Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai dadi,ki dauka cewa har yanzu kina tare POOR BAGGER kine ba wani ba. Nima zan dauka har yanzu ina tare da MISS EGO na da na sani tunda ne kinga kuwa zaman mu zai bada citta".yace yana dariya.

Cusa fuskanta tayi a kirjin shi tana dariya itama.

Zame mata rigan baccin jikin ta yayi tare aika mata sak'onni masu zafi da d'aukan hankali dan dama daurewa yake tun dazu saboda wannan humran ya gaba tayar masa da hankali ,biye shi tayi suna ta romancin din juna saboda ya saba mata hakan a baya.

Hankalinta ne ya tashi ganin yau da gaske yake son Angwacewa.

Ganin haka nima na basu waje dan wannan sirrin nasu yafi karfina bare in d'auko muku rahoto.
Farhan fuska cike da farin ciki yake ta aikin rarrashin Farhat da take ta zuba mishi kukan shagwab'a.da kyar ya samu bacci ya d'aujeta.

Da washe gari,shi ya taimaka mata tayi wanka tayi sallah dan jikinta duk yayi tsami more especially cinyoyinta.

Komawa bacci suka kara yi bayan sunyi sallah.basu suka farka ba sai wajan ten na safe wannan ma yunwar cikin su ya tada su.

Farhat fita tayi zuwa kitchen dan samo musu abinda zasu ci a lokacin Farhan ya tafi dakin shi dan canza kaya.

Da ya dawo bai ganta a d'akin ba.zama ya danyi a bakin gado a zatonsa tana wanka ne.jin shiru baiji motsin mutum a bathroom d'in ba yasa shi lekawa ciki amma bata ciki.

Fitowa yayi dan neman ta tare da tunain ina ta shiga ita da ba lafiya ne da ita ba.

Yana fitowa palour yaji motsin ta a kitchen.

Tana soya chips taji ya rungumota ta baya ya cusa kanshi a wuyanta.cikin muryan rad'a yace "why my shining star,keda bakida lafiya mesa kika fito?i should have do this".

Bata juyo ba tace " bakomai zan iya shiyasa na fito,je kayi kwanciyar ka na hutar dakai".

Baya son aikinta yafi son taje ta kwanta.ya san in yabi ta lallami bazata je ta kwanta ba dan haka cikin muryan tsokana yace "ke nifa jagwalgwale ne bana son ci,dan haka ki bari in karasa".

Cike da masifa ta ture shi tace" eh dole kace baka iya cin jagwalgwalo ba mana tunda ka sha min kwacen ko satan abinci".

Shima cikin fushin ya nufa yana cewa" waye b'arawon abincin?"

Hanyan fita a kitchen d'in tayi tana dariya tace " in kamanta bari in tuna maka dana gaji har nasa maka maganin........"

Ganin ya nufo ta gadan gadan yasa ta fita a guje tana darya.rufa mata baya yayi suka rinka zaka zagaye palourn suna ta dariya.

Hanyan sauka kasa tayi yayi saurin cafkota,d'agata sama yayi yana juyi da ita.kankame wuyan shi tayi tana dariya tare da magiyan ya sauke ta kar ta fadi.

Bai dire ta a ko ina ba sai kan 3 seatern,kwantar da ita yayi shima ya haye saman tare da yi mata rumfa suna sauke numfash.a hankali ya kai bakin shi kan nata yana kallon cikin idon ta.saurin lumshe su tayi.

Kaurin girkin da taji ne ya sata ture ta mik'e tayi hanyan kitchen da sauri.bai bi ta ba saima lumshe ido yayi dan baiso wasan ya kare a nan ba.

Fitowa tayi daga kitchen d'in kaman zatayi kuka tace" kaga shike nan abincin ya kone kuma bansan ya zanyi ba".

"Je ki sa hijabin ki muje resturant muyi breakfast a can".

Cike da jin dad'i tayi part d'inta da gudu dan shiryawa.

Bakin abaya ta d'ora akan riga da wando dake jikinta,tayi rolling da farin veil mai d'an fad'i ta fito ta iske shi ya canza shiga shima cikin half jamfa na d'anyan voiel milk colour,bai saka hula ba sai gashin kansa da ya kwanta lub yana shek'i.

Wani lafiyayyan resturant suka je a can circula road.

