Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta juyo.

Farhan ne ya fito daga wanka,daga shi sai Dan karamin towel a kugun Sa daya kuma yana goge gashin kansa dashi.baima San da mutum a dakin ba,ita kuwa ya fito a haka yasa duk ta daburce Dan tunda take bata taba ganin namiji haka ba.da sassarfa ta nufi kofan fita,sai da ta kama handle din kofan sannan tace"they are waiting 4 u at d dinning"ba tare da ta juyo ba kuma bata saurari abinda zaice ba tayi ficewar ta da sauri tana sauke ajiyan hrt.dariya yayi yana gurgiza kai,ya cigaba da shirin Sa a gurguje.

Fitowa yayi ya same su har sun fara cin abinci sakamakon karya da farhat ta tsula musu,cewa wai
yace shi ba yanzu zai ci abinci ba.dukawa yayi har kasa ya gaida su,amsawa sukayi cikin sakin fuska.Abba yace"Ai mun dauka baccin weekend din ne yayi dadi da kace ba yanzu zakayi break din ba".kallon farhat yayi da ta matse tana cin abincin ta hankali kwance,cos yasan aikin tane.kujera yaja ya zauna opp dinta sannan yace"eh abba naso taba baccin ne kuma sai na tuna ina da meeting"ok yana da kyau,ka kara himma"abba yace ya cigaba da cin abincin sa.

"Serve him" ammi tace ba wasa a fuskan ta.tashi tayi ta zuba mishi amma na mugun ta dan sai da ta cika plate din kaman cin mutum 2 sannan ta koma ta zsuna ta cigabs da cin abincin ta.

Bismillah yayi ya fara ci yana satan kallon ta,itama hakan ta kasance dan tana dago ido suka hada,bakin ta inda jiya ya dana mata yatsa ya dan taso yayi ja.alama ya mata da bakin yana mata dariya. duk haushi ya cika ta,bayan shi ya mata mugunta kuma ya zauna yana mata dariya.kwafa tayi tare da galla masa harara.dariya ya karayi, yakara nuna mata bakin shi ya mata alaman kiss.a zuciye ta mike tana cewa"ammi bari in shirya zan tafi islamiya"bata tsaya jin amsan ammi ba tayi gaba.raka ta yayi da ido yana dariya.

Juyawan da zaiyi yaga abba na kallon sa,sukuyar da kai yayi yana sosa keya tare da in ina sai kame kame yake, da yaga bazai fitar da shi ba shima tashi yayi ya fice daga parlourn gaba daya.dariya abba da ammi suke,abba yace swthrt ina ganin gata da muka saka date din bikin nan a kusa if not yaran nan?hmmmm"yace yana girgiza kai.ammi tace"ni da nake tare dasu kullum ina ganin drama kala kala,sai kauda kaina nake inyi kaman ban harbo jirgin su ba".

A bakin gate ta tarar dashi yana zaune a bencin bamodu mai gadi,suna hiran su da yaran kanuri.lbr mai ban dariya ba madu yake bashi dama shi ba dai surutu ba.shiko sai kyalkyala dariya yake.ko inda suke bata kalla ba a zuciyar ta tace da alama daga kyauye daya abba ya dauko su.

Da kafa take tafiya saboda islamiyan nan kusa ne bayan layin su dan haka bata daukan mota.

Tana cikin tafiya taji ta bayan ta ance"hi yam mata ji mana"a masifan ce ta juyo dan taga wani dan rainin sence din ne da yake mata magana a cikin anguwan su.a iya sanin ta duk guys din anguwan shakan ta suke,wasu dan kudin babanta.wasu kuma saboda rashin mutuncin ta yasa bada kula ta.

Arba tayi da kyakkyawan fuskan sa asual yana mata murmushin sa mai kara masa kyau.wara ido tayi ba shiri ganin shine ya biyo ta,shima wara mata idon yayi yace"ya kika fasa masfan?ko da yake kinga mijin ki dole ki nutsu".

