya dawo hayyacin sa ya maida duban sa da farhan da ya zuba masa ido.nan da nan farhan ya sauke kansa cike da ladabi ya karaso ya tsuguna gaban abba yana kwasan gaisuwa.

Innalillahi wa innailahi rajiun kawai yake nanatawa"tun yaushe kuke zaune haka farhan"abba yace yana kallon farhan da ke masa kallon rashin fahimta.
"Abba ban fahimce ka ba"yace kansa a kasa.

"Waye poor bagger"abba ya kara jeho masa wata tambayan.da matukar mamaki farhan ya dago yana kallon abba,na ina abba yaji sunan nan,cos shi kam ya riga yasan sun shirya da matar shi.yaushe ma rabon da yaji sunan nan a bakin ta.
"Abba a ina kuma kaji wannan suna".

Nan abba ya bashi lbrn abinda yaji farhat tana fada.

Mamaki da rudani suka hana farhan magana.meye yake damun farhat,anya bata da aljanu?yarinya lafiya lau suka rabu dazu da safe bayan haka yau sama da sati guda suna zaune lafiya.in dai idonun sa basuyi karya ba yana hango soyayyar sa a cikin idon ta den wats going on?

"Na hada ka da girman allah kar ka boye min komai ka gaya min gaskiya"muryan abba ya katse mishi zancen zuci da yake.

Nan farhan ya bashi kadan daga cikin lbrn abinda ya sani game da farhat sannan yace"wallahi abba yanzu ta canza sosai cikin kwanakin nan kuma nasan kuruciya ne zata daina".

Cire hula abba yayi cikin tashi hankali yana cewa laifi nane!!!yanzu ace abinda kunnen sa yaji shine tayi sauki a hakan.lokaci yayi wanda zan gyara kuskuren da tafka a baya.

"Ina son kaje ka taho min da ita gida yanzu ina jiran ku kuma karka nuna mata naji wani abu game da zaman ku"yace yasa kai ya fice ba tare da ya jira amsan farhan ba.


Farhan har ya isa gida bai fita daga rudanin da ya shiga ba.yana sallama a palourn sama ya ganta zaune cikin shiga na alfarma sai huhhura hanci take kana ganin ta kasa bala 'i taka ji.


Da kyar ta amsa sallaman da yayi tana dauke kai,bai damu da sabon reaction din ta yazo ya zauna a kusa da ita.saurin matsawa tayi tana masa mugun kallo kana tace "mallam ka dawo min da car keys dina harda wani zubawa a wata akwalan safe din ka salon wataran kace naka ne ko?


Ya ma rasa me zsi ce mata illa idanu da ya zuba mata"kalle ni da kyau tsiddabarun ka ya daina aiki a kaina"tace tana hararan shi.

"Tashi muje mu gaida ammi"yace yana mikewa.

Dariya tayi tace"kasani ko me ka shirya nafi karfin ka"


A mota ma sai takalan sa da fada take amma ko inda take bai kalla ba dan yanzu ta daina bashi mamaki tsoroa take bashi.sun kusa isa gidan abba aka kira shi a waya bata ji me aka ce masa ba taji yace toh insha allah.


Koda suka shigo cikin gidan ko parking bai gama ba ta balle murfin motan tayi cikin gida da gudu tana kiran sunan ammi.da ido ya bita har ta bace masa sanna shima ya fito yayi palourn bakin abba.


Sallama yayi ya shigo ya samu abba a zaune da alamu shi yake jira.can gefen kafan abba ya zauna yana jiran yaji me abba zai ce masa.


Yace"kana jina farhan ina so kayi hakuri da hukuncin da zan yanke,kana tashi anan nake so ka cire layukan ka da kasan farhat ta sanka da su kuma ina son ka tafi ka barta anan har sai lokaci yayi zan neme ka.