Breakfast mai rai da lafiya ya musu order suna ci suna hiran su gwanin sha'awa kana ganin su kasan sun jik'u cikin soyayyan juna.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha Allah 🤝)


Page 61~62


Imagration office dake custom area suka wuce dan fara shiye-shiryen tafiyan su london.basu bar office din ba saida suka kammala abinda ya kaisu.

Kusan karfe 2suka shigo gida a gajiye lis,part din shi yaja ta dan suyi wanka.

Ba k'aramin lokaci suka bata ba a bathroom da sunan wanka da kyar tayi masa dabara ta fito tana masa dariya.

Fitowa yayi ya same ta sai tana aikin duba mayukan shafawan sa na kan mirrow.

A bayanta ya tsaya yana kallonta ta cikin madubin sannan yace " me kike dubawa ne,ko inje in kwaso miki naki?"

"No ina dubawa ne ko akwai na bleaching" tace tana yatsina fuska.

Matsowa yayi jikinta sosai ya rungumota ta baya yana dariya yace "ni kuma me zai hadani da bleaching sai kace mace?wannan ai sai ku".

Juyowa tayi tace " serious Allah in naga maza sun cika fari sai inga kaman bleaching suke shiyasa suke bani haushi".



"Kice nima ina ciki kenan"yace yana kokarin zame mata towel din jikin ta ya cigaba da cewa "bari in shafa miki ki gani dan tabbatarwa ko".


Rik'ewa tayi da sauri tana cewa" a'a wallahi ba sai ka shafa min ba na yarda".

Dariya yayi yace " matsoraciya kawai".

Murguda mishi dan karamin bakin ta tayi tace "eh din na yarda".tare da fucewa a d'akin dan zuwa part d'inta dan canza kaya.

Kitchen ta shiga bayan ta shirya cikin 'yan k'ananan kaya,riga pink da boom short fari sunyi bala'in yi mata k'yau.

Tsayawa tayi a kitchen tana tunani,dan ta rasa me zata girka musu mai sauk'i.

Ahaka Farhan ya shigo ya same ta,shima ya shirya cikin farin wando 3 quater da armless dark blue shirt.

"Ya dai my shining star?"yace yana jawota jikin shi.

Fuska ta shagwab'e kaman zatayi kuka tace" bansan me zan girka mana ba 4 lunch".

Dariya yayi cikin muryan tsokana yace " abu mai sauk'i,kiyi mana tuwon semo da miyan kuka.hmmm so yummy".yace yana lashe baki.

Turbune fuska tayi kaman taga kashi " haba dai .iyan kukan kakewa haka?"

"Ni dai gaskiya shi nake son ci". Yace yana kunshe dariyansa ganin yanda Farhat ta had'a fuska kaman ta fashe da kuka.

Juyawa tayi zata shiga store,ya dakatar da ita yace tayi musu indomine kawai saboda yunwa yake ji sosai bazai iya jiran tuwon ba.

Cikin.jin dadi ta fara aikin yana taya ta suna hiran,har suka kammala.a babban.plate ta juye musu suka fito suka zauna a dinning suka fara ci.

A parlourn sama suka yada zango,Farhan zaune a kan rug ta mik'e kafafu shi kuma Farhan ya d'ora kansa a kan cinyanta suna kallon wani series da ake a zeealwan.

Wayan farhan ne yayi ringin Farhat tasa hannu ta d'auko mishi,"wake k'ira?"ya tambaye ta.

"Ummi ce"ta amsa a gajarce.

Karb'a yayi da sauri ya amsa,gaisawa sukayi da Ummi harda Sumayya tana tambayan shi Farhat dan Ummi ta bata labarin yayi aure.nan ya had'a su da Farhat suka gaisa."aunty tare zaku zo da yaya ko?"Sumayya ta tambaya.

Su Farhat iyayen son girma sai wani jinta on top take saboda Sumayya ta kirata da Aunty.

"Karki damu lil sis tare zaki ganmu very soon" tace mata.karb'an wayan farhan yayi yana mata dariya yace " shekara d'aya kawai kika bata shine harda wani cewa lil sis?"

Hararan wasa ta auna masa tace "ashema na girmetan kenan?kuma ba ban girmeta ba dole ta kirani Aunty cox ina auren yayanta".