Zataui magana ta fasa,ta juya ta kama tafiya sauri sauri,"hey easy mana,kar kije ki karya kafa ko kin manta hills ne a kafan ki"bata kula shi ba,duk yanda yaso tayi magana taki.har bakin gate din islamiyan ya rakota sannan ya koma.

Duk da anguwan nasu na masu kudi ne ba mutane sai daddaya.wayanda suka gansu tafe yana mata magana kuma bata mishi rashin mutuncin da ta saba ba.sun jinjina mishi kuma ya ciri tuta koda yake shima ya hadu koma ace ya fita haduwa.dalilin da yass taki kula shi kenan kar yan anguwan su su rainata.(nace toh su farhat abi a hankali dai).

Cikin tashin hankali ta kira frnds din ta akan su zo gida su same ta,tana cikin Matsala.nan ko sukace gasu nan zuwa.bata taba daukan zancen bikin da muhimmanci ba sai yau da taji ammi tana waya da kannen ta mata 2 game da bikin kan gobe zasu wuce da babbar yayar su zainaba zuwa dubai dan yi mata sayyan kayan daki dana kitchen.kuma taji yayar abban ta ba gaaji zata zo gobe ta tafi da ita gidan ta dan gyaran amarya.

Sai bayan azahar suka samu karasowa suma cikin tashin hankali dan sun san abinda zai sa farhat sanyi haka ba karamin abu bane.

Tana kwance idanun ta a rufe suka shigo suka same ta,ramlat tace"ba dai bacci kike ba star,ko baki da lafiya ne?"tashi tayi ta zauna idon ta duk ya canza kala zuwa ja."subhanallah wai beb meke faruwa ne?kin bar mu a duhu"rukky tace tana zama kusa da ita.nan ta kwashe abinda yake faruwa ta fada musu.ramlat har da dan ihun murnan ta,tace"kice ke dama kan ki kikayiwa tanadi shiyasa in na nuna kulawa ta a kanshi kike jin haushi"kefa wata banza ce when it comes abt boys sam baki da tunani.in ba haka ba ina ni ina wannan banzan"farha tace tana huci.Ruky tayi ajiyan zuciya tace"ni a ganina star ba abun tada hankali bane,tunda yabiyo tanan kema ki nuna mishi ruwa ba sa an kwando bane.kiyi amfani da wannan daman kiyi ta gasa mishi aya a hannu.in har kika bari ya ganki haka,zai ce kin tsorata da game din kar ki yarda yayi winning a kanki.kuma mu zamu baki tips na yanda zaki wana shi sosai yasan lalle yayi kuskure da ya taro wasa dake".

Haka suka zauna suna ta bata shawara da karfin guiwa,har taji yes zata iya.daga nan kuma suka fara tsara yanda bikin zai kasance.
[11/30, 8:31 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by ummee yusuf(maman yusuf).


Page 23~24


Ana sauran 10 days biki ammi da kanwar ta sukaje dubai danyi mata kayan daki dasu kayan kitchen.itama a ranan yayar baban ta tazo ta wuce da ita dan gyaran amarya.farhan shima ya koma can gidan yan uwansa da suka zo saboda biki acan dambuwa road. dan haka basu kara haduwa ba kowa harkan gaban shi yake but farhan yana nan yana fama da missing dinta amma haka yake ta dannewa.


sun buga iv na events kala kala_kala umar shine mai rabawa anan cikin garin maid,shi kuma farhan duk wayanda sukayi karatu tare a abroad ya gayyace su.farhat tana gidan auntynta ana mata gyara jiki bata da time din fita sai su ruky ke aikin rabon iv.


Bangare 2 duka angama ahirye shirye sai biki ake jira.


A al'adan yan maiduguri,ranan wednesday ake fara shagalin biki. kuma a ranan yan gidansu ango suke kawo kayan yin snacks gidansu amarya. irin su flour mai sugar da sauransu.