My little yusuf is sick pls kusa shi a addu an ku allah ya bashi lpy.
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by Ummee yusuf
(Maman yusuf)


Salam ina mika gaisuwa da jinjina ta gare ku masoya na,kuma ina mika godiya ta musamman saboda addu'oin ku ĝa little yusuf alhmdllh ya samu sauki.allah ya saka da alkhairi ya biya muku dukan bukatun ku na alkhairi ameeen.


Page 43~44


Cikin wani yanayi farhan yake kallon abba,can dai ya kasa daurewa murya na rawa yace"uhum abba.....abba ban fahimce ka ba"

Murmushin su na manya abba yayi kana yace"nasan hukuncin ba zai maka dadi ba'amma ya zama wajibi a gare ka kayi hakuri da wannan hukuncin gaba zaka gane nufi na.saboda haka ina son ka tabbatar ka toshe duk wata hanya da zata hada ku hatta gidan nan ban yarda ka shigo ba sai na neme ka.yanzu tashi ka tafi allah yayi maka albarka.

Jiki a mace ya mike ya bar palourn bayan yayiwa abba sallama.tuki yake amma hankalin sa va a jikin sa yake ba dan kwata kwata hukuncin abba yayi tsauri dayawa.how can he manage his life witout farhat?koda da suke zaman draman su ba zai iya jure rabuwa da ita ba bare yanzu da ya dandani zama mai dadi da ita.

Bayan fitan farhan abba ya kira ammi bedroom din shi dan suyi magana.zama tayi kusa da shi tare da maida hankalin ta gare shi saboda taga alamun magana mai muhimmanci zai mata.

Nan ya kwashe abinda ya faru tsakinin shi da farhat ya fada mata sannan ya dora da hukuncin da ya yanke.ajiyan zuciya ammi tayi jin abinda abba yace ,kana itama tace"alh wannan abinda ka fada banyi mamaki ko kadan dan nasan ta da wannan halin na kin talaka tun tana yar karamar ta.kuma tun a lokacin da na farga nake kokari na inga na raba ta da wannan mugun dabi'an nata.nd tabbas ina sane da irin rashin jituwa tsakanin ta da farhan kamin auren nasu.

"Haba dear kin san da wannan shine kika rufe ni a duhu"abba yace yana mata kallon tuhumA.

"Ba haka bane alh tsaya kaji yanda abin yake"cewar ammi.nan ta kwashe duk wani abinda abu da ta sani tsakanin farhan da farhat ta fada mishi na irin sharri da sauran su da ta mishi sannan tace"wallahi alhj abinda yasa ban gaya maka ba shine ganin yanda farhan din yake sata abu tayi ko ba tayi niyya ba dan akwai ranan da har wanki ta mishi da kuma yanda na yarda da tarbiyan shi,shiyasa na bada goyon bayan auren nd tabbas nasan ba soyayyar farhan a zuciyar ta,sai dai shi farhan yana matukar son ta ,shiyasa nake ganin zai iya tankwar mana da ita da zaran anyi aure.wallahi bansan abin zai munanta haka ba".

"Har yanzu lokaci bai kure mana ba da sauran lokaci da zamuyi kokarin canza ta in har kin bani hadin kai.koda yake tunda can baya kina iya bakin kokarin ki na daura ta a hanya ina rusawa".
Ammi cikin jin dadi tace"insha allah komai zai zo da sauki tunda na samu goyon bayan ka".haka sukayi ta tattaunawa tare da tsara yanda zasu bullowa lamarin cikin sauki.

A bangaren farhat kuwa tana can cikin bedroom din ta hankali kwance,sai dudduba kayakin ta take yanda suke tsab kaman tana nan har yanzu.

Wayar ta ce tayi ringing ganin ruky ce yasa ta dauka,nan take ce mata ya bata karaso ba har yanzu bayan ga yan depertment din su duk sun iso,tayi maza ta shigo dan kar tayi missing.

"Hey beb i cant make it".

"Why?bayan kince zaki zo har na fada yagana ta ajiye miki most precious table,ko dai poor bagger n kine ya hana ki fitowa".