Haka yacigaba da tsokanarta,ita kuma sai kumfan baki take.wayar shi ta karb'a tana tab'awa ya kawo ba security kenan.

Kallonsa tayi tace" mesa baka son sa lock a wayarka"?

"Haka nan kawai,sai kayita sa lock a waya sai kace mara gaskiya?" ya amsa mata hankalin shi na kan kallo.

Shiru tayi na wani lokaci tana tunani kana tace " ya kamata kasa koda na tump print ne saboda baka san mugu ba".


D'an murmushi yayi sannan ya tashi zaune daga kwancen da yayi yace " kina tsoron kar wani ya min abinda kika min kwanaki a gidan ku ?"

Saurin rufe fuskanta tayi saboda kunya kamin yayi yunkuri tayi part d'inta da gudu.

Kiran sallahn magrib da akayi shi ya hana shi binta da yayi niyya,dan haka alwala yayi ya fita masallaci dan gabatar da farali.

Farhat ta dad'e a tsaye jikin k'ofa duk kunya da sabon nauyin Farhan sun hanata sukuni barin ma in ta tuna irin abinda tayi masa a daren da tayi niyyan yi masa mummunan sharri.sai nadaman tado da zancen lock d'in take.

Bata tashi akan sallaya da tayi sallah magrib ba saida ta had'a da sallahn isha'i sannan ta tashi ta shiga wanka,tana fitowa shirin kwanciya kawai tayi tabi lafiyar gado saboda a yanda take ji bazata iya had'a ido dashi ba.duk da yunwar da take nurk'usar ta haka ta hakura ta kwanta.

Farhan shima bai shigo gidan ba saida yayi sallahn isha'i sannan ya shigo.yanda yaji gidan shiru kuma ga kan dinning d'in wayam yasa shi fita dan yi musu take away.

Har ya dawo baiga alamun ta fito ba,murmushi yayi a ranshi yace "DRAMA QUEEN" ajiye kayan hannun shi sannan ya fad'a part d'in shi dan wanka.

Ciki kayan bacci mai k'yaun gaske milk colour ya fito.direct part d'in Farhat ya wuce yana addu'an Allah yasa bata sa key ta ciki ba.

Cikin sa'a yana tab'a k'ofan yaji ta bud'u,shiga yayi har can cikin bedroom d'in.

A kwance ya same ta ta rufe ido kaman mai bacci.

Ba wasa a muryan shi yace ta tashi suje taci abinci kar ta kwana da yunwa.saboda yasan halin ta inya ce lallab'ata zaiyi,toh ba zata tashi ba

Yanayin da taji muryansa ne ya hana ta yin musu,ta sauko suka fito tare.

Ita ta kawo komai na buk'ata ta juye musu abincin.

Ko kallon inda take bauyi ba saima had'a fuska da yayi yana cin abincin sa hankali kwance.

A dole Farhat take tura abuncin zuciyarta ba dad'i tana tunanin ko abinda ta tuna masa ne ya bata masa rai.

Suna gamawa yace ta same shi a d'akin shi yanzu. yayi tafiyar shi ya barta da fargaba dan bata manta wahalan da ta sha a hannun sa ba jiya.

Brush taje tayi bayan ta tattara wajan da suka ci abincin sannan ta nufi part d'in shi tana jan k'afa.

A kwance ta same shi ya kashe wutan d'akin sai dim light da ya bari a kunne ya dan haska d'akin kad'an.

"Wani abu kike jira ne a can d'in,da bazaki karaso ba".yace yana kallonta ta cikin duhun d'akin ya dariya k'asa-k'asa.

Bata bashi amsa ba ta karaso jiki a sanyaye.

Zama tayi a bakin gadon idonta duk sun ciko da kwalla tace " dan Allah Ya Farhan kayi hakuri in na b'ata maka rai".

"Ni ba abinda kika min.oya hau ki kwanta da k'yau" yace yana nuna mata gefen shi.

Hawowa tayi ta kwanta d'an nesa da shi.

Jawota yayi jikin shi yana dariya yace " matsoraciya kawai wa yace miki kin min laifi?inba hakan nayi miki ba da kina can d'aki wai ke kunya.

Kukan shagwaba tasa mishi tana d'an dukan kirjin shi da hannu tace "kai ko,wallahi sai na rama".