Su kuma yan gidan amarya su shirya snacks in a different ways akai gidan su ango.


Sun kawo kayan a mutunce, amma har yanxu amarya tana can gidan auntyn ta shiyasa basu samu daman ganin ta ba.


On 1hurs kuma shine ranan lalle,shima yan gidan su ango, su suke kawo kayan sata a lallen.


Tun kaman 10 na safe ammi ta aika druver ya dauko su ita da frnds da cousins dinta da suke mates. tasha gyara na musamman kowa yasan yan maiduguri da iya gyara ,fatan nan nata yayi sumul dashi sai sheki take ga kuma wani special kamshi da take na wani hadin darrot da aka mata.cikin yan uwan ammin ta akwai wacce take aure a sudan ita ta taho da mai lalle tun daga can.ta mata nagani nafada.ya kara haskata ta fito amarya sak.


kawayanta sai hayaniya suke irin na kawayen amarya but banda ita,duk ranta a cunkushe yake fuskan nata ba yabo ba fallasa dan zuciyar ta yaki mata dadi sam'ba zata iya cewa ga yanayin da take ciki ba.


At night kaman da karfe 8 ammi ta shigo daki ta same ta cikin kawaye tace"farhat kije can compound farhan na kiran ki,nd dont waste time"ammi tace sannan ta fice,shewa sauran yammata suka sa suna mata tsita wai angonta ya kasa hakuri akai masa ita ya biyo ta. tana jinsu ta share sai da ruky tace"ta tashi taje mana karta bata musu plan,tana kokari tana dannewa kar ya gane kuma mutune ma zasu fahimci wani abu dan haka ki saki ranki ki nemo smile kisawa a face dinki har agama bikin daga nan sai musan abinyi da zamuyi next".a nan ta samu kwarin gwaiwa,tasa dogon hijab har kasa sannan ta fito compound din tsayawa tayi tana kallon cars da suke birgik ta rasa a wace car yake,shi kuwa tunda ta fito yakura mata ido ko kiftawa ba yayi duk da hijab ne a jikinta bai hana kyaun ta fitowa ba. flash light din car din ya danno mata sannan ta juyo tana karewa motan kallo.


Wata mota tagani mai balain kyau Modern 2018 ne, black colour sai sheki yake a ranta tana mamakin yanda abbanta yake sakewa mutane kudi kaman bai sun zafin suba. dakewa tayi ta nufo motan da gayya ta canza takunta sai wani yauki da rausaya take,baki ya sake yaba kallonta har ta karaso bai sani ba.


Tafa hannayen ta tayi a fuskan shi sannan ya dawo hayyacinsa. murmushin nasara ta sake ganin kama shi ba zaiyi wuya ba.shima yana ganin ya fara sakin layi,wayance wa yayi yace"me na wani claping a face dina kina tsammanin banga fitowarki bane ko me just come in da car i hav important things to do".

matsewa ita ma tayi tace"no need just fada min me ya kawo ka nima ina da baki nd they are waiting for me"baice mata komai ba ya fara kokarin bude kofan motan.ganin haka yasa ta dan matsa ta bashi waje a zatonta fitowa zaiyi dan suyi magana.ba zato ba tsammani sai ji taji ya finciko ta cikin motan ta zube a jikin shi,sannan ya maida murfin motan ya rufe.

Kiciniyar kwace kanta ta fara yi amma ta kasa dan ba rikon wasa ya mata ba.

"Wai meye haka ka wani matse ni?koda yake irin karatun da ka koyo a london kenan,toh kasani ni ba tambadaddiya bace ko ka manta irin aauran da zamu yi ne?"

Kallon karamin bakin ta yake yanda take motsa su ya bala'in bashi sha awa.