Tsaki farhat taja sannan tace"could u even tink of dat?waye shi da har ya isa ya hana ni.abba ne ya kira ni yanzu haka ina gida nd kema kinsan halin ammi amma let me see in na gama da wuri zan leko".

"Ok sai kin shigo"tace tare da katse wayan.zama tayi bakin gadon ta tana wondering me ya faru aka kira ta zuwa gida kuma har yanzu bata ga idon abban ma bare tasan dalilin zuwan.

Tashi tayi ta fito wajan ammi ko zata samu haske kuma tana son komawa gidan ta da wuri ko zata samu daman leka partyn

Ammi na ganin ta tace"yauwa yanzu nake shirin aikawa a kira min ke"zama tayi kusa da ammi tare da dora kanta a kan kafadan ammi tace"i missed u ammi na".

"Ba wannan na tambaye ki ba,wuce kitchen ki dorawa mana abincin dare.yau abban ki yace sakwara da miyan shuwaka yake so.akwai sabon kayan ciki da aka kawo dazu shima ki diba kiyi kammomiye.yauwa ki dama kunun mardam da mixed fruit juice".

Baki sake farhat take kallon ammi ba tare da ta iya cewa komai ba.saboda mamaki,dan tasan tun da can ita bata shiga kitchen a gidan in ba abban ta bane zai dawo daga tafiya shima in ta shiga shiririta kawai take musu.amma yanzu wannan abu ta ina zata fara wayanan abubuwa da ammi ta lissaafo mata.

Can dai ta kasa hakuri tace"ammi duk wannan aikin ni kadai, ina su ya falta ne yau?"kara tamke fuska ammi tayi tace"ina saki aiki kina tambaya ta ya falta,ko cewa akayi bansan da ita bane?oya tashi ki wuce kar ki bata min lokaci".

Tashi tayi fuskan nata kaman ta fashe da kuka,har tayi hanyan kitchen taji saukowan abban ta.aiko cike da farin ciki taja ta tsaya tana kallon abban ta cis ta san ba zai yarda tasha wannan wahalan ba..

Zuwa tayi jikin shi tana"abbana i missed u ka dawo lafiya"?cikin basarwa ya amsa mata sannan ya zauna yana kallon ammi fuska a hade yace"me take a nan ne ko baki fada mata sako na
bane"?

"Yanzu na gama fada mata," ki wuce mana kika tsaya kallon my,lokaci na tafiya".cikin mutuwar jiki tayi hanyar kitchen tana mamakin meya samu abban ta yau har da shi ake sata aiki.ba yanda ta iya haka ta shiga kitchen din ita kadai ta fara aiki.ta matukar jigata kamin ta karasa saboda yawan abincin cos daga baya ammi tace abincin duka gida zatayi.

Wanka tayi da ruwan dumi saboda gajiya sannan tayi sallah isha'i,ita kadai taji anincin ta cos ta son shiryawa da wuri kamin farhan ya dawo su koma gida.riga da skirt tasaka na atampa dark blue da ratsin fari a jiki,kwaliya tayi nagani na fada wai kar farhan ya ganta ba kwalliya ya raina ta.(nace anya kuwa farhat)kwanciya tayi kan gadon ta da sunan tana jiran farhan,saboda gajiya bata san lokacin da bacci yayi awun gaba da ita ba.

Sanyin asuba ne ya tashe ta,lalumar farhan ta fara dan ta samun shigewa jikin shi ta koma bacci amma taji wayan hakan yasa ta kara bude idon ta da kyau tana kallon gadon sai a sannan ta tuna ashe fa a gidan su ta kwana.

Kara kwanciya tayi wondering me ya hana farhan dawo ya dauke ta.

Koda tayi sallah kara komawa bacci tayi,sai dai ba tayi wani nisa a baccin ba ammi tazo ta tashe kan ta fito ta dora break fast.