Dariya yake mata yace "ba sai kin rantse ba nasan ai ba'a miki ki kyale sai kin rama".

Kissing d'inta ya fara ganin takiyin shiru,aiko kaman jira take tayi mukus.

Da kyar ta kwaci kanta ganin yana son zarcewa.rungumeta yayi tsam a jikinsa yana maida numfashi.

"Kana da hoton Sumayya a wayanka?" yaji ta tambaya kaman mai rad'a.

D'ayan wayansa dake kan side drower ya d'auka ya kamo mata galary,yace "gasu nan harda na ummi da abby"yace tare da mik'a mata wayan.

Hotunan iyayensu ta fara cin karo dasu kala-kala duk cikin shigan alfarma.

"Kunfi kama da abby akan Ummi sai dai yafi ka fari sosai" Farhat tace idonta akan wayan.

Murmushi yayi yace" haka kowa ke cewa,amma ni nafi ganin kaman mu da Ummi".

Masha Allah tace da tazo kan hotunan sumayya kala-kala wasu tana k'arama da lafiyarta, wasu kuma ta girma duk da tana kwance ba lafiya amma kyanta bai b'uya ba.

Nan ma tace " Sumayya tafika k'yau".

Haka ya rinka nuna mata pics d'in uncles d'insa dasu aunt d'in sa.ba suyi bacci ba sai wajan 11 da wani abu.

Tun ranan da abu ya shiga tsakanin su,ba abinda ya shiga tsakanin su sai dai wasanni da yake mata wajan wanka,wajan Kallo ko kuma in bed.tun tana dari dari har ta saki jikinta sosai dashi.

Bayan kwana 5 komai na tafiyan su ya kammala,ana gibe zasu tafi suka je gidan Abba dan yi musu sallama.

Sosai su abba suka ji dad'in ganinsu cikin kwanciyar hankali.

D'an nasiha sukayi musu sáñnan sukayi musu sallama suka koma gidan su.

Fitan safe sukayi karfe 8 a airpot tayi musu dan ta abuja zasu tashi.

Saiga su Farhat a jirgi.

Sanan readers zasuyi mamakin innace duk rawan kanta yaune farkon hawan ta flight.

Ita da kanta dariyan kanta take saboda da kuruciya ya rufe mata ido tana kiran mutane villagers,ashe itace babbar villagern.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha allah🤝)


Page 63~64


Sanarwa aka fara a cikin jirgi kowa ya d'aura seat belt d'in shi jirgi ya kusa tashi.

Kokuwa da nata Farhat ta fara,Farhan yana kallonta ya share yayi kaman bai ganta ba.

Zata juyo yayi saurin maida hankalin shi kan wayansa da yake daddannawa.

Kaman zatayi kuka ta cigaba da gwadawa.yana kallonta ta gefen ido tare da kunshe dariyansa.

Dakyar ta samu ta rufe ya bata wahala sosai,d'agowan da zatayi suka had'a ido.aiko dariyan da yake rikewa ne ya k'wace masa.itama taya shi tayi sukayi mai isar su sannan suka tsagaita.

Yana kallonta har yanzu dariyan bata barshi ba yace" haba ace unimaid star guda bata iya d'aura seat belt ba,ya akayi haka ta faru?"

Turo baki tayi alaman tayi fushi ta juya masa baya.dai-dai kuma jirgi ya fara yunkurin tashi,gam ta kama hannun Farhan ta rik'e tare da rintse ido.

Bata bud'e idon ba saida taji jirgin ya dai-daita a sararin samaniya.tana budewa suka had'a ido da Farhan da ya zuba mata ido yana kallonta.

Duk kunya ya gama rufeta.

"Abba bai tab'a yarda na fita ouside ba,shiyasa hawa na flight yayi karanci.munje hajji dasu Abba tun ina 6years daga nan ban kuma fita ba.
Akwai lokacin da Abba ya biya mana umra dukkanmu,time din ina 15 years unfortunately nayi wani mugun rashin lafiya aka fasa tafiyan dani daga nan kuma ba'a kuma yunkurin fita dani ba.hope ka gane". tace ba tare da ta kalle shi ba.

Hannu yasa ya jawota jikin shi sannan ya sunkuyo dai-dai kunnenta yace " waya tambaye ki madam i love my wife d way she is?"