Ganin tsura mata ido kawai yai,duk masifan da take ko a jikin sa,yasa tace"kai villager ko poor bagger zan ki........"hannu tasa ta rufe bakin ta da wuri ganin yana shirin dana mata dan yatsa a baki.

Dariya yayi yace" mesa kika rufe?ki bari mana in koya mushi hankali.yasan abinda zai furtawa hubbynki".

"Hubby my foot"tace tana hararan shi,still hannun ta na kan bakin ta.hannu yasa a seat din baya ya dauko wani bban leda hadadde kana gani kasan ba ta kasar mu bace.

Daura mata akan cinya yayi yace"wannan kaya ne da zaki sa ranan dinner".

Wani ledan ya kuma daukowa yace"wannan kuma get pass ne ki rabawa frnds danki",wani madai daicin leda ya kuma daukowa bounches ne na kudi a cikin yace na liki. dariyan rainin sence ta fara mishi tace"hmm na jinjinawa abba na nasan all dis are from him,dama ammi ya bawa ta bani will be better.

Kallon ta yake cikie da takaici,can dai ya daure yace"nima bada son raina na kawo ba,nabi umarnin abba ne.if not baki isa in taso takanas ta kano da kawo miki abu ba.now get lost".yace a fusace.

Fita tayi sannan ta juyo taja tsaki tace"in mantuwa kayi bari in tuna maka,motan dai na uba ne ba na............"

Ganin ya bude mota a fusace ya nufo ta yasa ta kwasa a guje tayi cikin gida.murmushi yana yana girgiza kai yace"zamu hadu ne yarinya.
[12/1, 6:35 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by ummee yusuf(maman yusuf)

Page 25~26


Yau friday ana gobe daurin aure kenan kuma yaune za'ayi wushe wushe a gidansu amarya,dan haka tun safe ake ta decorating din garden dan a nan za'ayi shagali.

gidan cike yake dankam da yan uwa da abokan arziki duk sun hallara kowa hidimomin sa yake.


bayan isha'i alokacin kowa a gidan abba manya da kanana mata da maza,dq kawayenta duk sun hallara a wajen da akayi decoratig din suka zazzauna akan fararen kujeru,ga kuma inda aka tanadar dan zaman amarya da ango. zuwan ango da yan uwansa ake.


Basu dade da zama ba,kuwa ango da yan uwansa suka iso tare da masu kidan gargajiya irinsu ganga kura dasu kullecham, farhan yayi kyau cikin shaddarsa wagambari wanda aka masa rinin gargajiya wato dongashau, blue and black da hularsa ma black abokansa suna mara masa suka rakoshi har inda aka tana da dan zamansa.


Bayan kaman 15min aka fito da farhat itama cikin shaddarta irin na farhan sai dai banbacin colour ita nata pink and black ne,aka nada mata wani lafiyayyar luffayanta white wit pink flowers ajiki ta bala'in yin kyau kama ka sace ta ka gudu.


Ga manyan frnds dinta suna take mata baya kanwar amminta na rike da wani designer koskon turaren wuta kamshi sai tashi yake,a haka suka rakata mazauninta kusa da angonta.


Tunda suka fito farhan ya zuba mata ido,tunda yake bai taba ganin kyaunta haka ba. tana zama kusa dashi wani fitinannen kamshin turaren wuta ya masa maraba, amma dan neman fitina irin na farhan yayi kasa da murya yace "kai kai wannan wani irin turare kikasa ne haka?kwata2 ba kamshin sa ba dadi nd ga yanda liffayan nan ya maida ke kaman wata tsohuwa".


yanda yake magana kasa kasa kuma fuska sake in kana wajan zaka zata abin arziki yake fada mata.duk da tasan ya fada ne dan neman fada sai da taji haushi amma itama tayi murmushi mai kayatarwa tace,


"Wayyo poor bagger duk irin kokarin da abbq na yake na yaga ya rabaka da tsohuwar yun uwanka amma abin yaci tura tunda har yanxu baka gani mai kyau."

tsuke dan karami bakinta tayi tace "so sorry."

murmushi ba tare da yace komai ba ya kamo hannunta yana murzawa da dan karfi ,tana jin zafi amma ta shanye a haka aka fito dasu filin rawa anata musu liki shima haka ya fara mata ruwan kudi.anci ansha sai wajan 11aka tashi daga taron.


RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA.

Yau asabar,ranan daurin auren kenan.
Taron motocine birjik tun daga kofar gidan alh abubakar har zuwa kusan lagos street duk motoci ne, baki daga gida da kasar waje duk sun taru ciki kuwa harda skehun borno da governor,anan ckin massalaci kofar gidan abba aka daura auren MOHAMMED MUSTAPHA dA amaryarsa AISHA ALH ABUBAKAR ALIBE akan sadaki naira million1 da sisi 20,inga farhan a ranan kaman bashi ba,shagan manyan kaya da yayi ciki fararen kaya su kara haska shi kana ganin sa kasan shine agon.bakin nan yaki rufuwa sai gaggaisawa yake da manyan baki da suka hallarci daurin auren da kyar samu ya kwaci kan sa,ya sbiga cikin mota ya rubuta mata short msg.


FINERLY D GAME START NOW!!!.abinda ya tura mata kenan.

Tana zaune bakin gadon ta,yau tunda ta tashi jikin ta yake a mace murus kaman ba farhat uwar tsiwa ba.sai kallon mutane take da suke ta kai kawo,ko wanka ta kasa yi.

Karsn shigowan msg a wayan ta yasa ta duba, zuciyar tane ya buga da karfi ganin abinda msg din ya kunsa.ita fa wlh ta dawo daga rakiyan wanan game din da ba kai ba gindi.a kan wannan abin take son wasa da rayuwar ta?gaskiya da sake ya kamata insan abinyi b4 is too late.tace a ran ta.

Da kyar su ruky suka kwantar mata da hankali tare da lallaba ta tayi wanka.a fatima beauty saloon a nan aka dauko mai mata make up.ba bata lokaci ta fara tsantsara mata make up cikin kwarewa,nan da nan ta zama kaman wata tauraruwa sai kyalli take.wani danyan less ta saka fari kal dashi mai adon flowers pich colour,aka nada mata head shima pich ga dan kunne da sarka wanda na daham tare da abin hannu da zobuna.kai ta fito masha allah.ganin jama a yasa ta dan saki ran ta ana ta hidima tare da ita.


Bayan la asar ammi ta hada walima inda aka gayyaci malama aisha mairi ta wa aztar sosai akan hakkin aure.kowa jikin sa yayi sanyi a wajan bama kaman farhat da ta rasa ya zatayi.

A lokacin aka kawo kayan lefen ta,dan a al adar yan maiduguri sai ranan daurin aure ake kawo lefe.kaya kam ba mgn dan akwati 12 aka mata ,fadan kayan cikin ma bata lokaci ne,saboda gaba daya na kasar waje ne disigners masu tsada.kowa sai san barka yake.banda farhat da taji suna koda kayan tabe bakin ta cos tasan wannan aikin abban ta ne.


Sai yamma likis aka tashi daga waliman,kowa dauke da katon jaka shake da savaniour mai hoton amarya da angon ta.


Ruwan wanka aka hada mata da yasha kayan kamshi na asalin shiwa da kanuri,sai a sannan hankalin ta ya kara tashi ganin fa wai da gaske auran ta ake,auran ma da wannan poor bagger da tafi tsana a rayuwar ta.kin shiga wankan tayi,ganin za a takura mata,yasa ta fita tayi hanyan bedroom din ammin ta.a bskin kofan dakin suka hadu da ammi tana fitowa.

Kallon tuhuma ammi ta bita dashi"farhat me kike anan ?ke da ya kamata ace kina wanka"?.