Turo baki tayi irin itafa ta gaji nan buge bakin ammi tayi tace"zaki gyara zaman bakin nan ko sai na kumbura miki shi,dallah ku wuce ki dora kinsan abban ki zai fita office da wuri nd kar ki fara cewa abu daya zaki mana make sure kinyi abu uku zuwa hudu".

Haka farhat ta fito ta yi girkin nan kala uku kaman yanda ammi ta umarce ta,duk ta jera su a kan dinning zata wuce dan yin wanka ammi da abba suka fito cikin shigan alfarma sai zuba kamshi suke.

Wucewa zatayi dan yin wanka bayan ta gaishe su amma ammi ta tsaida ta kan ta zauna tayi break fast tukun ta wuce.zama tayi a takure dan gani take at any moment farhan zai iya shigowa nd bata son ya ganta a haka.

Tattare kayan tayi bayan sun gama ta wuce kitche yayin da ammi ta raka abba.koda ta dawo ta same tana shirin fitowa a kitchen nan ammi tace mata"ina zaki je bakiyi wanke wanke ba kuma wa zai tattare miki kitchen din ?"

Idon ta duk ya ciko da hawaye ta koma ciki ta fara wanke kayan fa suka bata,tanayi tana hawaye koma mene farhan ya zo su koma gidan su dan ta lura yanzu iyayen nata sun tsane ta.

Ammi ta tausaya mata amma dole ta danne zuciyar ta.

Koda ta gama da kitchen zata wuce ammi ta kira ta kan taje bedroom tayi mata kabbasa ma suturun ta sannan ta wanke mata toilet.

Farhat tunda tazo duniya bata taba aikatuwa irin na yau ba,saboda wankin toilet din yabata wahala sosai cos bata taba yi ba gwara girkin shi ta iya ki wuya ke hana ta.

Tana shigowa dakin ta wayar ta ta raruma ta shiga neman layin farhan dama dan jan aji taki kiran shi jiya amma ganin yanda take azabtuwa a gun ammi gwara tattara ta koma gidan ta.sai dai tana kiran layin taji switch off.haka ta zauna dawayan a hannu bayan tayi wanka ta shirya,ta kira sau ba adadi.

Ammi ta kyale ta bata sata gurkin dare ba ganin ta galabaita sosai.

Suna zaune a palour da iyayen ta ana hira amma ita hankalin ta gaba daya ta tattara ta maida shi kofa tana ganin kaman yanzu farhan zaiyi sallama ya shigo.

Kasa daurewa tayi tace "abba bansan meya hana farhan zuwa ba kuma ina ta gwada layin shi bata shiga".

Abba hankalin shi na kan t v yace"mama na kinsan poor baggers din nan basu iya samun waje ba sai sun nuna maka halin su,ni bansan ma ya akayi na yarda da auren ku bama.ina ganin tsiddabarun su na talakawa ya mana kuma zamu nuna mishi bokan sa yay kadan.ki kwantar hankalin ki dole in nemo shi kuma in raba auren nan kaman yanda na hada shi".

Zuciyar tane ya shiga bugawa da sauri sauri sai bin su da ido take ta kasa furta kada kalma daya.
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by ummee yusuf
(Maman yusuf)


Page 45~46

Kwakkaran motsi farhatbta kasa sai ido da ta zuba musu mai cike da tashin hankali,wani wahalellen yawu ta hadiye da niyan yin magana ammi ta riga ta.

"Bana son yawan surutu,ai kinji abinda abban ki yace so ki kwantar da hankalin ki.yanzu dare yayi je ki kwanta in allah ya kaimu gari ya waye sai mu karasa maganan" ammi tace mata da murmushi akan fuskan ta ganin yanda duk ta rude lokaci daya kuma wannan yana nuna alaman tana son shi sai dai girman kan ta ya hana ta fahimtan hakan.

Mikewa tayi tana jan kafa kaman kazan da kwai ya fashewa a ciki.tafiua take amma bata san a wani yanayi take

Please Login or Register in order to submit comment