Gyara kwanciyanta tayi a jikin shi tare da lumshe ido tace " ba dariya kake min ba".

Sun sauka lafiya a abuja,zaman awa d'aya kawai suka yi a airpot sannan suka d'aga zuwa london.

A cikin jirgi Farhat tana manne a jikin Farhan tana ta bacci abinta.

Sun sauka a london by 7pm, a gajiye lis bama kaman Farhat da b'ata tab'a dogon tafiya haka ba sai yau.

Motoci ne kusan 5 suka zo taran su ga guards d'in shi birjik fararen da bakin fata duk suna cikin bakak'en suit.

Cikin girmamawa guards suke musu sannu da zuwa yana amsawa da fara'a shimfid'e a fuskan shi.

Tunda suka sauk'a Farhat ta sake baki da hanci tana kallon tsaruwan airpot d'in.

Wata had'ddiyar mota Lamborghini bak'a wuluk sai shek'i take,shi aka bud'e musu suka shiga gidan baya suka zauna.guards d'in shi kuma suka shiga sauran motoci 4 suka kama hanya.2 a gaba 2 abaya ya zama nasu na tsakiya,sannan suka kama hanya.

Farhat tayi mukus ko tari ta kasa in banda raba ido da take cike da mamaki.

Wani tangamemen gida taga suka dosa,suna zuwa bakin get d'in d'aya daga cikin guards d'in ya danna remote.da kanshi get d'in ya bud'u suka shiga ciki.

Dogon tafiya sukayi kamin taga sunyi parking agaban wani mansion mai dan karan k'yau.

Yawu ta samu ta had'iye dakyar sannan ta dawo da idonta kan Farhan da yake ce mata su sauka.

Bata tab'a zaton haka Farhan yake ba,dan yanzu ta daina mamaki tsoro ma yake bata.

Kamo hannunta yayi suka sauka,har yanzu kalle-kalle take.ko ina fitulu ne masu haske wanda ya maida gidan tamkar rana.zata iya rantsewa gidan su Farhan ya ninka nasu a girma so hamsin.

"Welcome to my home".taji yace mata yana murmushi.

Yake kawai ta iya yi dan ta kasa furta kalma ko daya.

Wani madaidaicin k'ofa ta suka nufa suna zuwa ya d'ora babban yatsan hannun shi a wani d'an k'aramin glass dake gefen k'ofan.

Scarnning d'in d'an yatsan yayi sannan taji muryan mace na cewa welcome home Farhan.tana ji k'ofan ya unlocking kansa sannan ya bud'e.

Wani ratsatsen parlour suka shiga wanda tsaya bada labarin shima bata lokacine.

Matan turawa ne sun kai su biyar a jere suna musu barka da zuwa.wani k'ofan suka kara shiga nan wani parlourn ne da yafi na farko ga kuma hanyan hawa stairs guda 2 hagu da dama.

Na daman suka hau shima wani sabon duniyan ne,wata dattijuwar mace fara sol suka tarar tana tsaye,tana ganin su ta karaso da saurinta ta rungume Farhat tace " barka da zuwa 'yata".

Yake Farhat tayi mata kawai dan har yanzu bata tan-tance a ina take ba.

Langwab'ar da kai gefe Farhan yayi kaman zaiyi kuka yace " mamy ni kuma kin mamta dani ko?"

Rungume shi tayi tana dariya tace " ina ni ina manta d'ana? Zumud'in ganin surkata ce yasa.".

Shima dariyan yayi sannan ya canza fuska yace " mamy sumayya fa?"

Kamin ta bashi amsa sai gata wata baturiya ta turo ta akan wheel chair sun fito daga wan d'aki.

Da sauri ya karasa gabanta ya rik'o hannayenta hawaye na tsiyaya daga idin su.baki na rawa tace "Yaya"

Farinciki kaman yayi me haka yake ji yau lil sis d'insa ce haka? Kanta ta d'ora a kafad'ansa ta fara kuka,bubbuga bayanta yake yana share mata hawaye.

D'ago kanta tayi tana kallon Farhat da itama hawaye ya gama b'ata mata fuska tana kallon su cikin tausayi da sha'awa.mik'o mata hannu Sumayya tayi tana murmushi,da gudu ta karasa gurinsu ta rungume Sumayya tana cigaba da hawaye.