Hannun ammi ta kama ta fara tafiya ba tare da tayi mgn ba,ganin haka yasa ammi itama tabi ta ba musu.

Basu tsaya a koina ba sai can garden,ba kowa a wajan.suna zuwa ta zaunar da ammi akan kujera ita kuma ta durkuss agaban ta.ammi bata ce komai ba sai bintq take da ido.



Dago idon ta tayi da ha cicciko da hawaye tana kallon ammi tace"bana so auran nan ammi dan allah ki fadawa abba na a fasa".

A rude ammi ta dagota tace"wat farhat kina cikin hankalin kuwa?........."



Pls kuyi manage da wannan muna biki ne.
[12/2, 7:02 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by ummee yusuf(maman yusuf).

Page 27~28

Hawayen da take rikewa ne ya zubo,jikin tane yayi sanyj ganin yanda ta tashi hankalin ammin ta.ta yaya ma zata fara fada mata auren game zatayi,wasa fa kenan?"bana son barin ki ne Ammi"tace wasu hawayen na zuba a idon ta.

Ajiyar zuciya ta Sauke tare da rungumo ta zuwa jikin ta,dama ta riga da ta harbo jirgin ta sai dai ba zata so miji kaman farhan ya kubcewa yar ta ba.dan haka cikin rarrashi tace"haba habibty wannan da kike gani shine yakin mata kuma shine darajan ki.da an kai ki zaki saba ne,nd nasan will take care of u sosai.ki kwantar da hanklalin ki,wata rana ba mu ba,kema zakiyi alfahari da auran nan kinji ko?"


Kai kawai ta iya gyadawa,hawaye na cigaba da zubo mata.can kasan zuciyar ta tana shirya yanda Zata bakanta masa ya sako ta a daren yau din nan kowa ya huta.

Har bakin bathroom ammi ta rako ta,tayi wanka ba wani dogon make up aka mata ba.

Shirya ta akayi cikin wani white sari hadadde sannan aka dora mata farar alkbba a kanta,tayi kyau kamar wata yar sarauta.sai dai hawaye yaki tsaywa a idon ta.

Wajan abba da yan uwan sa aka fara Kai ta,suka hadu suka mata dan nasiha tare da fatan alkhairi.daga nan aka wuce da ita bedroom din ammi,itama tana zaune cikin yan uwan ta suka mata nasiha sosai.yanzu kam kuka take kaman ta shide,sai cewa take su taimaka mata wlh ta fasa auran.duk dauriyan ammi sai da tayi kwalla,da kyar aka sata a mota akayi hanyan gidan ta dake jiddari filin polo.


Gida ne nagani na fada komai na gidan sai ya burge kadan kaman kana outside saboda tsaruwan gidan.flowers ne kala kala zagaye da compound din,ga wani round about a tsakiyan gidan da yake fitar da ruwa gwanin ban sha awa.

Akwai garden,swimming pool da b/b fild da sauran su.hawa daya ne gidan, katon palour ne a kasan mai dauke da 3 bedrooms,palon yasha kujerun alfarma komai na parlour ash nd black ne.bedrooms din akwai toilet aciki kuma an kawata dakunan da royal bed masu kyau,akwai kitchen hade da storen shi anan kasan.saman kuma madaidaicin palour ne mai dauke da royal cushions kana gani kasan yafi na kasan yafi na kasan tsada,shi kuma komai na ciki brown nd milk colour ne.a cikin parlour akwai kofofi hudu,daya dakin din shine na farhan da palourn sa a ciki,kayan part dinsa sun fi na ko ina kyau da tsada an kawata shi komai blue nd white.daya kuma na farhat ne yanda tsarin na farhan yake itama haka nata yake an shirya mata shi wit her best colour pink nd white.sai dayan kuma single room ne da toilet shima an shirya shi da kaya dark nd light green.dayan kofan kitchen ne da store a hade.kai komai na gidan yaji zan zan.