Mamy da take tsaye tana kallonsu,share d'an hawayenta tayi sannan ta karaso itama tace" ya isa haka Farhan kuje kuyi wanka da sallah sannan kuzo kuci abinci.

Kama hannunta yayi suka sauka k'asa,stairs na hagun suka hau nan taga yafi ko ina k'yau da tsaruwa.wani bedroom taga ya bude suka shiga wanda yayi parlour wani 2.

Rage kayan jikinsa yayi ya juyo yaga tana nan tsaye bata da niyan motsawa.

D'agata yayi cak,sai cikin bathroom room dake cikin d'akin.nan ma abin kallo ne.shi ya tayata cire kayan jikinta sannan sukayi wanka suka fito.

A gurguje suka shirya sannan yaja su sallah,suka rama salloli da ake binsu.

Suna idarwa ya buk'áci su fita ana jiran su wajan cin abinci.

Jiki a mace ta mik'e tana gyara veil d'in kanta.yana so su had'a ido amma taki d'ago da kai bare su h'ada.

Hannayen shi duka 2 yasa ya tallab'o fuskanta yana kallon k'wayan idonta da suka cicciko da k'walla.

Girgiza mata kai yayi yana mufmushi.

Fad'awa tayi jikinsa ta kankame shi ta saki kukan da take dannewa.ita ya zatayi,dama haka yake har ya iya zama a gidansu tare da juran wulakancinta k'wando-k'wando.

Bayanta yake shafawa a hankali yace" meya faru kuma uhum..."

Cikin kuka take cewa ya yafe mata dan Allah badan ita ba.

"Shhhhhhh.....stop that muje muci abinci su mamy na jiranmu".yace ya jata suka fita.

Dinning arean babba ne sosai shake yake da abinci kala-kala kaman na cin mutane 20 ga kujerun 12 zagaye da table d'in.anan suka samu Mamy,Sumayya da sauran uncles d'insa su uku da suka zo masa sannu da zuwa.


Bayan gaishe-gaishe turawa guda 2 da suke tsaye a gefe suka fara serving d'insu.ga mamakin Farhat harda abincin gargajiya na kanuri sauran kuma bata ma san su ba.

Hira k'adan suka tab'a akace suje su kwanta sun gaji zuwa gobe zasu dawo tare da matansu da yaransu.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha allah🤝)


Page 65~66


Suna kwanciya sai bacci saboda gajiya da suka k'waso.

Da washe gari sai karfe 10:30am sannan suka fito saboda komawa baccin asuba da sukayi.

Sun fito fes dasu kaman masu zuwa dinner,a dinning area suka tarar da Mamy da Sumayya suna jiransu.

Har k'asa Farhat ta duka tana gaishe da Mamy,cike da jin dad'i take amsawa da murmushi a fuskanta.

"Tashi ki zauna daughter,ki bar durkusa min dan ni ba surkuwarki bace ki d'auke ni matsayin mahaifiya kinji?"

Kai Farhat ta daga mata tana murmushi dan sosai matar take mata kwarjini.

A kusa da Sumayya ta zauna tana mata ya jiki,da fara'a ta amsa mata da sauki.

Farhan yaja kujera ya zauna kusa da Mamy,d'ora kansa yayi a kafad'anta sannan yace " good morning Mamy".

Shafa gefen fuskan shi tayi kana ta Amsa tana tare da zolayansa da girmansa yake shagwab'a.

Murmushi yayi har fararen hak'oransa suka bayyana yace "shagwab'a sai Uncle tahir yazo ma zanyi mai dalili".

Dariya Mamy tana girgiza kai dan tasan yanda yayansu tahir ke jida Farhan.

Bayan sun gama breakfast ne suka dawo d'aya daga cikin palourn suka zauna.Sumayya kanta akan cinyan yayanta.Mamy tana basu labarin likitan da yayi nasaran farfad'owan Sumayya.

Sallaman Uncle tahir ne ya katse musu hiran da suke,da gudu Farhan ya tashi kaman wani k'aramin yaro ya k'arasa gurin Uncle d'inshi tare da rungume shi.cikin jin dad'i shima yasa hannu ya rungume shi yana cewa " i miss u my boy".

Janye shi yayi jikin shi tare da cewa " dagani na mant u re not a boy now ka zama big man tunda har ka ajiye mata".