Akan makeken gadon ta aka zaunar da ita har yanzu kuka take but bai kai na dazu ba.

7:30pm suka ce a shirya za a tafi dinner.sabon kwalliya aka mata ta masifan kyau cikin white wedding gown,sai net din kayan da aka yafa mata akan ta da yasha gyara.pink high hills da poss din shi ta saka,turare masu kamshin dadi aka feshe ta da su.

8:00pm aka fara kwasan yan mutane zuwa gurin dinner.sai da aka kwashe duka mutane,saura amarya da sauran frnds dinta.fitowa sukayi su ramlat sun sata a tsakiya sai kuma wata cousin dinta mai suna amma buwa da ashe.roko ta sukayi har bakin wani sport car fari kal dashi sai dsukan ido yske,suna zuwa suka bude kofan baya suka tura ta ciki su kuma suka juya zuwa motan da zata kai su.

Gunguni ta fara tana turo dan karamin bakin ta gaba,dan ita a zaton ta tare zasu zasu tafi amma dan wulakanci irin nasu suka barta ita kadai.

Tunda ta shigo motan yake kallon ta,duk masifan nan duk akan idon sa ji yake kaman ya kaman ya kamo ta ya tsotse lip stick bakin ta amma ya dake.

Jin kaman ana kallon ta da kamshin turaren sa da taji yasata juyowa da sauri,ganin shi tayi zaune ya zuba mata ido.ya sha suit ash colour da farar shirt a ciki da pink neck tie,agogo da takalmin kafan sa duk black ne.ya bala''in yi mata kyau sosai ya fito a angon sa sak.

Ta shagala da kallon sa ko kifta ido ba tayi,ya wara mata ido yace"kallon fa,ko kin kyasa ne?"tabe baki tayi tana yatsina fuska sannan tace"meye abin birgewa a villager,kana ganin kayi clean ko?kalli kan ka a mirrow har yanzu kana nan a villagern ka".

Kura mata ido yayi yana kallon ta,motsowa yayi still ido shi akan ta.jawo ta yayi sosai jikin shi ya manna ta a kirjin shi ,dama yana nema ya fake da wannan .matse ta sosai yanda zata ji zafi yace"me kika ce miss ego?"ganin yanda ya matse ta yasa tayi shiru tana hararan shi kasa kasa,"magana zakiyi yan mata ba juya ido ba"yace yana kokarin kai bakin shi kan nata.

Jin tsayuwar mota yasa ya ture ta daga jikin shi cikin borin kunya yana gyara zaman coat dinsa.

Sun kai 2mins kamin aka bude musu kofa suka fito,har lokacin ba wanda yace dan uwan sa kala.zagowa yayi inda take ya rike mata hannu ga kawayen ta sunyi layi cikin ankon su na wani pink material.taku suka fara zuwa cikin hall din ana take musu bayaamma buwa tana bin su da kaskon turaren wuta.sauran kawayen ta suna rike da spray suna ta fesa musu,sai hasken flash light ke tashi.suna shigiwa cikin makeken hall din d.j ya saki wakan auren su,har kan high table suka rako su sannan kowa ya nemi table din shi ya zauna.aka fara gudanar da shagaki cikin tsari da wayewa dan biki ne na zallan yan boko.

Ga abokan farhan mafi yawa masu jajayen kunnuwa ne.

Bayan bude taro da addu a,aka nemi abokin ango ya fito ya bada tarihin ango wani wani bature mai suna mark shi ya fito ya bada tarihin ango.tabe baki farhat tayi a ranta tana tir da son rayuwar karya da farhan ya dorawa kan sa,in ba haka ba ina shi ina fito da wannan katon arne kuma bature a matsayin aboki ina abokan sa na nan din?kwafa tayi tana hararan sa kasa kasa.

Sunkuyowa yayi wajan kunnen ta yace"in na fito ds abokaina na

Please Login or Register in order to submit comment