Turo baki yayi kaman k'aramin yaro yace " ka daina fad'an haka Mami zata mana dariya".

Dariya Mamy tayi tace " na yaushe kuma aina gama ji".

Zama sukayi kan kujera hannun su sakale dana juna kaman wasu abokai.

Dan d'ago kai Farhat tayi ta saci kallon mutumin,ganin shi tayi cikin suit grey colour wanda ya dace da farar fatan shi.k'yakk'yawan gaske ne shima.

Zamewa tayi daga kan kujeran ta gaishe shi cikin fara'a ya amsa yana tambayarta su Abba.

Farhan ne yake tambayan Uncle ina su Aunty fadila da me sunan Ummi n shi.

"Maryam tana Malaysia ta raka Auntynku wani business trip ,su Abdallah kuma suna nan shigowa anjima ka'dan tare da sauran yan uwanka.

*******************
Uncle tahir shine babba acikin 'ya'ya 6 da iyayen su suka haifa.yana mata d'ayaHajjiya Fadila da yaransu uku,Salim,Junaid sai auta sai Maryam wacce taci sunan mahaifiyarsu Farhan.dukansu shida matarsa y'an kasuwa ne ga boko kuma dan haka suma suna da kud'i bakad'an ba.

Maryam mahaifiyarsu Farhan ita ke bi mishi.


Sai jabir shima matarsa d'aya Hajjiya nooratu ita bata aiki tana zaune abinta,basu da d'a ko d'aya.

Usman shike bin Jabir matarsa d'aya da d'ansa d'aya yaseer.

Hamza shima Allah bai basu haihuwa ba shida matarsa Hajjiya hafsat

Hajjiya salma wato mamy itace autarsu mijinta ya dad'e da rasuwa ya barta da yara 2 duka maza hanif da huzaifa.

Alhaji Mustapha wato baban farhan duk shi ya dawo da 'yan uwan Ummi nan kusa dashi tare da basu jari mai tsok'a.wanda yazama sillan arzikin su.ita Mamy bayan rasuwan mijinta ta dawo nan london cikin 'yan uwanta tare da kula da Sumayya.

Familyn kansu a matuk'ar had'e yake suna son 'ya'yan da 'yar uwarsu ta bari saidai shi Uncle Jabir nashi na daban ne.sun shaku da Farhan sosai tun Umminsu nada rai.

Suma yaran gaba d'aya kansu a had'e yake kaman yanda suka ga iyayensu sunyi.

Maryam kowa na nuna mata kulawa da gata sanadiyan ita kadaice mace a cikinsu dan lokacin Sumayya na kwance ba lafiya.sunfi shakuwa da Farhan dan tasu tazo d'aya kuma yafi shagwab'ata sabida takwaran Umminsa ce.
Wannan kenan.

Uncle Tahir bai dad'e suna hira ba sai ga sauran 'yan uwansu sunzo tare da iyalan su.

Nan gida ya kacame da hayaniya ganin iyayensu sun wuce.tsiya suke tayiwa Farhan wai ya zama magidanci.

Shi kuma sai kare kansa yake Sumayya na taya shi.

Farhat duk sai taji zaman parlourn ya isheta duk da suna kok'arin janta a jiki.amma sam ta kasa sakewa dasu.

Basu bar gidan ba sai bayan sallahn isha'i sannan suka tafi.


Sai da suka shigo bedroom sannan suka samu kad'aicewa.

Fitowan ta kenan daga bathroom d'aure da d'an karamin towel tana goge ruwan jikinta da d'ayan.

K'uri Farhan ya mata da ido yana kallon manyan cinyoyinta da suke waje.bata kula shi ba taja kujeran gaban dressing mirrow ta zauna.

Jawo wani lotion tayi da niyan shafawa taji ta rik'e mata hannu,d'ora kanshi yayi tsakinin wuyantay yana kallon fuskanta ta cikin madubin yace mata " bari in shafa miki tunda kinki jirana muyi wankan tare".

"Na yafe je kayi wankan zan shafa da kaina".tace mishi dan tasan ba 'a iya shafa man zai tsaya ba.

Ko sauraronta baiyi ba ya lakato man ya fara shafa mata cikin wani irin salo,yanayi yana kallon idonta.sunkuyar da kai kasa

Please Login or Register in order to submit comment